Showing 138001 words to 141000 words out of 224014 words

Chapter 47 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1090

bayan ke sai mu, wanda hakan shawarar ki ce, har zuwa lokacin da kika bayar da shawarar ta je Saudiyya wurin ɗan uwanki kawu mahadi, ta zauna ta raini cikin a can, idan ya isa haihuwa ta dawo Nigeria, duk dan kaucewa hatsarin da ka iya faruwa da cikin, muka yi nesa da juna ni da ita.
Bayan na kai ta ta yi watanni huɗu, na sake komawa Saudiyya umara, na dubata, na dawo babu daɗewa ta ce mini ita ta gaji da zaman Saudiyya so take ta dawo gida. Ta ce mini wannan kakar ta ta, mariƙiyar mamanta babu lafiya, dan haka ita so take ta dawo ta je ta ganta, kar ta rasu basu gana ba. Gudun ɓacin ranki, ya sanya ta dawo babu wanda ya sani, sai dai a lokacin cikin yayi girma sosai ta sanya rigima a kan lallai sai ta je duba matar, an ce ba ta gane kowa, wankin ƙoda ake yi mata ma. Duk sauƙin kan Aisha, haka ta kafe a kan lallai sai ta je katsina duba matar, a daidai lokacin kuma ni tafiya Abuja ta kamani, bayan tafiyata ta sanya ɗaya daga yarana, masu tsaron lafiyarta ya kai ta katsina. Ta turo mini saƙo a waya tana bani haƙuri a kan ita fa ta tafi, ba zata iya jira na dawo ba, a tsorace take kar kakarta ta mutu. Bayan dawowata daga Abuja, sai samun saƙo na yi, an tsinci gawar yarona da motar, ita kuma ba a san in da take ba, tun da ga wannan lokacin nake ƙoƙarin gano in da take, har zuwa wannan lokaci, daga ni sai Bashir muke ta ƙoƙari, dan ko su Jabir basu sani ba, na san na yi laifi ammi amma ba da gayya na yi ba.

"Adam nika ɗai zan fuskanci wannan bayanin naka, duk mutane sun san da cewa tana Saudiyya, babu wanda ya san ta zo Nigeria haka zalika babu wanda ya san tana da cikin ma, kawai sai mu ce ga ɗa to ita tana ina, na gaya maka bana samunta a waya, amma ka yi ta yi mini ƙarairayi, dama akwai abun da zaka iya ɓoye mini Adam? Me zaka cewa Turaki?".

A raunane Adam ya ce "Ko babu wata cikakkiyar shaida,ni na san da cewa ɗana ne, babu yadda za ayi yarinyar nan ta san wasu abubuwan idan ba gaya mata tayi ba, amma ammi ni yanzu ba abun da mutane zasu ce ne ya dameni ba, samo aisha ne ya dameni, babu wata hujja da nake jira yaron nan nawa ne, ko a fuskarsa kamanni na ne, sannan da kaina zan gayawa turaki komai, duk hukuncin da zai yi mini zan ɗauka".

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Zan cigaba da yi maka Addu'a, Allah ya kawo mana mafita, amma yarinyar nan ka bita a hankali dan Allah, in sha Allah yadda jaririn ya kuɓuta, ita ma zata kuɓuta".

Adam ya jinjina kai kawai, ya tashi ya fita daga ɗakin, su Nusaiba suna falo a tsaye cirko-cirko, adam ya zo ya fice.
Cikin rige-rige suka tafi ɗakin Ammi, amma suka tarar ta shiga toilet, ko da ta fito umarni ta basu, na su je su kwanta sai da safe, dan kar su bi diddigin abun da ya faru, sai dai a tsorace take da abun da ka iya faruwa idan zancen nan ya fasu.

A asibiti kuwa, Aliyu ne ya dubi rumaisa ya ce "Ke dai a rayuwarki ba a taɓa rasaki da matsala, an samo uban yaro kin ce ba shi ne ubansa ba, sai ki nuna mana waye ubansa?"

