Showing 108001 words to 111000 words out of 115235 words
Chapter 37 - Halin Girma Hausa Novel Complete
saka su cikin tashin hankali, rige rigen lekawa suke kowa yana so yaga da wacce yazo, ba karamin kaduwa sukayi ba ganin shi cikin shigar saurata yayi masifar kyau, ya dauki wani siririn glass fari ya dora akan fuskar sa, murmushi ne kwance a fuskar tasa yana tafiya irin ta kasaita. Fada ya wuce kansa tsaye, bayan ya tabbatar da an gama tattara duk wasu masu fad'a aji na masarautar tasu, shi kanshi Bubu a cike da Mamaki yake musamman da irin hakan bata taba faruwa, ba ruwan Muhammad din da harkar cikin gidan balle har ya nemi ganawa da manyan fadar.
yadda ya shigo fadar kai tsaye ya saka wasu da yawa daga ciki yin mutuwar zaune, sakon shi ya iso musu tun kafin ya karaso. Wajen da ya saba zama ya samu ya zauna bayan ya kwashi gaisuwa. Su hudu suka shigo a tare hadda Kamal, suka samu waje suka zauna, daga nan bubu ya soma magana cikin nutsuwa da makasudin taruwar su a wajen.
"Mun taru ne domin danmu Muhammad yana da bukatar ganawa da manyan masarautar saboda muhimmiyar maganar da ta kawo shi, wadda muke kyautata zaton zata kawo cigaba a masarautar tamu baki daya."
Mikewa tsaye yayi ya sake gaisuwa sannan ya soma magana idon sa fes akan wambai da jama'ar sa.
"Tsawon lokaci na dauka ina bin diddigin mutuwar marigayi tsohon sarki. Duk da karancin shekarun da nake dashi a wanchan lokacin amma ban manta ba, ban manta fuskokin mutanen da sukayi sanadiyar mutuwar sa ba."
Hayaniya ce ta cika fadar kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa cikin tsananin mamakin maganganun Mohammad din wanda shi kansa Bubun be san da wannan maganar ba. Murmushi ne a kwance a fuskar sa yana karanta tashin hankali dake kwance a fuskokin su, tuni suka fara jikewa da gumi cikin yanayi na wahalarwa
" Wacce irin magana ce wannan yarima?"
Gyara tsaiwar sa yayi, ya sake kafe su da ido yace
"Ayi min afuwa, na dauko maganar daga sama, sai dai ba kai tsaye nazo da maganar ba sai dana tabbatar da ina da gamsashiyar shaida wanda zasu zama madafa a gareni."
Babu be tanka ba, ya dai zuba masa ido yana kallon sa yadda ya dake ya sake burgeshi, ya kuma ji a ransa lallai Muhammad ya shiryawa koma menene ,yadda ya dade yana nuna halin ko in kula da harkar gidan sai ya dauka be san komai ba, ashe yana sane har yana kokarin samun hujjar da zai tsayawa wan nasa da ya tabbatar da akwai wani bayanin a cikin labarin mutuwar tasa.
"Mecece hujjar taka Yarima? Ko zamu iya sanin ta?"
"Kwarai." Yace yana matsawa gaban Bubu, ya fito da envelope ya ajiye a gaban sa. Wannan ita ce hujjar da na rik'e nake kuma fatan abi duddugin abinda ya faru tun daga farko sannan ayi hukunci ga duk me hannu a ciki.
Wani irin zillo wambai yayi, ya kalli Kamal ya kafe shi da ido yana masa alama da ya kasa ganewa, gaba daya ma shi baya cikin nutsuwar sa sakamakon maganar mahaifin sa da Mohammad ya taso da ita haka ta sama ta ka.
Matsawa jikin wambai hakimi yayi, yayi masa magana cikin rada yace
"Nayi zaton mun riga mun samu shaidar da yake magana a kanta a wajen Kamal ko? Ko wata shaidar ce daban da bamu sani ba?"
"Yanzu ba lokacin maganar nan bace hakimi, kasan Kamal din be san flash din menene ba ya kawo mana, muyi fatan babu wata shaidar kuma."
