Showing 147001 words to 150000 words out of 173829 words

Chapter 50 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1156

takusan katsewa sannan ya daga ya kara a kunne yace
"Uhum?"

"Ango! Ango!! Ango!!! Ango kasha qamshin ne koko dasaura?" Inji sadeeq cikin shaqiyanci

Tsaki ashraf yaja yace
"Fadi abinda zaka fadi am busy right now"

"Inyee? Ka fadi hakan Ai amma wajen neman taimako ka iya marairaicewa kana qanqan da kai kamar dan maula"

"Mtcheew, kamar yadda nafada maka dazu am busy so idan bakada abin fada kindly hang the call"

"You're busy doing what?" Sadeeq ya tambaya in a naughty way

"Bansàniba"

"Kar Allah yasa kasani, dullie kawai wanda besan arziqiba" inji sadeeq cikin son qular dashi

"Naji nagode, Ai kai kasan shi ko? Hakan Ai ya wadatar" ya amsa in an i-dont-care mannar

"Mtcheew ba laifinka bane, laifinane Dana kiraka"

"Gwara daka gane hakan, gwauro kawai"

"Gwauraye dai"

"Kana hauka, waye gauron, kai bakama ji kunyar fadin haka ba"

"Kunyar me? Ba gaskiya bane?"

"Oho dai, idan zaka ajiye shiririta kayi aure ka aje kayi don na kusan Barin mu'amala da gwauro" yafada yana taje kanshi

"Hmm wai kura zatacema kare maye, kai har kanada bakin yima wani gori? Aikin banza kawai bansan abinda yasama na kirakaba at the first place, mtcheew mood spoiler kawai" yana kaiwa nan ya katse wayar

Dariya ashraf yayi yana ajiye wayar kan mirrorn yanufi closet dinshi

Agurguje ya shirya cikin wasu qanannun kaya wando da T-shirt baqaqqe tareda feshe jikinshi da turarenshi mai dadin qamshi ya dauki wayoyinshi ya fice daga dakin...✍️

Manage pls👏


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️



👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)


Story written by Ashaanty love💖


097


Dole ta tashi tabar falon jin ana kiraye kirayen sallar magrib

Alwala ta dauro tazo ta gabatar da sallar magrib ta zauna bayan ta ida ta zabga uban tagumi

Tunani kala kala na kai kawo a kwakwalwarta

"To ko fushi yayi? Amma Ai ita yayima laifi meyasa shi ke fushin kuma?" Tambayar datake tayi ma kanta kenan

Tarasa dalilin dayasa rashin kulawarshi agareta na yini daya yayi affecting dinta sosai har haka

Gashi ego dinta ya hana ta lalubeshi ta waya koda ta text dinne, gani take hakan zubda mutunci ne agareta.

Tana nan zaune tana karatun jaki har aka fara kiraye kirayen isha'i, saida ta chanzo alwallarta sannan tazo ta gabatar da ita itama


Zaune suke a dining sunayin dinner

Ummy tun dazu take nazartar saudart ganin yadda take tsakurar abincin kamar bataso dama tana lura da ita duk yau kamar bata cikin walwalarta don takoma wata sukuku daita

"Daughter?"

Dagowa saudart tayi ahankali ta kalleta

"Meke damunki ne? Is anything bothering you?" Ta tambaya cikin kulawa

Itama baby tsayar da cin abincinta tayi tana kallonta don itama tun dasafe ta lura yau Auntyn tata bata cikin walwala don ko magana bata cika son yiba


Murmushin yaqe saudart tayi tace
"Am fine ummy, kawai am not feeling well ne"

"Me yasameki to, is it fever?" Tafada tana ta6a wuyanta donjin temperature dinta

"No ummy kawai slight headache ne kuma banida appetite" ta amsa asanyaye

Cikin jimami ummy tace
"Eyyah, now ki daure kiqara cin abincin ko yayane saina baki medicine, ok?"

