Showing 12001 words to 15000 words out of 173829 words

Chapter 5 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1101

fall murmushin mugunta

"Ehh...Sir"

Furzar da iska yayi yana lumshe idanu cikin jindadi sannan ya budesu akanta.

Kanta na sadde Kasa hawaye na diga zuciyarta na wani irin zafi.

"Yanzu kinsan koni wanene?" Ya tambaya

"Yes"

"Yes what?"

"Yes sir" tafada tana girgiza kai ahankali don takaici.

"Yakamata kisan gabama da gabanta, nafi qarfin cakuri cici irinki, kamar yadda nafada abaya wutsiyar raqumi tayi nesa da kasa , so maintain ok?"

Nan ya dauko wata paper acikin wani file ya ajiye mata gaban desk dinta.

"Gashi na taimaka nabaki ba don halinki ba ko dan kinkai, sign and get lost"

Cize lips dinta nakasa tayi sannan ta dauki pen din hannunta nadan rawa, batareda ta karanta shirmen da'aka rubutaba tanemi inda zatasa hannu ta Dora hannu sama.

Shiru kamar bazatayiba saita daure tayi signing zuciyarta na wani irin karta.

Ajiye pen din tayi tana sauke ajiyar zuciya.

Shima dauka yayi yayi sign inda yakamata sannan yace
"DEAL!" Yana buga stamp akai.

Bata ankaraba taji ya fizgo hannunta na dama, saurin dagowa tayi tana kicin kicin kwace hannunta Amma takasa.

Wani box yafiddo a aljihunshi da hannu daya dayan na riqeda hannunta.

Budewa yayi sannan yafiddo wani hadadden zobe mai kyau yazuramata a yatsa ta karshe.

Kukane ya kufce mata zuciyarta kamar ana haura wuta.

"Welcome, welcome to the famous's world, ba suna kikeso ba zakiyi suna"

Yafada haryanzu yaqi sakin hannun.

Zaremata glass din idanunta yayi yana kallonta.

"Idan kika zare wannan ring din... Deal cancelled! Kuma kinsan har tsinemiki kwadayayyen babanki na iyayi"

Yayi wurgi da hannun a kyamace.

"Get lost, gobe by four zan aiko driver ya dauko ki ki kasance cikin shiri. GET LOST!"

Yafada yana komawa bisa kujerar shi.

Ahankali ta dago idanunta ta zubamashi, gabanshi ne yafadi ganin kallon tsantsan tsana datake mashi.

"Mekuma kike jira, ki 6acemin nace"

Glass dinta ta dauka Daga kan desk din still tana kallonshi sannan ahankali ta bude baki cikin wata iriyar murya tace

"I HATE YOU....WITH PASSION"

sannan tajuya tafice cikin sassarfa.

Bin kofar yake da kallo kamar still tananan, zuciyarshi namashi saqe saqe.


Unlike ranan yau ahankali tafito, ta maida glass dinta don haka babu Wanda yasan yanayin fuskarta.

Wuce Helen tayi ko kallonta batayi ba, itakau Helen tabita da kallon tuhuma.



Mota tashiga ta tada sannan ta figeta da wani irin gudu ta halba titi...✍


Ummin fasihu ce🧚‍♀


🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)





016





Tuqi take Amma ita kanta tasan kariyar Allah ce kawai ke tareda ita, Jitake kamar tacire zuciyarta ta jefar saboda radadi

'He blackmailed me'
'He made me beg'
'He forced me'

Wasu hawaye suka qara gangarowa fuskarta ta sharesu afusace.

Qara gudun motar tayi, batayi koina ba sai gidan maminta (inda take aure)


Budemata gate akayi ta Danna hancin motarta ciki.

A parking space tayi parking Saidai takasa fitowa, Duk Jitake jikinta kamar ba nataba , ga wani Sara da kanta keyi.


Tafi minti biyar ahakan sannan tasamu tafito dakyar hannu daya dafe da kai.

Kwankwasa kofar tayi sannan ta murda tashiga da sallama.

Babu kowa a falon kasancewar Duk qannenta ('ya'yan mamy) suna Maiduguri wajen kakansu Hutu.

Su biyar mamy ta Haifa a wannan gidan.

Aminulah dan shekara 16, sai kamalideen dan shekara 14, sai Ibrahim 11, habeeb 09 sai auta Abdul baseet 05.

