Showing 150001 words to 153000 words out of 173829 words

Chapter 51 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1126

kasa riqeta sai komawa dayayi da baya ya jingina da kujera ya sakarmata idanunshi dasuka fara chanza launi

Tashi tayi da sauri ta nufi hanyar barin dining din

Binta da kallo yayi a kasalance harta bar wajen sannan ya maida kanshi jikin kujera ya lumshe idanu yana sauke numfashi ahankali

Ya dade sosai ahakan kafin yafarajin dan daidai, dakyar yatashi yafice daga part din yanufi part dinshi cikin jan kafa


Saudart ma dakyar takai sama saboda harhardewa dataitayi

Tana kaiwa sama dakin baby kawai ta nufa ta bude kofa tashiga

Hango baby tayi tayi daidaya agadon tanata sharar barcinta hankali kwance

Qarasowa tayi ciki a kasalance ta fada gadon itama tayi ruff da ciki tareda lumshe idanuwa


A bangaren ashraf kau abin juyemashi yasoyi don ya tadowa kanshi 6alli, shima ruff da ciki yayi hannunshi dafe da mara

Shikanshi yasan yau sai Allah dama ya lafiyar giwa? Gashi shi Bashan maggungunan nan yakeba tun can acewarshi bazai cutar da kanshi ba don sha'awa sign din lafiya ne rashinta shine cuta don me zai cutar da kanshi da kanshi?

Ya dade ahakan idanunshi lumshe yana daddana wajen daya qulle tamau har can wani wahallalen barci yayi gaba dashi



WASHEGARI


Tun ana kiran farko ta tashi ta tada baby suka dauro alwalla tare suka gabatar da sallah.

Baby bata zauna ba ta tashi tahau shirin makaranta kasancewar sunfara exams

Tana nan zaune har baby tagama shirinta saita tashi suka fita tare zuwa dakin ummy domin gaidata

Koda suka shiga isketa sukayi tana qoqarin gyara gadonta

Shigowarsu yasata juyowa tana amsa sallamarsu tare suka gaidata cikin girmamawa ummy ta amsa cikin jindadi tana tambayar baby badai harta shirya ba

Amsamata tayi da eh yau exams din safe garesu nan ummy tace sutafi qasa tayi mata package din breakfast idan ta Isa can saitaci

Saida baby tayima saudart sallama sannan suka fita tare da ummy

Ganin haka yasa ta ida gyarama ummy gadonta tahau kalkale dakin kamar yadda tasaba


Shigansu ummy kitchen keda wuya ashraf yashigo falon shima cikin shirin office saidai fuskarnan a murtuke take ta koma ta ainahin A.A marar M

Yau dama da 6acin ran jiya ya tashi, idan yatuna da badan ummy ta mashi buqulu ba da yanzu wannan lalular tashi yazama tarihi sai ranshi yasake 6aci shiyasa yau yashirya dawuri don zuwa office ko zai danji dama dama

Haurawa sama yayi yayi knocking a kofar ummy, bejira ayimashi isoba ya bude yashiga bakinshi dauke da sallama


Saudart da fitowarta kenan daga wankin toilet ta dago sukayi ido hudu

Sanye take cikin doguwar cotton gown dark green, hannun rigar attatare iya gwiwa hannayen ajike alamun tayi amfani da ruwa

Gabanta ne yafadi ganin mutum tsaye a bakin kofa ya tsareta da idanu

Sauke idanunta tayi qasa yayinda abinda yafaru jiya yayi flashing a kwalwarta

Dagowa yayi daga jinginen dayake jikin kofa yafara takowa gareta

Jin takunshi yasata dagowa itama tana kallonshi

Qarasowa yayi gabanta sosai sannan ya tsaya yana cigaba da tsareta da idanu

Kasa jure kallon nashi tayi hakan yasata sauke kanta qasa

Hannu yasa ya dago habarta ahankali suka tsurama juna yayinda kibiyoyin qauna ke fita a idanun kowannensu yana shiga najuna


