Showing 21001 words to 24000 words out of 173829 words

Chapter 8 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1105

Ina hankalinki yatafi? Ehh?"

"Am sorry mamy, bazan sake ba"

"Kima sake din sakaran banza, yaje yawani nunaki wa mutane, idan be aureki bafa? Wannan ai sakarcine..."

Nan taita fada ta inda take shiga batanan take fitaba, itadai Saudart haquri kawai take bata, nan Daga baya fadan yakoma nasiha, nasiha mai ratsa jiki tayi mata har saida zuciyar Saudart ta karye tafara hawaye.

Sai wajajen 12:pm ta var gidan Tawuce bakery.

A bakery ma ranan ranta a dagule yake, anya tayima kanta adalci data yarda da wannan auren, ga kuma sa6ama ubangijinta datayi.

Haka tawuni ranan zuciya a cunkushe sai istigfari take akan Allah ya yafemata da ita da daddynta.





Suna zaune falo suna kallo sukaji sukaji qarar doorbell.

Ganin baby batada niyyar motsawa yasa Ummy cewa
"Bakiji ana danna bell ne?"

"Wayyo Ummy dan Allah kiyi hqr idan natashi wuceni za'ayi kuma ba damar tariyowa, please kiyi hqr"

"Zaki tashi ne ko saina sa6amiki"

Baki a cinne ta tashi tanufi kofar tanayi tana waigen tvn

Qara danna doorbell da'akayi yasa ta qarasa wajen kofar a afusace tana cewa
"Ana zuwa, haan?"

Tana budewa sukayi four eyes da Ashraf sai Sadeeq bayanshi.

Saurin ja dabaya tadan yi tana yaqe

"Laa! Ashe kune? S..sannunku Ku shigo"

Wata uwar Harara ya gallamata sannan yashigo zaiwuce tayi saurin ra6ewa ya wuce, Sadeeq na shima yashigo yana dariya ganin yadda baby ta bude azafafe tana ganin Ashraf Duk ta daburce.

Harara ya wanka mashi.

"Meye abin dariyar?"

Sake dariyar yayi cikin tsokana yafara waqa

"Taji tsoro abata ruwan mad'aci ta kuskure..."

Kwa6e fuska tayi cikin shagwa6a tareda juyawa zata tafi tana cewa

"Wlh yaya Sadeeq mun 6ata kuma baxamu shiryaba nan kusa"

Wari idanu yayi ya biyota ganin tasa gudu.

"Haba autas, tsaya mana"

Amma harta haye.

Dariya yayi sannan yajuyo suka hada ido da Ashraf daketa yimashi antayen Harara tundazu.

Shima antayamashi nashi yayi sannan ya qaraso falon a kunyace ya zauna gefen Ashraf.

Zamowa yayi Daga kujera ya tsugunna yana gaida Ummy.

Amsawa tayi cikin fara'a tana tambayar Yasu mamanshi.

Komawa yayi kan kujerar yana amsamata suna lfy.

Nan fira ta 6arke don dama Sadeeq dan gidan Ummy ne, kusan Duk weekend dama yana zuwa gidan ya yini kamar yadda shima Ashraf ke zuwa gidansu, idan suka yini gidansu Ashraf ranar Saturday to gidansu Sadeeq zasu yini ran Sunday, idan kuma ran Saturday sun yini gidansu Sadeeq to ran Sunday gidansu Ashraf zasu yini.

Wannan abota nasu na burge mutane musanmman su Ummy, don da wuya kaji Kansu, idanma sun 6ata saikiga babu mai sukuni acikinsu har saisun shirya.



Hira suketayi gwanin sha'awa dama Sadeeq qaqa lafiyar giwa? Ashraf kau takaici ya rufeshi sai zungurin Sadeeq yake kan yafadi abinda yakawosu Amma yayi banza dashi kamar bejin zungurin, dariya fall ranshi.

Dadai Ashraf yaga abin nashi rainin hankali ne saiyayi Fushi ya tashi yana cewa Ummy zai shigo, a fito lafiya tayimashi sannan yayi gaba kamar zai tashi sama.

Dariya Sadeeq yayi yana girgiza kai saida ya sake 6ata kusan mintuna talatin sannan yacema Ummy bari shima ya haura.

Izuwa yanzu saura kadan Ashraf yayi bindiga.

