Showing 24001 words to 27000 words out of 173829 words
fuskar kamar aljannu.
Binsu taitayi da kallo kafin Daga bisani tayi musu murmushin nan nata mai tafiya da mutane.
"Sannunku please have a seat" tafada cikin faran faran.
Kallon juna sukayi suna kya6e baki.
"Please Ku zauna, maryam a aiko da Kayan motsa baki"
"No need, ba wannan ya kawomu ba, magana ce ta fatar baki ta kawomu muyi mu fice Tun kafin numfashi ya gagaremu a wannan garbage din" inji beebah
Suzy kau tunda ta Dora idanu akan Saudart jikinta yayi Sanyi sbd tama wuce yadda take ganinta a pics ga wani nutsuwa da kwarjini da Allah yaimata.
Nan take kishinta yaqara ninkuwa a zuciyarta wata Wutar qiyayyarta na sake ruruwa.
Dukda bataji dadin amsarsu ba sai bata nunaba ta wayance tana cewa
"Ok, how may I help you?"
"Help who?" Inji beebah tana aikamata kallon raini.
"Baki kai matsayin da zamu nemi taimakon ki ba, we came here ne sbd muja kunnenki for your own good, ki fitar harkarmu don bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane"
Shiru Saudart tayi tana kallonta don ita tunda take bata ta6ama ganin fuskoki Masu Kama da wadannan ba bare wani Abu ya hadasu, to kodai 6atan kai sukayi?
On the other side kuma maryam ce Wanda dama bata fitaba, sai huci take qasa qasa don dama saida sukayi rashin mutunci kafin su shigo mafarin shigowartama kenan fuska a cunkushe.
"Amm.. Excuse me, gaskiya inajin 6atan hanya kukai don ni gaskiya banma ta6a ganin fuskarku ba sai yau"
Wani makirin murmushi mai sauti Suzy tayi sannan ta qaraso tana Jawo kujerar dake facing din Saudart ta zauna tana Dora kafa daya bisa daya Wanda hakan yaba cinyarta damar fitowa gabadaya.
"Really? Are you sure baki ta6a ganin fuskar mu ba? More especially ni? Kenan Darling din naki be fadamiki komai akainaba"
Calculation tafarayi, Darling? Darling dina? Waye kenan?
"Well, am A.A's girlfriend, his babe" ta qarashe zancen tana cire Google din idanunta tana juyi da idanun tana kalkadasu a duniyance.
Wani murmushi ya kufcema Saudart, lallai iska na wahalar da mai Kayan kara, tofa Ashe dama yanada budurwa, lallai aikau sunyi matching.
Itama cikin duniyanci tadan Waro idanu
"Wow! Ashe anty ce? You're highly welcome, Aida kinfada tunfarko, Saidai how come baby boo na beta6a bani labarin ki ba, you're welcome please maryam akawoma anty abin ta6awa"
Wani qululune ya Tsayawa Suzy a wuya, baby boo? Lallai.
Beebah dake tsaye haryanzu ta bata amsa.
"Ba abun mammaki bane idan baby boo din naki be ta6a baki labarinta ba, kinga kenan yaudararki yake, Bayan ke yanada wata kuma 6oyemiki dayake ya nuna ba sonkiba yake, playing dinki yake" tafada cikin son cusamata Kishi.
Wata yar siririyar dariya Saudart tasaki tanayin luuu da idanu sannan takuma budesu, Wanda Duk saida suka saki baki suna kallonta don abin ba qaramin kyau yaimata ba.
"Dani da ita wa yake yaudara? Look" tafada tana nunamusu zoben hannunta Wanda yasamata Tun ranar datayi signing din contract din.
