Showing 51001 words to 54000 words out of 173829 words
nuna batamasan da wanzuwarshi ba.
Ajiye mug din coffee daketa faman tururi agabanshi ya katsemashi tunani.
Dagowa yayi yana kallonta qasa qasa.
"Sugar or honey?" Ta tambayeshi batareda ta kalleshi ba.
Banza yayi da ita tareda cigaba da rubutunshi.
Bata sake tambayarshiba ta dauki sugar cube biyu tasaka mashi ta jujjuya sannan ta maida sugarn da zuman ma'ajinsu tayi hanyar fita.
"Stop!" Ta dakatar daita da hakan.
Cak ta tsaya batareda ta juyoba.
"Come back here" yafada still hankalinshi nakan rubutunshi
Babu musu tadawo ta tsaya gabanshi not saying anything
"Throw the coffee away" yafada batareda ya dagoba.
Jimm tadanyi sannan ta dauki mug din tawuce toilet ta juye a sink ta dauraye mug din tadawo ta kifa, harta kusan kaiwa kofa taji yace
"Make another one"
Wani Abu taji ya zo daidai maqoshinta ya tsaya yaqi wucewa.
Me wannan gayen ke nufi da itane? Ta hadamashi yasata zubarwa kuma yace ta hada wani? Me yakeso daita ne?
'He want you angry'_wata zuciyar ta rada mata.
'Then he should hug transformer' tafadawa zuciyar
Juyowa tayi batareda nuna dumuwar komaiba a zahiri amma a badini tafasa take, kai tama fara kamu, jitake kamar ta Dora hannu aka taita ihu.
Haka takoma tasake hado wani coffee din, wannan karon honey tasa teaspoon daya takawo mashi.
Yanzunma be tashi yimata magana ba saida takusan kofa sannan yace ta zubar.
Gani yake abin nata gaba gaba yakeci, wato she can't ask twice? Lallai
Sake sata hada wani yayi, tahada again this time around sugar tasa saida ta ajiye yasake sata zubarwa.
He want to show her ya isa and she must follow his instructions a matsayinshi na boss dinta.
Itakuma a 6angarenta she know exactly abinda yake nufi amma ta nuna batasaniba, her ego won't let her ask again.
Haka taita zaryar hadawa tana zubarwa, sosai zuciyarta ke suya kawai daurewa take ga maqoshinta har wani yaji yaji yakeyi amma taurin kai ya hanata surrender
Ahakan sadeeq yashigo don ajiye wani file sannan ya wuce masjid.
"Throw it away" yasake cewa batareda ya dagoba
Itama bata kalleshi ba tashiga toilet tadawo da empty mug.
Da mammaki sadeeq yatsaya yana kallonsu cikin son fahimtar meke faruwa.
"Make another one" yasake umartarta.
Babu musu tasake hada wani takawo ta ajiye.
"Throw it away"
"What?" Inji sadeeq cikin tsananin mammaki
Wani kallo Ashraf ya wurgamashi yana kauda kai.
Itakau saudart bata tsaya sauraron su ba tawuce toilet din.
"Ashraf meye haka?"
Banza yayi dashi.
"Look Ashraf, da baban wannan yarinyar kake da case bada itaba, why zaka dinga wahalar daita? Plus almubazzarancin dakake, kasan wani nacan ba Neman Rabin wannan vesamuba amma kai kesawa a zubar?"
Nanma banza yayi dashi, zai sake magana tafito riqeda mug din
"Ermm.. You can go please" inji sadeeq yana kallonta.
Batace komaiba ta kifa mug din tawuce zuciyarta kamar tayi bindiga.
Saida tafita sannan sadeeq yasake cewa
"A.A kaji tsoron Allah, sbd kaga mutum na qarqashinka zaka dinga zaluntarshi"
"Dakata mallam! I have the right din sakata ko hanata, am her boss ok?! Inada right to do anything ok?! Don haka karka sake questioning dina, muddin zata cigaba dayimin girman kai to bataga komaiba ma, mtcheew!"
