Showing 123001 words to 126000 words out of 224014 words
haƙuri dan Allah, na gaji ne ban san a halin da mama da yayyena suke ciki ba, na gaji da zaman wurin nan, dan Allah a tunaninka abin da ku ke yi ɗin nan kun yi mana adalci, kalli fa jaririn nan, ya rasa mamanshi an haife shi a tsakiyar daji, ko kaya babu a jikinsa fa, ga yunwa yana ji, kalli wurin kwananmu, yau a kashe wannan, gobe a wulaƙanta wancan ya kuke so mu yi? Galibinmu fa duk talakawa ne, ba 'yan masu kuɗi ba".
"Kin san meyasa nake ta baki kariya kar a kashe ki?" Ta girgiza masa kai.
Ya ce "Gyaɗar da ki ka bani a kasuwa, ki ka ce idan ina da 'ya'ya in kai musu, na gaza samun tsaro a ƙasata, a kan idona na rasa iyayena, da 'ya'yana biyu da yunwa ce ta kashe ɗaya, saboda hare-haren 'yan ta'adda bana iya fita samo musu abun da zasu ci, aka sace ɗan uwana, sai da na sayar da komai nawa domin karɓo shi, aka kashe shi, shiyasa da aka yi mini tayin wannan harkar ban ji ko ɗar ba na karɓa na shiga, idan ya so duk ayi mutuwar kasko, kuma na samu ƙwarin gwiwa ne, tun bayan da na san iyayen gidanmu su ne tsaro a ƙasar nan..... Sule ne ya kaste barde ta hanyar cewa "Kai fa nake jira mu yi magana, ya za ayi ka karɓo mana jaririn nan mu kashe shi, mun riga mun yi wa mutanen smoke wannan alƙawarin, yarinyar nan ta ƙeƙashe ƙasa ta hana yaron nan, ina tsoron muyi mata illa, mu saɓa waccan yarjejeniya da ke tsakaninmu da ku".
Barde ya kalli rumaisa, sannan ya kalli sule ya ce "Kar ka damu, gobe zamu kawo muku mutanenku, ku bamu ita, mai gida da kansa zai zo wurin nan"
Sule ya yi murmushi ya ce "To madalla, ai hakanma yayi"
Suka cigaba da tattaunawa, ruma kuwa ta samu wata ledar pure water, ta zuba kokon nan a ciki, ta zazzaga madara, ta dinga bawa jaririn nan.
Haka nan yaron nan ya din ga shan kokon da ruma ke ɗura masa, ba ta san ya ƙoshi ba, sai da ya din ga kwarara amai ta hanci ta baki.
"Rumaisa ya zaki bawa jaririn kwana biyu koko, ai sai ki ja masa wani abun" cewar wata dattijuwar mata.
"To baba ko in baki shi ki shayar da shi ne? Idan ban bashi koko ba mai zan bashi, da ma aka samu kokon, tausayinsa nake ji, da mamansa na nan, da ya samu sauƙin wani abun, ka yi haƙuri ka ji yarona, Allah ya kula mini da kai, ya jiƙan anty aisha" tayi maganar tana zubar da hawaye tana goge masa aman da yayi da zanin da yake ciki.
Bayan tafiyar barde, sule ya cewa ruma "Sai ki gode Allah, gobe zasu bamu mutanenmu dan su karɓeki, mu kuma a goben zamu kashe ki, ba zamu basu ke ba".
Duk da tsiwar da ruma take yi musu, a kan su kasheta, sai da gabanta ya faɗi jin ya ce gobe zasu kashe ta, to yaya jaririn nan zai kasance kenan? A zahiri kuwa ko gezau ba ta yi ba, sai cigaba da gogewa jaririnta amai da ta cigaba da yi.
Azabar galabaita ta sanya yaron ko kukan kirki ya daina yi, sai dai yai kaɗan yayi shiru, ga wani irin numfashi da yake yi, iya ƙirjinsa kai da gani ka san ba shi da cikakkiyar lafiya.
Yau tun da garin Allah ya waye, bayan rumaisa ta yi sallar asuba, ta zubawa wurin da suke zama ita da aisha ido,, sai wasi-wasi take yi, tayaya jaririn nan zai rayu? Ance kasheta za ayi, waye zai kula da ɗan ta san dai ƙarshenta shi ma kashe shi za su yi, ga wata irin soyayyar yaron da ke ratsa zuciyar rumaisa.
