Showing 42001 words to 45000 words out of 173829 words

Chapter 15 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1116

zuba ga iska don kwata kwata be ganin gabanshi sosai.

Babu yadda ya iya don haka ya koma gefen titi yayi parking yana sauraron ikon Allah.


Wani irin shiru motar ta dauka, bakajin komai sai sautin saukar ruwan saman.

Kashe a.c din motar yayi ya kunna warmer don dama shi can sarkin jin sanyine, ya kwantar da kujerarshi ya jingina da ita.


Itakau dama saudart jingine take da bayan kujerar ta ta lumshe idanu tana sauraron sautin saukar ruwan.


Tunawa tayi da ranar dasukaje gathering dinnan ruwa ya ritsamusu a hanya kamar dai yau.

Ajiyar zuciya tayi taqara lafewa a kujerar idanunta still a lumshe tanata tunane tunane har barci 6arawo ya saceta.


Shikau a 6angarenshi latse latsen waya yaitayi har ruwan yadan tsagaita.

Jin ruwan ya tsagaita kuma dare qarayi yake yasashi dagowa yana maida kujerar daidai.

Kallon gefenta yayi ta qasan ido yaganta lafe a kujerar ta jawo gyalenta ta rufe fuska.

Tada motar yayi suka cigaba da tafiya har suka kawo gida.

Parking yayi a parking space sannan ya kashe motar.

Izuwa lokacin ruwan yakoma yayyafi sai iska daddada dake kadawa.

Qara kallon side dinta yayi Wanda yanzu tajuyo tana fuskantarshi cikin barci kuma gyallen yadan yaye.

Samun kanshi yayi da kasa janye idanunshi daga sleeping face dinta.

Bin fuskar yake da kallo kamar yau ya ta6a ganinta.

Daga lumsassun idanunta da Zara zaran lashes dinta sukadan lankwasa saboda tsawo zuwa girarta mai dan yawa tadasha gyara ta sun kwanta luff zuwa madaidaicin qaramin hancinta mai dan tsayi zuwa kumatunta masu dan cika Wanda dukda barci take dimple dinta na haggu saida yadan lotsa sai qannanun lips dinta da sukasha maroon din lipstick sunyi dasa dasu gwanin birgewa.


Kasa janye idanu akan lips dinta yayi don ba qaramin tafiya dashi yayiba.

Besan iya kar lokacin daya dauka yana kallonta ba don yadda kasan yau yafara ganinta haka yakoma.


Saudart kau barcinta take hankali kwance.

Sai can cikin barcin tafarajin zafi, tana warmer daya kunna dazu gashi glass duk Asama suke gata batada jumurin zafi ko kadan hakan yasa barcin yafara daina yimata dadi.


Ahankali tafara bude lumsassun idanunta dasukayi nauyi saboda barci, basu sauka a koina ba sai cikin nashi.


Gabansu ne yafadi gabadaya kuma suka kasa janye idanunsu daga cikin najuna.

Jin hasken idanunshi na Neman narkar daita yasata saurin miqewa zaune tana gyara zaman mayafinta.

Shima sai a sannan ya janye idanunshi ya maidasu ya lumshe cikin takaicin kamashi datayi yana kallonta.

Shiru motar ta dauka babu mai magana sai can yasa hannu ta bude murfin kofar yafita yana maida kofar da don har saida ta tsorata.

Binshi da kallon takaici tayi da side mirror harya shige ciki sannan taja dogon tsakin takaici sannan itama a fusace tafito ranta a 6ace itama tayi banging din kofar ta nufi ciki.


Koda tashiga bata ganshiba kuma dama bason ganinshin takeba ta hayewarta sama tana gunguni.

Itadai Allah yasa dad yasamo mata aiki mai kyau tasamu asan yadda za'ayi abiyashi damn kudinshi kota huta.

