Showing 18001 words to 21000 words out of 115235 words

Chapter 7 - Halin Girma Hausa Novel Complete

tambaya ya saraki"jawahir tayi caraf ta gaya mata,sai data tabbatar ta aikawa jawahir saqon harara sannan ta maida dubanta ga mony da nufun yin nata bayanin
"momy wai ba....."wani kallo momyn ta aika mata,sannan ta daga hannunta kawai ba tare da tabi takan qorafin da takeso. sako.mata ba tace
"bata kudinta"fuska ta bata
"momy...."
"nace ki bata kudinta ha'an...?"ta fada da dan zafi zafi yanzun a muryarta,fuskar najwa a cunkuse,ta zaro kudin ta jefawa jawahir,ya fada saman cinyarta,bata damu ba ta dauki kudinta taci gaba da irgawa,momyn ta kalleta
"ajjiye kudin nan kizo kitchen ki hadama daddynku drink"
"to momy"ta amsa mata tana miqewa da kudinta a hannu tabi bayanta,yayin da najwa ta bita da harara,tana jin kamar ta shaqeta,saita gyara glass din fuskarta,ta kuma gyara zaman qaton littafin dake ken cinyarta taci gaba da dubawa,can qasan ranta abubuwa da yawa na mata yawo,inda tana da qarfin iko da sai ta canza abubuwa da dama cikin gidan nasu,abubuwa masu tarin yawa da basuyi rayuwarta yadda takeso ba,basu zauna kuma a gurbi da muhallin da takeson ganinsu ba.


*_9:30 am_*


*_DARMANAWA HOUSING ESTATE_*

*_PROFESSOR RASHID USMAN AZARE RESIDENT_*


Daya ne daga cikin jerin qawatattun gidaje dake gine cikin unguwar,,wanda suka qawatu aka kuma ginasu bisa basira da kuma kyakkyawan tsari.


Gini ne na alfarma mai cike da qayatarwa da ban sha'awa,kamar yadda akasan ire iren gidajen masu sukuni suke da kuma unguwaninsu.


A hankali momy ta daga kanta,fuskarta na fidda wani irin murmushi mai haske tunda ta jiyo sautin muryarsa,tun gabanin ma ya iso inda suke din,yayin da ta tsaida dukkan abinda takeyi,ciki harda cin abincinta,da kuma hira da take da 'yammatan dake gefanta su uku,najwa jawahir da kuma ramla da take 'yar ruqo a wajenta.


Dukkaninsu sunsan meye ta baiwa hankalinta haka gaba daya,ba wacce bata saba da ganin tarin kulawa da qauna daga gareta ba zuwa ga samir,wadda ta banbamta da ta kowanne da dake cikin gidan.


Kallo daya professor yayi mata yaci gaba da cin abincinsa a nutse,don shi din ma hakan ba baqon al'amari bane a wajensa,illa dai ya kada kansa sannan ya maida hankalinsa ga farantin gabansa.


Cikin sakanni da basu kai goma ba ya bayyana cikin falon dab dasu,matashin saurayi muhammad samir me laqabin saraki,ma'abocin tsaho,wanda murjewar jikinsa ta hana bayyanuwar tsayin da Allah yayi masa yadda za'a fahimta,ya mallaki kalar fatar da hausawa suke kira da wankan tarwada amma irin wankan tarwadan nan dake da haske,taqi kadan zai dada ka kirayeshi da farar fata,matsakaicin kyau gareshi,saidai abubuwa guda biyu sun taru sun qarawa siffarsa kyau da cikar haiba KWARJINI da yake dashi,da kuma wasu lumsassun idanuwa masu kama da na me jin bacci.


Yana da sanyin murya,irin sanyin da bai hana bayyanar cikar mazantakarsa gami da jarumtarsa ba,sam ba miskili bane,kamar yadda wasu mutane da yawa suke masa kallon haka,abubuwa ne guda biyu suka sanya suke masa wannan kallon,baya shiga sabgar da bata shafeshi ba,bashi da shishshigi sam,hakanan bai fiya magana kan abinda yasan yana da qarancin muhimmanci,koma kwata kwata bashi da muhimmancin,yana da kamewa da wata irin nutsuwa mai jan hankali,yana da zurfin ciki a yawancin lokuta,komai nasa bisa tsari da dacewa yake tafiya,shi yasa wasu ke ganin abune mai wuyar gaske iya zama dashi,abunda basu sani ba shine,zama dashi din wani abune mai dadi ga duk wanda ya soma mu'amala dashi.