Usman ya ce "Ai ko da uban me ki ke yawo, sai an mayar musu da ɗan su"

Mama ta ce "Yanzu dai a bar wannan maganar, Allah ya dawo mana da ita, daga dawowarta sai a bari ta sarara kan a hau yi mata faɗa, Ali ku je gida haka, kwa sanar da mutane an ganta"

Mai sunan Baba ya ce "Eh amma kar su sanar da Asibitin da take, kar azo a takura mata, ko ayi ta surutu saboda jaririn nan, a bari komai ya daidaita"

Mama ta ce "To hakan ma babu laifi, kar ku gayawa Abubakar a daren nan tun da ba a samu wayarsa ba, ku bari sai da safe kar ya ce zai bsro dutse yanzu"

Usman ya ce "In sha Allah"

Mai sunan Baba ya saka hannu, ya karɓi jaririn da ga hannun rumaisa, sai bin sa take da ido, kar ya fita ya bawa Adam yaron, ya ƙarewa yaron kallo ya ce "Bari na bawa nurses ɗin nan, su mayar da shi ɗakin da ake kulawa da sh, mama gobe in Allah ya kaimu zan zo mu koma ki ga likitan ki"

Mama ta ce "Ga mara lafiya ni ina zani? Dama rashin lafiya tawa saboda ita ne"

Ya ce "Duk da hakan, yakamata ke sai da safe, ki nutsu ban da gardama da taurin kai ki yi addu'a ki kwanta ki huta"

Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce "Dan Allah mai sunan Baba kar ka bawa kowa shi, wallahi zan iya rasuwa idan aka rabani da shi" bai ko waiwayo ba ya fice daga ɗakin.

Mama ce ga rungumota tana rarrashinta ta ce 'Ba wani zai bawa ba kin ji, ki yi haƙuri ɗakin da ake kula d shi zai kai shi" rumaisa ta yi lamo a jikin mama, can ta ce 'Mama"

Mama ta amsa mata da na'am.

"Ba mafarki nake ba ko, ba zan kuma farkawa na ganni a dajin ba, na ga kun daɗe a wannan mafarkin nawa".

Mama ta shafa bayanta ta ce "Ba mafarki bane ba, duk muna tare da ke".

"Mama kin ga yadda ki ka rungumenin nan? Haka maman yaron nan take rungumeni tana rarrashina idan na tunaki ina kuka, sarƙarta da zobuna ne a cikin ɗankwalin nan, ɗan kunnen da ki ka cire a kunnena shi ma nata ne, mama ba zan manta da ita ba" rumaisa ta yi maganar cikin kuka.

"To ya isa, ita ma in sha Allah zata kuɓuta cikin amincin Allah" rumaisa ta cigaba da kuka, dan ba wanda ta gayawa aisha ta rasu.

Aliyu suna zuwa unguwarsu, ya wuce gidan su Habiba, lokacin kusan ƙarfe goma na dare, ya aika yaro ya ce yana sallama da Habiba.
Maimakon Habiba sai babarta ta fito tana masifa, wani watsatstsen ne ya zo neman habiba a wannan daren, yar habiban guda nawa take?

Tana ganin Aliyu ta yi sak, ta ce "Ya aka yi ne, ko laifin ta kuma yi maka, ko ƙanwar ta ka ta kuma duka ka zo rama mata, duk da ance an yi garkuwa da ita"

Ya ce "Ba ɗaya, wani abu zan gaya mata".

"Wani abu ne kenan?"

Aliyu ya ce "Shikenan tun da na ga hankalinki bai kwanta ba"

Sai kuma ta ce "A'a, bari na taso ta" ta koma cikin gida, mintuna uku sai ga habiba ta fito tana mutsutsuka ido.

"Habiba" ya kira sunanta, ta kalleshi ta ce "Yaya Aliyu ina wuni"

"Albishirnki" yayi maganar cikin murmushi.

Ta ɗan yi saroro ta ce "Goro".

"To zaki bani goron nan, Alhamdilillah addu'a ta karɓu, rumaisa ta kuɓuta yau, tana asibiti ma"

Gigicewa ta yi ta ce "Innalillahi, dan Allah da gaske, dan Allah kar ka ce da wasa kake yi, dan Allah mu je in ganta".

"No, ba a zuwa wurinta yanzu, ba ta da lafiya, amma zan zo da kaina na kaiki ki ganta"

Hawaye ta fara matsewa tana "Allah sarki ƙawata, Alhamdilillah, Allah na gode maka"

Ya ce "Maza ki je ki cigaba da baccinki, Sai da safe"

"Dan Allah yaushe zaka zo ka kaini na ganta, gobe?"

