Showing 39001 words to 42000 words out of 224014 words

Chapter 14 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1072

ga ta da shegen ƙarfi, da ƙyar Aliyu ya riƙeta aka ɗebi jinin nan.
Kuka har da majina, Aliyu ya dinga dungure mata kai yana zaginta.

Ya gama gwaje-gwajen da zai yi mata, ya ce "Malaria ce ke damunta, dan haka akwai buƙatar ayi mata allurai, da kuma magunguna"

Ruma ta yi masa zuru da ido, tana jiran ta ga a ina za ayi allaurar.

Ya haɗa alluransa ya nufo ta, ta miƙe tsaye.

"Ke malama ki tsaya, dan ba zaki sake wahalar da ni ba"

"To a ina za ayi mini allurar?"

Mai chemist ya ce "Ai a baya ake yin ta"

"Wai bayana" tayi maganar tana nuna bayanta.

Nasiru mai chemist ta ce "A'a a mazaunai"

"Suwaye mazaunan?"

Aliyu ya haɗe rai ya ce "Ke juya ki tsaya ayi miki allurar nan mu tafi, kin san sarai a in da za ayi".

Ta riƙe skirt ɗin ta gam ta ce "Ni wallahi ba zai ganni ba"

Aliyu ya fizgota, ya riƙeta da ƙyar suka danneta suka yi mata, Aikuwa ta din ga zunduma ihu, kamar sun mata wani abu.

Haka aka gama yi mata treatment, suka taho gida, ban da uban kuka babu abin da take yi.
"To subhanallah, ko me aka yi mata kuma take wannan uban kukan haka oho" mama ta yi maganar tana fitowa tsakar gida.

Aikuwa suna shigowa, ta nufi mama tana kuka.

"Meye haka, kukan me ki ke haka,ki ke ɓare baki?"

"Mama yaya Aliyu ne da Nasiru mai chemist"

"Suka yi miki me?"

"Bayan ya ɗibar mini jini, kuma suka buɗe mini tsiraici na aka yi mini allura"

Mama ta ce "Subhanallah"

"Mama ba ke ki ka ce ɗuwawu tsiraici bane ba, amma har da Yaya Aliyu ya riƙe ni, Nasiru mai chemist ya ganni, wallahi ban yafe ba"

Mama ta girgiza kai, ta ƙiftawa Aliyu ido sannan ta ce "Haba Haidara, ya zaka yi mini haka, dan me za'a buɗe mata jiki ayi mata allura?"

Aliyu ya ce "To mama ai larura ce, ko a addinance ba haramun bane".

Cikin masifa ta ce "To shi yayana ne da zai ganni? Har da taɓani ya yi mini allura a wurin"

Aliyu ya ce "Sa'anki ne ni, uban me za a kalla a jikin naki?"

"Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, Allah ya jijjigo bala'in duniya da lahira ya ɗora masa, tun da ya ganan mini tsiraici na"

Mama ta ce"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin Addu'a ce haka, kar in kuma ji, baki san larura ba?"

Aliyu ya ce "Sakarya, kamar ba tsairaicin ki ka je kina kaɗawa a gaban mutane ba jiya"

Umar ya shigo ɗakin mama, suna magana, bai kula ruma ba amma dan ya duba jikinta ya shigo.

Tana kwance ga zafin ciwo, ga na takaicin allurar da aka yi mata, zafin allaurar bai dameta kamar ganinta da mai chemist ya yi.

Sai da yamma mama ta sakata ta yi wanka, ta canza kaya ta ɗan ji ƙwarin jikinta.
Sai da ta kwana uku tana fama, sannan ta ware gaba ɗaya, sai dai rashin lafiyar da tayi ya sanya aka mance da laifin da ta tafka, kowa sai lallaɓata yake, ban da Huzaifa.

Ta ware sarai har ta koma makaranta, kullum mama cikin nasiha take yi mata, tare da yi mata addu'a da fatan shiriya.
Tun daga ranar ruma ta daina bi ta hanyar chemist ɗin Nasiru, idan kuwa ta ganshi ko kallonsa ba ta yi, balle ta gaishe shi, a cewarta ɗan iska ne tsairaicin ta ya kalla.

"Mama wai yaushe zaki haihu ne, babannin 'yan ajinmu sai haihuwa suke yi, amma ke ban taɓa ganin kin haihu ba"

Mama ta ce "Ikon Allah, ba gaki na haife ki ba, ai ke ce auta ha zan kuma haihuwa ba, sai dai in kin girma kin haifa na ɗauka"

"To ni yaushe zan haihun?"

