Showing 93001 words to 96000 words out of 224014 words
cikin daren suka ingiza su zuwa cikin daji, ciki har da ruma.
Tafiya suke tamkar suna kaɗa dabbobi, an tattaro mata manya da ƙanana sai maza 'yan tsirari.
Tafiya suke a tsananin duhu, ba tare da sun san in da suke sanya ƙafafuwansu ba, ruma ganin abin take kamar a mafarki.
Tun suna tafiya ruma tana saka ran tafiya za ta ƙare, har ta sare ta fara galabaita ta gaji tiƙis, dan haka ta ja ta yi burki ta durƙusa tana hutawa.
Cikin tsawa wani ya ce "Ke! Tashi ki wuce mu tafi"
"Na gaji wallahi, ba zan iya tafiya ba"
"Ba zaki iya tafiya ba? Tashi kan na ɗauke kanki da harsashi"
"Wai ya ka ke so na yi, ba ka ga ni yarinya bace ba, wallahi sai dai ku kasheni, nace na gaji ni wallahi ban taɓa ganin bala'i irin wannan ba"
"Dalla kasheta mu wuce, ba zata ɓata mana lokaci ba" cewar ɗaya daga cikinsu.
"Tsaya in zauna daga nan, sai ku harbeni, ina zan iya wannan wahalar, Allah yasa idan na mutu na je a sa'a, na san mama za ta mini Addu'a" tayi maganar tana zama.
Waɗanda suke kan babura ne suka iso, wani yayi parking ya ce "Tsayuwar me kuke yi ne?, ku wuce mana".
"Oga wai ta gaji, shine ta samu wuri zauna ta ce mu harbeta"
Hasketa na kan babur ɗin ya yi da fitila, ta saka hannu ta kare fuskarta tana mucincina ido, saboda hasken fitilar.
"Ke 'yar gidan waye a garin nan?" Ya tambayeta.
"Nifa ba 'yar garin nan bace, ziyara kawai na zo, gwaggo ta yaudareni aka kawo ni nan, wai sai zamu koma makaranta zata mayar da ni gida "
"Taso ki hau mu ƙarasa" yayi maganar yana nuna mata babur ɗin da yake kai.
Babu musu ko wani abu ta kama babur ta ɗane, ya ja suka tafi.
Aka cigaba da kaɗa sauran a ƙafa, tamkar shanu, a iya sanin ruma ita dai kawai sun yi tafiya mai nisan gaske, kafin su ƙaraso wani ƙaton wuri, bayan wani dutse tsakiyar daji sosai da sosai.
Wasu mutanen suka tarar riƙe da manyan makamai, ga wasu mutanen da aka kama duk a zube a ƙasa a zazzaune kamar fursunoni.
Ya karkata babur ɗin ya ce wa ruma ta saukko.
Ta cimimiye shi sannan ta sauka, tana kallon wurin, sai dai duk da hasken farin watan ba kowa take iya ganewa ba.
Ɗaga kai tayi ta kalli mutumin da ya kawota a babur. Da kayan jikinsa ta gane shi, mutumin ɗazu da duka haɗu a kasuwa.
Cikin mamaki ta ce "Kaii, kai ne?"
Ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce "Shhhhhh, wuce ki nemi wuri ki zauna"
Ta ƙarewa wurin kallo, sannan ta kalleshi "Wai a nan zan kwana? Akwai sanyi fa, kuma a wannan filin babu abin rufa ba katifa?"
Wani daga cikinsu ya gyara bindigarsa cikin tsawa ya ce "Zo ki wuce, au ke daɗi ma ki ke nema, zaki gane kuskurenki kuwa".
Ba ta motsa ba ta sake duban wanda ya kawota, ya jinjina mata kai ya ce "Wuce ki zauna"
A hankali ta ja ƙafarta ta wuce ta zauna a in da aka nuna mata, wani irin sanyi take ji har cikin ƙashinta, ga bishiyoyin wurin sai rausayawa suke yi, ƙafafuwanta duk sun yi tsami ga ƙaya da ta taka.
Wasu daga mutanen suka koma gefe, suka kunna sigari suna sha.
"Allah mai iko, yau kuma nan Allah ya kawo ni" ta takure jikinta tayi shiru, da yanzu tana gida kusa da mama, mama tana lulluɓeta.
