Showing 102001 words to 105000 words out of 173829 words

Chapter 35 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1125

tashi hankalinta.

Haka suka fita daga gidan suka dau hanyar gidan mamy kowanne da irin fargabar dayake....✍



Sorry for the short chappy🙏


Please sai kun dinga hqr dani yanzu, wlh bansamun zamane kamar da.

Da ace yadda nake samun lokaci ne kamarda da yanzu book dinnan yaqare.

Yanzu typing dinma kanshi wahala yakebani don am always busy.

Please bear with me, yanzu ba kullum zaku dinga jinaba, amma duk ranarda am less busy zan dinga yimuku mai yawa🙏

Nagode da qaunar dakukemani da littafin nan.

Masu cigiyata da masu kirana duk nagode, Allah yabar qauna da zumunci, Allah yabarmu tare har abada💖


Ashaanty loves you so much😘💖💖💖💖💖

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)




Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)




075



Fitowa duk sukayi daga cikin motar duk suna kallon qaton gate din gidan.

Asanyaye saudart tajuyo ta kalli daddy kallo daya zakamata kasan a tsorace take

"Kishiga sweetheart, kimin sallama da Abban nayi losing din contact dinshi"

Nodding tayi a sanyaye sannan ta nufi gate din kamar wanda kwai yafashe mawa aciki.

Saida tayi knocking sau uku sannan taji alamun za'a bude gate din

Budewa akayi fuskar maigadin ya bayyana, yana ganinta ya washe baki yana mata maraba.

"Anty kece? Yau banda mota kikazo?"

Murmushi kawai tayi tace "eh bani kadai bace, Abba fah?"

"Yana ciki bema dade da dawowa ba ma"

"Ok" daga haka tashige ciki gabanta na faduwa.


Ahankali ta danna doorbell din kofar cikin sanyin jiki.

Shirun dataji yasata qara dannawa.

Gani tayi an murda handle din daga ciki hakan yasata dan ja baya gabanta na faduwa.

Abdul ne tagani yana turo baki, yana ganinta ya waro idanu tareda kiran sunanta da karfi ya rungumeta.

Dukda bacikin nutsuwa takeba saida ta murmusa tana riqeshi itama

"Aunty kece? Kitaho" yafada yana jawo hannunta zai shigar daita ciki.

Saurin tirjewa tayi tareda jawoshi baya ta tsugunna daidai tsawonshi sannan tafara magana cikin muryar rada

"Ina Abba?" Tafada tana dan wara manyan idanunta

"He's upstairs" ya amsa shima cikin rada

"Mamy?"

"Tana falo"

"Doing what?"

"Tana tayamu homework"

Ganin tana kallonshi atsorace yasashi qara qasa da murya
"Aunty menene?"

Furza iska tayi daga bakinta sannan tace
"Nothing... mushiga"

Da sallama suka shiga, Abdul agaba jaye da hannun saudart dake taka kasa kamar mai tausayinta

Su kamal da tundazu suke kallon kofar don tabbatar da ita dince suka miqe aguje suka nufeta suna murna banda Aminu dake murmushi kawai daga inda yake zaune.

Wara masu hannu itama tayi absentmindedly tana kallon mamy da ko dagowa daga kallon littafin habeeb batayiba fuskarnan murtuk

Jiki asanyaye tayimasu habeeb murmushi ta qaraso ciki simi simi kamar marar gaskiya.

Dan nesa da mamy taxauna qasa tana kallonta a sanyaye abdul sai zubamata surutu yake.

Saida tagama amsamashi sannan ta dago takalli mamy a raunane
"Mamy ina wuni?"

Idan ku masu karatu kun amsa to itama ta amsa.

Sake gaisheta tayi wannan karon ma babu amsa saima tattara littafan gabanta data shigayi tana maidamasu cikin jakka.

"Mamy aunty na gaisheki" inji abdul don shi atunaninshi bataji bane.

Wani kallo ta watsamashi tace
"If i slap you, kutashi kuba mutane wuri!" Ta qrashe a tsawace.

Simi simi suka tashi harda aminu dake kan kujera sukayi sama.

Sunkuyar dakai qasa saudart tayi hawaye na kawo mata.