"Shiya sakamun zube a gwiwowinsa yana roqona na aureshi, secondly ya nunani wa jama'a and am quite sure kuma labari yajemuku and lastly maganar danake muku haka akwai baikonshi akaina, yanzu wa yake yaudara? Waye main chick a cikinmu kuma waye side chick? Look it normal saurayi yayi budurwa samada goma, what matters is wa yakeso kuma yakebi Amma ba Wanda ke sonshi kuma take binshi ba, he's my fiancée kekuma he is your boyfriend ko makaho ya laluba yasan akwai banbanci a tsakanin sunayennan biyu, so zan baki shawara kafin kice ko kuce zaku yanke hukunci Ku fara auna abin a mizani Ku fara tantance matsayinku sannan kuyi bursting, ok?"
Tsit kakejin office din, Wutar su gabadaya ta dauke, maryam dake baya tundazu kamar taita rawar zanku don murna.
A afusace Suzy ta miqe tsaye tana bugun saman table din da karfi sannan ta nunata da yatsa
"Who the fuck did you think you are? Ehh? Kinsan koni wacece? Ehh? Kinsan koni diyar wanene?!"
"Ta yaya za'ayi in sani? Bayan a fuskama sai yau nafara saninki? Wacece ke din? Diyar wacece? Diyar bill gate? Ko mangal? Ko dangote? Please ki Sanar dani Atleast sai nayi keeping record kan na ta6a Kasa diyar wani shege a fagen love" tafada tana murmushi.
Kutt... Nufota tayi gadan gadan beebah tayi saurin tareta.
"Easy, easy Suzy, ki barta just calm down ba girmanki bane.."
"Ato, gayamata dai don da alama tayi nisa batajin kira, be kamata tana irin wannan abun yaranba inhar tanaso a taimaka a karata"
Wani kallo beebah ta watsa mata
"You'll definitely regret this, and also ruwan kine ki fita harkar A.A ruwanki ne karki fita, Amma a shawarce zaifi miki kwanciyar hankali kifita harkarshi for your own good, if not..." Saita saki murmushi tana kada kai.
"If not?.."
Inji Saudart tana langwa6e kai tana wani jujjuyawa saman kujera.
Matsowa beebah tayi gab da ita tana dafa table din da hannaye biyu tadan sunkuyo cikin rada tace
"If not Daga ke har almajirin babanki sai kunyi danasanin zuwanku duniya.. Have a nice day"
Ta qarashe zancen tana kalkadamata yatsu sannan ta kama hannun Suzy tajata suka fice.
Binsu da kallo tayi har suka fice sannan ta saki wani murmushin takaici.
'Dad Kaga abinda kaja ko? Kaga abinda kwadayinka yaja mana ko?' Duk acikin zuciya take wannan zancen.
Jingina tayi da kujerar tacigaba da juyawa ta maida idanunta ta lumshe, zuciyarta fall da baqinciki.
Ganin haka yasa maryam lallabawa ta fice ta jamata kofa zuciyarta fall da tausayin ogansu...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu.
Wayyo fans, nayi missing dinku irin totally dinnan☹, kwana biyu kunjini shiru wlh hidimace ta tisoni gaba, ban samu kainaba sai yau.
Masu bugomun waya donjin ko lfy da Masu cigiyata a group, ina godiya da kulawarku agareni.
Ashaanty na yinku irin totally dinnan😍
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
025
Wasa wasa ranakun sai tafiya suke, dukkan 6angarorin wato na Saudart da Ashraf sun Shiga busy.
Su Ummy an dage wajen hada lefe na gani na fada, donma wannan coronar tahana fita waje da acan za'ayi sayayar Amma dukda hakan kayane ba gani na fada wanda kallo daya zakayi musu kasan anci uban naira.
6angaren daddy ma ba'a barshi abayaba don Kayan daki haddadu kayattatu yayi ordering har set biyu.
Ga shima ya hada mata nashi lefen na musanmman abinka da mai irin sana'ar.
Set daya na akwati wato akwati shidda maqare da kaya Nagani na fada yayima shalelenshi.
