Showing 126001 words to 129000 words out of 173829 words
tayi mai sauti tana cewa
"Allah ya shiryaminke, yanzu tashi kishiga wanka saiki fito da alwala kiyi isha'i sannan ki shirya, kinji yar maminta?"
Kada kai tayi ahankali bakinta a so6are sannan ta tashi tacire hijab din jikinta ta fiddo towel tawuce bathroom.
Girgiza kai mamy tayi tana murmushi sannan ta tashi tafita daga dakin itama don zuwa gabatarda isha'i.
Bayan tagama takoma dakin ta isketa itama gamawarta kenan.
Wucewa tayi sip dinta ta ciromata wata dakkakiyar pupple shadda dinkin doguwar riga mai wrapper 'o' shape taji paint work tareda farin gyale mai stones ajiki.
Ita dakanta ta shiryata tana yi tana fadamata kalamai masu kwantar da hankali cikin tattausan murya wanda hakan ya kwantar da hankalinta sosai.
Tana cikin dauramata dankwalin kayan phone dinta yayi ringing.
Dagawa tayi ganin abba ne, nan yake gayamata ta taho da saudart falonshi ga ashraf dinma nan yazo, da to ta amsa sannan ta katse kiran.
Bata cewa saudart komaiba ta ida dauramata dan kwalin tayimata simple cool makeup sannan ta fesheta da turare mai shegen qamshi mai dadi sannan ta doramata gyalenta saman kai ta ajiyemata fararren takalminta saitin kaffafunta.
Tashi saudart tayi asanyaye ta zira takalmin ta dauki purse dinta dake kan mirrorn sannan tabi bayan mamy data kama hannunta.
Zaune ashraf yake kan centre carpet ya tankwashe kaffafunshi kanshi dayasha baqar hular dara akasa.
Sanye yake da dakakkiyar farar shadda dataji aikin boda kalar baqi, wrist dinshi sanyeda agogon rolex kaffafunshi sanyeda baqaqqen safa sai tashin qamshi yake.
Sallamarsu ce ta katsesu suka dan dago suna amsa sallama.
Tare suka shigo saudart kanta aqasa tayi wani mugun kyau cikin shigarta sai zuba qamshi take.
Tuna suka shigo qamshinta ya dabaibaye mashi hanci, alokacin babu abinda yakeso alokacin kamar ya dago ya kalleta amma kunya ta hanashi saima qara duqe kan dayayi don sosai yake kunyar mamy.
Jin motsi yayi kusadashi yadan saci kallon gefenshi ta qasa yaga itace ta zauna dan nesa dashi, kallo yabi hannunta dayasha henna baqi da ja data dora kan cinyarta kamar yakamo hannun don sosai qunshin yatafi dashi.
Jin mamy namashi magana yasashi saurin janye idanun daga hannun nata yashiga gaisheta cikin girmamawa.
Amsawa tayi tana tambayarshi ya mutan gida ya amsa da duk suna lafy.
Gyaran murya abba yayi yafara masu nasiha mai ratsa jiki gameda zaman aure da haquri dajuna.
Sosai nasihar tashigesu don har saida saudart ta zubda kwalla.
Yana gamawa mamy ma tadora da nata sannan sukasamusu albarka da addu'o'i sosai.
Bayan haka abba ya umarci ashraf yatashi yatafi da matarshi.
Kuka sosai saudart keyi kamar yaune ranar aurenta, haka su mamy suka rakota har bakin dalleliyar farar motar dayazo daita tashiga gaba gefen driver tana kuka sosai shikuma yashiga mazaunin driver.
Nan ya tada motar yana satan kallon saudart data rufe fuskarta da mayafi tana kuka sosai sannan ya ja motar su abdul nata dagamusu hannu a sanyaye suka bar gidan...✍
Ummin fasihu🧚🏻♀️
[9/14, 12:51 PM] +234 902 212 2569: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
089
Tuqi yake cikin normal speed gwanin burgewa, motar ta gauraye da both qamshin turarenshi da nata wanda suka hadu suka bada wani scent mai mugun dadi ga sanyin a.c din motar daya qarasa cikin motar extra cool.
