Showing 171001 words to 173829 words out of 173829 words
bayada aiki sai kulada saudart da unborn dinshi
Duk motsinta akan idonshi saiya tambayeta meke damunta, ko me take buqata
Saida yayi kwana uku agida yana kula daita sannan ya koma aiki shima koda yaushe suna maqale a waya da kuma zuhr tayi zai dawo gida ya duba lfyar matarshi sai bayan asr zai koma
Saudart likafa taci gaba, yanzu dai babu zuwa aiki babu aikin komai saina ci, koda yaushe ka ganta to bakinta yana motsi don irin cikin nanne mai tara yawu, sosai takeba ashraf tausayi musanmman idan yaga tana barcin nan nata na fama, wani irin sonta yakeji a zuciyarshi da tausayinta yana addu'ar Allah ya rabata da abinda ke cikinta lfy
A bangaren maganarsu sadeeq kau tuni akasa rana, nan da wata hudu Wato bayan graduation dinsu baby
Zokaga murna wajen sadeeq, nanfa yafara yima ashraf wani gani gani wai shima yakusan zama angon yaga ta gori
Shidai ashraf dariya yakemashi yace Ai kuma na gaba yayi gaba kuma dole akira mijin iya baba, wai yabishi ahankali don shi surukinshi ne idan yakawo mashi raini saiyayi mashi buqulu yaga ta tsiya, Dariya sadeeq keyimashi yace wannan labari ne
Haka akaita rarrafawa inda saudart da ashraf suka cigaba da rainon cikin dasuke ma so marar misaltuwa while su baby da sadeeq ana gefe ana shirye shiryen biki wanda saudart tayima laqabi da *Auren zafafa biyu* don a tsakanin sadeeq da baby ba'a San gwani ba don hallayarsu daya daga zafin dumin har rawar kan, tasan dai gidansu dandalin drama zai zama don zani ce ta tarda muje
***
Biki fa ta matso inda ake shirye shirye tako wanne bangare
Kallo daya zakayiwa shirye shiryen bikin ka tabbatar da na yana gaban goshi ne bana bayan qeya ba
Ashraf shi ya dauke nauyin komai da za'ayiwa baby both kayan daki da kitchen
Sosai ya narka kudinshi wajen hidimar tilon qanwarshi da duk duniya baida kamarta
Saudart itace jagaba amara qahon qirjin biki don duk da ita ake zuwa siyayyar kayan kitchen, agefe kuma tana koyawa baby nau'ikan girke girke iri2 don shiririta yasa bata wani iya girkin kirki ba
Ummy kuma anata 6angaren zagewa tayi ta gyara diyarta kuma autarta ciki da bai, abin dai chakwai👌
Basu wani tsara bidi'o'i ba a bikin sai kauyawa party da za'ayi ranar Daren biki sai walima ranar biki
Abin yaba kowa mammaki don babu wanda beyi tunanin za'asha shagulgulaba a bikin dubada yadda yanayin amaryar mai jiran gado da angon suke
Qawayen baby dasuka shirya ma bikin sosai suna dokin shi suka shiga mita wai ta za'ayi bikin *mhiz meebie* guda ace event daya za'ayi wai kuma qauyawa?
