Showing 63001 words to 66000 words out of 173829 words

Chapter 22 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1127

shiyasa zamu tafi, ke ke tunawa da abinda yafaru ni harna manta, yanzu haka zuwa nayi naji babu inda zaki anjima Ku rakani shopping ke da Loveth?"

Sai a sannan hankalin Reyna ya kwanta har wani sauke ajiyar zuciya tayi

"Better, nazaci sbd haka zaku tafi and maganar shopping? It's capital YES! ko da inda zani bazan bari wannan damar kasancewa dake na qarshe ta su6ucemin ba, waya sani ko bazamu sake ganin junaba?" Tafada tana langwa6a kai gefe

"Insha Allah zamu sake hadewa ok? Koba yanzu ba" tafada itama tana langa6e kai

"I'll miss you" tafada tana rungumeta

"I'll miss you much" inji saudart tana murmushi

Ganin batada niyyar sakinta yasata yimata chakulkuli Wanda hakan yasata saurin sakinta suna dariya tare

"Ok now tafiyar nanan? Loveth zata samu zuwa?"

"Yes, yaushe zamu?"

"4:00pm dot zanzo nan, idan Baku shiryaba zan tafiya ta" tafada cikin kashedi

"Yes ma'am" inji Reyna tana sarawa sukayi dariya gabadaya sannan suka fito tare tayi mata rakiya harta kusan kaiwa gida sannan ta koma





*****************************************


*4:33pm*

"Mtcheew zanyi tafiya ta fa!" Inji saudart dake kofar gidansu Loveth fuskarnan a hade.

Reyna dake gefenta sanye da wando da shirt sai purple jacket ita gwiwa akai gashinta awaje ta kama hannun saudart tana cewa

"Kinga zomu tafi, she's not serious"

Saudart sanye take cikin lace jaa Riga da zani ta yafa gyale baqi stylishly, kallo daya zakamata kasan cikkakiyar bahausa ce.

"Mtcheew mutafi" inji saudart din tana bin Reyna.

Dagudu Loveth tafito daga cikin gidan takalmi a hannu tana cewa

"Kujirani please!"

Saida ta iso motar sannan ta ajiye takalmin tasaka tana numfarfashi wai don tayi Gudu.

Sanye take cikin baqar English gown mai tsaga a baya kanta kuma daukeda hula fara sai qatuwar handbag hannunta.

Haka suka shiga motar Reyna din sunama juna tsiya.

Reyna ce ta zauna mazaunin driver sai saudart gefenta sai Loveth abaya, haka suka tada motar suka bar wajen suka kama hanyar fita daga estate din.







Babu laifi sunyi spending din good time at are, shopping sukayi kamar babu gobe, duk abinda tagani ya burgeta saita dauka.

Haka suka jero suna shopping suna fira da dariya gwanin sha'awa, saida suka gama kaff sannan fa aka bude babin selfie, wai hotunan tarihi.

Sunyi hotuna harna hauka, daga qarshe rasa style din dazasuyi sukayi sai sukaita style din hauka suna dariya, it's a happy moment for them don jisuke kamar karsu dawo gida.


Ataqaice dai sai gab magrib suka baro supermarket din.

Nan suka sako duk kayan dasuka siya a mota suka shiga.

Wannan karon saudart ce ta tuqosu, suna tafe suna tsokanar juna suna dariya.

Koda suka iso gida har angama sallar magrib.

Kofar gidansu saudart suka yada zango don duk tafisu kaya, saida tagama sauke kayanta kaff sannan sukayi sallama akan saisun zo bankwana gobe idan ransu yakai.

Haka ta cicci6i kayan Niki Niki tashiga gidan.




A falo ta ganshi zaune yana danne danne a laptop, kallo daya tamashi ta kauda Kai tawuce shi kayan na rinjayarta.

Binta da kallo yayi harta kai bakin kofarta ta ajiyesu ta bude kofar sannan ta kuma kwasa tayi ciki tarufo kofar.

Ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kanshi ahankali sannan ya cigaba da abinda yake.






