Showing 3001 words to 6000 words out of 115235 words
abinda zaki samu kenan ko da ita mahaifiyar taki ce."
"Haka ne." Tace a kasalance
"Yawwa ki dinga dan daurewa kina shiga cikin yan uwanki kinji? Zaman shirun da kike babu dadi."
"In sha Allah zan gyara."
"Yawwa... Haka nake son ji."
"Ya batun yajin aikin nan kuwa? Kun dauko karatu tiryan tiryan yajin aiki ya tsaidaku da tuni wata maganar ake ba wannan ba."
"Wallahi shiru ba labari, muna dai ta addu'a Allah ya sa a daidaita."
"K'asar nan kenan ai, dan karatun ma yanzu nema ake a hana dan talaka yin sa."
"Wallahi."
" Allah yayi mana maganin abinda yafi karfin mu."
" Amin ya Allah!"
" Shiyasa nace duk ku fidda mazaje kawai da zarar wadanchan sun tafi kuma azo ayi naku zaman haka nan ba zai yiwu ba."
Shiru tayi gabanta ya fadi, bata son taji ana maganar auren su, gashi kuma taga alamar ba za'a dauki lokaci ba za'a ce su fidda mazaje, ya zatayi da ranta? Da ganin suna makaranta yasa maganar ta lafa amma yanzu yajin aikin da aka tafi da ba'a san ranar dawowa ba ya saka iyayen nasu yanke shawarar suma su aurar dasu kawai sai karasa karatun a dakin su.
Tashi tayi tayi ma Gajin sallama ganin lokaci yayi, taje tayi alwala ta saka Hijab dinta ta fito, a falo ta tarar da Mama tayi saurin tsugunnawa ta gaishe ta
" Mama barka da gida."
" Saura idan an tashi ki tsaya shiririta a hanya ko ki tsaya gidan Gaji karki zo kiyi abinda ya dace, jiya kam kinci darajar babanku yana nan."
"In sha Allah." Tace sannan ta mike ta fice Maman ta rakata da harara.
****Sati biyu tsakani aka fara bikin gidan nasu, duk yadda taso gujewa wasu abubuwan amma Maryam bata barta ba, komai idan za'a yi sai ta sakata a ciki, haka kunshi da gyaran kai tare suka je da wata kawar Maryam din.
Alhamis suka fara bikin, a compound din gidan Anty Mabruka sukayi bridal shower iya su da kawayen su, juma'ah akayi kamu asabar aka daura aure hade da yini, lahadi aka kai kowacce gidan ta.
Ranar litinin suka tashi gidan da sauran bakin da basu riga sun tafi ba wanda yawanci dangin Gaji ne, a babban kitchen din gidan suka hadu aka hada breakfast Masa da miyar taushe, har rana tayi sosai basu kammala ba hakan ya sake haifar mata da wata irin gajiya bayan wadda take fama da ita, tasan halin Mama sarai idan ta makale taki fitowa ayi aikin da ita duk da akwai masu yi din amma dolen ta ne ta fito, duk da hakan ba karamin taimaka mata yayi ba wajen gogewa da kalolin girke-girke mabanbanta. Sannan uwa uba girkin mutane da yawa wanda ba kowa bane ya iya.
Da saurin ta, ta karasa dakin su, ta kwanta a gefen gadon saboda wani irin sanyi da take ji alamun zazzabi ne ke neman rafke ta, rawar sanyi ta fara hakoranta suka shiga haduwa waje daya, ta saka hannu da k'yar ta jawo bargon Zeenat din ta lulluba.
Shigowar ta kenan ta tsaya daga kofar
"Kut! Lallai ma." Tace tana karasawa ciki, ta fuzge bargon da karfi
"Dan Allah zee ki kyale ni bani da lafiya." Tace muryar ta chan ciki. Shiru Zeenat din tayi tana kallon ta, sai kuma ta sakar mata bargon ta juya ta fice daga dakin. Har dare zazzabin be sake ta ba, babu kuma wanda yazo neman ta. Tayi tunanin Zeenat din zata fad'a wa Maman ne duk da bata saka rai ba, amma jin shirun ya tabbatar mata da ta fad'a mata dan da ba haka ba da tuni Maman ta turo neman ta akan wani aikin.
Wajajen Tara Zeenat ta dawo dakin, ta kalle ta a zaune saman abun sallah ta kudundune, juyawa tayi ta fita ta dawo da paracetamol a hannun ta da ruwa ta mika mata. Karba tayi da sauri tayi mata godiya, bata amsa ba ta sake fita sai gata ta dawo da katifar Iman din, ta shinfid'a mata sannan ta dauko bargon ta, ta dora mata akai ta haye gadon ta kwanta ta rufe idon ta. Sosai Iman taji dadi a ranta, ko ba komai tayi mata abinda bata taba ba, tashi tayi da k'yar ta lallaba ta fita kitchen ta hado tea sannan ta dawo ta sha da k'yar ta sake komawa ta kwanta ta kudundune.