Tashi itama mamy tayi zata wuce hakan yasata saurin dagowa

"Mamy don allah kiyi haquri" tafada cikin muryarta dake dan rawa

Wucewa xatayi tayi saurin riqe tip din gown dinta

"Please mamy.."

Fizgewa mamy tayi tajuyo tana bankamata wani mugun kallo.

"Are you alright?"

Sunkuyar dakai tayi hawayen dake maqale a idanuwanta na gangarowa

"Am very sorry mamy, don girman allah kiyi hqr" tafada voice dinta na breaking

"sorry for what? Dama wani abu kika yimin?"

Kasa amsawa tayi sai matsar qwalla datake

"Ni bakimin komai ba, koma menene kanki kikaimawa, so you should be sorry for yourself, Aure dai shine kuka mayar abun wasa ko? Zaku kwashi kashinku a hannu daga ke har baban naki"

Jiki na rawa taqara matsota tana qoqarin riqe kafarta mamy taqara yin baya

"Ni kibar matsoni, me zan miki? Dama kinsan da zamana ne? Inada wani matsayine awajenki? No, so go to your guardian dama tare kuka tone kuka binne, stop including me" tafada cikin 6acin rai.

Taffukan hannu saudart tasa ta rufe fuskarta tana kuka sosai mai ban tausayi, jikinta har rawa rawa yake.

"Kinga tashi ki tafi, na me zakizo kicikamin gida da hayaniya? Idan zan baki shawara ma cewa zanyi ki adana hawayen da iface ifacen zuwa gaba don zaifi yimaki amfani alokacin.

Saudart kin bani kunya, am really disappointed in you, wlh ko a mafarki banta6a tunani zakiyi abinda kikayi ba.

Ina tarbiyar dana baki? Ina hankalinki, ina iliminki? Ina tunaninki?

Kin biyema kwadayyayen ubanki ya kaiki yabaro don ke keda kaico ba shiba, soon zaki zama bazawara kishiga layin zawarawa babanki kau babu abinda yashafeshi, iyaka yaga wani wanda zai qara tatsa ya auramiki shi shima bayan wasu lokuta ki fito kafin ya qara hango wani.

Ko shi Allah kanshi dayace mubi iyayenmu cewa yayi idan basu kaucewa koyarwar musulunci bane

Yanzu saudart ke bamai nusar da mahaifinki bane? Ke bame ganardashi bane ki nunamashi hanya idan yaso kaucewa? Amma kika biyemashi kega mai uba ko?

And the painful thing is ina raye? Ina raye saudart kikayi wannan abin batareda shawarata ko sanina ba? Banida matsayinda zaki kawomin damuwarki? Ya huremaki kunne baki ganina da mutunci?

Ace wai 'yata ce da auren contract? Auren kwadayi?.." tafada tana nuna kanta idanunta na kadawa.


Kuka sosai saudart keyi tana jin duk ta tsani kanta, jitake dama tamutu kafin wannan lokacin, dama batayi witnessing din wannan lokacinba a rayuwarta.

"Ku kuka sani ai, kuje can ku qarata, badai zawarci ba? Kije kiyi kiji ko akwai dadi, kikuma cigaba da biyema ubanki, watarana sai an hallakaki ta dalilinshi... yaje yayi laifi anzo andauki fansa akanki, keda bakijiba baki ganiba, go ahead Allah yabada sa'a"

Tsaki taja tajuya tayi wucewarta sama zuciyarta na quna.


Ahankali saudart ta dago kaffafunta ta dora kanta bisa gwiwa ta rungume kaffafun tacigaba da rera kukanta, nan take taji kanta nadan sarawa zazza6inda bagama sakinta ba na neman sake tasomata.


Batasan iya dadewarta awannan yanayinba taji anyi tapping din kafadarta.

Saurin dago fuskarta tayi datayi ja saboda kuka.

"Saudart?" Inji abba dake sanye da jallabiya a mammakince.

Sauke rinnanun idanunta tayi ahankali wasu hawayen na gangaromata ta gaidashi da muryarta dabata fita

"Lfy lau, what happened? Why are you crying?"

Batace komaiba sai cigaba dakukan datayi ahankali.

Miqar daita yayi tsaye yana rarrashi don yasan kwanan zancen

Dakyar yasamu tayi shiru sannan ya tambayeta daga ina take.

