Showing 33001 words to 36000 words out of 224014 words

Chapter 12 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1070

an idar da salla dan Allah a sanar"

Wani malami ya kalleta ya ce "A sanar da me?"

"Na yi ƙoƙari a makarantar boko mana, har na ciyo kyauta, word kusan ɗari biyu da hamsin fa na haddace yadda ake spelling ɗin su"

"To amma ai nan ba makarantar boko ba ce ba, ki bari idan ki ka yi bajinta a nan ma, sai a sanar wa ɗalibai"

Ruma ta ce "A'a malam gara ai a sanar, saboda masu ce mini daƙiƙiya su san ƙwaƙwalwata na aiki, wataran zan bayar da mamaki".

Malam Habibu ya yi caraf ya ce "Ƙwarai kuwa, dole a sanar da ɗalibai wannan namijin ƙoƙari da ki ka yi, nima ba rannan na yi ƙari kin iya ba, duk za a sanar kar ki damu" cikin jin daɗi ruma ta ce "Yauwwa malam na gode"

Bayan tafiyarta ya yi dariya ya ce "Yanzu idan ba ku yi yadda take so ba, Allah kaɗai ya san wace tijarar zata yu, amma yanzu idan aka faɗa ɗin, za ta ji daɗi da ƙara samun ƙwarin gwiwa".

Ruma da ta ga an idar da salla, ana neman a watse ba a sanar ba, ta tafi ƙofar masallacin maza, ta leƙa ta ce "Malam Habibu kar ka manta fa, na ji ba a faɗa ba".

Malam Habibu ya ce "To bari a sanar, ai yakamata wannan abin arziki haka"

Haka malam Habibu ya tashi ya ce "'yan uwa ɗalibai da malamai, a taya 'yar uwa murna, wato 'ya ta rumaisa, bisa nasara da ta yi a wata gasa da aka shirya a makarantar bokon su, har ta samu kyaututtuka dan Allah ayi mata Addu'a, Allah ya ƙaro nasarori"

Daɗi kamar ya kashe ruma, masu dariya na yi, masu jin haushi na yi.

Huzaifa da suka yi salla sahu ɗaya da Yasir ya ce "Ka ji abin da wannan mara kan gadon ta yi ko?"

"Bar motsatsiya, suma malaman da suka biye mata, idan ba tayi wasa ba sai na ƙona banzayen litattafan da aka bata, kowa ma ya huta".

Cike da annashuwa ruma ta tafi gida, ta je ta bawa mama labarin yau har a wurin salla, aka sanar da ta ci kyauta a makarantar boko. Tana shiga gidan ta tarar da Yaya Abubakar ya zo hutu, da kuma waa dattijuwar mata a zaune a tsakar gida.
Da sauri ruma ta nufi dattijuwar ta faɗa jikinta ta ce "Gwaggo Atine, yaushe rabon da na ganki?"

Dattijuwar ta washe baki ta ce "Dama ina zaki ganni, nayi-nayi da babarki ta din ga kai mini ke ina ganinki, amma ta ƙi saboda ina ƙauye".

Mama ta ce "Haba Yaya Atine, wallahi ba haka bane ba, kin san yanayin makaranta kuma ruma ba ta ji idan aka kai miki ita sai ta gallabe ku"

Ruma ta haye kan cinyar matar cikin jin daɗi ta zauna.

Matar ta ɗora da cewa "Ba wani rashin ji, a kawo mini ita a hakan ina son ta, duk rashin jin ta. Ɗan uwana ya ƙallafa rai a kan ta yana son ta, nima ina matuƙar ƙaunarta da na ganta shi nake tunawa amma ba za a kawo mini ita ba, sai wannan ƙartin ne kawai suke zuwa in da nake" ta yi maganar tana fashewa da kuka.

Mama cewa take "Allah ya baki haƙuri, in Allah ya yarda za a dinga kawota".

Ruma kuwa ta kalli Gwaggo ta ƙyal-ƙyale da dariya ta ce "Dan Allah Gwaggo ki daina wannan kukan, ni wallahi fuskarki dariya take bani idan ki na yi, kin ga yadda ki ke yamutsa kuwa?"

Yaya Aliyu ya ce "Ai gara ta fara gwada miki halin"

Gwaggo ta tsaya da kukan ta ce "Rumaisatu, kukan nawa ne yake baki dariya?"

