Showing 3001 words to 6000 words out of 173829 words

Chapter 2 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1100

baki Ashraf yayi sannan shima yabishi abaya.

Mota daya suka shiga da sadeeq dayan kuma bodyguards dinsune aciki suka cilla kan kwalta.




**************************************





"Sir munyi nazari akan buqatar ka, kuma mun yarda zamu Baka adadin daka buqata ko fin haka, Saidai da sharadi Bamusan idan ka amince" inji sadeeq

Murnar Alhaji taso komawa ciki, kallon sadeeq yayi sannan ya maida kallonshi kan Ashraf dake faman jujjuyawa kan kujera idanunshi lumshe.


"Inaji, wane sharadi kenan?" Inji Alhajin

"Bansan yadda zaka dauki zancennan ba but believe me, it's just business, bamuda wata manufa akan hakan, zamu Baka loan na 30 million Naira ko fin hakan na shekara daya zaka maidosu ciff babu d'ori babu ragi Saidai kamar yadda kasani bakada abinda zamuyi holding akan idan Baka biyamuba zamu fanshe ta wajen, koba hakaba?"

"Hakane" inji Alhaji

"Shine mukayi shawara why not muyi haka, muyi trade by barter, mubaka kudin kaikuma kabamu wani abun dazamu riqe harsaika maido kudin sannan mubaka" yafada cikin nutsuwa.

"Me kenan?" Alhaji ya tambaya cikin rashin fahimta.


Kallon Ashraf sadeeq yayi Wanda haryanzu yana jujjuyawane akan kujera sannan ya maido dubanshi ga Alhajin.

"Diyarka" ya bashi amsa ataqaice.

"Diyata?" Ya tambaya cikin rashin fahimta.

"Eh ina nufin kabamu diyarka saimu Baka kudin.."

"Wait, nufinku inbaku diyata sbd kudi? Ko nufinku son kudi zaisa in lallata rayuwar 'yata? This is unbelievable!" Alhaji ya katseshi cikin tsananin mammaki.

"Calm down Alhaji, ba nufina kenanba, you misunderstand us, abinda nake nufi shine zakaba Sir Ashraf auren diyarka bisa yarjejeniyar daka biyashi kudin shi zai sakoma ita, babu abinda zai shiga tsakaninsu, kawai sunan an daura aurene, zai Baka bashin har zuwa 50million idan kana so, all you'll do is sign a contract with him, Amma fa bawai tilas bane, Mr shamsu remember kanada option, this is just...Business" yaqarashe zancen yana mai stressing din business din.

Shiru Alhaji yayi don kanshi yayi mugun kullewa, contract? Aure? AUREN KWANGILA fa kenan? To meye ribarsu? Shikuma meye ribarshi? Tambayoyin daketa mashi kara kaina akai kenan.


"Alhaji kayi shiru" inji sadeeq dake kallonshi.

Dagowa yayi yana kallon Ashraf, yes he's handsome, damn hot! Irin namijin da kowacce mace zataso samu a matsayin miji, ga kuma uwa uba kudi, he's damn rich, zaici riba idan Ashraf yazama sirikinshi koda na kwana dayane, gaggarumin riba kuwa, Amma shi Ashraf din meye ribarshi idan yayi hakan? Dolene yanada manufarshi nayin haka, meye manufarshi to?

"I'll take your silence as NO" Inji sadeeq.

"No, bawai nayi rejecting bane, Saidai shi meye ribarshi idan yayi hakan? Nasan akwai wata manufa akai" inji Alhaji shamsu.

"Good. Kayi tunani mai kyau, dolene yanada manufa, eh yanada ita, as you can see, Ashraf matashine mai ji da kudi da kyau, he's clocking 28 yrs wata mai zuwa, iyayenshi sun tasoshi gaba da mgnr aure har suka bashi wasu adadi lokuta na idan be kawo mataba zasu hanashi da wadda sukeso, shikuma wacce yakeso na schooling ne, sai nanda shekaru 2 zata gama, so shine daya bincika yaga kanada 'ya yaga why not ya aureta, AUREN KWANGILA, Inyaso daka biyashi saiya saketa at that time kuma yarinyar dayakeso is over sai kawai ya aureta, this is just a CONTRACT MARRIAGE, kamar yadda nafadama babu abinda zai shiga tsakaninsu, yadda ka kawota haka zaka amsheta"


Shiru Alhaji shamsu yayi yana sauraronshi, yana kuma hada kalmominshi yana rarrabawa, abunka da businessman harya fara hango hanyoyin samun ribarshi na sosai ma, yes akwai riba, huge riba, babba ma kuwa.