Gyada mata Kai tayi ta dauki spoon dinta

"Sorry aunty" inji baby

Itama kadamata Kai tayi tashiga cigaba da tura abincin badon dadi ba

She's just missing him so very much

Ayyanawa take aranta da yananan da yanzu yananan ya takurata da wannan mayen kallonshi, da yanzu duk hada idon dazasuyi sauya kashe mata ido, da yanzu yakusan cika mata waya da texts

Haka dai tasamu tadan qaracin abincin, ummy ta rakata sama ta 6allamata maggunguna tasha ta kwanta bisa umarnin ummy

Tana cikin bargo taji ummy na waya da ashraf

Shiru tayi cikin bargon tana sauraronta harsukayi bankwana

Dago wayar dake hannunta tayi tacikin bargon tana kunnata tana kallonta

Gani take kamar daya gama wayar da ummy zai kirata or yaturo text amma har aka kusa shafe awa ba kodaya daga ciki dayayi

*why are you angry?* ta tambayi kanta still tana kallon wayar

*Are you fed up with me already?*

*am I too harsh?* duk wadannan zantukan acikin zuciya takeyinsu

Lumshe idanu tayi tanajin zuciyarta na daci sosai

*am missing you.... So much* tafada under her breath tana dora wayarta akan qirjinta tareda rungumeta

Ahakan barci ya dauketa batareda ta saniba

A bangaren A.A kau dama tun jiya sukayi arranging meeting da wani company mai muhinmmanci

Koda saudart taqi kulashi kyaleta yayi ya kwanta saidai Sam barcin yaqi zuwa hakan yasashi tashi yajawo laptop yadan rage ayyuka wanda hakan yasashi raba dare sai can wajajen uku yasamu ya kwanta

Da asuba bayan yagama sallah kawai yahau shirin office dukda zuciyarshi na azalzalarshi akan yakira saudart ko yamata text yadda yasaba saikuma ya fasa acewar gwara yabata space tahuce ganin yadda tahau sosai jiya inda shi harga Allah besan hakan zai 6atamata rai ba

Koda yafito don gaida ummy sai yaci karo daita a kitchen hakan yasa besamu Damar haurawa sama ba

Dayake sauri yake ko break be tsaya yayi ba yawuce zuciyarshi cikeda son ganinta


A office kau tunda yaje yashiga busy don aiki ne sosai a desk dinshi kasancewar yayi sati rabonshi da office din kuma be samun damar ragewa a gida sanaddiyar shiriricewa dayake da saudart ta waya

Ga kuma meeting din dazasuyi wannan yasa be dawo gidaba sai wajajen 10 don sosai aikin ya riqesu gashi ba secretary bare adan samu saukin aikin

Koda yadawo a matuqar gajiye yake hakan yasa yanufi part dinshi kai tsaye yayi wanka yayi shirin barci don dama yayi dinner awaje, hakan yasashi kiran ummy yayimata saida safe don a yadda yake agajiyen nan be iya sake fitowa

Koda suka gama waya saida yashiga contact dinta yanaji kamar ya kirata sai kuma wata zuciya tace mashi ya kyaleta kawai yadan bata space yadda zata huce sosai hakan yasashi ajiye wayar ya shige cikin duvet nan da nan barcin gajiya yayi awon gaba dashi

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


Washegari ma tun bayan sallar asuba yayi shirin office don yau dinma sunada aiyuka da meeting masu muhinmmanci dazasuyi.

Wajajen 7:30am yafito daga part dinshi yashigo cikin gida saida suka gaisa da maid dinsu dake falo tana mopping sannan ya haura sama dakin ummy

Saida ya kwankwasa sau biyu sannan ummy tabashi izinin shigowa

Da sallamarshi yashiga yaci adonshi cikin blue suit da farar inner yayi kyau sosai sai baza qamshi yake

Amsawa ummy dake zaune akan sallaya hannunta riqe da hisnul Muslim tayi tana dagowa daga littafin

Zaunawa yayi shima qasa kusada ita yana satar kallon saudart dake qudundune a bargo da alamu ma barci take