Ahankali yaqara juyowa ya kalleta, kanta kifeda da cinyoyinta tana sheshekar kuka ahankali wanda yakejinshi har cikin ranshi.
Dauke kai yayi ya maida ga tuqin dayake yana jin badadi, duk zumudinshi da dokinshi duk sun kau dalilin kukan datakeyi.
Jiyayi shima yadamu sosai, meyasa take kuka? Kenan haryanzu she hate him? Yasan bata sonshi amma ai yaci ace ixuwa yanzu ta yafemashi koda bazata bashi zuciyarta ba.
Qara kallonta yayi asanyaye yasake maida idanunshi a kan titi yanajin badadi don sosai kukan nata ke ta6amashi zuciya, jiyake kamar ya rungumota ajikinshi yaita patting dinta hartayi shiru.
Horn yayi a bakin tangamemen gate din gidansu, ko minti biyu ba'a qaraba gate din ya wangale,
Jan hand brake din yayi baya sannan yaja motar yashiga cikin gidan dayake tarr da haske kamar ba dareba.
Parking yayi abaki bakin parking space don yasan yanzu zasu fito.
Dan satan kallonta yayi yaga haryanzu bata dagoba kuma bata bar kukan ba.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasa hannu ya bude murfin kofar yafita ya zagayo side dinta yabude mata kofar.
Qin dagowa tayi dukda taji tsayuwar motar dakuma bude murfin 6angarenta.
Sosai take cikin fargaba, fargaban irin zaman dazasu sakeyi dashi, tama kasa misalta zaman nasu a zuciyarta.
Kallonta kawai shima yake, da ba a wannan gidan bane da babu abinda zai hana ya dauketa kamar baby doll yakaita har dakinta amma that must wait, bazai iyayin haka ananba.
Hannunshi yakai yakamo tsintsiyar hannunta dayasha qunshi ya riqo softly.
Hakan yasa kukan nata ya tsaya cak kamar anyi ruwa an dauke, gabanta yashiga faduwa kadan kadan.
Qoqarin amsar hannunta yake amma takasa don ya riqe sosai.
"Ki sauko don allah, yi haquri" yafada cikin sigar rarrashi
Shiru tayi still bata dagoba, tanajin wani iri sakamakon riqemata hannu dayayi.
Ahankali yadan jawo hannun kamar zai dagota.
Haka yasa ta dago saidai kanta aqasa, ta ziro kafa daya ahankali sannan ta ida fitowa asanyaye feeling so awkward and weak.
Besaki hannunba dukda tafito din saima sake damqe hannun dayayi yafara tafiya.
Dole tabi bayanshi badon tasoba fargabarta na qara qaruwa.
Tafiya suke hannunsu acikin na juna, jinshi yake so on top, jerawa da ita haka hannu cikin hannu ba qaramin shauqi abin yasashi ba.
Wani abu ma saima sunyi settling, yayi alqawarin saiya kasheta da salo salo na love, saiya tsundumata a kogin soyayyarshi tasha tayi tatul.
Murmushi yadan saki daidai sun qaraso bakin kofa.
Dayan hannun dake free yasa ya danna doorbell din yana satan kallonta.
Shiru saudart tayi wondering meyasa yake danna doorbell, dama basu kadaine agidanba?
Budewar kofar ya katse mata tunani.
"Oyoyo my daughter! Maraba lale, marhaba biki" taji muryar ummy ana rungumota.
Saurin dagowa tayi takalleta taga ita dince tana qoqarin shiga daita ciki.
Saurin sunkuyar da kai tayi cikin tsananin kunya suka shiga ciki tana jikinta.
Murmushi ashraf yayi ganin ummy batama bi takanshi ba shima yashiga cikin ranshi yana cewa
"Saukin abin matata ce ba taki ba"
Saida suka shiga falo sannan saudart ta ida tantance inda suke, gidansu ashraf.
Haka ummy taqarasa daita ciki tana mata marhaban cikin fara'a harta kaita kan wani kujera ta zaunar daita kamar tana zaunar da kwai, itakau saudart tsabar kunya ko dago kai takasa.
