Showing 216001 words to 219000 words out of 224014 words
shi wasu lokutan.
***
Tun da rumaisa suka yi waya da ammi, take ta zuba ido ta ga ta ina za a kawo mata Sabir ta ganshi, danne zuciyarta kawai take yi, mussaman idan ta tuna da alwashin dabta yi wa Adam, a akan ba zata sake zuwa gidansu ba.
Ammi kuwa ta kasa ta tsare, ta ce lallai Adam ya ɗauki Sabir, da shi da Iman su je a kaiwa rumaisa shi, ko awanni su yi tare ta ganshi, tun da dai an yi mata alƙawarin yin hakan, a duk lokacin da ta buƙata.
Tun da Iman ta ji za su je gidansu rumaisa, gabanta ya faɗi, saboda tana matuƙar fargabar haɗuwa da yayan rumaisa mai sunan baba, dan ita gaba ɗayansa tsoro yake bata.
Adam dan dai babu yadda zai yi da ammi ne, ba zai iya bujerewa maganarta ba, amma a ganinsa tun da ya yadda da auren, wannan aika shin da ammin take, ba abun da zai janyo masa sai raini.
Da la'asar suka shirya, aka shirya Sabir suka fito domin tafiya gidansu rumaisa, Adam na gaba iman na bin sa a baya da Sabir. kasancewar Mahmud ƙafarsa ta fara sauƙi, ya fara yawonsa a cikin gidan, hango Iman yayi da yaron a hannunta, wanda ko ba a gaya masa ba ya san shi ne jaririn, haka nan ya ji ya kwaɗaitu da son ganin fuskar yaron, tun da a yanzu, kansa kawai ya hango, mai ɗauke da tulin suma baƙa wuluk.
Suna tafe a hanya Iman na yi wa sabir wasa, yana ta miƙa hannu yana son kamo sitiyarin motar.
"Iman" Adam ya kira sunanta.
"Na'am yaya".
"Abubuwa sun fara yi mini zafi, na san magana zata fara yawo a kan auren nan nawa, dan Jamil ya zo ya tutsiyeni na gaya masa idan maganar gaske ne, kuma na tabattar masa da gaske ne, abun da nake so da ke, dan Allah ku yi shiru da bakinku, kar wanda ya san wa zan aura, idan an yi auren sa ganta"
"Yaya kunya ka ke ji ace rumaisa ce matarka?"
"Ke rabu da ni kawai, banda rigimar ammi, ina ni ina wannan Yarinyar da a rayuwarta babu wanda ta raina kamar ni, kuma bana son a cutar da ita, Samha haryanzu tana son aurena, a wannan karon ma ba zai yiwu ba, shiyasa bana son kowa ya san wacece".
"In sha Allah yaya ba zan faɗawa kowa ba, ammi ma ta gargaɗemu a kan hakan"
Ya ce "Good, ku shiga ki kai mata shi, ni zan je gidan gona, wancan karon ban samu na je ba, saboda wani dalili " yayi maganar lokacin da ya yi parking.
Ta ce "To shikenan, sai ka dawo" ta sauka ta ɗauki kayan rumaisa da ammi ta sake bayarwa a bata, ta shiga gidansu rumaisa da sallama.
Sai dai gidan shiru, babu alamar aksai mutane a gidan.
Iman ta yi sallama, sai dai muryar da ta amsa mata sallamar ce ta razanata. Kasa shiga ta yi, ta kuma kasa komawa baya.
Shi kuma bai kuma tankawa ba, sallama ta kuma yi, ya ce "An amsa a shigo mana" daga ɗakin mama take jiyo muryarsa, kamar mai shirin arangama da horo, ta shiga ɗakin.
Mai sunan baba ne a zaune yana cin abinci, mama kuma tana salla.
Cikin ɗar-ɗar, ta shiga ta zauna hannunta rungume da Sabir, kanta a ƙasa ta ce masa "Ina wuni?"
Bai kalleta ba ya ce "Lafiya lau" Sabir ya ƙurawa mai sunan baba ido, "Miƙo mini shi" yayi mata maganar cikin umarni.
Kai a ƙasa ta miƙa masa Sabir, ya rungume shi yana cewa "My boy, ka ƙara girma Masha Allah" bai yi masa ƙyuya ba, ya cigaba da cin abincin sa, iman ƙoƙarin satar kallon mai sunan baba take tana tsoro, shi kuma da ya lura da hakan, sai ya tsareta da idonsa tana ɗaga ido suka yi ido huɗu, aikuwa ta razana ta sunkuyar da kanta.
