Showing 165001 words to 168000 words out of 173829 words
bataci yasashi dagowa ya kalleta
"Why are you not eating?" Yafada yana kallonta
Kallonshi tayi fuska a kumbure saikuma ta juyamashi baya
Dan lekota yayi ta bayanta yace
"Menene?"
Matsawa tayi daga gefenshi takoma can dan nesa dashi tace
"Ni ka kyaleni"
Galala yayi yana kallonta yace
"Ni menayi kuma?"
"Oho? Bacewa kayi zaka samu wata ba? Saikaje kasamu" tafada idanunta nakawo
Shiru yayi na wani lokaci yana kallonta saikuma yafashe da Dariya sosai yana nunata
To dama mai neman kukane aka jefa da ledar kashi
Ganin hakan yasata 6ata fuska ta maida kanta tsakankanin gwiwa tafara hawaye
Da farko ya dauka wasa take amma jin sheshekar kamar ta gaske yasashi dago fuskar
Mammaki yakamashi ganin fuskar jage jage da hawaye
"Subhanallilah, wai dagaske kuka kike?"
Ture hannunshi tayi ta maida kanta bisa gwiwa tana cigaba da kukanta
Dariyar dake neman kufcemashi ya danne ya rungumota jikinshi yace
"Oh am so sorry, wlh bansan kinji haushi ba"
Fizge kanta tayi daga jikinshi tana cewa
"Leave me alone, kaje kasamu watan saime?" Tafada cikin muryar kuka
Riqe baki yayi saikuma yasake kamota ya maidata jikinshi yace
"Haba my princess, meyayi zafi? Kefa kikace bakiyi?"
Qara fizgewa tayi tace
"Ni yaushe nace hakan?"
Wara idanu yayi yace
"Kefa kikace bakya ra'ayi"
"Yanzu kuma nace inayi" tafada tana murguda mashi baki
Dariya yafashe da ita harda tafi yace
"Someone is jealous here oh"
Fadawa tayi jikinshi tana dukan qirjinshi tana kukan shagwa6a shikau sai Dariya yake
Ganin bazata bariba yasashi kamo hannayenta ya riqe yana qara rungumeta
"It ok..it ok, yanzu kin yarda zakiyi?"
Turo baki tayi ta qara sinne Kai ajikinshi
Dariya yayi ya dagota yayi cupping din fuskarta
"Uhmm?"
Saida ta harareshi sannan tace
"On one condition"
Dariya yayi yace
"Harda sharadi?"
Bata amsamashi ba sai hura hancin datake
"To inaji meye sharadin"
Sniffing tayi sannan tace
"Saika gayawa ummy sannan"
Dan kafeta da idanu yayi sannan yace
"Why?"
"Saboda yin shawara da nagaba dakai musanmman mahaifa yanada kyau domin sunfimu hangen nesa"
Sosai yaji dadin abinda tace sai cewa yayi
"Naga dai alamar sokike ki nuna kinfini son ummy, to ummin nan dai tawace naga alamu qwace kikeson yimin tuntuni, to kin makaro" yafada yana mata gwalo
"Kwace tun yaushe nayimaka? Kaidaine baka farga ba" tafada tana mashi hararar wasa
"Eh din kidau ummin dama ta isheni ni zan komawa Mamy" yafada shima yana hararta
"Oho dai, idan Mamy ce gaka gata"
"Jealousy kawai" yafada yana Dariya yayinda itakuma ta hade rai tacigaba dacin abincinta
Haka suka qare cin abincin cikin raha da tsokana sannan yatashi ya dauketa kamar Yar tsana ya haye daita sama...✍️
Ummin fasihu🧚🏻♀️
[12/13, 7:16 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
105
*WASHEGARI*
Hannun su sarqahe Dana juna suka fito suka nufi parking suna tafe suna hira qasa qasa suna dariya
Kallo daya zakayi musu kaga sunyi bala'in dacewa dajuna
Sanye yake cikin buggagiyar shadda dark blue mai baqin aiki agaban rigar sai takalmi baqaqe da baqar agogon fata dake sanye a hannunshi na dama sai baqar hula zannah bukar dake riqe a hannun saudart wanda ke sanye da Atamfa dinkin zane simple da half gown wanda ya kawomata har gwiwa tayi daurin Zahra buhari, sosai atamfar tahau jikinta kasancewar black and pink colour ce hakan yasa ta haskata sosai
Koda suka Isa jikin motar dazai hau saida suka tsaya nanma suna cigaba da firarsu wadda da alama tayimasu dadi don sai kwasar dariya suke
Kallon wristwatch din hannunshi yayi ya wara idanu
"Kingani ko? Ni bani hulata idan na biyemiki saina rasa sallar juma'ar gabadaya"
Dan turo baki tayi sannan ta doramashi hular akai tana gyarawa saida tagama sannan tadan Jada baya tana kallonshi
Dan wara hannu yayi yana dan jujjuya yace
"To ya?"