Akwai boyayyun halayyensa da ba kowanne ya sanshi dasu ba,ciki kuwa harda makusantansa,yana da tausayi yana da taimako,a wasu abubuwan ba zaka taba tsammanin cewa ya fito daga gidan girma da arziqi irin wannan ba,rayuwa sassauqa da yakan gudanar....saidai,matuqar kazo lokacin da yake kan tsininsa,zaka dauka baida kirki ko kadan.


Muhammad samir,da namiji guda daya tilo da Allah ya mallakawa professor rashid usman azare,wanda tarin banbamce babancen halaye da zabi na rayuwa yaso ya zama babban shinge tsakaninsa da mahaifinsa da samun dukkan wata yarda da qauna tashi.


"welcome son.....na tsammaci yau ba zaka fita ba?,naji shurun yayi yawa,duk da na kira wayarka taqi shiga....saina zabi na barka ba tare dana aika ba,wala'alla kana bacci ne kada a katse maka shi" hajiya jidda wadda auke kira da mommy ta fada,dukkan kulawarta tana tare da samir din,fuskarta na fidda wani kalar murmushi dake nuna farincikin dake tattare da ita na ganin fitowar samir din,kamar yaune lokaci na farko data fara ganinsa,ko kuma wani gari yayi tafiya mai nisan zango ya dawo a yau din.


Washewa fuskarsa tayi da wani murmushi mai aji,ya soma qoqarin jan kujera daya don yiwa kansa mazauni sannan ya amsa mata
"A'ah anna....bani da wani abu da zan aiwatar ne da safen....shi yasa na zabi na huta kafin na fita yau,don jiya ban samu zama yadda naso ba" ya qarashe maganar yana duqawa zuwa qasa gefan mahaifinsa,muryarsa cike da tsantsar ladabi ya furta
"Barka da asuba daddy" kallo daya yayi masa ya maida kansa ga abincinsa yana amsa masa da
"Ka tashi lafiya?"
"Lafiya alhmdlh" sai ya maida dubansa ga mommy wato hajiya jidda
"Barka da asuba mommy"
"Barka kadai yarona....da fatan ka tashi lafiya"
"lafiya qalau alhdmdlh"
"To ma sha Allah" ta amsa masa fuskarta na nuna jin dadin samunsa lafiya da tayi kamar kullum,saita miqe da kanta ta fara bude dukkan wani kwano dake saman teburin sanda qannensa ke gaisheshi daya bayan daya yana amsa musu,kamar yadda ta saba tanayi kullum kwanan duniya matuqar ya halarci wajen cin abinci,zata bude masa dukka ya zaba abinda yakeson ci,don wani lokaci ma abinda ya zaba yana so shi za'a dafa kowa da kowa,koda ba zabinka kenan ba,tun suna yiwa mommy mita da qorafi har ya zame musu jiki.
"Me zakaci a ciki samir?,Allah yasa akwai wanda ya dace da ra'ayinka" mommy ta fada tana murmushi kamar kullum,wanda baka rabata dashi saman fuskarta,sai a sannan alhj mukhtar yayi magana tun fitowar samir din,idanuwansa saman fuskar mommy,wani abu na yawo saman zuciyarsa,wani abu mai nauyin daya wuce a aunashi a mizani
"Ki kalleshi mana da kyau,ba yau ko jiya ko shekaran jiya aka haifeshi ba,amma kullum kina kallonshi ne kamar ranar nan da aka miqo miki shi cikin tsumman goyo,a qa'ida ya isa aure,a kuma qa'idance kamata yayi ace a gaban matarsa yake" kanta ta langabe tana duban professor
"Haba daddy.....kai kake ma samir kallon yayi girma har haka,ni kam a wajena har yanzu kamar yaron goye nake kallonsa.....bugu da qari ma daddy idan ba'a kula da samir ba...wa zamu kula dashi?,karka manta shi kadai Allah ya bamu...."
"Abbaaaa"sautin muryar jawahir tayi kutse cikin maganar mummy,sautin daya fito a narke,kamar me shirin sakin kuka,waiwayawa suka dukka suna kallonta,sai daddyn ya daga hannayensa duka biyun kafin yace
"You see.....su kuma daughters dina ki kaisu ina?" Murmushi ya saki,wani abu na lilo can qasan ranta da zuciyarta
"Dole dukkaninsu subi bayan samir a wajena" a nutse tsaf daddyn ya waiwaya ya dubi samir din sosai kuma kai tsaye,duk da idanun samir din na kai kawo ne tsakanin yan uwansa,fuskarsa tana fitar da wani murmushi me sanyi mai kuma cike da nutsuwa
"Gwara da kika ce a wajenki,ta ina yaronkin zai kama qafar yarana?,yaron naki da ba jin magana yake ba,wanda ya sarayar da alqiblarsa,babu wanda ya gane har yau inda yasa gaba" samir ya gama fahimtar qorafinsa na jiya da yaketa gujewa shi yakeson sokowa a yau din,saiya dan sunkui da kansa,kana ya daga kan nasa,yana muradun rushe wannan maganar,don baida sha'awar ci gaba da yinta,don haka cikin girmamawa yace da ita
"Kome akayi yau din zanci mommy,ki zauna ki huta....zan zuba da kaina,ina sauri ne ma,jiya akwai taron da zanyi da ma'aikata,ban samu zama ba nasa aka maidashi yau"ya fada yana miqa hannu zai hada tea.