Bude kwandon shara baby tayi tasakasu aciki ta rufe acewarta batada lokacin su
Biki ba saura 1 week su nafeesa da mardeeya (cousins din saudart) suka antayo daga Maiduguri don tun bayan bikin su ashraf suke zumunci sosai da baby
Sosai baby taji dadin zuwansu, babu 6ata lokaci suka tare dakinta aka shiga maida yadda akayi
Lokacin da su nafeesa suka hade da saudart sosai suka shiga yimata dariya don alokacin ta chanza sosai, ciki ya hurata dukda bawani girman ciki gareta ba saidai ta chanza tawani ajiye wasu tayani muni a fuska nanfa suka shiga saida halin dasuka saba na tsokanar juna irin na abokan wasa
Biki na saura kwana uku wasu qawaye uku ba baby suka qara zuwa gidan cikinsu harda teema aminiyarta
Alokacin daka shigo gidan zaka tabbatar da kashigo gidan biki don yafara cika da yan biki kama daga dangin ummy na yola har dangin abbansu ashraf na wudil
Aranar kayan lefen baby suka duro gidan
Masha Allah, ko hasiddin ida hasada yagani saiya yaba don sosai sadeeq yataka rawar gani a kayan
Su saudart sune gaba gaba wajen ganin lefe sai yabawa ake
Saudart anshiga busy, Ku kau bikin autares kuma qanwar miji guda? Duk hidindimun da akeyi agidan da ita akeyi donma ummy na dan hana wani abin saboda condition dinta
Duk kayan snacks da drinks da ake amfani kuma ake kan amfani a bikin daga bakery dinta suke tana gaba akan wannan
Shima ashraf a bangaren shi yashiga busy, gashi babban aminin ango gashi babban yaya ga amarya
Sosai kanshi yadau chaji don sosai yanuna shi dan halak ne don komai tare sukeyi da sadeeq yayinda ya dauke mashi abubbuwa da dama yayimashi da aljihunshi
Ranar Daren biki wanda yayi daidai da kauyawa day
A wani gidan gona na ashraf aka yishi
Cä6 duk wanda beje party dinnan ba yayi missing
Watakan ya qayatu kamar me, dukan jama'ar wajen sanye suke cikin kayan ainahin kauyawa wadanda suka amsa sunansu kauyawa don bazaka ta6a tunanin akwai daya daga cikin su daya ta6a taka gate din makaranta ba don kowannensu da irin shigar ban dariyar dayayi
Shidai ango sanye yake da wata kodaddiyar malun malun mai jirwaye jirwaye don asalinta blue shadda ce aka jiqata a hypo dukta 6aci, babbar rigar har tadeshi take saboda girma da tsawo yasa wani dan iskan three quarter aciki wanda ba'ama hangoshi don malun malun din ta rufeshi sai rawanin daya Nada akai da wani blue din soson wanka abin gwanin dariya
Itakau baby sanye ake cikin riga daban, zane daban kallabi daban tawani tamke kai fuskarta kau tasha makeup din qauyawa da dige dige
Ashraf sanye yake cikin wata kodaddiyar Yar shara sai baqin three quarter shima wanda shine shigar manyan abokan ango sunsha irin wannan cover shoes din na Fulani
Saudart itama sanye take da kaya duk daban2 ga dan tumbinta daya qara qawata abun itama fuskarta tasha makeup din kauyawa kamar wata aljana hakama sauran qawayen wasuma abin nasu harda hauka
Ranar masu rake sunyi ciniki don kowanne da Yar sandar rakenshi a hannu
Waqa aka samasu ta qauyawa akafara shiga kamar a dandali ana rawa
Can aka saka waqar Naira Marley da cblvck mai taken *baby kingsway*
Duka manyan abokan ango idan ka cire ashraf da aka nemeshi ko sama ki qasa suka shiga Tareda mai girma ango daketa fama da malun malun dinshi ta fama
Suka shiga yin rawar waqar iri daya wanda da alama sunsha training kafin su iyata
Nan take wajen ya dauki tafi da sowa, abinda zaifi baka dariya shine rawar sadeeq don kafin sugama ya jigata sakammokon shan qasan dayake idan babbar rigarshi ta tadoshi kuma haka Yake tashi ya cigaba da rawanshi ko ajikinshi
Ansha dariya har saida cikin wasu ya kulle don wani abin da gangan sukeyi duk dan suba mutane dry
Saida suka gama sannan akaba Amarya da ango fili don su danse, aka saka masu waqar macukule suka shiga maming yadda kasan su suka yita dama
Kai fadin abubbuwan da akayi awajen 6ata bakine don sosai wajen yazama dandalin barkwanci don wasu saboda dariya cikinsu harya qulle
Can na hango yan group din *AUREN KWANGILA 1&2* da yan group din *OFFICIAL MARCY NOVEL* da yan group din *HOME OF NOVELS*
Can na hango *Maman naseer* na kallon *ayiya baby* dake qoqarin kwaikwayon rawar tingarangajam da wasu maxa keyi a filin wasan yayinda *beebat* da *Fatima haruna* ke tsamo2 cikin qawayen baby da alamun dai ansamu shiga