Moh na ankare dasu, yana kuma lura da yanayin su, wato a tunanin su sun zata flash din da ya basu a matsayin Musaddik shi kadai ne shaidar sa, lallai suna wasa dashi.
Budewa Bubu envelope din akayi, flash guda biyu ne a ciki sai hoto da aka dauka amma yayi dishi-dishi alamun ya kwana biyu. Kallon hoton Bubu yayi sosai amma be gane komai ba. Projector aka kawo, aka jona Moh ya harde a wajen zaman sa yana fatan duk wanda yake cikin video din ya yanke jiki ya fadi a wajen saboda tashin hankali.
Jikin wambai ne ya soma kakkarwa lokacin da aka kunna video, shine yake magana da Kilishi,maganar sa radau a lokacin da yake ce mata in dai suna so su rufe sirrinsu sai dai su kawar da maimartaba, da fari batayi na'am da maganar tasa ba, amma yayi yadda zaiyi ya saka ta amince, daga nan sai hoton ya dauke sai kara shuuu da ta cika wajen, zare shi akayi aka saka dayan, wanda yafi tayar da hankalin mutane, tsohon sarki ne a kwance sanda suke kokarin kashe shi, babu irin magiyar da be musu ba, amma suka ki, suka kashe shi ta hanyar danna masa pillow har sai da ya daina numfashi gaba daya, akan dalili daya tal, dalilin ya gano zaluncin da suka dade suna masa shi da Kilishi, dalilin da su da kansu zasuyi wa fad'a bayani kafin yasa a tusa keyar su.
Salati ne ya cika a fadar, Bubu ya kawar da kansa yana jin dadi da Aji baya wajen, dalilin kenan da Muhammad din ya hanashi zuwa yace ya zauna a gida, dole idan yaga tashin hankalin nan ya rikice ga yanayi na girma.
Mikewa wambai yayi ya hau fad'a yana nuna Moh
"Karya yake yi wallahi karya yake, wannan shiryawa akayi amma karya ne, ni zaka wulakanta ko?"
Wasu fadawa ne majiya karfi suka taso, suka dankwafar dashi sannan suka ce
"Karya kake yi dan talakawa, Yarima yafi karfin ka jefe shi da wannan kalmar."
"Ku kyale shi." Yace kamar be damu ba, ya kalli Bubu da shima yake kallo ya yi masa murnushin kafin yace
"Za'a ji sauran bayanan da dalilin su na aikata wannan mummunan aikin daga wajen su."
"Me zuku ce game da wannan video da Yarima ya gabatar?"
Bubu yayi maganar yana dubansu dukkasu, kamar wanda aka soma a ruwan zafi haka sukayi tsamo tsamo, babu me magana a cikin su dan basu da bakin da zasu karyata shi, hawaye sosai Kamal yake bayan ya gama amincewa dasu ashe mayaudara ne. Juyar da fuskar sa Bubu yayi, yan sandan da Moh ya kira suka shigo, suka tattara su gaba daya suka fita dasu, jikin kowa yayi masifar sanyi da abinda ya faru, sannan sun yabawa kwazon Moh, sun kuma yarda da chanchantar sa na zama shugabansu, a take wasu suka fara maganar, Bubu na jinsu ya dinga murmushi yana kallon tilon dan nasa, cikin so da kauna, a yanzu ya kara tabbatar masa da shine zabi na kwarai da zai wa al'ummar sa, ya kuma gane dalilin sa na kin amsa tayin sa tsawon lokaci, ya kuma gane dalilin sa na zuwa a sauya dukkan tsarin sarautar gidan tasu.
Yana kallon yadda mutane suka dinga zuwa suna kwasar gaisuwa, fuskar sa a sake yake amsa musu, da haka ya samu ya zame ya fice daga fadar ya nufi bangaren Kilishi wanda yasan sakon sa ya riga ya iske ta, ko tana wanne hali yanzu? Zai je ya gani da idon sa kafin ya karasa wajen Ammin sa, yana son ganin Laila suyi maganar Samha bayan nan.