Da sallama Sadeeq yashiga yana qumshe dariya.

Ashraf dake rigingine kan gado kafaffunshi zube qasa yayi saurin tashi kamar Wanda aka tsikara,

"Get out dan ubanka!"

Waro idanu Sadeeq yayi sannan ya dan dafe kai

"Ohni wannan uban nawa na shan zafi wajenka"

"Nace out!"

"Sai kazo ka fiddani din, ba'a fita yafada yana riqe qugu yana girgiza kamar dan daudu.

Tasowa Ashraf yayi yana nad'e hannun Riga yana cewa

" wlh koka fita ko in fiddaka"

Cikin girgiza Sadeeq yace

"Fiddani din"

Nan suka hau kokowa, sai Ashraf takaishi bakin kofa dakyar sai yakuma zille yadawo ciki dagudu, shikuma bazai haqura ba, yana nishi yana komai zai sake maidoshi bakin kofa saikuma yasake zillewa yadawo yana kyakyatamashi dariya.

Babu abinda ke tashi dakin sai nishi da dariyar Sadeeq.

Ganin babu sarki sai Allah yasa Ashraf haqura yawani laftashi kan kujera yamike yana haqi

"Shege.. Rusheshen banza"

Dariya Sadeeq keyi sosai

"Naji raggo ajeebo kawai, d'an ni dinne bazaka iya fiddawaba? Shame!!"

Tsaki yaja yawuce bedroom dinshi yana gunguni.

Shidai Sadeeq saida yagama dariyarshi sannan ya tashi ya shiga bedroom din yaga Ashe wanka yashiga.

"Woo yaji maza dole yaje ya watsa koko juye akeyi oho?"

Ashraf dake jinshi yaja tsaki kawai.

Sai Bayan kusan 20mins Ashraf yafito yana tsane jiki fuska a tamke.

Ganin Sadeeq na lasta mashi laptop yasa yaje ya kwace yana mashi mugun kallo

"Bi sannu kar towel din ya kunce inshiga uku, ca6! Dakau Saudart saita daure ni"

Tsaki yaja yana ajiye laptop din kan mirror.

"Get out zan shirya"

"Yo ai hikenan" inji Sadeeq shima yana Fadawa bandakin.

Koda yafito Ashraf harya bar bedroom din.

Bude closet din Ashraf yayi yaza6i wasu qananun kaya yasaka sannan yafito ya iske Ashraf falo yana kur6ar coffee.

Shima hada coffeen yayi yazo ya zauna kusadashi yana kur6a.

"Wai dude Duk hade haden rannan Duk na menene?"

Banza yayi dashi

"Kaji?"

"Please ka kyaleni Sadeeq, please"

"Haba aminin, kayi hqr ka gayamin, please"

Harara ya antayamashi.

"Dan ubanka ya mukayi dakai?"
"Name fa?"

"Bansaniba"

"Wohoho, please ka gayamin mana, idan Nasani zan nuna ban sani bane"

"Na nawa kuma? D'an rainin sense kawai"

"Naji, yi hqr ka gayamin"

"Mtcheew, batun damn contract marriage din mana, ya mukayi dakai, ba cewa nayi ka gayama Ummy ba?"

"Sannu😒 niga rasa kunya kazar birni ko?"

"Au bazaka fada mataba?"

"Ni zan aureta? Kaji qarfin hali"

"Ok, sai kaje kacema wannan tsohon banzan ya dawomin da kudina nafasa"

"Wannan kuma ake kira impossible tense, ka lashe"

Shaqoshi yayi

"Dan ubanka ina wasa dakai?"

"A'a..A'a, yi hqr, bari mufita zan gayamata, Shikenan?"

Sakinshi yayi yana Harara

"Idiot"

Shima harararshi yayi.

"Expired element".







*****************************************

" Ina jinka Sadeeq"

Sosa qeya yasakeyi sannan yace
"Ehmm dama..dama.."

Takaici kamar Ashraf yayi me? Jibeshi kamar wani na Allah.

"Sadeeq Wai ya haka? Menene Wai?"

"Ummy dama Ashraf ne... Ehm...yakeson..ehm.. Atura...ehm atura gidansu Saudart"

Ya qarasa zancen yana susar qeya.