*********************************

Washegari tunda ta tashi da asuba takasa komawa, dama jiya ba wani barcin kirki tayiba, jitake kamar tajawo lokacin don lokacin be wani yimata Gudu.

Flight din 10:00am garesu amma tun 7:00am take falo zauna sai gyara zama take agogo kau ta dubashi yafi a qilga.


9:00am sai jitayi ana knocking a kofar falon.

Saurin tashi tayi taje ta bude, ihu tasaki ganin Loveth da Reyna ta qanqame su cikin murna

"Hmm muda ba'a ganmu ba saimu juya" inji wata dake baya.

Sai a sannan saudart ta ankare dasu taga sunada yawa ma harda Dr zahra.

Saurin sakinsu tayi tana yi musu iso ciki fuska washe.

Nan suka shigo suka zauna taje ta kawo musu ruwan sha sai washe baki take.

"Hmm sai murna ake za'a gida kamar irin can yafi nan dinnan" inji wata cikinsu

Kamar jira ake nan falo ya kaure da cafta kowa na fadin albarkacin bakinshi itakau Dr sai dariya take musu.


Jin hayaniya a falo yasashi cikin mammaki sosai, to gidan dai babu kayan kallo bare yace kallo aka kunna kuma ma wannan beyi kamada kallo ba yafi jin hayaniyar a zahiri.

Saurin kammala shirin yayi yana duba agogonshi don har Tara da Rabi.


Turus yayi daya fito yaga gugun mutane zaune a falo saudart tsakiyar su suna dariya.

Ganinshi yasasu natsuwa suna gaidashi.

Qarasowa yayi yana amsawa yana kuma gaida Dr.

"Sai Nigeria ko?" Inji Dr zahra cikin tsokana.

Dariya kawai yayi yana shafa kanshi

"To Allah ya tsare, wish you safe journey, Ku gaishe da mutanen Nigeria, insha Allah zanzo watarana har gidanku, tunda duk munyi exchanging din number" tafada cikin fara'a

"To Allah yasa" inji Ashraf yana satar kallon saudart daketa murmushi.

Farincikin datake aciki afili yake baya 6oyuwa.
At last zasu koma qasarsu.


Fitowa sukayi tareda gungun mutanen sai tsokanarta suke tana biyemasu, har mota suka rakata harda budemata kofa tashiga.

Sai kuma a sannan suka fara marairaicewa wai zasuyi missing juna.

Haka dai suka rabu zuciya babu dadi sai dagawa juna hannu suke har suka bar hangen juna.

Komawa tayi ta jingina da kujerar tana sauke ajiyar zuciya tana murmushi.

Shima dayake satar kallonta tundazu murmushin yasaki ya kauda Kai yana mammakin saurin sabo irin nata, ji yadda mutane sukazo rakiyarsu kamar sunyi shekaru a qasar.


Haka motar tayi tsit har suka qarasa airport din.

Suna fitowa daga motar tafara bin airport din da kallo, kamar jiya ne suka shigo airport dinnan da niyyar shigowa qasar amma wai yau sune aciki da niyyar barin qasar zuwa qasarsu.

"Can't wait" tafada cikin zuciyarta tana murmushi

Saida aka gama komai sannan suka shiga jirgin.

Kamar wancan karon kusada juna suka zauna.

10:00am dot aka fara sannarwa na kowa ya daura belt dinshi.

Wannan karon ba'ayi qauyanci ba nan da nan ta daura.

Jin ana sanarwa na jirgi zai tashi yasa ta koma ta lafe a kujera murmushi a fuskarta.

Jin yafara tafiya yasa bugun zuciyarta qaruwa, jin ya daga yasata Sakin nannauyan ajiyar zuciya

"Bye Madrid, bye Spain" tafada ahankali tana bude idanu tana yiwa qasar kallon qarshe...✍


Kuyi hqr babu yawa, haihuwa akamana ban samun zama, wannan ma dasafe nake samu nadanyi kafin infita, da babu kwata kwata Gwara kadan, bear with me har komai ya warware🙏



Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲





Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)






052






Tafiyar awa biyar ne babu yan mintuna, kamar wancan tafiyar, barci ne yayi awon gaba daita ba ita ta farkaba sai gab da zasu sauka.



