Showing 117001 words to 120000 words out of 173829 words

Chapter 40 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1137

baby*

Wara idanu tayi tana sake maimaita text din wondering who the sender is.

Tsaki taja ta goge text din sannan tafita tashiga call log takira daddy.

Saida suka dan ta6a fira kadan sannan sukayi sallama kowa ya ajiye waya, tayi addu'ar barci ta shafa sannan ta kwanta.
Sharp sharp barci yayi awon gaba daita don dama tagaji sosai...✍


Ummin fasihuπŸ§šπŸ»β€β™€οΈ


[9/1, 11:13 PM] Hayat: πŸ‘°πŸ»πŸ€΅πŸ»AUREN KWANGILAπŸ€΅πŸ»πŸ‘°πŸ»
(Contract marriage)



083



Washegari yana tashi first thing daya farayi shine duba phone dinshi ko zaiga reply don har mafarki yayi jiya tayi mashi reply din.

Ganin babu komai yasashi ajiye wayar dissapointedly ya tashi ya nufi bayi don daura alwala.

Bayan yan mintuna yafito daure da alwala yana dan yarfe ruwan hannunshi.

Wayar ya dauka yana kallo na yan seconds sannan ya sauke ajiyar zuciya yafara typing din short good morning text yayi sending sannan yajefa wayar a aljihu yafita.


Tana zaune tagama raqa'atainul fajr tana jiran a kabbarta sallar asuba taji ringing din shigowar txt a wayarta dake jikin socket.

Bata bita kanta ba tacigaba da danna counter din hannunta.

Saida tayi sallar asuba tadanyi tilawa sannan ta tashi daga sallayar ta linketa ta ajiye sannan tabi lfyar gado don yau weekend ba batun shirya su abdul makaranta.

Ba ita ta farkaba sai wajajen takwas nasafe.

Brush tashiga bayi tayi sannan tafito ta yafa dan qaramin veil akan rigar jikinta ta zare wayarta gindin chaji ta fita da nufin shiga kitchen.

Tana tafe ta danna power botton din wayarta taci karo da message agaban screen din.

Kallo daya tama number din ta ganeta don the number is too special to forget.

Sliding din wayar tayi wayar ta bude sannan tashiga message din taga ansa

*it is very important to start our day with a positive affirmation, we are the greatest gift of the universe, we are loved and appreciated. I prayed this day will bring you alot of happiness and muslim ummah altogether...SABAHAL KHAIR*

Tsayawa tayi daga tafiyar datake tana qara maimaita saqon again and again wondering waya turomata.

Kamar tayi replying da wanene? Saikuma ta fasa ta goge text din ta qarasa kitchen din.

Mamy ta tadda ciki tana peeling din irish.

"sabahal khair mamy" tafada tana dan rungumota daga baya.

Fizgewa mamy tayi takaimata bugu tai saurin kaucewa tana dariya.

"Ja'ira" inji mamy tana kwafa.

Murmushi saudart tayi tace "yau irish zamuci? I thought abdul yace indomie yakeso"

Harara mamy ta 6allamata
"Don yace ita yakeso shikenan kowama ita yakeso? Idan biyemashi za'ayi kullum ita zamu dinga ci kamar yan yari, idan bazaiciba yabarshi"

Kwa6e fiska saudart tayi
"Kai mamy autan naki?"

Ta6e baki mamy tayi batace komaiba.

"Ni bari to na dafa mashi" inji saudart tanufi inda kwallin indomien yake

"Dadai yafi, dama ke ke qara 6atashi" inji mamy.

Haka suka hada breakfast din tare suna dan fira jefi jefi har suka kammala sannan sukakai dining saudart tawuce sama don watsawa.


Da rana ma saida ashraf yasake turamata text, dukda be iya love text ba but yana qoqari wajen ganin ya rubuta something meaniful and educative, sai text din yake shige da irin quotes dinnan na encouragement.

Shima shiru babh reply, bejin dadin rashin ganin reply dinta amma hakan be saremashi gwiwa ba cos he's determined to fight for her love.


