Showing 45001 words to 48000 words out of 173829 words

Chapter 16 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1114

Dole ne saikin gwada bakida manners? Well unfortunately nasani, nasan you're ill-mannered before I even get to know you"


Kasa cewa komai tayi sai kallonshi datake ga wani daci datake ji cikin maqoshinta jin ya kirata marar manner.

"Kina sauri zaki yawon tazubar ko? Well I don't fucking care ina zaki, kawai don't drag my good name to mud, don a matsayin Matar A'A kike ga mutane, behave yourself karki kuskure mutunci na ya ta6u a idon jama'a"

Yayimata wani kallon up and down sannan yawuce ciki yabarta nan tsaye.


Bata waigo ta kalleshiba dayake wucewa, zuciyarta takeji namata wani irin zafi kamar ana hura garwashi aciki.

Muquut.. Ta hadiye yawu mai daci daya taru abakinta ta gyara rolling din veil dinta jin ansake yin horn.

Bude kofar tayi ta fita asanyaye ranta a matuqar 6ace, tafito har wajen gate wajen drivern daya zo daukarta tabude bayan seat ta zauna.

Cikin fara'a drivern yace
"Sannu da isowa hajiya"
Don dama akwai kyakyawar alaqa tsakanin ta da tan aikinsu don lafiya tana wasa da dariya dasu.

Yaqe tayi tace "yauwa bala, ya aiki?"

Da alhamdullilah ya amsa daga nan kuma babu Wanda yasake magana.

Shiru tayi abaya tana sauraron tafiyar motarsu a kwalta, yayinda abinda yafaru yanzu ke dawomata.


Babu abinda yafi bata haushi kamar marar manner daya kirata.

Itadai tasan qumewa sukayi kuma both of them sunji zafin, why zaiyi insulting dinta?


Wannan na cikin abubuwan dayasa tun farko take qauracewa ganinshi, a duniya idan akwai abinda ta tsana to cin mutunci ne amma batun yauba ta lura ya qware akan hakan shiyasa ma batason haduwarsu don bazata iya dauka ba, tafison har ta qaraci zamanta su rabu babu abinda yashiga tsakaninsu daidai da maganar fatar baki.

Jin an tsaya ana horn yasata sauke ajiyar zuciya tana kauda tunaninta don yaune ranar farkonta a aiki yakamata tazama tana cikin nutsuwarta.


Direct parking space yayi daita sannan yasamu wuri yayi parking.

Ajiyar zuciya tasake saki tana addu'ar farawa a sa'a sannan tasa hannu ta bude murfin kofar tafito.


Abinda tagani ne yasa numfashinta daukewa na wuccen gadi....✍




Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)




Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka qaramana zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲


Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲


Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





039



Mitsitsike idanunta tayi taqara kallon wajen don tabbatar da ba idanunta kemata gizo ba amma still wajen ne, companyn ne.

Juyawa tayi wajen bala dake niyyar yin reverse tace

"Bala ka tabbatar nan ne inda Dad yace ka kawoni?"

Cikin yashe baki yace "eh hajiya, nan ne"


Sauke numfashi tayi tana dafa goshinta tareda lumshe idanu.

*kiyimin alqawari bazakiyi disappointing dinaba, zaki qar6i aikin nan duk yadda kikaga yazo miki*

Maganar dad na jiya yadawo mata a qwanya.

"Why dad? Why?"


"Hajiya? Lafiya dai ko?" Inji bala daketa kallonta tundazu.

Bude idanunta dasuka fara canza launi tayi ta kalleshi tama kasa magana.


"You're welcome Mrs A.A" Sukaji anfada daga bayan su.

Juyawa sukayi gabadaya suna kallon mai maganar.

Sadeeq ne ya qaraso yana washe baki yana cewa

"You're highly welcome ma'am, mushiga ciki mana"

Kallonshi tayi sannan ta daga kai tana bin company din da kallo batareda ta bayyanar da yanayin datake aciki ba a fuska ta sake maida kallonta kan sadeeq tasaki murmushin takaici sannan tajuya ta fara kiciniyar bude motar dasukazo daita.