Jan hanci tayi sannan dakyar tace
"Gida, tare muke ma da daddy"

"Alhaji shamsu? Yana ina?"

"Waje" tafada tana sauke tagwayen ajiyar zuciya

"Ya sallam, since when? Shine baki gayama kowaba?"

Shiru tayi don ita saima yanxu ta tuna data barshi waje.

Fita yayi batareda yasake cewa komaiba.


Awaje kau daddy ne tsaye sai safa da marwa yake.

Sai imagining din abinda ke faruwa ciki yake gashi yakira number saudart yafi aqilga amma ba'a dagaba.

Jin ana bude qaramar qofar gate yasashi kafama gate din idanu sai ganin Abba yayi yafito.

Murmushi suka sakarma juna, abba ya qaraso sukayi musabaha sunama juna sallama.

"Alhaji shamsu, ashe kana waje? Wlh saiyanxu dana sauko saudart ke gayamin, kayi haquri please"

Murmushi Daddy yayi
"Bakomai Alhaji Isma'il, dama cewa nayi taimani iso, i thought baka nan ma danaji shiru"

Shiga sukayi Abba agaba daddy biyedashi suna dan ta6a fira.

Falon saukar baqi yakaishi sannan yajuya da niyyar sawa akawomashi abin ta6awa

"Alhamdullilah Alhaji, am ok" daddy ya tsaidashi da hakan

Dawowa abba yayi ya zauna yana facing din Daddy don jin abinda yakawoshi.

Dan daburcewa yayi ganin yadda ya kafamashi idanu

"Akan maganar auren yarannan ne.... it's was a mistake.... and... am regretting it" shiru yayi, shi kanshi yasan he sound stupid

"Nasan kanada labari kou?.."

Ajiyar zuciya Abba dake kallonshi tundazu yayi sannan yace
"Yes, yau kwana uku kenan dazuwansu in-law dinmu nan gidan"

Kallonshi daddy yayi yana dan wara idanu saikuma ya sauke idanunshi qasa feeling so humuilating

"I caused it all... duk laifi nane... i forced her"

Dan murmushi Abba yayi yace "yes, you made a big mistake, meyasa kayi haka Alhaji shamsu?"

Shiru yayi yakasa cewa komai, jiyake kamar qasa ta tsage ya rufta ciki, wani matsanancin kunya yakeji kamar ya 6ace ya huta.

"Yanzu dai faduwa ce tazo daidai da zama, dama nayi niyyar zuwa mall dinka mu tattauna, zamu hadu gidanka dasu in-laws din namu damu mu sassanta komai, saika fidda rana"

Shiru Daddy yayi haryanzu yakasa hada ido da abba.

Wai agaban abba kadai yakejin haka, inaga agaban in-laws din? Kokuma mai gabadaya agaban allah ranar sakamakko?

"Look everything will be alright alhaji, kawai gani nayi hakan zaifi, ahadu a samama kai mafita, aurennan yayi involving su biyu ne, dole saida yarda dukkansu, we want to hear from both of them kafin a yanke hukunci, sai inga hakan zaifi"

Hannu daddy yasa ya share gumin forehead dinshi sannan ya sauke ajiyar zuciya

"To, yanzu... yaushe zasuzo din?" Yafada ahankali

"Choose a date... duk ranarda yaimaka"

Shiru daddy yayi, tayaya zaiyi facing dinsu da wannan abun kunya, kai kwadayi beyiba, gashi da mutuncinshi da komai zaizama qaramin mutum awajen ahali mai daraja irinna A.A

"Gata... sunday kenan? Koko?"

"Hakan yayi, zan gayamasu, insha allah komai zai warware" inji abba daya lura da uncomfortableness na daddy.


Saida sukadan dade suna fira, abba na nunnunamashi abubuwan dayayi dabai kamata ba cikin hikima, dakuma illar wasa da aure.

Sosai jikin daddy yayi sanyi don magangganun abba sun shigeshi sosai.

Sai gab da magrib suka fito, abba yashiga yakira saudart dake inda yabarta suka fito yana sake rarrashinta yana assuring dinta mamy zata sakko ta kyaleta yanzu fushi take.


Sallama sukayi da abba, daddy nata mashi godiya don sosai yaqara qima a idanunshi.


