Showing 99001 words to 102000 words out of 224014 words

Chapter 34 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1106

kawai"

Wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya mama ta sauke, ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.

Huzaifa ya fashe da kuka, Yasir ma ya taya shi.

Cikin dakiya mai sunan Baba ya haɗe rai ya ce "Meye haka kamar wanda ba su je islamiyya ba, ba ku yi imani da ƙaddara bane? Yanzu kuka ne ya kamace ku ko kuma addu'a?" Haka ya din ga yi musu faɗa alhalin shima da zai samu space kukan zai yi. Ya tashi fuuu ya tafi ɗakinsu, yana zuwa ya tarar da Abubakar a zaune yayi shiru ya lula duniyar tunani.

Mai sunan Baba ya zauna a kusa da shi, ya ce "Akhi na dawo?"

Banza yaya Abubakar ya yi masa bai kula shi ba.

"Na san na yi maka laifi, amma yakamata ka yi mini uzuri, ba a hayyacina nake ba, idan ka gama fushin sai mu yi magana" ya yinƙura zai tashi Abubakar ya ce "Yaya ku ka yi da ka je, an samu labarinsu?"

"Babu wani labari mai daɗin ji, sai ma kayan takaici, ance mu saurara idan sun kiramu sun ce mana wani abu shikenan sai mu sanar".

"Idan kuma ba su kira ba a haka zata cigaba da zama a hannunsu?"

"I have no idea" mai sunan Baba ya faɗa cikin damuwa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Aki meye abin yi?"

"Addu'a" ya bashi amsa a taƙaice.

Dare ya tsala, wasu daga cikin al'umma sun kwanta suna hutawa, yayin da wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da iyalansu suke kwanan zaune, ciki har da mama da yaranta maza yayyen ruma gaba ɗaya mama ta manta da wani abu wai bacci a wannan halin da take ciki, a zaune take tamkar an dasata tun tana iya lazimin da addu'a har ta kasa ta rasa abin da ma zata ja.
Zuciyarta sai zafi take mata, da tunanin a wani hali ruma take ciki.

Wurin baccin ruma ta kalla, da yanzu tana nan mama tana faman gyara mata kwanciya ko tashinta fitsari, da yanzu ta yi ɗai-ɗai sauro na cizonta mama tana mita tana sake gyarata, ko ta ƙaro fanka idan ta fuskanci zafi yayi mata yawa, ko ta kashe fanka ta lulluɓeta idan sanyi yayi yawa.

"Ruma ko a wani hali kike? Ko kina raye? Ko kin ci abinci? Ya in da ki ke kwance? Sanin gaibu sai Allah, ya rabbilarshil azim, dan girmanka Allah ka tsare mini 'ya ta da sauran 'ya'yan musulmi, Allah ka dawo mini da ita cikin aminci" ta ƙarasa addu'ar kuka yana kufce mata, sai a lokacin ta ɗan ji nutsuwa da ta samu hawayen idonta ya zuba.

Ɗakin 'yan mazan ma gaba ɗaya idonsu biyu, wasu da Alqur'ani wasu a kan sallaya, wasu suna kuka, dan basu taɓa tsintar kansu a cikin mummunan tashin hankali kamar wannan ba.

Ruma ta yi rigingine a filin Allah, wani irin sanyi yana ratsata ga cikinta kamar ya haɗe da bayanta saboda azabar yunwar da take ji, ga ƙaiƙayi da jikinta yake mata saboda rashin wanka, ga wani irin sauro na bala'i da ƙwari suna gasa mata cizo.

A hankali ta furta "Mama, mai sunan Baba" sai kuma ta yi shiru hawaye ya fara zirarowa ta gefen idonta.

Tana tsaka da tunanin, wurin yayi tsit, mutanen sai kewayasu suke yi da manyan bindigogi.

Wani irin sauti ruma ta din ga jiyowa na motoci ƙasa-ƙasa, daga bayan dutsen da ke nesa da su.

"Sha tara ga motocin smoke can suna aiki fa" cewar ɗaya daga cikin 'yan bindigar.

" 'yan wahala ba, ni mamaki nake yadda suke iya fitar da sabgar nan ba wata matsala" ɗayan ya bashi amsa.