Niko nace anya be manta cewa auren na dan taqaittacen lokaci bane🤔
Bangaren mamy ma ba wasa, Kayan kitchen na musanmman take hadama angel dinta, abinka da ita kadai ce diyarta mace, Duk burin duniya ta Dora akan auren diyarta, sosai naira tayi kuka wajen hada Kayan kitchen din, shima Abba wato mijin mamy ba'a barshi abaya ba don dangin electronics wato su plasma, generator, deep freezer, ovens e.t.c
Duk shi yayi mata, abin dai zai😉
Su dangin mamy da Abba suma ba'a barsu abayaba don sosai suka bada gudunmawa dukda yanzu bawai kudi ke akwai sosai ba.
Sosai suke son Saudart saboda kirkinta da zumunci ga uwa uba girmama na gaba da son mutane.
Ataqaice dai kallo daya zakayima hidimar bikin kasan na yan gatane, yan gaban goshi kuma
Duk wannan haukan da'ake Daga amaryar har angon babu wanda yasan Anayi.
Kowa harkar gabanshi yake hankali kwance.
Don wani sa'in har mancewa da wani aure suke.
Bikin na sauran sati biyu mamy ta buqaci Saudart tadawo gurinta har zuwa bikin.
Alhaji shamsu be hanaba haka itama Saudart dadi taji sosai koba komai zata rage zaman kadaici tunda ga su Abdul.
Saida taje sannan tasan manufar mamyn na dawowarta nan, wato gyarata mamy zatayi ciki da bai.
Da farko taso qin yarda da Gyaran Amma da mamy ta tambayeta dalili Kasa amsawa tayi Dole t hqr ba don tasoba aka fara gyarata wasan zuciyarta kuma tasan asarar kudi kawai ake, Auren da na yan wattani ne?
Gyara sosai akema Saudart, abinka da yan Maiduguri.
Cikin yan kwanaki Saudart tafara riqidewa, ga dama yaya lfy giwa, dama can mai kyauce kuma tana bama fatarta muhinmmanci sosai take sheqi Amma yanzu tafi sheqi sbd dilkan da'ake mata ta musanmman.
Hakan a 6angaren Kayan mata da maganin Sanyi Duk ba'a barta abayaba.
Ingattatun Kayan mata da aka hada da fruits ake bata, ga yawan shan farfesu da ake sata tayi, gashi yanzu batada abinsha sai tattaciyar madara ko kindirmo.
Haka a bangaren lectures gameda auratayya, sosai mamy ta cire kunya ta zauna ta nusar da Saudart abubuwan da batasaniba gameda aure, tana kuma koyarda ita dubarun zama da miji, abinda wasu iyayen mata yanzu basu iyawa Wai kunya, qarshen kunya dai shine ki Tisa diyarki gaba ki bata Kayan mata, tunda itama tasan me kike bata da kuma amfaninsu tunda yanzu kai ya waye, a wajen karance karancennan ma wata Duk tasan komai.
So iyaye mata ba'a maganin mata kawai yakamata mu tsaya ba, mu nusar dasu miye auren da kuma abubuwan dasuka qumsa don dayawa yanmatan mu basusan ainahin menene auren ba sundai san in anyi aure ana tarraya tsakanin miji da mata, Amma basusan yadda zasu kula da mazajensuba dadai sauransu don ba'a koyamusu ba, Abu daya kawai aka koyamusu shine shan Kayan mata sai kiji har akwai mai suna, mallake miji, bita zai zai dade sauransu.
Babu abunda zaisa ki mallake miji yadawo tafin hannunki kamar biyyaya da tsantsan kyautatawa tunda zuciya tana matuqar qaunar mai kyautatamata.
Duk Kayan matan dazaki dirqa a banza don wasu sai sunason harkar zasu mutuntaka daka basu sun gama nan take suna iya sufkama rashin mutunci, Amma mace mai biyyaya da kyautatawa bazata ta6a wulaqanta ba awajen mijinta.
Tun Saudart najin kunyar mamy idan tafara mata ire iren lectures dinnan harta Bari don mamy ba ruwanta.
Su Abdul baseet sunji dadin dawowar Saudart gidan don sosai take debe musu kewa.
****************************************************
"What?! 5 million? 5million? Kam bala'i? Lallai kana wasa da wuta"
Afusace ya miqe ya nufi hanyar waje ko Dora suit dinshi dake rataye beyiba.