"Erm.. Mrs A.A please listen to me, atleast mufara shiga ciki inmiki bayani"

Banza tayi dashi ta bude kofar zata shiga

"Mrs A.A..."

"A.A my foot! Karka sake dangantani da sunan nan" tafada a fusace

"Amma wannan ne company din dazaki..."

"Fuck the company!" Tafada tana jawo murfin motar da qarfi.

Tsawa ta dakama bala akan yashigo sutafi, aikau dagudu ya bude motar yashiga ya tada suka fice.

"Shit!" Sadeeq yafada yana riqeda kugu.





Gudu bala keta tsulawa batareda yasan inda zashiba saidai kuma yana tsoron tambayarta don yasan idan tayi fushi akan kowama hucewa take duk yadda kau kuke daita.

Can dai ya sadaqat yace
"Ranki shi Dade ina zamu?"

Wani kallo ta watsa mashi ta glass din gaba Wanda hakan yasashi maida hankalinshi kan tukin

Can kamar bazata yi magana ba tace
"Daddy.. Take me to him"

Dukda besan me tace daga bayaba jin ta ambaci daddy yasashi sanin wajen shi zaya kaita.


Jingina kanta tayi da kujera ta lumshe ido tana sauraron yadda zuciyarta ke zafi.

Meyasa dad a duniya bayada burin da yawuce ya zubarmata da mutunci?

Meyasa dad beda burin daya wuce ya quntata mata?

Meyasa yacika son kanshi?

Yarasa inda zai nemomata aiki sai wannan companyn?

Wane irin kallo yakeson suyimata?


Jin motar ta tsaya yasata bude idanu tana kallon mall din sannan tasa hannu ta bude murfin kofar tafito.


Shiga mall din tayi direct tanufi office din babbanta batareda tako tankama masu yimata magana ba.

Murda handle din kofar tayi ta bude tashiga batareda ko sallama ba.

Wanda hakan yasa daddy da wani mutum dasuke tattaunawa tare dagowa suna kallonta.

Batace komai ba ta qarasa gefen office din dake akwai cushion ta zauna ta zaro waya tana danne danne.

Maida hankalinshi dad yayi kan mutumin suka cigaba da tattaunawa har suka gama suka tashi sukayi musabaha mutumin yafita.

Kallon wajen saudart yayi yaga haryanzu bata dago daga kan danne dannen datakewa wayarba.

Wani irin murmushin manya yayi yanufi fridge din office din ya Ciro ruwan gora da glass cup ya qaraso ya zauna kusada ita ya tsiyaya mata a cup yabata.

Hannu tasa ta amsa batareda ta kalleshi ba ta kafa kai tasha kusan Rabi sannan ta ajiye.

Shiru office din ya dauka, kowannensu beda niyyar magana.

Kamo hannunta daya yayi yana murzawa ahankali yana kallonta itakau haryanzu idanunta na bisa wayar hannunta.

"Am sorry" yafada cikin rada.

Lumshe idanu tayi zuciyarta na cigaba da tafasa.

"Saudart nasan a halin yanzu kin tsaneni, kuma na cancanci haka, nasan am not a good father, ina yawan 6atamiki rai, ina yawan saki a damuwa...saidai banida yadda na iya ne"

Qara damke hannunta yayi cikin sigar dadin baki daya qware akai yace
"Banida kowa saike, banida uwa, banida uba, banida mata, banida 'ya'ya bayan ke, ke kadai zan iya samun sassauci awajen ki, ke kadai zaki iya taimaka min, ke kadai nakedashi dazan iya dazan iya fadawa damuwa ta inkuma saka ran zaki taimaka min, wataqila da na haifi wasu da ban takuramaki dayawa ba, da nasan akwai Wanda zai tausayamin aciki, da akwai Wanda zai iya jure komai akan samun farinciki na"


Haryanzu idanunta a lumshe suke saidai in banda hawaye babu abinda ke gangarowa daga cikin lumsassun idanunta.sosai maganar daddy ke shiga direct cikin zuciyarta tana narketa kamar yadda ake narke darma.