Tana zaune a gefe, tana saƙawa taan warwarewa, ta ji tamkar ta tashi ta gudu, amma ta san da ta gudu zasu harbeta, sun ce yau za su kasheta, amma ta ga cikinsu babu wanda ya saurareta. Sha tara ne ma ya dubeta yana dariya ya ce "Duk shirin tafiyar ne na ga kin nutsu, sai ki bi masoyiyyar taki, ƙarshen ƙauna har ɗan naku ms zamu haɗa mu turo muku ku ci soyayya" tsaki tayi ta kawar da kanta gefe. Ya din ga ƙyaƙyata mata dariya.
Sai dai wunin ranar ya shuɗe barde bai dawo ba, balle ta san matsayarta, peak ɗin nan ta dinga zubawa a pure water tana ɗurawa jariri, sai dai duk girman nan nasa ya sace, fatarsa ta fara yamushewa, idanun jaririn suka yi yellow, ga zafi da jikinsa yake ɗauka, ga fatar jikinsa duk ta yi alamar ƙarancin jini da oxygen, idan jikin nan nasa yayi zafi, sai dai ta saka shi a gaba, tayi ta uban kuka, ba ta taɓa tsammanin cin karo da ƙalubale mai girgiza zuciya irin wannan ba.
A kwana na huɗu, tun safe sule yake masifa, ya ce idan har barde bai zo ba, sai ya kashe rumaisa, saboda ya riga ya sanar da mutanen smoke cewar ya kashe rumaisa da jaririn nan, babu babban abun da ya sake girgiza rumaisa, irin yadda suke commanding ɗin 'yan uwan aisha su kawo musu kuɗi, kuma da alama masu hali ne, dan miliyan ashirin suka caza, kuma sun haɗata, suna ta yi musu kwatancen in da zasu kai kuɗin, gobe da yamma.
Rana ta karya ta kusa faɗuwa, rumaisa ta jiyo ƙarar babura da yawa, tare da harbe-harbe.
Duk da ba yau ta fara jin ƙarar bindiga ba, amma ta ɗan razana, take 'yan bindiga suka zagaye su ruma, suka saita bindigoginsu, da shirin ko ta kwana suna saka ran idan jami'an tsaro ne, su kashe kowa a wurin.
A ƙalla sun kai babura goma duk sanye da kayan sojoji, sai dai fuskokinsu duk a rufe, sai manyan makamai da suke riƙe da su.
Suka yi parking baburan, suka sassako, sai a lokacin su sule suka nutsu, suka sauke makaman, kasancewar sun gane ko suwaye.
Barde ne ya fara buɗe fuskarsa ya ce "To yaya, kun shirya ayi musayar ko kuwa? Kun tattauna da iyayen gidan naku?"
Sule ya ce "Ai ba yau muka yi da ku ba, tun bayan kwanaki uku baya muka yi, amma ka saɓa alƙawari".
Ɗaya daga cikin mutanen ne, ya tako a hankali zuwa gaban sule ya tsaya nesa kaɗan da shi ya ce "Rumaisa zaka bani kawai, maganar mutanenku, ma yi daga baya".
Sule ya dube shi a fusace ya ce "Amma ka raina mini hankali, ba zan bayar da ita ba, kuma a yanzun nan zan kashe ta, yarjejeniyar ta watse, a cigaba da faɗan tsakaninmu, ko mu....
"Shhhhhh, ka san da wa ka ke magana kuwa?" Mutumin ya katse sule.
"Ban damu ba ko kai waye, yau zan kasheta kowa ya huta, na gaji da yi muku biyayya ina saɓawa iyayen gidana". Ita rumaisa mamaki ne ya kamata, duk a kanta ake wannan taƙaddamar, shi kuma wannan mutumin ko a ina ya san sunanta oho.
Sule ya nufi ruma gadan-gadan, sai dai kan ya ƙaraso gawarsa ta faɗi a gaban rumaisa, tare da watsuwar jininsa a wurin mutumin nan ya harbe shi. Ware ido ruma ta yi jiki na rawa take kallon gawar. Kan kace kwabo, sun fara harbe-harbe a tsakanin su, sai dai mutanen sule na ta ƙoƙarin su harbe rumaisa kawai.