Jin suna landing a airport yasata jin wani shauqi na dibanta.

"Home, sweet home" tafada cikin zuciyarta tana murmushi.

Jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta gida.

Saukowa aka farayi amma sai gani tayi Ashraf beda niyyar tashi don latse latsenshi kawai yake hankali kwance gashi dole saiya tashi itama zata samu damar fita sbd ita ke daga ciki shike waje.


Shiru tayi itama taqi tankamashi amma deep down she's burning.

Saida ya mula yasha iska sannan ya tashi ya kara wayar a kunne sannan yanufi hanyar fita cikin takunshi na qasaita.

Binshi tayi da kallon takaici sannan taja tsaki ta miqe itama tafito.


Kamar wancan karon drivern dazai kaisu gida haryazo.

Shiga sukayi dukansu gidan baya sannan drivern yajasu suka fice daga airport din.







A parking space yayi parking suka fito gabadaya, saudart na qarewa gidan kallo, jitake kamar tayi shekara rabonta da 9ja, komai na dabanne da nacan, hatta iskar damuke shaqa yasha banban Dana can.


Driver ne ya fiddo mata kayanta na booth yakaimata har falo ita kuma tana kaisu can dakinta a sama.

Saida suka gama shigar da kayan tsaff sannan drivern yatafi, shikau Ashraf tuni yasake fita don haduwa da sadeeq.



Saida ta kammala komai inda yakamata sannan tayi wani juyi tana fadawa kan gadon

"Bari na kira wannan chali chalin" tafada tana nemo contact din baby sannan ta Danna mata kira.



A bangarensu Ummy kuwa suna zaune baby tayi matashin Kai da kafar Ummy taji wayarta na ringing.

Kamar bazata dubaba saikuma ta daukota tana dubawa.

Wani ihu tayi tana zabura daga kwancen datake a kafar Ummy har saida Ummy tadan firgita.

"Oh my God! Wlh anty ce, itace!" Tafada tana qara ware idanu tana kallon screen din wayarta.

"Wannan wane irin hauka ne baby?" Inji Ummy a qule

"Sorry Ummy, kalla wlh anty ce da number Nigeria, kenan sun dawo? Bari na daga karta tsinke" tafada tana daga wayar.

Ihu ta challarawa saudart cikin kunne Wanda saida saudart ta janye wayar daga kunnenta tana dariya.


"Aunty? Dagaske kece? Yaushe kuka dawo? Shine ko agayamana ko? To munyi fushi" inji baby tana kallon Ummy dake kallonta itama fuskarta da murmushi


"Ayyah autar mata, am soo sorry, surprise mukayi muku, kuma wlh dawowarmu kenan, ina Ummy?"

"Gatanan tana jinki, abata?"

"Eh bata"

Nan ta miqama Ummy wayar

"Aslm alaikum" inji Ummy cikin muryarta mai cikeda natsuwa da kwarjini

"Wslm Ummy, barka da wuni Ummy" inji saudart cikin ladabi

"Barkanki dai daughter, ya kuke? Ya hanya? Wannan surprise visit haka?"

Dariya saudart tadanyi tana cewa
"Ayyah Ummy, kuyi hqr, surprise mukayi muku"

"Ai babu komai, surprise Nada dadi ai, amma da kun fada da na turo baby ta gyara muku gidan kafin Ku iso"

"Ayyah Ummy, babu komai ai, zanyi besides gidan bawani qura yayiba sosai"

"Dukda haka bari tazo ta kama maki, kunsha hanya kuma sai a Dora da wahala? Bari tazo yanzu"

Nan sukadan ta6a fira, itakau baby tanajin maganar tafiya daman ta haye sama dagudu don shiryawa.

Cikin dan qanqanin lokaci saigata ta sauko cikin shirinta, lokacin har sun gama wayar, ta amshi wayarta tayimata sallama sai rawar jiki take sannan ta fice.



