Showing 87001 words to 90000 words out of 115235 words
Chapter 30 - Halin Girma Hausa Novel Complete
hankali anan? Tana jin sanda suka sauke Musaddik yana masa sai da safe ya amsa da k'yar, suka ja motar sai gida.
Motar na gama tsayawa ya balle murfin motar ya fice ko bi ta kanta be ba, jiki a sanyaye ta fito itama, ta bi bayan sa cike da mamakin sa. Bata same shi a falo ba, kai tsaye ta wuce bedroom dan rage kayan jikin ta da suka dame ta, baya dakin kamar yadda tayi tunani, kuma be shigo ba har ta gama sauya kayan ta fito falon ta zauna tana bud'e wayarta. Ta jima a zaune a wajen, sannan ya fito sanye da kajaren wando babu riga a jikin sa, wuceta yayi ya dauki abu a cikin wata drawer a falon ya koma dayan dakin da ya fito. Ya sake dadewa sosai dan har tayi tunanin ta bishi ta gani sai gashi ya fito ya doro gajeriyar jallabiya a jikin sa, yana kamshin turaren sa na hugo boss.
"Abincin nan za'a kawo maka ko achan zaka ci?" Ta tambaye shi bayan ya zauna
"No ba zan ci ba."
Sak'alo tayi tana duban sa, yaki ko kallon sashen da take sai ma fito da waya da yayi yana daddanawa. Tashi tayi ta bar falon ta koma daki cikin rashin jin dadin abinda yayi mata, wannan ai wulakanci ne, me tayi haka? Ji tayi hawaye na kokarin zubo mata, kokarin maida shi tayi tana daga fuskar ta sama.
Tana tashi kiran Takawa na shigowa wayar sa, ya daga yana mikewa tsaye
"Barka da wannan lokacin Takawa."
"Barkan ka dai, kuna lafiya ya iyali?"
"Alhamdulillah wallahi."
"Toh madallah, alfarma akayi min akan tafiyar da zakuyi, dalilin da ya saka sunanka ya fito saboda ana bukatar jajirtattun mutane kamar kai, kuma kai zaka jagoranci tafiyar, sannan akwai alkwarin karin girma akan ka bayan an dawo, dan haka nake so ka ajiye komai ka tafi, Allah ya baku sa'a ku dawo lafiya."
" Amma..." Yace a firgice
"A'ah fa! Bana so naji komai Mohd, na jima ina neman alfarma irin wannan akan ka, komai idan har baka so toh fa an barshi, waya kawai zan, wannan kuwa takanas ya kira ni mukayi magana na kuma bashi tabbacin zaka je, toh kayi hakuri kaje."
" Shikenan Nagode Allah ya kara girma, zanyi duk yadda akace."
" Yawwa, Allah ya taimaka ya baku sa'a, Allah yayi albarka."
" Amin."
Ya amsa a dunkule zuciyar sa na wani irin suya, wato sai DG ya riga shi samun Takawa akan maganar ya kuma nemi alfarma yasan Takawa dole ya amsa masa, me ma ya saka shi wai kin tsayawa yaga Takawan a dazu ya tafi? Ai da duk haka bata faru ba. Wani abu me ya tokare masa makoshi, ya jefar da wayar a saman kujerar yana barin falon da sauri zuwa daki.
Tana zaune a gefen gadon tana tunani ya shigo, ya wuce wajen da jakar sa take ajiye ya ciro flash din, ya dauki system ya sake barin dakin. Hada su yayi da dayan na wajen Iman, ya kunna kowanne yayi copying dinsa akan system din, sannan ya saka su a envelope ya mayar jakar. Tafiyar da zai yi Itace zata basu kafa wanda har za'a iya samun matsala be samu dukka bayanan da yake son samu ba, yanzu dai zai damka wa Musaddik flash din guda biyu, ya ajiye a wajen sa dan sune manyan evidence dinsa idan ya tashi yin abinda ya jima yana shiryawa.
