Showing 39001 words to 42000 words out of 173829 words

Chapter 14 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1113

kuma babu amsa"

Shiru tadanyi tana qoqarin daidaita muryarta.

"Dad am sorry, baqi nayi shine nayi attending dinsu" tafada muryarta still na Dan rawa rawa.


"Ok, amma yanakejin muryarki wata kala? Are you okay?"

"Y..yes dad, kaina ke Dan ciwo"

"Subhanalillah, kinsha drugs, ko nazo nakaiki asibiti?"

"No dad, am okay, nasha Dana kwanta zanji sauqi"

"Ok Kije ki kwanta, zan bugo later akwai maganar dazamuyi"

"Alright dad"




Datse kiran tayi tana Sakin ajiyar zuciya.

Haryanzu takasa yarda da abinda yafaru dazu, wai yaushe ma yadawo gidan bata saniba?

Allah kadai yasan tun yaushe yake zaune yana qaremata kallo.
Ashe shiyasa takejin kamar ana kallonta.

*idiot* tafada cikin jin haushi da takaici.

Babu abinda yafi qonamata rai kamar kallon rainin daya bits dashi.

Tsaki taja ta tashi tana tattare plates din dining din don abincin ma kwata kwata yafita akanta.

Saida ta dauraye plates din data 6ata ta gyare saman sannan ta haye da niyyar ita da zama qasa kuma har abada saidai ta sauko tayi abinda zatayi ta haye sama.










Kwance take rigingine akan gado fuskarta na kallon ceiling saidai idanunta a lumshe suke amma ba barci take ba don duk abinda Beebah ke fadi duk a kunnenta ne.

Saida takai aya sannan ta numfasa ta kalli suzyn dake kwance tundazu kamar mai barci.

"Toyaya kikaji tsarin?"

Kamar bazata motsaba sai can ta saki ajiyar zuciya tana bude qananun idanunta akan fuskar Beebah sannan ta motsa la66anta dakyar tace

"Kenan duk wannan shirin da kike lissafowa duk inanan ina sagale da baki ina ganin su a tare za'ayi shi? You don't get me Beebah, banaso, vanason inwayi gari da tunanin my man tareda kowacce irin tsinnana, I want him for me, me alone, bazan iya jira harna tsawon lokacin da kike cewaba, na tabbata izuwa lokacin zuciya ta tariga da ta tarwatse"

Zama Beebah tayi bakin gadon kusada ita tana cewa

"Suzy, wannan itace kadai mafita, ya kike magana kamar batareda ke mukaje wajen ta ba, kamar bakiga yanayinta ba, yarinyar nan yar barikice, tasan takan barikanci, kalamanta ma sun nuna hakan, kawai zuru ne zaici zuru, ta hanyar data biyomana tanan muma zamu bida ita, ashraf nakine ke kadai, kisa wannan a ranki" tafada cikin qarfafa gwiwa.

Haka taita lallaminta harta samu nasarar bida ita hanyar datakeso, bata bartaba har saida taga ta dorata akan abinda sukeson cimmawa.






Yau kwana biyu da faruwar wannan al'amari tsakanin Ashraf da saudart.

Basu sake haduwaba don kowa yasake Jan baya da Dan uwanshi fiyeda da.

Ita tabar dadewa a qasa shi kuma yabar dawowa dawuri.

Don haryanzu kowanne cike yake da takaicin abinda yafaru ranar.




"Dad, I really need to get back to my work, I can't take it anymore, kullum ni kadai acikin gida kamar mayya? Nidai zanyi resuming on Monday, nagaji ai wannan deal din maku be shafi aikinaba, so am resuming" tafada cikin yanayin jin haushi don jitake kwata kwata ta tsani zaman gidan.


"Ban qi ta takiba shalele, it's normal idan kikayi resuming amma baki tunanin yakamata kiyi advancing din profession dinki? A matsayinki na Matar A.A be kamata ace kina zuwa bakery ba da sunan aiki, it's embarrassing"

Jim tayi tana sauraron daddy tana jin maganganun nashi wani bambarakwai musanmman *Matar A.A* daya ambata.