'Yarinyar nan tana da hankali kuwa?' mai sunan baba ya tambayi kansa.
Mama ta idar da salla da addu'a, ta juyo tana yi wa iman sannj da zuwa.
Iman ta gaisheta mama ta amsa mata cikin sakin fuska, Iman ta ce "Ammi ce ta ce a kawo wa Anty rumaisa Sabir"
Mama ta ce "Allah sarki, yanzu za ta shigo daga islamiyya, ya babansa?"
"Yana lafiya shi ya kawomu, zai dawo ya ɗaukemu ma"
Mama ta kalli Sabir ta ce "Mutumin, zo mu gaisa mana" ya sake kwanciya a jikin mai sunan baba, yana cin hannunsa.
"Allah ka aika munafukinmu ƙarshen nesa, mamarmamar, igiyar ƙasa ko da lafiya ko babu mamarmamar" Rumaisa ta shigo tana waƙe-waƙenta, da ƴan ciye-ciye.
Tana shiga falon mama sabir ta fara gani, ta buga tsalle zata ɗauke shi, mai sunan baba ya ce "Fita ki yi sallama" sumi-sumi, ta koma ta yi sallama, sannan ta ɗau sabir tana murna.
Ta kalli Iman ta ce "Anty iman sannu da zuwa, ya ammi?"
"Tana lafiya tana gaishe ki"
Babban abun da ya bawa mama mamaki, bai wuce yadda Sabir ya saki fuskarsa ba da ya ga rumaisa.
Rumaisa ta shimfiɗa tabarma a tsakar gida ta ce "Anty Iman, dawo daga nan mu yi hirarmu, ya fi iska"
Haka yayi wa iman daɗi, dan mai sunan baba ya takurata.
Rumaisa ta cire wandon uniform ɗin ta, daga ita sai rigar uniform, ba hijjabi ba ɗankwali, sai murna take yi.
"Anty Iman, bari na zubo mana abinci"
Iman ta ce "Wallahi a ƙoshe nake"
"Ba kya cin abincin gidan talakawa dai"
Da sauri Iman ta ce "A'a wallahi"
Rumaisa ta ce "To kawai zan zubo ki ci".
Rumaia ta zubo wa Iman jallof rice, mai kyau har da nama, ta kawo mata ruwa, ita kuma ta ɗauko tukunyar da aka yi girkin da cokali da yaji ta zo ta zauna.
"Anty rumaisa me zaki yi da tukunya kuma?"
"Ƙanzon shinkafa zan ci ya fi daɗi"
Iman ta zuba mata ido tana dariya, rumaisa ta din ga kankarar ƙanzo ta na ci, Sabir ya din ga zura hannu yana nema ya ci shi ma.
Iman ta na cin abincin tana yi wa rumaisa santin abinci yayi daɗi.
"Garadan mama ne suka girka, kuma ba wani daɗi yayi ba kar su ji ki ziga su" hira suke yi sosai da iman.
Suna tsaka da hirar suka ji sallamar Adam a ƙofar shigowa gidan, suka amsa masa, mama ta ce ace ya shigo, mai sunan baba ya tashi ya baro ɗakin mama, dan ya san nan zai shiga.
Adam na shigowa da rumaisa ya fara tozali, ta taƙarƙare tana kankarar ƙanzon tukunya tana ci, kamar mayuwanciya, ga kuma abinci mai kyau a gaban iman, Sabir kamar zai shiga cikin tukunyar, yana son ya duntsi ƙanzon ya kai bakinsa.
Ayshercool.
08081012143
PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228,AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143.
Sallamar Adam bai hana rumaisa cigaba da taƙarƙarewa tana ƙwaƙwalar ƙanzo da cokali tana cin kayanta ba, ba ta da niyyar tashi ma ta saya jikinta, abun da ya dameta kawai take yi.
Usman da tun zuwan iman yana cikin ɗakinsu, ya leƙa ta window, ji yayi kamar ya fito ya kifawa rumaisa mari.
Adam ya wuce su, ya shiga wurin mama, Iman ta kalli rumaisa ta ce "Anty rumaisa baki gaida takawa ba?"
Ruma ta kwaɓe baki ta ce "Kin ga ya kulani ne?"
