Showing 138001 words to 141000 words out of 173829 words

Chapter 47 - Auren Kwangila Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

1131

tayi faca faca tana kallonshi kamar zatayi kuka.

"Kizo mutafi, let someone finish it, ina baby ma tukunna"

Banza tayi dashi tafara qoqarin juye kingin smoothie din

Kamar daga sama taji muryar ummy a falo tana cewa
"Daughter! Daughter!! Wai haryanzu girkin ne?"

Ware idanu tayi tayi saurin juyowa.

"Yauwa gatanan tama sauko, bari inje inji dalilin sa matata aiki" inji ashraf yana nufar kofa.

Batasan ya akayiba sai gani tayi tasha gabanshi gabanta na mugun faduwa, cak ya tsaya yana kallonta kawai

Girgiza mashi kai tashigayi tana waiwayen kofa.

"Please ka rufamini asiri karta ganka anan, na bani" tafada tana zare idanunta a tsorace

Tsayawa yayi yana kallonta kawai ganin yadda tawani tare hanya tana leqen baya

"Wannan trolleyn fa? Daughter! Daughter!!" Suka sakejin muryarta tana nufo kitchen din.

Qara ware manyan eyes dinta tayi tayi saurin kamo hannunshi batareda tasan tayiba tana cewa
"Innalillahi, wayyo banso tazo taganka, please hide"

Tafada tana riqeshi sosai.

Wutar ashraf ne ta dauke diff jin yadda ta kama mashi hannu sosai kamar her life depend on it.

Bude baki yayi zaiyi magana tayi saurin saka dayan hannunta ta dode mashi baki tana girgixa mashi kai a mugun tsorave tana jin takun ummy daff da kofa...✍

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️




👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Alhamdullilah am back after almost two Months of vacations, fatan duk nasameku lfy, thank you all for your concern, wani sa'in tsoronma hawa whatsapp nake saboda jaje, amma that's all signs of love you guys got for me, nagode da qauna, Allah ya dorar da zumuncinmu har a aljannatul firddaus (Amin)


Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)




093


Bude baki yayi zaiyi magana tayi saurin saka dayan hannunta ta dode mashi baki tana girgiza mashi kai a mugun tsorace tana jin takun ummy daff da kofa.

Ganin yadda take a tsorace don hannunta dake a bakinshi har rawa rawa yake yasashi janye hannun yace
"Look, I'll hide but on one condition"

Saurin kada mashi kai tayi idanunta na kawo ruwa, idan ummy ta taddashi anan Ai ta banu, Ina zata sa kanta don kunya?

"Zakimin coffee anjima kikawo apartment dina, promise?" Yafada yana dago qaramin yatsar hannunshi alamun su qula

"Yes, promise... Please go" tafada tana turashi a kidime.

Wuff kamar iska haka ya ruga ya la6e a bayan kofar kitchen din yayinda saudart tayi saurin juyawa tana tatta6a abinda ke kan wuta batareda tasan abinda takeyiba.

"Daughter?" Inji ummy data shigo kitchen din

Saurin juyowa tayi tana washe baki cikin yaqe tana fadin
"Na'am ummy" yayinda take yawo da idanunta cikin kitchen din a fake tana son gano inda ya 6uya.

Ganin shi bayan kofa yana dagamata hannu yasa gabanta faduwa tayi saurin janye idanunta ta maida kan ummy dake bubbude pots din

"What?" Inji ummy ganin abinda take girkawa.

Qara Satan kallon kofar saudart tayi a tsorace don tasan da ummy ta juyo dolene ta ganshi.

Ganinshi tayi yafita sai leqo kai dayake kamar kusu mai shirin sata.

Narke fuska tayi tana kallonshi pleadingly alamun please ya fita.

Kashe mata ido yayi sannan yayimata alamun karki manta da deal dinmu

Ganin ummy na niyyar juyowa yasashi saurin ficewa

Saida Ummy tabi kofar da kallo jin kamar taji motsi awajen sannan ta maido kallonta kan saudart daketa raba idanu kamar marar gaskiya.