"I don't get you dad" tafada cikin Rashin fahimta.

Gyara zama dad yayi a bangarenshi yana murmushin samun nasara.

"Abinda nake nufi shine, tunda kinada bakery kuma kina iya gudanar dashi ko kina nan ko bakya nan, why not kisamu wani aikin daban da takardunki?"


Jimm tayi tana sauraron daddyn lokaci daya kuma kwakwalwarta na nazari akan maganarshi.

Katsemata tunani yayi da cewa

"Kinga zakifi samun kudi, ga na bakery ga salary, nima nan am trying my best, kinga saimu hadu mu hada qarfi wajen hada kudin mijinki mu biya a warware komai kowama ya huta"


Shiru tayi na yan daqiqu tana nazari akan shawarar Dad.

Eh hakane, wannan shawara ce, dukda bata cika son aikin office ba tana iya daurewa tayi kodan fita daga wannan vanzar deal din marar kan gado.

"Ya kikace shalele?"

"Deal, saidai ta ina zan fara?"

"Bakida matsala sweetheart, ba ganiba? Daddy zaiyi komai wa shalelenshi" yafada cikin fara'a.

"Awnn! Thanks dad, I love you"

"Love you more"







Tunda suka gama wayar yaketa aikin zabga murmushi.

"A.A, yanzu lokacina ne" yafada yana shafa gemunshi.








"Ummy please.. Zan kawota, I promised" yafada kamar zaiyi kuka


"Ni dalla tashi min, haka kake cewa kullum, sai yaushe zaka kawota din? Nida diyata ace sai an Mani rowarta? To wlh kaji na rantse gobe gobenan nakeson ganinta kaji ba gayamaka" tafada tana tureshi daga kan cinyarta.


Qin daga mata cinyar yayi, data tureshi saiya koma.

Itakau baby na daga can gefe akan kujera tana satar kallonsu tana ta6e baki.

"Wai bazaka tashi ba saika karya ni?" Inji Ummy tana qara tureshi

"Ummy please mana, wai me nayi ne?" Yafada yana qara komawa

"Mekayi? I told you I want to see her kana min rowa?"

"To ai Ummy magana tariga ta qare tunda har kinyi rantsuwa, you'll see her tomorrow, saiki cinyeta karki barmin ko kingi"

Rankwashi tabashi lafiyyaye

"Eh din zan cinyeta din, dagani"

Shafa kan yake yana yamutsa fuska kamar zaiyi kuka

"Kai Ummy wlh yanzu kinbar so na"

"Dama, ai yanzu nabar wayata yayinka, yanzu lokacin autata ce bakaiba godai godai dakai"

Kallon saitin baby yayi daketa Satan kallonsu tundazu tana qumshe dariya.

Ganin zai kallota yasata saurin kawar da idanu tana duba littafin hannunta a wayance.

"Ke jeki hadomin coffee" yafada yana tamke fuska.

"Bazata hadoba, kaje Matar ka ta hadamaka"

"Kai Ummy..."

"Ke tashi kiwuce sama kaima katafi gida ka baro diyar mutane ita daya"

Da sauri baby ta tashi tayi sama don dama tunda yace ta hado coffee take jinta kamar saman qaya.

Haka ta tisoshi gaba har wajen motarshi riqeda kunnenshi daya shikau sai qara yake saki qasa qasa, Kai kace ba A.A bane uban yan ji dakai.

Haka ta turashi mota ta rufe taja baya tana dagamashi hannu harya fice yana zum6urar baki...✍



No editing, kuyita hqr da mistake please🙏


Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka bamu zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





Note: nayi mistake a page daya gabata, page 34 ne maimakon 33 Danasa.

So yanzu na 35 ne zamu tashi.


Ina fans din Auren kwangila? Your comments is making me go gaga💃

Ina godiya, keep it flowing💖

Ina cigiyar sis hajara, maman twins da maman fateema, fatan suna lfy.

Koko babu data ne😂 gaskiya karku badamu please, kar ayimana dariya, kufito saudart na kewarku.