"Kai muke sauraro, ka amincene? Koko musami wani?" Inji sadeeq.

Qara kallon Ashraf yayi Wanda a wannan karon shima shi yake kallo yana jiran amsarshi, nima nayi kasaqe da Biro a hannu ina jiran amsarshi.

Bakajin komai a office din sai qarar A.C

Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ahankali ya bude baki yace......✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀


🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)




Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲





Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




006






Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ahankali ya bude baki yace
"Idan nace kubani lokaci inyi tunani fa?"

Wannan karon Ashraf yayi magana cikin husky cool voice dinshi
"You can have your time to think, is not as if tilastama akeyi, wannan deal ne kawai Wanda bazai yiwuba sai duka 6angarorin sun amince kuma sunyi sign, ni, kai sai daughtern ka, kanada ikon janyewa it's your right, Saidai remember millions of people are outside waiting for opportunity irin wannan, idan beyimaba karka ji kunyar fada. Am good with any of your answer" ya qarashe zancen yana qara balancing a kujerarshi.

Ajiyar zuciya Alhaji yayi.
'Thank God. At least fargabana na aurama diyata kurma ya kau' yafada cikin zuciyarshi.

"Babu matsala insha Allah, kawai dai kubani time inyi tunani"

"Zuwa yaushe?" Inji sadeeq

"Nan da Monday insha Allah"

"To Allah yakaimu"

"Amin thanks, I'll get going"

"Alright mungode sir"

"You're welcome" yafada yana miqewa tsaye tareda miqama sadeeq hannu sukayi musabaha sannan ya d'an sack kallon Ashraf sannan yafice.



Kallon juna Ashraf da Sadeeq sukayi Bayan sun rakashi da idanu.

"Did you think the jerk will accept?" Inji Ashraf cikin yamutsa fuska.

"Ina jiyo qamshin nasara dai, he won't afford to loose this opportunity, besides wazai the whole SIR ASHRAF?"

Murmushin gefen baki yayi yana sake balancing a kujerar.

"It better be" yafada yana shafa sajenshi ahankali murmushin still a fuskarshi.






****************************************


Tuqi yake Amma kwata kwata hankalinshi na wani wajen.

AUREN KWANGILA? Contract marriage? Da familyn A.A? diyata tazama daya Daga cikin familyn A.A?
Wow! What an incredible opportunity! Ni? In-law din A.A family?

As for me banda problem but Saudart...

Shiru yayi yana tuna aqidar Saudart na tsanar mutuwar aure, koyaya taji aure yamutu saita shiga damuwa da 6acin rai, musanmman idan antara iyalai.

Tashin datayi cikin broken family yasa ta tsani mutuwar aure, lokaci da dama takan gayamishi ra'ayinta na son yin auren MUTU-KA-RABA, Akoda yaushe maganarta baya wuce
"Dad katayani da addu'a Allah yabani miji na gari, ko bashi da kyau bashida arziqi ya kasance mai kyan hali, Wanda zamu Gina ingantacciyar zuri'a nan gaba, Wanda zamu hadu muba 'ya'yanmu tarbiyya, Wanda mutuwace kawai zata rabamu"

Wani sa'in ya kan tsokaneta da marar kunya tana fadamashi irin wannan mgnan a matsayinshi na mahaifinta.
Takan yi dariya lokuta da Dama tana rufe fuska sannan tace "Dad, ai gaskiyane, Aure wajibine ga dukkan musulmi Duk cikarka bazaka ta6a zama cikkake mai darajaba saikayi aure, name zanji kunya Bayan nasan koba dade koba jima saina yi auren?