***
Da ƙyar Adam ya iya kai kansa hotel ɗin da yake, bai tsaya ko ina ba sai ɗakinsa, ya je ya buɗe ya kwanta a ruf da ciki, yana ta maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un.
Cikin wani abu mai kama da bacci da kuma gizo, yake jin sheshsheƙar kukan ruma, kamar dai kowane lokaci itan dai yake gani tana kuka.
Haka ya wanzu a wannan yanayin, da shi kansa bai iya tantance wane iri bane ba.
Alarm ɗin wayarsa ne ya buga, alamar asuba ta yi, hakan ne ya sanya ya farka da kalmar shahada a bakinsa.
Ya tashi zaune ya ɗan yi shiru yana tunani, shi dai tun da Allah ya sanya ya taso da ƙuruciyarsa bai taɓa cikakkiyar lafiya ba, daga wannan sai wannan, bai taɓa tunanin zai kawo i yanzu ma a raye ba.
Ya yanke shawarar idan ya koma kano, zai kuma neman ruma ya ji meye matsalar sa da ita, da ta hana shi sukuni irin haka.
***
Har gari yayi haske, waɗanda aka ɗauko su ruma tare da su ba su ƙaraso ba, ruma ta kalli wani tsaye da bindiga ta ce masa "Zan yi sallar asuba".
"To waye ya hanaki?"
"Ban gane ba, zan yi fitsari ne in yi alwala, a bani abin salla"
"Duk ciki waye ki ka ga yayi salla a nan, kar in sake jin bakin ki".
Wani dattijo ya ce "Yarinya sai dai ki yi taimama ki juya ki kalli gabasa ki yi salla, amma babu mai baki wani ruwan alwala a nan" tsananin mamaki ya cika ƙwaƙwalwar ruma, ita haryanzu ma ba ta san dalilin da ya sanya a ka kawota nan ba.
Shawarar tsohon ta bi, ita kanta taimamar ba ta iya ba, haka nan ta batsaltsalata, ta yi salla.
Gari yayi haske sosai, sai ga waɗancan sun ƙaraso a mugun galabaice, wasu ƙafa sai jini take saboda taka ƙayoyi, wasu sai haki suke yi suna kuka, haka suma aka zube su a wurin gaba ɗaya.
Matan da suke ciki sai koke-koke suke, wani ƙato baƙi daga cikinsu yayi musu wata razananniyar ƙara "Ku rufe mana baki, ko tarwatsa ƙwaƙwalenku da harsashe".
Ruma tayi zurruu da ido tana kallon mutumin.
"Ke kuma na yi kama da ubanki ne da ki ke kallona?"
Jin maganar ruma tayi a sama ba daɗin ji.
"A'a meya kawo zancen ubana kuma, ubana ko da ban san shi ba, yafi ka kyau" tayi maganar cikin ƙunƙuni.
"Me ki ke cewa?" Yayi maganar yana yo wa kan ruma.
Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Babu wanda ya sake bi ta kansu, aka bar su a wurin nan.
****
Gidan iya kuwa sai da gari ya waye maƙwabta suka shigo, aka yayyafawa iya ruwa, aka tafi da ita Asibiti da ita da mijinta, su lawisa kuwa sai koke-koke suke yi.
Maƙwabtansu kuwa an yi wa yarinyar gidan fyade an kashe babanta an tafi da matar gidan. Nan da nan labari ya cika gari.
Babu shiri gwaggo ta shirya ta sanya lawalli ya goyata a babur ya kaita garin su iya. A nan ta iske cewar an yi garkuwa da rumaisa. A take ita ma ta yanke jiki ta faɗi, ita ma aka yi asibiti da ita.
Iya tuni ta farka, gwaggo kuwa da ƙyar ta farfaɗo, tunda ta farko take koke-koke tana faɗin "Na shiga uku me zance wa uwar yarinyar nan, da na sani na basu 'yar su, ƙaunar yarinyar nan ya sanya na riƙeta, da na san haka zata faru, da na barshi ya tafi da ita. Ni yanzu ina zan saka kaina"
Sai da ma'aikatan wurin suka taru suka yi ta rarrashin gwaggo suna bata haƙuri, amma cewa take "Ni dama tawan suka ɗauka suka bar 'yar mutane, bawan Allah baƙuwace 'yar wa na ce, ban san me zasu yi mata da suka tafi da ita, Allah ka fitar da yarinyar nan ni Shafa'atu ina zan saka kaina, ta ina zan yi wa uwar yarinyar nan bayani?"