Ya tashi yanufi toilet kamar zai tashi sama.
Binshi da kallo yayi harya shige sannan ya ta6e baki yad'an daga murya yace
"To zuciyatu, karka manta munada meeting bayan asr, idan kuma kaga dama cancel it, ruwanka" ya fice
Tsaki yaja cikin toilet din yanufi sink din, abinda yagani yasashi tsayawa yana kallo cikin mammaki.
Coffee ne ciki wani bowl yawuce rabi, kenan ba zubarwa ba take? Ya tambayi kanshi.
Wata takarda yagani qarqashin bowl din tadan leqo.
Dagawa yayi yazarota ta duba yaga an rubuta *ALLAH YA HANA*
Wani Abu yaji har cikin zuciyarshi Wanda be ita cewa ga yadda abun yake.
Tsaki yaja ya cimimiye takardar ya yadda ya dauro alwala yafito daukeda bowl din ya juye coffee din cikin flask dake office din da niyyar zaibayardashi kyauta.
Itakau tana fita office dinta tawuce sannan direct tanufi toilet dagudu tana toshe bakinta saboda kukan dake Neman kufce mata.
Sosai take kuka jikinta har wani rawa rawa yake, jitake ta tsani komai a rayuwarnan, rayuwar kwata kwata ta daina yimata dadi, she can't believe ita ake wulaqantawa haka, dama ance idan ka hau motar kwadayi zata ajiyeka a tashar wulaqanci, and this is all daddy's fault, koma me akayimata shi yaja mata, son kanshi da kwadayin shi yaja mata.
Saida taci kukanta ta qoshi sannan ta daura alwala tafito ta gabatarda asr.
Tana zaune bayan tagama sallar taji ringing din landline, kamar bazata tashiba saikuma ta tashi taje ta daga.
"Miss saudart hope baki manta da meeting din ba?" Inji sadeeq daga dayan bangaren
"Yes" ta amsa a gajarce.
"Ok it's time" yafada sannan ya katse kiran.
Gyara fuskarta tayi yakoma normal sannan ta fita.
Yanzu ma alhamdullilah the meeting is successful and saudart is becoming more popular, tana wani baiwa na shiga rai farat daya don haka nan danan tasiye zuciyar mutane dayawa.
Sosai suke yabonta don wasu saida suka magantu suna cema Ashraf wannan tafi wancan don Helen babu abinda ta iya sai shegen iyayi, a maqe murya ana rangwada , gata kullum a tsuke kuma irin matan nanne masu ga6a ga6an jiki, shiyasa wani sa'in idan tasa wasu kayan maimakon ta burge saima tazama abun kallo.
6:30pm tabar office din kamar yadda yafada.
Yauma haka tadawo agajiye saida ta kora da maganin ciwon jiki.
A ataqaice dai haka saudart taita fama, mugunta kala kala A.A kemata, duk yadda zai 6atamata rai saiya yi, haka kawai zai sata unnecessary Abu daga qarshe yasata yagewa ko lallatawa da kanta, hakan ba qaramin 6atamata rai yakeba hakannan take daurewa don shima ta gumamashi.
Sai yanzu tagane dalilin dayasa baby ke kiranshi mugu don yaci sunan kuwa, don kusan kullum saita la6e toilet tasha kukanta.
A bangaren daddy kuwa yashiga damuwa sosai, tun lokacin databar office dinshi yashiga damuwa, yasan be kyauta mataba Sam, yasan yaso kanshi dayawa, rabon daya ganta kosuyi waya tun ranar, ita bata kiraba shikuma kunya ta hanashi kira.
Addadafe ranakun satin suka wuce aka shiga weekend.
Sai a lokacin tasamu damar leqa bakery dinta da ice cream joint. Kuma babu laifi Allah yasamata albarka a harkar don tana samu sosai.