Shima qarasowa yayi ciki yana kallon yadda umminshi ke wani binta ahankali cikin so da qauna, murmushi yayi yana jindadin yadda ake tarairayar gimbiyar tashi.
Da dane da yanzu yana nan yanata kumburi anfi nunamata qauna, amma yanzu he's happy don masoyanta masoyinshine.
Ahankali tazamo daga kujerar ta zauna qasa tana gaida ummy da itama zamanta kenan cikin girmamawa kai aqasa.
Amsawa ummy tayi cikin fara'a tana cewa takoma kan kujera ta zauna amma taqi tashi saima sadda kai datayi tana wasa da fingers dinta.
Qarasowa ashraf shima yayi ya zauna yana facing dinsu, kallo daya zakamashi kasan zuciyarshi fess take, don sosai yakejin wani sabon farinciki a zuciyarshi kamar yaune aka dauramusu auren.
"Wai ummy hayaniyar me nakeji n.." baby dake saukowa qasa tafara fadi, ganin kamar saudart azaune kan carfet yasa kingin maganar maqalewa a iska.
"Aunty!!" Tafada da karfi sannan tayo qasa dagudu tana skipping din stairs bama ta lura da akwai A.A a falon ba.
Wani irin fadawa kan saudart tayi ta qanqameta cikin farinciki don ita batamasan da zancen tarewarta ba.
"Hey are you mad!" Inji ashraf cikin qaraji ganin tawani fadawa matarshi
Saurin zabura tayi tasaki saudart dahar yanzu kanta ke qasa ta kalli gefen dataji tsawan don ita harga allah batama lura dashiba.
"Karyata zakiyi koko? Zaki tashi daganan ko saina sassa6a miki!" Yafada cikin daga murya.
Saurin miqewa tayi kafinma ya qarasa maganar tadawo gefen ummy ta zauna tana shigewa jikinta tana turo baki.
"To sannu, hanata zakayi su gaisa da auntyn tata?" Inji ummy tana gallamashi harara.
Dan sosa qeya yayi yace "ummy kingafa fadamata tayi, karta karyata"
"Eh tunda ga pencil ba dole ta karye ba?" Tafada tana harararshi
Sunkuyar dakai yayi kawai bece komaiba yana kwafa acikin zuciyarshi, shidai suyi sugama yatafi da matarshi basai sun qara ganinshi ba? Dama ciki yake dasu yadda suka sashi wahala musanmman ummy data kusan samashi heart attack lokacin data buqaci takardarta, dama yadau alwashin duk sadda ya dauki saudart yatafi sai baba ta gani, sai sunyi missing dinshi sosai don yaga alamar dan zaman nan dayayi sun wani rainashi, musanmman waccan tsinken sakacen (baby😂)
"Aunty ina wuni?" Inji baby dake maqale da ummy haryanzu cikin zumudi.
Dan dago kai tayi ta kalleta ta sakarmata murmushi sannan ta maida kan qasa don sosai takejin kunyansu gabadaya.
"Baby kaita sama dakina, bari na hadomata abinci" inji ummy
Saurin tashi baby tayi kamar dama kan qaya take tadan saci kallon ashraf daketa antayamata harara ta qasan ido, tai saurin dauke kai taqaraso wajen saudart ta kamota tana mata rada a kunne
"Welcome back"
Batace komaiba sai tashi datayi suka wuce stairs tare, ummy da ashraf na binsu da kallo.
Saida suka shige sannan ummy ta maido kallonta kan ashraf da har yanzu be bar kallon inda sukabi ba tayi gyaran murya.
Saurin dauke kai yayi daga kallon dayake ya sunkuyar dakai cikin dan jin kunya.
"Saika tashi kaje kaima ga abincin can dining in zakaci" tafada cikin daurw fuska.
Dan ta6e baki yayi yace
"No ummy am ok"
Azuciyarshi kau cewa yayi
"Abincin yasha zamansa, Idan naci ina zan saka kazar dazan siyamana?"
"Kai kasani" tafada tana tashi tabi bayansu baby.