Sunkuyar dakai Ashraf yayi cikin kunya da takaicin Sadeeq, kai Sadeeq mumu ne, haka ake magana? Aikau zaici ubanshi.

Murmushi Ummy tasaki cikin jindadi

"A'a Masha Allah, shine kuke wani sinne sinne Tun dazun? Kai alhamdulilah, aikau zan aika Ayi magana da kawunanka insha Allah, Allah yayi muku albarka"

Sadeeq cikin qara sinne kai da sigar Neman magana yace

"Amin Ummy, Wai kuma yace kar asa da nisa. In so samune..."

Wani dundu Ashraf yakai mashi abaya Wanda ya hanashi qarasawa.

Tashi Sadeeq yayi cikin dariya yagudu sama ganin Ashraf na niyyar kaimashi wani dukan.

Shima Ashraf maramashi baya yayi sukayi sama.


Dariya sosai Ummy keyimusu, abotarsu na burgeta sosai.

Tashi tayi don ta dauko wayarta takira kawunnanshi don sanar dasu wannan abun farincikin...✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




023




Kan kace me? Har maganar Neman auran A.A ya zagaye family, Masu murna nayi, yan baqin ciki nayi, Masu Kishi nayi.

Nan da nan kawunnan sukayi bincike akan Saudart kuma suka sami gamshashen sakamako.

Cikin dan qanqanin lokaci aka fidda ranar da zasuje Neman auran Saudart.

Alhaji shamsu baki har kunne dayaji wannan daddadan labarin.

Shirye shiryen tarbar manyan baqi yake kamar zai tarbi sarakuna.

Sai rawar kafa yake, burinshi ya burge ahalin A.A

Alhaji shamsu har office yaje ya tadda mijin mamy ya fadamashi abinda ake ciki don yanaso ya kasance harda dangin uwar Saudart wajen.

Sosai mijin mamy yaji dadi itama mamyn haka don haka itama ta sanarda danginta aka samu mutum daya sai Abba (wato mijin mamyn).

Saudart kwata kwata batasan wainar da'ake toyawaba, sai ranar Daren zuwansu wato asabar taja kamar daddy nacikin busy sosai.

Koda ta tambayeshi ce matayayi baqi zaiyi gobe. Bata kawo komai aranta ba tace Allah yakawosu lfy.


Ranar lahadi kamar yadda tasaba tana gama abinda take Tawuce gidan mamynta.

Nan suka hade da qannenta aka bude chafter fira, sunata bata labarin Maiduguri, dakuma tsarabar dasuka samo.

Itadai mamy sai binta take da kallo tanajin dadi at last Saudart zatayi aure, burin kowacce mahaifiya kenan idan diyarta takai minzalin aure to tayi.

Dukda Saudart ta lura da kallon datake mata saita share tacigaba da biyewa su Abdul.






A Bangaren su alhaji Shamsu kuwa, tarbar mutunci sukayima dangin A.A, sosai ahalin suka shiga ran dangin A.A saboda karamcinsu, Bayan anci ansha anyi wasa da dariya nan suka bada kudin mungani munaso, sosai adadin kudin yakusan rikitasu da farko sukaqi amsa saida aka Kai ruwa rana sannan suka amsa nan take aka tsaida ranar biki, nan da wata daya.

Taro ya watse lafiya, Alhaji shamsu sai godiya yakema su Abba da abokanshi daya gayyato nan suma suka Kama gabansu kowa zuciya fall da murna.




Zaune suke Saudart na karanta musu wani story book na yara. Duk sun zuba mata idanu kamar TV basusan ko motsawa tayi saboda yadda labarin ya dauko dadi, cikin nutsuwa take Masu karantun cikin lafiyayyen turancinta ga yadda take acting kamar itace don da anzo inda mayya ke magana saita qarama muryarta girma takoma naban tsoro, da anzo inda diyar sarki zatayi magana sai ta maqe murya, da anzo wajen kuka saita kwa6e fuska tana magana cikin muryar kuka.

Hakan yasa labarin kemusu dadi sosai kowa ya maida hankali yana sauraronta harda mamy dake zaune kan kujera tana saqar hannu.

Sallamar Abba ne ya katsesu, dukkansu dagowa sukayi suna amsa sallamar Saidai sa6anin da dasuke rugawa su rungumeshi yau kowa Daga inda yake zaune yake aikamashi sannu da zuwa don basusan abinda zai katse musu story din.