Gaida ummy yayi cikin girmamawa yana dora kanshi kan kafadarta

Shafa kanshi tayi tana amsawa tana tambayarshi ya gajiyar jiya

Amarairaice yake amsamata da alhamdullilah


Maganar breakfast tayi mashi yace A'a zaiyi acan yanzu sauri yake

Haka yatashi sukayi sallama da ummy yana qara satar kallon saudart da batasan wainar da akeyi ba ya fita

Abakin kofa yaci karo da baby itama zata shigo

Gaidashi tayi ya amsa yayi gaba

Binshi tayi saurin yi tana fadin
"Please yaya inzo ka ragemin hanya?"

Banza yayi daita kamar bazai amsaba saikuma yace
"Don't waste my time"

Da sauri tajuya tashiga dakin ummy tayimata sallama a tsaitsaye ta fito tana gyara zaman jakkarta dake dauke da few books ta sauka da sauri gudun karya wuce yabarta

A parking space ta ganshi yana niyyar shiga mota hakan yasata saurin qarasowa itama ta bude dayan side din ta shiga ya kunna motar yaja suka fice daga gidan


Sai wajajen 9:30 saudart ta tashi barcin da ummy tasata dole takoma

Dama tana gama sallah da azkar dinta ta tashi zata gyara dakin ummy tasata takoma ta kwanta ganin haryanzu komai sukuku take yinshi kamar marar lakka

Tana kwanciya ba dadewa wani barci mai shegen dadi yayi gaba daita kasancewar dama jiya bawani barcin kirki tayiba

Batafi minti 15 da barci ba ashraf shikuma yashigo


Addu'ar tashi ta karanto tana yaye bargon jikinta

Dumm gabanta ya bada jin qamshin da mutum daya tasani dashi waige waige tashigayi a dakin kafin ta sauko qasa tana qara shaqar qamshin

Tabbas qamshinshi ne, hakan na nufin yashigo dakin? When?

Bude kofar da akayi yasata dagowa ta kalli saitin kofar

Ummy ce tashigo cikin fara'a tana cewa
"Daughter kin tashi? Ya jikin?"

Murmushi tayi tana cewa
"Da sauki ummy"

"To masha Allah, maza kiyi brush ki sauko ki karya"

Da to ta amsa tashige toilet domin yin yadda ummin tace


Koda ta sauko har an ajiye mata abincin, abakin maid dinsu takejin baby ta tafi makaranta tarema suka fita da Ashraf

Sosai ranta ya dagule fiyeda jiya ma, jitake komai yabar mata dadi, jitake kamar ta shekara bata ganshi, she's missing everything about him

Yauma haka ta wuni sukuku saidai she's trying her best wajen nunama ummy she's normal don sosai ummy ke nuna damuwarta akanta.


Wajajen two baby tadawo gidan hakan yasa tadanji sauqi sauqi saboda surutu da ban dariyar baby yadan rage mata damuwarta


*6:15pm*

Saukowa tayi daga sama hannunta riqe da qaramin bowl data gama shan farfesun cow leg da ummy tabata wanda yaji kayan qamshi da maggunguna masu inganci

Shiga tayi kitchen ta dauraye bowl din ta maidashi ma'ajinshi sannan tafito daga kitchen din tana dan yarfe hannayenta


Cak ta tsaya da abinda take tana kallonshi zuciyarta na chanza bugu

Ashraf da dawowarshi kenan yana zaune akan kujera ya duqa yana zare socks din kafarshi ya dago shima idanunsu suka gauraya

Kasa janye idanunta tayi akanshi tacigaba da kallonshi wani emotional feeling na tasomata daga Chan qasan zuciyarta

Shima hakan take agareshi, kafeta yayi da idanunshi kamar zaiyi devouring dinta yana sake jin kewarta acikin zuciyarshi

Sun kai kusan two minutes suna kallon juna kafin ashraf ya tashi ahankali ya nufota

Kallonshi tacigaba dayi idanunta na kawo kwallar da batasan dalilinta ba harya qaraso gabanta

Sai a lokacin ta sauke idanunsu qasa wanda yayi daidai da digar hawayen idanunta

Dago ha6arta yayi yana kallon fuskarta hakan yasata saurin lumshe idanunta wanda hakan yaba sauran hawayen damar gangarowa

Da mammaki yake kallonta don besan dalilin wadannan hawayen ba

"Saudart..."