Ataqaice dai kullum da kalan text din dazaiyi mata. Safe, rana da dare.
Kuma duk babu wanda yata6a samun reply dinshi amma hakan be dameshi ba kuma be hanashi sake yimata ba.

Saudart ma a 6angarenta kullum saita karanta text dinnan na wannan special number din.

Kuma kodayaushe kamar tayi replying ta tambayeshi wanene ko wacece sai kuma tafasa acewarta idan mai turowar yagaji ko tagaji da 6oye 6oyen zata bayyana kanta.


A 6angaren sadeeq kuwa yasamu nasarar persauding din suzy tabada number uncle dinta.

Babu 6ata lokaci ya sanar dasu yarsu fa na hospital.

Washegari saigasu, abin dai ba dadin ji don koke koke akaitayi ranar a ward din don labarin daya riskesu gameda diyarsu ba qaramin giggitasu yayiba.

Babu 6ata lokaci suka nemi transfer aka maidasu hospital din garinsu suka tarkata suka koma can.

A 6angaren saudart kau zaune take gidan mamy hankali kwance don har mancewa take dawani aure dake kanta.

Jin duk anyi shiru da batun yasa hankalinta kwanciya sosai tana addu'ar allah yasa a tafi ahakan don itakam tama kasa picturing din yadda zaman aurensu zai kasance a karo nabiyu aranta, gani take this will be worst than wancan zaman.

Mamy kau biris tayi daita dafarko amma ganin kamar abin bewani dameta ba yasa tafara yimata hade hadenta irin wanda tayimata wancan karon

Chanzamata sabbulan wanka tayi ta siyamata masu kyan gaske masu gyara fata takuma sa aka hadamata man shafawa mai hade hade kala kala don kamshin man ma kanshi ya isa kasan ba qaramin hadi aka mashiba sai turarrukan sawa a ruwan wanka data siyamata suma ba'a magana.

Sadda taba saudart su, tsayawa tayi tana kallonsu baki sake don ita ba yarinya bace tasan duk hade haden na menene.

Ganin kallon datake musu yasa mamy hade rai tabata umarnin takwashe tawuce dasu kuma daga yanzu suzama na amfaninta.

Babu musu takwasa tafita tana turo baki don ba haka tasoba.

Babu yadda ta iya haka tafara amfani dasu, saidai tun amfani na farko datayi dasu taji sun bala'in yimata don idan tagama wani cool qamshi takeyi mai sanyin gaske wanda hakan yasa taji takamu da qaunar kayyayakin don dama ita ma'abociyar son qamshice.

Can kuma mamy ta tsiri yimata ferfesu duk daren allah bazata bari ta kwantaba saita sha farfesu da pure milk sannan ta kwanta sai kuma fruit datake yawan tilasatata ci don duk ba'a son rantaba take ci dondai bata iya yiwa mamy musune sai jitayi dama zamanta tayi can wajen daddy da duk hakan be faruba.

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–


Yau thursday, suna zaune a falo dukkansu mamy na waya, saudart kuma da abdul da habeeb na baje qasa suna buga game, su aminu kau basu gidan suna gidan granny (mamansu Abba)

Dan ihu habeeb yayi ahankali gudun kar mamy dake waya taji yayiwa saudart gwalo yana maida fuskarshi puppy face.

Kallon juna saudart da abdul sukayi suka 6ata fuska tare.

Dauke papern game din abdul yayi ya cikwikwiyeta yana cewa
"Dama don kaga kai kadai ka iya shiyasa ka nace ayi to munfasa mu buga ludo"

Dariya habeeb yafashe daita yace
"Nadaiyi winning dinku, taar! Imagine ku biyu akan ni daya amma naciku 5:0 shame!!"

"Don dai bamu iya bane yaro da shi kadai ya isheka" inji saudart tana harararshi

"Me wannan ajebon ya iya banda shirme?" Inji habeeb yana fashewa da dariya don ya qule abdul

6ata fuska abdul yayi ya kalli saudart kamar zaiyi kuka.