"Haba, sun gama sai ta komai nake gaya maka, babu wanda ya isa ya tare musu hanya, babban controller na ƙasa ma fa nasu ne, kuma akwai na sa kason a ciki mu suka mayar 'yan iska kawai".

Sha tara ya ce "Aikuwa sai mu yi tawaye, ko dai su yi wani abu a kai ko mu bujure, haba ma'adanan nan fa da suke kwasa ba dan muna gyara musu aikin nan ba da ba zai yiwu ba, amma kura da shan bugu gardi da kwashe kuɗi".

"Kai ni ba wannan ba ma, oga nake jira ya zo ayi wadda za ayi a san yadda za ayi da mutanen nan"

"Eh gobe zasu shigo ai"

Haka suka cigaba da hirarsu, amma kan ruma ya ɗaure, wasu ma'adanai ake kwasa meye ma ma'adanan?

"Zan yi fitsari" ta faɗa cikin rawar murya".

"Yi a nan" ɗayan ya bata amsa.

"Ina jin yunwa ma"

"Idan ki ka kuma magana sai na taka ruwan cikinki"

Guntun tsaki ruma ta yi, tayi juyi wani abu da ba ta san menene ba gasa mata cizo, wata uwar ƙara ta saki, ta miƙe tana kuka.

"Wai wannan wace irin iblishiyar yarinya ce meye kuma?"

"Wani abu ne ya cijeni" ta yi maganar a gigice tana soshe-soshe.

"Nemi wuri ki zauna ki rufewa mutane baki, ni wallahi da oga ya zo da na daɗe da harbe wannan shegiyar yarinyar da ba ta rasa matsala".

"To ku mayar da ni in da kuka ɗauko ni mana, meyasa zaku kawo ni nan" tayi maganar a sangarce

Hasketa ɗayan yayi da hasken fitila, ta saka hannu ta kare tana motsa baki, saukar wani abu ta ji a goshinta mai nauyin tsiya, daga haka ba ta sake sanin in da kanta yake ba.

Bayan sallar asuba, su Abdallah suka sanar da abin da yake faruwa a masallaci, tare da roƙon bayin Allah su taya su da addu'a, Allah ya fito da rumaisa cikin aminci da ƙoshin lafiya.
Mutane da yawa sun kaɗu da jin abun da ya samu ruma, dan ruma ta mutane ce, da yawan mutane sun santa, kan gari ya gama haske unguwar su ta cika da labarin yin garkuwa da ruma.

Gari na gama yin haske aka din ga sintirin zuwa yi wa mama jaje, tare da addu'ar Allah ya bayyana ta.

Mama duk yadda ta so ta jure, ta kasa haka ta dinga share hawaye, masu cewa ta daina kuka kuwa kallonsu kawai take yi, gani take ba su san a cikin tashin hankalin da take ba ne.
Hatta daga islamiyya su ruma haka aka yi tawaga guda, suks zo yi wa mama jaje suka gabatar da Adduoi, tare da yi wa mama alƙawarin za su cigaba da addu'a da karatun Alqur'ani har zuwa lokacin da Allah zai bayyana rumaisa.

Rumaisa kuwa a hankali ta motsa, ta fara ƙoƙarin buɗe idonta, amma ta ji goshinta yana mata zafi, a hankali ta kai hannu goshin ta ji ya kumbura, ga busashshen jini ta shafo.
Cikin ƙarfin hali ta tashi zaune, sai dai wani irin jiri ne yake ɗaukarta, saboda azabar yunwa, ga zafin dukan da aka mata da bakin bindiga.

Wani narkeken mutum ta gani, yana zagaya su, yana ƙare musu kallo.

"Ke a ina aka ɗaukko ki?" Yayi mata maganar cikin tsawa. Ba ta kai ga bashi amsa ba, ta ga mutumin da ta bawa gyaɗa a kasuwa.
Yayi saurin kawar da kansa da ga kallon ruma.

"Ke ya ina miki magana kin mini shiru?" Yayi maganar cikin muryarsa mara daɗin ji.

Gefe guda ta ja, ta tanƙwashe ƙafarta, tana jin yadda take jan numfashi da ƙyar.

A fusace ya saka hannu ya fizgo ruma, amma ta taƙarƙare iya ƙarfinta ta fizge hannunta ta ja da baya tana huci. Kallon kallo suka shiga yi, tsakanin shi da rumaisa.