Saudart nason qannenta sosai suma haka suna sonta sosai, Duk weekend idan tazo fira suke sha kamar me? Akwai shaquwa sosai tsakaninsu.


Zubewa tayi kan three seater din falon tana dafe kai.

Tafi mintuna biyar ahakan kafin mamynta tafito Daga kitchen da alama girki take.

Da farko bata lura daita ba saida tashigo falon sosai, tsoro taso bata data ga mutum kwance a falo.

Saida ta qaraso sannan tagane Saudart ce

"Saudart?"

Bude jajjayen idanunta dasukayi mata nauyi tayi ta kalleta saita tashi zaune a kasalance.

Qarasowa mamy tayi ta zauna itama daf da ita.

"Saudart lafiya?"

"Mamy ina wuni?"

"Lfy lau, meya sameki ne? Ji idanunki, ga muryar ki ma"

"Mamy bana jindadi ne" tafada tana kallon qasa.

"Kamar ya? Kallo daya za'a yimiki asan kinyi kuka, fadamin menene"

Girgiza kai tayi alamun babu komai.

"Wajen aikinkine?"

Nanma girgiza kai tayi

"Ko babanki ne?"

Murmushin takaici tayi sannan tace
"Mum please, nace babu komai, bana jindadi ne, kaina ke ciwo" tafada tana dafe kai.

"To Allah ya sauwaqe taso kishiga daki kisha magani ki kwanta.

Na musu ta tashi tabita wani daki, acan mamy ta bata magani sannan ta umarceta da ta kwanta tasamu barci.

Kasa barcin tayi koda mammyn tafita.

Qurawa ceiling kawai tayi tana tunane tunane.

Motsi kadan saita girgiza kai tana murmushin takaici.


Ahaka barci ya dauketa. Bata farkaba sai four shima mamy ta tadata tayi Sallah, da to kawai ta amsa dukda ba sallar takeba.

Watsa ruwa tayi a bandakin dakin sannan tafito.

Saida ta cika cikinta bam sannan ta bar gidan Bayan mamy tata bara shawarwari Masu amfani.

Gida tanufa kai tsaye, yanzu tarage jin zugin zuciyarta.

Horn daya tayi aka Budemata.

Da sallama tashiga falo ta hango dad zaune yana amsa waya

"Ok hang on zan kiraka" yafada yana tsinke wayar sannan ya miqe yanufota yana dariya.

Rungumeta yayi cikin jindadi yana ta suburbuda mata albarka don burinshi yacika, harma yaji alert.

Itadai Saudart iyakarta murmushi Wanda bana komai bane saina takaici.

Sai nan nan yake da ita, lokacin barci ma dakanshi yakaita daki yayi mata addu'a sannan yakashe mata wuta yajawo mata kofa.

Murmushin takaici tasakeyi tana girgiza kai.

Ta dade kafin barci Yaa dauketa, don data runtse ido abinda yafaru dazu take gani.

Dakyar tasamu barci ya dauketa can biyun dare.
Asuba tagari😴







Washegari bata wani damun kanta wajen shirin bakery ba, don bazata jeba, wanka kawai tayi ta kintsa kanta sannan tahau yin aiki a laptop.

Haryanzu fuskarta a cunkushe yake don haryanzu bata warwareba Daga abinda yafaru jiya.

Zobe kuwa bata cire shiba, yana a yatsarta ko meyasa oho?

Daddy ma yau be fitaba Wai zai tayata zaman gida tunda batajin dadi.

Saidai waya dayake tayi da mutane akan business, kallo daya zaka mashi kasan yana cikin farinciki.

Hakan yasa itama Saudart taji Dama Dama don farincikin daddynta natane.



3:40

Suna zaune a falo, Saudart na kallo Alhaji na aiki a laptop sukaji qarar door bell.

Tashi tayi tana cewa "bari naduba"

Koda tabude maigadi tagani tsaye, fuska a washe suka gaisa tana tambayarshi lfy?

"Hajiya wani ne yazo daukanki"

"Wani?"

"Eh hajiya"

"Tofah wanene?"

Alhaji shamsu shima yataso

"Shalele menene?"

"Dad Wai wani yazo daukata Wai"

"Dauka? Waye?"

"Wlh Alhaji nima bansanshiba"

"Cemashi ya qaraso"


Sunanan tsaye saiga wani saurayi ya qaraso cikin shigar suit.

