Showing 198001 words to 201000 words out of 224014 words

Chapter 67 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1126

razana mini ƴa ko? Kuma ka ce baka son in haɗa auren ƴaƴana haba mai sunan baba laifin me muka yi haka ne"
Abubakar ya yi murmushi ya ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau ya gida ya ƙoƙari?"

"Alhamdilillah"
Iman ta ɗan ƙura masa ido, kamar ba wannan ne mai muryar nan ba.

Mama ta ce "Ɗan uwan mai sunan baba ne, shi gashi can a bayanki yana jinki, wannan dattijon arziki kenan malam habu"

Ammi ta ce "Au, ashe fa ƴan biyu ne ai ni duk kama suke yi mini" ta waiwaya ta kalli mai sunan baba ta ce "Mun zo neman aure gidanku ka hana, a sassauta adawar nan ba a san in da rana za ta faɗi ba, ina da tarin ƴan mata a gidana kar ka zo neman aure nima na rama".

Suka yi dariya gaba ɗaya, mai sunan baba ya ɗan sunkuyar da kai be ce komai ba.

Ammi ta ɗora da "Dan Allah ayi mana addu'a, na samu duk sun amince in sha Allah lamarin nan alkhairi zai zama, tun da Allah a ka nufa da lamarin, ba za aji kunya ba, karatun rumaisa da komai zamu kula da shi, kuma adam zai riƙeta cikin mutunci da kulawa, mu sanya a ranmu wannan haɗin Allah ne, a tayamu da Addu'a".

Mai sunan baba ya ce "Allah ya tabattar da alkhairi "

Ammi ta ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, yauwwa mai sunan baba ko kai fa, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarku, ya baku mataye nagari sanyin idaniya, ya tsare mana ku daga sharrin zamani". Ya amsa da amin.

Abubakar ya ce "Hajiya babu wata damuwa, har kullum alkhairi muke fata, kuma dama babban burinmu bai wuce rumaisa ta yi ilimi, sannan ta samu abokin rayuwa nagari ba, Allah ya sanya haɗin nan ya zama alkhairi".

"Amin ya Allah, na ji daɗi sosai na gode da karamcinku, Allah ya yi muku albarka, Allah ya yayi muku jagora".

Adam har ya fara ƙulewa, gaba ɗaya ya gaji so yake su tafi, har ya je ya kunna mota, amma ammi tana ciki tana ta faman hira.

Iman tuni ta bi bayan Adam ta shige cikin motar, sai sauke numfashi take, saboda ba ƙaramin razanata mai sunan baba yake yi ba.

Aka yi sa'a mama ta yi musu sallama ta fito, maƙwabtan su rumaisa har sun fara surutun, yawan zuwan da mota daban-daban take yi ƙofar gidan su rumaisan.

Suna tafe a hanya ammi tana faɗin "Alhamdilillah, na ji daɗi an gama da wannan babin, gobe in Allah ya yarda zan je na samu turaki, sai dai dole mu yi shiru da bakinmu, babu wanda zai ji wa za ka aura, sai Allah ya kaimu lokacin".

Adam a ransa ya ce "Sai ka ce wata matar arziki, ni dan ta ni ba wanda zai san ma an yi auren, wannan har wani aure ne"

Ammi ita kaɗai tayi ta hirarta da farincikinta, Adam yana saƙe-saƙensa, iman kuma na cigaba da jin wata irin fargaba da bugun zuciya, a haka suka ƙarasa gida, yana ajiye su ammi ya ja motar ya juya ya tafi.

Rumaisa kuwa tun da ta amsawa ammi, abun duniya ya isheta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, mai sunan baba ya je ya turketa a ɗakin mama ya ce "Ya muka yi da ke? Shi ne ki ka yadda ki ka amsa ko? Ki je ki yi ba dai aure ba gaki nan gashi. Meye a cikin auren gidan sarauta ban da tarin ƙalubale da tsaface-tsaface ke da ko ciwon kanki baki gama sani ba, amma kin tari aradu da ka, ke ko tausayin rayuwarki ba kya ji, ki je ki ƙarata".

A take jikin rumaisa ya kuma yin sanyi, wata irin dana sani ya mamayeta, tare da tashin hankali, wani irin tsoro ya shigeta dan ita kanta tun da ta amsa gabanta yake faɗuwa.

