Showing 153001 words to 156000 words out of 173829 words
dai basu suka dawo gidaba wajajen six na marece saboda harda qunshi akayi musu duk jaa both kaffafu da hannaye, sosai qunshin ya fito a fararen fatarsu gwanin sha'awa
Agajiye suka dawo gidan, saida suka fara biyawa dakin ummy dake zaune robobin fresheners da turaren qamshi kala kala da humrori agabanta tana packaging dinsu
Sosai ta yaba kyawun dasukayi tana santin qunshinsu sannan ta umarcesu suje suyi sallah kasancewar anfara kiraye kiraye alokacin
Saida sukayi har isha'i sannan suka sauko sukaci abinci suka koma saman
A dakin ma hira suka dasa wanda duk baby ce mai surutun itakau saudart dakyar take amsamata don a matuqar gajiye take burinta kawai takai kaffadunta qasa kewar ashraf dake maqale a qasan zuciyarta, rabonta dashi tun jiya, duk yau bata sashi a ido ba saidai hakan yamata daidai don yanzu tsoron haduwarsu take don ta lura bashida self control, idan sun hade duk abinda yazomashi akai yi yake beko la'akari da inda suke
Tunawa tayi da kissing dinshi na jiya hakan yasata jin tsigar jikinta na dan tashi, ganin hakan yasata yakice wannan tunanin a zuciyarta ta maida hankalinta akan baby dake zuba kamar Yar tsanar da aka sawa battery
Ashraf kau tunda yafita be dawo gidan ba sai wajajen 10, amatuqar gajiye yadawo hakan yasashi wucewa part dinshi kawai
Yana shiga ya rage kayan jikinshi ya kwanta ko minti goma beyiba barci yayi awon gaba dashi
*WASHEGARI*
Juma'atu babbar rana! Yau kowannensu cikin nishadi ya tashi, kowannensu najin farinciki wanda basusan dalilinshi ba kodayake saudart ce za'ace batasan dalilin farincikin ba amma Oga A.A yasan abinda yataka dama
Yauma kamar jiya tunda safe yafita saidai sa6anin jiya yau saida yashiga ya gaida ummy kafin yafita dukda bata amsamashi ba da kyau amma hakan be dameshi ba don bayajin ga yadda yakejin kanshi akwai abinda zai 6atamashi mood dinshi
Koda yafita saida yaje ya qarasa settling din aikinshi na jiya sannan yawuce saloon shima aka dan saisaye Mashi suma dukda bawani yawa gareta ba akaimashi trimming din sajenshi yafito gwanin kyau, sannan akaimashi gyaran farce da filing nails sannan akaimashi foot bath
Bashi yafito daga qayattacen saloon din maza dinba saida aka kusan shiga sallar Juma'a
Gidanshi yawuce daga nan ya shirya cikin sabbabin shaddarshi Yar gaske mai shegen maiko kalar golden ya kashe hula kamar wani sabon ango yafice massalaci a gaggauce don karya rasa sallar juma'a
A bangaren saudart kau tunda tashiga gyara dakin ummy, ummy ta riqeta don abinci ma saidai takawomata nan dakin, ga cimmar datake bata taci ayau din na musanmman don duk dangin fruits ne da farfesu da pure madara dasukaji hadi
Wankama kanshi yau ruwa musanmman tayi amfani dasu wanda yasha hadin turarrukan wanka masu shegen qamshin dadi
To tun anan saudart tafara shan jinin jikinta don ita ba qaramar yarinya bace tasan ko me akebata, kanta ya kulle sosai yayinda zuciyarta tashiga fargabar Allah yasa ba abinda zuciyarta ke rayamata bane zai faru
Hakan yasa tanemi dan kuzarinta data tashi dashi ta rasa saita koma wata sukuku daita gashi ummy bata bata fuskar tambaya ba kodayake kota bata me zata cemata?