Dariya tayi tahada yatsarta manuniya da babban👌tace
"Fabulous!"
Murmushi yayi yayi mata nuni datazo tahowa tayi da sauri suka rungumi juna sannan yasakarmata kiss a kumatu ya bude kofar motar yashiga yana cewa
"Saina dawo, zan dawo maki da babban baqo"
"To Allah ya maidoku lfy" tafada tana tura murfin kofar yarufe sannan taja dabaya tana dagamashi hannu harya fice daga gidan
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tajuya takoma ciki
****
A parking space motar tayi parking sannan aka bude murafen motar ta kowane gefe suka fito gabadaya
Rufe kofar 6angarenshi ashraf yayi sannan ya zagayo wajen sadeeq dashima yasha manyan kayanshi milk saidai kanshi babu hula sai yar sumanshi daya Tara dake walqiya saboda gyara
Shima rufe murfin kofar side dinshi yayi yana cefa wayarshi a aljihu
"Ya? Muje ko?" Inji ashraf yana danna ma motar remote
Harararshi sadeeq yayi yace
"Ko baka fadaba, mtcheew sai wani rawar kafa yake anzo gidanshi",yaqarashe yana yatsina
Dariya ashraf yayi yace
"Ba doleba, idan haqori banzane kaza ma tayi mana"
"Saka ranka a ruwan sanyi, me kakeci nabaka na pouring, wlh albarkacin madam kaci harna zo gidannan, wlh badon itaba ba abinda zaisa naqara taka cikin gidannan tunda nalura kai bakasan arziqi ba, nan nan kazo fuska sha6e2 da hawaye da majina an kwace maka mata, nayi ruwa nayi tsaki wajen nemomaka hanyar dawowar matarka amma don rashin mutunci saidai inji labarin tarewarta abakin wani"
Ashraf daketa dariya tunda yafara magana yace
"To Ai banga amfanin gayamaka bane, amfaninka yaqare tun lokacin dakayi ruwa kayi tsakin wajen nemo mafitan, kaga meye nawani gayamaka?"
Saboda quluwa sadeeq beqara cewa komaiba don yasan ranshi ne kawai zai 6aci
Knocking ashraf yayi a kofar sannan ya murda kofar yasa hannu daya ya tare sadeeq dake baya ya zuro kai yana leqen falon
Shidai sadeeq tsayawa yayi yana kallon ikon Allah harya gama leqe leqenshi kamar tsohon 6arawo sannan ya dago ya juyo yace
"Yauwa mushiga bata ciki da alamu tana sama"
Cije lip din qasa sadeeq yayi yana kada kai yana ayyana irin wulaqancin dazaiyiwa ashraf shima idan yayi aure sannan yabi bayanshi suka shiga cikin falon dake tashin qamshin turaren wuta mai dadin qamshi
Direct sama ashraf yawuce yana kwala kiran 'princess'
Shidai sadeeq samun kujera yayi ya zauna yana ayyana da zuciyarshi marar qwari ce da tuni ta buga saboda wulaqancin ashraf amma bakomai lokaci ne kuma wlh saiya gane kurenshi
Kwafa yayi yana girgiza kaffafunshi daya hade waje daya yanabin falon da tsarinshi yaburgeshi da kallo
Saudart dataji kiran ashraf ta taso da sauri ta bude kofar sukaci karo dashi shima yasawo kai
Jada baya sukayi tare suna Sosa goshi suna tura baki
"Wannan kai naki masha Allah kamar na kwakwa? Aisaiki fasa nau" yafada yana harararta
6ata fuska tayi tace
"Nice mai kan kwakwa?"