Wayar sa da ya jefar dazu ya dauko ya kira Musaddik din, sukayi magana sannan ya ajiye yana dafe kansa. Zai iya jure komai amma banda abu biyu, iyayen sa da matarsa, idan har aka samu matsala zai dauki matakin da ba zai ma kowa dadi ba.
Tun tana jiran shigowar sa har ta gaji ta hakura, ta kwanta tana matsar kwalla, bata ga abin fushi ba sam, bata kuma san ta yadda zata fara bashi hakuri ba, ba wai dan tana ganin ai bata yi laifi ba me yasa zata bashi hakuri, sai dai ta rasa fuskar da zata iya bashi hakurin.
Chan cikin dare ta farka bayan bacci ya dauke ta da k'yar, ta ganshi a gefen gadon yana bacci hankalin sa kwance, ya riga ya saba mata tun farko tare suke kwanciya, cikin bargo daya amma sai gashi yau, akan abinda bata da laifi akai,yana fushi da ita. Baccin ne ya kaurace mata gaba daya, ta dinga tunanin wai dama haka auren yake kenan? Sai wajen asuba sannan ta samu baccin ya kwanshe ta bayan ta sha kuka ta gode Allah.
A kanta ya tsaya yana kare mata kallo, yadda ta kwanta sai ta bashi tausayi sosai, be san me ya hau kansa jiya ba, amma ba wai haushin ta yake ji ba, bayan ma wayar da yayi da Takawa zai iya cewa ya manta abinda ya faru, tunanin abinda zai faru idan baya nan shi yafi daga masa hankali har ya hanashi zuwa ya kwanta sai dare sosai.
Hannu ya kai ya shafi gefen fuskar ta, ta bud'e idon tana salati a hankali, ganin shi da tayi a tsaye akanta yana mata murmushi ya sakata tashi da dan sauri tana gyara jikin ta
"Good morning Baby,."
Yace kamar babu wani abu da ya faru, bata amsa ba, sai zuro kafarta da tayi ta sakko, ta wuce shi zuwa toilet dan ta makara daga ganin yadda haske ya cika dakin. Hijab ya ciro mata ya shinfid'a mata abun sallah, ya zauna yana jiran fitowar ta. Ko da ta fito bata kalle shi ba, ta tada sallar ta, da ta idar ma sai kawai ta kwanta a wajen tana janyo hijab din ta rufe fuskar ta dashi. Tasowa yayi tsam yayi zaman dirshan a gaban ta, ya janye hijab din yana dagota, hawayen da ya gani a saman fuskar ta yayi mugun bashi mamaki
"Innalillah, kuka? Don't tell me kuka kikayi tayi the whole night..."
"Ya Salam...Look at your eyes, I'm very sorry, ki yafe min dan Allah."
Bayan hannun ta tasa tana share hawayen da suka ki tsayawa, ita kanta bata san na menene ba, kawai tasan she's weak, tana jin wani irin weakness a tattare da ita, she can't take fushin sa a gareta, he's so nice to her ko yaya yayi fushi zai bata wahala sosai. Rarrashin ta ya dinga yi da kalamai masu taushi, har sai da ya tabbatar da kukan ya tsaya, sannan ya taimaka mata suka bar kasan suka koma saman gado.
"Dole zanyi fushi, shi zaman aure dama zo mu zauna ne zo mu saba, I can equally make mistake, ina da kishi sosai Fatima, ba kuma wai dan naji a raina wai kin kula shi bane, son da nake miki ya saka, please ki kula sosai. "
" I'm so too. " Tace bayan ta amsa masa da toh.
" Baki komai ba ai, nasan wacece matata, kawai dai... "
" Me?"