Wai yau daddy yakejin inama yanada wasu yaran bayan ita?

Sosai abun ya ta6amata zuciya.

"It ok saudart, nasan kinzo nan ne don kice bazakiyi aiki a company din ba, babu komai, zan cigaba da Neman yadda zanyi in hada kudin, koda ban hadaba idan wa'adin yacika zan saida mall din saina bashi kudin kingin kuma saina samu wata yar Sana'a nayi... It ok kinji? Kibar kukan hakan, I love you, Allah yamiki albarka"


Tashi yayi zai tafi yaji ta riqomashi hannu Wanda hakan yasashi tsayawa batareda ya juyoba.

Idonta still a lumshe ta bude bakinta dakyar tace

"Aiki a company din zai sakaka farinciki?"

Juyawa yayi yana kallonta yace

"A'a shalele, I want your happiness, don't worry"

Bude idanunta tayi tana kallonshi da idanunta dasuka ida rinewa sannan ahankali tasake cewa
"Zai sakaka farinciki?"

Shiru yayi yana kallonta kafin yace
"Eh saudart, babu company dazamu samu mai biyan albashi mai tsoka kamar wannan, kuma..."

"It ok" ta katseshi da fadin haka sannan ta tashi tsaye tana gyara nadin gyalenta ta dauki Jakarta tayi hanyar kofa. Yabita da kallo


Harta sa hannu zata bude kofar muryarshi ta dakatar da ita.

"Shalele.."

"Ina sonka, kaine silar zuwana duniya ko me nayimaka bazan biyaka, bazan so naganka cikin damuwa ba bayan inada maganinta, bazan so a dalilinaba kayi danasani ko kukan Rashin 'ya'ya dayawa ba, zan iya sadaukar da farincikina kamar yadda kasha sadaukar da naka wajen samamaka farinciki.
Saidai... Saidai karka yi tunanin zaka iya sani sa6awa Allah na bayan wadda kasani nayi abaya, idan dagaske saboda na taimaka maka wajen biyan bashin kanka yasa ka nemomin aiki fine, amma idan kanada wata manufa akan haka saidai kayi haquri, wata qila anan zan Gaza sama maka farinciki"

Tana kaiwa nan tabude kofar tafice.


Alhaji shamsu yadade nan a tsaye yana bin inda tabi tawuce da kallo.

Sai yanzu yafara tuhumar kanshi akan anya yayi mata adalci? Anya kalaman dayayi amfani dasu basuyi tsauriba, yasan saudart batada wani Wanda takeso takeson sashi a farinciki bayan shi, meyasa yayi amfani da wadannan kalaman wajen karya mata zuciya.

Komawa yayi ya zauna yana jin badadi har cikin zuciyarshi.





Key din motar ta amsa hannun bala ta bude motar tashiga ta tada sannan tafice daga harabar mall din.


Tafiya take hawaye na gangaro mata duk kau kokarin datake na tsaidasu.

Ba komai kesata hawaye ba sai kalaman dad na inama yanada wasu yaran, wannan Kalmar tafimata ciwo kuma tasan zata Dade tana cimata zuciya.


Ikon Allah kawai ya kaita company din lfy.

Parking tayi a parking space sannan takoma ta jingina da seat din tana lumshe idanu.

"Ya Allah give me strength"

Ganin zaman be yiwuwa yasata budewa ta zuro kafafunta tafito waje.


Sake kallon harabar company din tayi tana tuna farkon zuwanta company din dakuma abinda yafaru a ranar.


Maida murfin kofar tayi tarufe sannan tafara takawa jiki a sanyaye tanufi main entrance din.

Wajen wanke hannu taje ta matsa sanitizer tafara wanke hannun yayinda komai na farkon zuwanta company din ke dawomata a qwanya.