Saudart taji dadin zuwan baby sosai don tare suka gyara gidan kuma tasata nishadi sosai, surutu kau kamar an kunna radio, saida suka gama sannan tayimusu girki suka zauna sunaci tana gwadamata hotunan dasukayi dasu Reyna a supermarket, baby sai santin hotunan take.


Sai wajajen isha'i driver yazo daukar baby, nan ta hadata da tsarabar datayo musu, trolley qananu biyu.

Sosai baby tasaki baki tana kallon kayan don batayi zaton sunkai hakaba.

Zata fara qorafi saudart ta hayewarta sama tana cewa ta gaida Ummy ta maida kofa ta rufe.

Babu yadda ta iya haka ta kwashi kayan tafito suka wuce.






Agida ma saida Ummy tasaki baki ganin tsarabar, trolley daya na baby daya nata.

Shaqe kowanne yake da gown gown masu kyan gaske sai kayan kwalliya da mayamayai a trolley din baby Itakuma Ummy turarruka da takalmi masu kyan gaske.

Suna zaune suna duba kayan Ashraf yashigo.

Shima bin kayan da kallo yayi don besan dasuba.

Saida ya zauna suka gaisa sannan Ummy tafara mashi qorafin kayan sunyi yawa, anan ya nunamasu shi bema San dasuba.

Sosai Ummy taji dadin abinda saudart tayi kuma hakan ya linka soyyayar datake mata ada.

Nan take ta kirata tana mata qorafin kayan sunyi yawa, itadai iyakarta dariya batace komaiba, sai daga baya Ummy tayimata godiya sosai kamar irin uban kayan nan akayimata amma kasancewar duk qanqantar alhairi dadi ke gareshi yasa taji dadi sosai.


Ashraf kau duk wayar dasukayi yana jinsu, sai bin kayan yake da kallo yana mammakin halin saudart.

Meyasa take son ahalinshi? Meyasa bata tsanesu ba kamar yadda ta tsaneshi?
Meyasa take girmama ahalinshi bayan be dauki nata a bakin komaiba?
Ko sau daya be ta6a takawa gidansu ba ko wajen daddy ko mamy da niyyar gaisuwa tun bayan aure, be ta6a zuwa ba bare su saba dajuna amma gashi ita tazama kusan jininsu don yana ganin zallar qaunar dasuke mata dakuma Wanda take masu.

Haka yabar gidan jiki a sa6ule, kwakwalwarshi chunkushe da tunani Kala kala, yanajinshi cikin wani yanayi marar misaltuwa.



Koda ya isa gida har goma takusa, be isketa a faloba kamar yadda yayi tsanmmani.

Kashe wutan falon yayi ya haye sama ahankali.

Kofar dakinta dake rufe ya tsaya yana kallo batareda yasan dalili ba.

Ada babu ruwan shi da dakinta don gar mantawa yake tana nan, amma yanzu jiyake kamar yaje ya bubbuga ta fito yaganta.

Ya Dade yana kallon kofar sannan ya sauke ajiyar zuciya ahankali ya murda handle din kofar dakinshi yashiga jiki a mace.

A ranar haka yaita juye juye yana tunane tunane har barci barawo yayi awon gaba dashi.




Washegari basu hadeba, lokacin data fito harya fita, office dama sai Monday zatayi resuming don haka yau gida zata ta wuni.


Taji dadin zuwanta gida don murna sukayi tayi dasuka ganta kamar su maidata ciki, Suma tsarabarsu ta fiddo musu ta basu sai murna suke.

Anan tayini sukasha firarsu sannan da marece as usual tawuce mall din daddy.

Sosai daddy shima yayi murnar ganinta sai nan nan yake daita ya rasa inda zai sata don murna.

Shima yasha tsaraba danginsu agogo, takalmi, turarruka da sauransu.

Ba ita ta dawo gida ba sai bayan isha'i.


Koda tadawo shi be dawoba don haka hayewarta tayi sama.

Shima kamar jiya saida ya Dade yana kallon kofarta Yanajin inama ta fito daidai lokacin yaganta.