"Mai sunan baba, ka daina tsoratata, duk abun da yak cikin littafin ƙaddarar bawa bai isa ya kauce masa ba, wataƙila ba dan dalilin auren nan ba za a saceta ba, wataƙila sanadin sai an yi auren nan ne ya sanya aka yi garkuwa da ita, kar ka sake ka ce zaka zafafa, ko ka yi jayayya da ikon Allah"

Mai sunan baba yayi ajiyar zuciya, ya ji mama ne kawai, amma bai ji yana son auren nan a ransa ba.


***
Samha kuwa ta saka Jamil a gaba a kan ya ake ciki game da zancen da suka yi, na son maye gurbin aisha.

Jamil ya ce "Mun yi magana da mai girma turaki, sai dai ya ce na ɗan bashi lokaci tukuna"

"Amma har zuwa yaushe tukuna? An kusan kwana goma da zancen fa, amma babu wani feedback"

"To amma ai shi ya ce in saurare shi, bai kamata na cigaba da takura masa"

Samha ta ce "Ya salam, wallahi yaya Jamil bana son a kuma samun matsala a wannan karon"

"Babu wata matsala ai in sha Allah, dama ita Aisha Allah ya ƙaddara sai ya fara aurenta ne"

"A'a yaya Jamil, ina tsoron Allah ina tsoron ya ce zai auri wannan banzar iman ɗin, kusancinsu yayi yawa fiye da yadda ka ke zato, tsoro nake ji wallahi, tsaf ammi sai ta ce a wannan karon ya auri iman".

"Amma ai ya ce idan har zai iya auren iman to zai auri su nusaiba, kin ga ya harantawa kansa auren iman kenan".

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu tabbas yaya, komai zai iya faruwa fa"

"Ni fa na ce ki kwantar da hankalinki, in Allah ya yarda a wannan karon, zan yi duk mai yiwuwa ki auri adam"

Ta ƙaƙalo murmushi ta ce "To shikenan, Allah ya sa yaya jamil".

"Amin, bari na je gida, Hamida babu lafiya"

"To Allah ya sauwwaƙe"

Ya amsa da amin ya fita.

***
Mama tana ankare da rumaisa, har garin Allah ya waye, jikinta a sanyaye yake, gaba ɗaya ba ta da karsashi yau, abinci ma da ƙyar take ci.

Mama ta dubeta a tsanake ta ce "Rumaisa"

Ruma ta ɗago ta kalli mama.

"Meke faruwa ne? Ki ci Abincin mana"

Rumaisa duk ƙaunarta da shayi, ta ture kofin, ta ce "Na ƙoshi tafiya zan yi"

Mama ta ce "Zo nan" Rumaisa ta ƙarasa ta zauna a gaban mama.

"Maganar auren nan ki ka saka a ranki ko?" Rumaisa ta jinjina kai alamar eh.

"Ki kwantar da hankalinki, kar ki kuskura ki saka damuwa a ranki, ki yi ta Addu'a, sannan ki ja bankinki ki yi shiru, kin san abun da ƴan unguwar nan ke ya surutu a kanki, auren nan ne kawai rufin asirinmu"

Ruma ta kalleta ta ce "Me suke cewa a kaina?"

Mama ta tuna ashe fa rumaisa ba ma ta san zancen ba, mama ta ce "Babu komai, ki tashi ki tafi".

"Dan Allah mama ki gaya mini"

"Ba zan faɗa ba tashi ki tafi, karki makara"

Ganin mama ba ta da niyyar faɗa mata, ya sanya ta ɗau jakarta ta fice, ta ƙudurce a ranta sai ta san ko menene.

Tana tafe a hanya ta ji muryar habiba tana ƙwala mata kira, rumaisa ta tsaya ta waiwaya, habiba ta ƙaraso tana haki ta ce "Ruma, kwana biyu, kin ce zan rakaki kotu, amma baki kuma dawowa ba, lafiya kuwa?"

Jiki a sanyaye rumaisa ta ce "Ke rabu da ni, na fasa zuwa kotun nan"

"Amma meyasa, kin haƙura da karɓar ɗan?"