"To? Yau ba tarba? Wato antynku tazo anbar yayina ko?"

Dariya sukasa gabadaya harda Saudart.

"Abba sannu da dawowa" inji Saudart

"Yauwa daughter, ya weekend?"

"Alhamdulilah Abba"

"Oya kutashi mutafi sama, oya oya get up" tafada tana zungurin qeyarsu don suba su mamy waje.

"Saudart idan kin kaisu kidawo muyi magana"

Dukda gabanta yadan fadi saitayi murmushi tace "to Abba"

Sannan ta tisasu gaba suka haye sama.


Aminullah dake sama dama don acewarshi baya shiga cikin yara Wai karsu rainashi. Yana ganinsu yamiqe zaune yana hade rai.

"Anty lafiya naga kun dawo nan?"

Harara ta dalla mashi

"Lafiyar ce takawo hakan"

"Haba anty ni dan Allah Ku chanza room wadannan yaran damuna zasuyi da hayaniya" yafada yana gallama su Abdul Harara

"Sannu babba, wlh Saidai kai ka chanza room. Ace mutum kwata kwata beson qannenshi su ra6eshi? Kuma wlh karka saki ka ta6asu. Ka ta6asu nida Kaine" ta gallamashi Harara sannan tafice.


Afalo ta taddasu da alama suna cikin farinciki don fuskarsu Duk a washe suke.

Qarasowa tayi ta zauna qasa dan nesa dasu.

"Qaraso nan daughter"

A kunyace ta qaraso kusadashi tana sinne kai.

"Masha Allah, Alhamdulilah. Babu abinda zamuyi a wannan lokacin sai godewa Allah, dakuma fatan Allah ya sanya alhairi acikin lamarin.

Allah ya tabbatar da alhairi kuma yasa abokan rayuwane Ku har mutuwa ta raba"

Kan Saudart ya kulle sosai don tarasa inda batunshi ya dosa.

Nasiha sosai Abba yayimata mai kashe jiki mamy ma ta Dora da nata, sai Daga baya taji Abban nacewa ansa biki, waikuma bikinta da A.A ban da wata daya kacal.

Diff.. Wutar Saudart ta dauke, tashin hankali wanda bata ta6a tunanin zata shigeshiba tashiga, Aure? AUREN KWANGILA? kenan ya tabbata AUREN KWANGILA zatayi? Kenan ya tabbata A A din zata aura.

Zufa yaita qetomata Daga inda take zaune. Gabanta banda bugun uku uku babu abunda yake.

Sudai su mamy basu wani luraba, koda suka gama mata nasihar suka sassamata albarka sai suka sallameta.

Ahankali ta nufi stairs idanunta na kawo ruwa. Haka taita takawa ahankali har takai sama dakyar tashige wani dakin da babu kowa ciki ta fada kan gado tana lumshe idanu Wanda hakan yaba hawayen idanunta damar gangarowa.

Maido kallonta mamy tayi kan Abba dake kallonta itama adorably.

Rungumeshi tayi cikin farinciki shima ya qanqameta.

Saida ya dagota yaga Ashe hawaye take.

"Subhanalillah Rahma ya haka"

Share hawayen tayi tana murmushi

"Abbansu. Am very happy, words can't express my happiness, Wai yau diyata aka sama biki?"

"Saiki godewa Allah kuma azo afara shirye shirye don wannan biki da alama na manyane"

Dariya sukasa gabadaya nan mamy taita kiran yan uwa da abokan arziqi tana fadamusu shima Abba hakan take awajenshi don Saudart yarinya ce yar gata mai shiga ran jama'a koda yini daya tayi dasu.

Duk Wanda aka gayamawa sai yayi farinciki musanmman idan sukaji Wanda zata aura don aganinsu sun dace dajuna sosai.

A bangaren oga Alhaji shamsu hakan take, don tuni yafara yagama shelar sa bikin ga abokan kasuwancinshi da kuma abokan arziqi.

Nan suma sukaita tayashi murna suna mai fatan alhairi.


A bangaren baby kau labari nakai mata ta danna wani uban ihu tana tsalle.

