Showing 57001 words to 60000 words out of 173829 words
meeting din daya kawosu.
Cikin farin suit mai Jan shirt daga ciki ya shirya, yasa necktie ja irin dan guntun nan, ya taje sumar kanshi daketa walqiya saboda gyara sannan ya feshe Jikinshi da turare sannan ya dauki briefcase dinshi ya fito.
Afalo ya isketa lafe jikin kujera idanunta a lumshe Amma yasan ba barci take ba, kallo daya yayimata ya dauke kai cikin basarwa yana gyara necktie dinshi.
Taji fitowarshi amma taqi bude idanu don iya shaqa ta shaqa.
"Coffee" yafada in his usual husky voice
Saurin bude idanu tayi tana kallonshi cikin mammaki, she was like, what the hell?
Shikau babu abinda yadameshi ya duqufa sai gyara takalminshi yake.
Ganin bata tashi ba yasashi dagowa yana kallonta, sai yaga itama shi take kallo fuskarnan har wani ja ja take don 6acin rai, abinda ta Dade yanaso kenan, ya 6atamata rai.
"Hello??" Yafada yana waving hannu a fuskarta
"Nace coffee and fried spiced egg" yafada cikin son qara qular daita
"What? Ni kuku ce?" Tafada cikin tsananin fishi don yau kwata kwata takasa controlling din fushin ta
"Then mecece? Am your boss kuma komai bazaki sai kinyi it's part of your job, after all biyanki zanyi ba kyauta bane" yafada Yanajin wani nishadi a zuciyarshi ganin sai qara hawa take
"Yes aiki nake maka but am not a cook, am a secretary for crying out loud" tafada tana yarfa hannuwa cikin fishi.
"Wannan ke ya shafa, nidai kawomin abinda nasaki, now!" Ya qarasa maganar cikin dan daga murya
Shiru tayi ranta a mugun 6ace, tunda take bata ta6a shiga 6acin rai data kasa controlling irin yau ba.
Ya shanyata na kusan 2hours sannan kuma yace ta hadamashi coffee harda wata shegiyar fried spiced egg?
Dakyar ta iya controlling din kanta sannan ta tashi fuu tashiga kitchen.
Binta yayi ta kallo harta shige sannan ya juyo yana murmushin jindadi
Cikin yan mintuna saigashi ta dawo riqeda mug din coffee ta diremashi a gabanshi tanufi hanyar dakinta a fusace
"Karki qara step guda anan" yafada yana dakatar daita.
"Kijirani ingama mutafi" yafada yana daukar mug din batareda yayi complaining din Rashin ganin kwan ba.
Nanma saida ya 6atamusu lokaci sannan ya gama sha ya miqe yayi gaba yana cewa "shall we"
Binshi tayi da mugun kallo sannan itama ta biyo bayanshi zuciyarta kamar zatayi bindiga.
Saida yashiga mota ya zauna sannan tafito.
Tunda tafito yake kallonta tacikin motar.
Ta taho sanye da fuskar angry bird yan kumatunta sun dan turo alamun she's still angry.
Tunda yake beta6a ganin Wanda fushi yaima kyau ba kamarta, kamar fuskar taita zama ahakan.
Ganin ta qaraso yasashi saurin kauda kai yana basarwa.
Bude kofar tayi ta shigo ta zauna still fuskarta a tamke jitake kamar taita ihu don haushi.
Kunna motar yayi yaja suka fita daga harabar gidan.
Tsit motar tayi kowa da abinda yasha mishi kai, saudart sai cika take tana batsewa, jitake kamar tayi kuka, sosai take missing yan Niger she badly want to call them.
"The meeting will hold at 2:00pm" taji yafada
Yaitayi kamar bata jishiba don ko kallon gefenshi batayiba.
Hakan yasashi juyowa yace
"Are you deaf?" Ya tambaya cikin husky voice
Juyowa tayi ta watsa mashi Lulu eyes dinta sannan ta dauke kai tana cewa "ok"
Shiru yayi shima ya kauda Kai yana lumshe ido yana budewa ahankali don shikadai yasan abinda yaji data watsamashi idanun nan.
