Showing 141001 words to 144000 words out of 173829 words

Chapter 48 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1146

alamun zata katse wayar

Dakatawa tayi don jin abinda kuma zai sake cewa

"Don't tell me kin manta da deal dinmu"

"Deal?"

"Kinji kenan, am waiting"

"Waiting for what?"

"Our deal, you promised zaki hadamin coffee kikawo apartment dina dazun, don't you?" Yafada yana lumshe idanu don sosai yakejin dadin wannan little conversation din nasu


Itakau saudart mammaki nema ya kamata, ita sai yanzu ma ta tuna dawani deal, lallai ma

"Kinyi shiru"

"Hmm wane coffee kake magana akai? Ni bànsan abinda kake magana akai ba"

Murmushi yasaki yana shafa kwanttacen sajenshi yace
"Really? Ko kinsan promise is a debt? Musanmman ma nawa promise din cos bana yafe bashi"

Daga kafadu tadanyi sannan tace
"Bye"

Bata jira cewarshi ba ta katse kiran

Maganar da ashraf ke shirin yine ta maqale jin an yanke kiran.

Sauko wayar yayi yabita da kallo cikin mammaki sannan ya kada kai.


Kashe wayar gabadaya tayi sannan ta aza kan bedside locker ta kashe wutan dakin tabar dim light don bata iya barci cikin duhu sannan ta janyo bargon da baby ta lullu6e dashi itama tashige ciki tana sauke Ajiyar zuciya

Addu'ar kwanciya ta karanta ta tottofa sannan ta qara qudundunewa a bargo tana lumshe ido


Cikin barci taji kamar kofa na motsi, ahankali ta bude idanunta dasukayi nauyi don barci ta kalli saitin kofar a kasale.

Ganin tayi kamar inuwar mutum hakan yasa taji gabanta ya fadi.

Qara bude idanuwanta tayi don tabbatarda abinda tagani din gaske ne.

Ganin shadow din na nufo gadonsu yasata qara lahewa a gadon zuciyarta na racing sai qoqarin karanto addu'o'i take amma takasa saboda yadda ta tsorata

Baby kau batasan wainar da'ake toyawa ba saboda she's fast asleep gashi Allah ya horemata nauyin barci

Zufa ke tsatsafo mata takoina gashi tana tsoron yin kwakwarar motsi don kar 6arawon yaganta kamar yadda ta dauka

Saida yazo gaban gadon sannan taga yaja ya tsaya kamar mai tunani saikuma taga ya nufo 6aran datake kwance

Rawa jikinta ya dauka yayinda tashiga karanto duk addu'ar dayazo zuciyarta, abin mammaki kuma takasa ihu sai mazari kawai datake daga kwance

Ganin yazo dab da ita yasata tamke idanunta tana sauke numfashi sama sama cikin tsananin kidima

Jitayi an matso dab da ita sosai har tana iya jiyo saukan numfashin mutumin akanta hakan yasata dauke numfashi cikin sadaqatwa

"My coffee.." Taji anyi wishpering a kunnenta

Bata motsa ba bata kuma saki numfashin ba

"Nasan kina jina, fulfill your promise" yasake fada yana hurama fuskarta iska


kamar wanda aka tsikara tayi saurin miqewa zaune tareda danna plug din kwayakwan wutan dakin, take dakin ya gauraye da haske

Karo idanunta sukayi dashi zaune a bedside lockern dake gefenta hakan ya haifarmata da mummunan faduwar gaba don ko kadan bata tsammacci ganinshi ba don ita duk atunaninta yana can gidanshi

Jada da baya zatayi yayi saurin cafko hannunta, bude baki tayi zatayi ihu yayi saurin dora yatsarshi manuniya akan lips dinshi alamun tayi shiru

Kasamcewar a mugun tsorace take yasata saurin hadiye ihun tana kallonshi a tsorace

"Bani coffee dina sai intafi" yafada still riqe da hannunta

"A.A?.." Tayi wishpering cikin son gasgata shi dinne

Daga mata gira daya yayi yace
"Yes?... I told you Ai bana yafe bashi, you promised zaki kawomin coffee idan na 6uya , so nacikamaki alqawarinki kema ki cika nawa"

Yanzu kau ta tabbatar da shine don har qamshin turaren nashine wanda dazu tsoro yahanata jinshi, amma me yakeyi agidan nan at this hour of the night?