Ranar lahadi kuwa qannenta sukazo suka yimata yini, sosai taji dadin zuwansu don sun debemata kewa sosai, basu suka koma gidaba sai magrib bayan ta cikasu da gift sosai.
Suna tafiya itama ta hayewarta sama don batason ganinshi, rabonta dashi tun ranar Friday a office kuma batason ganinshi din sai goben shima don yazama dolene don yanzu tsanarshi qara farashi take kowacce daqiqa mai tafiya...✍
Sorry babu yawa, banda chaji🙏
Zanmaku another page da anjima insha Allah
Ummin fasihu ce🧚♀
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
044
MONDAY
jiki a sanyaye take shiri.tana tunanin ya kuma haduwarsu ta yau zata kasance.
Idan akwai abinda tafi tsana yanzu to bewuce ganin koda wulginshine ba, gani take kamar kullum qaramata tsanarshi ake, tasan yauma dakyar idan bazai sata kukaba.
Qarfe 8:00am daidai yayimata a office, tunda kuma tashigo tashiga busy
Abu guda dazai burgeka gameda ita shine duk tsanarshi da aikin datake hakan be hanata yin aikinta tsakani da Allah, she's so hardworking shima shaidane.
Be shigowa company din ba sai wajajen 9:00am, kamar kullum bata nuna taganshi ba harya shige office.
Can taji landline dinta na ringing, batareda ta dauke kai daga abinda takeyi ba ta daga wayar ta kara a kunne.
"Come" taji ance aka katse kiran.
Bin wayar tayi da kallo sannan ta saki tsaki ta ajiye ta tashi
Kamar dai yadda tasaba knocking uku tayi bata jira amsaba tashiga
"Good morning" be amsata ba yace
"Have a seat" batareda ya kalleta ba.
Jan kujerar gaban table dinshi tayi ta zauna.
Shiru yadan ratsa office din nawani lokaci kanshi kasa yana yan rubuce rubuce kafin ya dago ya kalleta.
Sanye take da dakkakiyar shadda dark purple sai farin gyalen data yafa stylishly fuskar kamar kullum babu tarkacen makeup. Sosai tayi kyau in her own way.
Balancing yayi sosai saman kujerar yana dan jujjuyawa yana kallonta.
Kamar mai ciwon baki yace
"Duk sadda nashigo office you should follow me kiji ko akwai magana basai na kiraki ba, ok?"
"Ok" tafada tana ta6e baki cikin zuciyarta
"Good, now take a look" yafada yana miqamata wata takarda yana kafeta da mayun idanunshi
Babu musu ta amsa tana dubawa
"It's a business trip" yafada yana kallonta Itakuma tana kallon takardar
"Tafiya ce mai matuqar muhinmmanci Wanda dole tafiyar saidake tunda you're my secretary, but am not sure of going with you don nasan akwai wata manufarki na aiki anan, tayaya zan yadda dake?" Yafada yana kallonta.
Ta6e baki tayi tana daga kafadu
"Then ka nemi wani, don't care"
"Hmm haka kike cewa amma ni da ke munsan yo do care"
Batace komai ba don izuwa yanzu gani take yawane musayar magana dashi, she so much despise him da ko magana bataso ya hadasu.
Ajiye takardar tayi ta harde hannu a qirji.
"Dake zani babu Wanda zan chanza so maintain"
Nan ma banza tayi dashi taba iska ajiyar shi
"Tafiya zamuyi qasar Spain, akwai wani contract dazamuyi signing da wani shararren company Wanda zaijama company dinnan cigaba, well meyasa nake ma fada maki, is not as if cigaban mu kikeso ba" yafada yana yatsina.