Danna botton din kofar tayi yabude tashiga sannan yakoma yarufe sannan daga can ciki kuma yabude tashiga.

Daidaikun mutane taga sunata kai kawo kamar dai ranan kowa da abinda yasha mashi kai.


Direct wajen elevator tanufa ta Danna number din floor din sannan tashiga.

Cikin yan daqiqu sai jitayi abun ya tsaya sai kofar tabude.

Shiru tayi tana kallon wajen batareda ta fitoba gabanta sai bugu yake.

Ganin elevator din zai koma yarufe yasata sauke wata nannauyan ajiyar zuciya sannan ta zuro kafarta tafito.


Kamar wancan karon, qamshi da sanyi yafara yimata maraba, babu abinda ya canza daga yadda yake lokacin datazo sai empty kujerar secretary data gani babu kowa akai Wanda yanzu ita zata dinga zama akai.


Ta Dade tsaye tana qarewa wajen kallo batareda tayi yinkurin motsawa ba taji a bude kofa an fito.

Saurin waigawa tayi suka hada ido.

Washe baki yasakeyi.

"There you are! Sanni dazuwa Mrs A.. I mean saudart, ga wajen ki can, muje please"

Babu musu tabishi ya budemata tashiga, wajen rufe yake da glass don haka kana hangen naciki kuma koda zaka ba nawaje Abu akwai inda zaka zuge ka fidda abun batareda ka fitoba ko na wajen ya shigo.


Bin office din take da kallo cikin takaici, don duk qawatuwar wajen be burgeta ba.

Sadeeq sai zuba yake yana nunnunamata abubuwa yana mata bayani itakau tana gefe ta rungume hannuwa a qirjinta tana saurarenshi.

Saida yakai aya sannan yace

"Erm.. Yanzu wadancan files din zaki kaima boss yayi signing" yafada a darare.


Jimm tayi kamar bazata motsaba saikuma can ta sauke ajiyar zuciya ta matso kan desk din dake cike da files da computoci tace

"Wadanne files?"

Tattaramata su yayi yabata tayi mashi godiya sannan yafice.

Itama fitowa tayi daga office din tanufi office din.

Daga kai tayi ta kalli abinda aka rubuta sama

*the c.e.o office*

Ta Dade tsaye awajen tana yunkurin shiga saikuma ta fasa.

Da ace mutuwarta zatazo a lokacin koko ta 6ace 6att datafi murna.

Yau zatayi facing dinshi a matsayin boss dinta, ita kuma a matsayin secretary dinshi, wannan wane irin zubarda mutunci ne?

Tunawa tayi da abinda yafaru dasafe kafin tabaro gidan, kenan don yasan zatazo office dinshi yasashi yimata hakan, no wonder, dama tayi mammaki, tunda sukayi aure magana ta fatar baki bata ta6a hadasuba sai yau, kenan saboda yasan zatazo company dinshi a matsayin mai mashi aiki yasa yayi hakan?


Idan hakane to ya tanadar mata cin mutuncin dayafi hakan kenan.

Ca6, Lallai, zata iya jurar komai amma banda cin fuska, bazata ta6a barinshi ya maida ta abun wulanqatawa ba.

Shaqar numfashi tayi da qarfi sannan ta fesar sannan ta daga hannu tafara knocking.


Sai ana ukun sannan taji ance

"Yes? Come in"


Gabanta ne ya tsananta bugu, hannunta na dan 6ari ta murda handle din kofar ta bude...✍



Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲


Sorry for the late posts guys, wlh jiya nakusan awa biyu ina typing nakusan zuwa qarshe wayar tayi shut down, yadda kukasan inta😭😭


This page is for you *Ummu Muhseen*

Marubuciyar littafin *GALADIMA AARIB*

Allah yaqara basira da kaifin ido da zaqin hannu🤲

Ga page din nakine kiyi yadda kika gadama dashi🤷‍♀




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





040




Tattaro sauran jarumtarta tayi ta tura kofar tashiga kamar Wanda kwai yafashe mawa aciki.