"Amma da kin yi masa magana zai kula ki"
Rumaisa ta ce "Wallahi ba zai amsa ba"
Cikin mamaki iman ta ce "Meyasa ki ka rantse"
Ruma ta ce "Mufa gidan nan babu mai kalar halin da babu, dan haka ko sau ɗaya na haɗu da mutum zan gane halinsa, ni ba dan Sabir ba kuma a daina ce mini ƴar iska ba, ba abun da zai saka na aure shi, kuma dai ina son ammi ita ma ina jin maganarta, amma wannan mak faɗan da zuciyar taɓ"
Iman ta ce "Wai ni, meyasa ba kwa shiri ne, wallahi takawa mutumin kirki ne sosai Anty rumaisa, ko wani abun yayi miki?"
"Hmm ba ruwanki a wannan faɗan"
Iman ta ce "Haka ne, faɗan masoya ne" aikuwa rumaisa ta ƙware da ƙanzo jin abun da iman ta ce, "Taɓ lallai kin tafka saɓo"
Iman ta kuma cewa "Allah Anty rumaisa, yaya Adam yana da kirki sosai, ki din ga yi masa uzuri, abubuwa sun saka shi a gaba, kawai kina ganinsa a haka ne, idan ki ka ji abubuwan da yake ciki sai kin tausaya masa".
Ruma ta taɓe baki ta ce "Da zai gane da ya daina ɗaukar damuwowinsa a zuciyarsa, babu abun da zasu ƙara masa sai nauyin zuciya, ya din ga ɗaukar damuwowinsa a ƙwaƙwalwarsa, ita ke da ma'aunin samar da mafita"
Mamaki ne ya kama Iman, jin rumaisa na wani lissafi, da ba ta gane ba.
"Ban gane me ki ke nufi ba".
"Kar ki damu, manta da ni kawai, bari na ɗauko takarda da biro ki rubuta mini lambar wayarki, zan din ga kiranki muna hira".
Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai jotter a jakata, bari na rubuta miki" Aikuwa ta rubutawa rumaisa lambarta, a lokacin rumaisa ta shagala da wasa da sabir, sai dariya yake yi.
A daidai lokacin Adam ya fito, mama ganin a yadda rumaisa ke zaune ba ƙaramin ƙular da ita ya yi ba.
Iman ta ce "Anty rumaisa kawo shi mu tafi" a take jikin rumaisa yayi sanyi, ta sake rungume Sabir.
Mama ta ce "Ke bana son shirme, ki ba ta shi su tafi"
Kawai ta fara kuka, hawaye wani na bin wani, wanda a ganin adam kawai shagwaɓa ce da wulaƙanci.
"Mama dan Allah a bar mini shi a nan, mu kwana tare" mama ba ta saurari rumaisa ba, ta karɓi sabir ta bawa iman.
Wadda jikinta yayi sanyi, tausayin rumaisa ya mamaye mata zuciya.
Kallon ruma da take kuka Sabir yake yi, Iman ta ce "Ka yi wa maminka bye-bye"
Kwaɓe baki ya shiga yi, zai yi kuka, Adam ya karɓe shi ya yi waje da shi, saboda haka nan ya ji tausayin su ya kama shi, wata irin Soyayya mai ban mamaki tsakanin yaro da zuciyar da ba ta uwassa ba.
Iman ta dafa kafaɗar rumaisa ta ce "Anty ruma ki yi haƙuri kin ji, da kun yi auren nan, za a dawo miki da sabir ɗinki, ki daina kuka" ruma ta jinjina mata kai ta ce "Ki gaida Ammi, da wannan ɗin nan mai kamar da baban sabir"
"Tom za su ji in sha Allah"
Suna tafiya mama ta dirarwa da rumaisa faɗa, mussaman a kan rashin hankalin da ta tafka, a gaban wanda zata aura ta taƙarƙare tana kankarar ƙanzo tana ci, babu ko kunya balle kawaici, ga wannan koke-koken na babu dalili da take yi, a duk lokacin da aka kawo sabir.
Ita dai rumaisa a wurinta, ba ta ɗau adam wani na mussaman ba, balle idonsa ya hanata abun da take yi, tun da duk gidansu maza ne, ita ba ta ɗau abun da ta yi wani laifi ba.
Maganar Sabir kuwa, ta barwa ranta cewa babu wanda ya san halin da take ciki sai Allah a kan yaron nan, dan haka ta daina damuwa a kan mitar da ake yi mata.