Likitan ya ce "Ai uwar yarinyar na tabattar musulma ce, kuma tayi imani da ƙaddara, dan haka ko a gabanta ne za a iya sace yarinyar "
Girgiza kai gwaggo ta yi ta ce "Ba zaka gane ba"
A social media Abubakar ya fara ganin abin da ya faru, kuma ya san da batun an kai ruma katsina, ƙauyen da iya take, duk da yana makaranta.
Ba shiri ya kira Aliyu a waya ya sanar masa da a kan lallai ya bincika, su ji ya ruma take, sannan su gaggauta zuwa su ɗaukota.
Usman ma ya gani, dan haka a burkice ya ja Aliyu yake nuna masa abinda ya gani.
Aliyu ya ce "Yanzun nan Yaya yayi mini magana a waya, ina son na kirasu a waya amma tsoro nake ji, babban tashin hankalina kar mai sunan Baba ya ji balle mama, dama ya ce gobe in Allah ya kaimu zai je ya ɗauko ruma".
Usman ya ce "Ka ga ba wannan ba, ka kiras lawalli a waya ka tambayeshi yaya rumaisa take?"
Aliyu ya girgiza kai ya ce "Usman gabana faɗuwa yake yi fa, ance an karkashe wasu an tafi da wasu, kai dai ka kirasu"
Usman ya kira wayar lawalli, amma taƙi shiga, dan haka ya kira ta ɗanlami babban ɗan gwaggo, dan tabattar da abin da yake faruwa.
Sai da ta kusa katsewa sannan ɗanlami ya ɗaga wayar.
Ba tare da sun gaisa ba, cikin zaƙuwa Usman ya ce "Yaya ɗan lami, ya ake ciki ne? Na ji 'yan ta'adda sun kai hari garin su Iya, ya ake ciki ya ya ina ruma?"
Yaya ɗanlami ya ce "Wallahi kuwa, dan kaga gwaggo ma tana gadon asibiti, Baba kawai aka sallamo"
Aliyu ya karɓe wayar ya ce "To Allah ya kyauta, ya ya rumaisa, gobe in Allah ya kaimu yaya umar zai zo ya ɗauketa ya taho da ita, dan Allah a ɗaukota daga garin nan kan ya zo".
"Aliyu sai dai fa mu tsananta addu'a, an samu matsala 'yan bindiga sun tafi da rumaisa!!!"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, me ka ke cewa ne...?"
Usman ya girgiza Aliyu ya ce "Me ya ce maka ne?"
Kan Aliyu yayi magana, suka ga mai sunan Baba a tsaye yana kallonsu, Allah kaɗai ya san iya adadin lokacin da ya shafe a tsaye yana jin su ba tare sun sani ba.
Ayshercool
KANWAR MAZA
BOOK 2 PAGE 5
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Tsuru-tsuru suka yi suna kallon umar, sai dai yanayinsu ya nuna a razane suke, kuma aka rasa wanda zai yi magana.
Ƙarasawa yayi gabansu, ya karɓi wayar daga hannun Aliyu, ya yi dialing lambar ɗanlami, yana kira ya ɗaga tare da yin sallama. Sai dai ɗanlami na jin muryar mai sunan baba cikinsa ya kaɗa, dan ba ƙaramin tsoron tijarar mai sunan Baba suke ba.
Cikin kakkausar murya Umar ya ce "Me ka gaya musu? Ina ruma take?"
Ɗanlami ya ɗan rikice sannan ya ce "Malam umar a saka addu'a, amma Akwai damuwa, ka san shi lamarin ƙaddarar Ubangiji ba ayi mata shamaki".
Cikin hasala ya kuma cewa"Ba nasiha na ce kayi mini ba, tambayata zaka amsa mini, damuwar me, ka yi mini bayani ina rumaisa take?"