Hakan daya tuno ba qaramin tada mashi hankali yayiba.

Me zaice mata? Zan hadaki AUREN KWANGILA da A.A sbd farfadowar company na? Impossible!
Bazai iya kiyasta tashin hankalin fasata shigaba idan taji hakan, aure? Na Wanda bata saniba kuma bata ta6a ganiba? Kuma qarin gishiri a ciwo Aure na taqaittacen lokaci? Kai da kamar wuya.


Haka yaita tunane tunanenshi harya iso gida jikinshi yayi matuqar la'asar.
Shidai abinda yasani no matter what, bazai bar wannan damar ta wuceshiba.




WAIWAYE (Adon tafiya🕴)



Manage please🙏


Ummin fasihu ce

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲

Ya Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




007







WAIWAYE (Adon tafiya🕴)



Alhaji shamsu d'ane tilo ga Mallam yahya.

Su yan asalin garin kanjiyane dake jahar katsina.

Tun yana Dan shekara shida mahaifinshi yakaishi cikin birnin katsina almajiranci.
A makaranta wani babban malami wato mallam Ballo.

Haka suke rayuwa a wannan makarantar Wanda yawanci abincin dazasuci sai sunje bara suke samu, wani sa'in idan basu samuba haka suke haqura su kwanta kasancewar iyayensu basu wani had'osu da abincin kirkiba, gashi shima malamin ta kanshi yake don bazai iya daukar nauyinsuba kasancewar shima bamai wani hali bane ga d'aliban dayawa.

Haka rayuwa ta kasance basa komawa qauyensu saiga damina don taimakawa iyayen da noma, da kaka tayi sai asake turosu da guzurin dabe taka kara ya karyaba.

Rayuwa suke irin na sakakku wadanda babu mai tsawata Masu sai malaminsu shima a lokacin karatu, wani sa'in karatun ma ba dauka sukeyiba saboda ai sai ciki ya dauka sannan za'a maganar karatu, wani sa'in saisun yi aikatau sannan zasu sami abinci.

Haka rayuwarsu ta kasance wani sa'in tufafin dazasu sa sai sunyi bara suke samu shima dakyar, wasu kau Kayan jikinsu sbd tsabar datti ko zanen Kayan ba'a gani, wasu kuma kaya sun 6e66ere Masu ajiki Amma babu halin dinkawa.

Acikin wannan rayuwar wasu suke kauce hanya su fada munanan hali batareda an ankaraba tunda babu Masu sanyamusu ido, sai aga ba'a samo karatunba kuma 'ya'ya sun kangare sun gaggari al'umma.

Shamsu shi Allah ya tsareshi da fadawa irin wadanan halin Saidai yataso da kwadayin abin duniya, kudi ko ta hanyar haram ne yanabi yasamesu, gashi da tarin karatu Saidai be amfaneshiba.

Duk buga bugan dazaiyi yasamu kudi saiyayi don a tunaninshi kudi shine komai, idan kanada kudi to kowama kana iya takawa.

Tun yana komawa kauyensu Duk damina don taya babbanshi noma har ya daina.

Alokacin dakowa ke komawa kauye sai shi yashige cikin gari yana buga buganshi na Neman kudi, wani sa'in ya kwana a tasha wani sa'in a massalaci.

Babu yadda babanshi beyi dashiba don ya dinga leqosu koda sau dayane a shekara Amma firr yaqi, don aganinshi baya iya zaman kauye kuma, yasaba da riqe kudi da cin Abu mai maski mezeje yi kauye?

Abun ba qaramin damun mallam Yahya yayiba gashi shine d'a talin qwal nashi.

Haka ya haqura yazuba mashi idanu don yariga ya kangare bawai maganar kowa yakejiba.

Shamsu likafa taji gaba, Tun yana buga buganshi a katsina harya koma kano jin can anfi kasuwanci kuma anfi samun kudi.

Wani babban shago yasamu aiki na yaron shago inda ake siyarda Cosmetics Kala kala.

Sosai yake samun kudi don shagon shahararene kuma mai shagon na sallama mai tsoka.