Huremata idanu yayi tayi saurin lumshe su
"Kallon fa?" Ya tambaya yana daga mata gira daya

Dan Satan kallon baby tayi dake qudundune cikin bargo batasan me duniyar take ciki ba sannan ta dago ta kalleshi tana dan frowning face dinta

"Ka cikani please, am sleepy"

"My coffee" yabata amsa batareda ya saketanba

"Zan Maka ihu ummy tazo and you know she won't take it slightly with you" tafada threateningly

"Go ahead, zanfi kowa jindadin tazo ta iskemu hakan maybe hakan sesa tasan I need my wife"

Dan wara idanu tayi kafin takuma maida fuskar puppy face

"Please ka kyaleni, this is not right" tafada tana qoqarin kwace hannunta

"Menene ba daidai ba?" Yafada still riqe da hannun

"Everything, please leave me alone am sleepy" tafada kamar zatayi kuka

"Idan kinaso in kyaleki ki hadamin coffee dina kikaimin apartment dina"

"But dare yayi for crying out loud" tafada tana yarfe hannuwa

"And I won't leave without my coffee for crying out loud" yafada shima cikin yanayin data fada

Sauke Ajiyar zuciya tayi tace
"Ok kasaki hannuna tukunna"

"Ki gudu?"

"Zuwa ina?"

"Oho but I assure you kina yunkurin guduwa zan daukeki cak wlh bazan direki koina ba sai cikin mota and direct gida zan kaiki saidai ummy ta farka taga babu ke, kuma try me and see" yafada in a very serious tone

Tsayawa tayi tana kallonshi a mammakince, ganin zai iya yasata sauke Ajiyar zuciya tace
"Alright naji sakeni"

Babu musu ya sakarmata hannu yana kallonta without blinking

Dan murza ankle din hannunta tayi sannan ta bude baki dakyar tace
"Yanzu me kakeso nayimaka?"

"Simple.. Just make my coffee ki kaimin apartment dina shikenan"

"Ok zanyi maka gobe i promised"

Wani kallo yayi mata
"Are you kidding me?"

"Please.. Kaga yanzu dare yayi and ummy na iya jiyomu ta tashi and you know what the result will be, I promised gobe insha Allah zai zama first thing tomorrow morning, I promised"

"Hmm, I need my coffee now not tomorrow miss, idan ma ummy kikeji yanzu am sure she's fast asleep kuma aiba hayaniya zamuyiba... You know what? Da wannan 6ata lokacin damuke da yanzu kin manta da kin hada kin dawo kin kwanta, all I know is yau bazan kwanta ba saina sha coffee dina" yafada firmly yayinda cikin zuciyarshi Dariya kawai yakemata ganin yadda take kallonta in confusion

Dafe kanta tadanyi cikin rasa abin yi ga takaicin baby dake kwance kamar gawa wai ace duk abinda ake bataiba saikace mai barcin mutuwa?

Dagowa tayi ta kalleshi taga shi dinma ita yake kallo yawani jingina da bango ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta kamar ya samu mirror

Sauke Ajiyar zuciya tayi nannauya sannan ahankali tace
"Ok"

Murmushi yasaki sannan yamiqe tsaye yace
"Let's go

Badan ranta yasoba ta ziro qaffafunta qasa ta sauko.

Sleeping gown baqa ce a jikinta mai kauri wanda takaimata har qasa sai hular net ja dake kanta wanda ta cusa duka gashinta aciki.