Ruma ta ce "Eh mana, amma ki daina ce mini wata rumaisatu, sai ka ce wata masara, kowa aka saka masa suna mai daɗi a gidan nan, amma aka saka mini wata Rumaisa kamar masa"

Gwaggo ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah"
"Gwaggo wai ina wannan 'yar ta ki, mai kamar ni ɗin nan?"

Jin ruma ta tambayi 'yar autarta ya sanya Gwaggo yin murmushi ta ce "Au Lawisa tana nan ƙalau, ta na ta a gaishe ki, ita ana biki sun tafi da tuni tare zamu zo"

Ruma ta yi dariya ta ce "Wai Lawisa, ai har gara nawa sunan ma da nata, wata lawisa kamar za ace lawashi, ta fini girma yanzu?"

"A'a zaku yi tsayi ɗaya da ita"

Ruma ta yi murmushi tana kaɗa ƙafa.

Abubakar ya ce "Ruma ɗaga mata ƙafa mana"

"A'a ƙyaleta, ai haryanzu yarinya ce, Allah dai ya kai ni auranku ke da Lawisa"

Ruma ta ce "Amin, ki yi mini Addu'a, Allah ya sa na yi tsawo na isa aure, kuma Allah ya sa na auri kyakykyawa mai kuɗi sosai"

Mama ta riƙe haɓa ta ce "Ruma, ƙanƙanuwarki da ke, har kin san wani miji mai kyau mai kuɗi?".

Gwaggo ta ce wa mama "Wai ke ina ruwanki da mu ne, muna hira kina saka mana baki" ta mayar da hankali kan ruma ta ce "Amin 'yar albarka, Allah ya kai ki in da zaki huta, mu ci mu sha mu yi wadaƙa".

"Amin, kuma Allah ya sa na auri me kyau".

Aliyu ya ce"Da wannan shegen hancin naki kamar na aladae zaki auri me kyau?"

Gwaggo ta ce "Ƙarya ka ke dan ubanka, wallahi kamar ta ɗaya da babanku, kuma hanci ne da shi har baka, in Allah ya yarda sirikina kyakykyawa ne kuma mai abin hannu, tun da 'ya ta ba daga nan ba"

"Gwaggo kin san wa nake so na aura?"

"A'a sai kin faɗa"

"Kina kallon wrestling?"

Gwaggo ta ce"A'a ni ban san shi ba"

'To ball fa?"

"Ni ina zan ga wannan shirmen"

Ruma ta ce "Da kina kallo, da na gaya miki wanda zan aura a cikin su".

Cikin son katse surutun da ruma ke yi ba kunya ba tsoro mama ta ce "Ruma tashi ki canza kaya, zan aike ki" ruma ta miƙe daga cinyar Gwaggo ta tafi sauya uniform.

Tun da Allah ya sa Gwaggo ta zo gidan nan, ruma taɓara ta ƙaru, don ko me ruma za ta yi ba zata bari a yi mata faɗa ba, gashi kullum cikin faɗa take da mai sunan Baba, dan kome za ta yi idan ruma tayi laifi hukunta ta yake yi.

"Wannan yaro da fuska kamar bajimin sa, ba ka da imani, wannan 'yar tatsitsiyar yarinyar guda nawa take, da zaka dinga azabtar da ita wallahi Hauwa wannan ɗan naki mugu ne"
Gaba ɗaya ruma da Gwaggo suka gallabi gidan nan, ruma kuwa aka samu tikitin rashin ji dan ma tana tsoron mai sunan Baba.

Yau Malam Habibu yana babban aji, ruma tana tare da shi, yayi musu ƙari, tana ta wasanninta da ciye-ciye, sai da ya kammala yana amsa tambayoyi sannan ruma ta ce "Malam ka ce idan mace tayi mafarkin namiji sai ta yi wanka zata yi salla, to ni kuma kullum sai na yi mafarkin yayyena, Kuma ni sai zan tafi makaranta nake wanka watarana kuma mama ta ce bana fita tayi mini wanka, to yan.....
Kan ta ƙarasa 'yan ajin suka hau dariya, dan ba zaka taɓa cewa hankalinta na kan abin da yake koyarwa ba.