Dayake Shamsu Allah yayimashi farin jinin mutane, cikin d'an qanqanin lokaci yasan kwastamomi dayawa, kusan kowa yasanshi saboda barkwancishi da iya mu'amala.

Ahankali ahankali yafara yiwa ubangidan nashi cuwa, yana mashi rinto, wani sa'in idan aka aikashi saro kaya saiya Dora nashi Asama kokuma wurin Saidawa ya qara akai.

Dayake uban gidan nashi ya yarda dashi kuma becika sa ido sosaiba, beyi saurin ganewaba, saida yayi mashi mummunar 6anna, sbd Duk kusan customers dinshi sunbar zuwa sbd yadda kayanshi suke tsada.

Ataqaice dai shago yarushe babu riba kullum sai faduwa, Daga qarshe Saidai ya sallami yaran shagon gabadaya yarufe shagon sbd rashin jari.

Shamsu daketa Tara kudaden dayake samu wajen rintonshi, yasamu wani qaramin shago cikin kasuwar yabude shima yazuba irin Kayan da oganshi ke Saidawa ada.

Ahankali ahankali, kasuwancinshi yadinga ha66aka, Allah yasa mashi albarka a kasuwancinshi.

Abu qarami yakoma babba Tun yana sari garuruwa harya fara fita qasashen waje.

Cikin shekara biyar ya bude wani qaton company mai suna A.S GALLERY

Duk abinda akeso na Kayan alatu yana Saidawa. Company nashi yazama shaharare Wanda ake tutiya dashi garin kano.

Wata shekara yadai runtse ido yayi aikin hajji shima sbd matsa mishi da abokan kasuwancinshi kemashi na yaqi aikin hajji.

Haka dukiyar Alhaji shamsu yacigaba da bunqasa Wanda Duk yawanci na ha'incine don sosai ya kware wajen ha'intar mutane.

Saidai abinka ga Dan kauye, Duk tarin dukiyarshi beta6a marmarin sayan kadaroriba sbd gaba kokuma yabude reshe awani wajen, Shidai Duk abinda yasamu ya narkawa company dinshi.


Ana haka rasuwar mallam yahya ta riskeshi, sosai ya girgiza don rabonshi da kankiya harya manta, yana dai yimusu aike bakin gwargwado.

Ba shiri yanufi qauyen, yayi kuka sosai jin baban nashi yadade kwance ba lfy, haka yaita Neman gafarar inno (mahaifiyarshi) harta yafe mashi.

Bayan Arba'in ya tarkata inno sai kanon dabo don acewarshi bazai iya cigaba da zama a kauyeba.

Shekara daya da rasuwar mallam inno ma tabishi, babu laifi mutuwar ta girgizashi na Dan lokaci sannan yacigaba da rayuwarshi.

Yana Dan shekara 32 yayi aure ya auri wata shuwa Arab Wanda suka hadu da ita awata tafiya dayayi Maiduguri.

Mace mai kyau, hankali da tarbiyya.

Bayan shekara ta sulu6o Masu da kyakyawar baby mai kammaninta sak masha Allah.

Saidai Tun Daga sannan suka fara samun sa6ani dashi a dalilin sata dayayi Wai tacire mahaifarta beson haihuwa diya daya ta isheshi.
Wai 'ya'ya babu abinda suke jawowa sai talauci.
Itakau firr taqiya Wanda hakan yaja mummunan sa6ani tsakaninsu Wanda Daga qarshe suka rabu da Abu yaqi dadi.


SAUDART Nada shekara biyar Alhaji shamsu ya amsota sbd yaji mahaifiyarta zatayi aure acewarshi 'yarshi baza taje wani gida agolanciba.

Saida aka kai ruwa rana sannan suka bashi ita da sharadin sai ta dinga zuwa Duk sati suna ganinta kuma yasata both islamiya da boko.

Soyayya sosai Alhaji shamsu ke nunama Saudart, wata irin shaquwa ke tsakaninsu na qin qarawa don sunfi shaquwa dashi bisaga mamanta.

Ya sakata both islamiyar da boko, Duk wani gata da diya zata samu wajen iyayenta tana samu don Saudart tadauko dukan halin iyayenta.
Kyaun fuska da hali na mamanta sai farinjini da siye zuciya irinna bbanta.