"Habeeb banson wulaqanci, mind yourself" tayi warning din habeeb tana gallamashi harara.

Sunkuyar dakai yayi yana dariya qasa qasa ganin yadda abdul din keta rau rau da idanu hawaye harsun taru a idanun.

Sallamar megadi ne ya katsesu.

Duk kallon kofar sukayi harda mamy da tagama wayar sai danne danne datakeyi.

"Habeeb get the door" inji mamy tana maida kallonta akan wayarta.

Tashi yayi yawuce yayinda saudart ta ciro wayarta zata shiganma abdul game din ludo kamar yadda yace.

Adan jima kadan saiga habeeb yadawo dakin.

"Mamy baqine" inji habeeb

"Who?"

"Don't know sundaice inzo ince zasu shigo gaidaki"

Kallon juna saudart da mamy sukayi sannan mamy tace "ok saudart jeki daukomin mayafi na, abdul tattara rubbish takardun nan kayi sama"

Tashi saudart tayi tanufi upstairs dakin mamy while abdul ya tattara takardun games din hannunshi riqeda wayar saudart dayake game daita.

Can saiga saudart da mayafin mamy ta bata tajuya takoma sama abinta.

Kallon habeeb tayi dake tsaye tundazu bayan tagama yafa mayafin tace
"Jeka shigo dasu"

"Tou" yafada yajuya don shigowa dasu din.


Ajikin motarsu ya taddasu tsaitsaye, qarasowa yayi yana murmushi yace
"Mamy tace kushigo"

Shafa kanshi sadeeq yayi yace "alright good boy muje"

Habeeb yayi gaba sadeeq yabishi.

Saurin kamo hannunshi A.A yayi yana wiqi wiqi da idanu kamar marar gaskiya.

"What" inji sadeeq daya juyo yana kallonshi cikin takaici.

"Please sadeeq, am shy" yafada cikin marairaicewa

Tsaki sadeeq yaja cikin takaici yace
"You know what? Idan najuya nabar gidannan natafi kenan wlh, wannan wane irin wulaqancine, ka tilastamani rakoka kuma kazo kana behaving annoyingly? Haka kabani kunya wajen daddy agidanshi dazu, kasan bazaka iya zuwaba ka jiji6oni?" Yafada yana harararshi

"Mtcheew yanzu am sorry muje, wai maimakon ya kwantar ma mutum hankali saiya rufe mutum dafada"

"Hankalin ya dade be tashiba, yafi rocket tashi" inji sadeeq.

Wuceshi ashraf yayi cikin fushi yanufi habeeb da harya kai bakin kofa.

Binshi shima sadeeq din yayi yana harararshi yana gunguni qasa qasa.

Koda yakai bakin kofar kasa shiga yayi saida yajira sadeeq ya iso sannan.

Harara sadeeq ya gallamashi sannan yasa hannu yatura kofar ahankali yana sallama.

Shima ashraf daduk yake very nervous ya maramashi baya shima yana sallamar.

Akan kujera suka tadda mamy zaune fuskarta asake tana amsa sallamarsu tareda yimusu sannu dazuwa.

Ahankali suka qaraso cikin falon kansu a sunkuye suka zauna kan carpet suna fuskantar mamy.

"A'a? Ku zauna kan kujera mana"

Duk murmushi sukayi kansu a sunkuye suka shiga gaidata batareda sunyi yadda tace dinba.

Amsa musu tashigayi tana kallonsu most especially ashraf don kallo daya tayimusu tagane kosu waye.

"Ya mutanen gida? Ya aiki?" Inji mamy

"Alhamdulillah, yasu Abba" inji sadeeq yana murmushi shikau ashraf kunya ta hanashi cewa komai sai sunkuye kai dayayi kawai yana sauraronsu.

Amsamasu tayi da yana wajen aiki be dawoba.

Saida suka gama gaishe gaishen sannan mamy ta tashi tsaye ta kalli habeeb dake zaune can gefe yana qoqarin chanza channel ta 6allamashi harara a fakaice tace
"Zoka kaisu falon baqi"

Tasowa yayi yazo wajensu ya tsaya, tashi duk sukayi suna yimata sallama tana amsawa cikin fara'a tanacewa su gaidamata Hajiya fateema idan sun koma sannan itama tajuya tahau sama bayan sunfita.