Tamkar an ritsa ɗan lami da bindiga ya ce "Umar wallahi 'yan bindiga sun tafi da rumaisa, kuma ba da ita kaɗai suka tafi ba, amma an sanar da jami'an tsaro za su yi ƙoƙari a kai, za abi bayansu"
Cikin tashin hankali ya ce "Ya isa haka ɗanlami, amma kun san garin nan babu cikakken tsaro kuka tura yarinyar nan? Babu yadda ba ayi ba a kan gwaggo ta bayar da yarinyar nan a dawo da ita gida amma taƙi, ta turata in da ta san babu tsaro, duk yadda ake ciki ku san yadda zaku yi, ni ban san wata magana ba kawai an haɗa baki da ku an yi garkuwa da yarinya ku san yadda zaku yi".
Ɗanlami zai yi magana, mai sunan Baba ya kashe wayar ya cillar ya fice a fusace dan gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun miƙe saboda ɓacin rai da tashin hankali.
Mama ce ta fito tsakar gida ta na faɗin "Wai babana shi da wa yake ɗaga murya, me kuka yi masa ne yake ta magana sama-sama?"
Cikin sanyin jiki Usman ya ce "Saɓani ne aka samu, kin san halinsa da zuciya da saurin fushi"
Mama ta ce "A'a ai kuwa bai fiye yin magana ba, sai an ƙure shi, wani abun dai ku ka yi masa, ko kuma faɗa kuke a tsakanin ku" gani tayi sun jeru basu ce mata komai ba, sai dai fuskokinsu ɗauke da damuwa, kamar a firgice suke.
Ta dubi Aliyu da kyau ta ce "Gadanga wai menene, na ganku duk wani iri me yake faruwa ne, ko akwai wata matsala ne?"
Aliyu ya dake ya ce "Babu komai mama, ni bari na fita zan sayo omo na yi wanki".
"Ban da omon da babana ya sayo shekaranjiya ya shigo da shi kaya guda, kusan kayan, wane omon kuma ka ke nema ko ka manta ne?"
Ya dafe kai ya ce "Ohh na manta, aski zani, ai na manta shaf da Oman ne, idan na dawo daga askin sai na yi wankin" yana yin maganar yayi waje, Usman ya rufa masa baya.
Gaba ɗaya mama ta kasa gane kansu, kuma ba wanda yayi mata bayanin wani abu. Kawai ta share ta cigaba da sabgoginta.
Duk yadda usman ya so dakewa abu ya gagara, a soro ya durƙusa ya fashe da kuka, shi ya riga ya karaya ya san ubangijin da ya halicci ruma ne kawai zai fitar da ita.
Aliyu ya rungumo shi ya ce "Haba usyy so ka ke sai mama ta gane ne? Dan Allah ka jure kan mu san abin yi, kar mu bari ta gano akwai matsala idam ta gane, ka san tana da hawan jini, yanzu zai iya tashi"
Usman ya ce "Wane abun yi da me zamu karɓota? Me muke da shi? Mutanen da ba imani ne da su ba, 'ya mace ce fa, Allah kaɗai ya san me zasu yi mata, gara ace mutuwa ta yi ga gawarta da wannan tashin hankalin, wa zai kula da ita?".
Aliyu da tasa zuciyar ma ke daf da karyewa ya ce "Na sani, amma addu'a ba ta bar komai ba Usman ita zamu dagewa, kayi haƙuri tashi ka daina kuka kar mama ta zo ta samemu" haka yayi ta rarrashin Usman.
Mai sunan baba kuwa ji yayi duniyar ta yi masa zafi, ina ma shi aka ɗauka aka bar ruma. Yaya mama za ta ji idan ta samu labarin an yi garkuwa da rumaisa?.
Zuciyarsa ta din ga zafi yana jin da zai ga gwaggo sai yayi mata rashin mutuncin da bata taɓa tunani ba, dan yana jin zai iya mangareta dan duk ita ta janyo wannan masifar, duk da tana ƙanwar mahaifinsu, cewar da aka yi tana gadon asibiti jininta ya hau bai dameshi ba, dan da jinin tasa uwar ya hau ko wani abu ya samu ruma, gara duk abin da zai faru ya faru.
***
Zuwan takawa a Abuja a wannan karon ya sanya ya samu abubuwa masu muhimmanci da bincikensa bai kai masa ba a baya, sai dai zuciyarsa na ta azalzalarsa a kan lallai ya koma gida, jinsa yake tamkar a kan wuta, idan bai bar garin ba kamar wani mummunan abu zai faru da shi, dan haka babu shiri, ya tattara kayansa ya taho Kano, dama ga Ammi na ta waya dan duk a tsorace take, saboda yanayin jikinsa, Jabir ma duk ya addabeshi a kan nan kano ma akwai aiki, dan haka ya haɗa kayansa ya koma kano.
