Showing 54001 words to 57000 words out of 173829 words
ace nazo gidannan amma ko lura dani bakiyiba sbd wancan" yafada yana gallama saudart harara, aikau akaci sa'a shi take kallo lokacin daya watsamata hararar, hakan yasata kauda kai tana ta6e baki cikin zuciyarta.
"Saika rungumi sorry, aini idan daughter na waje macewa nake da kowa" inji Ummy cikin halin ko-in-kula
"Amma ai kinsan da tsohuwar Zuma ake magani ko?" Yafada yana turo baki
"Waya gayamaka? Sabuwar ma tanayi, wani sa'in ma tafi guarantee" tafada tana antayamashi harara sannan ta maida hankalinta Jan saudart data sadda kai tana saurarensu tafara janta da fira tana amsawa a kunyace itakam baby anyi 6amm ankasa magantuwa.
Ahaka aka gabatar musu breakfast sukadan ci sannan suka tashi zasu tafi baby sai liqewa saudart take tana mata rada Itakuma saudart na antayamata harara.
Haka suka fito har wajen da motarsu take.
"Anty ayimana tsarabar honeymoon, yan biyu nakeso masu kyanki" baby ta sake radamata a kunne.
Tsarabar harara tasamu harda mintsini Wanda yasata Sakin qara tana dariya.
"Ummy zamu wuce, ayafe" tafada a kunyace.
"To Allah ya yafemana gabadaya, Allah ya tsare daughter ya kaiku lfy ya maidoku lfy kinji? Ya tsareku daga sharrin masu sharri"
Baby ma tayi caraf tace "Anty Allah ya tsare kuma karki manta da tsarabata" tafada tana kashemata ido daya
Harara ta bankamata tana jinjina kai alamun zata gane kurenta ne.
Ashraf dake gefe yanata kumburi ya matso kusa yana cewa
"To saura saniyar ware, nima a taimaka ayimani addu'an"
Dariya sukayi gabadaya sannan Ummy ta rungumoshi shima tana mashi addu'o'i sai wani basarwa yake yana amsawa da amin ala dole fishi yake. Sannan shima yashiga motar driver dake ciki tundazu ya tada motar yajasu suka fice suna dagawa juna hannu.
Ajiyar zuciya yayi bayan sunfita ya koma ya jingina da kujera yana mammakin irin son dasu Ummy suke mata dakuma irin girmamawar da takewa Ummy dukda shi be wani dauki nata iyayen da darajaba.
Cikin yan mintuna suka isa airport din, lokacin shadaya da Rabi saura.
Cikin dan qanqanin lokaci aka gama komai suka shiga jirgin suka zauna mazauninsu dake kusada juna ita daga ciki shi daga baki baki.
12 dot aka fara announcing din kowa ya maqala seat belt dinshi jirgi zai tashi.
Komawa itama tayi zata daura amma duk yadda taso daurawa takasa abinka da sabon shiga😆
Tana cikin kiciniyar sawa taga an ziro an amshi belt din Wanda hakan yasa fatarsu ta gogu da tajuna.
Saurin sakar mashi tayi tana qamewa kujerar idanunta a ware tana kallon spotless light hannunshi harya gama dauremata ya janye yakoma ya jingina da seat dinshi ya cigaba da danne dannenshi cikin basarwa.
Ajiyar zuciya tayi ganin ya janye sannan ta gyara zamanta itama tana basarwa.
Jin anfara announcing jirgi zai tashi yasata fiddo wayarta tayi plugging earpieces ta maqalama kunne don batason jin tashin jirgin, she's so nervous ga tsoro fall cikinta saidai batason bada kanta musanmman datasan wannan marar mutuncin na kusada ita.
Lumshe idanu tayi tana sauraron waqarda ta kunna, Rabin hankalin kuma nakan tashin da jirgin keyi.
Jikinta a qanqame yake amma saika samata ido sosai zaka gane don kallon farko zakaga kamar she's normal.