Yinƙurawa yayi zai maketa, mutumin nan ya shiga tsakaninsu, ya ce "Yi haƙuri, yarinya ce"

"Ban gane yarinya ba, bani bindiga kasheta zan yi"

Ya girgiza masa kai ya ce "A'a, da alama ubanta wani ne, za a samu kuɗi a hannunsu, ka bari mu karɓa sai a kasheta".

"Ni bani da uba" tayi maganar cikin ƙwarin gwiwa.

"Ina magana kina saka baki? Zan ƙyaleshi ya kashe ki" da ƙyar ya shawo kan mutumin ya ƙyale ruma.

Ya ɗauki wata leda ya jefa mata, buredi ne a ciki sai ruwan pure water. Tamkar ta shekara ba ta ci ba, haka ta dirarwa buredin nan, tana ci tana yinƙurin amai.

Tana zaune tana cin abincinta, tana kallon yadda ake karɓar lambobin waɗanda aka ɗauko su tare, ana cinikin nawa za a biya a karɓesu kamar wasu dealer kaya.

Mutumin nan dai na ɗazu, ya zo kan ruma ya ce "Bani lambar babanki".

"Dama ana zuwa kabari da waya?"ta tambayeshi.

"Kamar yaya?"

"Na gaya maka bani da uba ya mutu ai"

"Bani lambar wani ɗan gidanku"

Rumaisa ta ce "Ka ga nifa gidanmu in dai kuɗi zaka ce musu su kawo, basu da shi,  sai dai ku yi mini abin da zaku yi mini"

Ya ƙare mata kallo ya ce "Haka ki ka ce?"

"Eh"

Ya miƙe tsaye ya ce "Biyoni".

Ayshercool.

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*


Gaba ɗaya suka bi ruma da kallo, ita kuma ta ƙare masa kallo ta ce "in biyo ka mu je ina?".

"Cewa ki ka yi sai dai ayi miki duk abin da za ayi miki, abinda yakamatan zan miki ai".

Ruma ta ce "Koma mene ka yi mini a nan ba in da zani"

Mutumin da yake ta ƙoƙarin bata kariya ya fara fusata ya ce "Wai ke wace irin yarinya ce?, duk yadda za ayi a kare mutuncinki a rabu lafiya ana yi, amma ke sai ka ce baki san ciwon kanki ba, ke kin san me zai miki ɗin ne ki ka tura baki kina cewa ayi miki koma menene?".

Cikin kuka ta ce "Ta ina kake kare mutuncin nawa, da kuka haɗamu maza da mata kuka rabo ni da 'yan uwana, yanzu ka gama cewa a kasheni, wallahi babu in da zani daga nan, koma me zaku yi mini ku yi mini ni na gaji"

Su kansu waɗanda aka kamo su tare da ruma mamaki suke yi, yadda take rashin mutuncinta yadda ta ga dama.

Ƙaton nan ya sanya ƙafarsa iya ƙarfinsa ya taka ƙafar Rumaisa, ta riƙe kanta ta yi wata irin ƙara, ba ta warke daga waccan azabar ba ga wata ana gana mata, ji ta yi kamar ya karyata, saboda azabar da ta ji, dan ƙato ne na gaske.

Mutumin da haryanzu ba ta san sunansa ba ya ce "Ina ga daga yanzu ba zan sake magana ba, su yi miki duk abin da zasu yi miki, akwai dalilan da yasa nake baki kariya, amma tun da ke na fuskanci baki da hali, duk abin da aka yi miki ke ki ka saya, idan baki nutsu ba haka zaki ta shan baƙar wahala, kina raye amma na lahira sai yafi ki jin daɗi, ki cigaba mara kunyar banza".

Fuska duk hawaye cike da dakiya ta ce "Eh ayi mini ɗin, ku kasheni daga nan sai me?, wallahi ba zan daina magana ba sai kun gaji kun kasheni, kuma ba lambar wanda zan bayar a gidanmu, ku da Allah ba zan yafe muku ba, ba laifin da na yi muku kuke cutar da ni, Allah ya saka mini duniya da lahira".

Buɗe baki yayi yana kallon rumaisa, ga fuska duk busashen jini, amma sai kwaroroto take ba tare da ta na tsoron ayi mata wani abu ba.

