Showing 66001 words to 69000 words out of 173829 words
yadda ya Waro idanu cikin kidima.
"W...what! Tayaya? Kardai dasa hannunki aciki?" Ya tambaya bakinshi na 6ari
Murmushi saudart tayi sannan ta fiddo wayarta ta kunna wani video ta miqamashi
Amsa yayi yafara kallo .
Da farko magana kawai yakeji be ganin mutanen sannan daga baya fuskarsu ta bayyana.
Wadannan mutanen ne uku dasukayi meeting dasu a Spain tsaye suna magana akan yadda zasu tsara yadda jirgin zai kife a ruwan shi yadda baza'a zargi wani Abu ba Wanda a zahiri jirgin dauke yake da gwalagwalai na bogi.
Sannan suka tsara yadda zasuyi kason abinda suka samu idan komai yatafi daidai, duk wannan abin da turanci suke magana.
Zufa sadeeq keyi takoina har saida yagama kallon video din sannan ya dago yana kallon saudart totally speechless.
Itama shi take kallo, ganin kallon dayake mata Yama kasa magana yasata cewa
"Ni nayi video din.... Ranar bayan meeting din mun fito muna tafiya sai igiyoyin takalmi na suka since, shine na aza purse dina a wani dakali da duqa na daure... Cikin ikon Allah saina manta da purse din nafita saida zan shiga mota natuna nadawo domin dauka.
Harna dauka zan wuce naji maganar su saikuma naji ya danganci meeting din damuke saina kasa kunne.
Ahaka suka fito daga office din suna maganar cikin turanci don da alama baqin cikinsu bejin Spanish, jin abinda suke fada yasani shiga firgici, narasa yadda zanyi saina la6e ina sauraron su, anan idea ta fadomin na dayi recording, da voice naso nayi sainaga Gwara video tunda fuskarsu is showing clearly, hannuna na 6ari nafiddo wayata na dauke su har suka gama tattaunawarsu suka shige dayan office din"
Dagowa tayi tana kallon sadeeq daya tsuramata idanu kamar T.v
"Haka nafito rai a jagule, naso nafadama A.A saikuma nakasa, firstly at that time ya 6atamin rai ina fushi dashi, secondly dukda wannan ya isa hujja gani nake be cika hujjaba Gwara nabi a sannu inta bibbiyarsu insamu enough evidence"
"Muna cikin mota yafadamin jibi zamu koma Nigeria, hakan yasani cikin rudani sosai don sonike in bincikesu sosai, haka na kwana ranar ina tunanin mafita"
"Washegari mukaje shopping din tafiya dawasu qawayena biyu, daya mai suna Loveth masanar computer ce sosai, kamar wasa na tambayeta ta iya hacking din account din mutum tace eh, nace ta koyamin tace zata koyamin amma saina fadamata dalilin hakan, dafarko naqiya saikuma daga baya na gayamata, jin hakan yasata taimakamani nayi hacking din account din zahid, ya kasance duk abinda suka turamashi duk ina gani.... Gasunan"
Tafada tana Ciro wasu takardu a Jakarta ta miqa mashi.
Hannu na 6ari ya amsa yana dubawa.
Waro idanu yayi don komai na ciki, yadda suka hada komai.
Koda takardun kadai sukayi amfani saisun dauresu bare uwa uba ga video.
Dagowa yayi yana kallon saudart dake kallonshi itama, sai 6ari bakinshi yake yakasa magana
Murmushi tasaki sannan tace
"Wannan ya isheku Ku dauresu, aciki idan ka duba sosai zakuga ba akanku suka faraba, sun yaudari mutane da Dana ta wannan hanyar, go ahead a sue them, best of luck" tafada tana fita daga office din tabarshi nan tsaye yakasa ko motsi...✍
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
Gaskiya naji dadin comments dinku na page daya gabata, sai jiya nasan AUREN KWANGILA Nada masoya dayawa.