Hakan yasa takoma wata sukuku daita tanayin duk abinda ummy tasata.
A bangaren ummy kau tana lure da yanayinta amma tayi kamar bata ganiba
Saida tasata tayi wanka tayi sallah sannan ta fiddomata wani jan danqareren lace mai touches din baqi tabata akan tasa
Ba yadda ta iya haka ta amsa tasaka dinkin riga da skirt sunmata ciff kamar ajikinta aka dinkasu
Ko ita kanta ummy saida tayaba da kyawun datayi don sosai kalar kayan suka fitoda glowing skin dinta
Saida tagama shiryawa sannan ummy ta zaunar daita don suyi magana
Tunda tafara magana saudart ta tsinci kanta cikin faduwar gaba
Da nasiha ummy tafara mata, nasiha mai kashe jiki da sage gwiyagu
Tun anan saudart ta sadaqat don ko makaho ya laluba yasan mezai faru
Saida tagama mata nasihar sannan tacemata tazama cikin shiri anjima mijinta zaizo yatafi da ita
Kasa tsaida hawayenta tayi hakan yasa tabarsu suna digowa kanta aqasa, dukda tasan koba dade koba jima saita koma dakinta hakan besata jin wani iri ba, saida ummy ta rarrasheta sosai ta sassamata albarka sannan tabarta ta sauka qasa don ida shirye shiryen datake tun safe
Haka saudart takoma ta kwanta zuciyarta namata nauyi
Koda baby tadawo a wannan halin ta sameta, tambayar duniyar nan tayimata amma tayi banza daita don bata tata takeba
Ganin hakan yasa baby maida akalar tambayarta ga ummy inda ummy ta gayamata yau zasu koma gidansu
Sosai itama baby taji ba dadi don yan kwanakin nan ba qaramin dadinsu tajiba tareda ita saboda tana debemata kewa sosai haka itama tadawo dakin ta zauna kusada ita ta zabga tagumi tanajin kewarta tunma kafin ta tafi
Haka dai suka qarasa wunin ranar jiki asanyaye
*8:00pm*
Wata sabuwar mota baqa wulik mai sheqi tafara horn a bakin gate din gidan
motar qawace take da decorations masu qyalqyali both gaba da bayan motar
Saida aka gama scanning din motar sannan gate din ya wangale motar tashigo ciki
Maimakon motar tayi parking space saita wuce har gaban entrance din gidan ta tsaya
Saida aka kusan shafe minti daya da tsayuwar motar sannan aka bude driver seat, nanma saida aka ja daqiqu 20 sannan aka ziro qafa daya mai sanye da half cover farare tass sannan gangar jikin mammalakin kafar yabiyo
Tsarki ya tabbata ga mahallincin wannan kyakyawar hallitar mai cikeda kwarjini da haiba
Wato fadin haduwar A.A a wannan Daren 6ata bakine don duk yadda zan misaltamuku shi ya wuce nan
Sanye yake cikin baqar shadda yan ubansu wanda akaiwa aiki kalar fari
Dinkin Riga da wando ne na samarin zamani rigar da kadan tawuce cinya
Kanshi sanye da hula fara an wani kasheta a gefen kai, hannunshi na dama sanye da tsaddadiyar agogon fata itama fara sai takalmin shi half cover suka farare
Sosai yabada kala cikin shigarshi ta black and White ga wani daddaden qamshi dake fita daga jikinshi
Maida kofar yayi yarufe sannan ya zagayo yanufi kofa fuskarshi na fitar da annuri irinna angwaye
Knocking yayi a kofar falo yasa hannu ya murda handle din kofar batareda ya tsaya jiran isoba
Tura kofar yayi yashiga da sallama.