Saida jirgin ya daidaita a sararin samaniya sannan taji normal tasaki jikinta.
Lafewa tayi a kujera idanunta a lumshe tana jinta duk a takure musanmman datasan yana gefenta ga qamshin turarenshi daya addabi qofofin hancinta.
Koda waiter din jirgin tazo tambayar abinda sukeso bata tambayeta ba don duk tunaninta barci take.
Ashraf kadai ta tambaya shima yace beson komai.
Tun tanajin abinda ake sama sama harwani barci mai shegen dadi yayi gaba daita.
*SPAIN - MADRID*
cikin barci taji kamar ana janye mata bargo, hakan yasata qanqame abinta tana yatsine fuska.
Jitayi an qara ja ana cewa "hey wake up"
Ahankali tafara bude lumsassun idanunta da barci be ishesuba.
Dishi Dishi tafara ganinshi har ganinta yadawo daidai
"Wake up sleepy head" yafada yana tashi tsaye
Saurin miqewa zaune tayi har bargon na faduwa.
Saurin duqawa tayi ta daukeshi zata linke sai wani tunani yafadomata arai.
Daga ina wannan bargon? Tasan daga ita sai kayan jikinta tayi barci, to shi bargon daga ina yafito.
Gani tayi wata waitress tazo taba Ashraf wata Leda tana murmushi.
Amsa yayi sannan ya miqawa saudart yana cewa
"Saiki basu bargonsu ko?"
Amsa tayi batareda tasan ko menene ba sannan ta miqama waitress din bargon tabi bayan Ashraf dayayi gaba.
Wani irin sanyi ya suroma saudart data fito daga jirgin, yadda kukasan tana cikin fridge
Qanqame jikinta tafara yi tana bin ashraf, saida suka amshi kayan su sannan Ashraf yajuyo yaga yadda take dan qanqame jiki.
Guntun tsaki yaja ya ajiye trolley din ta tako gabanta har suna musayar numfashin juna.
Saurin dagowa tayi tana kallonshi da alamun tambaya a fuskarta, batayi auneba ya fizge ledar hannunta yana gallamata harara sannan ya bude yaciro abin ciki ya sunkuyo yana doramata qatuwar jacket din pink Wanda takaimata har gwiwa.
Dagowa tayi tana kallonshi ganin yana antayamata mugun kallo yasata kauda kai tana yatsina baki sannan ta zura hannun rigar, ganin yana Neman ballemata buttons din yasata saurin riqewa tana cewa
"Thanks ina iyawa"
Saki yayi yana tsaki
"Thank God at least kauyanci da sauqi tunda kin iya balle buttons" ya juya yayi gaba
Rakashi tayi da harara sannan tayi sauri ta balle buttons din ta kama trolley din ta bishi kafin ya 6acemata.
Haka taita binshi Rabi tafiya Rabi Gudu don karya 6ace mata don airport din bade mutane ba gashi saiwani zabga uban sauri yake.
A gaban wata baqar dalleliyar mota taga ya tsaya wani da alama driver ne ya bude mashi yashiga, itama tana Qarasowa drivern yayi saurin zagayowa yabude mata yana gaidata cikin turanci, amsawa tayi tana murmushi sannan tashiga yarufe ya saka kayan a booth sannan ya zagayo dagudu gaban motar yashiga ya bata wuta sannan suka fice daga airport din...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
046
Cikin wani estate drivern yashiga dasu.
Estate ne hadadde Wanda ya amsa sunanshi estate.
Estate din shiru kamar babu mutane aciki.
Gidajene bungalow Jere duk iri daya.
Bazaka iya banbancesuba saika duba number dake liqe a kowanne kofar gidan kasancewar gidajen Jere suke according to their numbers.
Kowanne gida an qewayeshi da furranni masu kyau da ban sha'awa.
"Wow!" Saudart tafada cikin zuciyarta tana qara ware idanu tana kallon gidajen ta windown motar.