Sauran mutanen da suke tare da rumaisa, sai ihu suke yi, mutanen da suka zo a babur, suna kama su, suna ta ɗaurewa.
Mutumin da ya harbe Sule ya kalli ruma ya ce "Ɗauki yaron ki tashi ki tafi".
"In tafi ina?".
"Koma ina ne, ki tashi ki bar wurin nan kawai, saboda ke na zo" ya ƙarasa maganar yana sauke takunkumin fuskarsa, wa zata gani, mutumin nan da ya bata kaza a hanyar zuwansu katsina.
Kan tayi magana ta ga ya saka bindiga ya harbe Barde, ya furta 'Kai ma amfaninka ya ƙare"
Sake gigicewa ta yi ta ce "Na shiga uku, meyasa zaka kashe barde, ya taimakeni sosai, meyasa zaka yi haka, ta nufi gawar barde tana kuka.
Fincikota mutumin yayi ya ce "Rumaisa, ki tafi na ce, mu a irin wannan aikin namu, babu tausayi ko sanayya, barde yana da alaƙa da iyayen gidan su sule, yarona ne, shi ya yi mini kwatancenki na ganeki, na shirya yadda zan kuɓutar da ke, da ya karɓeki kin zama mallakinss, ko kina so ki rayu da ɗan ta'adda babu aure?" Cikin tsuma ta girgiza masa kai.
"Dan haka maza ki bar wurin nan, na san yanzu za a kawo musu ɗauki, Allah ya tsare" tsyawa ta ɗan yi tana kallon gawar barde, da ke yashe a wurin da aisha ta mutu.
"Ki tafi ko in kasheki da hannuna!"
A hankali ta juya, ta ɗau hanya, hannunta rungume da jariri, ɗanyen goyo.
AYSHERCOOL
*₦paid book ne, 500 via 0009450228 aisha adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Da farko ta na yi tana waiwayowa, daga baya ta ƙule ta nausa cikin daji, kawai tafiya take yi, ba ta san ma in da take sanya ƙafarta ba, sai dai maimakon ta ganta a hanya sosai, sai gani ta yi tana kuma nausawa cikin surƙuƙin daji, daji ne na gaske da ya amsa sunansa daji, babban fatan ruma Allah ya sa ta gane hanyar da aka shigo da su, abun da ta manta shine, tafiyar da suka yi a kan babur ta awanni ce, a cikin duhun dare, kuma in da ta nufa ma ba ta nan hanyar aka shigo da su ba.tafiya kawai take yi, ga rana na ta tafiya gangara zata faɗi, gashi babu alamun ruma ta kusa hanya.
Duk addu'a da ta zo bakinta yin ta kawai take, ganin abun take tamkar mafarki, ta rasa ta ina ma yakamata ta bi, gashi yau jaririnta ko kukan kirki ba ya yi, amma ta ta'alaƙa hakan da yunwa yake ji, fatanta ta isa gari ta samu abun da za ta bashi ya ci kar ya mutu.
Lokaci guda mutuwar aisha da ta barde ta faɗo mata, aikuwa ta fashe da kuka, tana kuka tana faɗin "Anty Aisha ina ma tare muke tafiyar nan, ko ina suka kai gawarki oho, Allah ya yi miki rahama, kai kuma Barde ban sani ba ko Allah zai yafe maka, amma Allah ya baka ladan tausaya mini da ciyar da ni da ka din ga yi, ni dai na yafe maka duniya da lahira.
Ruma ba ta san jikinta babu ƙwari ba, sai da ta fara tafiyar nan, sannan ta gane ashe a galabaice take, jikinta babu ƙwari da ƙarfi kamar yadda take jin ta a da, gaba ɗaya ta gaji, ƙishirwa take ji, ga duhun magariba ya fara yi, kuma babu alamar samun hanya, ƙafafuwanta tuni suka yi tsami, gashi sai taka abubuwa take yi, kama daga ƙaya zuwa ƙananan duwatsu, amma zuciyarta ta cigaba da bata ƙwarin gwiwar ta tafi, tana jin zata iya fita hanya a kowane lokaci.
***
Takawa ne yake ta safa da marwa a ɗakinsa, yana daddana wayar hannunsa, kallo ɗaya zaka yi masa ka san ya rame, duk yayi wani iri kamar mara lafiya.