Wani gauron ajiyar zuciya ashraf ya sauke bayan sun fito yana dafa chest.

Harararshi sadeeq yayi yace "matsoraci kawai"

Shima hararar ya rama batareda yace komaiba sukabi habeeb dake gaba don kaisu falon baqin.



Kwankwasa kofarta da akayi yasa tadago daga linkin kayan datake, kafin tace komai har mamy ta bude kofar tashigo.

Murmushi saudart tayi mata tace
"Har baqin sun tafi?" Tafada tana ajiye zanen data linke.

Fuska ba yabo ba fallasa mamy tace
"A'a kije suna falon baqi and kitafi da refreshment"

Dan waro idanu saudart tayi tace
"Nikuma mamy?" Tana nuna kanta da yatsa.

Wata harara mamy ta gallamata tace "no ni, zakiyi abinda nacene ko kuwa? And change into something more decent kuma karkiyi wasting dib time" tana kaiwa nan tafice tabarta sake da baki.

Asanyaye ta maida kayan data linke cikin sip dinta sannan taciro wata dark blue din hijab doguwa ta dora kan kayan jikinta tadan gyara fuskarta ta fesa cool turare sannan tafita.

Bata tadda kowaba falo hakan yasa tanufi kitchen tadauki tray ta bude fridge tafiddo drinks uku ta daura akai da cups ma uku don batasan adadin baqinba ta debi snacks ma sannan tafito kitchen din tanufi falon baqi.

Tafiya take tana tunani nason gano su wanene, haka kawai taji beating din zuciyarta na chanzawa. She feels very nervous and uncomfortable.

Koda takai bakin kofar saida tadanyi jimm na yan daqiqu sannan ta daga hannu ahankali tayi knocking sannan ta tura kofar bakinta dauke da sallama.

Sadeeq kadai ya amsa sallamar while ashraf da muryarta ta saukar mashu da wata iriyar kasala ya kafe kofar da idanu cikin son ganin ta inda zata 6illo.

Anitse tashigo dakin kanta qasa tana sake maimaita sallamar datayi hannunta riqeda tray.

Lumshe idanu ashraf yayi akanta ya bude jin wani sanyi na ratsa zuciyarshi by the mere sight of her...✍


Ummin fasihuπŸ§šπŸ»β€β™€οΈ
[9/1, 11:13 PM] Hayat: πŸ‘°πŸ»πŸ€΅πŸ»AUREN KWANGILAπŸ€΅πŸ»πŸ‘°πŸ»
(Contract marriage)



Story written by Ashaanty loveπŸ’–
(Ummin fasihu)




084



Wannan karon ma sadeeq yasake amsa mata sallamar cikin fara'a.

Dumm.. gabanta yafadi jin muryar sadeeq wanda hakan yasata dago idanunta don ganin ko kunnenta ke decieving dinta.

Caraff suka hada idanu dashi wanda dama tunda tashigo idanunshi ke kafe daita.

Saurin janye idanunta tayi gabanta beating sosai don ba qaramin kashemata idanu idanunshi sukayi ba, there is something about his eyes dake sata jin takasa kallonsu na lokaci mai tsayi.

Ahankali tashiga takowa falon kamar mai kirgan steps making extra sure bata harde ba don sosai take jinta a takure jin piercing idanunshi akanta.

Saida tafara ajiye tray din hannunta akan centre table din dakin sannan takoma can kujerar dake fuskantarsu ta zauna ta sauke kai qasa tana wasa da zira ziran yatsun hannunta.

"Good afternoon ranki shi dade" inji sadeeq cikin barkwanci.

Dan murmushi tayi na kunya don sosai takejin kunyar sadeeq yanzu musanmman idan ta tuna abinda yafaru haduwarsu ta qarshe

"Ina wuni?" Tafada ahankali batareda ta dagoba.