"A'a zan zo dai, ki je ki cigaba da baccinki" yayi maganar yana ɗaga mata hannu ya tafi.

Ta shiga gida da gudu tana murna.

Adam kuwa yana zuwa ɗaki ya zauna ya fashe da kuka kamar yaron goye. Wai matarsa ce ta haihu a daji a hannun 'yan bindiga, ko a yaya ta haihu oho, ko a wani hali take sanin gaibu sai Allah.

"Why aisha, meyasa ki kasa jira na dawo ki ka tafi? Duk yadda muka tssra rayuwa bayan kin haihu, ƙarshe a tsinto mini ɗana babu ke, haba aisha kin ga sakamakon rashin jin magana ko, matar da ki ke so ki je ki duba ita bata mutu ba, amma ke kin shiga wahala. Amma bakomai, Allah ya sa kina cikin ƙoshin lafiya, zan fito da ke ko da zan rasa rayuwata ne!


ƘANWAR ₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*

Ayshercool
08081012143.


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


*₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam, jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*





Haka Adam yayi ta surutai, kamar zai zauce.

Mama kuwa kwana tayi tana salloli tana miƙa godiyar ta ga Ubangiji, na bayyana mata rumaisa da yayi, idan aka jima sai ta je ta leƙa fuskar rumaisa, kasancewar ita da Abdallah ne a wurin ruma, Abdallah yana gefen  gadon rumaisa sai kallonta yake yi, shima ganin abun yake kamar wasa wai rumaiss ta dawo.

Mama tana tsaka da salla, ruma ta farka daga bacci tana cewa zata yi fitsari, Abdallah ya ɗagata cak ya kaita banɗaki, mama tana ta gyaran murya, amma ya kai ta tayi fitsarin, sannan ya mayar da ita kan gadon ya kwantar.

Ta kalleshi ta ce "Yaya Abdallah"

"Na'am rumaisa".

"Kaga haryanzu ban tashi daga baccin ba"

Yayi murmushi ya ce "Ai a gaske ki ke ba bacci bane ba".

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ai na kasa ganewa ne, wataran sai in ganni a dajin, wataran a nan amma dan Allah mai sunan Baba bai bashi jaririna ba ko?".

"Bai bashi ba, yana can ɗakin yara".

"Alhamdilillah, ina son yaron nan bana son a rabani da shi"

Abdallah ya ce "To maman boy"

"Abdallah ban zaci zan rayu ba, na sha wahala sosai, ranar da aka tafi da mu, na din ga kuka na gaji da tafiya, aka goyani a babur, aka kaini wurin".

"Amma dai basu yi miki wani abun ba ko?"

"Wallahi sun yi mini, abubuwa ma da yawa, zan baka labari da safe, wannan ciwon na ƙeyata ne yake mini zafi, jikina ma duk babu daɗi, kwanana uku fa ina tafiya a daji".

Gaban mama ne ya faɗi, jin rumaisa ta ce an yi mata abubuwa da yawa tana matuƙar tsoro da fargabar ace sun lalata rumaisa, gashi haryanzu likita bai faɗi sakamako bincikensa ba.

Da safe mama ta tashi rumaisa, ya yi salla, ta wanke mata baki, ta yi mata wanka, ta saka mata wata 'yar riga domin ta samu ta sha iska, nurses suka shigo suka yi wa rumaisa dressing ɗin raunukan jikinta. Mama ta kalleta ta ce "Ko kina buƙatar wani abun? Ga kayan marmarin nan, wanne zan baki a ciki ki ci?".

"Ba ko ɗaya, kawai ki zauna a kusa da ni in rungumeki in ji ɗuminki" mama tayi murmushi ta ƙarasa kusa da ruma, ta rungumeta.
Abdallah ya koma gefe ya ɗan samu bacci, saboda daren bai yi bacci ba saboda farinciki.

"Rumaisa" mama ta kira sunanta, ruma ta ɗaga kai ta kalli mama.

"Ina fatan babu abun da suka yi miki, lokacin da ki ke wurinsu?"

Ta mayar da kanta ta kwantar a jikin mama ta ce "Mama ni meye ma ba ayi mini ba, bana son tunowa tsoro nake ji, mama ki ɗauko jaririna shi ma ayi masa wanka".