Malam Habibu ya ce " 'ya ta ta kaina, ai wankan da mama take yi miki ya wadatar, duk ɗayane"

Ta ce "Au ho, na gane"



Tana dawowa daga islamiyya ta turke Abubakar ta ce "Yaya Sadik yau ka san meyafaru a makarantar islamiyya ?"

Sadik ya ce "A'a"

"Ka san na canza aji a islamiyya, saboda malaminmu baya ƙaunata, Ajin su Yasir kuma ya ce idan na ƙara zuwar musu aji sai ya dakeni, sai na koma ajin malam Habibu gaba ɗaya ajin 'yan sauka"

Abubakar ya ce "To ban da abinki kin taɓa ganin an fara gini daga roofing, ai daga tushe ake farawa"

"Oho dai koma yane, wani karatu aka yi nake son na tambayeka, da zan tambayi malam Habibu na manta"

"To ina jin ki"

" 'yan ajin ne da su da wasu na ga wataran ba sa salla fa, ko su ƙi zuwa da Alqur'ani izifi sittin wai Haila suke yi. Na tambayesu sai suka ce mini wai ai mata ba kullum suke salla ba, idan ba su yi salla ba haila suke yi ko biƙi. Aikuwa nima na ƙi yin salla, wata prefect ta ce me yasa ba na salla nima na ce biƙi nake"

Gwaggo da ta idar da salla ta ce "Subhanallahi" jin maganar ruman kamar saukar aradu.

Ita kuwa ko a jikinta, ta cigaba "Shi ne ta ce dan ubana ni na isa in yi biƙi, na ce ba dai ubana ba sai dai na ta, kuma tun da nima biƙi nake ba zan salla ba, ashe wataran mata ba sa salla amma ni kullum mama sai ta ce sai na yi"

Abubakar ya ce"To, wannan zancenku ne ke da maman ita zata baki amsa".

Ruma ta ce "Mama....."
Mama ta katseta ta hanyar cewa "Rufe mini baki, kar ki sake ki yi mini shirme, kuma ki tashi ki yi sallar da ki ka ce baki yi ba dan ubanki"

"To mama ai idan ana biƙi ba a salla"

"Biƙin ubanki, ke kin san meye biƙin ne?"

"To meye biƙin?"

"Ba zaki tashi ki yi sallar ba, sai na zane ki da bulugarin nan?"

Ta kalli Gwaggo ta ce "To ke gaya mini"

Kamar wadda ta tambayi meye wani babban zunubi Gwaggo ta ce "A'a ni babu ruwana, ga uwarki nan ta baki amsa ni zaki tambaya wannan babban al'amari ba a bakina ba, 'ya'yan binki wayewar ku ta yi yawa".

"Ohh ni ruma, komai na yi laifi ne, ai shikenan"

Tun daga lokacin ba ta kuma kula kowa ba, ta koma tayi shiru wai ita ta ji haushi.

Har zuwa sallar magariba, ba ta sake kula kowa ba, Gwaggo ma ta gaji da yi mata hirar, amma Ruma taƙi saurarata.
Yaya Sadik ne yayi gyaran murya ya ce "Ruma, wai ni kuwa idan kin girma me ki ke son ki zama ne? Da na je taron PTA ɗin ku an ce da kun shiga primary 6, za'a fara shirin common entrance, shi ne na ce idan kin shiga Sakandire me ki ke sha'awa Art zaki yi ko science?"

Ta kalle shi ta ce"Wai in din ga drawing?"

"Wane irin drawing kuma?"

"To ai ji na yi ka ce Art, Art ba drawing ba kenan?"

"A'a ba wannan ba"

"Ni dai kawai sana'ar da zan samu kuɗi nake so, ko kuma in zama 'yar sanda, in dinga tsayawa a titi ina bada hannu masu mota suna bani kuɗi, ko kuma a buɗe mini kanti, ko na zama mawaƙiya ko 'yar film!"


Ayshercool
08081012143
A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊINA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ƊAYA A SATI 😒*
[11/07, 4:25 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.






P11

Girgiza kai kawai Abubakar ya yi, ya ja bakinsa ya tsuke.

"Yaya ya na ji kuma kayi shiru?"

"To ruma ba dole na yi shiru ba, kowa yana nemawa kansa mafita a rayuwa, amma ke in da ki ka dosa daban?"

"To wai me na faɗa ba dai-dai ba?"