The page is dedicated to all Auren kwangila fans, kuyi yadda kukaga dama dashi💃💃💃💃💃







035




Tana kwance tana sliding din wayarta tana shiga da fita acikin groups don yanzu itama tafara gwanancewa a chatting don shi ke debemata kewa yanzu tunda tarage zaman qasa.


Tana cikin shafe shafen taga massage yashigo na baby.

Shiga tayi don gani

*yeee sweat Matar yaya💃*
Abinda taga ta turo kenan

*hmm ina sallamar kuma?*

*oops na mance, am just too happy ne wlh*

*ai haka kike, yar rainin sense😒*

*kai aunty wani sa'in ke joy killer ce wlh😕*

Sticker dariya saudart ta tura mata

*😆😆 lol, seems autar tamu farinciki, am sorry to, fesamin naji👂*


*anqi din😏*

*haba autaras, c'mon please🤕*

*anqi din, sai kinzo zakigani, bake bace kike cewa ban iya girki ba? Gobe ki sako wani extra takalmi a jakka don saikin mance na kafarki don santi😂*

Dariya saudart tayi a zahiri, sosai take jin baby har cikin zuciyarta, shirmenta da barkwancinta ba qaramin sata nishadi yake ba.


*Tofa, zuwa zakiyi kiyi girki ne*

*laa badai be fadamaki gobe zai kawoki ba?😳*

Daga gira daya saudart tayi, cikin zuciya tana cewa 'to haka akayi?'


*dagaske😳💃💃💃 yee finally! Kullum saina mashi nacin zuwa yana cewa ba yanzu ba, qila surprise zaiyimin*

Ta tura tana ta6e baki tana yatsine fuska.

*oops🤦‍♀ ko meyasa na fadamiki? Please karkice nafada maki👏*

Murmushi saudart tayi sannan ta turamata

*zanyi tunani akai😎*

*please anty ta ta kaina, mata a wajen sweet Ashraf dinta, an buga dake anbarki, daga ke babu qari, kiyi Kane Kane kiyi bake bake ki wala ki sarara keda kishiya saidai kiji wai, wai dinma wai😜*

Sosai saudart tayi dariyar kirarin datayimata.

Haka sukayita fira har goman dare sannan suka sauka.

Sosai saudart taji dadin fitar daxatayi gobe, ko babu komai zata fita ta shaqi iskar rahama.

Bata Dade ba sosai barci yayi gaba daita.










********************************



Tunda gari ya waye take jiran tsammani, tasan dolene yazo yayimata maganar tafiyar amma shiru kakeji wai mallam yaci shirwa.


Yau Friday so sai wajajen 10:30am yafito.

Kamar kullum batareda ya kalli side dinta ba ya nufi stairs, yana tafiyarshi daya saba hannu daya cikin aljihu dayan kuma riqeda briefcase.



Tabbass taji fitowarshi hakan yasata gyara zamanta tayima kofar ta quri tana jiran jin yabugo tana ayyana Jan ajin dazata yimashi kafin ta budemishi.

Batayi auneba taji tashin mota.

Da sauri ta miqe ta nufi window dinta dagudu saidai harya fice daga gidan.

Wani Abu taji ya tokareta a wuya.

Kutt.. Badai playing dinta baby tayiba?

Gashi tasaka ran fita sosai, a hassle ta jawo wayarta da niyyar kiran baby sai kuma tafara tunanin me zata gayamata? Ai hakan kamar tona asirin yanayin zaman su ne.

Haka takoma ta zauna cikin jin haushi da mutuwar jiki.


Haka ta yini a ranar tana jinta wata suku suku daita.



Tana kwance wajajen qarfe dayan rana taji ana Danna doorbell.

Tsaki taja ta gyara kwanciya.

Jin ba'a da niyyar bari yasata tashi ta yafa gyale ta sauko fuska babu walwala don haryanzu takasa daina jin haushi.

Tana budewa tayi tozali dashi.

Kallon sama da qasa tayimashi tana nazarin shigarshi.

