Showing 141001 words to 144000 words out of 224014 words

Chapter 48 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1112

riga ta faru, so kake jama'a su fuskanci wani abu kafin mu kai ga samun mafita? Ka tashi ya ce so yake ku je ko akwai bayanan da zaku samu a bakin yarinyar"

Adam bai kums cewa komai ba ya tashi ya shiga banɗaki, bai san a yaya yayi wankan ba ma, ya fito, Ammi ta saka shi a gaba, ya ɗan zuƙi shayi kaɗan ya fita. A falo ya tarar da Bashir, su Iman suna gaishe shi, amma babu wadda ya amsawa haka ma barorin da suke wurin, ya ce wa bashir tashi mu tafi.

Ammi ta bi bayansu tana yi musu magana ƙasa-ƙasa.

Nusaiba ta yi wa iman kallon meyake faruwa ne, iman ta ɗan ɗage kafaɗa alamar ita ma ba ta sani ba.

A harabar gidan suna shirin hawa mota, sai ga motar Jabir ya shigo gidan, takawa bai tsaya ba ya shiga motar bashir, saboda baya son magana da kowa a halin yanzu, kuma ya san jabir ritsa shi zai yi da tanbayoyi masu ma'ana da marasa ma'ana.

Takawa suna tafe a hanya shi da bashir, babu mai cewa komai, can bashir ya ce 'Adam ka kwantar da hankalinka, komai zai tafi dai-dai ina kyautata zaton zamu samu duk wani information da zai iya taimaka mana a kan binciken mu".

"Bashir, komai ya hargitse mini, ban san ta ina zan kuma sake fuskantar matsalolina ba, jiya kwana na yi ina tunani, yaya aka yi yarinyar nan ta kuɓuta da jariri ina Aisha take, wani irin tashin hankali da tozarci ne haka ace matarka ta haihu a hannun 'yan ta'adda?" Yayi maganar cikin tsananin damuwa da zafin rai.

Bashir ya dafa shi ya ce "Calm down, ka bi komai a hankali, komai zai dai-dai ta in sha Allah".


Baba uwani ta kasa zaune ta kas tsayez babban burinta shine ganin yadda za ta yi ta san meyake faruwa, ta samu ta kaiwa Mummy labari, domin a kan idonta Ammi da takawa suka shigo a daren jiya, haka zalika yanayin yadda ta ga fuskokinsu a wayewar garin yau ta sake tabattar da akwai wani abu da yake faruwa kuma da alama babban al'amari ne, amma babu wata hanya ko kafa aka bari balle ta ji labarin.


Bashir sai da ya tsaya a hanya ya sai carton carton na ruwa da maltina, suka ƙarasa Asibitin da rumaisa take.

Bashir ya sanya masinja ya ɗauko kayan da suka zo da su, ya biyo su.

Da sallama suka shiga ɗakin da rumaisa take, ba dan ƙarancin shekarunta ba, kai ka ce mai jego ce, saboda yadda take rungume da jariri a hannunta, usman ya amsa musu sallamar ruma kuma ta ɗago ta kallesu.
Bashir ya sallami masinjan nan, sannan suka zauna, suka gaisa da usman, suka tambaye shi mas jiki ya ce da sauƙi, wanda duk bashir ne yake yi, Adam ba ya iya magana.

"Rumaisa ba magana, ina kwana ya baby?".

"Lafiya lau" ta faɗa tana satar kallon takawa da yayi zuru-zuru ta taɓe baki.

Mu ga babyn yayi maganar yana karɓar jaririn yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, kin ga babyn zai warke ya barki, gaskiya ki daina langwai" ita dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Bashir ya miƙawa adam yaron, ya kuma kallonta ya ce "To ya jikin naki?"

"Ba sauƙi" ta faɗa kai tsaye.

Usman ya ce "Ke fa daɗina da ke ƙarancin tunani, ba zaki godewa Allah ba ki ce da sauƙi, zaki ce ba sauƙi?"

Sai ta fara kuka ta ce "To ina sauƙi? Mama ta aske mini gashi, bana iya taka ƙafata ƙeyata ma ciwukan zafi suke yi mini, ga haƙarƙarina ciwo yake mini".

Bashir ya ce "Ya salam, kin gayawa likita? Ko kin faɗi da wurin ne?"