"Dole kiyita zare idanu Ai, I told you kiyi light food shine kika tarki wannan uban girkin ko? Besides Ina baby danace ta tayaki?"

Shagwa6e fiska saudart tayi tana cewa
"Ummy barci fa take and na tadata taqi tashi shiyasa na kyaleta"

"Ai kinyi daidai, zanga Wanda zai sake bari gobe ki shiga kitchen, yanzu kwashe naga duk sunyi Bari naje ni na tadata narasa wane lalaci ke damun Baby kwanan, mutum kullum ba abinda ya iya sai kwanciya kamar mai?" Tafada tana nufar hanyar fita

Ajiyar zuciya saudart ta sauke da qarfi bayan fitarta sannan ta juya tana kashe gas din tana hamdala a zuciyarta


Jin takun ummy na tunkaro falon yasashi saurin gyara zama ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi yana dannawa.

Sosai ummy tayi mammakin ganinshi amma sai ta basar tanufo cikin falon tana tsuke fuska

Dagowa ashraf yayi daga wayarshi ya kalli saitin ummy dake tahowa ya Dan sakarmata murmushi yana maida wayar a aljihu.

Zama ummy tayi tana kallonshi tana qara nazarinshi ganin yadda fuskarshi ke fayau bawani alamun damuwa unlike jiya ranan dayabar gidan rai 6ace.

Zamewa yayi qasa ya gaidata cikin girmamawa kamar yadda yasaba.

Amsawa tayi ba yabo ba fallasa tana dauke kai don tayi tunanin maganar ranan zai sake dauko Mata


Ganin yakoma ya zauna batareda yace komaiba saima maida hankalinshi dayayi a t.v yasata cewa
"Yaushe kashigo?"

"Ban dadeba" ya amsa a gajarce

"Wannan fa? Na wanene?" Tafada tana nuna trolley din dake tsakar falon

"Oh.. Nawane, yanzu zan wuce dashi ciki" yafada batareda yanuna yaga kallon datake Mashi ba.

"Naka? Tafiya zakayi?"

Dan murmushi yasaki ya girgiza kai yace
"A'a kayana anjima zan kaisu apartment dina"

Sai yanzu tagane inda ya dosa.

Lallai kenen shima yadawo nan da zama yake nufi ko me?

Aikau in yasan wata besan wata ba.

Bata qara cemashi komaiba itama ta maida kallonta kan t.v don Tama fasa zuwa tado baby din tinda saudart na kitchen


Haka suka cigaba da zaman kurame har saida sukaji motsin saudart ta fito daga kitchen din hannunta dauke da warmers.

Caraff suka hada ido tayi saurin dauke kai tanufi dining tana doddorawa akai

Binta da kallo yake harta gama doddorawa takoma kitchen din

Janye idanunshi yayi daga binta da kallon dayayi ya maida kan ummy, cikin taushin murya yace
"Ummy ina maid dinmu ne?"

Batareda ta kalleshi ba tace
"Ta tafi kasuwa"

"Baby fa?"

"Tana sama" ta amsa a taqaice

"Doing what ummy?"

Dagowa tayi ta gallamashi harara tace
"Bansàniba"

Dauke kai yayi yana dan turo baki sannan qasa qasa yadda yasan zataji yace
"Kowa nata hutawa sai matata akabari da aiki"

Dan dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta janye idanunta ta cigaba da kallonta


Haka saudart taita fitowa tana jera dishes din dukda duk acikin qarfin hali takeyi saboda yadda take junta very uncomfortable saboda kallon dayake binta dashi

Saida tagama komai sannan ta qaraso falon adarare

Dagowa ummy tayi ta kalleta cikin fara'a tace
"Yauwa Yar albarka, kin gama ko?"

Murmushi tadan Saki tana sinne kai

"Sannu to, kije kiyi haramar zuhr naji anata Kira"

Kada kai tayi kawai, kamar zata wuce saikuma tadan juyo saitin ashraf daya maidata mirror tundazu.