Sai ka ce a wannan karon ya fara tafiye-tafiye, Ammi sai hamdala take a kan dawowarsa gida lafiya, dan ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, da yayi tafiyar nan dan sam ji ta yi ba ta son tafiyar ta sa.
A gidan Turaki suka haɗu, da takawa, da Jabir da kuma Jamil da ya kasance wa ga Samha kuma cousin ɗin sa.
Hira suke yi sosai, suna tattaunawa a kan rayuwa.
Jamil ya zunguri Takawa ya ce "Kai, wai me kake nufi da ni ne, ba fa ka taka gidana ba, ranar da na tare ma ko rakiya ba ka yi mini ba, kuma ba ka zo ba sai harkokinka kawai kake"
Ɗan shiru Adam yayi, tun daga lokacin da ya ji muryar ruma a ranar ya rasa nutsuwarsa, kilisar ma da ƙyar aka ƙarasata da shi, tunani ya fara yi ko zuwa unguwar su zai yi.
'Ka je ka yi mata me?' wata zuciyar ta tambayeshi.
Tsaki yayi wanda ya fito fili bai sani ba.
"Tsakin me kake kuma?" Adam ya tambaye shi.
Girgiza kai yayi bai ce komai ba.
Jabir ya ce "Yauwwa Takawa, ina mutuniyarka kuwa wannan yarinyar?"
Haɗe rai Adam yayi tare da basarwa, Jamil ya ce "Wace yarinyar, budurwa yayi ne? Kai ka isa ka yi wa ƙanwata kishiya?"
Jabir ya ce "To bana ce ba, wata 'yar figigiyar yarinya ce mai kama da bainu, ban taɓa ganin yarinya mara mutunci da rashin tsoro irinta ba".
Adam a ransa ya ce "Ai ba ka san mara mutunci ba, sai ka ga wasiƙar da ta rubuta mini' amma a zahiri yayi shiru kamar ba da shi suke hirar ba.
***
"Ina sonka Adam, so bana wasa ba, so mai tsananin gaske son da nake jin zan iya komai domin na mallake ka, duk da na rasa dalilin da ya sanya bana gabanka, ko da yake ba rasa dalili na yi ba, nafi kowa sanin dalilin da yasa bana gabanka, kuma ina daf da magance komai domin in samu miƙaƙƙiyar hanya ɗoɗar ta cimma muradina na rayuwa da kai, ko baka aureni ba ina son kasancewa da kai na rayu ƙarƙashin kulawarka. Ban sani ba ko zuwa nan gaba asirina ya tonu duk da bana tunanin faruwar hakan, amma idan ma ya farun ka yi mini uzuri soyayyar ka ce ta janyo mini hakan" tamkar taɓaɓɓiya haka samha ta saka hoton Adam a gaba ta na surutu, hoton yana sanye da kaya ne na sarauta, ya ɗan sauke rawaninsa yana murmushi, wanda aka ɗauka da hawan wata salla.
Sai da ta gama soki burutsunta, ta mayar da hoton ma'ajiyarsa, ta tashi ta ƙarasa shirinta ta fice.
Mummy ce tare da aminiyarta zaune a ƙuryar ɗakin Mummy suna tattaunawa.
"Wai hajiya Lubabatu babu wani zazzafan malami ne, abubuwa kamar sun tsaya mini, sun ƙi cigaba kamar yadda nake so".
"Haba Jamila, ke kin san an daɗe muna haƙa rijiya, rijiyar da muke saka ran samun ruwa a kowane lokaci, mun shirin da idan balli ya tashi akwai rikici, ke dai mu cigaba da haƙuri".
Mummy ta girgiza kai ta ce "Ya ci ace burina ya gama cika, nifa da dai da mintuna biyar bana son ruhin Binta ya kasance cikin kwanciyar hankali da farinciki, so nake ta dauwwama a baƙin ciki har ƙarshen rayuwarta".
Dariya Hajiya Lubabatu ta yi ta ce "Haba Jamila, ai ko a haka kika barta wallahi ta yabawa aya zaƙinta, kuma ta ɗanɗana kuɗarta, amma ki cigaba da haƙuri ai mun ɗana