Babu kowa a falon sai t.v daketa haukanta ita kadai
Hakan yasashi nufar sama direct cikin takunsa na qasaita
Suna zazzaune ummy na ida packing din kayyakin da tasaimata dangin kayan qamshi itakuma baby na yima saudart simple makeup wanda dakyar tasamu ta yarda ayimata
Knocking din kofar da akayi yasasu danyin Jim da baby da ummy yayinda zuciyar saudart tabada damm har saida tadan dafe saitin zuciyar
"Baby get the door" inji ummy jin ansake kwankwasawa
Ida shafamata janbakin tayi sannan ta ajiye ta nufi kofar da sauri yayinda saudart taja lifayar dake nade ajikinta ta rufe fuskarta
Harzai qara knocking sai yaji alamun za'a bude kofar hakan yasashi fasawa ya zubawa kofar ido
Cak baby ta tsaya tana kallonshi from head to toe baki sake ganin yayan nata ya wani transforming kamar bashi ba
Harara ya gallamata ganin yadda tawani bake hanyar ita bata barshi yashiga ba sai kallon datake binshi dashi kamar yau tafara ganinshi
"Jira kike inyi ball dake sannan?" Yafada yana harararta
Sai a sannan ta wara idanu tace
"Kai yaya! You look soo takeaway👌" tafada cikin murna
Dan yatsine fuska yayi sannan yace
"I know"
Ganin yanufota yasata saurin komawa baya ta ra6e gefe yashige sannan tabashi abaya tana kumburi
Da sallama yashiga wanda yayi daidai da faduwar gaban saudart
Qara sunkuyar dakai tayi tana jin ummy na amsa sallamarshi
Koda ya shigo dakin da saudart yafara yin tozali wanda ke can gefen gado kanta a qasa
Kasa janye idanunshi yayi akanta ganin yadda tayi mugun kyau cikin baqar lafaya dake nannade a jikinta, ba qaramin kyau tayimashi ba dukda ba gannin fuskarta ba yake
Tanaji suna gaisawa da ummy, haka kawai ta tsinci kanta da matsananciyar fargaba da tsoro, yanzu fa tafiya zaiyi daita, shikenan daga ita saishi, hakan data tuna yasata jin hawaye na tararmata a idanu na tsananin fargaba
Shikau gogan zama yayi qasa yana gaida ummy kanshi a sunkuye don haka kawai yaji yau yana kunyarta sosai
Itadai ummy amsawa tayi sannan ta umarci baby dake tsaye tundazu akan tabasu waje
Ba don tasoba ta juya tafita tana tura baki acikin zuciyarta tana cewa 'mumafa wataranan auren zamuyi, abinda ba'aso muji din Dole afadamana'
Sudai basusan tanayi ba
Sawa ummy tayi saudart ta sauko itama ta zauna kusada ashraf sannan tashiga yimasu nasiha mai ratsa zukata inda acikinta tafi jaddadamasu Kalmar haquri don duk zaman dakaga ya dore kuma yayi qarko to haquri yayi tasiri sosai a wannan zaman
Sosai nasihar tashige su don har saida takawo kwalla a idanun saudart
Saida tagama musu nasihar sannan tasama auren albarka dasu kansu sannan ta dago saudart daketa hawaye yayinda ashraf yadauki tilin kayan da ummy tayi packing a qaramin trolley suka nufi qofa
Baby na zaune a falo taga su ummy na Saukowa, ummy riqeda da saudart
Hakan yasata tasowa itama takama hannun saudart din suka rankaya waje
Awaje kau ba qaramin mammakin ganin wannan sabuwar dalleliyar motar sukayi ba gashi tasha decoration sai qyalli take
Baby da bakinta yaqi rufuwa ta bude front seat gefen mai zaman banza
Ganin hakan yasa ummy ida qarasowa da ita
Gab da zasu shiga saudart ta juyo zata duqa ummy tayi saurin tarota
Cikin muryar kuka saudart kecewa ta yafemata duk abinda tayimata a iya zamansu
Sosai ummy taqara jin qaunarta na linkuwa a zuciyarta hakan yasata rungumarta tana saka mata albarka tareda cewa babu abinda tayimata sai alhairi itama baby dake gefe tana shedding crocodile tears ta qaraso ta rungume saudart tana wai itama ta yafemata