Ya rasa dalilin son ganintan amma kawai jiyake yanason kallon fuskarta, rabonshi da its tun jiya amma jiyake kamar yayi wata be ganta ba.


Saida yagaji da tsayuwa sannan yasa hannu yana shafa kanshi ahankali

"Ya rabb, take it easy on me" yafada yana kallon kofar again, sannan yayi ajiyar zuciya ya bude nashi kofar yashige.




Agurguje🙏



Yau Monday.

Rabon da Ashraf yasaka saudart a idanu tun ranarda suka dawo daga Spain.

Yau kwana hudu kenan, tun yana daukan abinda yakeji a wasa har abin yafara bashi tsoro.

Sosai yabi ya sussuce don ma miskiline shiyasa ba'a ganewa amma shi kadai yasan abinda yakeji.

Gashi gida daya suke amma miskilancinshi ya hana yaje wajen ta yaganta don gani yake hakan kamar zubda ajine.


Itakau saudart har mancewa take ma dashi don a ranakun nan tashiga busy ba kadanba, shi kadai ke haukanshi don wani sa'in mancewa takeyi da wanzuwarshi.



Tunda wuri ya shirya yau yawuce office badon komaiba sai don yaganta, he was glad cewa finally zai ganta tunda dole yau tazo aiki.

Haka yaci gayunshi cikin grey suit Wanda yayi bala'in amsarshi sannan yafice.


Saidai me? Yana zuwa company wani mummunar labari ya riskeshi Wanda yayi matuqar girgizashi.



Yayi parking din motarshi ya hayo sama cikin nishadi da Farincikin zaiga muradin idanunshi.

Saida ya kalli empty office dinta yaga wayam batanan sannan ya kalli agogon hannunshi yaga duka duka 7:45

Murmushi yayi yana shafa kanshi ganin uban safkon dayayi saboda ganinta.

Office dinshi yashiga Wanda yake qal qal sai zuba qamshi yake.

Be Dade da zamaba saijiyayi an bude kofar batareda anyi knocking ba Wanda hakan yasashi saurin dagowa don duk a tunaninshi saudart ce.


Ganin sadeeq ne yasashi binshi da kallo ganin kamar fuskarshi na daukeda damuwa.

Ahankali sadeeq ya qaraso gabanshi fuskarnan a dagule babu fara'ar nan babu tsokana da shaqiyanci.

"Kai kuma fa lfy?" Inji Ashraf yana kallonshi

Bece mashi komaiba sai wata takardar daya ajiye mashi agaba yana kallonshi.

Ganin hakan yasashi dauka tareda dubawa.

Abinda yagani yasashi zabura tsaye yana ware idanu

"What!" Yafada cikin firgici yana sake ware idanu akan takardar

"Am sorry Ashraf" inji sadeeq asanyaye

"Innalilahi waina ilaihi rajiun, innalilahi waina ilaihi rajiun, innalilahi waina ilaihi rajiun" yafada cikin dimuwa...✍

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)


Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲




053





Jiyayi kaffafuwanshi na Neman Gaza daukanshi yasashi komawa ragwaf akan kujera yana cigaba da maimata innalilahi

"Ashraf please don't take it easy on yourself" inji sadeeq yana Qarasowa wajen shi yana dafa kafadarshi

Kasa magana yayi sai kallon takardar dayakeyi

"Sadeeq how come? Garin yaya hakan yafaru?" Ya tambaya cikin surewa

"Destiny.. Ashraf qaddara ce, please kayi tawwakali, Allah shine me badawa kuma mai amshewa, shiya hallici riba da faduwa" inji sadeeq cikin tattausan laffazi

"Sadeeq kasan millions nawa nayi asara? Why? Why me?" Yafada yana dafe kai zuciyarshi na wani irin quna

"Kayi hqr Ashraf, bakai kadai kayi asara ba harda su, remember Rabin kudin ka bada, kaga kenan Suma sunyi asarar, tunda matsayin Suma Rabin kudin sukayi asara" yafada yana dan murza kafadarshi.