Sosai wurin ya qawatu gashi babu mutane sosai a unguwar sai yan jefi jefi dake wucewa a qasa ko bisa abin hawa.
Kowanne yasha kayan sanyinshi saboda sanyin da'ake surawa.
Allah mai iko, Allah daya gari banban.
Acan Nigeria ana can ana sheqa musu ruwa sukau nan sanyi ake zuba musu.
Haka taita kalle kallenta hartaji tsayawar motarsu.
Kallon inda suke tayi taga agaban wani bungalow irin wadanda suka baro suke babu ko banbanci harta fentin
Jin an budemata kofar yasata barin kallo ta dauki handbag dinta tafito tana kallon harabar wurin.
A wayence take qarewa wajen kallo.
Gidane bungalow dan qarami kamar dai wadanda suka wuto.
Kewaye yake da furrani that are well trimmed, butterflies (mallam bude takarda) sai kara kaina akai suke gwanin sha'awa. Ga koina tsit bakajin komai sai kukan tsintsaye masu dadin sauraro
"Wow" tasake fada cikin zuciyarta tana jin wani shauqi na dibanta, the place is soo perfect.
"Idan kin gama qauyancin saiki shigo" taji an fada a bayanta.
Saurin juyowa tayi taga harya shige ciki.
Harara tabishi dashi sannan itama tafara takowa janye da trolley tana humming din waqar wonderland na film din yar tsana barbie ahankali tanajin nishadi har cikin zuciyarta.
Saida tashiga ciki sannan taga Ashe gidan daga waje yake dan qarami don cikin ba laifi akwai girma sosai.
Wani makeken falo zaka fara cin karo dashi dake kewaye da wasu qayattatun guntayen kujeru sai kofofi uku dake jikin falon a different direction Wanda hakan ke nuna dakuna ne awajen sai daga haggu wani ke6anttacen wuri da akasa dining table aka zagayeshi da chairs, daga dama kuma idan kadan bi kusurwar wajen zai sada ka da kitchen.
"Your room" ta tsinkayi muryarshi yana cewa haka.
Kallonshi tayi taga yana gwada mata daya daga cikin dakunan Wanda dakin shi kadai ne babu wani kusa dashi sa6anin kingin biyun dake kusada juna.
"Mine" ya nuna daya daga cikin biyun dake Jere.
"Study room" yafada yana nuna dayan sannan batareda ya qara cewa komai ba ya juya yashiga dakin dayace nashi ne yabar ta nan tsaye tana binshi da kallo.
Tsaki taja tana kwaikwayonshi
"Your room... Mine... Study room, mtcheew botorami kawai"
Tafigi trolley dinta tashiga dakinta.
Dakin dan madaidaici ne bawani girma ke gareshi ba.
Akwai dan qaramin gado a dakin shima dan dunqullale kamar kujerun falon, sai wardrobe mai dan girma sai mirror da babu komai Asama sai wani study table and chair daga gefe.
Ajiye trolley din tayi ta cire jacket din saman rigarta tashiga qalqale dakin dukda ba irin dattinan yayiba, yadaiyi qura sama sama
Canza bedsheet tayi ta goge wardrobe din ta fiddo yan kayanta ta jera sannan ta goge saman mirror ta jera jera mayyukan shafawanta da kayan kwalliyarta akai dukda bawasu yawa ke garesu ba sannan tabi koina ta share ta goge sannan tashiga toilet ta wanke shi Tass.
Fitowa tayi falon taga babu kowa babu 6ata lokaci ta shiga gyara falon shima dayake beda wani tarkace nan da nan tagama gyaranshi takoma kitchen nanma ta gyara ta gogeshi tsab.
Abinda zai burgeka gameda ita shine batada qyashin aiki gata da kazar kazar tana aikine da dukkan kuzarinta.