Haka taita gunguninta harta gama shirin barcinta ta kwanta da niyyar idanma dad besamomata aikin ba ranar Monday babu abinda zai hanata zuwa bakery...✍



Manage please



Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)




Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka qaramana zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




037



The next day is Saturday, yau weekend babu aiki, tunda yaje gida ya gaida Ummy kamar yadda yasaba yawuce gidansu sadeeq.


Zaune suke, Ashraf akan cushion din dake dakin abinci agabanshi yana aikawa ahankali shikuma sadeeq na kwance kan gado yana waya murya can qasa qasa don ko Ashraf dake dakin yayi qarya yace yaji kalma daya cikin maganganun dayake da alama dai da budurwa yake wayar.


Juice yadauka yakai bakinshi yana kur6a yana kallon yadda sadeeq din ke dariya ciki ciki cikin salon burgewa sai wani iyayi yake saikace bashi bane idan yana dariya har Wanda ke kilometer 2 dashi najiba.

Tsaki yaja ya ajiye cup din hannunshi ya dauki cokali ya cigaba dacin abincin shi.


Harya gama ci begama shegiyar wayar da shi yarasa ubanme ma suke cewa.

Tsaki yasake ja yana goge bakinshi da tissue sannan ya miqe ya nufeshi.

Fiit.. Yaji an fige wayar Wanda hakan yasashi saurin dagowa.

Harara ya 6allamashi yana kashe wayar yayi jifa daita kan gadon

6ata rai sadeeq yayi yace

"To dan black stomach, meye ruwan ka da wayata?

Mugun kallo yasake watsamashi sannan yace

" bansaniba, na zo wajen ka kawani hadani da plate din abinci ka shareni, niga mayunwaci ko?"

Shima hararar ya 6allamashi

"To dama miya kawoka? Mutum da sunan yayi aurene amma qaton gaurone, shikenan dan taqamar kazo sainaqi yin waya da sweetheart dina, a'a ba dalili yanzu tunda kaci ka qoshi sai aqara gaba ko?"

Tsayawa yayi yana kallonshi baki bude

"Ni kake wa Rashin mutunci?"

"Eh din, bakai taqamar Rashin mutunci ba? Har muce zamuzo gidanka cin taliyar Amarya kayimana baqinciki, ai kadanma kagani". Inji sadeeq yana jawo wayarshi dake tsakiyar gadon yasake dialing din number.

"Hello sweetheart.. Wani yaro ne yashigo yana damuna shine nakashe na korashi..."

Daidai nan kawai yaji yafita daga dakin yana ayyana mugun Rashin mutuncin dazai shufkamashi.


Be zarce koinaba sai gidan gonarshi inda yawanci dama can yake zuwa a irin wannan rannakun ya huta don bejin yana iya zaman waje daya da wannan aljannar yarinyar don dole kawai tasa yake kwana gidan.


Itama a bangarenta tayi duk abinda yadace tayi, ta koma sama, bata saukowa sai idan wani Abu takeda buqata kuma data dauka zata koma, hakan yasa basu hade ba har weekend din yaqare.







Yau Monday, yau tunda ta farka dasafe take cikin farinciki don ko komawa barcin datake da safe ba tayiba.

Shirinta kawai take na zuwa bakery.


Tea kawai ta hada da electric kettle din dakinta kakkaura tasha cikin yadan warware sannan tahau shiri.



Wajajen 8:25am tafito cikin shigarta ta atamfa brown da Orange Riga da skirt sannan ta zumbula hijabi har qasa brown, abinka da farar mace sai ya haskata sosai ta ratayo wata brown handbag mai kyau sai dayan hannun riqeda waya.

Ahankali ta sauko daga stairs din zuciyarta fess yau zata fita tashaqi fresh air.

Fita tayi tanufi parking space inda motarta (Wanda aka hadamata da lefe) take.

Caraf suka hada idanu dashi shima yana niyyar bude murfin kofar.

Janye idanu sukayi gabadaya suka kauda kai.

Shigewa yayi cikin motar ya maido yarufe, kwata kwata be nuna damuwarshi na fitarta ba vare yadamu da ina zataje.