Dariya yayi yayi saurin riqo hannunta ganin tajuya cikin fushi
"A'a.. Haba ina? Bake bace"
Juyowa tayi ta kalleshi tana tura baki tace
"To waye?"
"Na qasa ne" yabata amsa
Dan waro idanu tayi tace
"Yana qasa? Waye please"
"Guess"
"Sadeeq?"
Dunqule hannu yayi yaimata jinjina yace
"Kwaret! Yanachan yana fama da ciwon zuciya" yaqarashe yana dariya sosai
Wara idanu tayi atsorace tace
"Ciwon zuciya kuma?"
Dariya yasake fashewa dashi yace
"Eh mana, badai shi dan rainin wayau ba? Tundazu naketa hadamashi zafi nasan qiris zuciyarshi ta buga" yasake fashewa da dariya
Tsayawa tayi tana kallon yadda yake dariya, ita wlh idan yayi wani abin saitaga kamar ba A.A din data Sani bane don bata ta6a tunanin hakan wannan side din nashi yakeba, ita idan yayi wani abun saitaga kamar baby ce
Huremata idanuwa yayi yace
"Kallon fa?"
Lumshesu tayi tana murmushi tace
"Muje kabar bawan Allah qasa shi kadai"
Dariya yayi sannan yace
"Hmm bawan kanya dai, kisa hijab don bamai kallonmin mata"
Wara idanu tayi tace
"Hijab kuma? Ina laifin gyale"
Hade rai yayi yana kallonta bece komaiba hakan yasata sauke Ajiyar zuciya tace
"To naji karka hanani barci dawannan fuskar taga da daddare"
Murmushi yayi while itakuma tazaro wata farar hijab iya gwiwa tasa sannan ya kama hannunta suka fito.
Sadeeq na zaune yana typing din wayarshi yaji motsin su hakan yasashi dagowa ya kallosu
Ganin yadago yasa saudart qoqarin zame hannunta daga cikin nashi amma yaqi bata damar hakan dan qara riqewa yayi gamm
Janye idanunshi yayi shima yana murmushi ya jefa wayarshi a aljihun gaba acikin zuciyarshi yana gulmar dacewarsu
"Allah yaja da daran gimbiyarmu kuma madam dinmu Mrs A... au Miss saudart" yafada yana dan dafe baki
Kunya saudart taji don tasan tunamata yayi hakan yasata sunkuyar dakai tana dariya sannan ta zauna a kujera dake facing din nata shima ashraf ya zauna gefenta
"Ina wuni" tafada a kunyace don harga allah kunyarshi takeji sosai dubada rashin m datayi mashi abaya
"Lfy ma'am, kuma shikenan ko ànememu kunjimu shiru ko ajikinku"
Dariya tadanyi tace
"Aikau muna cigiyarku, kullum saina yi cigiyarka awajenshi" tafada tana Satan kallon ashraf dake wani shan qamshi shi adole ga mai mata
Kallonshi shima sadeeq yayi yace
"Wa? Wannan? Ai dabaki faraba don nima kaina kwanan nan ba gane kanshi ba nake, shikenan kuma daga tarewa sai kulle? Dan Allah ataimaka asakar mana shi yadawo company don wlh muna buqatar shi"
Kunya sosai taji hakan yasata dan murmusawa sannan ta miqe tana cewa
"Ina zuwa"
Saida tawuce sannan ashraf ya kalli sadeeq yace
"Kai wayace maka ana fira da matata"
Wani kallon up & down sadeeq yayi mashi ya watsar ya zaro wayarshi yacigaba da abinda yake dazu
Kwafa ashraf yayi sannan ya miqe ya marama saudart dake kitchen baya
Can saigasu sun fito tare shi dauke da warmers itakuma eating utensils
A falon suka kawo kamar yadda ashraf ta buqata don talura yafison cin abinci a qasa
Saida suka ajiye sannan takoma takawo local juice data hada da ruwa ta ajiye.