"A'a, zan karɓe shi"

"Hmm kin ji abun da ake ta cewa a kan ki ko, wallahi maƙociyarku munafuka ce"

Cikin mamaki rumaisa ta ce "Me ake cewa?"

Habiba ta ce "Au baki sani ba?"

"Ban sani ba"

"Taɓ, to da suka je asibiti dubaki, suka ga ɗa, suke cewa wai ɗanki ne, cikin shege ki ka yi, aka kai ki garinku ki ka haihu, yanzu an sallamoki kin dawo gida babu jaririn wataƙila kasheshi ku ka yi"

Galala rumaisa ta bi habiba da kallo ta ce "Cikin shege kuma? Kamar yaya, to ai ko a gurin ƴan bindiga, bana yarda su taɓani, sai dai bisa tsautsayi ya za ayi ciki ya fito mini na haihu, na yi abun kunya fa kenan, ɗan anty aisha ne fa ta mutu ta bar mini shi"

Habiba ta ce "To wallahi duk wadda aka ce ta yi cikin shege, to ƴar iska ce"

Rumaisa ta yi tsaki ta ce "Sai su yi ta yi ai, na tafi kar na makara,ke ma ki tafi makaranta"

Habiba ta ce "To shikenan, amma dai wallahi maƙwabciyar nan ta ku munafuka ce"

Rumaisa ta yi gaba, sai dai maganar Habiba ta din ga yi mata yawo a ka.

Har ta je makaranta ta dawo, ba ta cikin nutsuwar ta, mama ba ta kawo komai a ranta ba, sai rumaisa tana cikin alhini ne kawai na batun auren nan, ita kuwa rumaisa tuni zancen aure ta ajiye shi a gefe, zancen da habiba ta yi mata ya cigaba da damunta.

A islamiyyar ma kasa sakin jikinta ta yi, maganar ta cigaba da ci mata zuciya.
Har a yanzu rumaisa ba ta da takamaiman ajin da take zama, duk in da yayi mata kawai tafiya take zauna.

Yau ma a ajin su Yasir take, ta matsa ku sa da wata ɗaliba, duk ƴan ajin mata da take mutunci da su, yayata take ce musu.

Ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Yayata, duk wanda aka ce yayi cikin shege wai da gaske ɗan iska ne?"

Ɗalibar ta riƙe haɓa ta ce "Ke rumaisa, meye haɗinki da wannan maganar? Duk wanda yayi cikin shege ɗan iska ne, kuma wasan banza yake da maza, yana bari suna ta ɓa shi ko taɓa al'aurarsa.

A rikice rumaisa ta riƙe mararta ta ce "Wurin fitsari kenan?"

"Ƙwarai kuwa" ta bata amsa.

"Mama ta ce mini ba a wasa da al'aura, kuma ba a bari wani ya taɓa maka".

"Sosai haka ne, dan haka kar ki kuskura wani yayi miki wasan banza, duk wanda ki ka bari ya taɓaki, to cikin shege zaki yi, a gidanku ma korarki za ayi kowa ya tsaneki, a din ga yi miki kallon mutuniyar banza ƴar iska, Allah ya yi fushi da ke, idan wani ne yake miki ki je ki faɗa a gidanku"

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a tambayarki kawai na yi na gode".

Tun da aka yi wa rumaisa wannan bayanin hankalinta ya tashi, wato kallon ƴar iska ake yi mata, mai wasan banza da maza, da aka ce ta yi cikin shege. Ita banda ƙaddara da tsautsayi da ya sanya takawa ya taɓa ƙirjinta, ita babu wani namiji, da ko da wasa yayi mata maganar banza balle ya kai hannunsa jikinta, iyaka dai ta san tana dambe da maza, amma ba wasan banza ba.

Duk jarumtar rumaisa sai da ta yi kuka, tare da ganin an cuceta, yanzu duk in da ta wuce kallon da ake yi mata kenan.

Malami ya shigo ajin, yayi musu ƙarin alƙur'ani, ana tsaka da ƙari rumaisa ta ce "Malam dan Allah ina da tambaya" yayi shiru sannan ya ce "Ina jinki rumaisa".