Dafe kanshi yayi da hannu biyu ya Dora a desk zuciyarshi na tuquqi

"Why? Jirgin betashi collapsing ba saida ya dauko kayana? Ya Allah wannan wace iriyar qaddara ce?" Yafada cikin matuqar surewa.

"Ashraf please karkayi sa6o, ka dauki qaddara please, wannan na cikin cikar imaninka, qar6ar qaddararka aduk yadda tazo maka" inji sadeeq cikin jimami.

Ringing din wayarshi ce ta katse su.

Kasa dagawa yayi hakan yasaka sadeeq dagawa yasa hands free.


Labari dayane, can su Hussain suka bugo suke fadamashi yadda abin yafaru har jirgin ya jirkice cikin ruwa, kuma ba'a tsira da komaiba.

Ashraf na sauraron su amma yakasa cewa komai har suka gama wayar, he felt soo empty don sosai ya zuba dukiyarshi hundreds of million don aganinshi sana'ar ta samuce.

Sunanan jugum jugum sukaji ana knocking din kofa.


Kamar yadda ta saba knocking uku tayi sannan ta bude ta shigo.

Turus tayi ganin su jigum jigum, hakan yasata Qarasowa ciki ahankali tana kallonsu.

Dauke kai yayi daga kallonta zuciyarshi na tafasa don yanzu besan ganinta musanmman da zuciyarshi ke kitsima mashi wani Abu.

"Good morning" tafada tana kallonsu daga wannan zuwa wannan.

Sadeeq ne yayi qarfin halin qaqalo murmushi ya nunamata wajen zama yana cewa

"Morning miss, please sit"

Zama ta qarasa tayi tana kallon Ashraf daya kauda Kai gefe sannan ta maida kallonta kan sadeeq da alamun tambaya a fuskarta.

"Mr sadeeq, hope everything is ok?" Ta tambaya innocently

Murmushin yaqe yayi mata yana cewa
"Yes miss, da dai sauqi za'ace" inji sadeeq yana Satan kallon Ashraf

"What happened?" Inji saudart

Zai bude baki yayi magana Ashraf ya katseshi da.

"Look keep quiet my friend! Me zaka gayamata Wanda batasaniba? A matsayinta na secretary na ita wannan labarin zai fara riska kafin kowa, so meye na pretending? Kifito fili ki nuna Farincikin dakike aciki mallama, dama abinda kikeso kenan, my downfall, now kinsani, go and celebrate"

"Ashraf..."

"Kaga kyaleni mallam, don't Ashraf me ok? Ba gaskiya bane? Eh! Ki gayamin baki tsaneni ba? Da bakin ki kika fada, kullum kina cikin addu'ar taggayyarata kuma gashi Allah ya amsa, sai kiyita murna, keda kwaddayayyen babbanki, now leave! Kibarmin office dina! Get out of my life!" Yafada cikin qaraji.


Daskarewa saudart tayi inda take zaune.
Tarasa inda maganar shi ta dosa, sosai kanta ya kulle.

"Haba Ashraf? This is wrong..."


"Look mallam ban kasa dakai ba ok? Kacemata tafita before I do something stupid, taje ta gayawa Shamsu tau burinshi yacika!, kufita dukanku!!" Yafada kamar wani sabon kamu.

Saurin miqewa tayi ta dufi hanyar waje cikin sassarfa.

"Damn you!" Sadeeq ya fadawa Ashraf cikin fushi sannan ya maramata baya.





A office ya taddata ta juyama kofa baya.


Shigowa yayi da sallama Wanda hakan yasata saurin goge hawayenta da bayan hannu.

"Miss saudart dan Allah kiyi hqr..."

"It ok" tafada tana juyowa ta kalleshi da idanunta dasuka farayin ja

"Miss saudart wlh baya cikin hankalinshi ne, he's in shock, dazu takarda yazo mana cewa..."


"Jirgin gwalagwalai yayi collapsing ko?" Ta katseshi da hakan

Kallon mammaki yayimata sannan yace

"Kinji labari kenan?"

Jan hanci tayi ahankali sannan tace

"Eh nasani, tun kafin mubaro Spain, nasan jirgin zaiyi collapsing" tafada tana kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login