Gwada mata hanya yayi ganin batada niyyar wucewa hakan yasata gittashi ta wuce ya bita abaya

Maimakon tanufi qofa saita maida akalar tafiyarta ga wardrobe din dakin ta bude taciro long milk colour hijab dinta tazira sannan ta nufi qofar fuskarnan hade kamar zatayi bindiga, binta yayi yana murmushi yanajin kamar ya rungumota ta baya ya dauketa in a bridal style yakaita har kitchen din.

Kamar munafukai haka suke sanda wurin sauka stairs din, saudart agaba hannunta tattare da gaban hijab dinta dake jan qasa shikuma biye a baya suna tafiya sadaf sadaf.

Suna gab da sauka qasa hijab dinta ya tadeta tayi gaba zata fadi.

Saurin riqo hannunta yayi ya janyota jikinshi ya tallabe

Ajiyar zuciya ta sauke don ta sadaqar faduwa zatayi

Dagowa tayi daga jikinshi ta sakarmashi harara mai cike da jin haushi sannan taqara sa hannu ta tattaro hijab din ashraf na tayata sannan suka cigaba da tafiya sadaf sadaf kamar qwarrarun 6arayi dasuka qware wajen sanda...✍️


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[12/2, 8:33 PM] +234 701 416 6830: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)


Story written by Ashaanty love💖




096


Cikin gida yanufa cikin tafiyarshi ta qasaita.

Koda yashiga falo be tarar da kowaba hakan yasashi haurawa sama domin gaisawa da ummy

Tsayawa yayi yana kallon kofar dakin baby kamar mai shawara can kuma ya janye idanunshi yashiga knocking din kofar ummy

Saida yasake knocking sannan yaji muryar ummy daga ciki tana bashi izinin shigowa.

Murda kofar yayi ya bude yashiga bakinshi dauke da sallama

Caraff suka hada idanu da saudart dake zaune saman bedside locker din ummy tana ninke mata kaya

Sauke idanunta tayi qasa gabanta na faduwa yayinda mafarkinta na dazu yashiga dawomata a qwanya

Kanta a duqe tana cigaba da ninkin kayan hannunta tana sauraron gaisawar dasuke cikin soyayya da nuna kulawa da juna dukda haryanzu ummy bata sakarmashi fuska sosai

Saida suka gama gaisawar sannan itama saudart ta gaidashi batareda ta yarda sun hada idanu ba

Amsawa yayi yana kallonta cikin so da qauna ko kunyar yimata irin wannan kallon agaban ummy beji.

"Kayi breakfast?" Inji ummy batareda ta kalleshi ba

"No, saukowata kenan Ai" ya amsa batareda yabar kallon saudart din ba

"Ok sai kaje kaci" tafada tana janyo wayarta tana dan dubawa

Kallonshi yamaida akan ummy sannan ya yamutse fuska yana yin alamun gajiya yace
"Ummy akawomin nan, am very tired"

Dan kallonshi ummy tayi sannan tadan ta6e baki tace
"Aikin me kayi harka gaji?"

"Ummy jiya fa sai wajajen two na kwanta, am busy working with my secretary"

Jin hakan yasa saudart Satan kallonshi suka hada ido ya kashemata ido daya yana smirking

Janye idanunta tayi tacigaba da abinda take

Ta6e baki ummy kawai tayi bata qara cewa komaiba, can ta dago ta kalli saudart dake ninke kayan wanda ba abinda yasamesu kawai son aikine irin nata da rashin son zama hakanan yasata takuramata saida tabarta tayi din

"Daughter"

Dagowa saudart tayi ta kalleta tana murmushi tace
"Na'am ummy?"

"Jeki ki kawomashi breakfast dinshi kinji?"