Duk abinda suke ashraf na gefe yana kallonsu har sukayi suka gama sannan aka sakata a galleliyar motar da cikinta keda sanyi kamar fridge
Sannan suka rufo qofar
Ganin hakan yasa shima shiga mazaunin driver yana dan Sosa qeya ganin mugun kallon da ummy ke watsa mashi
Shi besan me ta tarewa ummy ba duniyar nan tasamashi ido, haka yashiga yajawo kofar yarufe yanadan murmushin gefen baki, saida yasaci kallon yadda tawani makure scan gefe guda yayi murmushi yana kada kai sannan ya tada motar yayi reverse yana hango yadda baby keta dagamusu hannu baki a washe yayinda ummy ke kallon motar kawai harya juya yanufi gate dake wangale yafice daga gidan zuwa matrimonial home dinsu a karo na biyu....✍️
Ummin fasihu🧚🏻♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
101
Tuqi yake ahankali cikin normal speed, motar is so silent inka cire cool music dake tashi ahankali cikin motar
Satan kallonta yayi akaro na ba adadi yana qara jin wani shauqi a zuciyarshi wai yau gashi ga sahibarshi zasu matrimonial home dinsu akaro na biyu
Wanda wannan tafiyar tasha banban da wancan
Wancan sun tafine da bada niyyar zama na dindindin ba, sun tafi ne sa niyyar zama ba dan taqaittacen lokaci, suntafi ne kowa da nashi manufar dayake son cimmawa wanda da hakan ta samu kowa zai kama gabanshi
Amma wannan tafiyar tako ina tasha banban da wancan
Wannan tafiyar bata taqaittacen lokaci bane
Zasu tafine da niyyar zama tare na har abada
Zasu tafine batareda wata manufa ba sai ta zama irinna ma'aurata
Zasu tafine amatsayin masoya dukda ita haryanzu baida tabbacin tana sonshi amma yanada tabbacin babu tsanarshi ko digo a zuciyarshi
Ko ahaka aka tsaya he's happy
Qara satan kallonta yayi yaga tawani lafe a kujera ta makure can gefe kanta a qasa
Murmushi yadanyi sannan ya dora hannunshi na dama saman nata dake bisa cinyarta
Ahankali ta dago ta kalleshi wanda dama abinda yakeso kenan
Kashe mata ido daya yayi fuskarshi still da murmushi
Sauke idanunta tayi tareda qoqarin zame hannunta daga qarqashin nashi
Qara riqe hannun yayi gamm yacigaba da tuqi da dayan hannun
Ganin yaqi bari ta janye hannun yasata kyaleshi tasake lafewa a kujerar tana lumshe ido
Basu wani jimaba suka iso gidan
Direct parking space yanufa da motar yayi parking
Sake juyowa yayi gareta yaga haryanzu kanta na qasa rabin fuskarta a rufe don be iya hango komai sai cute red bakin dayasha janbaki
Dan murza hannunta yayi tenderly sannan ya saki hannun ya bude murfin bangarenshi ya sauka
Tana jinshi amma ko motsawa batayi ba hartaji an bude murfin bangarenta
Ahankali ta dago ta kalleshi taganshi tsaye yana miqomata hannu alamun ta taho
Tunawa tayi da wancan zuwan nasu wanda ko arziqin kallo bata isheshi ba saima barinta dayayi a mota yayi wucewarsa saidai tagaji ta fito don kanta
Jin an kamo hannunta yasata sake dagowa ta kalleshi
Pulling din hannun nata yayi hakan yasata ziro qaffafunta ta sauko a motar still hannunta acikin nashi
Rufe kofar motar yayi sannan yajuyo wajenta
Batayi auneba taji ya cirata daga qasa ya dauketa in a bridal style
Waro idanu tayi tana qara qanqameshi ganin kamar zai yadata
Zatayi magana ya katseta da "shhhh" hakan yasa maganar maqalewa