Tada motar yayi yayi reverse ya fita daga gidan.

Ta6e baki tayi itama ta maido murfin kofarta tarufe sannan ta daura seat belt sannan ta tada motar itama tayi reverse tafito akayi scanning dinta sannan gate din yabude ta fice itama.






Yau saudart tana cikin farinciki sosai don sosai taji dadin zuwanta bakery din, Suma yan bakery sunji dadin zuwanta don sunyi missing dinta sosai, sai nan nan suke daita suna nunamata cigaban dasuka samu tanata yabon qwazonsu suna jindadi.

A ranar saida tayi cake uku manya masu haddadun decoration sai santin cake din ake.

Ataqaice dai ranar sai shidda da Rabi na marece tadawo gida agajiye don yau qara'in ayyukan data kwana biyu batayiba tayi.


Shikau bedawoba sai 9:00pm kamar yadda yasaba.

Ganin motar data fita dashi a parking space din yasashi sanin tadawo.

Ta6e baki yayi in an I don't care manner ya fito daga motar ya shige ciki.



Washegari ma yana zuwa parking space zai ya taddata tana qoqarin shiga mota.

Kallo daya ta mishi ta shigewarta motar, shima beko qara kallon gefenta ba ya bude tashi motar yashiga.


Ita tafara fita daga gidan sannan shima ya tada motar yafito.


Yau kam kasa kawar da tunanin ina zata yayi, tunda sukazo gidan bata ta6a fitaba sai jiya da yau.

Dukda yasan be kamata yadamu ba amma sai kawai ya tsinci kanshi dason sanin inda take zuwa.

Acewarshi a badini ne sukasan wannan auren na tsari ne amma a zahiri matarshice ta sunna kuma haka kowa kemata kallo bazaiso tayi tarnishing din image dinshi ba ta zubdamashi da girma.

Haka ya yini a office din sukuku yarasa meke damunshi dukda ba'ace besan meke damunshiba saidai bai gasgata eh saboda fitarta yashiga damuwa ba koda kuwa itace shi bawai don wani abuba yadamu saidan karta zubdamashi da mutunci (kunji fa🤔)




Yana nan zaune yana operating din laptop din gabanshi sadeeq yashigo da sallama dawani file a hannu


Amsa sallamar yayi batareda ya dago ya kslleshi ba.

Be damuba saima file din daya Dora a saman table din yana cewa

"Sir, maganar new secretary dazamu dauka ne, mutane dagawa sun kawo CV dinsu mun za6i wasu wadanda insha Allah zamuyiwa interview, gasu" ya qarshe maganar yana bude mashi file din.


Beko kalli file dinba yace

"Kuma ka tabbata babu arniya kodaya aciki don wannan karon I won't tolerate nonsense, ita wancan korarta nayi idan wata tayi kwatankwacin abinda tayimin saina daureta harsai igiyar tayi rara"

Murmushi sadeeq yayi yace "karka samu damuwa, insha Allah nitsatsiya za'a samu, duk Muslims ne kaduba"

Dan kallon file din yayi kafin yace "ba damuwa kawai proceed with the interview, I badly need the secretary kasan sati nasama zanyi tafiyar sonake kafin lokacin tasan komai"

"Ok sir, insha Allah gobe za'ayi zuwa gata an fidda mai nasara, saita fara zuwa Monday"

"Hakan ma yayi" yafada yana maida hankalinshi kan abinda yake.

Har ya juya zai tafi yakuma dawo

"Is something bothering you?" Ya tambaya cikin kulawa.

Dagowa yayi ya kalleshi

"Me ka gani?"

"Gani nayi kamar kana cikin damuwa"

"Naaah, babu komai, kana samun information wajen spy dinnan kuwa?"

"Yes, ko jiya yayi updating dina"

"Good, ka cigaba da keeping in touch dashi ok? Sonike komai ya kammala cikin gaggawa ko nahuta"

Dariya Sadeeq yayi yace
"Karka damu komai yakusan zama tarihi ai"

Nan suka dan qara tattaunawa sannan sadeeq yakoma office dinshi.