Janye idanu tayi sanaddiyar hada idon da sukayi, cikin calm voice dinta tace "ina yini" tana dan russunawa

Wani farinciki ya ziyarci zuciyarshi nan take hakan yasakashi sakarmata murmushi yana cewa
"Lfy.. Sannu da aiki"

Bata amsa ba sai wucewa datayi tana jinta so uncomfortable saboda shigar dake jikinta dukda yanzu ta yafa gyalle Wanda dama aiki yasata cireshi a kitchen.

Saida ta haye sama sannan ummy ma ta tashi itama ta haura saman batareda tace mashi komaiba

Murmushi yayi sannan shima ya tashi ya nufi trolley dinshi yaja yafice yanufi apartment dinshi yana tafe yana cilla keys dinshi sama yana cafewa zuciyarshi fess.

Da sallama yashiga dakin jaye da trolley dinshi

Dakin bawani datti don ana gyarashi koda bayanan bare dama yan kwanaki yayi rabonshi da dakin.

Ajiye trolley din yayi kawai yanufi bathroom ya dauro alwalla a gurguje yafito don har Ana shirin kabbara sallar

Koda aka gama sallar yadan jima be dawoba.

Lokacin daya dawo duk suna dinning da alamu abinci sukeci.

Qarasowa yayi cikin takunshi na qasaita idanunshi kafe da saudart da kanta ke qasa tana jujjuya spoon dinta a abinci

Zuwa yanzu ta chanza shigarta zuwa deep blue Arabian gown buba wadda hannun yadan tsuke a daidai gwiyagun hannayenta, sai adon fararen tutar flowers da aka jera round din wuyan rigan, sai veil din rigar data yafa simply akanta.

Tayi kyau sosai dukda bawani kwalliya tayiba amma glowing din fatarta kadai abin kallone da sha'awa.

Saida ya qaraso sannan ya janye idanunshi akanta yana jan kujerar dake facing din saudart baya sannan ya zauna.

Dagowa yayi suka hada ido da baby dake shirin kai spoon abaki, wata uwar harara ya gallamata yana kada kai

Sadda kai tayi tana kumburo fuska

"Anan kikafi afki ai, a girka kici" yafada yana ziran plate at the same time yana cigaba da hararanta.

Qara turo baki tayi tadan saci kallon ummy taga abincinta kawai takeci hakama saudart dako dagowa bataiba

Hakan yasa itama maida kanta ga abincin tanaci a sanyaye don saitaji duk ya ficemata akai duk dadinshi.

Itadai saudart tin shigowarshi bata yarda taqara dagowa ba don tanajin yadda idanunshi ke yawo akanta abin har mammaki yake bata, kodai ya manta ummy na a dinning din ne.

Bata ida tsinkewa da al'almarinshi saida yaji yace
"dear serve me mana, yunwa"

Shiru dining din ya dauka don they're all confused sun rasa dawa yake

Gaban saudart yafadi jin yasake cewa
"Kinji wifey? Am hungry" ya qarashe maganar a shagwa6e kamar yadda yakema ummy

Daburcewa saudart tayi yayinda wata matsananciyar kunya ta lullu6eta.

Dagowa tayi ta saci kallon ummy taga kamar ma batasan dasuba don abincinta kawai takeci.

Hakan yasata maida kallon akanshi, kashe mata ido daya yayi sannan yace "kinji?"

Rasa inda zata sa kanta don kunya tayi, tashi tayi kamar wanda aka zarewa lakka tana Satan kallon baby Wanda ta sadda kai tana qumshe dariya da wutsiyar ido sannan ta bude warmern fried rice din kamar zatayi kuka

Turo mata plate din daya zara yayi yana qoqarin danne dariyarshi ganin yadda tayi da fuska da yadda take zuba abincin a daburce

"Yauwa ya Isa hakan" yafada yana janyo plate din sannan ya turamata glass cup daya yana cewa
"Saura drink"

Bata kalleshi ba ta dauki glass din ta bulbula smoothie din dayayi gwanin kyau aciki sannan ta zari wani glass din ta zubamaahi ruwan gora masu sanyi.