Binta da kallo yayi harta haye sannan ya ta6e baki yana wondering meyasa kwananan ummy ke dauremashi fuska, gashi yanzu tagama washema saudart baki amma shi tawani hade mashi fuska.
Ta6e baki yayi yakoma ya kishingida a kujerar yayi balancing yaciro wayarshi yana daddanawa yana jiran tagamaci ta sauko su tafi😒
Sosai yakejin zuciyarshi fess, sai practicing din abinda zai faramata yake a zuciya, soyake ya koyamata darussan sonshi dalla dalla, zai maidata queen dinshi, sarauniya, yalla6iya, ko tsinke bazai bari ta dagaba, shizai mata breakfast, yazo ya tadata daga barci romanticly ya rakata har bathroom dama yariga ya hadamata ruwan wanka mai dumi da qamshin gaske, yajirata kofar bayin harta gama tana fitowa ya sunkuceta yakaita kan gado, ya zaunar daita, ya shafamata mai ya ciromata kaya tasa sannan yakaita dining, A'a sama zaikawo abincin, zaifi bada kala, ya bude yayi serving dinta ya saka cokali ko fock yafara feeding dinta, da ana iya taunamata ma dashi zai taunamata, tagama yabata ruwa tasha sannan yayo clearing din wajen yadawo ya sungumeta yakaita falo ya kunnamasu kallo ya kwantar da kanta bisa cinyarshi suna kallo yana massaging din kanta.. wooh soyayya dadi! Saiyafi sharukh khan ma iya zuba love, saiya rudata da salon soyayya ya tsundumata tsundum cikin kogin soyayyarshi yadda duk numfashinta saita shaqane da sonshi.
Haka yaita lisafe lissafenshi shikadai sai sakin murmushi yake, jin yafara gajiya dazama babu su babu alamar su yasashi daga kai yaduba agogo.
Waro idanunshi yayi ganin har goma ta gota.
Wannan cin abincin na lafiya ne kuwa? Almost two hours?
Shiga contact yayi ya dannawa number baby kira ya kara a kunne yana tamke fuska kamar tana gabanshi.
Saida takusan tsinkewa sannan aka daga
"Hello?" Yaji tafada cikin muryar barci
"Ke! Ya akayine? Haryanzu bata gamacin abincin bane?" Yafada cikin husky voice
Zaune tamiqe tana murza idanu don ita tama dan dade da kwanciya
"Wacece?" Ta tambaya tana hamma
"bansaniba! Nace ina saudart" yafada a fusace
Turo baki tayi sannan cikin marairaicewa tace
"Nifa tunda ummy tahau sama ta korani daki wai karna takuramata"
Tsaki yaja ya katse wayar kawai. Bin wayar tayi da kallo cikeda takaici sannan ta kasheta gabadaya tayi tilli daita kan gadon ta kwanta taja bargo.
Yana gunguni yashiga neman number ummy.
"Yanzu this is 10 sai dayan dare nufinta zamu tafi?" Yafada yana danna mata kira.
Itama saida takusan katsewa sannan ta daga
"Uhum?" Tafada daga dayan 6angaren
Turo baki yayi cikeda jin haushi yace
"Ummy this is past ten fa"
"Sai akayi yaya?" Inji ummy tana daure fuska daga dayan 6angaren.
Haushi ne yasake qumeshi
"Ummy sai midnight zamu tafi? Bata gama cin abincin bane haryanzu?"
"Wa kenan?" Taqara tambaya
Shiru yayi gabanshi nadan faduwa.
Wani tunani ne yazo mashi, saurin kauda tunanin yayi yana cewa no..no..no ummy bazakiyimin hakaba.
"Look idan bakada abin cewa zan kashe wayata, dama barci nike ka tadani" ta katsemashi zancen zuci da hakan.
Cikin dan rawar murya yace
"To kiyi haquri ummy, wai gani nayi dare nayine ga securities, idan nahau hanya yanzu suna iya tareni""yafada cikin zuciyarshi yana addu'ar allah yasa ba abinda yake tunani bane zai faru
"Ehen? Katafi mana, dama wani ya tsaidaka?"