Babu abinda ya canza a office din, yananan yadda ta sanshi tun farkon zuwanta.

Qasa qarasawa tayi taja ta tsaya a bakin kofar zuciyarta na dukan Tara Tara.

Jitake kamar qasa ta bude ta hadiyeta ta huta.

Wannan zubarda mutunci dame yayi kama?

Duk abinda A.A yayimata tabbass ita ta siya da kudinta, da wane ido zata kalleshi? Dawane ido zai kalleta? Yaya zai fassarata?

Jin shirun yayi yawa yasata dagowa Tadan saci kallonshi taga kanshi na kan system bemada niyyar dagowa.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ida tattaro kingin kuzarinta ta qarasa cikin office din.

"Good morning" tafada cikin nutsuwa

Cak ya tsaya da typing din dayake yakasa cigaba saboda muryarta datayi mashi dirar mikiya a kunnuwa.

Dora files din tayi saman table din sannan tace
"I was told to bring these files to you, your signature is needed" tafada cikin nutsuwa amma deep down she's dying.

Juyawa tayi saurin yi tanufi hanyar kofa.

Dagowa yayi yana kallonta, saidai harta kusa kaiwa bakin kofar, hakan yasashi dakatar daita da

"Wait!"

Cak ta tsaya tana runtse idanu da qarfi zuciyarta kamar zata Faso qirjinta ta fito dan bugawa.

Ganin batada niyyar juyowa yasashi cewa

"Who are you?"

Yawun bakinta taji ya qafe jitake kamar ta 6ace 6att daga office din.
Dakyar ta tattaro yawu a bakinta ta hadiye sannan cikin calm voice tace
"Am your new secretary"

Yes itace, tabbass muryarta ce, bazai ta6a Qin gane muryarta ba, kallon bayanta yake don still bata juyoba, dukda be cika qaremata kallo ba amma still yasan wannan jikin, jikinta ne.

Ganin ta cigaba da tafiya zata fita yasashi cewa
"Stop!" Da qarfi.

Ja tayi ta tsaya again batareda ta juyoba.
Cikin qufula yace "come back here!"

Anzo wajen! Dama abinda take Gudu kenan, facing dinshi, bataji tana iya facing dinshi, her emotions won't let her.

Hawaye taji suna Neman tarrarmata a idanu tayi saurin maidasu, tayiwa kanta alqawari duk rintsi bazata ta6a barinshi yaga weak point dinta ba.

Juyowa tayi ahankali ta kalleshi suka hada idanu.

Dumm.. Gabansu yafadi gabadaya yayinda Ashraf yayi mutuwar zaune awajen yana kallonta baki bude.


Qarasowa tayi har gaban table dinshi fuska ba yabo ba fallasa tana kallonshi

"What! W..what the hell are you doing here?"

Fuskarta normal batareda ta bayyana yanayin datake cikiba tace
"Sorry, banyi introducing kainaba, I'm miss saudart shamsu by name, your new secretary" tafada cikin mugun wayancewa yadda kasan yau dama tafara saninshi.

Sagale yayi da baki yana kallonta don he's totally speechless ma.

Batareda ta nuna damuwa da tsaretan dayayi da idanu ba ta cigaba dacewa

"Today is my first day, guess I have a lot to handle, zanje in hada scheme of work"

Tana kaiwa nan tajuya tanufi qofa cikin takunta.
Kasa tsaidata yayi harta fita.

What!
What the hell is going on?

Hannu na 6ari ya jawo landline din dake kan table dinshi ya daddana lambobin landline din office din sadeeq.


Fita tayi ta rufo kofar ta jingina daita hannunta dafe da qirjinta tana numfashi sama sama.

Ita kadai tasan jarumtar datayi wajen facing din Ashraf.
This is the toughest time ever in her life.

Saida tagama dawowa daidai sannan tamiqe daga jikin kofar ta wuce jiki a sanyaye office dinta ta bude tashiga.


Tsayawa tayi tanabin tsararren office din da kallo Wanda desk din dake daga gefe cike yake da computoci ga files files da scripts agefe ajere gwanin sha'awa.