Fitowa tayi riqeda bokiti da mopper aciki hannun rigarta a tattare zuwa gwiwa Wanda yaba siraren fararen hannunta bayyana.
Dagowar dazatayi sai idanunta ya sauka akan nashi.
Tsaye yake bakin dakinshi ya sauya shiga zuwa qananun kaya baqaqe sai qatuwar jacket fara daya Dora akai.
Janye idanu sukayi gabadaya daga kan juna cikin basarwa.
Wucewa yayi hanyar waje yana cewa "karki fita" ya fice
Bin bayanshi tayi da harara harya fita sannan taja tsaki tana cewa "to ubana"
Maida kayan datayi amfani dasu tayi ma'ajinsu sannan itama ta shige dakinta don yin wanka.
Cikin yan mintuna tafito ta sauya kayanta zuwa wata gown din baqa sannan ta shimfida sallayar ta gabatar da sallar la'asar da aketa kira.
Tana nan zaune kan sallayar taji ana bubbugo kofarta.
Jimm tayi tana sauraron bubbugar kofar tana tunanin wake bubbugamata kofa.
Qara bubbugawa akayi wannan karon da dan qarfi hakan yasata miqewa ta nufi kofar ta bude ahankali.
Shi tagani tsaye bakin kofar ya juyawa kofar baya.
Yanajin an bude yaja tsaki sannan ya miqamata ledar hannunshi batareda ya juyoba.
Amsa tayi babu musu sannan batareda ta jira komai ba ta rufe kofarta cikin bugowa da qarfi.
Juyowa yayi yana kallon ruffafen kofar a mammakince sannan yayi qwafa yana jinjina Kai sannan shima yawuce ya zauna falon ya bude takeaway dayayi yafaraci.
Itakau tana shigewa dakin ta tsaya tana antayama kofar harara sannan tawuce ta zauna bakin gadon tana bude ledar tana yatsine fuska.
Takeaway tagani na fried rice da fried plantain akai sai robar fresh milk mai sanyi.
Ta6e baki tayi sannan tabude tafaraci don dama yunwar takeji rabonta da abinci tin a gidan Ummy.
Koda tagama kwanciyarta tayi kan gadon tanata buga game don debe kewa.
Sosai takeson yin kyau waya da yan gida amma bata chanza layi ba so it's impossible.
Tananan kwance har aka fara kiran sallar magrib.
Tashi tayi ta dauro alwala tayi ta zauna tana tilawa har aka kira isha'i sannan ta tashi ta kawota itama.
Tana cikin linke sallayar sallar taji ana bubbugo kofar dakin.
Waigawa tayi tana kallon kofar batareda tabar abinda takeba.
Jin anqara bugowa yasata cewa "waye?"
"Open the damn door!" Taji anfada cikin tsawa ta waje
Guntun tsaki taja ta cigaba da linke sallayar sannan ta maidata ma'ajinta sannan tanufo kofar tana kumburi.
Ganinshi tayi a tsaye ya tattara komai na fuskarnan ya hade waje daya.
"Menene?" Ta tambaya cikin halin ko-in-kula da yanayinshi
"First and last warning, karki sake barina tsaye ina knocking a kofar nan ok, gidanane ba nakiba ok?!"
"Mtcheew amma ai dakin dakinane ko" tafada a zuciya a zahiri kuma tace
"Ok, menene?" Tafada hannunta riqeda kofa alamun jira take yafadi meya kawoshi takoma ciki
"And secondly, karki manta am still your boss, speak to me in respect, ok?" Yafada Yana hararar ta
Ajiyar zuciya ta sauke tana harde hannunta a qirji don taga abin nayi ne
"Ok" tafada tana kallonshi
"Now jeki shirya kifito and kar qauyanci yasaki barin jacket din kizo kina bina kina kakkarwa kamar mai falfadiya" ya juya yawuce
Binshi da kallo tayi sannan taja tsaki tana cewa "psycho kawai"
Sannan takoma ciki.