Nanma ta6e baki tayi without saying a word
"Wednesday zamuyi tafiyar, jibi kenan, nabaki hutun gobe saboda shirye shiryen tafiyar, flight din12:00pm zamubi, your visa and everything Will be ready by tomorrow, don't forget 12:00 flight zamubi" yafada bossily
"Ok" ta amsa absentmindedly
"Coffee" yafada yana sake jingina da kujerarshi
Babu musu ta tashi ta hadamashi coffee din don yanzu kullum saita hadamashi.
Be sake cin arziqin tambayarshi sugar yakeso ko zumaba, duk wadda taga dama shi take samashi shima beyin complain haka yake amsa.
Tana gamawa ta ajiye mashi tafice.
Koda takoma office tunani taitayi, business trip? Spain? What has dad got her into? Me zatacewa mamy akan tafiyar? Kullum suna waya dolene idan suka tafi zata kira taji baya shiga kuma dole idan sun isa can ta kirata da foreign number.
Daddy?
Tunaninshi ne yafadomata a rai, rabonta dashi tun ranar databar office dinshi, sati guda ciff kenan.
Wayarta ta janyo tashiga contact ta dannama number shi kira.
Harta gama ringing ta katse ba'a dagaba, taqara kira nanma shiru hakan yasata turamashi gajeren SMS
*good morning dad, fatan kana lfy, kasaka mu cikin addu'a jibi insha Allah zamu Spain*
Tana aikawa ta kashe wayar takoma ta jingina da bayan kujerar tana lumshe ido.
Dad na ganin kiranta amma yakasa dagawa, kunyartar yakeji kamar me?
Jin txt yashigo yasashi saurin dubawa.
Jikinshi ne yayi sanyi bayan ya gama karantawa.
He missed his dear daughter badly, kusan koda yaushe saiya dauki waya zai bugomata amma saiya rasa me zece mata sbd yasan he's not a good father to her, kullum burinta ta faranta mashi, tana mashi biyyaya daidai gwargwado amma yasaka mata da wannan amma he's regretting sosai.
Kwana biyun nan dayayi beji muryarta ba jiyake kamar yayi shekaru bejitaba.
Sosai yake nadaman abinda yayi, yasan ba qaramin zubda mata da mutunci yayiba Wanda shi a lokacin duk beyi tunanin hakan ba kawai shi hangenshi me zai qaru dashi be tunanin me zai ragu dashi.
Danna number ta yayi ya kira amma switch off, sake kira yayi nanma haka, Qin haqura yayi yaita kira dan sosai yakeson jin muryarta, jiyake dolene ya nemi yafiyarta kuma ya warware komai.
Bata kunna wayartaba har takoma gida.
Saida tagama komai na aladarta ta haye gado sannan tajawo wayarta ta kunna.
Massages ne sukaita shigowa babu qaqqautawa dukna daddy.
Tsayawa tayi suka gama shigowa sannan tafara budewa, na farkon taga ansa
*shalele na...am sorry*
Na biyun kuma akasa
*I know am not a good father, am ashame of myself, will you find a place in your heart and forgive your dad?*
Jikinta ne yayi sanyi, a sanyaye ta bude na ukun
*please switch on your phone.. Please*
Zata bude na hudun kiranshi yashigo wayar
A sanyaye ta daga ta kara a kunne tayi shiru
"Shalele?.."
Kamar yace fara kawai saita fara hawaye.
"Shalele am sorry, am soo sorry"
"Daddy me nayi maka da tsanani haka harka shareni na tsawon one week?" Tafada cikin kuka
"Ai nayimaka abinda kakeso ko? Then why did you abandon me?"
"Shalele kiyi hqr.."