Tana shirin serving dinsu ashraf ya dakatar daita yace ta tafi kawai zasu qarasa dakansu
Dik abunda suke Shidai sadeeq na zaune yana kallonsu ta qasan ido yana mammakin yadda cikin kankanin lokaci ashraf yashawo kan saudart don idan baka saniba bazaka ta6a cewa ada basa shiri ba
Ganin tawuce yasashi mayar da wayarshi a aljihu ya sauko qasa yafara bubbude kulolin
Ashraf nata mashi shaqiyanci amma ko kallo be isheshi ba
Haka suka zauna suka kwashi girki sadeeq sai santi yake yana cewa shima idan yayi aure irin wannan za'a dinga yimashi shikau ashraf inbanda dariya babu abinda yakemashi
Saida sukayi nak sannan suka sha ruwa suka koma suka zauna suna maida yadda akayi wanda yawanci labarin company ne da yadda abubbuwa ke tafiya
Sai wajajen la'asar sannan sukayi haramar tafiya, ashraf yaje ya kirawota Don suyi bankwana
Godiya sosai sadeeq yayiwa saudart yana yabon dadin abincinta yakuma dora da dan allah asakar masu boss yadawo aiki
Itadai dariya kawai ne nata sannan sukayi bankwana suka fita tareda ashraf
Dawowa tayi ta tattare kwanikan anan taci karo da bundle din yana #500 qasan tray
Ko ba'a fadaba tasan sadeeq ne ya ajiyesu
Kwashe kayan tayi ta dauke kudaden ta gyara wajen fess kamar ba'ayi komai ba awajen sannan ta haye sama donyin sallah
Su ashraf kau yawonsu suka wuce bayan sunyi sallar la'asar awani massalaci, sai wajajen magrib kana suka rabu
Direct gidan ummy yanufa inda acan yayi magrib dinshi da isha'i
Sai bayan yadawo yasami ummy har daki da maganar cigaba da aikin saudart a company dinshi
Ga mammakin shi sai yaji ta amince farat daya damasu addu'ar Allah yasa hakan shiyafi alhairi
Sosai yaji dadin hakan ya amsa da ameen suka cigaba da firarsu kafin yayimata sallama yawuce gida
Agida cike da farinciki yafadama saudart amsar ummy, itama taji dadi sosai hakan yasa itama tashiga murna
Saida sukaci abinci suka haye sama sannan ta gwadawa ashraf kudin dazu
Cewa yayi ta ajiye kawai tunda kyautarta ce
Godiya tayimashi sannan tace yayi extending din godiyarta ga sadeeq
Washegari saturday da marece suka wuce shopping din kayan aikin saudart
Itadai binshi kawai tayi amma zuciyarta fall mammakin wane irin kayan aiki kuma?
Saida sukaje tagane abinda yake nufi
Gown gowns kala kala ya jiddarmata kowacce da irin kalar zumbuleliyar hijabinta sai saffofin qafa tuli guda
Itadai binshi kawai take da basket din turawa mammaki ma ya hanata magana
Saida yagama sannan ya biya aka saka a ledoji aka jibgemasu a booth
Akan hanyar komawarsu take tambayarshi gameda kayan nan yake fadamata natane wanda zata dinga sakawa idan zasu office
Mammaki yakamata ganin ina zata da wadannan jibga jibgan kayan ko zafi baya tunanin ya kasheta
Akan hakan saida sukaso samun sa6ani don ta nuna ita bazata iyaba shikuma yace bazai bari tafita ba kowane Tom and jerry na ganemashi mata
Ranar haka suka kwanta kowa rai a 6ace
Washegari ma haka suka tashi amma ba wanda yanuna a fuska don lafiya lau suke mu'amalantar juna kamar babu abinda yafaru
Fadan nasu bewani dadeba suka shirya don bayan zuhr suna zaune sunacin abincin rana ashraf yatado maganar inda yake nusar daita dalilin dayasa yayi hakan, kishin matarshi yake kuma amatsayin ta na matarshi kamata yayi ta tayashi kishin kanta