Usman ya fito yana faɗin "Bagidajiya kawai, wannan ai yawa ne ki ka yi, to wallahi nan gaba rainaki zai yi, sai la ce wata budurwar ƙauye, ke ba wani class bakomai"
Abdalla da bai daɗe da shigowa ba, ya tambayi mai ta yi, Usman ya gaya masa, ya ce "Kai yanzu har wani aji kake nema a wurin rumaisa, ai tun da suka ce za su aureta a haka, sai fatan Allah ya sanya su gama lafiya"
Ko a jikinta, an mintsini tattaura, abun da ya dameta kawai shi ne a gabanta.
***
Su Iman da suka koma gida kuwa, Ammi ba ta nan, Iman ba ta son ta fita ta koma gida ta tarar Ammi ba ta nan, gashi tare suka fita da Nusaiba, Kasancewar Sabir yayi bacci, da shi Adam ya tafi sashinsa ya kwantar da shi, Iman kuma ta wuce ɗakinta.
Sai dai tana zuwa ɗakin, ta yi tozali da Samha a tsaye, sai da ta razana ta ce "Anty Samha lafiya kuwa?".
"Ban sani ba, munafuka tsintacciyar mage da ba ta mage" cikin rashin fahimta iman take kallonta, dan ba ta san me ya kawo wannan maganar ba.
"Saboda tsohuwar munafuka ce, shi ne ki ka je ki ka cewa giwa kina son Adam, za a haɗa aurensa da ke a maimakon ni, duk da irin kashedin da na yi miki ko?"
Kamar zata yi kuka ta ce "Ni kuma?"
"Ke ɗin fa, algunguma ni zaki yi wa pretending, to ki rubuta ki ajiye, gidan Adam kabarinki ne, yadda aisha ta shige shi ta bar duniya, duk wadda ta shiga bani ba sai ta bita, idan ba haka ba kuwa ayi babu, kowa ya rasa daga ni har ke, da ni ki ke zancen, zan yi maganinki baƙar annamimiya"
Gaban Iman ya faɗi da jin furucin da Samha ta yi, tana gama zazzage mata ta yi waje.
Jikin iman har rawa yake yi, saboda tsananin tashin hankali, da yadda hankalinta ya dugunzuma, a take rumaisa ta faɗo mata, wato a zaton Samha Takawa ita zai aura, tausayin rumaisa ya kamata ya ruma za ta yi da wannan manyan al'amura ta ko ina, ga maƙiyan mijinta, ga tarin ƙalubalen gidan, ga kuma masifar Samha, a kaf dangin nan babu wanda bai sarawa masifar Samha ba, an shakkarta sosai da sosai, saboda a tsaye take ba ta da kunya, yaya rumaisa za ta yi da ita, ita da take yarinya ƙanƙanuwa?.
Rasa abun yi ta yi, ta saɓule ta zauna a kan gadonta, ƙirjinta na cigaba da dukan uku-uku saboda tsananin fargaba.
Mintuna kusan sha biyar da fitar Samha, amma iman ta kasa kataɓus, ƙirjinta sai cigaba da bugawa yake yi.
Nusaiba ce ta shigo da sallama ta ce "Ashe kun dawo, bamu zaci zaku rigamu dawowa ba, mun je sai wa Sabir kaya, kin san ya kusa 6months, Ammi sai nuna mini irin kayan da za a zubawa amaryar takawa a lefe take, ya kuka baro ta?" Sai da Nusaiba ta kai aya, sannan ta lura kamar Iman a tsorace take.
"Lafiya kuwa?"
Iman ta jinjina mata kai ta ce "Lafiya lau"
Nusaiba ta ce "Kin ga idonki kuwa kamar mara gaskiya, ko wani abun ya faru a gidan da ku ka je ne?" Iman ta girgiza kai alamar a'a.
"Tsaya, ko jikinki ne ya motsa?"
Iman ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu ko ɗaya, cikina ne ya ɓaci zuciyata ce take tashi"
Nusaiba ta sauke numfashi ta ce "Har kin tsorata ni, bari na kawo miki anti acid, ina da shi a ɗakina" iman ta jinjina mata kai.
Da Nusaiba ta fita ta sanarwa da Ammi iman ba ta jin daɗi, ulcer ya tayar mata, a rikice ammin ta nufi ɗakin Iman, ta je ta tutsiyeta tana tambayar ko jikinta ne ya motsa.
Kamar yadda ta yi wa Nusaiba ƙarya, haka ta dake, ta ɓoye damuwarta, ta tabattarwa da ammi, ulcer ne kawai ya tasar mata.