A duk abinda ya faru abu daya ne yayi masa ciwo, shine bayyananr asalin Kamal wanda ya kasance da ne ga wambai da Kilishi, ba dan tsohon sarkin bane, dalilin da ya saka su kashe shi kenan, saboda su binne gaskiya, su binne cin amanar da sukayi masa, duk don soyayyar su da mulki. Amma dole ba yadda ya iya, dole ne gaskiya tayi halin ta, ko da be fad'a a gaban kowa ba, yasan wadanda suke da hakkin su sani zasu sani din.
Da kwarin guiwar sa ya isa shashen nata, ya shiga kai tsaye ba tare da wani ta tsaida shi ba, ya kuma sameta a zaune tana ta kuka wiwi, kamar wadda aka ce wani nata ya mutu, Kamal na tsaye a kanta ransa na suya, be taba tunanin abinda suka aikata ba kenan.
Wani abu ne ya daki Moha, a karo na farko yaji tausayin su dukka, yasan rudin duniya da shaidan ne ya dibi Kilishi ta aikata abinda ta aikata din, shiyasa a kullum take shakkar sa, ta kasa aikata masa komai saboda yasan wani bangare na sirrinta, a tunaniin ta maganin ta ne ya ci shi da ya nuna halin ko in kula da harkar gidan, bata san yayi hakan bane domin ya samu gamsassun hujjoji, wanda zai karya duk wani mara gaskiya da tsoron Allah, ya kuma karbi kujerar da ta jima tana dakon jiran shi. Ya kuma amsa sunan Sarki Muhammad Ahmad Santuraki!
*****
Satin ta daya aka sallameta, suka tattaro suka dawo gida,kwana daya su Mamma ta kara itama ta tafi dama Mummy ta wuce tun a kwana uku da tayi a asibitin. Gidan ne duk taji yayi mata ba dadi, ta mike daga kwanciyar da tayi tunanin mutuwar Mahfuz na bijiro mata, tayi kuka sosai da ta samu labarin dalilin ta ne ya gamu da iftila'in, shiyasa aka ce ajali ko aina yake komai nisan wajen sai kaje ka tarar dashi.
Ranar da Yaya mahaifiyar sa tazo sai da kowa ya tausaya mata, dan yadda take magana kadai zaka gane yadda mutuwar ta dake ta, mutuwar danka saurayi matashi ya tasa, bata tafi ba har yanxu kuma kusan kullum sai tazo asibitin taga Iman din wadda take sake sakata jin nauyin ta har ma da shi kansa Muhammad din, kwata kwata sai ya rage zuwa asibitin dan baya son suna haduwa zuciyar sa karye wa take, daga baya ma sai ya shirya tafiya adamawa yana kuma chan har aka sallame ta be dawo ba sai waya da suke yi.
Sallama taji anayi daga falo, ta mike a hankali saboda rashin kwarin jikin da take fama dashi, ta bud'e kofar ta fito. Da dan saurin ta ta karasa ganin yan matan nan ne da suka taba zuwar mata. Su biyu ne yanzu suka gaishe ta ta amsa a sake tana zama kusa da daya da take kan three seater tace
"Ashe zaku zo?"
"Eh Fulani ce tace muzo mu tayaki zama kafin Ya Moha ya dawo."
"Kai amma naji dadi, sannun ku da zuwa ya mutanen gidan?"
"Lafiya lou, ya jikin? Allah ya kara sauki."
"Amin ya Allah, Nagode."
Sai suka shiga hira suna bata labarin gidan su da wasu yan uwansu da duk sai a dubiyar ta sassansu. Ummimi ce ta shigo ta gaida su ta gyara wajen dining sannan ta fita, ta dawo dauke da manyan warmers ta jera a wajen tsaf sannan ta sake fita.
Su kadai suka ci abincin dan bata da appetite har lokacin, tea kawai ta sake sha tace zata dan kwanta, ta haye sama ta barsu suna kallo da danne dannen waya.
Tayi nisa sosai a cikin baccin ta wayar ta dake jikin socket ta shiga kara, kamar ba zata tashi ba, saboda yadda baccin ya soma dadi, kiran ne ya kara shigowa bayan wanchan ya katse, ta tashi da k'yar ta dauko wayar ta daga
"Hajiya kinyi bakuwa."
"Wacece?"
Mike mata wayar yayi
"Nice Iman..."