Awani bangaren kuwa *Maman Zainab* inkiya *nifa na nutsu😆* tana gefen ta nutsu tana kallon yadda wata kwaila daya daga cikin qawayen baby ke rawa kamar zata lauye
Akusada ita naga *Umma aliyu* da *malaash* suna tunsura dariya ganin kwalliyar wata wanda sak ya maidata wata ifrituwa
Agefensu kuma *Rahila Abba* ce tana rawar tambola har wani zaro harshe ake alamun rawa tayi dadi
Acan tsakiyar taro na hango *Maman Hassan* da ita da tawagarta su *ummukulthum*, *Dr halima* da *ummu sabira* tsaye kowa da Yar sandar rakenta ana wazga ana rausaya kai alamun abin na antayasu cikin shauqi sosai
*Ummu Muhseen* kau ana maqale bayan wasu yanmata yangayu masu selfie sai tantado take ita da tsiya sai an dauka daita (lol😆)
A bangaren ashraf kau dama fili na hargitsewa a rawar farko ya faki idon abokan shi ya lalla6a ya janye matarshi suka gudu
Dama jinsu bash yake lokacin dasuke cewa babu abinda zai hanashi dansewa ranar partyn ko training din rawan dasuka yi kallonsu kawai yake don bega lalacewar da zata sashi yin rawa a bikin koda kuwa ya iya bare shi zero over kunnuwa ne a fannin rawa, bega dalilin da zaisa yayi embarrassing din kanshi da kanshi ba
Saudart kau ta cika tayi famm don taji haushin gudowar dayayi da ita batareda taga komai ba a partyn hakan yasa ko kallonshi batayi saima kauda kai datayi tana kallon window din motar
Acan kau sai wajajen 10 na dare suka tashi kowa ya watse bakinshi dauke da labarin partyn
Washegari saudart taqara jin zafin tafiya daita da ashraf yayi sakammokon lbrin da yan biki ke badawa na partyn dama vidiyoyin da akayi, ta ciji yatsa sosai na missing datayi bama ita kadai ba harda wadanda suma basu samu hallata ba
Aranar gida ya ida kacamewa da jama'a kasancewar ranar daurin auren ne
Amarya ana can daki ita da zugar qawayenta masu halinta Wato duk yan iyayi ne, babu abinda ke tashi a dakin sai shewa da hirraraku, Amarya an qame akan gado taci adonta cikin wani danqareren pink lace mai touches din fari, fuskarnan tasha makeup ga kannan dashima yasha dauri
Babu ruwanta tana tsakiyar qawayenta suna shewa suna maida yadda akayi kamar ba ita za'a daurawa aure anjima ba
A bangaren saudart kau tana cikin jama'a komai da ita akeyi sosai dangin su ummy da Abba suka yaba qoqarinta don taxage komai daita akeyi.
Sai bayan an sauko sallar juma'a aka daura auren *ABUBAKAR SADEEQ UMAR* da *AMEENATU AUWAL (BABY)* akan sadaki mai daraja
Zokuga bakin ango, kasa rufe baki yayi don farinciki, mutane sai bashi hannu suke suna masu fatan zama lfy
Shima ashraf anci gayu cikin milk din yan ciki da babban riga kana ganinshi kaga aminin ango yayinda shikuma ango ke sanye da all white Wato komai nashi farine kama daga babbar rigarshi da yanciki zuwa takalmi zuwa hula kai komai nashi farine acewarshi yau farar ranace dole yayi shigar nuna hakan
Daga wajen daurin auren suka wuce reception inda akaci akasha cikin farinciki da aminci
Nanfa aka bude babin tsokana atsakanin angon da abokan ango, to dayake angon A ne shima sai caftar tayi dadi don duk abinda ka fada saiya samomaka amsarshi
Ashraf kau Kwata Kwata hankalinshi baya Kansu yakoma ga sarkin fushi Wato saudart da tun jiya tayimashi fushi don ya dauketa daga party, shi yanzu wani abin nata Dariya yake bashi don yanzu tazama wata rigimmamiyar qarfi da yaji, abu kadan sai kumburi
Tun dazu yake kiranta taqi dagawa, ganin bazata amsa dinba yasashi qyaleta yana cije lower lip dinshi
A bangaren saudart kau batama San yanayi ba don wayarta na cikin jakarta dake dakin ummy itakuma tana wajen Amarya da izuwa yanzu tayi laqwas, haka kawai taji jikinta yayi sanyi tun lokacin da labarin daurin aurenta ya risketa
Nanfa akazo aka zagayeta anata callara mata guda a kunne ana mata wakar tazama dauko riga
Tun baby na cijewa harta kasa riqe kukanta tashiga yin kayanta wurjanjan
Saudart ita abinma dariya yabata don bata manta yadda baby ke cika bakin babu abinda zaisata kuka ranar aurenta, ca6 kamar wani auren dole? Sai gashi tana kuka bilhaqqi da gaskiya
Dayake mutane duk sunsan shaqiyancinta babu wanda ya tausaya mata alokacin don kowa dariya yake mata yana qara tunzurata, saida akazo daukarta sannan tafara bawa mutane tausayi don kuka take sosai ta maqale umminta wai babu inda zata ita tafasa auren.