"Yanzu ke tsakanin ki da Allah, kin taɓa ganin mace a titi tana bada hannu a ƙasar hausa?"

Ta ɗan yi shiru sannan ta girgiza masa kai ta ce "A'a, to mawaƙiya fa ko film?"

Abubakar ya ce "Ba kushe sana'ar wani zan yi ba, amma ki yi tunanin wani abun daban"

"To ba sai a buɗe mini kanti ba"

"Yanzu a unguwar nan gaya mini shagunan da ki ka ga mata ne a ciki suke sayar da abu?"

Ta yi farat ta ce "Ga maman Olu beyerabiya"

"To ke bayerabiya ce?"

"A'a amma dai....."

"Kin ga, ya isa haka, dama ni a kan career ki nake magana, tun da baki gane me nake nufi ba shikenan" ita sam ba ta ga aibun abin da ta ce tana so ba, dan haka ko a jikinta ta share.

Gwaggo ta fara shirin tafiya, su Yasir suna ta murna, dan dama duk ta ishe su da faɗa da azabar saka ido.
Shi kansa mai sunan Baba murna yake ta tattara ta tafi ta bar musu gida su huta, dan ta saka shi a gaba da yawa, dan ma Allah ya taimaki Abubakar bai fi sati ba ya koma makaranta.
Amma kullum cikin surutu takewa mama "Hauwwa wannan zagada zagadan yaran naki, duk sun isa aure amma kin tare su a gaba kina ado da su a gida, ga ƙauye can muna da mata burjik, amma dan mugunta kin tare su kin hana su motsi'

Mama ta ce "Haba Gwaggo, guda nawa yaran suke, haryanzu su Baba basu haɗa talatin ba fa, duk girman jiki ne, kuma kina ganin irin rayuwar da ake sai godiyar Allah, babu mai ƙwaƙwarar sana'a sai ƙarfin hali, idan suka ɗauko aure da yaya za su riƙe?"

"Ba wani nan, idan mutum yayi aure Allah zai warware, amma kallesu dan Allah tuma-tuman gwauraye ki na ado da su a gida, babu mai mata, kalli dai wannan zagaren, sai dai ya shigo fuska kamar bajimin sa, ya zo ya ɗau abinci ya fita yana zazzare ido kamar wani zaki, ko fara'a ba ya yi, kai haka zaka yi wa matar ma idan an aureka?, ko da yake ma wace macence za ta auri mutum ba fara'a ba komai fuska kamar kunun kanwa ba rahama"
Lomar Abincinsa kawai yake kawai, ko motsi bai yi ba, balle ya nuna ya san da shi take, yana jin ta ya share ta.
Ruma kamar ta kwashe da dariya, jin an ce fuskar yaya Umar kamar kunun kanwa, amma sanin ruwa ba sa'an kwandon ba ne ya sanya ta ja bakinta ta tsuke.

"Umaru da kai fa nake" A hankali ya ɗago idanunsa ya yi mata wani irin kallo, ya mayar da kan sa ya cigaba da cin abinci.

"To Allah ya kyauta, ka ma dai mayar da ni mahaukaciya, ka je ka ƙarata, tattara kayana ma zan yi na bar muku gidan ku, gobe goben nan zan bar garin nan.
A hankali yasir ya ce "Alhamdilillah, Allah ya raka taki gona"
A rikice ruma ta ce "Haba Gwaggo, ni bana son ki tafi, dan Allah ki zauna bamu gaji da ganinki ba".

Huzaifa ya yi ƙasa da murya ya cewa Abdallah"Ji munafukar 'yar nan, ko a gidan uban waye bamu gaji da ganin na ta ba, mata duk ta addabi mutane?"

Abdallah ya ce "Ashe ka manta wacece ruma, ai wannan yarinyar tsaf sai ta haɗa yaƙin duniya na uku, duk abin da ta san za ta aikata wanda ba a so shi take yi"'

Kamar wasa ruma har da kuka, wai kar Gwaggo ta tafi, ji suka yi kamar su yi wa ruma taron dangi su zaneta.

Ganin ruma na kuka, ya sanya Gwaggo ta ce ba zata tafi yanzu ba, saboda ruma.

