Showing 66001 words to 69000 words out of 224014 words

Chapter 23 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1080

"Wuce ki tafi gida"

Ruma tayi gaba tana ɓata rai, ya ce "Zo ki karɓi kayan naki"

Ruma ta ce "Ka ajiye wa Yaya Aliyu ya taho da su"

Aliyu ya ce "Ni ne zan taho miki da aiken"

Kwasa ta yi da gudu, ko waiwayowa ba ta yi ba, dan kar ma ya ce sai ta ɗauko niƙan dan ta gaji.

Kamar korarriya mama ta ga ruma a cikin gidan, tana ta sauke numfashi.

"Lafiya ina aiken? Ko faɗan ki ka je ki ka yi?"
Ta girgiza kai.

"To menene, ina aiken?" Ruma ta sake tura baki.

"Ke magana nake miki kin shareni"

Kan tayi magana Aliyu ya shigo, da niƙan Mama.
Ya dire niƙan yayo kan Ruma, ta zura da gudu ta shige bayan mama.

"Wai meyene, lafiya?"

Aliyu ya ce "Ita ta san me tayi ai, wani bagidajen gaye ne, da wani tattararren ƙafar wandonsa, wai wannan bagidajiyar yarinyar ya biyo wai yana son ta, sai da na kusa ɗuɗɗura masa ashar, banda son lalata tarbiyyar yarinya, uwar me yake nema a wurin wannan yarinyar mai rabi hankali rabi hauka?"

Mama ta ce "Aliyu, ba ina sukar matakin da ka ɗauka bane ba, amma wanda ya ce yana son naka ai ba maƙiyinka bane, duk abin ku fa ko kuna so, ko ba kwa so dole watarana sai kun aurawa wani ta bar gidan nan, ku daina wulaƙanta mutane Sabo sun ce suna son 'yar uwarku".

"Ni bana son shi, ƙafarsa busu-busu ko mai bai shafa ba, kuma sai warin rana yake"

Hannu mama ta saka, ta mako ruma daga bayanta, ta din ga yi mata faɗa.

Duk da ita ruma ko faɗan ka yi mata ba ganewa take yi ba.

***
Iman ce ta shiga sashen Ammi da sauri, sai dai Ammi ta ɗan razana ta ce "Lafiya kuwa?"

Iman ta ce "Ammi, ina ga yaya Mahmud ne zai koma makaranta, na gansu a haraba kamar airport Mummy za ta kai shi".
Da sauri Ammi ta tashi, ta zaga ta ventilation ɗin ta, ta leƙa ta window, ta hangi Mahmud ya buɗe bayan mota ya shiga, Mummy ma ta shiga an kunna motar sun yi gaba.

Jiki a sanyaye Ammi ta saki labulen, ta shiga ambaton sunan Allah, Iman ta rungumota ta na faɗin "Ammi kina lafiya? Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki fa, kar ciwonki ya tashi" sai dai kan Ammin ta yi wata magana numfashinta ya fara sama-sama.



(Book 1 free ne, book 2 paid ne).

Ayshercool
08081012143
[04/08, 9:06 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

P 20

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.







P20




*Page ɗin sukutum guda naki ne masoyiyya Zainab kumurya, idan kin ga dama ki yayyaga shi ki zubar ko ki kashe Ruma, tun da naki ne😂. Ke kuma marubuciyar mijin malama Nimcy ki ji tsoron Allah, wallahi ana ta ƙorafi kin sako jaruma da masifu amma kin yi burus da mutane, zan karɓe rubutun mijin malamar nan fa😂 wanda bai karanta ba ya garzaya mijin malama an gama book1 labari mai tsayawa a zuciya*



A gigice Iman ta riƙo Ammi tana jera mata sannu, jinjina mata kai kawai Ammin ke iya yi, amma ta kasa magana.
Iman ta rungumota ta zaunar da ita a kan gado, cikin damuwa ta ce "Ammina, dan Allah ki yi haƙuri, ban nuna miki dan na tayar miki da hankali ba"

"Kar ki damu Iman, ba ki tayar mini da hankali ba, kawai dai tari ne ya taso mini, kawo mini ruwa a fridge mai sanyi na sha.