Dayawa sun tausayamata yayinda wasu irin su abokan wasanta sai qara tunzurata suke da waqar 'ke kikace kinaso'
Acikin masu tausaya mata harda saudart don sosai abin ya tuna mata da itama ranar aurenta hakan yasa take dauke hawayenta akai akai
Dakyar aka 6am6are Amarya jikin ummy da itama ke hawayen mixed feeling tana godewa Allah daya nunamata auren autarta lfy dakuma jimamin rabuwa da yarta wanda kowacce uwa mai aurar da diya keji
Haka aka fito daita akasata cikin galleliyar motar daaka tanadar ta daukar Amarya, cikin motar harda saudart don qin sakin hannunta baby tayi ta wani maqalemata dole saida ita aka shiga motar saudart na ayyana darun da za'asha idan zata taho
A wani qanqararren gida suka shiga, ba qarya gidan yabada don ya qawatu iya qawatuwa
Tarbar mutunci danginsu sadeeq sukayiwa su Amarya, gidan babu abinda ke tashi sai guda
Itade baby kanta na qasa fuskarta lullu6e da mayafi yayinda haryanzu take riqe da hannun saudart gamm
Saida aka rakasu hat dakinta dake sama yasha kayan alatu sannan ala barsu don suyi shirin walima
Chanza shiga duk sukayi inda Amarya taci adonta cikin maroon materials riga da skirt aka doramata alkyabba milk colour asama wanda hular ta rufe mata rabin fuska
Saudart dai shadda purple tasa riga da zane pieces sannan ta dora zumbuleliyar hijabinta wanda yanzu ya zamemata jiki don rabon datasa gyale harta manta don baban kishi be bari idanma zatasa saidai tasa cikin gida tayimashi kwalliya amma bawai tafita dashi ba
Sosai walimar ta qayatar, ango da Amarya sunfito sharr dasu kamar ka sace, ango shima dakkakiyar shadda milk yasha wanda sukayi ango shida dukan abokanshi, fuskarshi sai fidda annuri take
Ansha wa'azuzuka masu ratsa jiki sannan aka dora da zikiri mai antaya mutane shauqi sannan aka rufe da addu'a
Saida aka gama sannan aka maida Amarya dakinta dama kuma magrib tayi
Sosai baby ta tashi hankalinta ganin bata ga wulgin saudart ba, koina an duba ko sama ko qasa babu ita hakan yasa baby kuka sosai dukta tada hankalin mutane
Itakau saudart dama tun fitowarsu taga ashraf cikin zugan abokanshi, to tun kafin taron ya watse tabishi suka gudu bayan sun gama sassanta tsakaninsu
Baby kau taci kuka dakyar aka samu aka rarrasheta, qawayenta kau saida aka rako ango sannan suka samu suma suka fece tareda abokan ango, akabar daga Amarya sai ango (zakici ubanki ne😎)
*Agurguje*
Akwana atashi lokaci yacigaba da tafiya, kwanaki na zama sati, sattitika na zama watanni
Watan haihuwar saudart Yakama yayinda izuwa yanzu dukta chanza kammani saboda yadda cikin ya hurata
Ranar wata laraba ta tashi da naquda aka garzaya da ita asibiti
Saida ta wahala sosai sannan ta sulli6o danta masha Allah mai kamada ubanshi
Zokaga murna wajen wannan ahalin
Ashraf baki har qeya anyi da, anzama daddy
Sosai akayi hidima ga haihuwar wanda baby bata wani yi abin kirkiba awurin saboda qaramin cikinta dake bata wahala don mai laulayine sosai
Ranar suna baby boy yaci sunan kakanshi, Wato *AUWAL ASHRAF AUWAL (A.A.A)* sai ake Mashi laqabi da *Junior*
Ansha shagulgula a sunan inda sadeeq shima yayi bajinta donshi yabada abin yanka yakuma jidema baby kayyayaki masu tsada da yawa
Daddy ma yayi farinciki sosai kuma shima ya taka rawar gani a hidimar sunan inda shikuma yake kiran d'an da *Aminin*