"Sai kin girma kin yi aure"

Ruma ta ɗan yi jimm sannan ta ce "To ni so nake na haihu, ina son ƙani ko ƙanwa da zan din ga wasa da su"

"Ruma ki ka haihu yanzu ai a nemi tsari, sai an yi aure ake haihuwa"

"To gaskiya mama ni so nake na haihu yanzu"

Usman da yake jin hirar ta su ya ce "Ke, idan ki ka haihu ba aure tsanarki za ayi, a kore ki daga gidan nan da unguwar ma gaba ɗaya, shi ya sa ba a wasa da maza, ki ka bari namiji ya taɓa ki to ciki zaki ki haihu, kuma korar ki za mu yi"

Waro ido ruma tayi ta ce "Amma ku kuke taɓani?"

"Ai mu yayyenki ne, muharramanki ne mu"

Ruma ta dafe ƙirji ta ce "Allah ya rufa mini asiri, ai da ban sani ba, taɓ idan aka koreni ina zani?"

"Oho miki dai, wannan damben da ki ke da maza ma, idan ba ki daina ba, sai dai ki ga kin haihu, kuma sai kin bar mana gida"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "In sha Allah hakan ma ba zata faru ba, ai ni ban san hakan abin yake ba, Allah ya sa na yi tsawo na auri kyakykyawa mai kuɗi".

Mama ta ce "Ke zan ci ubanki ke da kyakykyawa mai kuɗin nan, miji na gari ake roƙon Allah, fitsararriya"

"Ni dai gaskiya bana son mummuna, mai kyau nake so"

"Ke dalla ware, da wannan munin za ki auri kyakykyawa?"

"Ni dai yaya Ussy, ka yi mini Addu'a, ka san wa zan aura a cikin 'yan ball".

Miƙewa ya yi ya ce "Ba ni da lokacin jij wannan shirmen na ki".

Tun daga wannan lokacin, ruma take kaffa-kaffa, da gudun kar wani namiji ya taɓa ta, saboda kar ta haihu a koreta ta shiga uku, kuma ta san idan aka koreta ba kuɗin mota za a bata ba, balle ta tafi ko ƙauye ne wurin Gwaggo.

Yau gaba ɗaya mama ta kasa gane kan ruma, tun da ta dawo daga makaranta yanayinta ya nuna kamar tana cikin damuwa.
Ba irin tambayar da mama ba ta yi mata ba, amma ta ƙi gayawa maman dalilin damuwarta ta, ta ce cikinta ne yake yi mata ciwo kawai

Mama ta aiki ruma sayen maganin sauro, ta je ta sayo, ta dawo ta tsaya a soro tana kuka.
Huzaifa ne ya sameta a soron tana kuka, dan sai da ya ɗan tsorota.
"Ke me ki ke yi a nan?"

Cikin kuka ta kira sunansa "Huzaifa"

"Na'am" ya amsa.

"Ka san wani abu?"

"A'a sai kin faɗa"

"Yaya Usyy ne ya ce mini idan namiji ya taɓani, zan yi ciki in haihu, kuma korata za ayi daga gidan nan, sai malam ya aikeni karɓo masa chalk, da na kawo masa hannunsa ya taɓa nawa. Na tambayi 'yan babban aji na gaya musu abin da yaya ussy ya gaya mini, suka ce eh haka ne wai ciki ne da ni, ka ga cikina ma ya fara kumbura yanzu ya zan yi bana son a koreni dan Allah ya zan yi" ta yi maganar har cikin zuciyarta tana rushewa da kuka.

Huzaifa a ransa ya ce 'Alhamdilillah, na samo maganinki'

"Tabbas Deluwa kin kwaso mana abin kunya, yanzu abin da zai faru shi ne, ki haɗa kayanki a ɓoye, cikin dare na kai ki tasha ki bar gidan nan, dan idan mai sunan Baba ya sani sai ya jefa ki a rijiya"

Sake rushewa ta yi da kuka har da majina, ya yi saurin cewa "Sai mama ta jiyo kina kuka asirinki ya tonu ko?"

Ta goge hawanyeta ta ce "To ya zan yi?"

"Shikenan, zan rufa miki asiri, amma zaki din ga yi mini wankin uniform".