Yauma tasha aiki sosai saboda ba qaramin missing din aikinta tayiba.

Zaune take tana shan fresh milk tana danne danne a laptop din gabanta.

Ringing din wayarta yasata ajiye kofin glass cup din ta dauki wayar.

Ganin mai kiran yasata dagawa ta kara a kunne

"Aslm alaika sweet dad"

Sautin murmushi taji daga dayan 6angaren sannan akace

"Wslm habibtie"

"Dad good afternoon"

"Ya kike? Ya zaman gida?" Yafada yana yar dariya

"Hmm Dad ina office dina ai"

Cikin mammaki yace "which office?"


"Bakery na mana"


"Seriously shalele, kina ina?"

"Allah kau dad ina bakery"

Nan take ran daddy ta 6ace

"Ya mukayi dake saudart? A iya sanina mun ajiye magana dake akan aiki"

Jikinta ne yadanyi sanyi jin kamar yaji haushi


"Dad.."

"It ok, idan aikinne bakiso fine, bye"

"Daddy please karka ajiye wayar, please"

"Mezaki fadamin?"

"Dad it's not what you think, zanyi aikin fa, kawai am bored ne shiyasa nazo bakery jiya da yau" tafada a shagwa6e

Wani sanyi yaji a zuciyarshi don duk a tunaninshi ta canza ra'ayi kuma yasan halinta tana iyawa don shegen wayau ne daita.


"Ok I thought kin koma bakery dinne, you see finding a better job with good salary is better"

"Hakane" tafada ahankali zuciyarta na bata anya Dad beda wani shirin don ba qaramin sani tayiwa dad dinta ba tasanshi ciki da bai.


"Inada daddaden labari agareki" yafada cikin zaquwa

"Ok fesamin daddy"

"Na Samar miki aiki!"

Dukda bataji irin farincikinnan ba sai tayi pretending tace

"Da gaske dad?"

*yes sweetheart "

"Wani irine?"

"A wani company nayi miji applying, kuma suna biya sosai, an za6eki cikin wadanda za'a yiwa interview, saidai online interview ne, zasu turomiki ma ta e-mail qilama sun turo, gobe ake interview din, please don't let me down"


"Insha Allah dad, wane company ne?"

"Na wani aboki nane, kuma shahararrene"

"To"

"Are you ok?" Inji dad jin ta amsa cikin wani yanayi

"Nothing Dad" tafada don haka kawai take jin aikin be kwanta mataba

"Ok daughter, do your best ok? Allah yabada sa'a dukda nasan ke mai sa'ar ce"

Dariya tadanyi tace "amin to Dad"

Nan sukayi sallama ta yanke wayar.

Ajiye wayar tayi tadanyi tagumi tana nazari.

Me dad ke shiryawa?

Jin yanayin maganar shi kawai datayi yasata sanin da wani Abu dayake shirya wa.

Her Dad was very cunny kuma tasani.

Haka taita saqa da warwarewa har suka tashi aiki ranar...✍


Manage🙏



Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Allah ya yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka qaramana zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)









038




Washegari saudart bataje bakery ba, tunda tagama aikin gida tayi breakfast ta haye sama.


Bude laptop dinta tayi exactly tafara yan danne dannenta kafin lokacin interview din dazasuyi yayi.


12:00pm suka fara and alhamdullilah tana saka ran samun nasara.


Ranar yini tayi a garden tana aiki a laptop dinta don tana so taqara advancing din bakery dinta ne, tana son ta bude wani qaramin shop kusada bakery din yazama wurin hada variety of ice cream.

Dama ta Dade tana tunani akan hakan, ganin yanzu takeda damar yi kuma kudi ba matsala bane, yin hakan zaisa hanyar shigowar kudinta yaqaru Wanda hakan zaisa ta taimaki dad dinta ya biya duk wani bashi dake wuyanshi.