Ta ce "A'a wani sule ne ƙato ya dinga takani da ƙafarsa a wurin, tun daga nan yake mini ciwo"

Bashir ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam ba shi jaririn a mayar da shi nursery dan Allah, dan na ji yana atishawa ko sanyin nan yayi masa yawa".

Adam bai motsa ba, ya zubawa yaron ido yana jin wani irin tausayinsa da ƙaunsrsa na shiga ransa, ya karɓi jaririn ya bawa usman, usman ya fita mayar da shi ya rage daga takawa sai bashir da ruma a ɗakin.

Bashir ya kalli rumaisa ya ce "Rumaisa, kamar yadda dai na yi miki bayani da fari, Adam abokina ne, dukkaninmu jami'an tsaro ne na farin kaya, zai yi miki wasu tambayoyi ne dan Allah ki bamu haɗin kai"
Rumaisa ta kawar da kanta gefe, taƙi ko kallon in da Adam yake.

Adam ya numfasa ya ce "Ta yaya zaki tabattar mini wannan ɗan na Aisha ne, ita ta haife shi"

Rumaisa jin tambayar ta yi kamar da rainin hankali a ciki "To ai ba sai ka tabattar ba, tun da dai ni na san ɗanta ne, shiyasa na ce ba kaine babansa ba".

Bashir ya ce "A'a ruma yi haƙuri, kin san komai a hankali muke bi tun daga tushe, ki bamu amsa Please".

Ta ɗaga filon da take kai, ta janyo ɗankwalin aisha, da yake a ninke, ta wurgawa adam cinyarsa "Ni banda wannan ban san me zance maka ba".

Ya saka hannu ya ɗau ɗan kwalin yana jujjuya shi, yana tuna wasu abubuwa da suka faru, tabbas ɗan kwalin aisha ne.

Ya ɗaga kai ya kalli Ruma ya ce "Ina aisha take yanzu? Ya aka yi ki ka kuɓita da jaririn? Ita tana ina?"

Tayi masa banza, dan ranar ƙarshe da ya wanketa da ruwan kwata ne ya faɗo mata.

"Ruma amsa mana, ina aishan take? Kar ki damu, adam ɗan sanda ne na farin kaya, ki yi masa bayanin komai"

Cikin tura baki ta ce "Saura na korayen kaya, ni ban san in da take ba"

"Kamar ya baki san in da take ba, ya ina magana kina shareni, ina Aisha take ina matata"

Ruma ta zaƙalƙale ta ce "Ka bita dajin ka ɗaukota, ka san kana sonta ka bari aka sace ta, ka ƙi zuwa ka fitar da ita, da ku ba gawara babu ba, ba da jami'an tsaro ake haɗa baki ba, haka aka ce da bakin su 'yan bindigar suka faɗa, in so kuke ku ganta sai ku tafi dajin ai, kuma wallahi idan kuma kun sani aka sace mu kuka ƙi taimaka mana a fito da mu, sai Allah ya saka mana, dukan da na sha a wurin mutanen nan ma ya isheni, ka zo zaka dameni"
Gaba ɗaya ido suka zubawa rumaisa, tana kuka tana tsiwa.

Adam ya ce "Ni kike gayawa haka?"

"Tsoronka zan ji ne, wallahi bana tsoron kowa sai Allah subhanahu wata'ala, kuma wallahi tun da Allah ya sa na fito sai ka gane ba ka da wayo, sai na rama abun da kayi mini"

Kallon tuhuma Bashir ya shiga yi wa rumaisa da Adam, kenan sun san juna, akwai wani ɓoyayyen abu kenan a tsakaninsu.

Usman ne yayi sallama, ya tarar da rumaisa tana kuka, su kuma sun zuba mata ido.

Ya ce "Lafiya kuwa?"

"Ba wannan ne ya sakani a gaba yana zare mini ido ba, wai sai na gaya masa in da matarsa take, kuma ni ban san komai ba, likita ma fa ya ce kar a din ga takura mini amm yake hantarata"

Adam ya dafe goshinsa yana tunanin meya dawo da wannan jarababbyar yarinyar rayuwarsa, meyasa take liƙe da ƙaddararsa ne.
Shi kuwa bashir mamaki ne ya ishe shi, maganganun ta sun girmi shekrunta, ya kalli usman ya ce "Tambayoyi kawai muke mata, so muke mu yi ƙoƙarin ceto uwar yaron ita ma, ba wani abun aka yi mata ba".