Saurin juyamashi baya tayi gabanta na bugawa sosai yayinda hawayen ta yaqi tsayawa

Ganin haka yasashi zagayowa ta gabanta yasake fuskantarta

Saurin rufe fuskarta tayi da tafukan hannu don batason yaga hawayen gashi ita ta kasa tsaidasu

Shiru yayi yana kallonta na wani lokaci kafin yace
"Saudart.."

Nanma shiru kuma bata sauke hannunta ba daga kan fuskar

"Are you still angry?" Ya tambayeta a tausashe

Nanma bata motsaba saima qara gudu da hawayenta sukayi

"Am sorry uhm? I don't mean to scared you" yafada almost in wishper

Nanma batace komaiba

"Please open your face"yasake fada amma bata bude ba

"Are you still angry?" Yasake tambayarta cikin damuwa

Shiru tayi bata kuma janye hannun daga fuskarta ba

"My presence is irritating you ko? Intafi?" Yaqara tambayarta cikin sanyi

Samun kanta tayi da girgiza mashi kai ahankali

"Then ki bude fuskarki please" yafada yana janye hannunta hakan yasa tayi saurin Zamewa ta zauna qasa tana cusa fuskarta a tsakankanin qaffafunta

Murmushi ya su6uce mashi shima yabita qasan ya zauna yana kallonta na wasu daqiqu yace
"Wai 6oye fuskar dikna menene?"

Banza tayi dashi takuma qi dagowa

Murmushi yasake saki sannan ya matso da fuskarshi dab da tata yace
"Did you miss me too?"

Sai a sannan ta dago fuska sha6e2 da hawaye ta gallamashi harara ta maida fuskar a inda ta dagota

Dariya sosai tabashi hakan yasashi yin kayanshi

Sake dagowa tayi ta kalleshi ta 6ata fuska ganin yadda yake mata Dariya

Yunqurawa tayi zata tashi yayi saurin kama hannunta yana Dariya yace
"It ok, it ok na daina" yafada yana dan toshe baki da dayan hannun fuskarshi dauke da murmushi

Dan kawar da kai tayi tana dan murmushi, aabin mammaki jitayi zuciyarta wasai babu digon damuwa ko kadan saima farincikin daya maye gurbinshi

Tankwashe kaffafu yayi ya buga tagumi da hannu bibbiyu yace
"Now tell me, wadannan hawayen na menene?"

Harara taqara gallamashi tana saka bayan hannu tana goge fuskar

Wani white handkerchief yafiddo daga aljihunshi yabata

Saida tadago ta kalleshi sannan ta amsa ta ida goge fuskar tanayi tana shaqar qamshin handkerchief din

"Inaji, why those tears?" Yasake tambaya yana kallonta

Qin dagowa tayi bare tabashi amsa

"Oho? Nagane, saboda Karna tambayi coffee Dina ko? Hard luck👎🏻 don wannan bazai ceceki ba"

Qara dagowa tayi ta dan harareshi

"That also won't save you miss emoji, I'll make sure you learn a lesson"

Sinne kai tayi tana Dariya marar sauti jin yace mata miss emoji

Qara kusanto da fuskarshi yayi da nata yace
"Yanzu gayamin, did you miss me?"

Dagowa tayi ta kalleshi tadan yamutse fuska tace
"No?" Kamar a sigar tambaya

Wara idanu yayi harda dan bude baki yace
"Really?"