jawahir ce ta miqe da hanzari ya dauka cup din ta soma hada masa,mummy tadan kalleta saita dauke kanta
"yi a hankali sarkin rawar kai,kada ki zuba masa a jiki"mummyn ta fadi sanda jawahir ke aje masa tea din,murmushi yayi ya dauka yana.kaiwa bakinsa,shi yasa yakeson autar tasu,sosai take nuna kumawa kan dukkan wani abu daya shefeshi,ba kamar 'yar uwarta ba,wadda har yanzu bai fuskanci inda ta sanya gaba ba,shegen sin jiki gayunbanza,izgili da yiwa.mutane kallon banza hadi da rashi iya magana dukka najwa ta hadasu,abu daya da yasa bata iya wani kyakkyawan abu a gabansa ko a kansa shine,baya daukar raini,kamar yadda baya raina kowa,tafi kowa sanin ainihin wayeshi,wannan shine ya ke mata waigi a kansa.


miqewa prof yayi yana yagar tissue
"idan ka dawo yau din bayan sallar isha'i,ka sameni zamuyi magana dakai"
"ok daddy"ya fada da muryarsa mai dadi,sannan yaci gaba da kurbar tea din a nutse.


cup din ya ajjiye bayan ya gama amsa wata waya,mummy ta dubeshi
"bakaci komai bafa samir?"
"mommy,am late"
"a maka packaging ka tafi dashi mana,ya zaka fita aiki babu cikakken abinci a cikinka"
"ba komai mommy,zan nemi wani abun naci idan na samu break"
"a'ah..,.najwa......maza,shiga kitchen ki cewa baraka ta baki warmers qanana"fuska tadan bata
"Mommy.....yace a barshi fa"idanu ta fitar mata gaba daya
"ni kuma nace ki dauko....."tuni ta miqe ma kafin mummyn ta qarasa bayani,saboda wani kallo da samir din ya jefeta dashi,harta soma takawa tajishi yana fadin
"dawo ki zauna,jawahir.....jeki dauko,guda daya ma is ok"taf tsoro ya cika cikinta,saboda ba kasafai yake bi takanta ba,tana tsoron irin wannan kallon nasa,saita ci gaba da tafiya ta miqe zuwa kitchen din,wata tsawa ya watsa.mata wadda ta sanyata tsaiwa,ta kuma kasa juyowa,har jawahir tazo ta wuceta da saurinta kuwa kamar yadda ya umarceta


bata motsa ba har sai dataji fitarsa yana cewa idan an zuba jawahir din ta miqa masa yana cikin mota.


koda ta koma harara Mommy ta bita da ita,sannan ta rufeta da fada,tana kallon fuskar jawahir,da alama taji dadin yadda mummyn ta balbaleta da fadan,sai tayi sakato,mamaki fal ranta,me yasa mummy ke mata fada da zafi har haka?,bata tanka ba har jawahir ta fice daga parlour din,saita dauki jakarta dake gefe wanda dama shirin makaranta tayi,kawai ta fice a falon.