Usman ya kalleta ya ce "Ke ki gaya musu abin da ki ka sani mana"

"Ni ban san komai ba"

"Kamar yaya, ya aka yi ki ka karɓo jariri ki ka gudo, ina babarsa take?"

"Tana can" tayi maganar tana share hawaye.

"Ke ya aka yi ki ka fito?"

Sake ɓare baki tayi tana kuka ta ce "Wallahi likita ya ce a daina takura mini, da me zan ji kai baka san wahalar da na sha ba, kun haɗu kuna hantarata"

Usman ya ce "Ke fa rumaisa makira ce wasu lokutan, uba waye ya hantarekin?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kalli su Bashir ya ce "Tun da ba zata faɗa abubuwan da ake buƙata ba, ku ɗauke ɗanku ku tafi, kar ta sake ganinsa ma"

Ihu ta fara yi "Ni kar ku ɗaukar mini ɗana".

"To ki yi musu bayanin abun da suka tambayeki*

"Ni ban san komai ba, ba 'yan sanda bane su, su je dajin mana su duba, ni nace ba abun da na sani, ni duk na manta wasu abubuwan ma".

Sarautar Allah bashir ya zubawa ido, bai taɓa zaton tana da baki haka ba, saboda yadda ya tsinto ta a galabaice.

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi da ƙarfi, da duk sai da suka waiwaya domin ganin waye.


*₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam, jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*
Ayshercool





*KANWAR MAZA*

*20*


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Abubakar ne ya shigo, yana dira daga tasha ya wuto asibitin ba tare da ko gida yaje ba, da gudu ya ƙaraso ya rungume rumaisa, ko sauran mutanen da ke ɗakin bai kalla ba, ya rungume rumaisa yana zubar da hawaye.

"Yaya Sadik ɗina" rumaisa ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana kuka"

Bashir ya kalli Usman ya ce "Abokina, wai har ku nawa ne yayyen nata ne?"

Usman ya yi murmushi ya ce "Mu bakwai ne, ita ce autar mu"

"Masha Allah, ba wanda zai ce mamanku ce ta haifeku, sam ba ta tsufa ba" yayi maganar yana murmushi.

Abubakar ya kalli Usman ya ce "Meyasa ba a gaya mini tun a jiya ba, sai yau da asuba Aliyu ya gaya mini".

"Mama ce ta ce kar a gaya maka, kar ka ce zaka taho a jiya, ga wanda ya tsinto ta a katsina nan" yayi maganar yana nuna masa bashir.

Abubakar ya nufe shi ya miƙa masa hannu yana faɗin "Ɗan uwa, mu gode mun gode Allah ya saka maka da alkhairi, tun da aka ɗauki rumaisa muka rasa nutsuwa mun gode sosai Allah ya biya" ya sake komawa wurin ruma yana dubata ya ce "Allah sarki autarmu, haka ki ka koma duk kin rame ruma, kullum tunaninki muke yi"

"Nima kullum sai na yi tunaninku, sai na ganku a mafarkina" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Bashir ya dubi Adam ya ce "Akwai buƙatar mu tafi, na san masu zuwa dubiya zasu yi ta zarya, mu ƙyaleta ta keɓe da 'yan uwanta" takawa bai iya cewa komai ba, Bashir ya ja hannunsa suka fita.

Suna tafe a hanya Adam ya ce "Ka wuce da ni gidana, bana son komawa gida yanzu".

Bashir ya ce "Shikenan, amma dan Allah kar ka je ka damu kanka, ko ka yi ta tunani, hakan ba wani amfani da zai yi maka" still dai Adam bai ce masa komai ba.

Can bashir ya kuma cewa "Amma it seems you know each other before kai da yarinyar nan, a ina ka santa?"

"Bashir, dan Allah ka ƙyaleni, ina cikin tsaka mai wuya, dole yarinyar nan ta yi magana, kan al'aamrin nan ya ƙara kwaɓewa" yayi ya a hasale.