Kwankwasawa yayi a afusace ya murda ya bude batareda yajira anmashi isoba.
Dagowa Sadeeq yayi yana kallonshi sai huci yake kamar mayunwacin zaki.
"Toha, lfy ango kasha qamshi? Wannan dirar mikiya haka? Ai sai Kasa in arci na dog"
"Sadeeq ina wasa dakai?" Yafada cikin Fushi
"Ehh" yabashi amsa hankali kwance.
"Dan ubanka Kalla, Kalla nace" yafada yana shaqoshi yana nunamishi screen din wayar shi.
"To ai ta dauke mallam, Wai ya haka? Ka sakarmin wuya"
Sake Kunna wayar Ashraf yayi sannan yaqara haska mishi
"Ubanmi aka rubuta?" Injishi yana huci
"Anyi withdrawing 5million" Sadeeq ya amsa yana matse idanu sbd shaqarar da Ashraf yayimashi.
"Dan ubanka me kayiman da kudi har 5million? Daga cewa za'ayi project saika zaremin 5million? Dan ubanka ina project din?"
"T...to ka sakeni mana in amsa"
Sakinshi yayi yana galla mashi Harara.
"Aradu badan Kai ango bane daka gane kurenka, mugu kawai"
"Naji, ina kudina?"
"Na cinyesu nikam, Haba!"
"Kasan Allah saika fadamin uwar ne kayi dasu"
"Mtcheew, banza to na cire naqara wajen hidimominka, Shikenan?"
"Wane hidima!"
"Bansaniba! Mtcheew dalla ficemin office aiki nake"
Shaqoshi yaqarayi
"Kasan Allah? Saika fadamin"
"Mtcheew to cikani"
Sakinshi yayi yana huci.
"Dan ubanka nufinka su mamy zasuyi maka komai? Nabasu 3million suqara wajen hada lefe kingin kuma zan bugo I.v sai aba Amarya kingin as pocket money, saima ka qaro wata 5million din don akwai events daza'ayi kuma munada buqatar money, real money"
Galala Ashraf yayi yana kallonshi tunda yafara mgn har yakai aya.
"Wai tsaya, come again, kana nufin da kudadena akayi wadannan abubuwan?"
"To da danawa? Bakada hankali, to Bari kaji jiya munyi mgn da qawar Amarya basu shirya wani event ba sai walima ta mata wanda zasuyi a bangarenmu kuma Ummy naji tace zasuyi mother's eve, Kaga kenan Kowanne bangare zaiyi nashi to Bayan daurin aure sai Ayi dinner gabadaya kafin ka shilla da amaryarka"
Ya karasa zancen yana kashe mashi ido daya😉
"Kaga dole mu basu enough money dazasuyi hidimar walimar hankali kwance, so please we need another 5million"
Kutt.. Kasama magana Ashraf yayi na wucen gadi.
Sai Daga bisani ya tashi yanufi kofa
"Kuma wlh kafara biyan bashi kenan Tun Daga wannan watan, saika biyani kudina don bazanyi asaraba wlh"
Dariya Sadeeq ya fashe dashi yana cewa
"Ba komai, yanzu yaushe za'a qaramana 5million din?"
,"kazo ka qwata don ubanka "
Yafada yana ficewa cikin Fushi.
*****************************""""'
"Wai Ashraf meke damunka ne? Sbd kawai zakaje ganin amaryar ka saika wani dinga jamana tsaki kamar wata tsaka? Aida Tun acan kace Baka zuwa bawai kazo nan ka cikani da tsuwaba"
"You know what Sadeeq, wlh idan Baka fita harkataba zan mugu mugun sa6amaka, munafiki Kasa bansan Kaine ka hada makalkashiyarba? Idiot dan sa idon kawai, wlh kaji haushi Sadeeq, banza mai zubin ifritai"
"Naji mallam, hakan dai bazai hana kajeba, shure shure baya hana mutuwa, kayi sauri kana 6atamun time ko nafasa rakiyar, ehe"
Takaici yaqara qume Ashraf, kwafa yayi yacigaba da shiryawarshi cikin 6ata lokaci dukdan yaba Sadeeq haushi Amma ko ajikinshi.