Tsaki taja don babu abinda ya burgeta aciki, ta qaraso ta zauna akan kujerar dake facing din desk din.









Ringing din landline din ya dakatar dashi daga rubuce rubucen dayake.

Saurin toshe baki yayi yana qumshe dariya ganin boss ke kira.
Saida ya daidaita nutsuwarshi sannan ya daga wayar.

"Hello?"


"Get the hell here! Now!"

Ding.. Aka katse kiran.

Murmushi sadeeq yayi don dama yasan za'a Rina.


Tashi yayi ya gyara suit dinshi sannan yafito.




Taga fitowarshi amma saita kauda kau ta fara plugging din socket din system din tanayi tana kallonshi qasa qasa harya shige office din.



Da sallama yashiga office din.
Ganin yanayin fuskar Ashraf yasashi kusan kecewa da dariya, mazewa yayi ya qaraso cikin office din.


"Good morning s..."


"Kaga riqe gaisuwarka Mr man, what the hell did you think you're doing?" Yafada cikin daga murya

"Menene..."

"Don't dare ask me menene! Kafini sanin dalilin zuwanka nan" yasake katseshi a fusace

"Sir.."

"Don't sir me! Ka Kirani da Ashraf dina mallam, ubanwa yasaka daukarta?!" Yafada cikin tada jijiyoyin wuya.


"Ashraf..."

"Just shut up! Yanzu kaje ka rubuta mata takardar sallama, she's fired!"

"What! Ashraf meye haka? Atleast ka saurareni"

"Nagama magana, she's fired"

"Amma..."

"Ammo! Get out!"

"A.A..."

"Out!!"


Shiru sadeeq yayi yana kallonshi cikin ido da alamu shima yafara fusata.

"Me kake jira? I said out!"

"Bazan fitaba! Zoka fiddani idan ka isa! Why zaka dinga yimin tsawa? Who did you think you are?!" Yafada shima cikin daga murya


"Atleast ka tsaya ka saurareni mana, kwana biyu da yad'a vacancy letter babanta yakirani akan na dauketa aikin, I was shocked nima a lokacin amma daga baya naga ai muma wani opportunity ne garemu na tracking dinshi
Nasan yanada wata manufa bayan dalilin daya karantomin na daukarta, he thought bamu sanshi bane, he thought bamusan me yake qullawaba ne.
Wannan itace the easiest and the fastest means na cimmashi.

I thought kaima cunkusashen kwakwalwarka zata baka haka amma am mistaken" ya qarshe zancen yana makamashi mugun kallo


"Koma menene bazan iya aiki da wannan aljanar yarinyar ba"

"Ita waya ce maka dason ranta tazo? She's forced kamar yadda aka tilastamata wajen qaddararen auren ka, bayan haka ko kallo baka isheta ba kaima kasani, kuma kafin ka kira wani da aljani kafara duba mirror"


"Hey watch your words! Am still your boss"

"Boss my ass! Nabi boss dagudu, idiot" yafada yana nufar kofa

"Kaje nayi suspending dinka saina nemeka"

"Sai kazo ka fiddani din, mtcheew" ya fita yana bugo kofar da qarfi.

Bin qofar yayi da kallo, yasan sadeeq yakai bango ne, shi dama be iya zuciya ba, kamar yadda yakeda wuyar zama haka yakeda wuyar sauka.

Tsaki yaja yakoma ya zauna yana huci.




Jin anbude kofa yasata dagowa, gani tayi sadeeq ne yafito daga office din.

Ta6e baki tayi ta kauda kai.

Kamar zai wuce saikuma yadawo yayi knocking akan glass door dinta ya tura yashigo.

Ko dagowa batayiba bare ta kalleshi, typing kawai take cikin qwarewa.

"Is everything alright? Ko akwai wata matsala?"

Batareda ta kalleshi ba idanunta akan screen din computer tace "No" ataqaice

Be sake cewa komai ba yajuya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login