"Eh na yadda, amma dan Allah kar ka faɗawa mama, bana son a koreni dan Allah"

Huzaifa ya yi wani murmushi cikin mugunta ya ce "To na ji, goge hawayen ba zan tona miki asiri ba"

Abu kamar wasa, ruma ko abinci ba ta iya ci, gashi kullum sai ta wanke wa Huzaifa kayan uniform.

Mama ta gaji ta ritsa ruma, har da bulala sannan ta zauna ta yiwa mama bayanin abin da yake damunta.
Mama ta yi salati ta sanar da Ubangiji, gaba ɗaya ruma ba ta da wayo, ga shegiyar tambaya idan kuma ka yi mata bayani yadda za ta fahimta, nan ma ta yi wata kwaɓar.

Sai da mama ta yi da gaske, sannan Ruma ta yadda ba ta da ciki, dan har da nunawa mama cikinta wai ya kumbura ɗa ne a ciki.

******

Ta na zaune a kan sallaya ta idar da salla, sai dai ta lula duniyar tunani, ba lazamin take yi ba.

Kamar daga sama ta ji ana kiran sunanta, ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.

"Ohh Nusaiba, an gama girkin daren ne?"

Nusaiba cikin damuwa ta dubi Ammi sannan ta ce, "Ammi, tunanin me ki ke yi haka ne? kin san fa ba ki da cikakkiyar lafiya"

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Nusaiba tunanin nan na dole ne, shi yake yin kansa, abubuwa sun yi mini yawa, bana son na nuna gazawata amma ni na san na gaza na kasa shawo kan komai, al'amura na ta ƙara dagule mini"

"Me kuma ya faru ne?"

"Mahmud, lamarinsa yana damuna, ga kuma yadda aka addabawa yarinyar nan a cikin gidan nan, haƙurina ya fara ƙarewa, duk wanda ya taɓa Iman ni ya taɓa raina ya na ɓaci fiye da tunaninki"

Nusaiba ta gyara zamanta ta ce "Ammi, kin san wannan duk shirin Mummy ne, so take ki magantu ku raba abin faɗa a cikin garin nan, ita take buga miki wannan wasan, ki ƙyaketa kuma ki yi haƙuri ki ɗauke kan ki daga Mahmud, ba ga takawa nan ba, mu da shi mun isheki rayuwa su je su ƙarata mana"

Ammi ta girgiza kai ta ce "Nusaiba kenan, ba zaki gane ba, tashi maza ki je ki tabattar an gama komai, sannan ki kira mini Iman, ba na son zamanta ita kaɗai"

Nusaiba ta ce "To shikenan Ammi, bari na je".

Sannu a hankali yake tafiya, tamkar ya na tausayawa ƙasar da yake takawa, har wani rangaji yake kamar wanda ake yiwa kiɗa.
Fuskar nan a murtuke babu annuri, in da ya sa a gaba kawai yake kallo, yake burin cinmma. Babu tsammani suka yi kiciɓis a baranda, ba tare da ɗaya ya san ɗaya ya taho ba, kuma aka rasa wanda zai bawa wani hanya ya wuce.
Kallon-kallo suka yi na wani ɗan lokaci, sannan ya lumshe idonsa a hankali ya buɗe. "Banihanya"
Kallonsa ya yi irin kallon ba ka isa ba ya ce "Ni da kai waye ya tarewa wani hanya?"
Cikin tsawa da zafin zuciya ya ce "Ka bani hanya na ce"
Murmushin gefen baki yayi, tare da rausayar da kai, yayi taku biyu ya koma gefe ya bashi hanya.
Sai da ya ƙare masa kallo, kamar ba zai wuce ba, sannan ya cigaba da takawa sannu a hankali ya wuce.
Ya waiwaya ya bi bayansa da kallo, yayi wani murmushi sannan ya ce "Zamu ga wanda ya fi iya buga wasan sa"
(A mini afuwa ban editing ba)
AYSHERCOOL
08081012143
[19/07, 8:42 am] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.