"Lfy lau, ya gida ya hutu?" Yafada yana satar kallon ashraf daya maidata mirror tsabar kallo

"Alhamdullilah" ta amsa a taqaice

Dan shiru falon ya dauka ganin hakan yasa sadeeq miqewa ya nufi centre table din yana cewa
"Bari kuga"

Dan daga idanu tayi qasa qasa tana kallonshi taga ya dauki drink daya ya debi snacks din kadan a wani dan plate sannan ya miqe.

"Tohm ni nayi nan" yafada yana nufan kofar fita ya fice.


Dakin ne yadauki wani deadly silent, bakajin ko kwakwaran motsi aciki.


Kanta haryanzu na aqasa tana fidgeting din yatsunta duk jinta take atakure kamar tasa kuka takeji.

Shikau maidata t.v yayi yana kallo, Allah knows yayi missing dinta, jiyake kamar yayi shekaru be gantaba, jiyake kamar su dawwama ahakan tana gabanshi yana kallonta, yarasa dalili kawai shidai yanajin wani irin farinciki ne idan yana kallonta.

Everything about her is different, fuskarta, shigarta, qamshinta, muryarya, everything! He's in love with everything about her.


Muskutawa tayi ahankali tadan gyara xama uncomfortably, allah ma yasan a mugun takure take, jitake kamar ta tashi ta fita, me yake nufi da yazo ya tusata gaba kamar mirror yana kallo? Meya kawoshi ma at the first place?

Ahankali ta dago idanunta da niyyar satan kallonshi

Gaurayewa idanunsu suka sakeyi a karo nabiyu ya sakarmata one of the coolest smile dinshi.

Saurin sauke idanunta tayi qasa tana dan runtsesu cikin kunyar hada idanun dasukayi.

Ita dayasan yadda takeji idan yana kallonta da wannan idanun da ya bari, kwata kwata bata sonsu, suna sata jin wani iri.

Wannan zaman nasu ya tina mata da zuwan dayayi gab da bikinsu, exactly kamar irin wannan saidai wancan bemata irin wannan kallon hasalima hankalinshi nakan waya while yanzu yawani tsareta da idanu kamar tsohon maye.

"Good afternoon" yafada cikin wani irin cool voice wanda hakan yasata dan dagowa da nufin satan kallonshi.

Hada idanu sukayi again tayi saurin janyesu ta kalli gefe sannan ahankali almost in rada tace
"Same"

Murmushi yayi sannan ya miqe yafara takowa wajenta.

Bugun zuciyarta ne yafara qaruwa jin kamar takunshi na kusantota.

Daidai centre table din ya tsaya ya dora hannu akan drink daya yana kallonta, sannan ahankali yace
"Should I?"

Qin dago kanta tayi ta kalleshi don batason qara hada idanu dashi ta daga kai ahankali tanajinta duk a takure.

Murmushi yayi ya bude drink din idanunshi a kanta ta tsiyaya kadan a glass cup din sannan yamaida ya rufe ya dauki glass cup din.

Maimakon yakoma mazauninshi saiya dawo kujerar dake gefenta ya zauna irin zaman balancing dinnan daya riga ya bi jikinshi ya kai cup din abaki yana kur6a idanunshi akanta.

Ji saudart tayi kamar ta dora hannu aka taita ihu, jitayi tafi dazu takura dukda akwai dan tazara tsakanin kujerun nashi.

Wani haushi takeji na kafeta da idanun dayakeyi, wannan kallon ko maye albarka, why zai tisata gaba kamar t.v ya takurata da wadannan mayun idanun nashi?

Dan kawar da kai tayi dayan gefen fuskarta a hade tanajin kamar ta tashi tabar dakin.

Haka suka qaraci zaman nasu in silent kowa da saqe saqen dayake a zuciya. Basu san iya lokacin dasuka daukaba ahakan sai jisukayi anyi knocking din kofa wanda hakan yayi sanadiyyar dawowar dukansu daga dogon tunanin dasuka lula.

Da sallama sadeeq yashigo riqeda bottle din drink dinshi dayasha rabi.