"Ni kau kinga you're sticked to my brain, ina aiki amma ke nake hange, because of you saida nayi mistakes dayawa wanda saboda cancelling da retyping kalli yadda yatsuna sukayi swelling ga wancan annoying fringe daya tasani gaba da ban haushi, Abu ya hademin goma da ishirin kamar inyi hauka shine zaki ce bakiyi missing dinaba nima? Kai amma kin gama dani" yaqarashe zancen yana dafe Kai🤦🏻‍♂️

Dariya yabata sosai hakan yasata sadda kai tanayi ahankali ga wani farinciki dake sake lullu6e zuciyarta

Zai sake magana yaji gyaran murya a bayanshi hakan yasasu juyowa gabadaya

Baby ce tsaye tadan Sosa qeya tace
"Erm... Dama ummy tace na gayamuku Ku tashi kuyi sallah"

Waro idanu saudart tayi tayi saurin miqewa tsaye don ita tama manta inda suke saboda shagala

Shima miqewa yayi yana kallon wristwatch din hannunshi yaga bakwai da kusan rabi, tuni aka gama magrib sai batun isha'i kuma

Saurin bin bayan baby da tuni tayi gaba Dariya fall cikinta tayi yayinda shikuma yabita da kallo

Saida takai bakin stairs zata taka saikuma tajuyo

Hada idanu sukayi ya kashe mata ido daya, saurin juyawa tayi ta haurawarta tana smiling itama

Saida ta 6acema ganinshi sannan ya kauda kai yana murmushi hadi da shafa kanshi

Zira takalminshi yayi yafice shima yanufi part dinshi dauke da murmushi a fuska...✍️


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️




👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)


Story written by Ashaanty love💖


098



Koda saudart ta haye saman kasa shiga dakin ummy tayi, tayaya zata iya facing din ummy? Wataqila ma ta gansu

Ta dade a bakin kofar tana shawarar shiga, ganin dai bata iyawa din yasata chanza akalarta zuwa dakin baby

Jin an bude kofa yasa baby dagowa tana kallon kofar

Tana ganin itace ta fashe da Dariya tana toshe baki

Ko gefenta saudart bata Kalla ba tanufi toilet

Alwala ta dauro tadawo ta zari hijab cikin wardrobe tahau sallayar da baby ta shimfida mata ta kabbara sallah

Koda ta ida har wasu massallatan sun fara isha'i don haka itama tashi tayi ta jona da ita



*DINNER*

zaune suke su uku suna cin abincin dare in silent

Tun saudart na dari dari da ummy harta dan saki jiki ganin ummy bata wani nunamata komai ba

Abincin takeci saidai rabin hankalinta naga kofar shigowa, she's wondering why haryanzu be shigo yin dinner ba

Haka kawai saita samu kanta da damuwa da hakan tanajin abincin ma na fita kanta

Sunyi nisa acin abincin taji screeching din handle din kofa hakan yasata saurin dagowa tana kallon saitin

Bayyanarshi yasata jin wani sanyi na ratsa zuciyarta yana maye gurbin damuwarta

Janye idanunta tayi cikin jin kunyar kamata dayayi tana kallonshi ta maida kan abincin ta tana tsakura

Da sallama yashigo dining area din ya chanza shiga zuwa blue three quarter da farar T-shirt

Duk amsa mashi sallamarshi sukayi yaja kujerar dake facing din saudart ya zauna yana kallonta ta qasan ido

Baby ce ta gaidashi ya amsa yana janye idanunshi daga kanta sannan ya dago ya kalli ummy yana gaidata

Amsawa itama tayi agajarce tana cigaba da cin abincinta

Dago idanu tayi da niyyar Satan kallonshi sai kawai suka fada cikin nashi kasancewar dama ita yake kallo

Kashe Mata ido yayi kamar yadda yasaba idan suka hada ido

Janye idanunta tayi dan murmushi na su6uce mata itama ta gaidashi asanyaye

Amsawa yayi in joy sannan yasa hannu ya janye plate din abincinta ya maido gabanshi yahau ci batareda ya damu da kallon reaction dinta ba

Dagowa tayi ta kalleshi tana 6ata fuska ganin beko dagoba bare yasan tanayi ba yasa tadan saci kallon ummy taga ita abincinta ma takeci da alama ma batasan abinda sukeba