" Ashe dai ana so na... "
Duka ta kai masa ya goce
" Allah da gaske, naji dadi sosai, zan biya bashin duk tears din da akayi min asarar su, amma kafin nan, zanyi tafiya, karshen week din nan. "
Da sauri ta kalle shi, sai ya kama hannun ta ya fara yi mata bayani yadda zata fahimta
" Kinsan yanayin aikin mu dama yadda yake, ni dinma dai kawai dai kawai dai, amma wannan karon ba zan iya kin zuwa ba, dole ne dan akwai Takawa a cikin maganar. "
" Dadewa zakayi? "
" Uhmm... Ban dai sani ba, amma in sha Allah ba zamu dade yadda kike tunani ba. "
" Allah ya kaimu, ya bada abinda aka je nema. "
" Amin ya Allah, an koma strike, akwai driver da zai dinga kaiki ya jiraki ya dawo dake, hakan nasan zai debe miki kewa, da ina tunanin ko a chanja school, amma kuma tunda har kun kai 300lv gwara ki karasa ko? ".
" Eh hakan yayi. "
" Yawwa my wife, yi min murmushi na gani toh."
Murmushi tayi, sukayi dariya a tare suka bar komai a bayan su, suka fita domin karya kumallo.
***Zaune yake a irin kujerar nan me jujjuyawa, kansa sanye da cowboy hat, sai bakin glasses da ya rufe kusan rabin fuskar, jujjuya yake akai yana busa sigari, daga bayan sa yara ne biyu majiya karfi, kowannen su ka kalla zaka tabbatar da zai iya aikata koma wanne irin aiki ne. Knocking akayi, ya daga kansa yana duban su, kafin ya gid'a kan nasa alamar eh, wanda yake ta bangaren kofar ne yaje ya bud'e yana matsawa baya, suka shigo su biyu mace da namiji, kujerun gaban sa suka zauna, ya cigaba da busa sigarin sa ba tare da yayi musu magana ba, sai da suka dau wani yan dakiku a wajen sannan ya jefar da sigarin ya saka kafa ya murje ta.
"Kun samo abinda ya kamata ku samo din?"
"Za'a samo dai, komai yana tafiya according to plan, gashi zai yi tafiya."
" Tafiya? " Yace yana kallon su
" Eh zaiyi tafiya karshen satin nan. "
" Wonderful, opportunity me kyau, lallai lokaci yayi da kowa zai samu abinda yake so. "
" Menene next? "
" Tafiyar sa, let me know when he's gone."
" Me zakayi?"
" Matsala ta ce wannan, bani da matsala da cikin gidan ku, abu biyu ne suka hada mu zuwa uku, a wannan gabar kowa has to play his on part dakansa. "
"Shikenan. "
Zaro wata sigarin yayi ya kunna mata wuta, suka mike suka fita, ya bi su da kallo kafin yayi murmushi. Moh zai yi tasting abinda yaji a lokacin da ya raba shi da abinda yafi so, shi abu daya ya raba shi dashi, amma shi zai raba shi da kusan abubuwa uku zuwa hudu masu matukar muhimmanci a rayuwar sa, ko zai mutu sai ya dauki fansa akansa, sai ya dandana masa bakin cikin da be taba dandana irin sa ba.
Mikewa yayi bayan ya gama zukar sigarin, ya tura kofar wani daki, ya shiga bayan ya kunne flashlight din wayar sa, saboda tsananin duhun da dakin yake dashi. A gaban mutumin da yake kwance magashiyan ya durkusa, yana tallafo kansa, sannan ya haske shi da wayar sa da ta kusan kashe masa ido
"Ka kusa samu yancin ka, bayan na tabbatar da na samu duk abinda nake so a wajen shi wanda yafi ma hatta iyayen ka, kayi hakuri aiki ne ya biyo ta kanka, kai kadai ne kafi kowa kusanci dashi, dan haka dole ne kaima ya sha wahala!"
"Gwara kayi ta ajiye ni a bakin dakin nan, akan kayi wani abu akan sa, wallahi wallahi kaji na rantse ma ko? Kuda idan ka bari ya taba wani abu na jikin sa, sai ya karar da duk dangin ku!"