Fara tafiya yayi daita hanyar main entrance din gidan kamar ya dauki Yar tsana ko nauyi beji
Itadai saudart is very uncomfortable, jitake kamar zai kadota hakan yasa tariqeshi matakam tana raba idanu, Allah Allah kawai take ya direta
Koda suka qarasa bakin kofa hannu daya yasa ya bude kofar sannan yajuya yasa baya ya turata ta bude
Matso da bakinshi yayi saitin kunnenta kamar zaiyi rada hakan yasa tayi saurin rintse idanu jin saukar numfashinshi akan kuncinta
"Kiyi mana addu'a zaman lfy da albarkar aure while ni nashiganmana da qafar dama" yafada in wishper
Shiga yayi da qafar dama still tana ahannunshi while ita tayi addu'ar acikin zuciyarta still idanunta a rufe
Wani irin qamshi mai tafeda sanyi ya kadomata wanda hakan yasata bude idanunta ahankali
Sake wara idanunta tayi ganin falon dirim cikin dim light sai yan kwayakwan disco light dake bata haske kala kala suna walainiya
Cigaba da tafiya yayi da ita cikin dakin da bata iya hangen komai saboda dan hasken dakin hakan yasata qara riqeshi tana wurwurga idanunta a falon tana wondering yadda akai yake gane hanya
Saida suka iso tsakiyar falon sannan falon yayi fau da haske mai tafeda wani romantic music a background din falon
Saudart da dafarko hasken ya kashemata idanu ta rintse su tashiga budewa ahankali kamar mai tsoron wani Abu
Qara wara idanunta tayi in amazement tana sake bin falon da kallo
Mutsu mutsun saukowarta yasashi direta qasa ahankali yana kallonta
Bin falon da kallo tashiga tana takowa tsakiyar cikin falon sosai while shi yana tsaye inda yake yayi pocketing din hannayenshi yana kallonta cikeda farinciki
"Wow!!" Tayi exclaiming ahankali tana dan wara idanunta ganin yadda akayi decorating din falon an chanza mashi fasali kamar bashiba don komai Sabone hatta kayan furniture din sabbine danqarraru wadanda suka amsa sunansu
Zame takalmin qaffafunta tayi ta taka lumtsetsen red centre carpet din tsakiyar falon ta qarasa ga wani centre table na glass wanda tun shigowarsu shi yafara daukar hankalinta
Qarasawa tayi gaban table din ta durqusa tana kallon qaton framed photo dinta ita da Ashraf da aka jingina da table din aka zagayeshi da coloured candles masu ci ahankali sai tarin cards dake Jere a table din
Qurawa Pics din idanu tayi tana mammakin yaushe sukayi wannan pics din
Subiyu ne acikin hoton tana jingine dashi suna Dariya su biyu
Ba qaramin kyau hoton yayi ba don kallo daya zakamasu ka hango dacewarsu da juna
Ganin yadda ta durqusa ta tsurawa hoton ido yasashi sakin murmushi yatako gareta yana murmushin jindadi
Tana durqushen taji an rungumota ta baya an zuro kai ta gefen wuyanta anyi mata rada a kunne da
"Welcome back *MRS A.A")*
lumshe idanu tayi jin saukar wet lips dinshi a gefen wuyanta bakinta na fidda wani sihirttacen murmushi
Juyota yayi suna fuskantar juna hakan yasata bude idanunta tana kallonshi still fuskarta dauke da annuri
Huramata iska yayi a idanu tayi saurin lumshe su tana murmushi
"How did you see that?" Yafada yana sa dan yatsarshi a ramin kumatunta daya lo6a sanaddiyar murmushin datayi
"It soo...amazing" tafada tana qara fadada murmushin ta
Sosai yaji dadin comment dinta hakan yasashi fadada murmushin shi shima yana hada goshinsu tareda sakin light kiss akan lips dinta yace
"Anything for mi-lady"
Itama murmushin tayi tadan janye jikinta tajuya ta kalli pics dinsu sannan ta kalleshi
"When mukayi pics dinnan?"