"Na ji, amma ina fatan..." Ba ta ƙarasa ba, ruma ta katseta ta hanyar cewa "Mama dan Allah ki daina tanbayata a kan mutanen nan, tsoro nake ji, dan Allah ki daina tuna mini" mama ta ce "To shikenan, bari in karɓo yaron".

Mama ta je ta karɓo jaririn, har nurses suke gayawa mama a kowane lokaci zasu iya sallamar yaron, zuwa yanzu babu abun da yake damunsa, kuma gwaje-gwaje sun nuna malaria ke damunsa, sai kuma pneumonia, amma ba wata mai damuwa ba.
Mama ta ce "To masha Allah, Ubangiji Allah ya ƙara afuwa".

Mama ta tafi da shi ɗakin da rumaisa take, ta karɓo pack ɗin da Bashir ya sayo na jaririn, da madararsa da komai.

Ta haɗa ruwa ta yi wa yaron wanka, ta shirya shi, ta haɗa madara ta bashi, ta miƙawa rumaisa shi. Ruma har da ajiyar zuciya ta zubawa yaron ido, sai ta fara hawaye.

Mama ta ce "To kukan na menene?"

"Mama tausayin yaron nan nake ji, mun sha wahala sosai da tuni an kashemu, ko shi an kashe shi, wasu mutane ne suka ce dole a kashe shi, kar ya rayu fa".

Mama ta ce "Wasu mutane ne?"

"Nima ban san su ba, Allah ya baka lafiya yarona" tayi maganar tana shafa kan jaririn, tana murmushi shi kuma sai cin hannunsa yake yi, yana kallon ruma yana lumshe ido.

Mai sunan Baba ne yayi sallama, shi da Usman, hannunsu ɗauke da kayan abinci.

Duk suka gaida mama ta amsa musu, ruma ta ce "Mai sunan baba ina kwananku?"

"Lafiya lau ya jikin naku?".

"Da sauƙi Alhamdilillah"

Umar ya ce "Allah ya ƙara afuwa, kai Abdallah tashi ka haɗa mata abun karyawa"

Abdallah ya haɗawa rumaisa shayi da uban ƙwai, ya bata da ƙyar ta sha shayin, ta ce ita bata son cin komai.

Mai sunan Baba ya sanya mama a gaba, a kan lallai sai ta tashi sun tafi gida, sai ta je ta huta ya kaita ganin likita, da ƙyar mama ta amince, ya sakata a gaba ya ce Abdallah ma ya tashi ya je gida ya huta ya dawo da yamma. Aka bar ta da ita da Usman, sai jaririnta da take ta shafa kansa tana murmushi.

Adam kuwa kwanan zaune yayi, yayi kuka kamar ya fita a hayyacinsa haka ya wayi gari, Ammi ma kusan a haka ta kwana, tunani kawai take yi a kan ina zasu samu mafita, ta ina za su fara.

Wajen ƙarfe goma na safe, Bashir ya je gidan su takawa, ya sa aka yi masa iso wurin Ammi, ta bayar da damar a shiga da shi, cikin girmamawa suka gaisa ya ce "Ammi dama na zo ne mu koma asibiti da Adam, muje mu ji ko akwai wani bayani da zamu samu daga bakinta yarinyar, tun da naga jikinta da sauƙi, amma na kira wayoyinsa a kashe na je can gidansa an ce bai kwana a can ba".

Ammi ta ɗan dube shi ta ce "Malam bashir ban ji daɗin ɓoye mini abun da ke faruwa da ku ka yi ba, gaba ɗaya kun jagwalgwala al'amura, amma shikenan na san ba laifinka bane, shi ya fi kamata ya sanar da ni, bari na duba ko a gidan nan ya kwana ma"

Ko da Ammi ta je ɗakin Adam a zaune ta tarar da shi, babu alamar ya runtsa, idanunsa sun yi jawur sun kumbura.

Ammi ta ce "Ka yi sallar asuba kuwa?"

Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Tashi ka yi wanka, ka karya ga Bashir can yana jiranka"

"Ammi dan Allah ya ƙyaleni, bana son jin komai, kaɗaici nake so".

"Shi kaɗaicin me zai maganta maka bayan mai faruwa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login