Cigaba da tuqin yayi yana sauraron bugun zuciyarshi data sauya a take.
Itakau cigaba da kallon waje tayi tana kumburi gashi tana son cemashi ya biya dasu wajen saida layi amma takasa.
Kamar wasa sai gani tayi yayi parking gaban wani babban shagon siyarda wayoyi.
Hakan yasata saurin gyara zamanta daga kishingiden datake tana kallon wajen murmushi na su6ucemata batareda tasaniba.
Jin kamar ana kallonta yasata juyowa suka hada idanu, yawani basar ta hanyar gallamata harara yana ta6e baki.
Kauda Kai tayi tana cewa "oho dai" cikin zuciyarta amma qasan zuciyarta fall farinciki at last zata samu kiransu daddy
Saida tabari yafita sannan itama tafito lokacin harya shigewarshi, hakan yasa itama ta shiga zuciyarta fall murna
Direct wajen wani saurayi taje cikin masu saida wayoyin shagon
"Hi" tafada
"Hello ma'am you're welcome, wane taimako zan iya yimiki?" Yafada cikin murmushi
"Layi nakeso" duk a harshen turanci suke maganar
Nan ya fiddomata ta sayi guda biyu tasaka nan take
"Zai fara aiki bayan awa daya" yafada mata yana bata receipt
"Ok thanks" tafada tana amsa fuskarta fall murna
Waje tafita fuskarta a sake sa6anin dazu ta taddashi jingine da motar ya rungume hannu a qirji.
Qarasowa tayi ahankali zata zagaya ya dakatar daita da "take" yana cillomata makullan motar.
Cafewa tayi tana kallonshi da alamun tambaya
"Drive us ai ba nikadai na iya driving ba" yafada yana zagayawa inda take zama
Mere baki tayi sannan tadawo ta bude mazaunin driver tashiga ta kunna motar sannan tajasu cikin driving dinta mai burgewa.
Tafiya suka fara yana gwada mata hanya har suka iso wani shahararre kuma qawattacen hotel.
"Ok shiga" yafada yana danne dannenshi.
Dan jimm tayi kamar zatayi magana saikuma tafasa ta shiga ta samu wuri a parking lot tayi parking.
Fitowa sukayi kusan tare suna kallon environment din.
Jin ana kabbara yasashi basu umarnin sufara sallah sannan.
Masjid din hotel din suka shiga shi bangaren maza ita na mata don yin sallar.
Koda aka gama sallar tayi addu'o'inta saita fito.
Hangoshi tayi da wasu mutane uku duk cikin shigar suit, biyu farare daya baqi suna magana da alama sune zasuyi meeting din dasu.
Qarasowa tayi wajen cikin Sakin fuska tana gaishesu suna amsawa Suma cikin fara'a
"Meet my secretary, Miss saudart shamsu" inji Ashraf yana nunata
"Nice meeting you miss" suka hada baki wajen fadin haka.
"My pleasure sir(s)" tafada cikin girmamawa
"Shall we?" Inji baqin cikin mutanen yana nuna hanyar ciki.
"Sure" duk sukace gabadaya suka dunguma suka shiga ciki suna tafiya suna fira jefi jefi...✍
Insha Allah idan nasamu lokaci zakuga next page ko zuwa dare ne amma idan kukaji shiru kuyimin uzuri🙏
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
048
Restaurant din hotel din sukayi reserving don gudanar da meeting din.
Zauna suka kan kujerun dake zagayeda wani round table, kowanne da robar swan a gabanshi da glass cup duk sunyi shiru suna sauraron bayyañin da daga daga cikin mutanen mai suna *Hussain* keyi.
Meeting ne akan wani contract na ordern gwalagwalai dazasuyi, kasancewar companyn A.A companine na dealer gwalagwalai da zinarai, yana daya daga cikin companyn dayayi fice a Nigeria dama Africa gabadaya, yana ordering din gwalagwalai a qasashe daban daban.