Shiru yayi yanajin yawun bakinshi na qafewa, besan sadda ta zame hular kanshi ba yana fiffita kanshi
"ummy dan allah kiyi haquri, kibani saudart mutafi dare yayi" yafada cikin mugun surewa yana ganin yadda budget dinshu ke rushewa agaban idanunshi
"Wace saudart?"
"Ummy don allah, don allah kiyi haquri, please ummy, don allah" yafada duk ya rude yayinda danasanin biyowa tanan ya dirarmashi nan take.
"Mtcheew meye nawani tisani gaba kana begging? Me kayimin?"
"Wlh nima bansaniba ummy amma don allah kome nayi karki hukuntani da wannan, please sweet ummyna kinji?" Yafada cikin sigar rarrashi still yana yima kanshi fifita.
"Mtcheew saida safe, ka kashe duk kayan wuta dake falon sannan ka kullemin kofa idan zaka tafi" tana kaiwa nan ta katse kiran tama kashe wayar gabadaya.
Sakin baki yayi jin abinda tace, me kenan? Oh no! Wlh bazata sa6uba.
Saurin ciro wayar yayi daga kunne yasake re-dialing din wayar amma wayar akashe.
Ca6! Yau ake yinta, idan ya yarda yatafi tsaye😡
Tilli yayi da hular hannunshi ya nufi sama kamar zaiyi fiffike yatashi sama yanajin kanshi na daukan zafi.
Beci burkiba akoina sai a kofar dakin ummy.
Bubbugawa yake yana huci, jin shiru yasashi qara bubbugawa wannan karon da qarfi don sosai zuciyarshi ke tafarfasa.
Jin kamar za'a 6alla kofar yasa ummy tasowa don ita guduma take kar ya tada saudart datayi barci tundazu wanda azahirin gaskiya ba barci saudart keyiba duk abinda ake harta wayar da ummy tagama yanzu duk a kunnenta ne.
Ganin ummy ta bude kofar tafita yasata dan dagowa ta yaye bargon kanta ta kalli sannan tasaki murmushin jindadi tajuya tagyara kwanciyarta tana dariya qasa qasa.
Shiru ashraf yayi yana kallon ummy kamar zai fashe da kuka, jiyake kamar yaita ihu ko zaiji sauqi.
"Nace menene! 6allemin kofar zakayi?!" Inji ummy tana binshi da harara
Qoqari yayi wajen sassauta muryarshi sannan ahankali cikin kwantar da murya yace
"Haba ummy, haba ummy? Dan allah ki tausayamin mana, dan allah kiyi haquri ki fiddota mutafi dare yayi"
Wani kallon uku saura kwabo take binshi dashi harya kai aya sannan tace
"Ka gama? To wlh ka fita idona in rufe ashraf, katafi kabani wuri tun muna mu biyu wlh, tun kafin in sassa6amaka"
Kallonta yake kamar zaiyi kuka, ahankali yace
"Ummi yanzu ina zani ni kadai?"
"Ohon maka amma wlh nakarajinka kusada kofarnan saika yabawa aya zaqinta" tana kaiwanan tajuya takoma dakin tareda bugo kofar.
Tsayawa yayi yana kallon kofar cikin rashin sanin abinyi, wai wane tsautsayima yasashi zuwa gidan ma tun farko, wannan shi ake kira rabon ayi, (nikuma nace ga qoshi ga kwanan yunwa😝)
Ya dade sosai tsaye a bakin kofar kamar mai jiran tasake fitowa har saida yaji kaffafunshi sunfara sanyi sannan yajuya afusace ya sauka qasa feeling so mad in anger, jiyake kamar yadora hannu aka yaita ihu.
Motarshi yashiga afusace ya kunna yayi reverse, wani uban horn ya danna kamar ana yaqi sannan ya fice a tsiyace bayan an bude gate din.
Tuqi yake yana huci ga idanunshi dasukayi jajir, jiyake kamar yaita kuka don takaici, kai amma ummy tagama dashi wlh, duk wannan tsare tsaren nashi duk ta rusheshi kenan abanza?
Kwafa yayi yana danna kan motar cikin gidanshi bayan anyi scanning dinshi.