Aikuwa ƙaton nan ya dinga takata da ƙafarsa, yana dukanta tana ihu tana "La'ila ha illa anta, subhanaka inni kuntu mina zalimin" shine kawai abin da take maimaitawa, dan idan ya takata ji take kamar ana buga mata itace, ko wani nannauyan ƙarfe.

Ɗayan kuwa yana kallo bai kuma cewa komai ba, sai da ƙaton nan yayi mai isarsa ya ƙyale ruma, ba dan ta yi shiru da bakinta ba, sai dai ihun ma da ƙyar take iya yin sa saboda ta galabaita. Haka kowa ya zura mata ido yana kallonta, duk wurin ita ce ƙarama sauran duk da girmansu, amma tafi kowa baki da rashin mutunci.

A gigice mama ta dafe ƙirjinta, hawaye na zuba daga idonta, mutane na ta bata haƙuri, amma a zuciyarta take jin kamar wani na faruwa da rumaisa, mussaman da zuciyar ta ta ta tsananta bugawa.
Idan ka ga mama sai ka zata wani ciwon tayi, duk da ba mace ce mai ƙiba dama, amma ba ramammiya bace ba, tana da kumarinta, amma lokaci guda duk ta zube sai tsawo.
Ba ta iya cin abinci sai su Abubakar sun yi da gaske, da rarrashi da ban baki, ake samu ta ɗan sha abu mai ruwa-ruwa. Duk wata walwala da ake a gidan nan suka dainata, bacci kuwa sai dai ɓarawo, babu mai iya yin sa yadda yakamata a gidan.

'yan uwa da abokan arziki ana ta shige da fice, ana yi wa mama jaje tare da addu'a Allah ya baiyyana ruma.

Habiba ce ta faɗo gidan su rumaisa a gigice, ta din ga kallon yayyen rumaisa da mutanen da suke zazzaune, can ta hango mama, ta ƙarasa wurinta da gudu, ta zube a kan gwiwoyinta "Mama, wai da gaske an sace ruma?"

Mama ta ƙura mata ido, amma ta kasa magana.

Maƙwabciyar su ruman ce ta ce "Eh da gaske ne, yanzu ku je ku yi ta yi mata addu'a, Allah ya bayyanata cikin aminci, ya tsareta a duk in da take".

Rushewa da kuka habiba ta yi, tana wata irin sheshsheƙar kuka, gaba ɗaya ta gigice tana wani irin kuka.

A fusace mai sunan Baba ya ce. "Dalla ku fitar mana da mai ihun nan, da wane zamu ji?"

Aliyu yayi saurin cewa "A'a ba haka yakamata ayi ba, akwai shaƙuwa a tsakanin su, bai kamata a hantareta ba"

Aliyu ya fita ya je ya samu Habiba, ta haɗa hawaye da majina tana kuka, ya tuna faɗace-faɗacensu na ƙuruciya tsakaninta da rumaisa, kullum cikin sintirin kan ƙara ake, da yadda yake zaneta ita da yayanta a kan ruma, amma yau ta tayar da hankalinta saboda ɓatan ruma.

Hannunta ya kamo ya ja ta gefe yana rarrashinta, amma babu alamar za ta yi shiru, duk jijiyon kanta sun ɗaga idonta yayi jawur saboda kuka.

"Kiyi shiri kar kanki yayi ciwo, sannan addu'a zaki taya mu, Ubangiji Allah ya bayyana mana ita, ki daina kukan, mu je na raka ki gida"

"Allah ya sa kar a kasheta, Allah ya sa ta dawo gobe" ta faɗa tana sake fashewa da kuka.

Ƙwalla ce ta cika idon Aliyu, domin kuwa dauriya kawai suke yi, ya wayance ya ce "Amin ya Allah, dan idan kin yi salla ki din ga sakata a addu'a kin ji"
Habiba ta jinjina kai, tana cigaba da share hawaye. ya saka ta a gaba ya rakata gida, amma yanayin tashin hankalin da take ciki, zai tabbatar maka da ta kaɗu sosai da ɓatan ruma.

Hauwwaliya ma da take a zaune tana jinyar karayar da ta yi kafin tafiyar runa, ita ma haka ta burkice, dan da har tana mitar ruma ta tafi ba ta zo ta dubata ba balle su yi sallama, sai labarin an yi garkuwa da rumaisa suka ji.