Jinjina gareku members din
*AUREN KWANGILA NOVEL GROUP*
*OFFICIAL MARCY NOVEL FANS*
*HOME OF HAUSA NOVELS*
*MATAR BAHAUSHE NOVEL FANS*
*FAUZZIYA D SULEIMAN NOVEL GROUP*
*KANO NOVELS*
duk naga comments dinku da fatan alhairi da addu'o'inku gareni, ina godiya sisters🙏 Allah yabar zumunci🤝
Masu qorafin short page suyi haquri, yanzu ban zama sosai, dakyar nakesamu nayi muku wannan dasafe kafin na fita, nima na qagara Nagama littafin, dama aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, please bear with me, mutafi ahakan har insamu kaina, ngd da qaunar Ku agareni💝💝💝
054
Saida yaji Qarar rufewar kofa sannan yadawo hayyacinshi.
A tamanin shima yafito office din amma sai gani yayi elevator din na rufewa daita aciki
"Miss saudart!" Yafada da qarfi yana nufarta amma har yagama rufewa.
"Shit!" Yafada yana nufan private elevator din Ashraf don cimmata.
Hannu na rawa ya Danna last floor yashiga.
Jiyayi kamar elevator din baya Gudu don jiyake kamar yafita yabi ta mattatakalai.
Finally elevator din yatsaya a last floor, tun kafin yagama budewa ya ra6a ta gefe yafita yayi waje dagudu.
Tayaya zaibari ta tafi bayan wannan abun datayi musu Wanda bazasu iya sakamata da komaiba.
Fitowa yayi a harabar company din yana wurge wurgen idanu don ganinta.
Can parking space yaganta tana qoqarin bude motarta.
A sittin ya nufi wajen yana kiran sunanta, tana jinshi tayi banza dashi ta bude motar tashiga, ta ziro hannu don maido kofar motar taji an riqe kofar gamm.
Dagowa tayi tana kallonshi da alamun tambaya batareda tayi magana ba.
"Miss saudart... Please karki tafi... Kizo mu warware komai tare please" yafada yana maida numfashin gudun dayayi
Murmushin nan nata tasakeyi sannan tace
"Warware me? I've done my part, ko babu ni zaku iya warware komai"
"Please saudart, kizo mu gwadawa A.A, yaga abinda kikayi please, don't leave just like that"
Guntun murmushin takaici tayi sannan tace
"Ni ba don wani nayiba, idan da danshi zanyi to believe me ya Dade be fada chakwakiyar datafi wannan ba, ni don Allah nayi, kuma wannan abun ina iya yiwa koma wanene, muddin na tsinci kaina a position na taimaka wa wani zan taimaka mashi badon komaiba saidan samun lada, duniyarnan yar qanqanuwa ce, batada tabbas bansaniba wataqila wannan shine aikina na qarshe a duniya, ina iya fita yanzu inyi clashing dawata motar in mutu, yanzu haka ina iya kai Kalmar nan tazamo itace ta qarshe a duniya, idan mutane zasu dinga tuna mutuwa dakuma nazari akan duniya da sun zage, sun nemi hanyar lada at any possible time or little opportunity, kana iyayin Abu Allah yabaka lada daya bazaka San muhinmmancin wannan ladar ba sai ranarda kake Neman ladar ruwa a jallo, lada daya yana iya hana mutum shiga aljanna yafada wuta, lada daya na iya hanaka shiga wuta kashiga aljanna, shiyasa duk abinda kasan zaka aikata kasamu lada komin qanqantarshi karka bari damar ya wuceka
Ni nayi saboda Allah ne da qwadayin lada, so basai ka kaini wajen shi ba don bayada abinda zai iya biyani asalima da saboda shi zanyi da ba zanyi ba, saidai a matsayinka na aboki kuma dan uwanshi zan baka shawara, ka fahimtar dashi meye duniya, dukiya ba itace komaiba, dan Adam daraja gareshi, musanmman mahaifa, yau mahaifinka ko mashayi ne yasha yayi tatul yazo yana Marisa tsakar hanya dole nakane, dole kaji zafi idan aka sokeshi koda yana yin abinda aka sokeshi akai muddin kasan darajarshi, mahaifa ba abin wasa bane saboda bakada tamkarsu kuma bazaka samu tamkarsu ba, duk wannan zai iya zagin mahaifan wani ko yayi maganar Rashin da'a gamedasu to ka bincika, besan darajar nashi bane, ko kisan kai mahaifina yayi hakan bazai sani gudunshi ba ko w sokeshi inkasa nuna jin haushina ba, saboda bayan Allah da manzonsa wadannan hallitun biyu sune mafi daraja acikin hallitu.... Nabarka lfy". Tana kaiwa nan ta rufo kofarta ta tada motar tabata wuta.