Haka suka isa gida sukuku, bayan dinner daddy yashigo dakin saudart lokacin hartayi shirin barci tana zaune tabuga tagumi.

Zama yayi yafara rarrashinta yana bata hqr akan duk abinda yaimata yana nunamata tsantsan nadamarshi, sannan yafadamata yadda sukayi da abba.

Sosai hankalinta ya tashi don jitake bazata iya facing din ummy ba.

Dakyar yasamu hankalinta yadan kwanta sannan ya lalla6ata ta kwanta sannan yafita.

Kamardai kodayaushe yana fita tamiqe zaune tahada kanta da gwiwa tana tunane tunane, barci 6arawo ya sadado ya dauketa wajajen ukun safiya.



*THREE DAYS LATER*


Sorry ba yawa🙏


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)



076



*THREE DAYS LATER*


A natse yake saukowa daga stairs hannayenshi zube cikin wandon dakkakiyar shaddarshi kalar brown.

Kanshi babu hula sai sumar kanshi da tad'an taru sai shining yake don gyara

Hannunshi na haggu na sanyeda agogo rolex sai baqaqen cover shoes a kaffafunshi.


Dagowa duk sukayi suna kallon yadda yake saukowa qasa cikin sanyin jiki kanshi asunkuye.

Cikin yan kwanakin nan sun rasa gane kanshi don yayi wani laushi kamar bashi ba, haka suka bishi da kallo harya qaraso wajenda suke zazzaune suna jiranshi.

Duqawa yayi batareda ya bari sun hada ido da kowaba ya gaidasu cikin calm voice dinshi.

Duk amsawa sukayi suna kallonshi cikin tausayawa.

Kallo daya zaka mashi ka hango ramar dayayi cikin yan kwanakin nan, yaqara haske wanda hakan yaqaramashi kyau.

"To saimu yi niyya ko?" Inji kawu ibrahim

Duk tashi sukayi suka fito waje.

Motocci biyu ne a harabar.

Ummy da umma suka shiga seat din baya sai Ashraf da sadeeq dake gaba inda sadeeq ne matuqin.

Dayar motar kuma kawu ibrahim ne da kawu zahradini sai drivern dazai jasu.


Haka suka jera suka fito daga gidan suka halba titi.


Shiru motarsu ummy ta dauka kowa da abinda ke kai kawo a zuciyarshi

Sadeeq dake tuqi yad'an saci kallon ashraf daya jingina da seat dinshi ya lumshe idanu.

Janye idanunshi yayi ya maida kan titi yana qarajin tausayin abokin nashi.


*zaka ita misalta adadin qiyyayar danake maka?* maganar saudart ta ranan tadawo mashi a kwanya

*A'a*


*nima haka... baxan iya misalta qiyayyar danake makaba ada.... saidai yanzu ina iya cewa... qiyayyar danake maka ada batakai kaso daya cikin kaso goma danake maka yanzu ba*

*ka tsaneni ko? Ka tsani ka ganni cikin farinciki da walwala ko? Tell me*

*I hate you....with passion*

Haka magangganun saudart sukayita mashi amsa kuwa a kunne.

Yasan yau ne qarshen duk wani alaqa dake tsakaninsu.

Kullum saiyayi tsayuwar dare ya roqi allah akan ya yakicemashi soyyayarta acikin zuciyarshi amma yadda kasan roqo yake aqara mashi, kowanne wucewar daqiqa da qaruwar son saudart ne a zuciyarshi.

He's so weak, so broke, babu abinda ke fadar mashi da gaba sai abinda zai fito daga bakinta.

Yarasa dalili, koyaya ta furta ta tsaneshi sai yaji kalmar harcikin zuciyarshi, bawai besan ta tsaneshin din bane, yasani amma furtawar datake ba qaramin tasiri yakeba azuciyarshi.

Yana fargabar wannan kalmar abakinta, besaniba ko wannan karon zuciyarshi zata iya daukar kalmar ba.

Da tashine dasun barshi gida, da bazai bisuba don yasan kwanan zancen, dole yauce ranar rabuwarsu kuma yasan dole ta furtamashi kalmar dake qonamashi zuciya.