***
Kwanciya ce ta isheshi, musamman da kwana biyun nan, a gida yake wuni saboda ƙafarsa, amma yanzu ta yi saƙi sosai, kawai dai fita ce bai yi ba, gashi ya kusa komawa makaranta.
Kamar wanda aka tsikara, ya tashi ya fita falo, ya ɗau lemon kwali mai sanyin gaske, ya koma ɗakinsa, corridor ya nufa, ya buɗe tagar a hankali, wata sassanyar iska ta dake shi, ya zuƙe lemon tare da lumshe idanunsa.
Dare ne sosai, manyan security lights, sun haske ko ina na gidan, kukan tsuntsye na ta tashi, da ƙanan ƙwari, ga ƙamshim furannin harabar gidan sun gauraye da sassanyar iskar da ke kaɗawa.
Yanayin yayi masa daɗi sosai, sai dai babu tsammani ya ga wani abu yana dudduƙe, yana motsi ta jikin fulawoyin da zai sadaka da sashinsu.
Tsayawa yayi ya ƙura ido sosai, yanayin inuwar abun, kamar mace ce, dan har da lulluɓinta.
Mamaki ne ya kama Mahmud, ganin maimakon ta shigo direct ƙofa, ta kutsa can ƙarshen ginin da kai tsaye ɗakin Mummy zai kai ka.
Bai yi wata-wata ba ya sauka, ya nufi sashin Mummy a hankali, sai dai bai buɗe ya shiga ba.
"Kin shanya ni, tun ɗazu nake zaman jiranki, amma baki zo ba"
Baba uwani ta risuna ta ce "Tuba nake Allah ya baki yawan rai, sawu ne bai gama ɗaukewa ba"
Mummy ta hura hanci ta ce "Ina jinki, bani labari, meke wakana da ki ke son ganina?"
"Allah ya baki yawan rai, labari ne nake tafe da shi, idan yayi miki daɗi haka nake fata, idan bai yi ba ayi mini aikin gafara"
Cikin ƙosawa Mummy ta ce "Hanzarta, ina jin ki"
"Takawa zai yi aure, sai dai alamu sun nuna kamar Iman zai aura, kuma zancen ya iske Samha ƴar wurin turaki, dan ɗazu ta zo har wurin Iman ɗin ta yi mata kashedi da zafafan kalmomi, dan na laɓe na ji komai"
"What? Aure kuma? A wannan karon kuma ita za a liƙawa, ita ma ya cinyeta, lallai giwa ba ta tsoron Allah, amma na yi mamakin yadda aka yi Samha ta zo ba ta ƙaraso nan ba, kuma ba ta yi mini wannan bayanin ba, ko da yake ni kujera ce, ko dan zama za a neme ni, jeki na gode na ga yadda wannan lamarin zai yiwu"
Baba uwani ta ce "Godiya nake, na barki lafiya".
Mahmud ya so shiga ɗakin Mummy, dan ganin wacece wannan, take zuwa a tsohon daren nan, amma ya fasa, ya lallaɓa ya buɗe ƙofa ya fita harabar gidan ya laɓe.
Can baba uwani ta fito tana dudduƙenta cikin duhuwar fulawoyi, ta nufi sashinsu ammi, tana buɗe ƙofar, fitila ta hasketa, dan haka ya ganeta da kayan jikinta.
Hakan ya fallasa ma wacece ita, domin kuwa baba uwani kayanta ba ɓoyayyu bane ba, duk da tarin alkhairai da suturar da ammi ke bata, amma kullum cikin kaya ɗaya zuwa uku take.
Kan sa ya ɗaure da mamakin me take zuwa yi sashinsu, a wannan daren cikin siga ta rashin gaskiya
A hankali ya koma sashinsa, gaba ɗaya baya son wannan halin na Mummy, na bin diddigi da shiga abun da babu ruwanta, ya san ƙarshe ba zai wuce rahoton wani abun ake kawo mata ba. Amma ya sha mamaki, idan har ace hadimar ammi ta kusa da ita, za ta aikata mata haka, to duniya kowa ma ba abun yarda bane ba.
***
Kwanci tashi asarar mai rai, mai girma turaki ya dawo daga aikin umara da ya tafi, duk da an riga an saba zuwa, amma ba a rasa ƴan sannu da zuwa da su kan zo, domin yi masa barka da dawowa.
Ammi ba ta son takura masa, dan haka ta bashi lokaci, tare da