*FIVE YEARS LATER*
Aguje wasu yara suka rugo suka nufi kitchen, ta gaban na qara tana kiran "mummy!" Da qarfi
Saurin juyowa saudart dake kiciniyar hadama Dad (ashraf) coffee tayi daidai yarinyar dabata fi shekaru uku ba ta fadomata ta rungume qaffafunta tana sakin qara
Burki yaron daya buyota yaja sanadin mugun kallon da mummy ke watsamashi, yaron bazai wuce 5 years ba, kallo daya zakaimashi kaga tsantsar kamarshi da babanshi
"Junior wai meke damunka ne? Kai kenan idan kana nan yarinya bazata walaba? What exactly is your problem?" Inji saudart rai 6ace
"Mummy wlh ita ta zubarmin da paint fa" yafada yana kumburi
Caraff yarinyar dake maqale still daita tayi tace
"Mummy wlh its not intentionally"
"Yimin shiru! Kin iya zuwa kijawo fada sannan ki rugo kina neman 6uya ko? Tom kacigaba, will apologize to him now ko saina makeki?" Tafada cikin zaromata idanu
Turo guntun bakinta yarinyar tayi sannan ta kalli Junior dake antayamata harara tace
"Am sorry"
"To zuciyatu kaji dai she's sorry, kuma kaima ka dinga sanin inda zaka ajiye abinka yadda baza"ayimaka barna ba kuma nasha fadamaka idan tayi maka abu kazo kayi reporting bawai kadau hukunci ahannunka ba amma bakaji ko?"
Sadda kai yayi qasa yace "am sorry"
"To oya kuwuce upstairs ganinan"
Juyawa duk sukayi ganin wanda ke bakin kofar yasasu sakin ihu tare sukaje suka rungumeshi
Duqawa yayi yana Shafa Kansu tareda jan kumatunsu
"Junior and zahra, Tom and jerry kunanan kuna sa mummy magana ko?"
Tare suka nuna juna zahra nacewa "it's him" junior na cewa"it's her"
Dariya yayi masu yajawosu ajiki yace
"It ok amma idan kuka sake bazan sake kaiku gidansu *Jidda* ba (diyarsu baby)
"Daddy mun daina!" Suka fada tare
"Ok now go upstairs Ku ida homework dinku ok?"
Jijjiga kai sukayi sannan suka juya sukayi waje aguje
Binsu da kallo sukayi saudart na girgiza kai sannan tajuya tacigaba da abinda take
Qarasowa yayi wajenta ya rungumota ta baya ya ziro kanshi ta wuyanta yana kallon abinda take yace
"Yadai matar contract"
"Ba lau ba mijin contract" ta amsa
Huramata iska yayi akunne yace
"Menene ba lau ba"
"Contract dinnan yayi due, yakamata akawo qarshanshi"
Juyo daita yayi suka fuskanci juna yace
"Ko?" Yana sissinar wuyanta
"Yes" tafada tana lumshe ido fuskarta dauke da murmushi
"Ok then, Ai alqawarinmu be cika ba, karki manta da deal din, sai munyi jikoki biyar, kinga ko yayan baki gamaba bare ayi maganar jikoki"
6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace
"To yanzu ya zamuyi?"
"Kawai Samar dasu zamuyi awuce wurin"
"How?" Tafada tana kallonshi seductively
Hade goshinsu yayi waje guda ta zura hannu tabayanta ya kashe gas din dakeci sannan cikin muryar rada yace
"By doing the do"
Kafin tasamu zarafin magana ya hade bakinsu wajen daya...✍️
Alhamdullilah!
Alhamdullilah!!
Alhamdullilahi rabbil alameen!!!
Godiya ta tabbata ga Allah s.w.t daya bani ikon kammala wannan littafin lfy
Kurakuren damukayi ciki Allah ya yafemana
Godiya gareku fans wadanda kuka jajirce kuna bibbiyar littafinnan har kawo yanzu da muka gamashi cikin qoshin lfy, Allah yabar zumunci yakuma dorar da zumuncin mu har a aljanna (insha Allah)
Taku akoda yaushe
Ummin fasihu🧚🏻♀️
Saikuma mun sake hadewa awani littafin
Ma'asallama🤝🏻