"Lokacin da ka bamu addu'a, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, ita na yi ta biyawa, lokacin da aka yi garkuwa da ni, har na kuɓuta. Dan Allah ka bani addu'a da zan yi mutum ya zama kurma, da bebe"

Ya ce "Ashsha subhanallah, me yayi zafi haka rumaisa?"

"Wata mata zan yi wa, da wasu mutane" ta yi maganar har zuciyarta.

Ya ce "A'a, ki yafe musu ko ki bar su da Allah, ki yafe musun ma shi ya fi, sai ke ma Allah ya yafe miki laifukanki"

Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, sai na yi addu'a Allah ya tattaro masifa ya jibga musu"

Malam ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan ba halin mumini bane"

Rumaisa ta tashi tsam tana kuka ta ce "Ni dai wallahi ba zan yafe musu ba, dama ka ce Allah ba ya juya addu'a wanda aka zalunta, in sha Allah sai matar nan ta zama kuturwa ma wallahi, dan ba zan yafe ba"
Statement ɗin ta ƙarshe sai da ya bawa wasu dariya, Yasir yana kallonta ya shareta ta fice daga ajin tana kuka, zuciyarta na wani irin tafasa.

Ba a tashi ba ta tafi gida, dama mai gadi ya daina tareta idan ta zo fecewa muddin an kusa tashi, tun da ta taɓa yi masa rashin hankali, ta fita da gudu garin bin ta ya faɗi yayi targaɗe, a hanya ta tsaya ta sai leda viva ta naira goma, ta cikota da manyan duwatsu, ta cika jakar makarantar ta da duwatsu, ta ɗora a ka, ta nufi gida.

**"

Takawa yana gidansa, yana duba wasu takardu da ya taho da su daga wurin aiki, saura sati biyu zai je lagos wani aiki, Jamil yana gefensa suna shan tea, takawa yana duba takardun.

Jamil ya ɗan ajiye kofin, ya kalli adam ya ce "Takawa ya batun aure ne? Yaushe zaka yi wani auren?".

Adam ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Maiyasa ka ke tambaya?"

"Saboda abu ne da yakamata ka fara zancensa, ka san very soon za a fara yi maka magana a kai"

Adam ya ɗan numfasa ya ce "Ba shi ne a gabana yanzu ba, cigaba da ayyukana na binciken da nake yi su suka fi damuna".

"Amma kana ganin zaka iya cigaba a haka, duk yadda aka sakoka a gaba, gashi ka ƙi cewa komai"

"To Jamil ya zan yi, duk mutanen da suka fito suka wankeni, ba su isa ba ba a fasa yi mini sharri ba, nima idan na yi maganar ba zai canza komai ba, kowa yayi abun da ya ga dama kawai, iyaka duk wanda ya ga ba zai iya haƙura ba ya nemi hujja ya kai ƙarata shikenan"

Jamil ya ce "Lamarin ƙasar nan ai sai Addu'a, Allah ya kyauta ya bada nasara, nima akwai special assignment da zan tafi jigawa, na ji kana cikin wanda za su je Lagos ko?"

Adam ya ce "Eh, aikin ma nake dubawa yanzu"

Jamil ya ce "Allah ya sanya mu gama da aikin nan lafiya, kalli yadda muke wahala a kan ƙasar nan amma ba a gani, kalli aikin da muka yi a kan tsohon ministan harkokin waje, amma dan wulaƙanci wai kotu ta bayar da belinsa, amma daina maganar ni gaba ɗaya sai in ji aikin ma ya fita daga kaina" Jamil yayi maganar cikin damuwa.
Adam ya ce "Haba Jamil, bai kamata mu karaya ba, ko da muna yi ba a ɗaukar mataki, wataran za a ɗauka, haƙuri zamu yi mu cigaba da yi, idan ba haka ba haka ƴaƴanmu da jikoki zasu taso su ɗaora da bauta babu ranar da talaka zai yi ƴanci"

"Kana da gaskiya, amma ni fa na tsorata da batun garkuwa da aisha, anya baka tunanin shiri ne, saboda abun da muke yi?"

"To ba na ce ba, zancenka zai iya zama gaskiya, kuma zai iya zama akasin hakan, duba da yadda dama ƙasarmu babu tsaro, kuma kai tsaye garin da babu tsaron ta tafi, dan haka bana zargin kowa"

"To, Allah ya yi mana jagora, ya bayyana gaskiya a duk in da take".