Tun tana yar shekara sha biyar tasauke Al qur'ani mai girma, a fannin boko kau tanada kwalin degree a fannin economics.

Saudart Tun tana yarinya ta tsani mutuwar aure, don shine silan rabuwanta da daya Daga iyayenta.

Tsanar yaqara karfine dataji a islamiya malaminsu ya gayamusu babu abinda Allah ya tsana kamar mutuwar aure don har sama girgiza take.

Tin alokacin take addu'ar Allah yabata miji nagari Wanda mutuwa kadai zata rabasu.

Tana gama degree dinta ta matsama daddynta ya bude mata bakery, sbd tsananin son datakema girki, da farko yaqi yarda don yafison tayi aikin office Amma data matsamashi dole yabude mata Wanda nan da nan Allah yasamata albarka a harkar har tayi fice a garin, babu Wanda beson ALHAIRI BAKERY ba.


Ana haka wannan cuta (covid19) tashigo duniya harta 6illa Nigeria Wanda hakan baqaramin rushe tattalin arziqin qasa yayi, cikin wadanda abun yashafa harda Alhaji shamsu don komai ya karye sakamakon rufe border da akayi.

Ga tarin basussukan da ake binshi na banki haka yasa dole yanemi taimakon shahararen kamfanin nan na A.A ENTERPRISES.

Saiga kuma yadda abun ya kasance...✍


Sorry babu dai editing🙏


Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)



Allah ka yayemana wannan cutar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)







008




Cigaban labari📖





Yau Saudart tafi zama busy saboda ita dakanta ke tsara cake din bikin Sir Wilson, abubuwa take cikin qwarewa while wasu tsirarun ma'aikata na gefe suna qara daukar kwas.

Aiki take Amma hankalinta na wajen daddynta.

Tun dazu take jiran kiranshi Amma shiru, Allah Allah take ta ida ta dawo gida, abindama yaja delay rashin samun kalar colouring dasukeso dawuri da tuni angama an hada da kingin snacks da akayi delivering dazu.


6:30pm ta kammala cake din, sai tashin wow! Wow!! Kakeji a dakin kamar jiniyar motar ambulance sbd haduwar cake din.

"Wow ma'am! This is the best cake I've ever set eyes on" inji wani mai suna Farouq yana tafawa.

Nan kowa yabi sahu sunata tafa mata.

Yar dariya tayi sannan tad'an dramatically tana cewa "thank you, thank you".

Ba ita tabar bakeryn ba sai 7:00pm Duk hankalinta yayi gida.

'Meyasa dad be kiraniba? I hope all is well' tafada acikin zuciya.




Da sallama tashiga parlourn, can ta hango daddy a dining yana sipping din coffee.

Dadi taji ganinshi cikin nishadi babu damuwar komai.

Amsamata sallamar yayi cikin fara'a saikuma yasha mur yana kai dubanshi ga wall clock.

Dan Waro idanu tayi tana Dan dariya ciki ciki yayinda ta qarasa wajenshi tana rungumo kafadunshi.

"Sorry dad, am late, wlh wani aiki ya tsayar dani"

Hararar wasa yayimata.

"Silly girl, harna fara damuwa danaji shiru" yafada yana dungure mata kai.

Shafa kan take tana turo baki
"Ai Dad Baka damu daniba, ko ka kira kaji lfy?"

Murmushi yayi yace "ai ina cikin shawarar kiranki sai gaki"

Jan kujera tayi ta zauna kusa dashi.

"So daddy how far? Guess ansamu nasara. Yadda kake washe bakinnan nasan ba banzaba"

Bugu yakai mata ta kauce tana dariya.

"Lallai kin maisheni kakanki ko?"

"Am sorry, Nidai ya kuka kaya?"

"Lau.. Tashi kiyi Sallah mufita, akwai outing yau"

Wani ihu tabuga tana tsalle
"Yeee! Kace anci nasara? Kai alhamdulilah! Dad am soo happy!" Tafada tana rungumarshi.