Sadda kai tayi tace
"To ummy"

Ajiye veil din hannunta tayi ta tashi ta nufi kofa a kunyace

Binta da kallo yayi harta fita ta rufo kofa sannan ya maida kallonshi ga ummy da ke kallonshi itama

Harara ta gallamashi ta dauke kai hakan yasashi sunkuyar dakai yana Sosa gefen wuya murmushi a fuskarshi

"Meya hanaka zuwa aiki?" Inji ummy batareda ta kalleshi ba

"Nayi taking leave ne" ya amsa a taqaice

Bata sake cewa komaiba saima maida kallonta datayi a wayar hannunta

Suna haka aka bude kofa ta shigo da sallama hannunta dauke da tray data hado kayan Karin akai

Qarasowa gabanshi tayi a kunyace ta ajiye mashi tafara niyyar tashi

Riqo hannunta yayi yana wishpering
"Wazai maki serving din?"

Saurin kwace hannunta tayi daga nashi tana satar kallon ummy a rude sai gani tayi hankalinta ma be wajen su

Hararar shi tayi da wutsiyar ido cikin jin haushi sannan tafara qoqarin hada mashi breakfast din

Ta rasa dalilin dayasa yakeson kunyatata agaban ummy, da tagansu fa? Gaskiya beda kunya ko kadan

Tana cikin hada mashi tea yadan sunkuyo saitin kunnenta ya rada mata
"Fatan baki manta da deal dinmu ba"

Saurin dagowa tayi tana kallonshi sannan taqara satar kallon ummy taga still basu take kalloba

Wai me ke damun wannan gayen ne? Abinda ta tambayi kanta kenan

Dan matsawa tayi daga kusadashi tana cigaba da hadawa a gaggauce don ta qagara ta tashi tabar wajen

Murmushi yasaki na gefen baki wanda shikadai yasan yayi abinshi.


Besake cemata komaiba harta gama hada mashi komai ta tashi takoma wajen kayan datake ninkewa

Jitake kamar ta tafi amma sai gani tayi bedace tabar kingin kayan ba hakanan

Cigaba tayi da ninkin wannan lokacin cikin sauri don jinta take a matuqar taqure

Tana cikin ninkin taji wayarta tayi beeping alamun shigowar massage

Bata damu da ta dubaba tacigaba da abinda takeyi kawai

Wani massage din ya shigo followed by another one duk atare

Hakan yasata dakyar wayar don ganin massage din dukna menene haka jejjere

Number data ganine yasata dagowa ta kalleshi

Kashe mata ido daya yayi yana smirking

Dauke kanta tayi yacigaba da abinda take taji wani text din yasake shigowa

Rolling din idanunta tayi sannan tasa hannu tayi sliding wayar ta bude lock din tashiga massages din

Samun kanta tayi da sakin murmushi ganin abinda ya turamata, kamar bazatayi reply ba saikuma tayimashi replying da emoji din *I don't care🤷🏻‍♀️*

Yana ganin haka shima yasaki murmushinshi yasake tura

*I'll make sure you do babe, it's better ki cika alqawari for your own good amma*

Ganin abinda yaturo yasata ta6e baki sannan ta turamashi emoji din
*oho dai💁🏻‍♀️*

Murmushi yasakeyi yasake mata text da
*hmm don't take it as a joke, am deadly serious, Zan baki mammaki idan kikayi tunanin playing dina cos there will be no mercy*


Data karanta nanma sake ta6e baki tayi tayimashi reply da emoji din🙄🙄🙄

*we shall see* yaturamata yana kwafa afili wanda yasa ummy dagowa ta kalleshi da alamun tambaya

Basarwa yayi yacigaba dacin abincin shi

Bata dadeba tagama ninkin duk ta maidasu cikin closet ta jerasu gwanin sha'awa sannan tacema ummy zata tafi

Cikin fara'a ummy ke mata godiya tana qarajin qaunarta acikin zuciyarta don saudart mutum ce data iya zama da mutane kuma tasan takan yadda zata sace zuciyar mutane da hallayenta kyawawa.