Kwanan ta uku a haka, har ta soma samun karfin jikinta, Mama ta shigo sau daya ta bata anti-malaria shima dan tasan Abban zai iya tambaya ne, shima da tasan zai shigo ya duba ta ne, tana jin sanda take ce masa sun je asibiti ma kuma jikin da sauki.
***Karamin daki ne da yafi kama da shago, katifa ce karama irin ta yan boarding school sai jakar kayan sa a gefe, bayan haka babu komai a dakin sai wani dogon mudubi dake rataye jikin bangon dakin.
Tsaye yake a gaban mudubin yana duba fuskar sa dake cike da kasumba ko ina har baka iya ganin komai na fuskar tasa sosai, kansa rufe yake da katuwar hular sanyi, ya nannade wuyan sa da abu, kafar sa da hannun sa duk rufe suke cikin hular sanyi, idan ka cire fuskar sa da itama kasumbar bata wani bari a ganta sosai, babu wani abu na jikin sa dake a bud'e. Kayan jikin sa a wanke suke tsaf, sai dai sun tsufa sosai, har da wata yar bula a jikin hannun rigar.
A ko da yaushe yakan tsaya ne a daidai hanyar da take hucewa idan ta dawo daga islamiyya, amma kuma kwana biyu ya rabu da ganin ta, shiyasa ya yanke shawarar zuwa gida duk da yasan ba tsarar sa bace amma zai gwada sa'ar sa.
*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
1/2/22, 22:47 - Buhainat: *HALIN GIRMA*
Hafsat Rano
3
****
Tsaye yayi jikin gate din gidan yana kare masa kallo, tunanin ta yadda zai fara shiga yake musamman da ba sanin sunan ta yayi ba, ya dai saka mata suna da zuciyar sa kuma be taba yunkurin tsaidata balle yaji sunan ta ba.
Lekowa maigadin gidan yayi, ganin mutum a tsaye yasa shi fitowa gaba daya
"Sannu." Yace masa yana kokarin daidaita muryar sa
"Yawwa sannu, wa kake nema?" Maigadin ya tambaye shi yana kare masa kallon cikin rashin sani.
Nan fa ake yinta, shiru yayi kamar me nazari shi kuma maigadin ya kafe shi da ido yana son jin abinda ya kawo shi.
"Am... Amm nazo wajen..."
"Malam Iliya." Zeenat dake fitowa ta kirashi tana leko wa.
"Na'am ranki ya dade!"
"Siyo min kati na 500 kayi sauri dan Allah."
"Yanzu kuwa, ga wani bako nan bansan wajen wa yazo ba dai kin tambaye shi."
Yayi gaba, kallon sa tayi tun daga sama har kasa a wulakanci ta yatsine baki tace
"Wa kake nema kai kuma Malam?"
"Yar uwarki nake nema dan Allah, wata me zuwa islamiya kasan layin nan doguwa haka fara."
"Waye kai a wajen ta?"
Kallon cikin ido yayi mata, ta ja tsaki tana juya fuskar ta
"Ban fiye son kallo ba Malam, ka shigo ciki bari na tura maka ita dama ai sai dai ita din..."
Gaba tayi tana cigaba da sababi
"A kaf gidan nan wa zai kwaso mutum irin wannman dan Allah! Ji shi kamar wani mahaukaci."
Sai ta kwashe da dariya tana sake daga kafa.
A kwance ta tarar da Iman tana danna wayar ta da ba kasafai ta cika wani amfani da ita ba, yanzun ma wani labari ne yaja hankalin ta a Facebook take karantawa.
" Kina da babban bako a waje da galleliyar ranar nan."
" Waye?"
" Idan kika je idon ki zai gane miki shi."
" Owk."
Tace tana tashi zaune, har yanzu bata gama dawowa daidai ba amma haka ta karfafa jikinta tayi ayyukan ta. Hijab ta saka madaidaici akan doguwar rigar jikinta ta fito. Daga chan hanyar gate ta hange shi a tsaye ya rataye hannayen sa a bayan sa, kansa a kasa yana wasa da kafar sa.