Jin an dafashi a kafada yasashi dawowa duniyar tunani daya fada yabude idanunshi yajuyo ya kalli sadeeq dake kallonshi shima.

Sai alokacin yaga kamar ba tafiyaba suke, waigawa baya yayi yaga su ummy basa cikin motar wanda hakan ke nufin sun iso kenan

"Be strong" inji sadeeq yana dan jijjiga kafadarshi cikin karfafa gwiwa.

Lumshe idanu kawai yayi ya bude batareda yace komaiba.

Bude murfin kofar sadeeq yayi ya fita ya maido yarufe.

Shiru ashraf yayi na yan daqiqu sannan shima yasa hannu ahankali ya bude murfin motar.

Saida yadanyi jim sannan ya sauko kafarshi daya sannan ahankali gangar jikinshi suka biyo baya.

Wani fresh air ne ya bugeshi wanda yasashi lunshe idanu yana shaqa tareda fesarwa ahankali.


Zagayowa sadeeq yayi side dinshi shima ya tsaya yana kallonsu Kawu dake gaisawa dasu Abba da daddyn saudart.

Shima Ashraf su yake kallo koko ince Alhaji shamsu yake kallo wanda kallo daya zaka mashi kaga rashin nutsuwa atattare dashi.

Kallonshi yake cikeda tsana da kyama marar misaltuwa.

A 6angaren su kawu ibrahim kau tarba ta mutunci suka samu wajensu Abba koko ince Abban kadai don daddy bemada nutsuwar dazai tarbesu sosai.

Jiyake kamar qasa ta tsage yashige don kunya, haka dai ake gaisuwan batareda ya yarda sun hada ido da daya daga cikinsu ba.

Kamar ance yakallo wajensu Ashraf, idanunsu ne suka gauraya wanda hakan ya haddasama Alhaji shamsu faduwar gaba don shi kadai ya hango abinda ya hango a idanun ashraf.

Ganin suna tunkarosu yasashi janye idanunshi daga kansu.

Qarasowa sukayi duk suka duqa don gaidasu.

"Ina wuninku?" Inji sadeeq a sanyaye.

Saida suka amsa sannan ashraf shima yabude baki dakyar yace
"Abba barka da wuni"

Amsawa abba yayi yana murmusawa shikau daddy bece konaiba sai kauda kai dayayi.

Haka suka dunguma suka nufi masaukin baqi dake gidan gabadaya.


Zaune take bakin gado ta jingina da kan gadon hannayenta harde a qirjinta, ita kadai tasan abinda ke axuciyarta, tunda taji qaran mottoci tasan sun iso, hakan yasa bugun ziciyarta qaruwa, yaune damarta ta qarshe na qwatarma kanta yanci, yaune damarta na qarshe na za6arma kanta irin rayuwar dazata cigaba dayi, rayuwar farinciki ko akasin haka. Today is the D-day.


Bubbuga kofar da akayi yasata dagowa ahankali tana kallon kofar.

Budewa akayi daddy ya bayyana bakin kofar ya tsaya yana kallonta.

Ahankali ta hadiye wani abu dake maqoshinta tareda sadda kai

"Come daughter" yafada asanyaye.

Qara dagowa tayi ta kalleshi da dara daran idanunta sannan ta miqe ahankali ta dauki hijab dinta dake gefenta ta warware ta zurata, saigata har tana kusan sharar qasa.

Anitse ta tako har wajen daddy kanta a sunkuye, kama hannunta yayi yadan murza
"Are you ok?" Yafada ahankali

Kada mashi kai kawai tayi asanyaye

"Ok muje" daga haka yajuya yayi gaba yana jaye da hannunta.

Bugun zuciyarta yashiga karuwa duk taku daya dazasuyi na tunkarar falon baqi.

Jitake kamar ta ruga don sosai zuciyarta je cikeda fargaba dakuma tsoro gakuma nauyin ummy datakeji.

Haka dai suka qarasa bakin kofar falon.

Sallama Alhaji shamsu yayi yashigo still jayeda hannun saudart da kanta ke qasa.

Duk dagowa sukayi suna amsa sallamar saidai duk idanunsu nakan Saudart.

Ahankali takebin daddy tana iya bakin qoqarinta naganin bata hardeba don tafiyarma dakyar takeyinta don tanajin yadda idanuwa ke yawo akanta.

