Showing 81001 words to 84000 words out of 224014 words

Chapter 28 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1120

bayan la'asar sannan suka sauka, Ruma ta sha mita, kamar Aliyu ya ari baki, tayi masa shiru ta ƙi kulashi.

Sai da mama ta kira ta ji sun sauka sannan hankalinta ya kwanta.

Gidan da suka je babban gida ne, mak ɗauke da part-part, galibi Ruma ta san su, dan suna zuwa gidansu dan haka ba ta ga wani abu na musamman a a wurinsu ba, sai dai yanayin garin yayi mata kyau.
A sashin Gwaggo suka sauka, Gwaggo Atine har da hawayen murna, ta rungume ruma tana yi musu maraba.
'yar autar Gwaggo lawisa, sai kallon ruma take, da yake za su yi sa'anni da ruma, sai kallon ruma take yi.
Ruma kuwa jikinta ne duk ya mutu, saboda uwar tafiyar da suka yi, ba ta taɓa tafiya mai nisan ta yau ba.

Aliyu ya yi alwala, ya ce ita ma ta tashi ta yi salla.
A kan sallayar da ta yi salla, ta nemi wuri ta kwanta, nan da nan jikokin Gwaggo suka fara zuwa ganin ruma.

Ruma a ranta ta ce "Ji bala'i, kamar an ajiye musu buranya, sai kallona suke" ta dunƙule a cikin hijjabinta ta ɓoye fuskarta.

Gwaggo tamkar zata goya ruma, su Aliyu su kan zo, shi ma sai a shekara wani daga cikinsu bai je ba.
Nan da nan ta ɗorawa ruma.
"Auta taso ki zo ki yi wanka, zaki ji daɗin jikinki sosai"
Ruma kamar ta ce ba zata yi ba yamma ta yi, amma ta ga kar ta watsawa gwaggon ƙasa a ido, daga zuwanta, ta tashi ta je ta yi wanka da ruwan zafin.
Bayan ta fito ta tarar da lafiyayyiyar alala ta sha manja.
Ruma haryanzu a ƙoshe take da kazar da ta ci, dan haka ta ci kaɗan ta ce ta ƙoshi.

Lawisa kuwa so take ta yi wa ruma magana, amma ruman sai wani basarwa take tana haɗe rai, gaba ɗaya jikinta a ciwo yake, saboda wannan wahalalliyar tafiyar da suka yi, ga wani ɓacin rai da take ji da ba ta san dalilinsa ba.
Ganin ruma ba zata kulata bane, ya sanya ta fara ƙoƙarin yin abin da zata burge ruman, sai ƙoƙarin shishshige mata take yi.

"Ba ki ci alalar da yawa ba, zaki sha fura?"

"Na ƙoshi" ruma ta bata amsa a taƙaice.

Lawisa ta yi murmushi ta ce "To rama fa"

"Baiwar Allah cikina ne a cike fa, na ƙoshi, ko haɗama ki ke so in yi?"

"A'a, ko in ɗauko miki fulo ki kwanta".

Ruma ta ce "Eh, dama na gaji sosai"

Lawisa ta je ta ɗauko fulo, ta kawo wa ruma, ruma ta kwanta babu jimawa ta hau bacci.

***
Nema yake ya fita daga hayyacinsa, duk Addu'a da ta zo bakinsa yi yake yi, amma kansa kamar ana buga masa wani abu, ga wayarsa na ta ringing amma ba zai iya ɗagawa ba, ya lumshe idanunsa, ya jin yadda cikin naman jikinsa ke wani irin zafi, idanunsa kamar za su fito saboda ciwon kai, ya dafe kan yana karanta alƙur'ani a fili, a hankali wani mawuyacin bacci ya kwashe shi.

Rumaisa ya gani a kan wani dutse a zaune tana kuka. Hayaƙi na ta tashi a wurin, amma yana iya gane fuskarta.

*Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai taƙamarka kuɗi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuɗin naka da sarautar ta ka sai ka durƙusa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka* kamar yadda ta gaya masa a haɗuwarsu ta ƙarshe, haka ma a yanzu take sake maimaita masa, ya buɗe idonsa a hankali a cikin dodon kunnensa yake cigaba da jin sautin muryarta.

Ruma ma da bacci ya kwasheta, a razane ta yi wata 'yar ƙaramar ƙara ta farka, tana haki kamar wadda ta sha gudu, a lokacin duhun magariba ya rufa! Gaba daya suka yo kanta suna tambayar ta ko lafiya?.

Ayshercool
[8/22, 11:41 PM] Maman Aslam: *Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*


Tamkar wadda aka tsamo da ga kwata haka ruma ta juya ta koma gida tana kuka, mutane a hanya wasu na tambayarta ko lafiya? wasu kuma suna mata dariya, yara sa'aninta kuma suna dariya ta kamo kifi soyayye, saboda yadda ta yi tsumu-tsumu da taɓo.

Takawa kuwa tafiya yayi yana jinjina taurin kai da tsagwaron tsageranci gami da rashin tsoro irin na Rumaisa.
Ya daɗe bai ga abin da ya bashi mamaki kamar rumaisa ba, amma babu mamaki kamar yadda ya sanya aka masa bincike an tabattar masa da a cikin maza bakwai ta tashi, har halinta na rashin ji sai da aka gaya masa, tare da makarantar da take zuwa, a nan ya tabattar da muryarta da yake ji tabbas ta ta ce, tun da gidan gonarsu a unguwar su yake. Amma ya aka yi ta san gidansu har ta bishi can.