Ahankali yafara kusanto fuskarshi gareta batareda ya janye eye contact dinsu ba

Itama samun kanta tayi da kasa ko motsawa sai kallon cikin idanuwanshi datake tana kar6ar saqonsu izuwa nata

Hada goshinsu yayi still idanunsu ana juna

Bugun zuciyarta yaqaru sosai yayinda jikinta yadan fara tsima

Hannayenshi yadora a waist dinta yajawota jikinshi yana neman hade bakinsu

Sosai jikinta yashiga rawa hakan yasa tafara tafiya da baya baya

Shima binta yashigayi batareda ya saketa ba har suka dangana da kofar toilet

Sake sunkuyowa yayi tsinin hancinsu na ta6a najuna, suka shiga musayar numfashi

Ahankali yafara kusanto bakinshi anata hakan yasata saurin rintse ido gamm

Lower lip dinta yafara kamowa da lips dinsu yajasu ahankali sannan ya sakesu

Jan numfashi tayi ta qarfi tana kwantowa jikinshi

Qara rungumo waist dinta ya hade bakinsu yashiga bata the romantic kiss ever

Sosai jikinta yayi lakwas kamar an zaremata lakka, jinta take kamar tana yawo agajimare, wani irin feeling da batasan tanadashiba yashiga tasomata yana sake tsumata

Shima a 6angarenshi yariga yagama fita hayyacinshi kissing din extra soft lips dinta yake kamar yasamu alawa, Kwata Kwata sun fita hayyacinsu bare sufarga Susan a ina suke.

Ummy ce data gama sallamar baby hartama tafi ta hauro sama tana amsa kiran waya daya shigomata yanzu


Hannu ta Dora akan handle din kofar ta murda tareda tura kofar


😱😱😱


Nayi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️


🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Story written by Ashaanty love💖



099


Hannu ta dora akan handle din kofar ta murda tareda tura kofar

Tura kai tayi ciki tana amsa waya fuskarta dauke da murmushi

Dago idon datayi bata saukesu akoina ba sai akansu

Gabantane yabada damm tayi saurin juyawa tana zare idanu

Saurin sake bude kofar tayi tafita cikin sassarfa


Sukau gwanayen basumasan tanayiba don sunyi nisa awata duniyar datasha banban da tamu

Kissing dinta yake so passionately yana kalkada harshenshi da nata yana sucking tenderly

Tuni lantarkin jikinta yaqara hawa jikinta yaqara yin laqwas badan kofar data taresu ba da tuni sun zube qasa

Saudart idanuwanta na alumshe tanajinta tana yawo a gajimare tama manta awace duniyar take ga yadda qasanta ke qara tsumuwa feelings na fizgarta takoina dama yaya lafiyar giwa? Qiris dama take jira dama an tsumu tun a gida

Bata dawo hayyacintaba saida taji hannunshi daya cikin rigarta a bare boob dinta guda

Hakan yasata zabura ta kwace bakinta tana bude idanunta ba shiri

Sai a sannan tunaninta yafara dawomata tafara qoqarin tureshi daga jikinta

Qara qanqameta yayi cikin fitan hayyaci
"No...please" yafada cikin muryarshi dabata fita sosai

"Please... stop A'A" tafada dakyar saboda yadda ya matseta kamar zai shige jikinta


Qanqameta yaqara yi yana sauke wani wahallalen numfashi yana qara cusa kanshi a wuyanta

"A.A.... Ummy, nashiga uku...ummy" tafada tana fashewa da kuka jikinta na rawa sosai

Jin sautin kukanta yasashi dan sassauta riqon dayayi mata yana sauke numfashi ahankali

Ganin tsayuwar na neman gaggararsu yasashi Zamewa qasa still tana wrapped a hannayenshi

Lumshe idanu yayi yana dora gefen fuskarshi bisa kanta yana cigaba da sauke numfashi

Shikadai yasan abinda yakeji, jiyake kamar zai shide saboda yadda mararshi ta qulle gamm

Qara turata yayi a qirjinshi yana sauraron sautin kukanta dake fita ahankali ga yadda yakejin bugun zuciyarta a qirjinshi