To anan ma hakan take, zuwa yayi don yin ordern wasu latest design na gwalagwalan masu tsadan gaske don sabbin design ne don ba'a gama saninsu a duniya ba.
Wani qaramin akwatin glass ne a tsakiyar table din Wanda ke dauke da sample din gold din.
Saida Hussain yagama 6a66atunshi sannan ya buqaci su duba suga ingancinshi.
Budewa baqin cikinsu yayi ya fiddo ya miqama saudart dake gefen Ashraf, ta amsa sannan ta miqama Ashraf.
Sundan Dade suna dubawa (Ashraf & saudart) suna jujjuyawa suna dan qus qus tsakaninsu da alamun shawara suke yankewa.
Sudai mutanen kallonsu suke har suka gama sannan Ashraf ya maidama saudart Itakuma ta miqama Wanda yabata.
Cikin inganttaciyar turancinta tace
"Yayi kyau sosai, amma kunzo mana da kala kalan designs dinsu ne, munason mu za6a" tafada tana kallonsu, Ashraf dake gefenta na kada kai alamun abinda tafada gaskiya ne
Baqin Wanda yakira kanshi da *zahid* yace
" sosaima, gashi Ku za6a" yafada yana bude musu laptop ya shiga hotunansu sannan ya turomusu Gabansu.
Nan suka shiga dubawa suna za6an choice dinsu suna qus qus, idan ka gansu a lokacin baka ta6a tunanin tom & jerry dinnan ne don dukansu sunci serious sosai.
Saida suka za6i iya Wanda sukeso sannan aka maida musu laptop din.
Nan sukayi cinikin iya adadin dazasu saya Wanda za'a turomusu ta jirgin ruwa bisa yarjejeniyar zasu fara bada Rabin kudin anan, Rabin kuma sai kaya sun isa.
Anan aka yanke shawarar zasu sake haduwa a companyn su Hussain din ranar Monday don biyan Rabin kudin kamar yadda suka tsara sannan suyi abun a rubuce kowa yasa hannu saboda yazama shaida.
Awa daya meeting din ya dauke su sannan su saudart suka miqe don tafiya kowanne fuskarshi fall fara'a.
Har mota suka rakasu, dayake makullan motar na hannun saudart sai kawai tashiga mazaunin driver ta zauna tana jiran Ashraf dahar yanzu suke magana da mutanen.
Can sukayi musabaha sannan shima yashiga motar suka bar hotel din.
Tunda suka hau hanya babu Wanda yacewa kowa uffan gar suka qarasa gida.
Lokacin da suka iso har anfara kiraye kirayen sallar la'asar don haka bema shiga gidanba yawuce masjid din estate din Itakuma ta shigewarta ciki don gabatarda tata.
Bayan tagama sallar ne taciro wayarta tafara kiran yan Niger.
Da daddy tafara, sosai suka sha fira dashi Wanda Rabi shagwa6a ce take zuba mashi yana biyemata sannan takira mamy nan Suma suka gaisa da kowa na gidan kowanne nabata sabtun tsarabar dazatayi mashi sai dariya take musu.
Sai bayan sunyi sallama sannan ta bugama Ummy.
Sosai Ummy taji dadin kiran nata, sunsha fira sosai kafin takaima baby wayar
As usual ihun nan nata na hauka taitayi da sunan murna, nan sukasha fira kamar ba gobe sai tsokanarta baby take wai ya? An samu tsarabar nata koko da saura? Itakuma tana amsa mata da zata gane kuranta ne saita gayamashi.
Haka sukaita firarsu, dakyar suka ajiye wayar kowanne najin qaunar dan uwanshi har cikin zuciyarshi.
***********************************
Tana cikin shirin kwanciya kasancewar har Tara tayi taji ana bubbuga kofarta.
Dan jimm tayi daga gyaran zanen gadon datake ta kalli kofar.