Dariya yayi yana janyeta.

"Tukunna dai, kidai je kiyi sallar ki shirya"

"Yanzu kuwa" tafada tareda yin hanyar dakinta da sauri harda hadawa da Dan gudu.

Binta yayi da kallo harta kule,
Ajiyar zuciya yayi yana sake qarfafama kanshi gwiwa.








Sosai Saudart taji dadin outing din don wurare daban daban suka je na shaqatawa, sannan sukaje wani had'ad'en restaurant sukaci abinci Daga qarshe suka biya shopping mall sukayi shopping Wanda Duk yawanci Kayan data kwasa dad dinta na siyarwa kawai shiya matsa saita saya.


Agajiye liqis suka dawo gida. Saida kowa ya watsa yayi sallar isha'i sannan suka dawo parlour suna kallo suna hira.

Soyake ya dauko mata maganar daketa cin ranshi Tun dazu Amma yakasa.

Can ya nisa ya kalleta da yanayi na seriousness yace "SAUDATU"

Dumm gabanta yafadi dajin yakira ainahin sunanta.

Kasa kai cokalin ice cream din tayi a baki ta ajiye sannan ta maida hankalinta kanshi.

Shiru ya ratsa falon yana tunanin yadda zaiyi mata presenting din maganar, can ya nisa yace

"Saudatu, baki tambayi yadda muka qare dasu mutanenki ba"

Ajiyar zuciya tasauke da qarfi

"Kai dad, harka bani tsoro, to ya kuka qare ba cewa kayi sun bakaba?"

"Eh sun bani Amma basu baniba"

Kallon rashin fahimta tayimashi
"Ya hausan sun Baka, basu bakaba?"

"Abinda yafaru shine....."

Cikin qwarewa da baiwarshi ta dadin baki ya labarta mata Duk yadda sukayi dasu Sadeeq.


Tunda yafara magana ta zubamashi idanu tana kallo ko blinking batayi don ita harga Allah batasan inda yadosaba.

Koda yakai aya batabar kallon shiba.
Shima kallonta yake don ganin reaction dinta Amma she's expressionless.

Kamo hannunta guda yayi yana Dan murzawa.

"Are you there shalele?"

Sai alokacin tayi blinking, ahankali ta motsa baki tace
"I don't get you dad, kaina ya kulle"

Murmushi yayi sannan yafito mata 6aro2 yace

"I mean so suke inbashi ke akan yarjejeniya Dana biya zai maidomin ke, ma'ana you guys are having contract marriage"

Zaro idanu tad'an yi sannan ga mammakinshi tafashe da dariya harda tafawa.

"Lol.. Amma dad mahaukatane ko? I guess company mahaukatane idan ba hakaba ina aka ta6a wannan irin auren? Ko a film ma banta6a ganiba, gaskiya a binciki brain dinsu"


Shiru Dad yayi yana kallon yadda tama maida abun wasa.

"Jewel this is not funny, please let be serious" yafada yana qoqarin danne 6acin ranshi.

"Ok..ok, naji sai kace musu me daddy?"

"Subani lokaci inyi tunani akai"

"Tunani? Tunani fa kace Dad? Meye abin Tsayawa tunani anan, amsar a Afili take, idan su jahilai ne mu ba jahilai bane, the amsa is capital NO!" Tafada itama cikin son danne 6acin ranta Amma deep down she's boiling.

Kamo dayan hannun nata yayi yahada biyu sannan a tausashe yace "shalele, please listen, ahalin yanzu banida za6in da yawuce..."

"Wait Dad.., come again, bamuda me? Bakada za6i fa kace? Don't tell me kana shirin yadda da jahilcinsune" ta katseshi tana kallonshi unbelievable.

"Saudart... Wannan ba jahilci bane, banida choice, sokike inzauna in nade hannu ina kallon company na yayi collapsing a gaban idanuna?"

Shiru tayi don she's speechless ma, kallon shi kawai take cikeda rashin yarda.

Matsa hannunta yafarayi a tausashe.

"Kinyi shiru shalele, please say something, yanzu kece last hope dina. Please speak up"

"Dad me zance? Ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login