Hadiye wasu yawu dasuka tararmashi a maqoshi yayi ya dago yayi kissing din kanta ya dago fuskarta dake a qirjinshi yafara binta da kisses takoina

"It ok uhm? Stop crying" yafada yana kissing soft kumatunta na dama

Zaro hanki dake gaban aljihun suit dinshi yayi yashiga tsanemata hawayen fuskarta

Saida yagama sannan yaqara kissing din goshinta dake qawace da qanannun gashi dake kwankwance

"Am sorry uhm? I don't know what came over me, it just that... I... love you"

Fadawa tasakeyi ajikinshi tana sauke numfashi ahankali tanajin yadda zuciyarta ke swelling in emotions

Shima zagaye hannayenshi yayi abayanta yana kwantar da kanshi akan nata


***

Ummy kau cikin harde qaffafu ta Isa qasa, kitchen ta zarce don ahalin yanzu bata buqatar ta hadu da daya daga cikinsu

Maid dinsu tajuyo ganin yadda tafado kitchen din kamar wanda aka jefo

Hakan yasata fara tambayarta lfy ganin yadda duk take a burkuce

Saurin saita kanta tayi tawani sha murr cikin basarwa tace mata bakomai ta tafi bari ta ida breakfast din

Bin umarninta tayi ganin ba wasa a fuskarta ta wuce sumi sumi tabar kitchen din

Dafe kanta ummy tayi bayan fitarta tana mammakin irin wannan rashin kunyar ta 'ya'yan zamani

Yanzu su rasa inda zasu baje kolin iskancinsu sai a dakinta?

Dama tun dawowarshi gidan tana lure da take takenshi

Ko tsiramata idanun dayake a dining duk lokacin cin abinci tana sane shiyasa wani sa'in idan abun yaso yin yawa saita tashi tabarmasu dining din

Su ke abinsu amma ita ke jimasu kunyar

Jiya jiyan nan tazo ta taddasu zaune afalo qasa kamar su shige jikin juna saidai tajuya tafasa yin abinda ya sauko daita, daga baya ma saidai ta aika baby takirata ganin har isha'i na niyyaryi bata dawoba.

Hakan be isaba sai gashi the same day da daddare ganin har kusan 10 bata shigoba kamar yadda tasaba yasata fitowa ta leqa dakin baby taga wayam sai babyn kadai daketa sharar barcinta

Fitowa tayi tana wondering ina take

Ganin kwayakwan falo a kunne yasata Saukowa taga ko tana anan saidai me kafin ta qarasa ta hangosu manne dajuna a dining hakan yasata juyawa bashiri takoma inda tafito

Yanzu kuma wulaqancin nasu harya kai yanzu su rasa inda zasu baje kolin rashin kunyarsu sai a dakinta?

Kai gaskiya tana ganin rayuwa, dolene ma ta tarkatasu ta korasu kafin sujamata abin kunyar dayafi wannan

Wasa wasa tun tana tsumayen fitowarshi har abin yafara bata tsoro jin shirun yayi over

Jan stool tayi ta zauna ta zabga tagumi tana jiran taji koda motsin daya daga cikin su ne


Ita sai yanzu ma take danasanin riqe saudart, dama ummar sadeeq taja mata kunne akan haka tace tsakanin miji da mata sai Allah qarshenta tazo taji kunya gashi hakan kau yafaru

Ita wai nan riqeta tayi don ta garashi yasan muhinmmancin ta Ashe ja'irar 6ulamata qasa a ido zatayi

Aiko tunda abin hakane gwara suzo Susan inda dare yayi masu, bata iyawa


Jin qauri ya turnuke kitchen din yasata saurin tashi ta kashe gas cooker din tana bude tukunyar dake akai

Ganin abin ciki yafara kamu yasata jan tsaki ta dauko wurin kwashewa ta kwashe tana ayyana dolene ma suzo su kama gabansu bazasu maidata uwar banza ba

Tana cikin jiqa tukunyar datayi kamun a sink taji motsi abakin kofa

Waigowa tayi suka hada ido da ashraf da saika rantse da Allah ba shi ta kamaba ya saka Yar mutane a corner don yawani maze kamar babu abinda yafaru

Dauke kai tayi tacigaba da abinda take

Qarasowa ciki yana cewa
"Ummy yau ke ke breakfast din? Ina maid din?"