Cikin rawar jiki Iman ta tafi ta kawowa Ammi ruwa, ta karɓa ta sha, sannan ta ɗan kwanta ta lumshe idonta. A take ƙwaƙwalwaarta ta shiga tariyo mata abin da suka wakana a shekarun baya, daga kafuwar gidan zuwa yanzu, abubuwa da dama sun faru masu matuƙar wahalar mantawa da kuma ruɗani, wanda haryanzu a haka ake, komai sake dagulewa yake yi. A hankali ta gyara kwanciyarta tana son ta kawar da tunanin daga zuciyarta, amma sai kaiwa da komowa abubuwa suke a ƙwaƙwalwarta suka hanata sukuni.

***
Ruma kuwa a 'yan kwanakin nan ta addabawa Yasir, kusan kullum tana liƙe da shi tana kallon waya, idan anjima ta ɗau wayar Usman ta fara game, ya zo yayi ta zaginta ya ƙwace, sai ta koma gefe ta ɗau wayar mama, ta yi ta yi wa ƙawayenta fulashin, wasu su biyo wasu kuma suma su yi ta mata fulashin, babban abin da yake ƙonawa mama rai fulashin, wataran wayar haske kawai take yi, ko sai ta fara ringing ta zo ɗagawa ta katse, mama ta yi ta masifa ta ce "Idan baki kiyayeni ba, da ke da ƙawayen naki sai na saɓa muku, gayyar rashin hankali".

Yasir yana ɗan taɓa gyaran wayoyi, ya iya harkar jagwal, shine gyaran waya, system da sauran kayan electronics.
Wata waya ya samu, ta sha jiki, ya sayo layin data, ya saka a wayar, ya bawa ruma ya ce "Gashi nan, ki dinga kalle-kallen ki a wannan ki ƙyale mini wayata, kuma ki daina ɗaukar wayar mama kina fulashin, ki yi da wannan, saura ki lalata kuma akwai lokacin da zan dinga karɓa, dan ba bar miki na yi ba. Na buɗe miki account amma ban saka sunanki ba, ƙanwar maza na saka na ɗora miki hoton flower a dp kar a gano mu".

Ruma tamkar ta goya Yasir dan murna da farin ciki, ta gurfana ta dinga yi masa godiya, tare da sanya masa albarka.

"Amma ki ja bakinki ki yi shiru, kar ki gayawa kowa"

"In Allah ya yarda ba zan gaya wa kowa ba, bakina ƙanin ƙafata, amma me yasa ba zaka saka mini sunana ba da hotuna na nima?"

"Dan ubanki gidanku kuna da background ɗin da zaki dinga hoto ne? Kuma ni ban baki dan ki saka hotunanki ba, dan wallahi kin san idan suka gano kashinmu ya bushe, idan kin san ba zaki bi abin da nace ba, to tun wuri na karɓe kowa ma ya huta"

"A'a Allah ya baka haƙuri, da wasa nake maka nima, idan bana komai sai ka dinga bani ina ganin duniya nima, a daina hantarata dan na leƙa waya".

Tun da Yasir ya bata wayar nan, aka samu sauƙin neman magana a cikin gida, kusan koda yaushe tana kan wannan jagwal ɗin wayar, kuma Yasir abubuwan karatu yayi mata following, dan haka su tafi gani, kuma sosai suke ɗauke mata hankali, ya fi bata da daddare idan ya tabattar ta gama ayyukanta, da assignment, sai ya bata ta zauna a kusa da shi ta kalla, da lokacin kwanciya ya yi ya ƙwace wayar ya korata ta kwanta.