Ja yayi da baya cikin mutuwar jiki yabata hanya tayi reverse yabita da kallo harta fice daga kamfanin.
Ya Dade nan tsaye yana saqawa da kwance wa sannan dakyar yasamu yajuya jiki a sanyaye yashige company din.
Direct office dinta yakoma inda ya ajiye takardun da wayarta Wanda bata tsaya amsaba.
"Wane irin zuciya saudart ke dashi? Gaskiya samun irin saudart acikin al'umma zaiyi wuya a irin wannan zamanin"
Kwasan kayan yayi ya nufi kofar Ashraf ya bude yashiga batareda knocking ko Neman iziniba.
Jin anshigo yasashi dagowa a masifance don ya balbale koma wanene.
Ganin sadeeq da yanayin dayake ciki yasashi fasawa ya tsaya yana kallonshi.
Qarasowa sadeeq yayi ya ajiye abubuwan gabanshi yana kallonshi.
Shima kallonshi yayi sannan ya kalli takardu da wayar kan table din.
"Wannan fa?"
"Ka duba mana, amsarka na aciki, na barka lfy" yajuya yafita batareda yajira single word from him ba.
Saida ya rakashi da kallo harya fice sannan ya dauki takardun yafara dubawa.
He was in shock sai zare idanu yake yana bin takardun da kallo, kanshi ya qulle ruff yakasa gane komai.
Wayar ya jawo ya kunna power dinta nan yaga ba password sai sliding din daza'ayi kawai.
Sliding yayi ta bude sai yaga video ne akan screen din.
Kunnawa yayi yafara ganin the shock of his life.
Daskarewa yayi a zaune, he was shocked, speechless, dumbfounded, ko kwakwarran motsi yakasa.
Zabura yayi ya miqe tsaye ya kwashi kayan sai office din sadeeq.
Shima ko knocking be tsaya yiba ya banka ya shiga yaga sadeeq zaune yana operating din computer hankali kwance.
Sadeeq yaji shigowarshi amma ko dago kai beyiba, dama yasan dolene yazo.
"S..sadeeq? Kaga abinda nagani kuwa?"
"Me kenan?" Inji sadeeq yana cigaba da danne dannen shi
"Kamar yaya me kenan? Kai ka kawosu fa?" Inji Ashraf yana zama kusada shi, fuskarshi still in shock.
"To tunda ni nakawo maka su, chunkusashen kwakwalwarka be isa yagayama naganiba" yafada in a harsh tone.
"Look sadeeq, ba fada ya kawoniba, now tell me ina kasamu wannan?"
Banza yayi dashi ya cigaba da aikinshi.
Cikin fushi Ashraf yayi unplugging din socket din computer din
"Fuck you! Am asking you!" Yafada atsakankanin haqora.
"Me kake tambaya ta?" Inji sadeeq yana qaremashi kallo yana qoqarin danne 6acin ranshi.
"The damn video and the damn paper! Ina kasamesu?!"
"The damn girl" ya amsa yana kallonshi
"Mene?" Inji Ashraf cikin Rashin fahimta
"Nace the damn girl ce tabani"
"Who?"
"Your secretary" yafada still trying to control his anger.