"At last! At long last!!". Duk Wanda yaganta zaiyi zaton Murnar auren take Saidai ita Murnar nata kashi biyune na farko yayanta zai auri balarabiya kyakyawa mai kirki na biyu zai tafi yabar mata gidan ta wala ta Shana son ranta.

Dagudu ta haye sama ta lalubo wayanta ta dannama Saudart kira.

Saudart kau kuka take hurjanjan tana tunanin makomarta, ringing din wayarta yasata dan tsagaitawa ta kalli wayar, ganin mai kiranta yasata Jan tsaki ta kashe wayar gabadaya tayi cilli daita.

Ganin bata dagaba harta tsinke yasata sake bugawa nan taji switch off.

" Tofah? Halan kunyata takeji" tafada tana ta6e baki.

Datarta ta bude tahau direct Tawuce group din CLASSIC LADIES tayi breaking din news din, zokuga hauka wajensu teema sai kakkafi suke suna kicihi suna fadin yadda bikin zaizama one in town, sukau team Suzy ana la6e Saidai su karanta massages dinsu Amma anrasa wacce zata fito ta tanka.


Suzy kau hauka tuburan tafara dataji labarin sa auren, sai kurma ashar take dana Zage Zage.

Beebah ta dannama kira tana dauka tahau masifeta, ta inda take shiga batanan take fitaba, beebah taita kwantar mata da hankali akan tabari Allah yakaisu gobe har bakery dinta zasuje su tisiyeta.

Dakyar tasamu ta lalla6ata harta haqura Saidai zuciyarta uwa ana hura garwashi...✍



More comments, more post.

Gaskiya aqara flow din comments sunyi kadan.

Aqara ko in nad'e hannu😏


Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲


Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




024


Mu leqa hajji A.A😕



Kwance yake kan gadon dake dakin Sadeeq, ya wani rigingine yayi matashin kai da hannayenshi idanunshi a lumshe, Kai ka zata barci yake Amma idanunshi biyu hasalima sauraron Sadeeq daketa waya da abokanansu yana gayamusu sa biki yake.

Ya kusan mintuna talatin yana Abu guda, sai bugama mutane waya yake kai kace bikinshine akasa.

Ajiye wayar yayi Bayan yagama sannan yazo gefen Ashraf dake kwance haryanzu ya d'ad'a mashi bugu a cinya.

Bude idanu yayi bashiri ya tashi zaune.

"Kutt.. Dan ubanka ni ka daka?" Inji Ashraf yana kaimashi bugu shima.

Dojewa Sadeeq yayi yana dariya.

"Dan ubanka ka barni sai qone credit dina nake wajen kiran mutane Bayan Kaine ka cancanta kayi hakan"

"Mtcheew, waya saka? Meye na wani shela a auren da atattashi yan wattanni? Mtcheew ni wlh ba haka naso abin ya kasance ba, banaso kowa yasan da bikin saisu Ummy, suma dan dolene Amma dayake kai dan iska ne shine ka 6atamun tsari Tun a gathering" ya qarashe zancen yana lafta mashi Harara.

Ta6e baki Sadeeq yayi wanda tunda Ashraf yafara magana hankalinshi na kan waya.

"Yanzu dai yaushe zamu fara hado lefe? Ga wasu kayanan an turomin sunada kyau, Kaga saimu fara dasu ko? Kalla kagani"

Wani kallo Ashraf ke binshi dashi

"Are you kidding me? Wa zanma lefen? You're mad"

"Haba Ashraf, auren A.A sunkutukum ace babu lefe, me kakeson mutane suyi tunani akai?"


"Whatever Sadeeq, whatever, I don't care, suje suce koma menene abinda Nasani shine bazanyi wasting din kudinaba akan auren da ba dorarreba" ya qarashe zancen yana juyamishi baya.

Ta6e baki Sadeeq yayi kawai shima ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi.







Sai can da magriba Saudart takoma gida, Duk tayi suku suku daita, ga zazza6in dake Neman cin galaba akanta.

Dakyar tayi parking tafito, tafara tafiya ahankali zuwa cikin gidan.


A falo ta tadda daddy sai waya yake, saida ta saurara dakyau tagane order Kayan furniture yake badawa.

Ganinta dayayi yasashi ware mata hannu daya.

Dagudu ta qarasa wajenshi ta rungumeshi tana sakin kuka.