***
Zuwa la'asar Ammi ta ɗan samu nutsuwa, sai dai kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa.
Takawa ya fuskanci damuwa ƙarara a fuskar ta, sai dai ganin yadda take basarwa ba ta son magana, ya sanya shi yin shiru bai yi ƙoƙarin tilasta mata jin abin da yake damunta ba.

Wurin Jabir ya tafi, domin samun sauƙin wasu damuwoyin da suke damunsa, kasancewar sa ɗan uwa ɗaya tilo da ya fi yarda da shi.
Jabir na ganinsa ya ce "Sarkin matsala, tun kafin ka yi magana, fuskarka ta nuna akwai damuwa, yau kuma menene?"

Takawa ya ɗan yi shiru, sannan ya ce "Khalifa Usman wakili"

Jabir ya tsuke fuska ya ce "Ba zaka rabu da sabgar wannan yaron da ahalinsa ba ko?"

A hankali Adam ya ɗan lumshe idonsa, ba ya son yin dogon jawabi da ga Jabir, tun da shi jabir haryanzu ya kasa gane abin da yake nufi game da khalifa, dan haka kawai yayi shiru ya cigaba da tunani.

"Ina Ammi?"

Adam ya buɗe idonsa ya kalli jabir, amma bai yi magana ba, so yake yayi masa zancen muryar nan da yake ji, wadda haryanzu ya kasa daina jinta a kunnuwansa, amma ya san da ya ɗago zancen Jabir zai yi masa wata fassarar. Bai gama fahimtar mai Jabir ya cigaba da cewa ba, sai jin sunan Iman da yayi Jabir ya furta.

Ya ce "Me ka ce ne?"

"Ni fa matsalata da kai wulaƙanci, duk surutun da nake ba ka ma gane me nace ba?"

"Sorry" ya faɗa a taƙaice yana tsare Jabir da ido alamar yana son ya maimaita masa me ya ce.

Jabir ya ce "Well, cewa na yi, wai me ƙaninka yake nufi da Iman ne, yana takura mata da yawa fa"

"And so...?"

"Kana nufin ba ka damu ba kenan?"

"Kaga ni ka ƙyaleni da sabgar gidan nan, bana iya tunanin komai a kai, ko na fara ma kaina ciwo yake yi, gaba ɗaya bana son yin tunani a kan matsalolin gidan nan ".

Jabir ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, ni auren Iman nake son ku bani, ka wuce mini gaba zuwa wurin Ammi mana".

Wani irin kallo Adam ya yiwa Jabir ya ce "Ba ka da hankali ne?"

"Ban gane ba ni da hankali ba?"

"Amma ka san ba abu ne da zai yiwu ba ko?"

Jabir ya ce "Saboda me, wai ni ko dai kai ne ka ke son ta ne?"

Tsaki Adam ya yi ya tashi ya ce "Ka san idan har zan auri Iman, zan iya auren su Nusaiba ko Fauziyya, kai ma ka san ba zan bari ka auri Iman ba, kuma ka san dalili".

"Amma a tunanina wannan bai kai hujjar da za a hanani aure ba"

A ɗan hasalae takawa ya ce "A ganinka ba"

"Amma....." Bai jira jabir ya gama maganar ba, ya fice ya bar Jabir.

****

Ruma ce a tsakar gida, ta zage tana ta dakan ƙuli-ƙuli, zata yiwa Yasir kafi kaza, dan ya ƙara samun ƙwarin gwiwar bata waya tana jagwalgwalo, dan wayar ta fara shiga ranta sosai, ga cacar kuɗin data yana yi mata, da na caji wasu lokutan, tayi kiran ƙawayenta a wayar iyayesu su yi ta shashashanci ta daina ɗaukar ta mama.
Mama tana ganin wayar a hannun ruma, tana mitar ba ta son yawan duba wayar nan da take yi, a zatonta wayar Yasir ce kawai yake bata ta yi game da wasanta ta bashi kayarsa.