A ladabce ya gaida Alhaji, ya amsa itadai Saudart nata ido.

"Tofah, kaikuma Daga ina?"

"Sir, sir A.A yace nazo na dauko madam"

Kallon juna Saudart da Alhaji sukayi.
Sai asannan Saudart ta tuna dayace mata zai aiko driver qarfe hudu, ca6 aikau za'a yita.

"Shalele, dagaske ne?"

"Tayaya za'ayi insani daddy? Nima bansaniba, kai kaje ka sake tambaya qila 6atan hanya kayi"

Tafada tana komawa ciki.

Alhaji ya maido kallonshi kan saurayin "ka tabbata nan aka aikoka?"

"Eh Sir, nanne"

"Ok kajira ina zuwa"





Hmm yau ake yinta, don firr Saudart taqi yarda da buqatar daddy

"Dad ya kakeso danine? Ni matarshi ce dazai wani aiko azo a dauko ni? Gidan ubanwa ma zai kaini? Dad kaima kasan this is not proper"


"Saudart..."

"Daddy nayima biyyaya, bada son rainaba na amince da AUREN KWANGILA, ka tilastani nayima biyyaya, Dan Allah karka tilastamin wannan saboda ina gudun in bijirema"


"Saudart, wannan fa abin ba komai bane kawai..."

"Agarekane ba komai ba dad, agarekane ba komai ba, daddy ka daina sona, Baka sona, kafi son kudi akaina? Kafison dukiya akaina? Kafison farantama wani akaina?" Saikuma tafashe da kuka.

Sosai jikin daddy yayi Sanyi, rungumota yayi yafara rarrashinta cikin baiwarshi ta dadin baki.

Yasha wahala kafin yashawo Kanta ta yarda zataje.

Fita yayi yabata wuri don tashirya.

Yana fita ta Dora babin kukanta saida tayi mai isanta sannan tashige bayi tayi wanka.


Da gangan taita Jan jiki sai wajajen 4:30pm tagama shirin.

Izuwa yanzu Daga Alhajin har drivern sungaji dajira.

Ahankali ta sauko, yauma kamar jiya idanunta dode cikin NO RESPECT

Sakin baki daddy yayi ganin irin masifataccen kyan datayi.

Sanye take ciki Jan less mai touches din baqi, anmata style din Riga fitted da skirt mai wrapper, gashi ta cogale kallabin Kayan tayi daurin ture Kaga tsiya, sai baqin gyale a kafada yayinda ta lullu6a fuskarta da baqin shade.

Tayi kyau harta gaji dukda bawani kwalliya tayiba.

Fuskar nan a tamke, kana ganinta kasan bazata bar kota yiniba bare ta kwana.

Yau saita gwadama A.A ko mema ake kiranshi wacece Saudart, yanzu bayada dammar blackmailing dinta tunda yariga ya turama dad kudaden.

"Wow! Sweetheart you look soo takeaway!"

Dan ta6e baki tayi sannan tace thanks ahankali.

"To kuyi maza kutafi please Saudart behave"

Bata amsaba tafice taje tasamu driver Wanda harya gaji da ji ranta.


Gaangaan!!

Yau akeyinta, sainaga ruwan comments zanyi typing, idan basu gamsheniba kuma zakuji shiru.


Ummin fasihu ce🧚‍♀


🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲



Wannan page din nakine ummin bilal da Duk members din AUREN KWANGILA NOVEL GROUP Amma fa banda yan le6el😏


Ngd da addu'o'inku agareni🙏
Allah yabar zumunci🤲



Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)




017






Cikin wani irin taku ta qarasa motar kafin tayi yunqurin budewa har driver din ya Budemata kofar baya aladabce harda dan russunawa.

Ta6e baki tayi sannan tashiga, rufewa yayi ya zagayo gaba yashiga.

Dad keta faman Daga mata hannu, yitayi kamar bata ganiba ahaka suka fice.

Ta6e baki Alhaji shamsu yayi, "kedai kika sani mutum arziqi na kiranshi yana guduwa"

Yaja tsaki yakoma ciki.




Shiru motar tayi, babu mai magana, tunda Saudart take bata ta6a shiga irin wannan motarba, watakau tahadu harta gaji, gashi kamar ba tafiya takeba don ko alamun tafiya bakaji.

Ga Sanyi mai hade da qamshi mai dadi Wanda ke saurin sa barci yakamaka idan Baka sababa.