yana daga zaune a driver seat ta buda gidan baya ta sanya warmer din sannan ta rufe,saita zagayo inda yake zaune din,fuskarta da murmushi
"a dawo lafya yaya"
"Allah yasa"ya amsa yana shirin rufe murfin motar,saidai jawahir din bata matsa ba tana tsaye still a wajen,kansa ya daga bayan ya sauke glass din motar yana dubanta
"ya akayi auta?"murmushi ta sakeyi
"kayi haquri yaya da abinda ya najwa keyi....ni kaina bansan meya canza ba"qawataccen murmushin gefan baki ya saki
"karki damu, she's still my sister.....ina tunanin tana da damuwa,but we will talk later"kaita gyada kawai kana taja baya,ya tada motar a nutse,ya qarasa bakin gate ya danna horn,idanunsa saman fuskar mai gadinsu da yaketa marmashe gyada yana zubawa cikin jiqaqqen garin kwaki,ya taso da hanzari ya durfafi qofar zai budeta,sai samir ya yafitoshi da hannu,don haka yabar bude qofar ya iskoshi da sauri ya iso bakin window inda samir ke zaune
"Allah ya taimaki saraki"
"an tashi lpy baba"
"lafiya qalau dana"
"abinda aka dafa ne yau baba bai maka ba,na ganka da garinka harda gyada?"samir ya tambayeshi yana dan murmushi,murmushin shima yayi,a ladabce yace
"ko daya mai gida,yau dai bamu samu abun karin bane"fuskarsa cike taf da mamaki bayan yadan yamutsata yace
"kamar yaya?,kune baku da sha'awar ci?"da sauri ya girgiza kai
"ko daya,Allah ya taimakeka wazaiqi abinci irin na gidan professor?,inajin dai yau da gobe ne irin ta bahaushe,wani lokaci ku samu,wani lokacin kuma saidai kowa ya siya abinda yake dashi"baice komai ba saiya duba agogon hannunsa,bashi da lokaci da cikin gidan zai koma,bai zaci wasu cikin gida dake rayuwa tare dasu ba'a basu abinci ba,saiya bude aljihun gaban motarsa ya aciro yan dubu dubu guda biyu ya miqa masa
"gashi,ka ajjiye wancan ka siya wani abun me dumi kaci"hannu bibbiyu yasa ya amsa kudin yana zabga masa godiya,sannan ya tafi qofar ya dage masa gate din,yaja motar da dan hanzari ya fice.
1/7/22, 08:18 - Buhainat: Halin Girma
    9

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb



***
Yana jin sanda motar ta tsaya, ya juyo da sauri ya kalle shi, hankalin sa na kan wayar sa yana dannawa, fuskar sa a hade tsaf babu alamun wasa ko kadan, tsoro ne ya sake shigar Khalil din sosai, yaji kamar yayi ta kurma ihu yana neman taimako, amma kuma ya san babu wanda zai taimaka masa musamman idan aka zo aka ga wanda yake tare dasu.
  Ji yayi an murda handle din bangaren sa, yayi saurin matsowa sai gashi a tsakiyar motar, daf da Moh, wani banzan kallo ya watsa masa da ya sakashi saurin komawa inda yake zaune.

"Come ou!" Wani murdadden soja yace matsa bayan kofar ta gama budewa, idanu ya soma rabawa tsakanin Moh da sojan fuskar sa ta nuna matukar tashin hankalin da ya shiga

"I said come out!" Ya daka masa tsawa da ta saka shi saurin fitowa

"Dan Allah Oga kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da rashin hankali, duk abinda na farfada ba wai har zuciya ta bane wallahi."

Ya hau magiya yana kallon Moh da yayi kamar baya wajen, damtsen hannun sa sojan ya kama ya shiga jan sa har zuwa wata kofa in da ya hangi sojoji sun fi su ashirin suna tsalle tsalle a wajen.

"Oga dan Allah ka bawa oganku hakuri Dan Allah!"

"Kasan waye oga kuwa?"

Da sauri ya girgiza kansa

"Ban sani ba wallahi, rashin sani ya jawo nayi masa abinda nayi amsa amma dan Allah na tuba yayi hakuri."

Dariya sojan ya saka sosai

" Baka da hankali amma, ka zo har nan wajen kayi tunanin zamu kyale ka, ka tafi free? Nah sai mun dan sassamaka yadda gobe ba zaka kara ba. "

" Dan Allah nace fa? Ka tayani bawa ogan hakuri. "

" Naka wasa ne. "

Yayi gaba yana rik'e dashi, yanayin rikon da yayi masa da yanayin jikin Khalil din zai baka dariya sosai, dama bashi da wani jiki sosai gashi kuma a hannun manyan maza, wani daki ya kaishi sannan ya sake shi yana masa dariyar mugunta

"Zaka kwashi kashin ka hannu yau, wallahi Oga zai iya sawa a batar da kai a k'asar nan, kasan waye kuwa? Tab."