"No dad, kai zan ba hqr, wataqila nayimaka wani abun ne, am sorry" tafada cikin matsanancin kuka zuciyarta na zafi
"Shalele please kiyi shiru,stop crying kokuma nima nayi, am soo sorry, am selfish, saboda sonkai irin nawa na zubda maki mutunci ba zubdama kaina, am sorry kinji? Daga yau no more zuwa aiki companyn, insha Allah zan yi qoqarin hada kudin a warware komai, nayi nadama, please forgive me" yafada cikin sanyin murya
"No dad, ni bakayimin komaiba, infact ina iyayin komai don farincikinka, am not leaving the company now, ba yanzu ba"
"No shalele, it's over"
"No dad, not yet..please banaso kasamu karayar arziqi"
"No shalele, I can sell the mall ma, samu da tashi duk na Allah ne, zan sayar, Zan kammala komai cikin week dinnan a biyashi" yafada sounding serious
'No dad not now, kabani lokaci"
Haka sukaita ja, dakyar daddy ya haqura but har cikin zuciyarshi dagaske ne yayi nadama, akan abin duniya yana Neman salwantar da farincikinshi, akan abin duniya yana Neman rysa kanshi, yasan yayi kuskure and he's regretting kuma ya quduri aniyar gyara wa.
Sun dan ta6a hira kasan sannan sukayi sallama, ranar tayi barci mai dadi don murmushi kasa barin fuskarta yayi ko acikin barcin.
Washegari gidan mamy taje ta yini, sosai taji dadin zuwanta don dama tayi kewarsu, wannan karon sun hadu da Abba kasancewar ranar yadawo daga wata tafiya, nan suka hadu sunata fira gwanin sha'awa.
Anan take gayamasu batun tafiyarsu Spain acewarta aiki zaije shine zai tafi daita.
Addu'o'i sukayi mata sosai da shawarwari nagari sai la'asar tabar gidan tawuce mall din daddy.
Dariya taita yimata daddy ganin sai kakkauda kai yake wai besan su hada ido.
Tun yana kunyarta harya ware sukaita fira don saudart bata wani dauki abun dazafi ba yadda yayi tunani.
Sai tambayarta yake ya A.A ke treating dinta sai tace lfy, beyimata komai.
Matsamata yayi akan tayi shopping na tafiya.
Dafarko taqiya amma daya matsamata saita dan tsinci gowns kadan.
Ganin haka yasa Dad yimata shopping din dakanshi, gowns yan kanti ya kwasanmata kala kala kowanne da March na shoes da bag dinshi.
Sosai taita complaining sunyi yawa amma shi ko a jikin shi Shidai burinshi ya faranta mata.
Ba ita tadawo gidaba sai wajajen 9:00pm shima daddy ya kawota dakanshi.
Fitowa tayi tana dagamashi hannu harya wuce, she's so happy, duk saita nemi baqincikinta ta rasa.
Haka tashigo gidan niqi niqi da kaya, tun a parking space tagane yana gidan.
Da sallama tashiga falon, hangenshi tayi kan daya daga cikin cushion din falon ,zaune sanye da baqar singlet da baqin wando ya duqufa kan laptop.
Kallo daya sukayima juna suka kauda kai.
Wuce shi tayi ta hayewarta sama batareda tasake kallonshi ba tashige daki
Toilet tawuce tayi wanka don ta kwashi gajiya sosai.
Koda tafito shirya wa tayi cikin kayan barci sannan tahau shirya kayanta.
Saida ta tabbatar ta kammala komai sannan tabi lfyr gado ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya...✍
No editing🙏
Ummin fasihu ce🧚♀
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
045
Qarfe goma daidai tafito daga dakinta sanye da wata jallabiya peach colour mai adon pink agaba tayi rolling din gyalen jallabiyar, hannunta daya riqeda handbag dayan kuma janye da qaramin trolley.
Saukowa tayi janye da trolley din jikinta sai tashin qamshi yake.
Tsayawa tayi a falon ta kashe komai na wuta kamar yadda tayi a kitchen da dakinta sannan tafito waje walking majestically kamar ba ita ake jiraba.
Ashraf ya qulu iya quluwa, tundazu ya aika drivern dazai kaisu yakirata amma sai yanzu taga damar fitowa.