Itama Saudart saida tayi dagaske don karta 6ingire, watakan idan kana cikin motar bakama sanin ana wani Abu waishi rana Awaje.

Haka taita kallon waje ta window hankali kwance, ganin ba hanyar A.A ENTERPRISES yabiba yasata muskutawa tace

"Mallam Wai ina zaka kaini ne haka?"

Cikin ladabi yace
"Kiyi haquri madam mun kusa zuwa"

Afusace tace "bashi na tambayekaba, where are you taking me to nace"

"Kiyi hqr madam mun kusa" yafada yana shan wata corner.

Masifa tashiga zazzaga mashi akan ya maidata inda ya daukota koya ajiyeta bata zuwa.

Shidai ko uffan beceba harta gaji tayi shiru.


A Gaban wani tangamemen gate ya tsaya yana horn.

Saida akayi scanning dinsu sannan gate din ya budu suka shiga.


Tun cikin motar tasaki baki tana kallon wajen.

Tunda take bata ta6a ganin qayattacen waje irin wannan ba, Waima ahakan tana cikine bata fitoba.

"Madam munzo, please come out" inji drivern da har yazagayo yabude mata.

Wani kallo ta watsa mashi Wanda bemasan tanayi ba saboda glass din daya kare idanunta.

"Are you serious? Nan inane ka kawoni?"

Kafin yasamu zarafin amsamata tajiyo muryar wani nacewa
"A'a? Harkun iso?"

Daga kai tayi ta kalleshi taga Ashe Wanda take ganine a office din A.A (sadeeq)

Cikin fara'a yadan qara Budemata murfin kofar yana cewa
"Bismillah gimbiya"

Cikin tsuke fuska tace "Wai inane nan? Kuma me nakeyi anan?"

"Yi hqr madam, wani dan shagalin nasarar da companynmu da kingin rassashi yasamu muka hada shine kema aka gayyaceki" yafada cikin fara'a.

Kamar tasake mgn saikuma tayi shiru.

"Please kiyi hqr kifito"

Kamar bazata fitoba sai can ta ziro kafarta a yangace tafito.

'Ya sallam!' Tayi exclaiming ganin zallar haduwa da wajen yayi.

Ga furranni ata koina.
Allah ya taimaketa akwai glass a idanunta da an lura da kauyancinta.

"Ma'am mu qarasa yana cikin waccan motar" inji sadeeq yana nuna wata dalleliyar mota fara qall

Bin inda ya nunamata tayi da kallo sannan ta kauda kai.

"Please ma'am Ku kadai ake jira a hall din"

Cikin tsantseni tace "shi bazai iya fitowa bane, am going nowhere" ta maida Kallonta kan wayar hannunta tana shafawa.

'Lallai ahe wannan tafishi ma girman kai' yafada cikin zuciyarshi.

"Ok bari na kirashi" saiya juya yanufi inda motar take.


Ashraf Dama tundazu su yake kallo, ganin sadeeq yataho shi kadai yasa ranshi qara 6aci.

Dama gashi famm yake saboda latti dasukayi gashi yanzu tana botsarewa, lallai saiya koyamata hankali.

Kwankwasa glass din motar yasashi sakin siririn tsaki yana kauda kai.

Budewa Sadeeq yayi yana cewa "to saika fito gimbiya dai taqi Qarasowa"

Banza yayi dashi ko kallo be isheshi ba.

"Ashraf?"

Wani kallo ya watsa mashi yasake dauke kai.

"Please Wai bakusan kun tara mutane bane? Haba jira babu dadi"

Nan ma shiru.

"Wohoho Ashraf for goodness sake dakai fa Nike"

Harara ya watsa mishi yana cewa "cancel the gathering"

"Me?! Are you serious?!" Yafada cikin Waro idanu

Harara yasake watsa mishi "you heard me ai"

"Haba Ashraf? Ka gama tara mutane kayi wasting din time dinsu sai kuma ka soke taruwar, wannan wane irin wulaqanci ne"

"Look sadeeq karfa ka manta matsayinka, the fact that kai abokinane bazai Baka damar mayar dani shashasha ba, am still your boss!" Yafada tsakankannin haqora cikin Fushi.

"Kayi hqr Ashraf Amma..."