Jawo masa kofar yayi ya rufe ta har da key yana kwasar dariya.
  Chan karshen dakin yaje ya tsugunna yana jin dana sanin barin zancen da yayi, dama a maida baya da ya goge duk abun da yace ma Muhammad din cikin rashin sani. Ji yayi cikin sa na kara alamar ya lalace, ya tabbatar bala'in tsoro da firgicin da ya shiga ne ya saka cikin nasa lalacewa. Mikewa yayi da sauri ya hau zagaye a dakin yana maimaita

"Innalillah wa inna ilaihi rajiun."

Ji yayi ana murda key din dakin, ya tsaya yana kallon kofar cikin tsoro. Captain Moh ne ya shigo sojoji biyu na biye dashi a bayan sa, daya rik'e da kujera yazo ya ajiye masa ya zauna yana wa Khalil murmush

"Alhaji Khalil barka da warhaka."

"Dan Allah dan Allah kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da yarinta wallahi amma ba zan sake ba."

"Haba Khalil, so soon haka? Ka sani ko sojan gona ne ni, kasan fa talaka da samun wuri."

"Wallahi ni dai ba zan sake ba, kayi min rai, mahaifiyta da ni ta dogara, dan Allah."

"Calm down magana zamuyi, ka nutsu ka saurare ni, warning ne me hade da dokoki, ina fatan zaka bud'e kunnuwan ka kaji ni sosai."

"Ina ji wallahi."

"Babu kai babu abinda ya zama mallaki na, Ina nufin Fatima, ko a hanya ka hadu karka taba nuna ka santa balle har magana ta hada ku, a da nayi niyyar barka ka gwada sa'ar ka akanta, amma kuma a yanzu na gama yanke wa, baka kai na nemi abu tare da kai ba, dan haka ko son ta zai kashe ka sai dai ka hakura... "

" Na biyu, a yau ba sai gobe ba zaka wuce in da ka fito, ba tare da ka bud'e bakin ka kace wa kowa komai ba, ina nufin, bakin ka ya zama kanin kafar ka, kar naji zancen a wajen kowa ciki har da ita yayarta ka da bata tsoron Allah. "

" Last but not the list ka koma bakin aikin ka, ka rik'e mutuncin ka sannan bakai ba wulakanta kowa. "

" Duk abinda ka fad'a wallahi zanyi, nayi alkawari, ni dai kar ka raba ni da mahaifiyata wallahi bata da kowa sai ni. "

" I'm done with you, gashi nan take him back, ku tabbatar ya bar Kano kafin karfe shida na yamma. "

Juyawa yayi cikin wani irin taku ya fice daga wajen, yana fita sukayi kansa

" Ai wallahi ba zaka shigo nan a banza ka fita bamu ci ladan ka ba. "

Wani soja yace yana kai masa rankwashi.

" Tashi kayi frog jump. " Dayan ya daka masa tsawa yana zaro belt dinsa. Da sauri ya hau yi yana hada zufa su kuma suna tuntsura dariya, sai da suka gajiyar dashi sosai sannan suka fito dashi suka sashi a mota suka maidashi har kofar gidan suka ajiye sannan suka tafi.

***Abba na zaune yaji text message ya shigo wayar sa, tunanin sa ma ko alert ne ya bud'e sai yaga sako daga bakuwar number da be sani ba, bud'e message din yayi ya soma karantawa

_" Dr. barka da warhaka, ya aiki? Allah ya taimaka. Dama wata magana nake son yi akan fatima, ina rokon alfarmar daka saka ido sosai akan abinda yake faruwa a cikin gidan, in sha Allah zaka gano wani abu da ya dade yana faruwa ba tare da sanin ka ba. Sai anjima a huta lafiya. "_
   maimaita karanta sakon ya dinga yi yana kokarin daidaita tunanin sa waje guda, waye ko wace wannan? Me sakon yake nufi? Me ya faru da Fatima din? Duk wadannan tambayoyin ne suka shiga yi masa yawo aka, be san me yasa ba, kawai sai yaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login