Adam ya amsa masa da Amin.

Rumaisa ba ta yi burki a ko ina ba, sai a ƙofar gidan maƙwabciyarsu, tana tafe tana kuka har ta je ƙofar gidan, ta sauke kayan dutsenta, ta shirya tsaf, ta tattare hijjabinta, ta fara auna manyan duwatsu zuwa cikin gidan nan.

A rikice matar gidan ta fito, a matuƙar tsorace, jikinta ko mayafi babu, domin ganin meke faruwa.
Amma tana buɗe ƙofar gida, rumaisa ta sauke mata wata ƙatuwar marmara a bakinta, take bakin ya fashe, kan ta yi wani abu wani dutsen ya sauka a goshinta.
Rumaisa ta cigaba da aika duwatsun nan babu ƙaƙƙautawa tana kuka, tana faɗin "Munafuka, wallahi ba zan yafe miki ba, ni ba ƴar iska ba ce".

Kururwa matar ta din ga yi, tana neman agaji, mutane suka fara taruwa, aka rirriƙe rumaisa, amma ta din ga kuka tana ƙoƙarin cigaba da jifan.

Gidansu rumaisa aka je aka faɗa, Allah ya sa usman yana nan, ya je ya danƙota, tana kuka.

"Meye haka rumaisa, baki da kai ne? Dan me zaki din ga yi wa mutane jifa a gida?"

"Ba ita ta je take gayawa mutane wai na yi cikin shege ba, tana nufin ni ƴar iska ce ina wasan banza da maza" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfinta.

Usman ya ja hannun rumaisa, ba tare da ya ce wa kowa komai ba, ya ja ta zuwa gida.

Hankali a tashe mama ta ce "Rumaisa, kanki ɗaya ki ka je ki na yi wa mace jifa a cikin gida, tana ta kurma ihu wai a taimaketa zaki kasheta?"

"Cikin kuka ta ce "Wallahi da zan iya sai na kashetan, dan me za ta ce mini ƴar iska? Cikin shege fa yana nufin mai wasan banza da maza".

Mama jiki a sanyaye ta ce "Rumaisa rayuwar duniya haƙuri ake yi, sai ki zo ki gaya mini, ni na ɗau mataki"

"Wallahi idan na gaya miki ba zaki ɗau mataki ba, cewa zaki yi na yi haƙuri, kuma wallahi ban haƙura ba, sai ta ga abun da zan yi mata"
Rumaisa ta shige ɗaki tana kuka, Usman ya ce "Ai wallahi mama ban da kin hana da da kaina zan ci uban matar nan, duk yadda ki ka ɗauketa ƴa ki ke mutunta mata, amma ta yi mana wannan wulaƙancin".

Mama ta ce "Dan Allah usman a rayuwarku ku koyi haƙuri, da ƙyale mutane da halinsu, wasu lokutan da kai da rumaisan duk halinku ɗaya ai".


Ammi kuwa sake kiran mama ta yi, domin ta sake tabattar da rumaisa ta amince, dan ta fuskanci rumaisa ƴar buyagi ce, kar sai ta je ta kaiwa turaki maganar rumaisa ta mayar da hannun agogo baya.

Ta kira wayar mama, mama ta ɗaga suka gaisa.

Ammi ta ce "Ina maman sabir ne, a bani ita mu yi magana"

Mama ta miƙawa rumaisa waya, ta ci kuka ta ƙoshi.

Muryarta a dashe ta amsa sallamar ammi.

Ammi ta ce "Rumaisa lafiya kuwa, na ji muryarki a dashe?".

"Ba maƙwabciyarmu ce ta ke cewa mutane na yi cikin shege ba, ƴan unguwarmu suna yi mini kallon ƴar iska mai wasan banza da maza"

Ammi ta ce "Subhanallah, ki kwantar da hankalinki, kin ga yana daga dalilin da ya sanya nake son ayi auren nan, ki yi haƙuri ki manta da su, yau zan je gidan turaki mu yi magana, dama kiranki na yi na sake tabattarwa idan kin amince, nan da watanni uku kacal za ayi in sha Allah".





Ayshercool.

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login