"Just shut up! Tagama 6atamin lokaci sannan tace bazata qarasoba? Ita wacece? Na ta6a jiran mace? Kai shaidane ban ta6aba sai akanta saikuma tanemi rainamin hankali? Cancel the damn party kazo mutafi!"

Kallonshi kawai sadeeq keyi ganin dagaske fah yake nufin Ayi cancelling din partyn Bayan Duk manyan mutane aka tara, lallai aikau bazata sa6uba.

Kwantar dakai yayi yaita roqonshi harya yarda dakyar yafito.

Izuwa yanzu har biyar darabi tayi.

Saudart nacikin motar don bazata juri Tsayuwa ba, itama a 6angarenta aqule take, lallai wannan gayen dan wulaqanci ne, Dama sawa yayi akawota don ya shanyata.

Ta cikin motar ta hango fitowarshi, ta6e baki tayi tana kauda kai.

Sanye yake cikin farar suit qall, sai jar shirt dake ciki da Jan necktie irin dan qaraminnan, sai hanki ja daya dan leqo ta aljihun gaba.

Wow, gaskiya A.A haddadene👌 ba qaramin kyau shigar sukayi mashi ba.

Tare suka taho da Sadeeq dake Bayan Ashraf.

Suna isowa wajen dazasu bi su shiga ciki yaja ya tsaya hannaye zube cikin aljihu, fuska tamke ga shima uban baqin shade daya kwama.

Ganin haka yasa sadeeq qarasawa motar Saudart don tahowa da ita.

Saida tasake Jan aji sannan tafito itama sannan suka tako wajen Ashraf.

Shikau Sadeeq sai ayyana yadda dan zamansu zai kaya don ya lura dukansu yan jin Kaine.

Koda sukazo wajenshi ko gefenshi bata kallaba kamar yadda shima yayi kamar besan da itaba.

"Ina zuwa" inji Sadeeq yayi gaba don zuwa sanarda isowarsu.

Haka suka tsaya ko nuna alamun sunsan da zaman juna basuyiba.

Daga nesa idan ka hangesu saisun burgeka don dukkansu sun hadu ba karya ga kayansu daya kusan marching.
Ita jaa da baqi shi fari da jaa.


Yadda yabarsu haka ya tardasu.

"Please Ku qaraso"

Nanma rasa wanda zai fara takawa akayi

"Please Ku ake jira kuyi hqr" inji Sadeeq daya gaji da dramar su.

Nan Saudart taci girma tafara takawa sannan fa dan jinkan shima yatako.

"Please kubar tafiya aware kufa fiancée ne"

Babu Wanda ya tankamashi suka cigaba da tafiya.

Haka suka qarasa entrance din, DJ na hangosu ya saki wani kida mai dadi.

Take kallo yakoma kansu, kowa na yaba haduwarsu.

Tafi aka dauka hall din anatayi har suka qarasa wajen zamansu.

'Ashe surprise Sir A.A zaiyi Masu? Ashe da masoyiyarshi zaizo wannan party din' haka kowa yaita saqawa yayinda mafi yawan matan dake hall din Kishi ya cika musu zuciya.

Mutane sukayi tazura mazauninsu Bayan sun zauna suna tayasu Murnar nasarar d company dinsu yayi da kuma taya Murnar samun mata.

Sai a sannan Ashraf yayi danasanin daukota don shifa yayi hakanne don ya gwadamata koshi wanene dakuma yadda yakeda iko.

Hasken flashes din hotuna kawai ke haskemasu fuska.
Ashraf kamar koda yaushe fuskarshi a tamke itakau Saudart babu yabo babu fallasa idan kuma akayi congratulating dinta sai tadan saki murmushi.

Ji take kamar ta tashi ta ruga don sosai tajita ta takura.

Dakyar akasamu mutane suka koma suka zazzauna.

Nan m.c yahau jawabin abinda ya tarasu cikin harshen turanci.

Itadai Saudart kawai tana wajen ne Amma hankalinta Duk yayi gida, Jitake wama yasa ta yarda Tun farko da zywan?

Duk inda ka wurga idanu yan media ne Masu dauka wannan mostly sunfi daukar su Ashraf.

Ashraf kau abinne yaso juyemashi don ba haka yasoba.

So yayi yakawota don ta raina kanta kuma beta6a tunanin yan jarida zasu hallarci wajen ba.

Kawai yakawotane don taga matsayinshi dakuma ikonshi.