Bashir ya ɗan gyaɗa kai ya ce "Haka ne, amma dole ka rage zafin zuciyar nan mu bi a hankali, dan yarinyar nan da alama gardamammiya ce ta fika taurin kai" ya cigaba da tuƙi, ba wanda ya kuma cewa komai.

Can gidansu Adam kuwa, su Iman suka ƙara shiga damuwa, ganin ammi ba ta fito karyawa ba, kuma sun je wurinta hadimarta ta tabattar musu da cewa ta ce kar wanda ya je wurinta, tana buƙatar kaɗaici.

Cikin damuwa Nusaiba ta ce "Iman, ko ke kin san wani abu ne da yake faruwa, why are they behaving like this? They all look strange today"

Cikin damuwa iman ta ce "Tare fa muka kwana muka tashi da ke, ban san komai ba, nima dai na shiga damuwa da mamaki, wani abu yana faruwa amma maybe ba sa son mu sani ne".

"Amma ko menene wannan, abu ne mai girman gaske, tun da har ta kai ga ammi ta ce kar wanda ya je wurinta, ga takawa tunda suka fita da abokinsa bai dawo ba" suka koma suka zauna suna tattaunawa a falo.

Baba uwani ce ta same su ta ce "Yaran nan meya samu giwar Galadima ne yau, daga ita har ɗan gidana na kasa gane kansu yau, ko abinci ba ta bari an shigar mata da shi ba, shi kuma ina magana bai ko kalleni ba, duk da miskili ne amma ba ya shareni idan na gaishe shi"
Iman ta ce "Zancen da muke yi kenan, bamu san meyake faruwa ba"

"To Allah ya sa dai lafiya" tayi maganar ba tare da ta ji daɗin rashin samun wani bayani ba.

Ƙamsshin turarensa da ya daki hancinta ne ya sanya ta san shine, a take ta ƙara tsuke fuska.

"'yan matan ammi, ya na ganku kun yi tsilli-tsilli da ido kamar marasa gaskiya ne?"

Nusaiba ce ta fara cewa "Uncle J ina wuni?"

"Lafiya lau" ya amsa yana ƙarewa iman kallo. Banza ta yi masa taƙi kulashi.

"Iman ba zaki kulani ba?" Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta.

Ya ja wata irin ajiyar zuciya ya ce "Ina ammi ne?"

Nusaiba ta ce "Tana hutawa ne, ta ce kar a dameta yau"

"Takawa fa, tun jiya rabona da shi, ga wayoyinsa ba sa shiga gaba ɗaya, a gidan nan ya kwana ne ko gidansa?"

"Eh a nan ya kwana, amma yanzu baya nan"

Ya ɗan yi shiru sannan ya kuma cewa "Ba ku san in da ya tafi ba?"

Nusaiba ta waro ido ta ce "Uncle J, takawa ne zai gaya mana wani wuri da za shi? Bamu sani ba".

"Wai ya nake ganinku duk wani iri ne, ko akwai abun da ku ke ɓoye mini?".

Nusaiba ta ce "A'a Bakomai".

Miƙewa iman ta yi zata bar falon "Iman" ya kira sunanta.

Ta tsaya cak ta waiwayo tana jiran abun da zai ce.

"Zo ki zauna ina da magana da ke"

Ji ta yi tamakar ta ce ba zata dawo ba, amma ta nemi wuri ta zauna.

Yayi wa Nusaiba alama da ido, a kan ta basu wuri. Ba musu Nusaiba ta tashi ta bar falon.

Kujerar two seater da iman ke kai, ya zo ya zauna, ya ɗan tsura mata ido, amma ta takure jikinta, kamar yana motsawa zata zura da gudu.

"Iman" ya kira sunanta, ta ɗan ɗago amma ba ta kalleshi ba.

"Meyasa ki ka yi blocking ɗina a what's app, da phone ɗinki gaba ɗaya?" Tayi shiru tana sauke numfashi.

"Am talking to you, or just because i ask for your pictures, you can deny it if you don't want, meyasa zaki yi blocking ɗina, bari abun da ki ke ta gudun kar in faɗa, i love you, ina son ki iman, kuma zan bi ta in da na san zan samu abun da nake so kai tsaye, kin san tsarin gidan sarauta ai, so gara ki kwantar da hankalinki ki daina kaucewa" hawaye ne ya cika mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login