Sai a sannan ta sauko takuma amince don tayi nazari cewa sai da so ake kishi kuma abin alfaharinki ne mijinki ya nuna kishi akan wata shiga taki don kar wani yagani har ya yaba
Nan take sukaba juna haquri suka koma yadda suke
Anan yake gayamata gobe insha Allah zasu fara zuwa companyn
Da daddare bayan isha'i yace ta shirya sufita
Cikin murna tayi hakan suka fice
Ga mammakinta dakuma farincikinta gidan Mamy sukaje
Taji dadin zuwa gidan sosai don sunsha hira da qannenta damasu Mamy bakidaya inda tayita mammakin shaquwar da qannenta sukayi da ashraf yadda kasan dan gida
Anan suke gayamasu gobe insha allah zasu fara zuwa aikin
Dayake dama sunada masaniya akai sai suka bisu da addu'a da fatan alhairi
Daga nan sai suka wuce gidan daddy
Zokuga murna wajen saudart yadda kukasan ta shekara bata ganshi ba ko jin muryarshi
Shagwa6a Kala Kala taita yamashi suna mata dariya ashraf na qara jingina soyayyar dake tsakaninsu don yadda tasake haka da daddy batayi hakaba da Mamy
Shima fatan alhairi yaimasu sadda suka fadamashi dakuma fatan nasara
Sundan jima a gidan sannan suka fito daddy ya rakosu har mota yana masu bankwana suka tafi
Direct bakery dinta suka nufa
Ganin hakan yasashi danneshi cikin tsantsar farinciki don yau ya faranta mata bako kadanba
Haka suka fito suka shiga bakery din wanda wannan shine karon farko da ashraf zai shiga cikinshi
Sosai wajen da tsarin wajen ya burgeshi
Haka sukaita gaisawa da ma'aikatan wajen masu aikin dare wanda bakinsu har kunne ganin madam dinsu da mijinta sunkawo musu ziyara sai rawar jiki suke wajen welcoming dinsu
Saida suka zazzagaya bakery din sosai sannan suka yada zango a office dinta inda cikin qanqanin lokaci aka cikamasu gaba da kayan snacks da kayan sanyi kala kala
Sun jima office din suna ciye ciye da fira sannan suka tashi da niyyar tafiya
Basu suka dawo gidaba sai wajajen 12, kowannensu agajiye yake liqis, haka suka shige ciki suna hada hanya kamar yan maye...✍️
Ummin fasihu🧚🏻♀️
[12/14, 9:43 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
106
Washegari tunda suka tashi sallar asuba basu komaba, tare suka tsaftace gidan sannan suka fada kitchen suka samarma Kansu abinda zasu karya dashi
Saida sukayi wanka suka shirya tsab sannan suka karya cikeda nishadi da raha
08:15am suka fito daga gidan ashraf sanye da brown American suit mai farar inner sai dan necktie dinshi daya matse wuya dashi takalmunshi brown hakama wristwatch
Itakuma saudart sanye take cikin English gown peach colour wanda yadan matseta daga sama ya bude daga kugu zuwa qasa, hannun rigar net ne dogo har zuwa wuyan hannu, anma rigar kwalliya da manyan tuttoci pink a gabanta saita dora zumbuleliyar hijabinta pink colour wanda badon tasa heels ba da saita ja qasa kafadarta rataye da pink side bag dayan hannunta riqe da faskekiyar wayarta
Tare suka jero suna tafe suna hira gwanin sha'awa
"Wa zaiyi driving?" Inji ashraf
"Kai mana, ni da wadannan zumbula zumbulan kayan zanji ko da driving?"
"A'a munriga mun ajiye deal ke zaki kaimu ni na maidomu"
"Uhn uhn? Allah nidai bana iya driving da wadannan kayan" tafada a shagwa6e tana folding hannayenta a qirji
"To muyi deal, wanda yafara kaiwa ga motar shizai zauna a 6angaren mai zaman..."