Bata dauki lokaci ba wajen shirya wa ba tafito sanye da light pink jallabiya ta yafa gyalen in a simple way ta Dora jacket din akai don ko Karen hauka ya cijeta tasan bazata iya fita hakanan ba.
Awaje ta iskeshi zai shiga mota.
Qarasowa tayi itama ta kama kofar baya zata bude.
"Mallama who is your driver?" Ya tambaya tana binta da wani kallo
Sakin kofar tayi tadawo gaba ta bude tanajan tsaki cikin zuciyarta 'kai wlh Dad ya hadata da qalli qallala wlh" tasake Jan wani tsakin
Shima shiga yayi sannan yaba motar wuta suka fara tafiya.
Tafiya suke cikin normal speed babu mai tankama wani kowa da inda yake kallo.
Koina fayau yake da haske kamar ba dare ba kuma ga mammakinta sai gani tayi akwai mutane da dan yawa yanzu awaje sa6anin dazun da rana.
Wasu zaune kan grass carpet suna fira wasu suna tafiya mostly mace da namiji hannayensu cikin juna.
Haka taita kallon garin tana yabawa kyawunshi a zuciyarta har suka qaraso inda zasu.
Shi yafara fita sannan itama ta bude kofar ta fito.
Gani tayi supermarket ne yakawota.
Ganin yayi gaba yasata binshi itama.
Basket ya dauka yawuce yafara shopping dinshi yabarta nan tsaye.
Da farko Qin motsawa tayi daga inda take, can kuma sai tayi wani tunanin, tabbass tana buqatar kaya most especially kayan sanyi don taga alamar sanyin garin bana irin nasu bane.
Itama basket din ta dauka tafara zagaya wajen tana daukar abinda takeso kama daga kayan sanyi, turarruka, air freshener na daki Dana toilet, mayyukan wanka da dai sauransu.
Saida tayi shopping son ranta sannan ta qaraso wajen biyan kudin.
Matar wajen ta zazzage kayan tana listing dinsu daya bayan daya harta gama sannan ta maidasu a wata shopping bag tabata.
Amsa saudart tayi sannan ta fiddo purse dinta da duk kayan amfaninta ke ciki ta fiddo ATM dinta taba Matar.
"No ma'am, the fee is paid" tafada tana murmushi
"By who?" Inji saudart kamar batasan wazai biya din ba
"By a guy" ta amsa
"Well bansanshi ba, bansan ya biyaba, abinda nasani shine nayi shopping and am paying myself" tafada cikin turanci...✍
Battery low!!!
Anmani hankali ranan, idan nacigaba wayata na iya mutuwa inyi biyu babu, please kuyi manage zan fanshemaku gobe insha Allah da page biyu.
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Jinjina gareku fans din AUREN KWANGILA gaskiya naji dadi sosai da nuna qaunar dakukema book dinnan.
*Ummu sadik* ta AUREN KWANGILA NOVEL GROUP ina yinki sosai, ngd da addu'o'inki agareni dama sauran yan group din gabadaya, Allah yabar qauna💖
Jiya nayimuku rushing😆 wlh banda chaji sosai ne shiyasa nace koyayane bari nadanyi yafi babu, amun afuwa🙏
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
047
"Erm.. Am sorry ma'am amma anbiya" Matar tafada.
(Note duk da turanci suke magana ni zan dan sirka da Hausa saboda sauqin fahimta)
"Then zan maida kayan" tafada tana qoqarin juyawa.
A halin yanzu babu abinda ta tsana kamar ayimata alfarma, alfarmar ma ta rasa Wanda zaimata sai A.A? No, bata ciba yamata gori inaga taci?
"Please ma'am, wait a minute" inji Matar tana yan latse latse a landline din gabanta sannan ta dauka ta kara a kunne.
Magana tafara cikin yaren Spanish, itadai saudart shiru tayi tana sauraronta dukda batasan me take cewaba.