Hakan yasata satar kallon baby itama, kashe mata ido baby tayi tana sunkuyar dakai don 6oye dariyarta

Janye idanunta tayi daga kanta ta zari wani plate din taqara serving kanta wani abincin

Gamawarta keda wiya taga anqara janye plate din an turomata wancan na dazu wanda yanzu babu komai ciki don dama abincin ciki bawani mai yawa bane

Sagale tayi tana kallon plate din leftover din sannan ta dago ta kalleshi

Daga mata gira daya yayi tareda sakin murmushin gefen baki na mugunta yacigaba dacin abincin shi yana kada Kai

Janye idanunta tayi tareda sadda kai cikin rashin sanin abin yi

Jin qarar jan kujera baya yasata dagowa taga Ashe ummy ce ta tashi tana goge bakinta da tissue

Batace komaiba tabar dining din tahayewarta sama

Ganin haka yasa itama baby shan ruwa ta tashi tun kafin akoreta itama tabar wajen cikeda jin haushin buqulun da ummy tayimata na ganin qarashen show dinsu

Barin baby wurin keda wuya itama saita matsar da kujerarta baya zata tashi yayi saurin dafe hannunta yana dagowa tareda sakarmata idanunshi

Dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta maida kanta qasa sanaddiyar kwarjinin dayayi mata

Tashi yayi ya dauki plate din abincinshi ya zagayowa wajenta yajawo wata kujera ya maidota gefenta ya zauna ya ajiye plate din gaban su yaqara spoon daya aciki ya tura plate din gabanta yana cewa
"Oya eat"

Bata dagoba saima wasa datakeyi da zoben yatsarta tanajinta amatuqar takure a dalilin kusancinsu ga qamshin turarenshi daya addabi qoffofin hancinta

Ganin taqi kulashi yasashi debo abincin a spoon yakai saitin bakinta

Dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta kauda kai

"Open up mana" yafada yana sake binta da cokalin abincin

qara kauda kai tayi tana cewa
"am full"

"You're not, idan dagaske kin qoshi meyasa kika zubo wannan?"

Qara janye fuska tayi ganin yana qara nufota da spoon din tana cewa
"Allah na qoshi"

"Baki isaba" yafada yana qara matsowa zaibata da tsiya hakan yasata yunqurawa zata tashi yayi saurin maidota ya zagayo hannunshi ta tiny curvy waist dinta yayi pulling dinta ajikinshi

Waro manyan idanuwanta tayi in shock tayi saurin sa tafukan hannu ta dafe broad chest dinshi ganin jikin su na neman hadewa

Wani yanayi ashraf yajishi aciki don sosai contact dinsu yakawo effect agareshi

"Now open up" yafada cikin muryarshi data fara chanzawa

Atsorace take kallonshi ga kuma yadda tsigar jikinta ke tashi sosai

Saurin kauda kai tayi again ganin yaqara nufota da spoon din

Yatsunshi biyu ya luma mata a kwarin kugunta wanda yasata saurin zabura ta fada jikinshi tana gasping.

Lumshe idanuwa yayi jinta ajikinshi yasaki cokalin hannunshi ya maida hannuwanshi ata bayanta ya rungumeta yana sauke nannauyar Ajiyar zuciya

Itama lafewa tayi a jikinshi idanuwanta a lumshe tana qara shaqar qamshin turarenshi mai sanyin dadi

Ga wani sense of security datake ji jinta acikin warm broad chest dinshi

Shima lumshe idanunshi yayi yana inhaling qamshinta yanajin kamar su dawwama ahakan

Sun dauki tsawon lokaci ahakan batareda sun Ankara ba don gabadayansu sun gama lulawa wata duniyar daban

Jin saukar numfashin shi a gefen wuyanta yasata bude lumssasun idanunta da sauri, ganinta acikin qirjinshi yana sake qoqarin cusa kanshi a wuyanta yasata saurin dagawa daga jikinshi tana ja baya

Kasancewar a kasalance yake yasashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login