Shidai A.A be dagoba hartayimata sallama tafita


Bata dade da fita ba shima yamiqe ya kwashe kayan yafita dasu

Saida yakai kitchen, maid dinsu dake kitchen din tana qoqarin Dora girkin rana ta amsa cikin girmamawa sannan yadawo yaqara haurowa saman

Wannan karon kofarsu baby ya nufa

Kwankwasawa yayi har sau uku sannan aka bude

Mammaki yakama baby ganin shine don rabonda yazo kofar dakinta har mantuwar ta mance idanma wani abun yake buqata saidai ya kirata a waya ko ya aika a kirata

"Yaya? Good morning"

"Morning" ya amsa cikin basarwa yace
"Tana ciki?"

Tasan wanda yake nufi don haka tabada amsa da
"A'a yanzu yanzun nan tafita wai ta tafi wajen ummy"

"Ok" kawai yace yajuya

Binshi da kallo baby tayi tana gulmarshi acikin zuciya ta shige ciki tana kada kai

Bebi takan dakin ummy ba ya sauka yafita yanufi parking lot

Yashiga motarshi yafice daga gidan

Koda yadawo ma be gantaba, haka yasha zamanshi a falo duk don yaganta amma ko wulginta be ganiba.

Da zasuyi dinner ma bata saukoba saisu ummy shikuma yakasa tambaya

Haka yaita zuba ido ko zai ganta amma shiru

Da daddare ma saida ya lalla6a yaje dakinsu saidai wayam baby kawai ke dakin wanda hakan ke nuni da yau dakin ummy saudart ta kwana


Haka yakoma part dinshi yana cizon yatsa tareda ayyana yadda haduwarsu zata kaya.


Wasa wasa kwana uku kenan suna wasan yan 6uya tsakaninsu

Basu haduwa sai a lunch da dinner don yanzu abinda ke sauko da ita kenan tinda taji yadawo gidan shima da zama, da angama zata haye sama tashige dakin ummy

Kwata Kwata bata yarda su hade a inuwa daya su biyu kacal, kullum tana maqale dakin ummy.

Saidai hakan be hanasu magana through text massage, koda yaushe cikin warning dinta na karta yarda su hade don with every passing day tana adding salt into injury ne

Itadai bata bashi amsa sai emoji da take turamashi na rainin wayau wanda tasan zasu quleshi.

Wasa wasa yau kwana biyar kenan suna wannan wasan 6uyan, izuwa yanzu sun saba fira via text massage don kullum saisun kusa raba dare sunayi

Kullum cikin threatening dinta yake na karta yarda su hade, itakuma taita yimashi reply da emojis na rainin hankali tana Dariya ita kadai

Hakan saiya wanzar da shaquwa tsakaninsu batareda sun farga ba

Da daddare su kusan raba dare suna cafta washegari kuma dasun hadu wajen cin abinci inda anan kawai yake ganinta don inbanda cin abinci babu abinda ke fiddata dakin ummy sai idan ta tabbatar baya gidan.

Haka zasu hadu a dinning inda zasu dinga musayar magana da ido suna murmushi

Duk abinda suke uwar sa ido (baby) tana ankare dasu don tsabar sa idonta har qagara take su sauko cin abinci


Yauma kamar kullum suna zazzaune suna dinner

Vibrating wayar saudart tayi hakan yasata dan satar kallonshi tayi taga shima kallon nata yake ta qasan ido

Dan ta6e baki tayi taqi duba wayar

Ba dadewa taqara vibrating, qin motsawa tayi bare ta duba wayan

Qara vibrating tayi akaro na uku, murguda baki tayi takuma qi dagowa

Baby dake ankare dasu cikin zuciyarta tace
"Yau naga dan anace, tace yau batayi batayi dolene?"


Itakau saudart tana sane taqi kulashi duk don ta yayinda take mashi Dariya cikin zuciya

Tana cikin taunar lomar bakinta taji an zunguro qafarta daya ta qasan table din

Furzar da abincin bakinta tayi ba shiri saboda shocking dataji ya zirgamata daga dan yatsa har saqar kai

"Subhanalillah, lfy daughter?" Inji ummy tana kallonta cikin kulawa

"Am..am ok, kawai kwarewa..."