"Ok, hang on, I'll call you later"

Katse wayar yayi ya ajiye sannan yaqara jawota jikinshi yana rarrashi.

Jin jikinta yadau zafi yasa hankalinshi tashi.

"Subhanalillah, shalele? Zazza6i kike?"

Cikin muryar kuka tace
"Dad, dama aurena za'asa shine Baka damu da ka sanar daniba?"

"Am sorry shalele, kiyi hqr kinji?"

"Dad yanzu kenan dole saina aureshi? Daddy AUREN KWANGILA? Dad ni zanyi auren yan wattani?" Saikuma tafashe da kuka.

Tausayinta ne Yakama Alhaji shamsu Amma daya tuna dinbin alhairin dazai samu sai ya kawar da tausayin.

"Shalele ta, akwai dinbin alhairi a wannan auren, am telling you zaki godemin watarana"

Kukanta kawai tacigaba dayi don ita bata wani hango alhairi a wannan lamari.

Dakyar yasamu ya rarrasheta ya kaita har daki ya 6allamata magani tasha sannan ya rufeta da bargo yajamata kofa.

Haka taita juyi a gado gashi tanason tayi barci Amma barcin yaqi zuwa, ganin hakan yasata miqe wa ta dauro alwalla tayi nafila raqa'a biyu ta Dora da karatun Al qur'ani mai girma har barci barawo ya saceta kan sallayar.



WASHEGARI



babu laifi izuwa yanzu tadanji sauqin zuciyarta.
Daily routine dinta tayi sannan tayi wanka ta shirya cikin wata Arabian gown mai shigen bubu kalar maroon mai adon golden stones.

Saita yafa gyalen rigar in a simple way.

Yaukam an danyi kwalliya dob harda jambaki maroon aka gogama le6e.

Fitowa tayi cikin nutsuwa ta tako qasa, a falo taga daddynta tsaye yana daura agogo da alama shima fita zaiyi.

Murmushi tayi ta qaraso wajenshi a sanyaye.

"Daddy na" tafada a shagwa6e

"Na'am shalele ta, kai Amma fa kinyi kyau
" Kai daddy, ina kwana? "

"Lfy lau shalele, ya jikin?"

"Jiki alhamdulilah daddy, as you can see, bakery ma zani"

"To dakyau, yanzu muje na rakaki motarki ko?"

Qara shagwa6e fuska tayi

"Uhm uhm daddy, Nidai kai zaka kaini"

"Tofah, yau kice rigima akeji, to muje, anything for my princess"

Dariya tayi sannan suka fito hannunta cikin Nashi.

Budemata kofa yayi yana dan sunkuyawa dramatically

"Get in Mi princess"

Dariya tayi sannan tashiga, shima ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar suka fice.


Sosai Saudart taware sai fira suke suna dariya har suka iso bakeryn.

Har ciki ya rakata yana zagaya bakery din yana yaba cigaban da'aka samu sannan Daga bisani yaimata sallama ya kama gabanshi.



Dukda haryanzu tanajin dan damuwa a cikin zuciyarta haka ta danne ta Zage tanata aikinta kamar koda yaushe.

3:00pm

Maryam ce tashigo office din fuska babu walwala tac gaida Saudart.

"Lfy lau...wani Abu?"

"Yes ma'am, kinyi baqi" tafada still fuskarta cunkushe.

Dukda taga yanayin fuskarta saita basar don bata cika son shishigiba.

"Ok ashigo dasu"

Bayan yan sakonni kofar tasake budewa suka shigo.

Dagowa tayi don ganin su waye baqin.

Yanmata biyu tagani dukkansu babu mai shigar arziqi cikinsu.

Ta farkon Suzy sanye take cikin wata armless top sky blue mai fidda sura sai baqin straight skirt wanda yasha tsaga Daga qasa har zuwa cinya kanta sanye da hula baqa Wanda Rabin kai tarufe hakan zai Baka damar hangen gashin dokin data qarama kai, ga wani qaton Google data kwamama idanu Wanda ya rufe kusan Rabin fuskar.

Habeeba kau sanye take da crazy jeans sai wata Riga mai kamada shimi fara saita Dora yar ficikar jacket sama kalar wandon Itakau kan ko arziqin hular besamuba.

Sunci uwar kwalliya an fente

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login