Dogo ne na ajin farko, jikin sa ko ina a murje babu alamun rama ko kad'an, yanayin shigar sa bata dace da tsarin zubin halittar sa ba, kafin ta karasa ta gama ayyana shi a ranta. Da sallama ta isa, ya dago da sauri a lokaci daya kwayar idon sa ta sauka a cikin ta ta, gabanta ne yayi masifar faduwa, tayi saurin janye idon ta, ta russuna kad'an tace
"Ina wuni?" Lumshe idon sa yayi ya bud'e, fuskar sa dake cike da kasumba ta dan yi fadi alamun farin ciki, ya tattaro dukkan nutsuwa da jaruntar sa yayi gyaran murya yace
"Kina lafiya?"
"Alhamdulillah." Tace a gajarce ta matsa wajen wasu kujerun roba guda biyu ta dauko daya ta kawo masa.
"Bismillah zauna kana ta tsaiwa."
Hannun sa ya dora a saman kujerar ta kalli hannun yayi saurin janye shi ya zauna sannan yace
"Kefa?"
Wani dan tudu a wajen ta nuna masa da hannu, ta zauna akai tana jin duk ta takura ganin yadda yake bin ta da kallo da wasu irin idanun sa da suka sake shiga ciki sosai.
"Na same ki lafiya? Ya gida yasu Mama da yan uwa?"
"Lafiya lou Alhamdulillah."
"Ban gane waye ba amma?"
"Me sonki ne, me kaunar ki da son duk wani farin cikin ki, yan kwanakin nan da na dauka banga wucewar ki ba, sun zame min kwanaki mafiya muni a rayuwa ta. Na kan zauna a duk yini ina dakon wucewarki, ban taba yunkurin yi miki magana ba, sai dai zuciya ta, ta gaza dauka har sai dana biyo bayanki, ina fatan ban takura miki ba?"
Girgiza kai tayi tana jin wani bawai, wai ita ake karantawa wannan kalaman, idan har taji daidai wato ya dade yana bibiyar ta, bata ma sani ba.
" Kinyi shiru!" Yace yana gyara zaman sa
Shirun ta sake yi dan bata san me zata ce masa ba.
" Nasan dama karambani ne irin nawa, ban kai ajin ko da me wanke miki takalmi bane, kiyi hakuri idan nayi miki shishigi a rayuwar ki."
" A ah wallahi, ba haka bane ba, a kalla mutumin da yace yana son ka ai yafi makiyinka, nagode sosai da soyayyar ka gareni." Tace da sauri sannan tayi murmushi, ji yayi kamar zuciyar sa zata fito daga kirjin sa, ya danne sosai ya maida mata murnushin
"Nagode Nuryyy... Nagode sosai."
Shiru ya biyo baya, ta dinga wasa da gefen Hijab dinta shi kuma yana satar kallon ta. Nutsuwarta tafi komai tafiya dashi.
"Bari na wuce."
Da sauri ta mike kamar me jiran kad'an,
"Ka gaida gida." Tace tana saurin yin gaba
"Ko zan samu number waya dan Allah?"
Tsayawa tayi ta mika masa hannu, ya shafa aljihun sa dukka
"Kinga garin sauri na manta wayar a daki, amma zan rik'e fad'a min."
"Ok ." Tace ta karanto masa,
" Nagode sunana Muhammad."
" Fatima, ka gaida gida."
Ta juya ta barshi a tsaye a wajen. Sake maimaita sunan Fatiman yayi, ya saki murmushi a hankali sannan ya juya ya fice daga gidan.
***A zaune a falo ta tarar da Mama na waya, zata wuce ta tsaida ta da hannu ta cigaba da wayar ta
" Ba za dai ka bar maganar nan ba ko Khalil? Toh shikenan sai kazo din dai ma sake tattaunata, idan yaso ko a dangi ne sai ka duba sosai ba za'a rasa ba ai."
Amsa ya bata daga bangaren sa, ta ja tsaki tace
" Matsalata da kai kafiya wallahi toh sai anjima, sai kazo din."
Ta kashe wayar ta dangwarar da ita a gefen ta
" Na rasa shegen taurin kai irin na Khalil wallahi, sam baya kaunar ya ganni cikin farin ciki, mtsw."
Ta sake jan tsaki a karo na ba adadi.
" Daga ina kike?"ta jeho mata tambayar bayan ta riga ta san inda take.
" Wani ne yazo dama."
" Waye shi?"
" Bansan shi ba nima, wai a bayan layi yake."
" Toh kina jina? Idan zaki yiwa kanki kiyamullaili ki rik'e shi hannu bibiyu toh, idan kuma kika yi wasarairai da shi shima ya gudu kamar sauran, sai ki zauna muyi ta jerawa a gidan nan,tunda dai bakin hali ya hana samarin zama kowa yazo sai ya tafi."