Duk tanayin wadannan ne a nonnoqe don wani irin kunyar ummy takeji wanda bata ta6a jiba.

Komawa tayi ta zauna tanajin kamar ta nitse don kunya

Shikau ko ajikinshi saima spoon daya saka a plate din ya debi spoon guda yakai baki.

Lumshe idanu yayi sakamakon karon da abincin yakaimashi harcikin qwalwa, abincin is so delicious kamar yadda look dinshi is so salivating.

"Hummm" yafada yana chewing din abincin ahankali ido a lumshe irin yakaimashi Karo dinnan.

Kasa qumshe dariyarta baby tayi wannan karon saida tafito tayi saurin dafe baki tanayi

Atare suka wurga mata harara ta gefen ido, fuskar saudart kamar mai shirin kuka, jitake kamar taita ihu don takaici

Itakau ummy ko alamun tasan abinda ke faruwa bata nunaba saidai can qasan ranta mammakin rashin kunyarshi take.

Cigaba da cin abincin shi yake hankali kwance yana wani lumlumshe idanu yana humming alamun yana enjoying din abincin

Baby kau dakyar take cin abincin saboda dariyar dake cikinta, musanmman idan takalli fuskar saudart dake blushing don kunya, Allah Allah take su ke6e ta amayar da dariyar cikinta


Saudart kau jitake kamar ta tashi tabar dining din saidai babu dama don tun farko saida ummy ta bigemata warning akan saita cinye wanda ta zuba, gashi ko Rabi bata ciba don tinda yashigo sai cin abincin yazama shiririta


Haka taita tsakurar abincin kanta a qasa feeling very uncomfortable kafin daga bisani ummy ta dauki ruwan gabanta tasha ta goge baki da tissue sannan ta miqe batareda tacema kowa komaiba.

Dan murmushi ashraf yasaki ganin tabar wajen tama hayewarta sama.

Sannan ya maido kallonshi kan baby data nutsu sosai yanzu tana cin abincinta.

Tamke fuska yayi sosai yana kallonta, hakan yasata sauke spoon din hannunta tana kallonshi idanunta rau rau

"Get lost" yafada fiska ba alamun wasa

Tashi tayi da sauri tana daukar plate din abincinta tafice daga dinning area din kamar zatayi kuka.

Saida yagama rakata da mugun kallo sannan yamaido dubanshi kanta.

Haryanzu kanta sadda yake sai jujjuya spoon take acikin abincin

Dora hannayenshi yayi saman table din ya buga tagumi tareda zubamata hazal eyes dinshi kamar yasamu mirror....✍️


Ummin fasihu🧚🏻‍♀️




[11/30, 7:06 PM] +234 909 007 1867: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻


Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)



094



Qin dagowa tayi dukda yadda takejinta a tsananin takure da kallon qurillarshi ya haifarmata.

Qurawa spoon din hannunta idanu tayi tana sauraron zuciyarta data sauya bugu.

"Saudart..."

Lumshe idanunta tayi ta budesu ahankali don taji kiran har tsakiyar kanta

Kallonta yacigaba dayi yanajin wani irin feelings akanta, jiyake kamar su dawwama a hakan

"Saudart..." Yasake kiranta saidai wannan karonma bata ko motsa ba saima hawayen dataji suna taruwa a idanunta wanda ta rasa ko namenene

"Kinyi kyau... Sosai" yafada yana dan murmushi still idanunshi kafe akanta

Still bata motsaba saima battling datake wajen maida hawayen dake neman zubomata wanda haryanzu batasan dalilin zuwansu ba.

Dan matsowa yayi jikin table din wanda hakan yaqara basu kusanci

Cikin muryar rada yace
"Shin wani yata6a fadamiki ke kyakyawace ta qarshe?"