Jin ansake bugowa yasata Sakin bedsheet din ta zura hijabin sallarta akan doguwar rigar barcinta sannan tanufi kofar.
Tana budewa taga shine, gyara tsayuwarta tayi tana kallonshi da alamar tambaya.
"Coffee.. Kikawomin a study room" yafada yana wucewa.
Galala tabishi da kallo harya shige.
Mene? Coffee cikin Daren nan? Wannan wane irin wahalarwa ne?
Mutum na shirin barci awani tsiromashi aikin hada coffee?
Sosai ranta ya 6aci don barci ke idanunta burinta kawai ta kwanta.
Babu yadda ta iya haka tawuce kitchen din ranta a jagule, tsaki kau tafishi yafi cikin kwando kafin tagama hadawa.
A study room din tasameshi zaune gaban laptop sai danne danne yakeyi.
Ciki ciki tayi sallama sannan ta qaraso gabanshi kamar bataso sannan ta dungure mashi mug din coffeen a kan table din gabanshi tajuya da niyyar komawa.
"Come back here" yafada batareda ya dago daga kan laptop din ba.
Saida tayi jimm kaman bazata juyoba sannan tajuyo tadawo gabanshi ta tsaya.
Dagowa yayi yana kallon yadda taketa faman kumburi tawani tsaya mashi akai.
"Da ina zaki?" Ya tambayeta
"Ina bayan dakina?" Tafada cikin son danne fushinta
"Na sallameki ne?" Ya fada cikin son qular daita
"Ba na hada cofeen ba? Ni Am sleepy wlh" tafada tana turo baki.
"Barci? Dama barci ya kawoki nan?"
"Bashi ya kawoni ba, amma ai yanzu na hadamaka coffee din ko? Zan iya tafiya ko?" Tafada cikin tsiwa tsiwa
Daukar mug din cofeen yayi ya kafa Kai ya shanye sannan ya diremata
"Make another one"
Wani Abu taji ta taso ya toshe mata maqoshi, Kutt...
"Bakijiba? Nace ki hado wani" tafada yana kallon yadda fuskarta ke yin ja ja ja ja alamun tana cikin tsananin 6acin rai.
Batace komai ba ta figi mug din ta fice tana bugomashi kofa har yana toshe kunne.
Binta yayi da kallo sannan ya jinjina Kai yana murmushi
"Shima wannan you'll pay for it" yafada yana maida hankalinshi kan laptop din.
Can saigata ta dawo ta qara dungure mashi mug din har coffee din badan zubewa.
Dagowa yayi yana kallonta da mammaki
"Wai kwakwalki qalau kuwa?"
'Kai ka cancanci tambayar' tafada a zuciyarta
Banza tayi dashi ta juyamashi qeya.
Qwafa yayi ya cigaba da danne dannenshi sannan ya dauki mug din yakai baki da niyyar kur6a.
Kur6a daya yayi yayi saurin furzoshi ko maqoshi be kaiba saboda wani zau dayaji a harshenshi.
Kauda Kai tayi saurin yi tana son hadiye dariyarta
"Kutt... Uban me kika samun a coffee? Kasheni zakiyi?" Ya tambaya yana kallonta cikin mammaki
"Ni me nasa?" Ta tambaya tana dan matsawa baya.
"Me kika sa ko? To wlh saikin shanyeshi yafada yana daukar mug din ya nufota.
Ai a sittin tayi wani turning tana fasa qara ta bude kofar tayi waje tana tsuwa.
Binta shima yayi dagudu saidai kafin ya taddota harta shige daki ta Danna sakata sama da qasa tana numfashi sama sama.