Dan ware idanu sadeeq yayi ganin ashraf yayi changing din wurin zama sannan yadan saki murmushi ya ida qarasowa.

"To love birds, time up. Naga alamar idan aka biyemuku kuna iya kwana anan" yafada cikin barkwanci.

Dan ta6e baki saudart tayi batareda ta dagoba don dama a qagare take sutafi ko tajita normal.

"To ai saika tashi mallam, ranki ya dade zamu ruga kauyenmu"

Dan dagowa tayi ta kalleshi sannan ta sadda kai tana cewa "allah ya tsare"

Amsawa yayi da amin ya kalli ashraf dashima daidai ya kalleshi ya daga mashi gira alamun yatashi su tafi ko?

Harara ya gallamashi sannan ya miqe daga xaunen dayake hakan yasa sadeeq ficewa daga dakin.

Takowa yayi har gabanta yana kallonta.

Bugun zuciyarta yaqarayin saman jin tsayuwarshi akanta ga kaffafuwanshi datake gani agabanta kasancewa qasa take kallo.

Ahankali ya duqa gabanta yana kallonta, saurin ja da baya tayi ta shige ma kujerar tana ware manyan idanunta akan fuskarshi a mammakince don kusancin nasu yayi yawa don har tanajin saukar numfashinshi.

Daga glass cup din hannunshi yayi ya miqomata yana murmushi.

Kasa ko motsi tayi sai kallonshi datake cikin mammaki tana tunanin anya lafiyarshi lau?

Kamo hannunta yayi ya sakamata cup din aciki ya hada yariqe tenderly yana mata wani irin kallo mai tsayawa a zuciya.

Saurin sauke idanunta tayi qasa tana qoqarin zame hannunta acikin nashi amma takasa hakan yasata lumshe idanu don wani iri takeji har cikin 6argonta

"Thank you" yafada cikin rada yana kallon yadda ta limshe idanu taqi budesu ga zara zara lashes dinta dasuka hade waje daya kamar na fixing

Matso da hannun yayi saitin bakinta wanda hakan yasata saurin bude idanu tana kallonshi kamar zuciyarta xata fado tana qoqarin janye hannun.

Ahankali yayi placing din light kiss kan yatsunta dake riqeda cup din batareda ya janye idanunshi daga fuskarta ba wanda hakan yasata saurin maida idanun ta rufe gabanta na faduwa sosai.

"I love you" yayi wishpering cikin wata iriyar cool voice.

Sake tamke idanunta tayi zuciyarta na bugu sosai tanajin kanta na juyamata ahankali.

Ganin kamar hannunta nadan 6ari yasashi zare glass cup din hannun nata ya ajiye sannan ya saki hannun nata tayi saurin maida hannun cikin hijab still idanunta arufe.

"Take care of yourself... for me" yafada cikin rada in an extra cool voice wanda saida taji tasirin hakan har cikin kwanyarta.

Miqewa yayi ahankali yafara tafiya da baya baya yana kallonta.

Jiyake beson tafiya, jiyake kamar yatafi daita, jiyake be gaji da ganinta ba amma he have no choice, dolene yabi komai ahankali if he really want her, zai jira, zai jure harzuwa lokacinda zayayi nasarar mallakar zuciyarta, zai cigaba da hqr har lokacinda zata koyi sonshi, so mai tsanani irin wanda yake mata.

"Bye" yafada ahankali daidai yakai kofa sannan yajuya yafita.


Ta dade ahalin datake ciki, takasa koda bude idanunta ne bare tayi wani kwakwarrar motsi.

Jitake kamar haryanzu yana gabanta, jitake kamar haryanzu yana riqeda hannunta, jitake kamar haryanzu watery lips dinshi na kan hannunta. Jikinta haryanzu yakasa dawowa daidai, abinda yafaru yakasa barin brain dinta.

Jin an dafa kafadarta yasata saurin bude idanu a zabure.

Ganin habeeb ne yasata sauke ajiyar xuciya tana dan waige waige.

"Mamy tace what are

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login