Saida yagama feshe jikinshi da turarruka sannan ta Dora hular kube yawani kasheta a gaban goshi.
"Kai kai Kai!! Kaga ango bada Lanka asare kaje gida kace yafadi, wannan gayu haka? Duk dan aaburge Amarya ne? Gaskiya Amarya saita rude idan taganka, Wai ja ganka kuwa"
Tsaki yaja yafice yanacewa
"Kasameni waje idan kagama haukan"
"Yo ai hikenan" yafada yana maramashi baya.
Saida sukayima Ummy bankwana, ta basu wata Leda Wai suba Saudart kuma tana gaisheta, Sadeeq ya amsa yayinda Ashraf harya kai waje.
Binshi Sadeeq yayi da sauri yana cewa
"To? Duk zumudin ganin amaryar ne haka, atleast kajirani mana tunda ko sanin gidan bakayiba, kuji qagarrare"
Banza Ashraf yayi dashi ya shige mota, shima Sadeeq mazaunin driver yashiga yarufo sannan ya tada motar suka shilla...✍
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Ka jiqan wadanda suka mutu sanadinta da dukkan musulmai da suka rigamu gidan gaskiya🤲
Ya Allah ka jabanci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
026
Zaune take ta tankwashe kafaffu sai shan farfesun da mamy tayimata take tana yatsina fuska.
Murda kofar da'akayi aka shigo yasata saurin dagowa tana kallon kofar.
Mamy ce tashigo tana murmushi.
"Wai haryanzu baki cinyeba Angel?"
Kwa6e fuska Saudart tayi tana turo baki
"Mamy wlh babu dadi"
"Mtcheew, shirmamma, Allah ya shiryaki yanzu tashi kidan watsa ki chanza kaya kuma kiyi sauri nabaki minti biyu"
Da sauri ta tashi dama ba son sha takeba.
Girgiza kai mamy tayi ta dauke bowl din farfesun ta fice.
A gaggauce ta warwatsa ta fito ta saka wata yaloliyar Riga ta fada kan gado tana Jawo wayarta tana danne danne.
Shigowar mamy yasake katseta.
"A'a? Meye haka? Baqi fa gareki kinwani kwanta, common change to something decent kizo ki fice"
"Baqi mamy? Su waye?"
"Bansaniba"
Tashi tayi ya chanza rigar jikinta da wata jallabiya jaa ta dora zumbulelliyar hijabi baqa akai wanda tsawonta yakai har idon qafa ta zura hannayen hijabin sannan tadan murza turare mai sanyin qamshi ta fito.
A falo ta tarda mamy zaune.
"Kiyi sauri dama kin 6atamusu lokaci, suna falon baqi, zan aiko Kamal da refreshment"
"Tou mamy" tace tana ficewa tana tunanin ko suwaye baqin.
Sallama tayi bakin kofar falon.
Saida taji an amsa sannan ta sanyo kafa ahankali tashigo kai a qasa.
Haka kawai taji gabanta yafadi batareda wani daliliba.
Kallo daya tayimusu na second daya ta dauke kai, hakan yasa tasan su biyune Saidai bata gane kosu wayeba.
"A'a? Gimbiya qaraso, lale sannu da fitowa sarauniya"
Jin muryar sadeeq yasa gabanta sake faduwa, to? Dama yasan gidansu? Shida waye?
Cikin nutsuwa ta isa kujerar dake facing dinsu ta zauna sai a sannan ta dago cikin nutsuwa ta kallesu.
Idanunta ne suka sauka cikin ba Ashraf dake maqale da waya a Kunne alamun waya yake.
Wani kallo ya watsamata wanda yasata saurin dauke idanu ta maidasu kan Sadeeq daketa yashe baki.
"Sannunku dazuwa, ina wuni"
Tafada cikin murmushi
"Lfy qalau gimbiya, ya hidima?" Inji Sadeeq yana dan take qafar Ashraf a fakaice alamun yabar wayar hakanan mana.