Can saita ajiye wayar murmushi a fuskarta tace "ok ma'am, kawo ATM din"
Babu musu ta miqamata tacire kudin sannan ta maido mata.
A bangaren Ashraf kuwa duk abinda yafaru yana sane don suna tareda managern supermarket din daya kasance tsohon abokinshi ne tun primary.
Agabanshi Matar takira manajan tana cemashi Matar tayi insisting kan ita zata biya kudin
Jin haka yasa manajan gayama Ashraf din, nunawa yayi babu matsala amma deep down kamar yayi bindiga yaji don a gurinshi ba qaramin zubda mashi mutunci tayi most especially da manajan ke tsokanarshi wai ya canza dubara wannan batayi aiki ba don duk tunaninshi irin yaganta dinnan ne ya qyasa yana son shigar da kanshi.
Shidai banza yayi dashi sukayi sallama sannan yanufi motarshi daidai itama ta qaraso.
Beko kalleta ba ya bude mazaunin driver yashiga, cikin zuciyarshi yana ayyana abinda zaimata ya huce.
Oho batasan yanayiba, itama budewa tayi ta zauna sannan yaja kamar zasu tashi sama sukabar wajen.
Yadda sukazo haka suka koma babu mai cewa komai.
So take ta tambayeshi inda ake siyarda layi amma tana gudun dizgi don taga fuskarshi babu alamun yakosan Kalmar dariya, hakan yasa tashafawa kanta lfy tayi shiru har suka iso gida.
Yana parking ta bude kofar kamar dama jira take tafita hannunta riqeda ledojinta, zata wuce ya dakatar daita dacewa
"Gobe 10:00am.. Be ready" yafada ataqaice.
Batace komaiba tajuya tashige tana ta6e baki.
Saida ajiye duk abubuwan data siyo inda ya kamata sannan ta jona ruwan shayi a heater data siyo ta shige toilet don yin wanka.
Kayan barci tasa bayan ta fito ta hada kakkauran shayi da kayan tea din data siyo tasha sannan ta shige cikin bargo sai 😴
Washegari tunda wuri ta shirya don sosai take bama lokaci muhinmmanci, idan aka bata appointment bata wucewa saida dalili, batada African time ko kadan
Tun tana jira adaki tana kasa kunnen jin fitowarshi harta fito falo ta zauna ta cigaba da jiranshi.
Sanye take cikin wata baqar Dubai gown Wanda yad'an kamata daga sama ya bude daga qasa. Tayi rolling da gyalen rigar ta Dora qatuwar rigar sanyi baqa akai mai flowers farare jefi jefi.
Kafarta sanye da baqin booth na mata Wanda yakai mata har gwiwa, fuskarta daukeda simple makeup, Jan la66anta sai walqiyar lip gloss suke, tayi kyau sosai cikin shigar abinka da farar fata.
Fiddo hannunta na dama dake cikin aljihun rigar sanyin tayi ta kalli baqar agogon dake daure da tsintsiyar hannunta taga har sha daya da minti goma.
Sake kallon kofar dakinshi tayi a karo na ba adadi tanajin kamar taje ta bubbuga kofar.
Tsaki taja cikin jin haushi, ita ba komai yasa ta qagara yafito sutafi ba saidan sotake sufita ta siya sim card tasa kozataji muryar yan gida taji sanyi.
Maida kanta tayi kan jikin kujerar, hannunta zube cikin aljihun rigar sanyin, zuciyarta ba suya.
Wannan wane irin wulaqanci ne? Yace 10:00am gashi har to 12 amma ko niyyar fitowa be dashi.
Shikau a bangarenshi yana sane daita kawai wulaqanci ne, acewarshi itama taji yadda yaji jiya a supermarket. Tundazu yana jin motsinta a falo yayi biris ya qyaleta.
Sai 11:20 ya tashi yashiga wanka bayan yan mintuna yafito sannan yafara shiryawa don qarfe 2;00pm sukeda