Jin an riqemata babban yatsar kafarta ta qasa yasata kasa qarasa maganarta taja baya da sauri tana sakin qara

"Subhanallilah! Daughter are you ok?" Inji ummy tana miqewa tsaye, itakau baby harta bar wajen tadawo bayan kujerar ummy

Itama saudart miqew,a tayi tana tura kujerarta baya tana kallon qasan table din atsorace

"Daughter lfy wai?" Inji ummy itama tana leqa qasan table din

"Wlh ummy wani abune mai shocking ya ta6a min kafa" tafada tana kallon qasan table din har lokacin

"Shock kuma? Son please dubamana kasan table din"

Ashraf dashima tinda aka fara drama din ya tsaida cin abincinshi yana kallonsu ya duqa don dubawa yayinda yake danne dariyarshi dake neman tonamashi asiri

Saida yagama leqe leqenshi sannan yadago yace
"There's nothing here nidai maybe imagination ne kawai"

Ganin irin kallon dayake mata qasa qasa da smirk din gefen bakinshi yasata gano abinda yafaru

Janye idanunta tayi cikeda takaicin tsoratata dayi.

"It ok daughter, maybe imagination dinne, relax babu komai OK?" Inji ummy cikin son kwantar mata da hankali

Gyada mata kai tayi takoma ta zauna tana qara Jin takaicin yadda ya tsoratata don ba qarya ta razanu.

Sai a lokacin itama baby ta dawo itama ta zauna adarare suka cigaba dacin abincin su inda suke hada ido da ashraf akai akai inda duk hada idon dazasuyi sai yayi jesting dinta itakuma ta qara fumming fiska ta kauda

Haka dai suka gama lunch din in silent sannan kowa ya tashi saudart ta haye sama as usual cikeda jin haushin abinda A.A yamata

Koda take daki tanajin yadda massages keta shigowa amma taqi bi takansu tayi banza da wayar taqi budewa

Yau Kwata Kwata bata biyemashi ba sunyi text din dasuka sabarma Kansu a yan kwanakin nan.

Tun yana turamata text din tsokana harya koma turamata apologizing text amma shiru taqi amsawa harya gaji ya kyaleta ganin dgaske ba kulashi zatayi ba, haka ya haqura ya kwanta yanajin ba dadi

A bangaren saudart kau duk text din dayake turamata saita bude ta karanta reply dinne kawai batayi


Jin shiru daga baya be qara turowa ba yasata jin badadi itama, ta dade tana kallon wayar kozai sake mata magana amma shiru hakan yasa itama ta haqura ta rintse ido ba dadewa barci ya dauketa.


Washegari duk sukuku suka tashi barin saudart data saba acikin yan kwanakin nan data tashi da text dinshi take fara karo saidai yau shiru kakeji

Haka ta zauna tana azkar din safe wayarta agefenta tana kallonta akai akai cikin saka ran ganin tayi beeping

Har tagama tayi tilawa dinta shiru kakeji, haka ta tashi jiki asanyaye tahau gyaran dakin ummy da yanzu yazama aikinta cikin sanyin jiki.

Sanin cewa kullum saiya shigo ya gaida ummy yasata zaman jiran shigowarshi saidai har 12 shiru be shigo ba, abinda bata saniba shine yau tunda safe yayi shirin zuwa office kuma koda yashigo, saiya tararda ummy kitchen anan suka gaisa, yaso yasameta daki ko don ganin hasken idaniyarshi amma haka ya haqura yafice daga gidan.

Wasa wasa har lokacin lunch babu shi ba text dinshi

Sosai saudart ta tsure, yayinda fargaba tacika zuciyarta musanmman data tabbatar da yau bema yini agidan ba Kwata Kwata kamar yadda yasaba a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login