Bata ko dagoba tace
"Na aiketa" a gajarce

"Ayyah nashiga dakine naga ban gankiba shine nace bari nazonan Ashe kina ciki ma"

"Hmm" kawai tace don ita bawai son firar takeba ita in so samune ma yatafi yabata wuri

"Ummy to nidai zan wuce office munada aiyuka masu yawa baxan iya tsayawa yin break ba, nayi a office"

Cikin zuciyarta tace
"Jikayi nace katsaya dama?"

Amma a zahiri tace
"To Allah ya tsare, take care" batareda ta juyoba

Da amin ya amsa yafice yana mammakin wannan tsare gidan na ummy, watsar da tunanin yayi tinawa dayayi aidama haks take yan kwanakin nan dukdan saudart amma yasan maganinta Ai idan tasan wata Ai batasan wataba


Koda yafita saida ta jima sosai a kitchen din kafin tafito tayi shahadar komawa saman

Kamar yadda tazata bata taddataba dakin hakan yasa ta maido dakinta ta rufe tana sauke Ajiyar zuciya

Bin dakin tayi da kallo taganshi tsab tsab. Kada kanta tayi ta wuce toilet tana ayyana dolene ma su tattara subarmata gida😆



A bangaren saudart tana samu ashraf yafita tayi sauri ta ida gyara dakin, batajin tana iya hada ido da ummy dukda batasan meya faruba amma gani take data kalleta zata gano abinda yafaru, hakan yasa tana gamawa ta lalla6a tabar dakin takoma na baby

Ummy kau maid dinsu takira akan taje tasamu saudart dakinsu tayimata maganar breakfast don ahalin yanzu batajin zata iya facing dinta

Saudart kau bata kawo komai aranta ba ta sauka tayi break dinta abubbuwan dasuka faru dazun naqara dawomata a qwanya, dolene tadan ja dabaya da ashraf idan ba hakaba watarana kunya za'aji, yanzu ace dazu ummy tashigo ta gansu ahakan ina zatasa kanta? Dolene ta takamashi birki tunda taga kamar kunya be isheshiba (ruwa kike yarinya😒)

Yinin ranar ummy bata fitoba bare su hade, gwara gwara ma da baby tadawo sun shigo tareda saudart dakinta akan lunch sai cemasu tayi suje suci kawai she's busy

Ba wanda yakawo komai aranshi suka fita don zuwa suci, baby na bata labarin yadda exam din yau yayi zafi.


***

Zaune take a dakinta tana dudduba wasu kaya da za'a kawomata sari daga China aka bubbugo kofa

Saida tadanyi jimm sannan tabada izinin shigowa

Ashraf ne yashigo cikin shigarshi ta jallabiya ash colour da alama daga massallaci yake don dama ba'a dade da idarda isha'i ba

Kallo daya tayimashi ta dauke kai tana amsa sallamarshi

Qarasowa yayi ciki ya zauna qasa kusada qaffafunta yadora kanshi à cinyarta

Saurin ture kanshi tayi afusace tana cewa
"Meye haka?"

Shagwa6a fuska yayi kamar zaiyi kuka yace
"Kai ummy"

Tsaki taja tacigaba da abinda take

Kumbura fuska yayi yana hura hanci wai nan yayi fushi besan dama ciki take dashi ba

Tsaki tasake ja ta dago daga abinda take tace
"Kana jina? Jibi ka dauke matarka kabarmin gidana na gaji da ganinku fatan kajini dakyau? Jibi jibin nan kaji na gayamaka, tom" tafada tanajan kunnenta daya alamun yajita dakyau sannan tayi kwafa tacigaba da abinda take

Wara idanu ashraf yayi cikin tsagwaron mammakin kalamanta

"Ummy jibi?"