Bubbuga kofar yashiga yi da karfi yana cewa tazo ta bude amma tayi banza dashi saima antayama kofar harara datake
" to wlh ki tabbatar nan zaki cigaba da zama har abada don ido na idonki..." Sai yayi Kwafa yana jinjina kai sannan yayi tafiyarshi
"Idan na fito karka barni da rai, mugu kawai mummuna" tafada tana murguda baki sannan ta haye gado tashige cikin bargo...✍
Kuyi manage🙏
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
Sorry for the late post🙏
Yanzu bazaku dinga ganin post ba akai akai, munada hidima, please bear with me🙏
Washegari Friday, bata yarda tafito daga dakinta ba saida ta tabbatar yabar gidan gabadaya.
Sai a sannan tasamu kwanciyar hankalin fitowa don yin aikace aikacen datasaba.
Saida ta share koina, ta goge, tabi da freshener sannan tashiga kitchen don samarma kanta abin ci.
Tana cikin suyar kwai taji ana bubbuga kofa.
Gabanta ne yafadi jin bubbugar kofar abinka da marar gaskiya don duk a tunaninta Ashraf ne.
Kwan ta kashe batareda ya ida soyuwaba ta saka a plate ta jidi kayan breakfast din tayi daki dasu sannan ta dawo cikin sanda ta qaraso kofar tana leqen wajen ta wurin nan na kofa don ganin waye.
Ganin wasu yanmata biyu tsaye yasata Sakin ajiyar zuciya sannan tabude.
Yanmata biyu tagani tsaye fararen fata kowacce tasha kayan sanyinta sai washe mata baki suke.
Itama washe masu nata bakin tayi Tanadan matsawa don basu wuri sy shiga tana cewa
"Please come in"
Babu musu suka shigo suna bin falon da kallo suna murmushi.
Maida kofar tayi ta rufe sannan ta qaraso ciki tana musu tayin zama cikin fara'a
Babu musu duk suka zauna
"Bari nakawo muku ruwa" tafada cikin turanci
Dakatar daita daya tayi dacewa
"A'a yar uwa, murda ga gidanmu nan kusada ku, bawani tafiya mai tsawo mukayi ba kuma ma sanyi ake ba'a cika shan ruwa ba"
Murmushi saudart tayi sannan ta koma ta zauna tana cewa
"Kenan Ku maqobtanmu ne?"
"Eh mana, fa gidanmu nan No 35 Itakuma wannan No 37" inji Wanda tayi magana dazu
"Wow, nice to meet you" tafada cikin Sakin fuska.
"Thank you, sunana Loveth wannan kuma Reyna" inji mai maganar
"Wow nice name, ni sunana saudart" tafada tana murmushi
"Wow nice name too, amma Ku baqi ne ko?" Inji Wanda aka kira da Reyna
"Eh kwananmu biyu yau" saudart tabasu amsa
"Ayyah ai naganku jiya dazaku fita, banma San akwai mutane saida naganku jiya" inji Loveth
"Ai saboda bamu Dade bane shiyasa" saudart ta amsa
"Ok, dama zuwa mukayi muji zaki samu zuwa wajen hada kayan Good Friday?"
"Good Friday?* inji saudart cikin Rashin fahimta
"Eh, good Friday wani taro ne haka mukeyi duk ranar Friday, duka yan yankinan zasu hadu don zumunci, anan muke sanin baqin dasuka shigo kuma mu qulla zumunci" inji Loveth
Reyna ta Dora dacewa
"Akwai wata mata a block 39, doctor ce kuma duk ta fimu shekaru, a gidan ta duk muke taruwa mu hada kayan da za'a dan ta6a a gathering din, muna zuwane da marece mukama aikin ayi agama da wuri, idan zaki samu damar zuwa saiki leqo ayi dake"
"Wow yayi kyau sosai, insha Allah zan leqo idan nasamu dama" inji saudart tana murmushi
"To Allah yasa" suka fada suna tashi zasu tafi.
Har waje ta rakasu suka nuna mata gidan doctor din daga nesa sannan sukayi sallama suka tafi.
*5:00pm*
Fitowa tayi cikin shigarta ta doguwar rigar atamfa mai A shape ta Dora Jan rigar sanyi mai hula akai kasancewar cikin atamfar akwai kalar ka, wannan karon ta Dora hular rigar sanyin.