P13

Kwanci tashi asarar mai rai, ruma ta kammala primary school za ta shiga sakandare, sai murna take yi, sai dai babu abin da ya sauya a halayenta na rashin ji, ta hanasu sakat,a gidan, da an jima sai ta buga tsalle ta ce "Wooo ni zan shiga sakanni in dire"

Yasir ya ce "Ji banza, me aka yi da maza meye wata sakandare, ai yanzu aka fara"

"A'a bar ni na yi tsalle, na samu cigaba a rayuwa ta, Sakandire fa, zan shiga jss1 ai girma ya zo, yanzu ni ma zan yi tsayi tun da zan shiga Sakandire"

Usman ne ya miƙo mata kuɗi ya ce "Yi sauri ki je wurin mai shayi, ki karɓo mini madara zan karya"

Ɗan ɓata fuska ta yi ta ce "Mama fa ta hana ni zuwa wurin mai shayi, da mai kifi da mai nama"

"Za ki wuce ki je ko sai na zo kan ki?"

Ba dan ta na son aiken ba, ta karɓa ta saka hijjabi ta fita, tama tafe tana shan farar ƙasa, bakinta yayi fari tas, kai ka ce akuya ce ta dumbuji dusa.
Ko da ta isa rumfar, dandzon matasa ne a ciki, sun cika kuma galibi abokan yayyenta ne, ba wanda ta kula a cikinsu ta miƙa kuɗi a bata madara.

"Rumaisa, ina Dambele?" Cewar wani matashi da yake ƙoƙarin kai lomar indomie.
Ta kalleshi ta ce "waye kuma dambele?"

"Ussy mana, na gidanku"

"Sai ka ce mini wani dambele kuma, kamar sunan rago, yana gida ya aka yi?"

"A'a ba komai, kawai na tambayeki ne, kin san Usman dambele wani ɗan ball ne, shi ma haka ake ce masa a filin ball".

"Ni zaka gayawa dambele ɗan ball me, ai sai dai na baka labari"

Kan kace me, aka ɓarke da hirar ball a teburin mai shayi tare da ruma, yadda take bayanin ball ya isa ka gane ƙanwar maza ce, gaba ɗaya ta manta da aike da aka yi mata, ta tsaya ana sharhi da ita.

A ƙalla ta kai mintuna arba'in a wurin, ta manta da aiken gaba ɗaya, ga wurin shayin a ƙofar gidan su yaje, ya ci ace ta je ta dawo, amma babu ruma babu dalilinta.

Ba shiri Usman ya sanya riga, ya fito nemanta, 'yar muryarta kawai yake jiyowa, tana bayani, har da dukan teburin mai shayi tana mayar da yadda aka yi.

"Ke! Meye haka?" Firgigit ta waiwaya, ta ga Usman a tsaye a bayanta.

"Aiken da na yi miki kenan?"

Kame-kame ta tsaya yi, dan har ga Allah ta manta da wani aike, musun ball na ɗibarta a rumfar mai shayi.

"Dambele yanzu nake tambayar ruma kai, ashe kana gidan ma, yarinyar nan ta burgeni, ta san ta kan ball abin mamaki, gaskiya na yarda ƙanwar maza ce"

A ƙule ya ce "Kai dilla ware, wannan ai hauka ne, kawai kun saka yarinya a gaba, kuna wani surutu, meye alaƙarku da ita?"

"Haba Usman, Ruma ai ƙanwarmu ce"

"Ba wani ƙanwarku, baku haɗa alaƙar komai da ita ba, ke kuma wuce kan na saka ƙafata, na kifa ki a wurin" sumi-sumi ta bar rumfar mai shayin ta nufi gida.

Ya bita gidan, ya dinga yi mata masifa, kamar zai cinye ta ɗanya.

*****

"Hutawarki lafiya uwar ɗakina ta kai na, jirgin sama maƙurar tafiya komai nisan ta"

Gyara zama ta yi ta dubeta ta ce "Bani labari, me ake ciki ne?"

"A'a, labarin bai gama nuna ba, amma ki bari ya ƙarasa tukuna, amma fa gida ya ƙara hargitsewa, ina ta gwara kawuna ta ko ina, na hanata sukuni, kusan tun bayan da Mahmud ya sa ƙafa yayi fatali da ƙudurinta"

"Hajiya Jamila, idan har muka tafi a kan tsarin da muka yi da farko, to tabbas zamu cimma buri, sarautar ta bar gidanku har abada"

Hajiya Jamila ta yi murmushi ta ce "Ai hakan na fi so, gara ai ayi biyu babu, sai na yi mata kassarawar da zata bar gidan nan da ƙafafuwanta, tun da dai na fuskanci asiri ba ya cin ta, gara ayi mutuwar kasko"

Dariya suka yi a tare, suna tafawa cike da duniyanci, tare da cigaba da tattaunawa a kan cikar muradansu.