Cikeda masifa ta zaburomashi tace
"Eh jibin! Dan wlh karma ka kuskura kuwuce..."

Kasa ida maganar tayi jin ya qanqameta yana ihun murna

"Kai ummy amma Allah ya tsundumaki a aljannar fiddausi, insha Allah ga kofar gidanki gana annabi (s.a.w), Allah ya baki duk abinda kikeso, Allah ya hadaki kema da Abba a aljanna"

Wani dundu takai mashi abaya tana tureshi ajikinta
"Dan gidanku zoka fitarmin a daki, marar kunyar banza kawai"

Dariya yake yana Sosa baya inda tazuba mashi qulli yace
"Babu komai ummy, dukda haka Allah ya saka da alhairi ya kuma farantamaki yadda kika faranta Mani"

Pillow din gefenta ta dauka ta jefeshi dashi tana cewa
"Bazaka fitaba nace?"

Saurin ficewa yayi yana Dariya harda dafe ciki

Kwafa ummy tayi tana kada kai, can kuma tayi murmushi tana girgiza kai tana fadin Allah ya shirya


Shikau qasa ya sauka yana cigaba da kaka6a dariyarshi don har kwarewa yake tsabar Dariya

Aqasa suka hade da saudart datayo hanyar sama itada da baby

Tsayawa sukayi kallon ikon Allah ganin yadda yake dariyar kamar sabon kamu

Ganin saudart yasa ya tattakura ya fashe dawata dariyar yana nunata yana tafi

Sororo sukayi suna kallonshi suka kalli juna sannan suka qara maida kallonsu kanshi

Dakyar ya iya hadiye dariyarshi yace
"Congrat *MRS ASHRAF AUWAL*" saikuma yaqara fashewa da Dariya yana tafi yawucesu yana cewa
"Well play momma, well play"


Daga saudart har baby binshi da kallo sukayi baki bude har saida yafice daga falon sai a sannan suka kalli juna

Fashewa da wata mahaukaciyar Dariya baby tayi harda rintse idanu

Sororo saudart take kallonta itama tanajin gabanta na dan faduwa, kodai sun haukace ne?

Qarfin halin cewa
"Kekuma lafiya?" Tayi tana danja baya kartaji saukar bugu

Qara kecewa da Dariya baby tayi kafin tace
"Wlh mijinki ya haukace, Allah ya zare, shikenan Yaya ya zare"

Takuma fashewa dawata dariyar tanayin sama dagudu

Binta da kallo saudart tayi adan tsorace zuciyarta na ayyana mata kodai dagaske basuda lafiyar ne?

Ita bataga abin Dariya ba anan, shi ya sauko yana Dariya marar dalili itakuma tana Dariya wai ya haukace, idanma haukacewar yayi aiba Dariya ya kamaceta ba, kuka ya kamaceta.

Ta jima atsaye tana jujjuya abin aranta sannan ta fara hawan saman jiki a sanyaye

Asama kau dakin ummy baby tafada tana cigaba da dariyarta mai kamada ta mahaukata

Kafin ummy ta dago harta fado Kanta tana cigaba da dariyarta

Tureta ummy tayi tana cewa
"Lafiyar ki lau kuwa?"

Cikin Dariya baby tace
"Wlh ummy yanzu muka hadu da yaya qasa yana gagga6a Dariya kamar sabon kamu, wlh harda tafi" takuma fashewa dawata dariyar

Wani dogon tsaki ummy taja bayan tagama binta da kallon takaici

Kofa ta nunamata tana cewa get out

Ba musu ta tashi tafita tana cigaba da dariyarta


Saudart na zaune a dosane gefen gado tana tunane tunane tajiyo dariyar baby na tunkaro dakin

Saurin dago Kai tayi tana kallon kofar.