Bayan jawaben nan aka shiga ci dasha, kowa da zaune a tebyr dinshi yana dan ta6a wani Abu.

Hakan take awajensu Ashraf. Dukda babu mai cin komai cikinsu, kowa da abinda yasha mishi kai.

Sadeeq ne yaqaraso wajen dawasu yan jarida biyu.

"Sir, gawasu yan media zasuyima kai da sarauniyarka tambayoyi" inji Sadeeq aladabce Saidai deep down dariya yake mishi.

Takaici ya hana Ashraf cewa komai don sai yanzu yasan Sadeeq ne ya gayyato mashi yan jaridar nan.

"Sir wane irin farinciki kake ciki ayau?" Inji wani yana saita mic dinshi gabanshi

Shiru yayi kamar bazeyi mgnba saiya daure cikin muryarshi mai dadin amo yace
"Ina cikin farinciki sosai"

"Sir wannan ne karo na farko da akafara ganinka da mace, ko zaka iya gayamana matsayinta agareka?"

Inji wani nakusada nafarkon.

Nanma shiru,

"Lallai Sadeeq you are in hot soup" yafada cikin zuciyarshi

Can cikin murya qasa qasa yace
"She's my fiancée"

"Wow congratulations... Ma'am zaki iya fadamana farincikin dakike ciki?"

Suka maida akalar tambayar wajen Saudart.

Jimm tadanyi sannan itama ayangace tace
"Ina cikin farinciki sosai"

"Ma'am wani matsayine sir A.A ke dashi awajenki"

Murmushi tadan saki

"Kamar yadda yafada am he's fiancée"

"Wow.. Zaki iya fadamana farkon haduwarku?"

Woo! Nabani, tafada cikin zuciyarta

"Eh"

"Ok muna jinki ma'am"

"Mun fara haduwane a bakery dina" tafada kai tsaye

"Wane bakery kenan?" Inji dayan.

"Alhairi bakery"

"Omg, badai kece mai alhairi bread ba?" Inji dayan cikin mammaki.

"Yes nice" ta amsa cikin basarwa.

Ashraf na gefe takaici kamar yayi hauka.


"Me sir A.A yajeyi a bakeryn?"

Murmushin gefen baki tayi irin Wanda shima yakeyi.

"Me zaije yi kau? Yaje Isar da saqon zuciyarshi ne"

"Wow! Me hakan ke nufi?" Inji dayan sai setasu da camera ake.

Dukda tagaji da tambayoyin Amma burinta na quntatawa Ashraf yasa tace
"Ina nufin yazone donyayi fighting for his love"

"Wow amazing! Sir Ashraf hakane?" Inji dayan yana saita Ashraf da mic.

Jiyayi kamar ya nutse don kunya don Dama tunda suka fara hankalin kowa yadawo Kansu.

Babu damar musawa yayi murmushi yana kada kai.

"Sir idan hakane akwai inda kafara ganinta kenan harka fola Mata, inane kafara ganinta?"

Ca6, da ace ana ganin zuciya da kunga yadda zuciyar Ashraf ke tafarfasa.

"A cinema" yafada ahankali, dukda cikin Fushi yake hakan be nunaba a fuskarshi. Lallai wlh saita gane kurenta, shi take zubarma girma agaban jama'a? Wai har binta bakery ko ubanmi ma yayi?

"Wow gaskiya labarin haduwarku yayi dadi, ma'am da Sir A.A yazo wajenki da qoqon bararshi ya kikaji?"

Kutt.. Qoqon me? Inji Ashraf cikin zuciya.

Cikin basarwa Saudart tace "well as expected nayi mammakin hakan, ganin yanayin halinmu ba dayaba. At first naqi yarda da soyayyarshi gaskiya ce Amma ganin yadda yaketa zarya bakery dina Dama gidanmu yasani giving abun a second thought, ahankali ahankali nafara kulashi har yayi nasarar yaqar zuciyata da soyayyarshi" tafada murmushin mugunta fall fuskarta


Wohoho nan hall din ya rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinshi, Shidai Ashraf komawa yayi yayi balancing akan kujerar tareda lumshe idanu, zuciyarshi kamar ana hura wuta.

dakyar hall din yayi shiru sannan daya Daga cikin yan jardan yace "yanzu zaki iya fadamana wane matsayin yake dashi azuciyarki?"

Murmushi tadan saki a kunyace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login