*****
Sauri-sauri take yi, tana tafe tana duba agogon hannunta, tana daf da makara zuwa wurin da zata.
Tana ƙarasawa harabar gidan ta ɗan ɗaga murya ta ce "Gali, gani na fito zo mu je na makara"

Cikin girmamawa da murmushi Gali ya taso ya ce "Allah ya taimaki 'yar gaban goshi, Allah ya ƙara miki lafiya uwar ɗakina, ai tun ɗazu ke nake jira, tun da tun huɗu ki ka ce mini"

"Kai dai bari, na tsaya na yiwa Ammi girkin dare, kar na je ban dawo da wuri ba ka san ba komai take ci ba"

Ya ce "Haka ne, bari na fito da motar" ya yi gaba ita kuma ta tsaya.

'yan mata ne su huɗu, suka fito ta ƙofar wani sashi na cikin gidan, suka tunkaro in da take wajen harabar gidan, hakan ya yi dai-dai da fito da motar da Gali ya yi.
Kai tsaye suka tinkari motar ba tare da sun kulata ba, suna ƙoƙarin buɗewa su shiga.
Da sauri Iman ta ce "Kai, fita fa zan yi, zai kai ni unguwa ne"

Ɗaya daga cikin su ta kalleta ta ce "Saboda ta ki fitar zamu fasa tamu ne?"

Iman ta ce "A'a ba haka nake nufi ba, na ga kun iya driving, kuma ga wasu motocin, ni Ammi ta hanani tuƙi ne, kuma na yi magana da Gali tuntuni a kan zai kai ni unguwa"

Cikin tsawa ɗaya daga cikin su ta ce "Shut up! Mu ki ke kallo ki ke gayawa haka, kin manta a tuna miki ne?"

"Me ku ke yi haka a tsatstsaye?" Gaba ɗaya suka waiwaya suka kalli mai maganar.
Jikin Iman ne ya yi sanyi, tare da shiga wani yanayi mai wuyar fassara, bayan sanya idanuwanta a cikin nasa.

Fauziyya ta cire glass ɗin fuskarta ta ce "Bro, wannan ƙanwar ta ka ce take yiwa mutane rashin kunya, duk motocin gidan nan ta rasa wadda za ta hau, sai da muka zo muka ce a kai mu unguwa, wai ita ma tilas ita zata hau a fita da ita"
Ya tsuke fuska ya kalli Iman ya ce "Wato ke tsagerancin naki har ya kai ki din ga yiwa na gaba da ke rashin kunya ko? Sa'anninki ne su?"

Jiki a sanyaye ta kallesu, sannan ta mayar da idonta kan sa, sai dai ta kasa magana, sai hawaye da suka cika mata ido.

"Ina magana zaki yi mini kuka, get out from my sight, stupid girl"

Gaba ɗaya ta rasa meya kamata ta yi, jiki a sanyaye ta nufi hanyar fita daga gidan.
"Ke zo nan" ta ji muryarsa ba tare da ta yi tsammanin hakan ba.
Ta juyo ta dawo in da yake tsaye.

"Ina zaki?"

"Napep zan je na hau"

"Wuce ki koma, ba zaki fita ba" yayi maganar cikin bayar da umarni. Ta kalli yadda motar da su Fauziyya suka shiga ta bar gidan. Ba ta ce masa ƙala ba, ta koma sashin su, sai dai duk yadda ta so ta riƙe hawayenta abin ya faskara, tuni hawayen suka wanke mata fuska.

"Subhanallah, abar ƙaunata ya haka? Meyafaru? ya baki tafi ba?" Ammi ta yi mata tambayoyin a jejjare cikin ruɗewa bayan ganinta ta na kuka.

Iman ta share hawayenta ta ce "Bakomai Ammi, kawai fasawa na yi"

No ban yarda ba, gaya mini"

"Ammi su Fauziyya ne da Yaya Mahmud".

Nan da nan Annurin fuskar Ammi ya ɗauke gaba ɗaya ta ce "Mahmud again? Tura fa ta fara kaiwa bango, meya yi miki?"

Iman ta share hawayenta ta ce "Ammi dan Allah ki bar maganar, kar ranki ya ɓaci, bana son ki damu"

Ammi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Na ji, amma me suka yi miki?"

"Dan Allah kar ki damu Ammi, bakomai ki yi haƙuri"

Jinjina kai Ammi ta yi sannan ta ce "Yanzu shikenan, kin fasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login