Be idaba yaga ta ruga cikin dan gudunta ta nufi motar, ganin hakan yasashi saurin maramata baya saidai ina? Harta rigashi qarasawa
Dariya ta fashe dashi ganin yadda ya 6ata fuska kamar zaiyi kuka
Yi yayi kamar zaiyi mata rankwashi tayi saurin noqewa tana karewa da hannu
"If I knock you ehn? Wannan ojoro ne wlh baki bari na ida magana ba kika ruga" yafada yana harararta
Fiddo harshenta tayi tana talemashi fuska tace
"Eh din, c'mon zokayi driving dina"
Kwafa yayi yana jinjina kai sannan ta zagaya bangaren driver ya danna remote ya bude itama ta bude sannan suka shiga
Rufo motar sukayi atare sannan yayi starting din motar yayi reverse suka fice daga gidan
Tafiyar minti sha biyar sukayi suka isa company din
Tun acikin motar take bin company din da kallo tana tuna wasu abubbuwa dasuka shude
Jin shiru be motsaba bare ya fita yasata kallonshi taga shima ita yake kallo yawani 6ata rai
"Yadai?" Tafada tana daga gira
"Mtcheew jinake wama ya hanani hadowa da nikab? yanzu haka zamu fita aita kallon min ke" yaqarashe yana so6are baki
Tsaya tayi kawai tana kallonshi, lallai tana da aiki yau Allah ya hadata da murdadden mutum, dama yasan yanada wannan kishin ya buqaci tayi aikin
"Kinyi shiru" yafada yana kallonta
"To me zance? Sokake ka maidani masquerade koina arufe abun tsoro kamar ninja?"
Tsaki yaja wanda ta lura habit dinshi ne yace
"Ni wlh sainaga ma kamar wannan shigar tafi yimiki kyau"
Ajiyar zuciya kawai tayi bata ce komaiba don itakam batada tacewa kuma
Sundan dade ahakan sannan yaja tsaki ya bude motar yafita, binshi da kallo tayi tacikin motar harya zagayo side dinta ya budemata
Murmushi tadanyi ganin yadda yake ta wani hura hanci ta dauki jakkarta ta ziro qaffafunta ta sauko ya maida yarufe
Kamo hannunta yayi ya riqe tightly kamar wanda akace za'a kwacemawa suka nufi cikin company din
Duk wanda yayi musu kallo daya saiya sake kallonsu don they looked soo breathtaking
Haka suke wuce ma'aikata suna kaimasu gaisuwa saudart na dagamusu hannu tana dan murmushi while gogan ko kallonsu beyi yawani hada rai kamar hadari
Ahaka suka shiga main door din company, maimakon su shiga da daddaya kamar yadda ya kamata sai yajawo hannunta suka shiga tare ganin tana neman tsayawa
Haka kofar takoma tarufe tasake budewa daga ciki sannan sukayi stepping out
Yadda wurin yake a sadda tasanshi haka yake so silent and cool ma'aikata kowa a post dinshi sai masu kai kawo jefi jefi, wurin sai tashin qamshi mai hade da sanyin dadi yake
Basu tsaya wata wataba suka nufi lifter inda duk inda suka gifta sai ma'aikata sun kwashi gaisuwa wanda saudart ce kadai mai amsawa itama ta hanyar murmushi
Direct private lifter dinshi suka fita wanda shikadai ke shiga ta cikinshi, saikau sadeeq idan takama
Daddana code yayi kofar ta bude sannan suka shiga
Satar kallonshi tayi suna atsaye a elevator din suka hada ido kasancewar shima ita yake kallo
Yi yayi kamar zai bangajeta yana cewa
"Naa.... Amebo kawai"
Dariya tayi tace
"Amebos dai, kaima Ai kallona kake"
Dan budemata idanuwanshi yayi yace
"Ni kike cewa haka? Kin manta ni boss dinki ne?"
Daga gira tayi saikuma ta juya idanu🙄 tace
"Boss indeed"
Hade face yayi yace
"To bani haquri"
Kallonshi tayi tana yatsina sannan tayimashi puppy face🥴
Wara idanu yayi yace
"Ni din"
Murguda baki tayi tace
"Eh din😏"
Kamo hannunta daya yayi ya jawota jikinshi yace
"Sake yin abinda kikayi yanzu"
Qoqarin kwace kanta tayi tana turo baki
Dama abinda yakeso