"Zeenat, sannu da zuwa bashi wayar."
"Sister dina ce, ku kyale ta."
Ta katse kiran ta mike gaba daya ta shiga toilet ta gyara jikinta ta sauya pad sannan ta sakko. Da fara'a take kallon Zeenat din dake zaune tana karewa falon kallo cikin yanayi me ban tausayi, bata san Iman din ta fito ba har sai da ta dan dafa ta, ta kira sunan ta
"Sannu da zuwa."
Tace tana murmushi
"Yawwa, bacci kike kamar na tashe ki."
"Wallahi kinsan har yanzu ban gama samun sauki gaba daya ba, ya gida yasu Mama?"
"Lafiya lou wallahi."
" Ya jikin?"
" Da sauki Alhamdulillah."
" Allah ya kara sauki, ya bada na aike me albarka."
" Amin."
"Sai kika ganni kawai."
"Umm..."
Tace tana mikewa tayi hanyar kitchen, taje ta fad'a musu abinda zasu kawo sannan ta dawo tace ta taso, suka shiga wani daki a k'asan, suna shiga ta cire mayafin jikin ta da dankwalin ta ajiye a gefe.
Sallama Ummimi dake dauke da tray da abinci da ruwa tayi ta ajiye ta gaishe ta sannan ta ja musu kofar.
"Bismillah ga abinci."
"Toh..." Ta jawo kayan ta bud'e, yawun ta ya cinke ta zauna dirshan ta shiga dibar abincin nan babu kakkautawa, Iman na kallon ta bata ce mata komai ba, sai data ci ta koshi tasha juice da ruwa sannan ta mike kafarta sanyin AC na ratsa ta sosai.
"Magana ce ta kawo ni, dan Allah taimako na zakiyi Iman."
"Me ya faru?"
"Dan Allah yallaban zaki ma magana ya kira Bashir dan Allah ya zo ya maida ni, wallahi na gaji so nake na koma dakin mijina."
"Kina nufin dama kina gida?"
"Tun yaushe? Tun sunan Anty Bilki fa."
"Kai wallahi ban sani ba, matsala kuka samu?"
"Uhmm.."
"Ina jinki."
"Shi da Mama ne, bayan yazo mu tafi mama tace ba in da zani taje ta same shi a waje bansan me ta gaggayawa masa ba, shikenan ya kyale ni."
"Abba kuma ya sani?"
"Ya sani, har magana yayi min wallahi, amma Bashir din yaki zuwa kemaimai, har gidansu Mama tasa Ya Habib ya kaini amma sam yaki, a dah ban damu ba, amma wallahi yanzu nayi karatun ta natsu, ko dan dan tahalikin nan da yake cikina."
"Kema kinyi wauta, ita rayuwar nan baki daya da kika gani kowa hakuri yake da yadda tazo masa, shi kuma arziki lokaci ne."
" Haka ne, na ga aya ai, son zuciya bacin ta, daga kin gaskiya aka ce sai bata, kema sam ban kyauta miki ba abubuwan da nayi miki a baya, ko yanzu kinga sakayya, Allah ya baki miji me sonki na nuna sa'a, gashi ya hada duk wasu qualities."
" Ni ban rik'e ki ba ko da din ma."
" Um um Iman, ni dai kiyi hakuri dan Allah."
" Na hakura toh."
" Nagode Allah ya saka da alkhairi, dan Allah ki taimaka ki masa maganar nasan shi idan shi ya kirashi ba zai taba ki ba."
" Bari kiga." Tace tana tashi, taje ta dauko wayar ta dawo, ta zauna sannan ta kirashi
" Bari naji idan yana free sai muyi maganar kawai."
"Yawwa dan Allah."
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikisalam Baby, na zata bacci kike ai, shiyasa ban kiraki ba ina jira ki tashi."
"Na tashi ai, ban jima ina baccin ba. "
" Kar dai yaran chan ne suka hanaki baccin da shegen surutun su. "
" A ah, Zeenat ce tazo. "
" Zeenat? " Yace cikin son tuno sunan,
" Zeenat fa. "
" Oh wai matar Bashir? "
" Kai ko? "
" Allah na manta ta, lallai ta kyauta, duba ki tazo. "
" Eh. "
" Ok yayi, ya gidan ya missing dina? "
" Ina nan inayi, amma kad'an. "
" Kiji tsoron Allah, ni nasan kinyi missing dina kamar yadda nayi "
" Umm.. haka dai kace. "
" Haka ne ma, idan na dawo zan gasgata kai na ai."