Dariya ya kece da ita mahaukaciyar dariya, ya saki kansa da ya tallafo ya bige da simintin wajen
" Idan yana takama da mulki ne, ko kuma khakin da yake jikin sa, toh bari kaji, babu abinda ya isa yayi min dan nayi nisan da bazaka taba tunani ba, k'asar nan tayi lalacewar da su kansu masu tsaron lafiyar taku ba tsira sukayi a wajen mu ba, shi karamin kwaro ne."
Soma takawa yayi har ya kai kofa, sannan ya juyo yace
" Daga yau zuwa gobe amfanin ka zai kare, zabi na ne, na barka ka tafi, ko kuma na kare rayuwar ka gaba daya Musaddik Izzeeddin!
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/14/22, 19:05 - Buhainat: Halin Girma
35
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�?
Da wuri Musaddik ya iso gidan, dan basu samu haduwa ba tun ranar da sukayi waya sai yau din da zai tafi, ya riga ya shirya shi kadai yake jira, yana zuwa ya dauko envelope din ya damka masa a hannun sa
"Ka kula sosai dan Allah, idan har lokacin da ya kamata yayi, ban dawo ba zan fada maka sai ka damka su a hannun Aji! Dan Allah kar kayi kuskure, ka kula sosai, kai kadai na yarda dakai da wannan amanar."
"In Sha Allah." Yace yana rik'e envelope din sosai.
Ciki ya koma, ya barshi a wajen ya tarar ta gama hada masa jakar sa waje daya, tana gaban jakar ta zabga tagumi har ga Allah bata son tafiyar tasa, amma kuma dole zata hakura saukin ta daya fitar da zatayi school, ga ma'aikata birjik an kara karo wasu ma, gate din ma kuma cike yake da jami'an tsaro da ba dan haka ba, ba zata iya zama a wannan tafkeken gidan ba.
Tashi tayi ganin ya shigo,ya kalle ta ya kalli jakar sai kawai ya rungume ta
"Zanyi missing dinki sosai, take care of yourself for me dan Allah, idan kina bukatar wani abu, reach out to me, idan baki sameni ba, Musaddik yana nan, nayi miki saving number dinshi kema zan bashi naki."
" Ai babu ma abinda zan nema, akwai komai."
"In case dai."
" Owk tam, nagode. "
" Yawwa, muje ki rakani. " Ya rik'e hannun ta suka fito har wajen mota, ta tsaya daga gefe bayan ya shiga ya zauna, yayi mata murmushin karfafa guiwa itama ta maida masa zuciyar ta na rauni, daga mata hannu yayi har suka fice daga gidan gaba daya.
***Abinda ya faru lokacin da Bashir yazo daukar Zeenat bayan tafiyar Iman, suna barin kofar gidan yana zuwa, adaidaita sahu yazo dan ya maida machine din wa maishi, aikawa yayi a kirata, dan babu waya a hannun ta, Mama na jin sakon kiran ta zira mayafi taje wa Zeenat din tana zuwa, ta je ta same shi a tsaye yana jira ta fito suna magana da me napep din. Be yi mamakin ganin Maman ba, dan dama yasan ba za'a yi komai ta sauki ba, gaishe ta yayi taki amsawa, sai ma cewa da tayi tana bud'e hannun ta
"Bani takardar yata."
"Ban gane ba Mama?"
"Eh ina nufin ka sauwake mata kaddareren auren ka dan ba zata koma ba ku karasa kashe ta kai da tsohuwar matar ka."
" Amma Mama Zeenat tana so na, nima Ina son ta, kiyi hakuri dai ta fito mu tafi."
"Wanne so? Bayan yaudarar da kayi har kana tunanin tana son ka?"
"Toh ni dai nasan auren soyayya mukayi da ita, kiyi hakuri ki bimu da addu'a kawai."
"Ba zan hakurin ba, Malam takardar 'yata kawai nake so ba dogon surutu ba."
"Ba zan iya sakin ta ba gaskiya, kiyi hakuri kawai."