Yar qaramar Dariya yasaki sannan ya miqe tsaye yana dagota yace
"Abin wani sirri ne"
Be bata zarafin sake wata magana ba yasake cirata sama yayi hanyar stairs daita yanabin cool music dake tashi haryanzu a falon
Jin yana waqa yasata jin kunya ta sinne kanta a qirjinshi tana Dariya jin yadda ya wani maqe murya ala dole waqa yake
Ahaka suka qarasa sama dashima yasha decorations masu ban sha'awa
Bude kofar dakinta yayi yatura suka shiga yana qara sautin muryarshi cikin bin waqar wanda hakan yaqara volume din dariyar saudart don she found it so hilarious
À bedroom din wani sabon kallon tayi don shima kamar falon an chanza mashi fasalinshi
Komai sabone ga makeken gadonta wanda yafi mafarko yasha shimfida ta alfarma gasu tiny tiny red flowers warwatse a gadon abin gwanin sha'awa
A kan gadon ya zaunar daita sannan ya maido qaffafunta saman gadon
Bin dakin tashiga yi da kallo daga zaune cikin mammakin uban kudin daya kashe wajen yin wadannan abubbuwan don tasan ko ba'a tambaya ba an kashe kudi sosai ma kuwa
Saida tagama kalle kallenta sannan ta maido kallonta kanshi
Hada ido sukayi hakan yasata sunkuyar dakai tana murmushi
Dan jan hancinta yayi sannan ya miqe tsaye yace yana zuwa
Binshi tayi da kallo harya fita sannan ta maida hankalinta akan kalle kallen datake
Ba'a jimaba ya dawo hannayenshi riqe da ledoji manya manya
Tana kallonshi ya ajiyesu saman carpet dake gaban gadon sannan yaqara fita can saigashi yadawo da tray mai daukeda plate da spoons, forks da cups
Ajiyesu yayi qasa suma sannan ya tattare hannun rigarshi kamar me shirin yin wani uban aiki ya jawo wata Leda ya fiddo banqarrarun kaji dasukasha gashi😋
Ya dorasu a tray din sannan ya dauki ledar fruits ya fiddosu ya daurayosu sannan yadawo yashiga yanyankasu
Duk abinda yake saudart na zaune kan gado tana wasa da zoben tanayi tana Satan kallonshi ta qasan ido tana mammakin yadda yake abin expertly kamar mace
Saida yagama sannan ya bulbulamasu fresh milk a koffufukan ya jejjera komai ya kwashe abubbuwan dabasuda amfani yafita dasu
Be jimaba yasake dawowa beyi wata wata ba ya dauke saudart ya maidota kan carpet gaban abubbuwan daya gama shiryawa
Sunkuyar dakai tayi tana mammakin yadda yake daukarta every now and then kamar bejin nauyinta
"Now da me zaki fara mi-lady?" Yafada yana bowing dramatically
Dan dagowa tayi ta harareshi sannan tayi saurin sunkuyar dakai
Dan wara idanu yayi sannan ya kada kai
"Zanyi maganin wannan ne very soon" yafada yana kada kai
Itadai bata dagoba bare ta tanka mashi
Cinyar kaza yaciro yanufo bakinta dashi, ganin hakan yasata kauda kai
Binta yayi dashi nanma ta maida kan wani 6aran
"Kinsan Allah? Zanmiki dura" yafada yana sake tunkararta da naman
Sake kauda kai tayi tana cewa
"Allah am full" adan shagwa6e
"You're not" yafada yana qara nufarta dashi
Yunqurawa tayi zata gudu yayi saurin kamota