Can ya kara wayar a kunnensa, cikin zaƙuwa ya ce "Ya ake ciki, me ka gano? Akwai wani labari ne?".
"Easy mana Adam, wacce zan amsa maka cikin tambayoyin naka tukuna? Ka yi haƙuri wannan bayanin duk ba na waya bane ba, kana da time ka shigo abuja gobe in Allah ya kaimu?".
Adam ya ce "Ni bani da wani time, am so much busy here, abubuwa sun yi mini yawa, koma menene kawai ka gaya mini ta waya, ina jin ka".
"A'a ni babu abun za zan gaya maka ta waya, ka bari ni zan shigo kanon in sha Allah"
Adam ya yakice gumin da yake tsatstsafo masa, ya ce "Bashir, bani da wani isasshen lokaci da zan baka, kawai ka yi abun da na ce, koma menene ka gaya mini, kar aikin da nake yi ya koma baya".
"Na fuskanci a rikice ka ke, idan ka sauko ma yi maganar, gaggawar ba ta da wani amfani " kan adam ya kuma magana, ya kashe wayarsa. Ya yi jifa da wayar a kan gado, ya san tun da bashir ya ce masa ba zai gaya masa a yau ba ba zai faɗa ba.
"Bashir why, kana ƙoƙarin mayar mini da aiki baya fa, dole na zo na sameka, ba zan iya jiranka ba".
Ya miƙe hannu ya ɗau waya ɗaya, ya sanya a aljihunsa, ya fita ya ɗau mota ya nufi family house ɗin su.
A sashen Ammi ya tarar da duk iyalan gidan ahalin marigayi Galadiman kano sun hallara, kama daga kan Mummy zuwa Fauziyya da ruƙayya, duk da ita ruƙayya ba ta fiye zama a gidan ba, tana can gidan yayar Mummy, ga kuma Ammi a zaune da iman da kuma Nusaiba, na gidan auren ne kawai ba sa nan. Takawa yayi turus yana kallonsu, wambai ya ƙure shi da ido, ya ƙaraso cikin falon yana sake tsuke fuska ya ɗam risuna ya ce "Barka da zuwa"
Wambai ya ƙi kulashi, shi kuma Adam bai tashi ba.
"Wato wuyanka har yayi kaurin da zan aika maka ka zo, ka yi burus da kirana ko?"
Yayi shiru bai ko motsa ba, sai ma alamun ɓacin rai da suka baiyyana a fuskar shi.
Da sauri Ammi ta ce "Allah ya taimake ka tuba yake yi, ayyuka ne suka sha masa kai, ga rashin lafiya da.....
"Ya isa binta, dama ke ki ke goya masa baya yake abun da ya ga dama, bai san darajar mutane ba sai zuciya ta banza da ta wofi, tabbas na fara gazgata jita-jitar da ake yi a kansa, na cewar yana shaye-shaye, duba da yanayin abubuwan da yake aikatawa, kalli yadda yake muzurai kamar zai kai mini duka, kalli yadda yake yawo a gari, kamar ba jinin sarauta ba, kalli ƙananan kayan da ke jikinsa, duk wani abu da ya shafi al'adar gidan nan nema yake ya watsr da ita, saboda kawai ya raina mutane.
Cikin dakiya Ammi ta sake cewa "Tuba yake, ayi masa afuwa".
Adam a zuciyarsa kuwa ji yake yi tamkar ya tashi yayi tafiyarsa, don cigaba da sauraren wambai, na iya sanya wa ya ɗuɗɗura masa ashar ya huta, saboda takaici.
Wambai ya mayar da idonsa kan Ammi ya ce 'Na san kina sane da maganar da take yawo a cikin masarautar nan, na yayi shaye-shaye yayi yimƙurin yi wa waccan yarinya fyaɗe, yayin da daga wata majiyar muka samu labarin ba fyaɗe bane ba, wani abu ne a tsakaninsu daban, to dukkaninku ku sani, ko da ɗan uwana baya raye, ba zan lamuncin mutunci da martabar gidan nan ta lalace ba, a hakan ka ke saka ran sarauta ta shiga hannunka, kana shaye-shaye ga kuma wannan mummunar maganar, ba zan lamunta ba, tun kan maganar nan ta je