Bejira amsarta ba sai kamo hannunta dake riqe da spoon dayayi ya riqe da hannunshi na dama ya dafe natan dana haggu yana binta da romantic kallo

Lumshe idanu tayi tanajin tsigar jikinta na tashi sosai

Sake qasa yayi da murya yana cewa
"You're the most beautiful creature that ever exist, and am the luckiest man that ever exist for having such glowing dem as my other half"

Dan matsa hannunta dake cikin hannayenshi yayi wanda saida ta sake tamke idanunta saboda yadda zuciyarta tayi zillo

"And I'll continue to thank Allah for granting me such rare, pure damsel with golden heart..."

Gyaran muryar dayaji daga bayansu ya dakatar dashi daga abinda zai sake cewa ya dan waiwayo don ganin waye

Saurin dauke kai tayi daga kallonsu tace
"Ehm.. Dama ummy ke kiran aunty"

Ganin kallon dayake binta dashi yasata saurin juyawa tabar wajen.

Tashi itama saudart tayi kamar wanda dama ke kan qaya ta zame hannunta daga cikin nashi ta gittashi tawuce batareda ta yarda ta dagoba.

Binta yayi da kallo yayi harta haye sama sannan ya saki slight smile ya maida kanshi akan abincin shi yanaci cikin nishadi.


Saudart kau tafiya take amma jinta take kamar ba a hayyacinta ba take don saida tayi dagaske don kartayi missing din steps tasamu ta ida haurawa sama

Direct dakin baby tashige don bazata iya facing din ummy ba ayanzu.

Taddata tayi zaune gefen gado ta jingina da jikin gadon waya kare a kunnenta.

Ganinta yasata katse wayar tareda sakin ihu mai tafe da dariya.

Saudart ko gefenta bata kalla ba ta zagaya ta dayan 6arin gadon ta kwanta tareda juyamata baya.

Dariya baby tasake fashewa dashi tana matsowa kusada ita tace
"Wuuuu! Love birds, gaskiya abin fa yabada show, wannan soyewa haka? I never knew yaya sharukhan ne sai yau, ca6 gaskiya ne da akace fear silent people, ca6!"

Itadai saudart ko iskar daya kwasota bata kulaba don ko juyowa batayi ba saima lumshe idanu datayi tana sauraron bugun zuciyarta wanda be dawo normal ba


Haka baby ta tisata gaba da tsokana iri iri harta gaji don kanta ta shafamata lafiya.

Saudart bata tashiba saida taji ana kiran sallar la'asar sannan ta lalla6a ta tashi ta dauro alwalla tazo ta sauke farali sannan tasake komawa kan gadon.

Itadai bazata iya fadin taqamaimai abinda takeji ba saidai tana jinta haryanzu ba daidai ba ga magangganunshi daketa eoching a kunnenta plus qamshin turarenshi daya kasa barin hancinta, wadannan suka taru suka haifarmata kasala tayi lamo a gado bata ko son tashi.

Haka ta qarasa wuninta a daki don kunyar fitowa ta hadu da Ummy take plus batason haduwa da ashraf dukda batada tabbacin haryanzu yana gidan don ita batasan da zancen dawowarshi gidan ba


Zaune take kan sallaya wanda tagama sallar isha'i akai wayarta a hannu tana yan danne dannenta.

Jitayi an bude kofa amma taqi juyowa don atunaninta baby ce

"Daughter"

Saurin juyowa tayi jin muryar ummy saikuma ta maida kanta qasa tana gaidata a kunyace.

Amsawa tayi fiska a sake tana cewa
"Ya baki fito dinner ba?"

Tashi saudart tayi daga kan sallayar tana cewa
"Yanzu zan fito ummy"

"Ok" ta amsa a taqaice tana fita

Ninke sallayar tayi ta maidata ma'ajinta sannan ta zira takalmin soso ta fito.

Ahankali take taka stairs din tana tunanin yadda zata iya zama taci abinci cikin sakewa agaban ummy don haryanzu kunyarta takeji sosai, jitake kamar tace aqoshe take saidai tasan ba dama.