Mai sunan Baba ya nutsu ya tattara hankalinsa a kan litattafansa, sai dai hankalinsa ba a kan litattafan yake ba, damuwa da tunani ne fal a ransa, zuwa yanzu yakamata a sake aikawa da Abubakar kuɗi ko babu yawa ne, dan har zuwa yanzu ya ce masa bai samu wani aikin ba, leburanci ne ya kan shiga cikin gari ya nema idan ba shi da lectures, kuma gashi ɗan abin da za a baka na leburancin nan, bashi da wani yawa ga wuni ana aikin ƙarfi.
Ga kuɗin saukar su Yasir, ga kuɗin Necon su, dan dai suma yaran suna da ƙoƙarin neman na kai, da karambani Yasir ya koyi gyaran fitila, da wayoyi gashi ya san kan computer sosai, yanzu zai kashe wata wayar  ya tashi wata yana da kai a wannan fannin.
Shi kuma Huzaifa big boy ne, shi baya tanadi, idan ya samu kuɗi kawai ya kashe su, a huta. Sai dai bashi da rowa, yana zuwa shagon ɗinki da na aski, amma mugun mashiririci ne na gaske.
Sallamar da aka yi ne, ta dawo da mai sunan Baba daga tunanin da ya tafi.

Wata yarinya ce sa'ar ruma, sai kuma wata 'yar budurwa suka yi sallamar.

Fuskarsu kawai ya kalla, ya san da ƙuyar idan ba ruma ce, ta yi wata tsiyar ba.

Suka gaida mama cikin ladabi, shi kuma ya mayar da hankali a kan littafin gabansa kamar bai san da zuwansu ba.

Zumbur ruma ta miƙe, za ta janye su, mama ta ce musu yaya aka yi, saboda ita mama a tarbiyyar ta ƙawaye ba sa biyo ruma gida, idan ba wani abu ne mai matuƙar muhimmanci ya kawo su ba.

'yar babbar ta ce "Kuɗin da ƙanwata take bin ruma, muka zo karɓa".

Cikin mamaki Mama ta ce "wane kuɗi kuma?"

Yarinyar ta ce "Ranar an aiki ƙanwata, suka haɗu da ruma, shi ne a canjin mamanmu, ruma ta ranci naira ɗari biyu ta bawa wani  tsoho almajiri, wai  ya bata tausayi da ga gani yunwa yake ji, wai zata bata kuɗin kuma haryanzu ba ta bayar ba, mamanmu kuma so take ta yi amfani da kuɗinta"

Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ita ruman? Uban waye ya ce ki karɓar musu kuɗi kiyi sadaka da su?"

"Wallahi mama tausayi ya bani, cewa yayi na taimaka masa, kuma idan na bayar da kuɗinki zaki yi mini faɗa, shi ne na ranci canjin babarsu, kuma malam ne ya ce mana sadaka maganin masifa ce"

"Ke a cikin wace masifar ki ke? Ko da yake akwai masifar da ta wuce ɗauko mini magana da ki ke yi ba yau ba gobe, baki yi sadaka da kuɗin uwarki ba sai na uwar wasu, saboda tsabar rashin ji?"

Abdallah ya ce "Wallahi mama yarinyar nan da ƙyar idan ba ta da taɓin hankali".

Mama rasa me zata yiwa ruma ta huce ta yi, saboda yadda take caza mata kai abin ya wuce hankali, sai ƙifta ido take kamar an kwashewa karya 'ya'ya, gefe ɗaya kuma tana hararar yaran.
Mai sunan baba ya kalli Ruma, ya ga tana yiwa yarinyar alamar idan suka haɗu sai ta yankata.
gashi yau Mama ba ta da wani kuɗin kirki, ga ruma zata ja mata fitar naira ɗari biyu ba dalili.

Mai sunan Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ɗari biyu ya ajiye ya kalli yaran ya ce "zo ki ɗauka"

Cikin fargaba da tsoro yarinyar ta tafi ɗaukar kuɗin, dan fuskarsa ma kawai abar tsoro ce saboda kwarjini.

Har ta durƙusa ta ɗau ɗarin, ya kalleta sai da hantar cikinta ta kaɗa, ta dakata da ɗaukar kuɗin.