Cikin girmamawa yadan russuna.

"Good evening ma'am"

Bejira amsarta ba ya cigaba dacewa

"Sir yace inzo inkaiki anguwa"

Tsayawa tayi tana kallon shi.

Lallai so yafi qarfin ya kaita shi? Hmm tafi nono fari dama batada niyyar sake ganin wannan mummunar fuskar tashi.

"Ok am coming"


Ta koma ciki ta rufe kofar shi kuma yakoma mota.

Haurawa sama tayi da sauri don kawai saita tsinci kanta cikin farinciki.

Quick shower tayi sannan tafito ta shirya cikin wani dakakken lace maroon da ratsin fari anmata style din simple Zane sa half gown mai tsaga gefe da gefe sannan tadaura kallabi style din zahra buhari ta Dora farin gyale akanta ta yafa ta dauki handbag fara takalmi ma farare, hannunta na dama daure da wrist watch fari sai zobunna.

Bata wani yi kwalliyar kirkiba saidai ta shafama sexy small lips dinta maroon din janbaki Wanda yasata yin kyau sosai, feshe turare mai sanyin qamshi tayi sannan ta kwashi wayoyinta da ATM sannan tafito.


Back seat ta zauna, ya tada motar suka shilla.

A hanya saida tasa drivern ajiye ta wani super market ta siyama Ummy turraruka ita kuma baby kayan maqulashe sannan suka wuce.


Jin horn yasa baby da tundazu tana zaune tana cika tana batsewa tayi saurin leqa wa, ganin motar daya daga cikin na Ashraf ne yasata qara la6ewa tana kallo don tsoron fitowa take don duk atunaninta Ashraf ya kawota.


Ganin emeka yafito daga gaban motar ya zagayo ya budewa saudart yasata qwala wata uwar qara Wanda saida Ummy dake zaune tana duba wani littafi tsoro.


Dagudu tanufi kofa ta bude tayi waje tana tsalle cikin murna.

Qwaqumeta tayi cikin tsananin murna tana tsalle itama saudart rungumeta tayi cikin murna.

Haka suka shiga ciki kowa fuska fall farinciki karma baby taji lbr.

Cikin fara'a Ummy ta tarbe saudart ita kau tayi qasa zata gaidata tayi saurin tarota tana rungumeta.

"You're welcome my dear, Allah yayimaki albarka"

Sinne kai tayi tana gaidata.

Amsawa Ummy tayi tana zauna daita akan kujera baby tazo ta zauna kusada ita sai washe baki take.

"Wai bazaki dauko mata kayan sha ba? Kinwani maqale mata" tafada tana antayamata harara.


Dariya baby tayi tamiqe ta ruga kitchen din.

Daidai nan emeka yashigo da kayan datayi shopping din ya gaida Ummy a girmame ya ajiye a tsakiyar falon yafita.


Fitowa baby tayi fuskarta da murmushi hannunta dauke da tray mai daukeda drinks da ruwa da snacks.

Doramata tayi kan stool dake kusada kujeranta daidai nan idanunta ya sauka akan ledojin qasa.

"Anty wannan fa?"

"Yours"

Da sauri ta jawo ledar tana murna ta bude, ganin kayan maqulashe yasata yin ihu tana rungumo saudart tana murna ummy namata fadan karta karya mata daughter.

Nan taware dayan ledar ta leqa taga turrarukan tace

"Wannan dai ko ba'a fadaba nasan na Ummy ne, Ummy gashi"

Ta miqamata.

Itama leqawa Ummy tayi tana fiddowa tana santinsu itama tana godiya.

Ita kau saudart kunya ma ta kamata.

Haka su kadan ta6a hira ganin kamar taqi sakewa yasa tace sutafi sama dakin baby.

Aikau nanfa abun nema ya samu, hira suke kamar wasu dasukayi shekaru dama dasanin Juna Wanda duk yawanci tsokana ce.


Sai bayan sallar juma@ Ummy tace su shirya akaisu gidan mamy ma.

Sosai saudart taji dadin haka.