She loves her Dad soo much, tunda ta taso batasan kowaba sai dad dinta, shaquwar dake tsakanin su baya faduwa, saboda shi yayi taking din both role dinshi Dana mamanta.

Tun tana yarinya da gari yawaye zaimata duk abinda yakamata uwa tayiwa diyarta.

Wanka, girki, yakaita school, yaje Dakota, suwuce mall dinshi su qarashe yinin tare.

Weekend kuma yakaita wajajen shaqatawa suyini a can kuma yakaita gidan mamanta tayimusu yini daya

Shaquwar da saudart tayi da Daddy ko kwatanta batayi da mamanta ba. Shiyasa matsayinshi ma na daban ne acikin zuciyarta.


Tasan Dad dinta is not perfect, dama kuma duk dan Adam ajizine, shi ajizancinshi shine son kudi.

Duk hanyar dayaga zaisamu yan gidan rana masu tsoka to saiyabi don acewarshi kudi sune komai.

Anan ne ra'ayinsu ya banbanta don ita basu wani dametaba kuma tana qoqarin ganar da daddy hakan amma Wanda yayi nisa ba Lallai bane yaji kira ba.

Shiyasa kullum take sakashi a addu'a don tayi imani cewa addu'a itace takobin mummunai.



Haka tawuni zur a garden din sai wajajen magrib takoma cikin gida tayi hayewarta sama.


Washegari ma batajeba don tunda Dad yanuna 6acin ransa akan hakan taji zuwan duk ya fita kanta.

As usual tagama komai gidan sai daukar qamshi yake, tana kwance tana waya da P.A dinta akan shirye shiryen bude ice cream joint dinta .

Sun dan jima kafin sugama sannan ta kashe wayar.

Kafin ta ajiye wani kiran yashigo.

Ganin daddy ne yasata Sakin murmushi ta kwanta tana maqalqale pillow cikin muryar shagwa6a tace

"Daddy?"

"Na'am shalelen daddy?"

Turo baki tayi tace "daddy I miss you"

"Miss you more baby, shine baki gayamin ba?"

"Menene?"

"Really? Bakima saniba?"

"Menene to dad? Kafadamin kawai"

"To albishirinki"

Cikin zaquwa tace "goro fari"


"You're employed!"

Waro idanunta tayi cikin jindadi

"Da gaske daddy?"

"Eh mana, yanzu muka gama magana da P.A din companyn"


"Wow dad, that's soo cool, naji dadi" tafada da murmushi a fuskarta dukda bawani farinciki takeyi canba.

"And guess what?"

"What?"

Ta amsa tana buga tagumi da hannu daya.


"A matsayin secretary aka daukeki a company din"

Waro idanu tasakeyi tana cewa

"Really dad?"

,"sosaima, with a sum of 250k duk wata"

Sake ware idanu tayi

"Wow! Wow!! Dad am speechless!"

Dariya Alhaji shamsu yayi mata, I told you? Ina gwadamaki annabi kina rufe idanu. Idan kika cigaba da yimin biyyaya zakiga fin haka, zakiyi bala'in kudi"

"Hmm zan daiyi kudi masu albarka dad, ba na bala'i ba"

Ta6e baki yayi yace

"Whatever, yanzu ki shirya zaki fara zuwa ranar Monday ne, please you have to be serious kuma kinsan I love you ko? Kuma bazan ta6a cutar dakeba"

"Yes, I know"

"Kuma kinsan komai nakeyi saboda ke nakeyi, banida kowa banida family bayan ke kuma banida mai farantamin bayan ke ko?"

Dan daga gira tayi alamun tambaya

"Eh dad, amma meya kawo wannan maganar? You know I love you so much, farincikinka shine nawa, shiyasa ma zanyi wannan aikin domin taimaka maka wajen ganin ka sauke duk wani nauyi dake kanka"


"Eh nasani dear, saidai kiyimin alqawari bazakiyi disappointing dinaba, zaki qar6i aikin nan duk yadda kikaga yazo miki"

Shiru tayi na dan lokaci kafin tace

"Ban ganeba dad, is something wrong with the job?"