"W..what!!" Yafada yana ware idanu cikin tsananin mammaki
"Yes... Itace ta dauki video din, takuma jajirce wajen samo evidence din dazamu iya sueing dinsu"
"No.. This is unbelievable" inji Ashraf cikin tsantsan rudani
Miqewa sadeeq yayi yana takowa gabanshi yayi folding din hannayenshi a qirji yana cewa
"But it is Mr A.A, it is"
Kallonshi Ashraf yake in Short of words, sai motsi bakinshi yake amma yakasa magana hakan yasa sadeeq cigaba dacewa
"Itace, ita ta jajirce harta samo mana evidence din dazamu iya kamasu dumu dumu....."
Nan yashiga bashi labari tiryan tiryan yadda saudart ta bashi shima daga farko har qarshe.
Kasa ko motsi Ashraf yayi, infact jiyake kamar jinin Jikinshi sun daina gudana sai bin sadeeq yake da kallo kamar zombie
Dafa kafadarshi sadeeq yayi yana cewa cikin sanyin murya
"Yanzu kaje, kayi pressing charges akansu, be happy komai zai dawo, amma ina tayaka baqin cikin rasa Abu Wanda yafi duk dukiyoyinka da qadarorrinka daraja, jeka please jeka"
Kasa koda motsi yayi, ganin hakan yasa sadeeq shigewa toilet yabarshi nan tsaye.
Ya Dade ahakan tsaye duniyar na juyamashi.
Tunawa yayi da lokacin da tacemashi ta manta da purse dinta.
Tunawa yayi da dadewar datayi kafin tadawo
Tunawa yayi da yanayinta data dawo
Ashe v lokacin taimakonshi tayi?
Tunawa yayi da abinda yayi mata a Daren ranar.
Jefata dayayi a kujera, shan gabanta dayayi, damqar hannunta dayayi, hawayenta, gangarowarsu.
*I hate you... With passion* kalmarta tayi mashi amsa kuwa a kunne.
*I hate you! Damn you!* Kalmar ta tasake dawo mashi.
Tunawa yayi da farkon haduwarsu.
Abubuwan dayaymata, auren su, fara aikinta a company dinshi, wahalhalun daya bata, baqaqen maganganun daya gayamata, muguntan dayayi mata.
Amma despite wadannan, ta taimakeshi? Tayi risking din life dinta da time dinta ta taimakeshi bayan muzgunawar dayake mata?
Tunawa yayi da maganganun daya ya6a mata da safennan, har kiran sunan baban ta yayi gatsau, yaci mutuncin ta.
"Innalilahi waina ilaihi rajiun" yafada yana zamewa ya zauna kan kujerar da sadeeq ya tashi.
Jingina kanshi yayi da jikin kujera zuciyarshi zafi, cikeda danasani marar amfani.
Lumshe idanunshi yayi yana hadiye yawu mai daci .
Saida sadeeq yakusan mintuna talatin a toilet sannan yafito don a tunaninshi yafita.
Turus yayi ganinshi zaune ta jingina da kujera idanunshi a lumshe.
"Yadaiyi mallam? Mekuma kakeyi anan? Kaje ka shirya komai mana, munada enough evidence zama be ganka ba"
Bude rinnanun idanunshi yayi ya kalleshi sannan ya Bude baki dakyar yace
"Ina.. Take?"
Kallon Rashin fahimta yayi mashi.
"Wa kenan?"
Shiru yayi yana maida idanunshi ya lumshe Yanajin zuciyarshi na zafi.
Can kuma kamar an tsikareshi saiya miqe tsaye wayar still a hannunshi ya riqeta gamm danshi sannan yafice da sauri sadeeq yabishi da kallo.
Office dinta yashiga amma wayam sai qamshin ta data bari.
Ahankali ya tako ciki yana qarewa office din kallo yadda komai is soo neat and unique kamar dai mammalakiyar office din.