Sai ya juya ya haye napep din,da sauri ta bishi tana kiran sa, me napep yaja suka bar kofar gidan. Tana juyowa da nufin komawa gida sai ga Abba a tsaye a bayanta, ya harde hannayen sa yana kallon ta ransa a matukar bace, bacin rai da be taba yin irin sa ba tun da aka fara hayaniyar auren Zeenatun, tsoro ne ya shige ta, dan yadda taga bacin rai a fuskar sa zai iya aikata komai.
"Dan Girman Allah..."
Daga mata hannu yayi
"Babu abinda zaki ce min, bana son naji komai!
Jikin ta ne ya hau rawa, yayi ciki ta bishi tana son yi masa bayani, ba zai tsaya jin komai ba, ba kuma zai dauki maganar da sauki ba wannan karon, tayi abinda ba zai mata uzuri ba. A zafafe ya shiga falon yana k'wala kiran zeenatu, ta tashi jikin ta na rawa har tana yar da dan kwalin kanta da yake hannun ta,
"Me kike yi har yanzu baki tafi ba."
"Uhm.. uhm.. dama..."
"Karya kike yi, munafuka!"
"Minti biyar kachal na baki, ki fice ki koma gidan mijin ki, na fad'a miki!"
Be jira ya sake jin ta bakin ta ba, ba kuma zai saurari magiyar da Mama take masa akan dalilin da ya saka tayi abinda tayi ba, yayi gaba kawai ya shige dakin sa ya rufo.
Kuka Zeenat ta fashe dashi, da gaske bata son komawa gidan Bashir, ya zatayi yanzu? Gashi taga wani irin fushi a fuskar Abban da bata taba gani ba,dama mama so tayi bayan ta kori Bashir din idan Abban yazo tace shi Bashir din ne yace Zeenat din ta zauna a gida zai yi tafiya ya dawo, daga nan sai suyi ta matsa mata har ya sake ta, shikenan Abban ba zai zargi komai ba, amma sai gashi komai ya lalace tun ba'a kai ko ina ba.
"Kina da number Bashir ko?"
Girgiza kai tayi
"Dan ubanki baki haddace number sa ba? Yanzu ya kike so muyi? Dole ya dawo ya dauki ki ku tafi kafin nasan abinda zanyi akai."
"Mama ni ba zan koma ba."
"Aikuwa sai kin koma, baki ga fuskar babanku ba? So kike yace na tafi gida shikenan ki rasa wanda zai tsaya miki? Tashi maza ki kira bashir ga wyata kice ya dawo, idan yaso sai mu san abinda zamuyi."
Kuka ta cigaba da rerawa a hankali, ta karbi wayar ta saka number tasa ta kira, tayi ta ringing amma be daga ba, ta cigaba da jera masa kira amma babu alamun zai dauka. Rasa yadda zasuyi sukayi, har goma saura gashi bata san gidan ba balle idan tafiya zatayi da kanta ta gane. Suna nan a falon ya fito, ya kalle su sannan ya fice gaba daya.
***Bayan tafiyar sa sai taji gidan yayi mata girma da fadi, ta kwanta a saman kujerar falon tayi lamo tana jin cikin ta na juyawa sama-sama. Bacci ne ya dauke ta a wajen bata tashi farkawa ba sai da rana tayi. Sallah ta fara yi taci abinci sannan ta zauna ta dauko littafan ta na islamiya ta shiga duba su, tana muraji'ar na baya, tana so ta cigaba da karatun ta ko ita da kanta ne ta dinga karawa kanta, zatayi amfani da damar duk da sun koma boko amma ba zata kyale na islamiyya ba, akwai wasu littattafi da take son koya wanda dole sai dai ta samu manyan malamai su koya mata, amma bata san yadda zatayi ba. Tana nan zaune yayi mata text message, tayi masa reply sannan ta cigaba da abinda take har zuwa la'asar, gaba daya sai taji ta rasa ma me zatayi, sai kawai ta zagaya baya wajen ma'aikatan gidan ta same su suna hira, suka tashi da sauri suna tambayar ta abinda take so, murmushi kawai cike da mamakin yadda suke girmama ta take