"No, absolutely no, kawai I want you to accept it ne duk yadda kika ganshi"

Ajiyar zuciya tayi tace

"Zanyi amma sai idan be sa6ama addiniba"

Cikin jindadi yace

"Yes na tabbata miki be sa6ama addiniba, wlh"

"To Allah yayimana jagora"

"Amin my jewel, Allah ya albarkaci rayuwarki"

Cikin jindadi tace "amin Abby"




Kingin ranakun tashiga busy sosai wajen ganin ta ice cream joint din ya kafu.


Kwana uku ana aikin kafin agama kuma alhamdullilah komai yatafi mata yadda takeso.

Ranar asabar aka bude wajen kuma tadanyi taro babu laifi akayi addu'a samun sa'a akaci akasha sannan aka watse.

Nanfa ta duqufa wajen ganin komai yatafi kan tsari.

Ice cream babu kalar da basu saidawa, acikin su akwai na vanilla, chocolate flavour, strawberry flavour, banana flavour ddss.

Alhaji shamsu kau ya dauki nauyin tallatar mata da wajen ta kafar yad'a labarai wato t.v, radio da social media.

Duk wannan abun da akeyi Ashraf na sane amma ko nuna yasan sunayi beyiba, to tayama zai nuna bayan haduwarsu ma aikine.

Kowa zaman kanshi yake a gidan so babu Wanda yadamu da abinda dan uwanshi ke ciki.


Su Ummy kau basuda masaniya akai saida suka gani a t.v ana talla, nan baby ta kirata tana tambayar dagaske ita ta bude.

Da eh saudart ta amsamata, sosai baby tayi murna wai likafarta taci gaba, dama ita mayyar ice cream ce, duk sadda taji kwadayi zatazo ta jidi son ranta.

Dariya saudart tayi tana cewa babu damuwa ai kayan Allah na annabi ne.





***********************************

Yau Monday, tunda wuri ta tashi tayi abubuwan data sabayi dasafe ta hada breakfast dinta taci sannan tashiga wanka.


Wajajen takwas da Rabi harta gama shirinta tsabb cikin wata sky blue din Arabian gown bubu Wanda yaji duwatsu masu daukar idanu daga gaban rigar.
Ta yane kanta da veil mai dan girma sky blue Wanda ya kawomata har saman ciki.

Ta rataya jakka baqa sai takalmi masu dan tsini baqaqe hannunta kuma daure da agogo kamfanin Apple baqa a hannu.

Fuskarta babu wata kwalliya bayan powder da kwallin data sakama idanunta sai lashes dinta data sharce da mascara, shikenan.

Bata fesa turare mai uban qamshi ba, mai sanyayan qamshi tafesa Wanda saikazo kusada ita zaka jishi.

Jin horn a waje yasata gane drivern da daddy yace zai turomata ya qaraso.

Saka wayarta da abubuwan amfani tayi a jakkar tasake kallon kanta a madubi tana gyara daurin veil din sannan tafito.

Da sauri ta sauko tana sake duba time tanufi hanyar fita.

Saurin bude kofar tayi tasaka kai zatafita sai quuum! Suka qume dajuna.

Ba qarya sun qumu don saida suka ja da baya suna Sosa wajen suna kallon juna.


Ganin beda niyyar tankamata ko matsawa yasata ra6awa ta gefenshi zata wuce.

Sai jitayi an chafki tsintsiyar hannunta an maidata baya da qarfi Wanda saida kafarta ta haggu ta murgude tayi baya baya zata fadi Allah ya taimaka ta dafe shoe shelves dake wajen.

Dagowa tayi a firgice tana kallonshi don bata ta6a zaton hakaba awajenshi.

Shima kallonta yake fuska a hade yana kallon direct tsakiyar kwayar idonta.

"Ke makauniya ce? You hit me and you're going without saying sorry?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login