Hatta malamansu ruma na makarantar islamiyya da take gallaba, gaba ɗaya suka shiga damuwa, makarantar kanta kamar ana zaman makoki, saboda babu wanda bai santa ba da halinta. Ita kanta tsohuwar da take sayar da kayan yara a makarantar, da suke yawan faɗa da ruma sai da ta yi kuka, dan wataran idan sun yi faɗa wata ran suna shiryawa, dan idan ruma ta zo da abinci wataran tare suke ci, duk rashin jin ta akwai shiga rai.

Takawa yana kwance a ƙaton falonsa a kan doguwar kujera, yayi zurfi sosai a cikin tunanin da yake yi, abubuwa da dama sun yi masa yawa, gaba ɗaya ya rasa wace matsalar yakamata ya fara tsayawa ya nemi mafita a kai, duk matsalar da ya tunkara, sai abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa.

Wani irin zazzafan zazzaɓi ne ya kama ruma, saboda wahalar da ta sha, ga azabar cizon sauro da kuma sanyi suka haddass mata zazzaɓin.
Babu wanda yake ta tata, balle ya taimaka mata, tuni wasu aka fara bayar da kuɗin fansarsu, idan sun ga dama su bayar da mutum, idan ba su ga dama ba su karɓi kuɗin sannan su kashe mutum su ja gawar zuwa bayan wani babban dutse da yake nesa kaɗan da in da suke ajiye mutanen su yar gawar ba tare da suturta gawar ba.

Ruma na kwance ta takure tana ta rawar sanyi, ga azabar ciwon jiki, saboda dukan da ta sha, wasu mutane suka zo a kan babur, wanda aka goyo hannunsa ɗauke da ƙatuwar jaka, ta ɗaga ido dan ta ga su waye, wa za ta gani, dattijon bafullacen nan, da ta haɗu da shi har ya rakota gida a garin su Gwaggo.

Kallonsa take, amma ya kawar da kai kamar bai taɓa ganin ruma ba, ya basu jakar, shima suka bashi wata jakar ya hau babur ɗin aka bar wurin da shi. Tunani ta shiga yi a kan abubuwan da ya gaya mata, da kuma tunanin meye alaƙarsa da wannan mutanen? Kenan duk shiri ne?" Idonta ya sauka a kan lambar dake jikin jakar, sak irin lambar jakar da aka nuna mata bullet a ciki lokacin da za su zo katsina!

Guntun tsaki ta ja, a lokacin da ihun wani mutum ya dawo da ita hayyacinta, kan ta gano dalilin da ya sanya mutumin yake ihun, sai ganin abu ta yi a jikinta kamar an watso ruwa, jinin mutumin ya ɓata su an kashe shi.

Gaban ruma ne ya tsananta faɗuwa, ta ma rasa wani halin yakamata ta shiga, tashin hankali ko kuma fargaba, ga jikinta babu daɗi, ta fara fidda rai da samun mafita.

A hankali ta tashi zaune, ta ƙarasa gaban wanda ya kashe mutumin, ta kalleshi ta ce "Dan Allah nima ka kasheni"

"Saboda me zan kasheki?"

"Na gaji da zaman wurin nan, dan Allah ku kasheni nima" tayi maganar cikin magiya.

Ya kwashe da dariya ya ce "Ai ke zaki yi mana amfani,  ko zamu kasheki sai mun koya miki hankali tukuna, dan ba zaki taɓa barin hannunmu ba, an jaddada mana mu kula da ke, bakinki ba shi da linzami, ko mun karɓi kuɗin fansarki kashe ki zamu yi".

"Idan kuma baku karɓa ba fa?" Ta tambayeshi.

Ya bata amsa da "Nan ma kasheki zamu yi"

"To ku kashe ni, dan ba wanda zai baku kuɗin fansata, bamu da kuɗi talakawa ne mu"

Dariya yayi, ya cigaba da busa sigari, ya share ruma.

***
"Daddy, ina ganin kamar yadda nace ka bar komai a hannuna, komai ya kankama, kawai mu cigaba da abin da muka saka a gaba"

Senator usman wakili ya girgiza kai ya ce "Ni fa haryanzu a raina ban gama gamsuwa da shirin nan naka ba Khalifa"

Khalifa ya gyara zama ya ce "Please Daddy, ka yarda da ni, ba zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login