Qarasa saukowa tayi ta nufi dining din kanta qasa

Jin masculine scent din turarenshi yasa gabanta faduwa don she didn't expect it

Dagowa tayi ta kalli saitinshi saita hangi bayanshi kasancewar yaba hanyar shigowa bayane

Maida kanta tayi qasa tana mammakin why yau ya Dade betafiba, koko dawowa yayi? Tabbas dawowa yayi duba da chanza shigar dayayi don kayan jikinshi bana dazun bane.

Ida qarasowa tayi daukeda sallama a bakinta

Duk dagowa sukayi suna amsamata tareda zubamata idanu.

Jan kujerar dake kusada baby tayi ta zauna tana dan murmushin yaqe.

Sannu tayi ummy tareda amsa sannu da baby ke mata sannan ta cije ta dago dakyar ta kalleshi

Kamar kau yadda tayi tsammani idanunta suka fada cikin nashi don dama ita yake kallo

Janye idanunta tayi sannan ahankali ta gaidashi

Amsawa yayi yana sakarmata murmushin shi mai tsada, ba qaramin dadi yakejiba idan ta gaidashi, jinshi yake so uptop

Serving din kanta tayi sannan takoma ta zauna tafaracin abincin a hankali

Shiru dining din ya dauka idan ka dauke qarar cokalan daketa haduwa da plate

Yanzun ma kamar dazun atakure takecin abincin don duk motsin dazatayi saitaji alamun idanunshi akanta, ga yawan hada idanun dasuke wanda duk sadda suka hada ido saiya sakarmata wannan cool murmushin nashi, haka dai take tura abincin badon tanajin dadinshi ba don duk a darare takejin kanta.

Ganin taci fin rabi dakyar yasata dagowa ta kalli ummy

Itama ummyn dagowa tayi daga abincinta tana kallonta batareda tace komaiba

Marairaice fiska tayi sannan tace
"Ummy am full" cikin sanyin murya

Ga mammakin ta sai jitayi tace
"Ok daughter you can go"

Dadi taji wanda saida hakan ma ya nuna a fuskarta, daukar glass cup tayi ta sha ruwa kadan sannan ta goge bakimta da tissue ta miqe tareda dan satar kallonshi.

Gani tayi fuskarshi ta nuna alamun rashin jin dadin tashinta


Kauda Kai tayi tabar wajen tana sauke Ajiyar zuciya don Allah yasani a matuqar takure take awajen

Bata jima ba da komawa dakin ba itama baby ta shigo.

Sun dan ta6a fira da baby kafin barci yayi awon gaba da baby

Ganin haka yasata jawo wayarta takoma ta jingina da pillow data kara da jikin gado tashiga danne dannenta.

Sosai tayi missing din laptop dinta don wasu abubbuwan dole saida ita zatayi.

Tana cikin danne dannenta kira yashigo wayar

Qurawa number idanu tayi batareda ta dagaba yayinda bugun zuciyarta yafara sama


Haka taita kallon wayar harta yanke, ko seconds biyu ba'a qaraba wani kiran yasake shigowa.

Saida takusan tsinkewa sannan tayi qarfin halin daga wayar ta kara a kunnenta batareda tace komaiba

"Beauty.." Taji anfada daga dayan bangaren

Shiru tayi batace komaiba

"Hello? Are you there?" Yasake cewa

Qarfin halin bude baki tayi tace
"Yes? Who's this?"

Sautin murmushin shi taji kafin yace
"You know better"

Shiru tayi bata sake cewa komaiba

"Shine kika tashi dazun without my consent?" Yasake fada bayan wasu daqiqu

Dan wara idanu tayi tace
"Your consent?"

"You heard me" ya amsa a gajarce

Ta6e baki tadanyi batareda tasake cewa komaiba

"Bakice komaiba"

"Me zance?" Tafada tana Zamewa ta kwanta

"You tell me why you leave without my consent ko kiyi apologising for that" yabata amsa

Dage giranta tayi alamun 'dagaske?' Sannan tace
"Bye.. Am sleepy"

"Are you kidding me" yafada da sauri jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login