Hannunta daya riqeda wayarta dayan kuma riqeda makullan gidan.
Direct gidan dasuka gwadamata ta nufa tana tafe tana qarewa surrounding din dayayi tsit kallo.
Tun kafin ta isa gidan tafara jin hayaniya da shewa shewa na fitowa daga gidan ga qamshin girki daya fara ziyartar hancinta.
Ida Qarasowa tayi tana kallon kofar gidan da akasa *39* agaban gidan
Ahankali tafara bugawa amma kasancewar cikin akwai hayaniya sosai babu Wanda yajita.
Ganin haka yasata fara bubbugawa da qarfi.
Ta dan Dade tana bubbugawa sannan tajiyo taku alamun ana tahowa hakan yasata gyara tsayuwarta tana kallon kofar.
Ana budewa tayi ido hudu da Reyna dake sanye da apron.
"Yeah! Gatanan tazo" tafada tana leqa bayanta da alamu da mutanen ciki take
Kan kace me? Sai gasu sunata leqowa don ganinta
Murmushi tayi cikin jin kunyar yadda suka zubamata idanu
"Hyy" tafada tana dagamadu hannu
"Hello... Hyy...hey" duk suka amsa gabadaya suna mata murmushi
Loveth ce ta leqo sanye da apron hannunta duk fulawa da alamun kwabi take.
"Welcome saudart, Ku matsa tashigo mana, kunwani tare hanya" tafada tana kama hannun saudart suna shiga ciki, taja hannunta har kitchen din gidan Wanda duk tsarin gidan irin nasu saudart ne kawai banbancin kayan ciki ne
Wata mata Wanda aqalla zatakai shekaru 40 suka gani da wasu yanmata suna aiki suna fira.
"Dr zahra, ga baquwar nan tazo"
Nan duk suka dago suna kallonta
"Wow she's so cute, welcome baquwar mu" tafada tana Qarasowa wajen ta tana murmushi
Itama murmushin ta maidamata tana gaidata sannan suka gaisa da duk yanmatan gidan sannan aka koma bakin aiki.
"Amma daga Africa kike ko?" Inji Dr zahra
"Eh daga Nigeria"
"Wow, ni daga Pakistan nake amma na ta6a zuwa Nigeria, a wane state kike?"
"A kano state" inji saudart tana amsar wuqar dake hannun Dr din da cabbage datake yankawa.
"Ohh nikuma Abuja naje, ai Nigeria is a lovely country, har yanzu nakasa mantawa daita" inji Dr zahra din
Haka sukaita fira a tsakaninsu, dayake saudart batada baqunta nan da nan ta ware duma fira kamar sun Dade da sanin juna sai tsokanar juna suke.
Babu abinda ke tashi a gidan sai hayaniya da darairaku.
Sosai saudart taji dadin zuwa gidan don tasamu nishadi sosai, da yanzu tana can qunqume cikin gida babu abokin fira.
Abinka da aikin yawa nan da nan suka kammala komai.
Tare dasu Loveth suka fito daga gidan suka Kamo hanyar gida suna tafe suna fira har suka iso gidansu saudart.
Lokacin har anfara kiraye kirayen magrib. Sallama sukayi da juna akan saisun hadu anjima.
*************************************
Tsaye take gaban gadonta sai kallon kayyayakin data baza kan gado take tarasa Wanda zata za6a don ruwan ido.
Can dai ta dauki wata dark purple din Arabian gown din roba mai dogon hannu tareda farar jacket marar hannu mai gashi ajiki Wanda takawo har gwiwa sannan ta yane kanta da farin gyale.
Kamar kullum yauma simple makeup tayi, sai kuma purple janbakin datasa abaki ta feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi sannan ta dauki wayarta ta fito.
Direct gidan Dr zahra tanufa.
Nan ta tarda su Loveth da sauransu ansha gayu sai hada hadan fita da abinci suke.
Suna ganinta suka