Nanfa baby aka dauki wanka aka cake dankwali suka tafi.


Sosai mamy taji dadin zuwansu kuma taji dadin ganin chanjin Da saudart tayi don taqara yin fresh tayi kyau.

Nanfa suka baje kolin fira dasu kamal Wanda mostly da baby sukeyi sai tsokanar juna suke.


Sai wajajen six suka bar gidan bayan mamy tagama kashewa saudart jiki da nasiha.


Direct gidan daddy suka nifa.

Nanfa baby taga tsantsar soyyaya tsakanin uba da diya, fira kau sunsha shi kamar babu gobe.


Koda dasu tafi kuka taitayi dakyar ya rarrasheta yasamu suka tafi.


A hanya baby sai tsokanar ta take.


Haka sukaita fira cikin jindadi har suka isa gidan.

Sosai saudart taji dadin fitarta yau don sosai take jin wani irin nishadi data jima bata jiba.


Parking sukayi suka fito suna dariya.

Can dariyarsu ta tsaya gabadaya a dalilin ganin motar A.A dake fake a parking space din.


"Seems sweetheart dinki nanan" inji baby cikin shaqiyanci.

Harara saudart tabata tayi gaba, baby tabita tana dariya qasa qasa.


Da sallama tashigo falon.

Kamar hadin baki ya dago ya kalli kofar daga inda yake kwance bisa cinyar Ummy itama daidai ta kallo cikin falon sai caraf idanunsu suka gauraya...✍



Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah kabamu zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲





Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)








036






Basu yiwa juna kallon second biyuba kowanne ya janye idanunshi.


"A'a? Kun dawo? Dama yanzu nake tunanin kiranku naji shirun yayi yawa" inji Ummy tana ture kan Ashraf daga kafarta shikau sai sake maqalewa yake.


"Wlh kau Ummy, mun dan taushe hannu" inji saudart tana zama akan wata kujera dake kallonsu.

Baby ma da sallama tashigo cikin nutsuwa kamar wata saliha ta zauna kusada saudart tana gaida Ashraf

"Yaya ina wuni?"

"Lfy" kawai yace yana qara gyara kwanciyarshi kan cinyar Ummy.

"Ya wajen su mamyn?" Inji Ummy cikin fara'a

"Wlh lfy lau tana gaidaku ma"

"Aikau muna amsawa, ai rananma na kirata mun gaisa"

Murmushi saudart tayi tana dan wasa da zoben yatsarta tace

"Allah sarki"

"Oh ni, waini son meke damunka ne? C'mon get up, saika karyani tukkuna?"

Tafada tana tureshi

"Shhhhh Ummy mana?" Yafada cikin shagwa6a yana sake maqale mata.

"Wai dukda kayi auren ma bazan tsiraba? Dama haka kike fama daughter?"

Sunkuyar dakai saudart tayi cikin kunya, a bangare guda kuma tana mammakin abinda Ashraf yakeyi.

Haka Ummy taita fama dashi yana wani narke mata yana zuba shagwa6a.

Itadai saudart takaici na ya qumeta, don kwata kwata be burgeta ba, mata akasani da zuba shagwa6a ba qaton gardiba.

Tsaki tajashi yafi cikon kwando acikin zuciyarta.

Ganin abun nasu bana qarewa bane yasata tashi murmushi a fuskarta.

"Ummy, Bari muke sama muyi sallah"


"Ok, ai gashinan kau anata kira, muma yanzu zamu tashi"

Tare suka tashi da baby da tunda tashigo bata sake cewa komai ba bayan gaisuwar datayima Ashraf.



Bayan sun shiga daki baby ta fashe da dariya harda kyakyatawa.

Binta da kallo saudart tayi daga bisani tace

"Ke kumafa? Lafiya dai ko?"

Bata amsamata ba saima fadawa datayi kan gadon ta tana mai cigaba da dariyar.

Tsaki saudart taja tana cewa

"To Allah yakawo sauqi" tashige toilet.


Alwala ta dauro sannan tafito ta tarar har baby ta shimfida mata sallaya.