Bata dago ba, bata kuma ce kala ba, tana jin Maman tana kuma ajiye kowacce magana a mazaunin da ya dace, sai da ta gama yi mata cin fuskar sanann tace
" Khalil zai zo gobe, babu ruwanki dashi da shiga harkar sa, ko falo bana so naga kina kaiwa da komowa har ya tafi, zan fi so ki tattara ki koma wajen Gaji da zama aikin ma na yafe miki, idan ya gama kwanakin ya tafi shikenan, bana son daukar magana dan shi ba kunya magana yake ji ba, kinji dai na gaya miki."
" In sha Allah."
" Jeki."
Tashi tayi ta bita da kallo ranta na tafasa, da gaske take kishi da ita dukda bata zauna da mahaifiyar ta ba, amma duk sanda ta kalle ta sai ta tuno abinda ya faru.
****A guje suka taso ganin ya fito, ya nufi wajen da jerin motocin ke fake suna jiran sa, ransa a bace yake da kiran amma bashi da ikon kin amsawa, dole ya ajiye shirin sa a gefe ya kirawo su domin ba zai taba yarda da shigar masa shirin sa ba. Shiyasa su kansu basu da yakini ko masaniyar komai, dan ya tabbatar da zasu taimaka wajen lalata masa shirin sa. Dan su din basu da ikon kansu sai abinda aka gindaya musu.
Bud'e masa bayan motar daya daga ciki yayi, ya russuna kad'an sannan yace
"We are very sorry sir!"
Be tanka masa ba, ya shige cikin motar ya jingina bayan sa da kujerar ya lumshe idon sa.
"Oga Main house zamu?" Yayi tambayar yana tada motar
"Lamido Crescent!" Yace yana sake rufe idon sa.
Chan suka wuce direct, suna isa ya fito ya shige ciki, tun daga falo ya fara wurgi da kayan jikin sa, ya rage daga shi sai boxer da farar singlet, kallon kansa yayi a jikin tangamemen mudubin dake tsaye kikam a falon, ya juya ya sake juyawa sannan ya wuce zuwa cikin bedroom din sa.
Wanka ya fara yi a gurguje sannan ya fito ya shirya cikin shigar babbar riga da jamfa da wando farare kal, sau cikin sa ya jawo ya ajiye a gefe ya fara saka farar socks a ciki sannan ya saka ya fito rik'e da babbar rigar a hannu.
Zama yayi sannan ya danna remote din kofar, da sauri suka shigo su biyu, ya mik'a wa daya babbar rigar, karba yayi ya taimaka masa ya saka sannan ya dauki abubuwan da yasan zai bukata ya fita dasu.
"Ka zauna anan zan kiraka da zarar na sauka."
Yace da dayan sannan ya tashi ya fice cikin takun da yafi kama dana jinin sarauta.
Motoci biyu ne suka fita daga gidan, shi yana cikin daya su kuma suna bin sa a daya har zuwa airport.
*Muhammad Ahmad Santuraki*
*(*Captain Moh*)*
*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
1/2/22, 22:47 - Buhainat: *HALIN GIRMA*
*_Hafsat Rano_*
4
****
*Adamawa-Yola*
Tun daga yanayin manyan motocin da suka cika harabar ya tabbatar da bakin dake cike da fadar, yana da yakini dalilin kiran Bubun kenan a kalla zasu ganshi sannan ayi masa maganar da tafi komai kona masa rai, maganar mulki da yake dukkan kokarin sa wajen guje mata.
Be jira an bud'e masa ba, ya balle murfin motar ya fito bayan hango Aji da yayi yana nufar ciki tare da tawagar sa, da saurin sa ya cimmusu,domin ya samu su shiga a tare, ko ya gujewa idanun Bubun daga zuwan nasa. Yasan a cike yake taf dashi
"Aji!" Ya kira shi da sunan da yake kiran sa
"Hoo d'an nema, na dauka ba zaka zo ba ai."
" Na isa naki amsa kiran ka ko na Bubu? Ai ban isa ba."
" Dadin baki, idan har da gaske ne ai sai ka amsa kiran da muka jima munayi maka ko?"
Sosa keya yayi ba tare da yace komai ba, suka karasa ciki. Da ido Bubu ya kafe shi tun shigowar sa, tabbas ya rame fiye da ganin da yayi masa kwanaki da suka wuce, sannan akwai wani yanayi a tattare dashi da be gamsu ba, a gabansa ya tare, ya kwashi gaisuwa ya cigaba da bin sa da idon ba tare da shi ya yarda sun hada ido ba, gefen Ajin ya samu ya rabe yana sake hade fuskar sa tamau, murmushi kawai Bubu yayi ganin da gaske Muhammad yake har yau yana nan akan bakan sa, ya rasa dalilin da ya saka shi baya son mulki ko kad'an, tamkar ba dan naga da ba, kamar wanda aka juyawa tunani kwata kwata akai,