Ahankali ya qarasa kujerar datake zama yajata baya ya zaune yana sauke ajiyar zuciya.
Ya Dade ahakan sannan ya dago wayar hannunshi yana binta da kalli.
Idan be manta ba kamar yana yawan ganinta da irin wannan wayar.
Kunnata yasakeyi yayi sliding tadawo still kan video din.
Danna home yayi nan take photon ta ya bayyana a screen din daro daro.
Photon fuskarta kadai, kanta nannade da Jan gyale, fuskarta dauke da wannan killer smile din nata me bayyana dimple dinta na hannun dama da haqoranta hudu na gaba.
Bin hoton yake da kallo yana kallon every noook and cranny na fuska kamar yau yafara ganinta.
Wet slippery red lips dinta yabi da idanu yana kallon yadda suka dan raba sukaba haqoranta damar fitowa cikin murmushin.
Hannu yakai ahankali kamar mai tsoro ya shafa fuskar kan screen din
*SAUDART* ya furta ahankali cikin yanayin shauqi da bege...✍
Kuyi hqr nasan yayi kadan please bear with me🙏
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
Ayyah fans naga cigiyarku, nima kuna raina, jiya throughout ban hau online ba saboda hidimar suna, jiya Daren suna yau suna, yanzu ma squeezing din time nayi nasamu posting amma insha Allah komai yakusan warwarewa. Ngd da qauna😘😘
055
A bangaren saudart tunda tafita take falfala uban Gudu a kwalta tana sa bayan hannunta tana share hawayenta akai akai.
This guy is unbelievable, duk rayuwarta bata ta6a sanin tsana irin wannan ba, tsanar datake mashi baya misaltuwa, baki yayi kadan ya misalta.
"It's coming to an end! Komai yazo qarshe insha Allah" tafada tana juya steering din motar tana shan corner wani junction ta dauki hanyar dazai kaita bakery dinta.
Ashraf besan iya lokacin daya dauka zaune ba kanshi kife akan desk din office din saudart.
Idanunshi biyu amma shi kanshi be iya cewa ga takamaimai abinda yakeji ko yakeso ba.
He just feel like being like that forever, jiyake kamar ya kasance ahakan har abada.
Sadeeq daya fito daga office dinshi don yin sallah yayi turus sanadiyar hangoshi dayayi ta glass din office din saudart.
Tsayawa yayi yana shawara da zuciyarshi yaje wajen shi ko ya kyaleshi.
Da kamar yawuce sai kuma ta sauke ajiyar zuciya sannan yanufi kofar ya budeta ahankali ya shiga da sallama.
Shiru babu amsa don ko motsawa beyiba.
Matsawa yayi kusada shi inda yake zaune kanshi kife a desk ya dafa kafadarshi Wanda saida yadanji ya zabura kadan alamun bemasan da shigowarshi ba saida ya ta6ashi din.
"Ashraf.."
Shiru yayi kuma be dagoba
"A.A?....get up it's zuhr already" yafada babu yabo babu fallasa
Sai a sannan ya dago ahankali ya kalleshi
Kauda Kai sadeeq yayi alamun still yana cikin fushi dashi ne.
"Lokacin sallah yayi" yana kaiwa nan ya fice batareda yaqara waiwayarshi ba.
Binshi yayi da kallo harya fice sannan ya bar kallon inda yabi yafita, ta tashi jiki babu qwari yashiga toilet din office din ya daura alwala sannan yafita shima masjid din companyn
Tare suka fito bayan sallar suka jero suka nufo cikin company din amma babu Wanda ya cewa kowa uffan.
Koda suka isa floor dinsu wucewa sadeeq yayi office dinshi batareda ya ko kalleshi ba.
Binshi da kallo yasakeyi sannan yadan saki murmushin dabai wuce iyakar le6enshi ba.
Shima mara mashi baya yayi har office dinshin ya taddashi jingine da kujerarshi yana dan wawwanawa.
Jin anshigo yasashi dagowa don ganin mai shigowa.