" Can't wait." Ta saka dariya
" Toh me yake faruwa? Babu wata matsala dai ko?"
" Eh toh, dama Zeenat ce tazo, shine tayi min magana akan tana so dan Allah ka kira Bashir kace yazo ya dauke ta, Ashe tun ranar da mukaje suna gida bata koma ba, shi kuma be zo ba."
" Toh... Ina Zeenat din?"
" Gata."
" Bata wayar."
" Gashi." Ta mika mata,
" Ina wuni?"
" Lafiya lou, ya gida?"
" Lafiya lou."
" Menene ya faru?"
" Dama..." Ta bashi labarin da ta bawa Iman bata rage komai ba, murnushin yayi yana daga zaune, a kalla yasan zuwa yanzu ta dawo hayyacin ta, ta kuma yi nadama tun daga yadda ta kwantar da kai tana masa magana, ya kuma tabbatar da uwar ta ma tayi laushi tubus, dama abinda yake so kenan, su russuna wa Iman dinsa har su nemi alfarma a wajen ta.
"Shikenan ki koma gidan zaizo anjima."
"Nagode Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara girma..."
"Amin."
" Hello..."
" Baby zan kiraki anjima, ki kula da kanki kinji? Bye."
" Bye." Ta kashe wayar
" Yace naje gida zai zo." Ta fad'a cike da murna
" Masha ALLAH hakan yayi."
" Bari kiga na tafi, Mama bata san nan nayo ba asibiti nace mata zani, Nagode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci."
" Amin."
Kofa ta rakota tare da bata kaya masu yawa a cikin leda tace ta gaida gida, ta kuma sa aka fitar da ita har in da zata samu abun hawa.
*Ayi min afuwa jiya nayi kuskure wajen cewa Iman tayi sallah bayan tayi bari, ban ma lura da aika-aikar da nayi ba sai daga baya, ban yi editing page din ba sam ina ta sauri na tura. Ayi hakuri kuskure ne
_ZAFAFA2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/25/22, 18:10 - Buhainat: *Hafsat Rano*
_Halin Girma_
*43*
***kiran Bashir din yayi bayan sun gama wayar, be same shi ba, kila baya kusa. Ajiye wayar yayi ya maida hankali sa wajen Aji da suke magana kafin shigowar wayar tata.
"Me ma kake cewa?"
"Ungo nace." Yayi masa dakuwa
Dariya ya saka har da buga kafa
"Dan tsohon nan akwai riciki, toh ba zan waya da matata ba, naga kaima idan yar tsohuwar chan ta kiraka cikin rawar jiki kake zuwa."
"Gwara ni ai, kai daga gani mijin tace ne ai, sai uban rawar kafa sai kace kanka farau a aure."
Sake fashewa yayi da dariya cikin son kular da Ajin yace
" Naga alama dai kana taya yar tsohuwar chan kishi ne."
" Oho dai, matanmu na dah sun fi naku na yanzu komai da komai."
" Habawa, banda tawa matar dai, tawa daya tamkar da dubu ce."
" Toh Baban masoyan duk duniya, kaine ma ramiyo yake ko wa?"
" Romeo ake cewa, ai nama fishi."
" Kaji dashi, Allah yasa dai kar ayi lusarin sarki wanda mace zata dinga jujjuya shi, ya kasa aiwatar da komai."
" Ai tunda kuka dage sai kun bani mulkin nan haka zaku hakura, ana cikin zaman fada zaku ga nayi fit na fice toh Itace tayi kira."
Mikewa Aji yayi cikin kuluwa yace
" Ka bada maza wallahi, kaga tafiya ta ba zan iya kin wannan shirmen naka ba mara kan gado."
" A gaida min tsohuwar sarauniyar taka, zan shiga anjima naci tuwon wajen yar tsohuwa."
Murmushi kawai