Kallonta tayi ganin tayi dai daya kan gadon tana latse latse a waya.

"Kefa? Ko bakiji an kabbara ba?"

"An yafemin ai"


Bata sake cewa komai ba ta kalli gabas ta kabbara sallar.


Koda tagama magrib bata tashiba har saida akayi isha'i sannan.

Nan baby uwar surutu tafara zubamata shi, itama tana biyemata har saida Ummy takira baby a waya cewa su sauko suci abinci.



A dining suka iskesu, Ummy na feeding din Ashraf kamar kodayaushe.


A kunyace saudart ta ja kujera daga can beda dasu ta zauna.

Ajiye cokalin Ummy tayi tana cewa

"Yauwa baby, Debi abincin ki ki komawarki daki nima inada abinyi"

Diba baby tayi tayi gaba itama Ummy ta miqe zata tafi

"Ummy banfa qoshiba" inji ashraf yana dan ware idanu

"Then? Aiga Matar ka nan, tabaka" tafada tana wucewarta.


Shiru wajen ya dauka na dan lokaci.


Ajiyar zuciya tasaki ahankali sannan ta miqe tsaya ta dauki plate ta bude warmer din.

Haddadiyar fried rice ce dataji kayan lambu tayi green shar daita.

Serving spoon tayi amfani dashi ta zuba kadan a plate din, shima don kar Ummy tayi magana plus batason yin girki idan sun koma gida.

Nan ta zuba banana juice din a glass cup takoma ta zauna tafara ci cikin nutsuwa da yanga.


Duk abinda take yana kallonta ta qasan ido, harta gama tafara cin abincin.

Shiru wajen yasake dauka idan ka dauke Qarar da cokalin da saudart take amfani dashi keyi ahankali.

Shi ya maida hankali akan wayar hannunshi yana shafe shafe amma duk movement dinta yana kallo ta qasan ido.

Itakau yitayi kamar batasan da mutum ba awajen maida hsnkalinta akan abincin ta dukda atakure take ga qamshinsa daya hanata saqat don duk numfashin dazatayi saita shaqeshi.

Sun dan Dade a hakan, can saiya maida wayar a aljihun wandonshi ya dauki glass cup ya tsiyaya ruwan gora yasha kadan sannan ya goge bakinshi da tissue ya miqe yabar wajen.


Ajiyar zuciya ta sauki harda dafa saitin zuciya

"At last" tafada tana rolling din idanu.


Saida tagama sannan ta tashi ta tattare abubuwan da aka 6ata takaisu kitchen ta dawo ta gyare wajen ta gogeshi kamar ba'a ci abinci ba wajen sannan takoma kitchen ta wanke abubuwan dasuka 6ata.

Tana cikin kifasune Ummy tashigo da mammaki a fuskarta.

"Daughter, why? Haba dakin bari baby tayi"

Murmushi tayi tana tsane hannunta da hand towel.

"Kai Ummy, ba komai fa, basuda yawa ai"

"Dukda haka daughter, yanzu bari baby zata ida, kifito kutafi don garin naga kamar da hadari kar ruwa ya ritsa daku ahanya"

Babu musu tabi bayanta


Har bakin mota su Ummy suka rakosu baby harda budemata kofa tana saramata.

Harara ta gallamata kafin tafita.

Wata Leda Ummy ta miqomata mai dan girma tana cewa gashi babu yawa.

Sosai saudart tayimata godiya cikin girmamawa sannan Ashraf ya tada motar yafara yin reverse.


Dagamusu hannu Ummy da baby sukayi tayi har saida suka fice daga gidan.






********************************


Tuqi yake cikin qwarewa da burgewa, kamar kodayaushe babu Wanda ya kula wani bare ya tanka, kowa harkar gabanshi yake.


Babu zato ruwan sama mai qarfi da iska ya tsuge kamar da bakin qwarya.

Gashi sunyi nisa don sunfi Rabi amma da saura kuma kafin sukai gida.


Duk yadda yaso ya cigaba da tuqin cikin ruwan kasawa yayi don sosai ruwan ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login