Ta side mirror yake kallonta ta taho kunnenta kare da waya da alamu waya take ga wani sihirtaccen murmushi datake saki Wanda ya bayyana jerrarun haqoranta farare Tass ga dimple dinta na dama daya lo6a.
Tsayawa yayi yana kallonta don tunda yasanta be ta6a ganin murmushinta ba she's always moody or expressionless.
Qarasowa tayi driver yayi saurin fitowa ya zagayo ya budemata kofar baya side din dama tashiga ya rufe sannan ya zagaya baya don saka trolley din a booth.
Qamshin turarenshi dataji gab daita yasa gabanta faduwa, batayi tunanin tare zasu tafiba don koda driver yazo dazu tazaci shizai kaita shi Ashraf din yariga yayi gaba.
Cikin dabara ta gyara zama tanasa style tana dan matsawa daga gefenshi.
"Ok sweet dad saina kira din, love yah" tafada tana blowing mashi kiss
Sannan ta katse kiran tana qara dan matsawa daga gefenshi.
Satan kallonshi tayi da wutsiyar ido taga hankalinshi nakan wayar hannunshi fuskar nan kamar anmashi bishara da jahannama.
Ta6e baki tayi ta maida kallonta ga windown motar tana kallon waje yayinda drivern ya tada motar suka fice.
Tsit motar tayi babu mai ko qwaqwaran motsi, kowanne ya maida hankalinshi ga abinda yashamashi kai.
Saudart sai kalle kallenta take ta window, ganin andauki hanyar gida Ummy yasata jin wani irin farinciki har cikin zuciyarta.
Horn daya yayi aka wangale musu gate din suka shiga sannan direct suka nufi parking space
Bata jira akazo aka budemata ba ta 6alle murfin motar tafita da sauri tanufi su Ummy dasuma suka nufi parking space din.
A tsakiyar hanya suka hadu suka rungume juna saudart da baby dake ta tsallen murna itakam saudart sai dariya take.
Sakin baby tayi ta qarasa wajen Ummy daketa washe baki ta duqa da niyyar gaisheta Ummy tayi saurin tarota itama ta rungumeta cikin farinciki.
Ashraf daya fito ya jingina da mota Kasa daina kallonsu yayi ganin yadda suke murna daga ganinta kawai kuma da alamu sunma mance dashi.
Be ida sanin sun mance dashiba saida yaga sun juya su duka sun nufi cikin gida cikin raha da dariya.
Kutt.. Yafada yana Waro idanu ganin dagaske fa mancewa dashi din sukayi, afusace yamiqe daga jikin motar shima yanufo cikin gidan kamar zai tashi sama.
A falo suka yada zanyi baby sai zuba take kamar ri6a6iyar radio, sai roqonta take wai dan Allah tayiwa Ashraf magana aje daita Ummy nacewa bata isaba saidai ita ta gayamashi da kanta itakau saudart sai dariyar dramarsu take.
Suna haka sukaji an banko kofa an fado ciki Wanda hakan yasasu dagowa dukansu suna kallon kofar.
"Laa wai Ashe kana waje" inji Ummy Wanda hakan yaqara fusatashi ya turo baki yana ida shigowa falon
Itadai saudart kauda kai tayi tana ta6e baki don ita kwata kwata shagwa6ar dayake haushi yake bata.
Saurin daidaita zama baby tayi tana qaqalo murmushi tana gaidashi.
Banza yayi daita yawuce ya zauna kan wata kujera nesa dasu sai cika yake yana batsewa.
"Ummy ina kwana?" Yafada yana hura hanci
"Lfy lau, lafiyarka kaketa hawa kamar flour da yeast yaima yawa?" Tafada cikin sigar tsokana
Kallon baby dake faman danne dariyarta yayi ya gallamata harara tayi saurin sadda kai qasa sannan ya kwa6e fuska
"Ummy yanzu