Yana jinshi yayi kamar besan abinda yakeba saima qara relaxing dayayi a kujera yana cigaba da amsa wayar shi cikin murya qasa qasa don ko Saudart batajin abinda yakecewa.
"Alhamdulilah" tafada tana ta6e baki cikin zuciyarta tana cewa, Masu hidima dai yakamata kayima ya hidima ba niba.
Kamaldeen yashigo da tray dake dauke da Kayan motsa baki da drinks da sallama a bakinsa.
Amsawa sukayi suna kallonshi, Qarasowa yayi ya ajiye saman centre table din sannan ya gaidasu a ladabce
Amsawa sadeeq yayi fuska asake while Ashraf yayi mashi murmushi kawai.
Juyawa yayi ya fita.
Shiru ne yadan ratsa falon.
Ganin wayar Ashraf ta iskanci ne yasa sadeeq miqewa.
"To Bari kuga yadda za'ayi"/yafada yana qarasawa centre table din ya dauki qaramin plate ya koda snacks ciki ya dauki robar hollandia daya yana cewa
" Ato, bari nabaku wuri Ku soye, kunsan masoya basu cika son shishigiba"
Yana kaiwanan ya fice ya koma garden ya zauna ka daya Daga cikin kujerun shaqatawa ya zauna, ya fara aika abinshi yana yi yana danne dannenshi a waya.
Tsit falon yayi yasake yin wani irin shiru sai qarar ac da akeji saikuma muryar Ashraf da ake danji qasa qasa alamun haryanzu be gama wayarba.
Itadai Saudart haryanzu kanta sunkuye yake don batama son sake kallonshi.
Sai tambayar kanta dalilin zuwanshi gidansu take.
Idan bata manta ba rabon data ganshi Tun wajen gathering, kusan wata daya kenan.
Shikau dakyar yagama wayar don dama sungama maganar dasuke kawai qara Jan mutumin da magana yake don beson ko kalma daya ta hadasu da Saudart, sai gashi mutumin ya kawo excuse na zaiyi attending din wasu.
Komawa yayi ya jingina da kujera yayi irin wannan shegen zaman dake bata haushi yacigaba da danne danne awaya.
Tsaki taja a zuciyarta ji yadda yayi wani balancing kamar yana dakinshi.
Shiru dakin ya dauka babu mai niyyar magana ita kanta qasa tana wasa da yatsunta, shima kanshi saman waya yana danne danne.
Sun dade ahakan Amma babu wanda keda niyyar motsawa, dukda kowa ya gaji da zaman.
Saudart Jitake kamar ta tashi tayi tafiyarta Amma ta hqr atleast gidansu ne, su kwana haka.
Shima Ashraf da ba abinda yake awayar Saidai yashiga nan yashiga can jiyake kamar yabar dakin Amma jin kanshi yaqi bari don be iya ma tashi ya taka gabanta, Wai raini zai jamashi.
Haka sukaita zama kowa da abinda yasha mashi kai, sunfi awa daya ahakan Amma still babu wanda jinkai yabari yayi magana.
Yadda kasan kurame aka akai zaman.
Sadeeq dadai yaji shirun yayi yawa kuma dare qarayi yake ya miqe yana daukar plate daya rage snacks yan kadan ya taho.
Da sallama yashigo, ga mammakinshi yadda yabarsu haka ya taddasu.
Ga Kayan motsa bakinda aka kawo musu ko alamar anta6asu be ganiba.
Basarwa yayi ya qaraso yana murmushi
"A'a romeo and Juliet, wannan soyewa haka, naga fira yayi dadi ko niyyar kirana bakuda shiyasa na dawo"
Murmushi kawai Saudart tayi akunyace.
"To mallam romeo mujeko? Ko anan zamu kwana?"
Ta qasan idanu ya watsa mashi mugun kallo sannan ya miqe yana saka wayar shi aljihu sannan ya fiddo bundle din yan dubu dubu biyu ya ajiye saman table sannan yasa Kai yafice