"Ke shashashar ina ce da wata za ta ce ki bata aron kuɗin babarki, ki bata ta bayar kina tsaye san sokwanci"

Jiki na rawa ta ce "Idan ban bata ba zata iya dukana"

"Idan ta dakekin ba zaki iya ramawa ba, ko ƙarfinki ta fi? Daga yau idan kuka kuma bata wani abinku, ku ka biyota gida kawo ƙara, da ku da ita zan haɗa na zane, ɗauki ki tashi ki bani wuri"
Kamar mai shirin ɗauko wani abu a wuta, haka ta miƙa hannu ta ɗauko kuɗin, ta tashi suka fice da sauri.

"Ke kuma zo nan" yayi ya yana kallon inda ruma take.
Jikinta har wata tsuma yake, ta taso ta zo in da yake ta durƙusa.

Ya ƙare mata kallo ya ce 'har kin manta sharaɗinmu ko?" Ta girgiza kai.

"Da kyau, nan da gobe in Allah ya ki nemo kuɗina da na bayar ki biyani, dan ba zan ɗau asara ba, kuma ban yarda ki tambayi wani a gidan nan ya baki ba, kuma ki ka je waje ki ka ɗauko magana sai na takaki a gidan nan, mara kan gado tashi ki bani wuri" da sauri ta zabura ta bar gabansa tana tsuma, ita yanzu a gidan uban wa za ta samo kuɗin da zata biya shi?.

Haka ta koma tayi zuruuu, kamar ruwa ya jiƙa mage, tana ji a ranta idan ta kama yarinyar nan sai ta daku, saboda ja mata damuwa da ta yi.

****
Samha ce zaune a falo, tana shan twa da biscuit tana yi tana kallon tv, tare da kaɗa ƙafa.
Wayarta ce ta fara ringing, dan haka ta ajiye kofin tean, ta ɗau wayar ta kara a kunnenta.

"Samha" ya kira sunanta a taƙaice.

"Waye?" Tayi maganar cikin ƙosawa.

"Khalifa Usman wakili"

"Wai meye haɗina da kai ne? Me ka ke so kuma?"

"Easy mana, a kan maganarmu ne dai da muka fara"

Samha ta ja tsaki ta ce "Wai kai baka ganewa ne? Ba mun gama wannan maganar da kai bane ba?"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ina ƙara baki lokaci ne, gudun kar ki dawo kina cizon yatsa daga baya, kin fi kowa sanin halin sa da taurin kai, ke a tunaninki ta ina burinki zai cika, kina daga zaune kina shashashanci lokaci na ƙure miki? Kiyi abin da ya dace ki samu burinki ya cika, ganin bayan Adam baya na nufin yi masa illar da ba zai amfanu a gareki bane ba, amma ganin bayan nasa shi ne samun damarki na biyan taki buƙatar. Idan so nake na kawar da Adam, abu ne mai sauƙi a gareni, amma ni ba hakan nake buƙata ba, haɗin kanki kawai kiyi tunani amma".
Bai tsaya jin amsarta ba, ya katse wayar, Samha ta bi wayar da kallo, tamkar za ta ga Khalifa a ciki. A hankali ta ajiye wayar ta yi shiru tana jujjuya maganar sa, sai dai ta kasa gano cikakkiyar mafita a kan lamarin.

"Samha, me ki ke tunani ne?"

Samha ta kalli mai maganar ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"Ki yi sauri ki je ki duba kayan nan, bana son sai an fitar mutane sun gama zaɓa tukuna"

Samha ta ce "Shikenan" sai dai hankalinta da nutsuwarta sam ba sa tare da ita.

***
Sam ruma ta rasa sukuni, gaba ɗaya sallolinta addu'a take a kan Allah ya sa mai sunan baba ya huce, idan bai huce ba bata san in da zata samo ɗari biyun nan ba, gashi ya ce kar ta sake ta tambayi kowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login