****
Tamkar mai shirin zarewa, haka yake kai gwauro, ya kai mari a cikin katafaren falon, da ya sha ado da kayan alatu kamar ba za a bar duniyar ba.

Gefe guda wani babban mutum ne, zaune a ɗaya daga cikin jerin kujerun da suke falon, hannunsa riƙe da wani kwagiri, fuskarsa ɗauke damuwa.

Matashin ya daki teburi ya ce "Daddy meye abin yi ne? Ka na zaune ba ka ce komai ba?"

Dattijon ya numfasa sannan ya ce "Ka bini a hankali, ina tunanin wani abu ne"

"Daddy ba mu da isasshen lokaci fa, you know am following your footsteps, idan aka ɓata siyasarka, zai shafeni, mutum mai girma da daraja, kamar kai wannan ɗan ƙaramin alhakin zai kawowa barazana, gaba ɗaya gidajen jaridu, da dandalin sada zumunta, an buga labarin nan, kamar kai ka cancanci haka a ƙasar nan"
Murmushi mutumin ya yi ya ce "Easy Khalifa, ai ja da baya ga zaki ba tsoro bane ba, shirin yaƙi ne, haka zalika yaro bai san wuta ba sai ya taka, ka ƙyale shi, a yanzu ba ta tasa ma nake yi ba, na zuba ido ne in ga wani mataki za a ɗauka a kansa. Saboda idan ya matsa sai ya fasa ƙwai, to ba ni kaɗai za ta shafa ba, zata shafi manyan ƙasar nan da dama, yaron tone-tonensa ya yiwa, amma yana daf da tona wuƙar da za ta yi ajalinsa"

"Ohh my God, Daddy sai wasu irin maganganu ka ke yi, amma haryanzu ba ka gaya mini menene mafita ba"

Alama ya yiwa Khalifa da ya je, Khalifa ya ƙarasa gabansa ya durƙusa. Ya tallafo kan Khalifa ya yi masa raɗa a kunne.
A take damuwar kan fuskarsa ta gushe, murmushi ya mamaye fuskar ta sa ya yiwa mahaifin na sa alamar jinjina da hannunsa.

****
Sati biyu kenan da fara zuwan ruma makarantar sakandare, kullum sai ta yi gugar kaya, wai kar ta je da ƙazanta kamar ba 'yar sakandare ba, amma idan ta tashi dawowa tamkar ta yi dambe da kura, kayan nan duƙun-duƙun haka take dawowa da su.
Haka kawai yau zuciyarta ta raya mata, ta bi ta hanyar gidan mai unguwa, kasancewar a hanyar makarantar da take gidan yake.

A layin gidan mai unguwar, ta ga manyan motoci a fake, da alama wani abun ake yi. Hankalinta na kan lambun da ta taɓa zuwa ta ɗebo mangwaro mai gadi ya ce mata ɓarauniya, dan haka ba ta tsaya jin me ake a layin gidan mai unguwar ba.

Sai dai ko da ta ƙarasa layin lambun, wasu manyan motoci ta tarar guda uku a ƙofar lambun.
Lelleƙawa ta shiga yi, ta na haɗiyar yawu, saboda yadda take iya hango cincirindon bishiyoyin mangwaro da yadda  suka yi 'ya'ya, ban da sauran 'ya'yan itatuwa.

"Ke uban me ki ke yi a nan wurin?"

Da sauri ta waiwaya, ta ga waye yake yi mata tsawa haka.
Ɗan gidan mai unguwa ne dai, da ya taɓa kamata.

"Taɓ dama kana nan?"

"Eh ina nan, yau ma satar ki ka zo yi?"

Ta tsuke ɗan bakinta ta ce "Ba yayana ya ce kar ka sake ce mini ɓarauniya ba?"

"Oho miki dai, ai ɗiba ki ka yi ba a baki ba"

"Eh amma ai dai ya biya"

Cikin hanzari ya ce "Wai me ma ki ke yi a nan wurin ne?"

Ruma ta ɗan riƙe haɓa ta ce "Hmmm, ashe haryanzu ka na nan, ba ka cigaba ba, ni gashi har na gama primary na shiga sakandare"

"Ke dalla ware, tun kan a haife ki na yi sakandare na gama, fitsararriya wai wani ban cigaba ba, ɓace ki bar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login