Ganin shi yasashi dauke Kai ya cigaba da jujjuyawa a kujerar.
Shima bece komai ba ya qaraso gabanshi yaja kujera ya zauna yana kallonshi saidai duk yadda yaso yadago su hada ido yaqi bashi dama don besake kallon gefenshi ba.
"Sadeeq.." Yafada cikin muryarshi datayi sanyi lokaci daya.
Banza yayi dashi ya cigaba da wawwanawa a kujerar
"Am...am sorry, very sorry" yafada cikin muryar rada.
Mammaki ne Yakama sadeeq don jin ya furta Kalmar ban haquri gareshi, abinda be ta6a yiba kenan.
Sunsha susami sa6ani kuma Ashraf keda laifi amma beta6a bashi hqr ba saidai yayita Neman hanyar dazasu shirya amma beta6a furta Kalmar sorry a gareshi ba.
Katse mashi tunani Ashraf yayi dacewa
"I truly am... Bansan abinda yahau kaina ba har nayi blunting haka, am sorry" yafada yana kallonshi
Sai a lokacin sadeeq yadago ya kalleshi yaga shima shi Yake kallo babu alamun wasa a fuskarshi
"Excuse me, haqurin me kake bani? Wani Abu kayimin ne?" Inji sadeeq cikin basarwa
Dan murmushi Ashraf yayi sannan yace
"Komai na, nasan nayi blunting dazu kuma abin ya 6atamaka rai am sorry"
Ta6e baki sadeeq yayi yana dauke kanshi daga gurinshi yana cewa
"A tunanina kanaba Wanda be kamata ba haquri ne, ni bakamin komai ba, kuma blunting dakayi ai bani kayi mawa ba, kafini sanin Wanda zakaba hqr" yafada cikin son danne 6acin ranshi.
Maida le6en qasa Ashraf yayi cikin bakinshi yana dan taunawa ahankali yana kallon table din gaban sadeeq.
Can ya miqa hannunshi ya dauki pen din sama yana dan dukan table din da pen din still yana taunar le66anshi na qasa ahankali
Har sadeeq yacire rai da zaiyi magana sai jiyayi ahankali yace
" will she ever forgive me?" Yafada cikin wata kan iriyar sanyayan murya still idanunshi akan desk din yana dan dukanshi da pen.
Shiru sadeeq yayi yana kallonshi batareda yasan abinda zaice mashi ba .
Jin shirun yasashi dagowa yana kallonshi
"Eh? Nace zata iya yafemin? She hates me" yafada cikin yanayin da kallo daya zakayi mashi kasan Yanajin ciwon abinda yafada
"Yes she hate you, kaga laifinta ne don tayi hakan? Laifinta ne data tsaneka ko kawai haka kawai ta tsaneka? You...kai ka koyamata tsanarka ba kowa ba, you caused it all!" Yafada at last batareda ta sake yunqurin danne 6acin ranshi ba.
"Nasha fadamaka yarinyar nan batada masaniyar abinda ke tsakaninka da mahaifinta, she has no case in this at all, amma ka saurareni? Instead kullum cikin Neman hanyar dazaka quntata mata kake, kullum cikin 6ata mata rai da cimata mutunci kake, what did you expect from her? So kake duk bayan abinda kakemata tazo tana godiya tana washe maka baki? Me zai hanata tsanar ka? Karka manta zuciya tana son mai kyautata mata ne tana kuma Qin mai muzguna mata, kai ka auna kanka a mizani kaga a wane bangare kafada kafin kayi complaining din ta tsaneka" yafada cikin bayyana fushinshi da baida kyan gani.
Haryanzu Ashraf be dago kanshi ba kuma bebar dan bubbuga desk din ba da pen ba amma idanunshi sun kada sunyi jajur don kalaman sadeeq direct suke wucewa cikin zuciyarshi suna mai barazanar tarwatsata.
"Ashraf, saudart mutum ce, tacika yar halak, despite abubuwan dakake mata