Zama Alhaji yayi kusada Abba itakuma ta zauna qasa kusada kaffafun daddy still kanta a sunkuye.


Tunda suka shigo yadago yafara kallonta harta iso ta zauna batareda yako kyaftaba.

Wani irin yanayi na shauqi yaji zuciyarshi nashiga by mere ganinta kawai, gani yake kamar yayi shekaru be gantaba, jiyake zuciyarshi na narkewa ahankali cikin begenta, kallonta yake ba qaqqautawa burinshi kawai tadago yayi arba da kyakyawar fuskarta dake antayashi cikin shauqi.


Qoqarin tattaro sauran nutsuwarta tayi sannan cikin murya mai dan rawa rawa ta gaidasu kanta qasa.

Duk amsawa sukai in chorus, kowanne da abinda kemashi yawo cikin zuciya.

Ahankali Ashraf ya lumshe idanunshi yana sauke numfashi silently jin muryarta ta doki dodon kunnenshi, sai yanzu yake qara regretting din biyosu dayayi don jiyayi duk abinda yakeji can gida gameda ita ba komaibane jiyake kamar ya rarrafa daga inda yake zaune qasa yaje gabanta ya rungumeta.


Shiru dakin ya dauka na wani lokaci kowa da abinda yake saqawa a zuciyarshi.


Ahankali saudart tashiga dago idanunta dasuke sheqi saboda taruwa da hawaye yafara a idon, bata saukesuba a koina sai cikin na Ashraf da shima ita yakafe da idanu.

Da sauri ta sadda idanun gabanta na faduwa don ba qaramin haskemata idanu idanun nashi sukayiba.

Shima sadda kai yayi ahankali yana lumshe idanu yana sauraron yadda zuciyarshi ke halbawa.

"Longest time Alhaji shamsu" inji kawu zahradini yana kallon daddy.

Sai yanzu daddy yasamu damar hada ido da daya daga cikinsu.

Tsayawa yayi yana kallon kawu zahradini sosai don he's face look familiar

Ahankali yashiga bin sauran mutanen da kallo don placing finger akan inda yasansu.

"Kaga ikon Allah ko? Bamu ta6a tunanin zamu sake haduwaba saigashi Allah ya hadamu again amatsayin in-laws" inji zahradini yana murmushi.

Kafe zahradinin yayi da idanu yanason tuno inda yasan face din.

Suma kingin mutanen falon kafeshi sukayi da idanu except Ashraf da haryanzu idanunshi ke a lumshe itakuma saudart kanta a sadde.

Ganin yakasa gano inda yasanshi ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "I gave up, Sorry but i can't recall you"

Murmushi kawu zahradini yayi sannan yace "zahradini ne, qani ga Auwal, *Auwal direba*"


Cak komai dake motsi ajikib Alhaji shamsu yatsaya na wucin gadi, ya kafe zahradini da idanu yayinda sunan wanda ya ambata yashiga masa amsa kuwa a kunne.

"Alhaji shamsu muhd na wudil.... *tsohon amininka*"

Gabanshine ya yanke yafadi yawara idanu yana kallon zahradini cikin dimaucewa


"Sh...shamsu? Shamsu na? Shamsu na? Kaine shamsu na?" Yafada cikin rawar murya yana nuna zahradini da yatsarshi dake 6ari.

Dan dagowa itama saudart tayi tana satan kallon daddy cikin rashin fahimta ganin yadda daddy duk ya rude lokaci guda.

Kafin kyaftawar ido har daddy ya qaraso gaban zahradini ya kamo hannunshi duka
"Kana nan dama shamsu? Ina ka shiga? Na nemeka koina, ashe zamu sake haduwa?"

Duk kallo occupant din falon suke binsu dashi cikin rashin fahimta banda ashraf dabe dagoba haryanzu.

"A'a bani bane, zahradini ne qannenshi"

"To yana ina? Ina yake? Ashe zamu qara haduwa dama?" Yafada yana wurwurga idanunshi dasuka kada a falon kamar mai nemanshi, kallo daya zakamashi kasan baya cikin hayyacinshi.

Kawu ibrahim dake kallonsu shima tundazu shaye da mammakin ganin reaction din Alhaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login