Ko parking din kirki beyiba ya sauko daga motar ya maidata ya rufe da qarfi sannan yayi cikin gida fuuu.
Jiyake kamar ya hadiyi zuciya kawai, he can't believe duk zumudin da zakwadin shi kadai zai kwana gidan at the end of the day, kai ummy tagama dashi.
Direct dakinshi yashige yawani bugo kofar da qarfi, baiwar allah yadda kasan ita tamashi laifin😕
Kokowa yashigayi da rigar jikinshi don cireta yadda kasan yasamu qaton gardi.
Dakyar yasamu ya cireta yana huci dukta cikwikwiye itama yayi cilli daita tana huci.
"Wlh ummy kin gama dani!" Yafada yana dafe kai cikeda takaici.
Tsaki yaja yafara safa da marwa dakin cikin tsananin 6acin rai, jiyake kamar yaita hauka.
Wayarshi yazaro daga aljihun rigarshi dayayi cilli daita ya lalubi number sadeeq ya dannamashi kira yana huci.
Kira har hudu amma ba'a dagaba da alamu dai ya dade dayin barci
Tsaki yaja yana cilli da wayar kan gado yana cewa
"Shege sleeping head kawai"
Ataqaice ranar ashraf kasa runtsawa yayi don baqinciki, tsaki kau yakashi yafi cikin kwando dama tusa hali bare anci wake😆
Yadda yaga rana haka yaga dare don azaune ya kwana don bakinciki...✍
Please kucigaba dasa brother na a addu'a🙏
Ummin fasihu🧚🏻♀️
[9/14, 7:23 PM] +234 902 212 2569: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
090
Yauma da 6acin ran jiya ya tashi, dakyar ya iya tashi yayi alwala yafita masjid bashi yadawo ba saida gari yadan fara haske.
Tunda yadawo yashige daki ya kwanta shiru zuciyarshi fall takaici.
Ringing din wayarshi yasashi bude idanunshi daya lumshe sannan yadauki wayar ahankali yana duba mai kira, tsaki yaja kamar bakin zai tsinke ya maida wayar ya ajiye batareda ya dagaba.
Saida aka mashi 4 missed calls be dagaba sai a ba biyar sannan ya daga yawani tamke fuska kamar mai kiran na gabanshi.
"Amma A.A kaci uwar rainani, inta kiranka kaqi dagawa don iskanci?" Inji sadeeq a dayan 6angaren.
"Qodarka aka ban ajiya halan dazaka addabeni da kira kamar wanda yayi maka sata, ni nace ka kirani ne?" Yafada cikin 6acin rai
"Sai kace in kiraka dama? Mtcheew dama don naga missed calls dinkane har hudu yasa na kira inji lafiya ashe iskancinka ne ya motsa"
"Eh shi ya motsa, and batun missed calls ai tun jiya namaka don iskanci sai yanzu zaka wani kirani kaji lafiya? Don ka maidani maloho?"
"To allah yabaka haquri, ba laifinka bane, laifi nane dana kira at the first place, bye"
Qiit.. ya katse kiran.
Wani haushi yakuma qume ashraf, ciro wayar yayi daga kunnenshi afusace yasake dannamashi kira yana huci.
Saida takusan katsewa sannan ya daga yana cewa
"Menene kuma?"
"How dear you hang up on me? Kai wanene dazaka katsemin kira?" Yafada afusace, dama neman wanda zai juyewa kwandon bala'i yake
"Tofa? Meyasa nayi hanging? Mezai hana inyi hanging? Na tashi naga missed calls dinka wajajen 12 ba dole hankalina ya tashiba? Nakira kuma inyi comfirming ka balbaleni mezai hana inyi hanging up?" Yafada shima da alama yafara qulewa
"Eh din, an balbaleka din! Mezakayi? Nace anje an balbaleka din, ko dukana zakayi?" Yafada cikin tada jijjiyoyin wuya abinda ummy tayimashi nasake dawomashi a qwanya, da yanzu suna tareda abar qaunarshi, nurul qalbi dinshi.
Shiru sadeeq yayi kawai