Shigowa tayi tana cigaba da dariyarta saidai yanzu tadan rage saboda cikinta daya fara amsawa

Bata ko kalli saudart ba ta fada kan gado tana qara dafe cikinta daya fara mata ciwo Dom Dariya

Itadai saudart na zaune tana kallon ikon Allah tana ayyana duk yadda akai baby bata rasa ingilmu akanta

Saida ta huta sannan ta tashi ta wuce toilet saudart tabita da kallo

Bata dade ba tafito daure da towel da alamu wanka tayi

Kallon saudart datayi zugum tana kallonta tayi tace
"Aunty ke ba yanzu zakiyi wankan ba?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace
"A'a yanzu zanyi"

Daga haka ta tashi ta wuce itama toilet din tana qara mammakin abinda yasamesu

Koda tafito har baby tayi barci

Chanza kaya zuwa na barci tayi tazo ta kwanta gefen baby tana kallonta

Saida ta tottofamata addu'o'i sannan itama tayi addu'ar barci ta rintse idanu

Ta dade tana jujjuya abinda yafaru dazun kafin wani barci mai dadi yazo yayi awon gaba da ita...✍️


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)



Story written by Ashaanty love💖




100



A bangaren ashraf kau he is super happy, shi bema wani lura da baby ba daya sauko qasa kodayake ga yadda yakeji alokacin koda ya gantan hakan ba zai hanashi bayyana farincikinshi ba.

Yau ummy ta sashi farincikin da be ta6a yiba arayuwarshi, haryanzu ganin abin yake kamar wasa

Koda yashiga dakinshi, saiti yayi kamar a wasan tsere ya falfala da gudu yayi wani qundunbala akan gado yana Dariya, jiyake kamar yayi hauka don farinciki.

Harya dauko wayarshi zai kira amininshi saikuma yayi tsaki ya jefar da wayar can gefen gado yakoma ya kwanta rigingine yana qiyasta yadda zasu shimfida sabuwar rayuwarsu su biyu a matsayin ma'aurata

Ranar dakyar barci yasaceshi can tsakiyar dare wanda ke cikeda da mafarkan saudart

Yau tunda yatashi da asuba be komaba, gari na danyin haske yafice daga gidan ko shiga gaida ummy beyiba


A bangaren su baby kau yauma da wuri ta shirya don yauma sunada exam na safe saidai dawuri zasu dawo don paper daya garesu

Tare suka shiga gaida ummy wanda ta amsamusu as usual cikin fara'arta ko kadan bata nunama saudart komaiba shiyasa itama bata kawo komai araiba

Baby tayimusu sallama ta tafi while saudart tahau gyara dakin ummy kamar yadda tasaba

Sai wajajen 10 tagama gyare gyaren dakunnan nasu sannan ta sauko qasa tayi break tana gamawa ta hayewarta sama don hutawa


1:30pm baby tadawo daga school, saida tayi wanka sukayi sallar zuhr sannan suka sauko yin lunch

Anan ne ummy kecewa idan sungama zata basu kudi suje saloon suyi gyaran kai da Kunshi

Zokaga murna wajensu, musanmman saudart da tunda tazo gidan bata sake leqa wajeba

Cikin zumudi suka qarashe cin abincin sannan suka haye sama don shiryawa baby sai tsokanar saudart take wai ba sabon ba yau akuyar daure tasamu sake, itadai saudart bata biyemata ba don a qagare take sutafi kafin ummy ta chanza shawara

Wajajen uku suka fito cikin shirin su ta kamala don duk hijabai sukasha har qasa, da baby gyale taso sawa amma ganin saudart ta zumbula hijab yasata fasawa itama ta zira tata har qasa

Tare sukaje suka amshi kudin ummy sai yaba kyawun su take sannan sukayi mata sallama suka fita zuwa parking space inda driver ne zai kaisu.


A wani qayattacen saloon driver ya ajiyesu, koda ganin yanayin wajen kasan na masu dashi ne

Shiga sukayi cikin sa'a kuma ba jira kasancewar yau alhamis ba mutane sosai ba kamar weekend ba

Cikin dan qanqanin lokaci aka fara musu gyaran kan wanda saida sukayi zaman tsefeshi sannan aka hau gyaran

A taqaice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login