Ya tsaya da mamakin ne a lokacin da ya tuna ɓarawo da ta laƙanta masa, a take ransa ya ɓaci, ya sake ƙudurar aniyar sai ya ladabtar da ruma ta hanyar da ta dace.

Idan ya tuna sharrin da ta sake liƙa masa, wai ya taɓa mata nono, sai ya rasa me ma zai yi, mamaki ko dariya?.

Mama ce ta kalli ruma ta ce "Meye haka, meya same ki?"

Cikin kuka ruma ta ce "Wani bugagge ne ya wanke ni da ruwan kwata, wallahi ba zan yafe masa Allah ya tattaro masifar duniya da ta gabasa da yamma kudu da arewa....

"Rufe mini baki? Ban hana ki yi wa mutum irin wannan addu'a ba? Wataƙila bai sani ba"

"Mama kalli jikina fa, ya na sane yayi mini, wallahi ba zan yafe ba, kuma in Allah ya yarda sai an sace motar, sai na yi masa tijarar da bai taɓa ganinta ba idan na kuma haɗuwa da shi, kuma sai an sace motar na ga ta tsiya"

"Wane mahaukacin ne yayi miki haka? Makaho ne shi?" Usman ya faɗa yana ƙarewa uniform ɗin ruma kallo, da suka jagalgale da taɓo.

Mama ta ce "A'a, kar ka zigata dan Allah, wuce ki je ji cire kayan, tsautsayi ne, kuma Allah yana tare da masu haƙuri"

Usman cikin takaici ya ce "Haba mama, kalli jikinta fa wallahi wannan da iskanci yayi mata, waye shi a ina yake? Kin gane shi? A nan unguwar yake?" Ya jero mata tambayoyin.

Ɗan shiru tayi ta tuna furucin takawa, na zai kama yayyenta ya rufe su, ya saka a rushe musu gida. Nan da nan ta ce ni ban san shi ba, zuwa ya yi wucewa, yayi mini haka, to wallahi Allah ya isa na"

Huzaifa ya ce "Ƙaraso na tayaki ki wanke jikinki" ta ƙarasa, Huzaifa ya ɗebo ruwa a rijiya ya hau sheƙawa ruma, sai da ta kusa shiɗewa, mama ta din ga yi masa faɗa, ƙarshe dai ruma ba ta je makarantar ba ranar, ba ta yi jarrabawar ba, wunin ranar kuka ta din ga yi, tare da janyo wa takawa jafa'i iri-iri.

A daren da yakamata washegari su ruma su tafi katsina, ta fara ciwon kai da ciwon ciki, har zuwa wayewar gari, dan haka mama ta ce sai dai a ɗaga tafiyar zuwa kwanaki biyu idan ruma ta warke.
Har zuwa azahar ruma tana kwance tana fama da ciwon ciki, Yasir ya ce "Shegen ciye-ciyenki na masifa ne yake janyo miki ciwon ciki, kece ci wannan ci wancan a islamiyya kullum cikin tauna kamar tunkiya" ruma ba ta yasir take ba, ta kanta take yi dan haka bata kula shi ba. Aka kai ruma chemist aka sayo mata magunguna.

Mama aka yi wa waya daga cikin gari,  babur ya buge Hauwwaliya ta karye a ƙafa, dan haka babu shiri mama ta shirya cikin tashin hankali ta tafi.

Ruma sai kuka take, ga karayar hauwwaliya, ga zafin ciwo kuma wai mama ba zata tafi ta barta ba. Mama ba ta saurareta ba, ta shirya ta yi ficewarta.

Burgima ta din ga yi a tsakar falon mama tana kuka, kamar wata yarinyar goye, sai gunji take "Wayyo cikina"

"Ke!" Ta ji tsawar mai sunan Baba daga ƙofar ɗakin. Take ta nutsu ta yi shiru.

"Mara hankalin ina ce ke? Dan baki da lafiya sai ki ishi mutane, ba zaki yi addu'a ba?"

Shiru ta yi tana kuka ƙasa-ƙasa dan ita kaɗai ta san abin da take ji.

Aka jima kuma sai amai, ga jikinta ya ɗau zafi sosai. In da ta yi aman a nan ta zauna ta kasa tashi. Sai Aliyu ne ya wanke mata baki ya ɗagata ya mayar da ita ɗaki, ya wanke wurin.

Har bayan azahar mama ba ta dawo ba, ga ruma jiki yaƙi daɗi, Aliyu ya ce zai samo abin hawa ya kaita asibiti. Usman ya ce a fara ba ta abinci ta ci tukuna.

Cikin ruma ya sake ƙullewa, har cikin ƙafafuwan ta, ta tashi da ƙyar, ta tafi toilet yin fitsari.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku dan Allah ku taimake ni " suka jiyo ihun ruma a toilet.

Mai sunan Baba ne ya tafi da gudu ya buɗe banɗakin a razane, dan duba meya sameta, suma sauran suka rufa masa baya, amma suka tsaya a waje saboda ya na bakin ƙofar.

Ruma ce a tsaye, ta gama fitsarin ta miƙe tsaye tana kallon yadda fitsarin na ta ya gauraya da jini, duk da ba wani mai yawa bane ba.

"Meye haka?"

Cikin rawar jiki ta nuna masa ta ce "Mai sunan baba ka ga, fitsarin jini nake, mutuwa zan yi" tayi maganar idonta na cika da hawaye.

"Yaushe ki ka fara irin wannan fitsarin?"

"Yanzu kawai na gani" tayi maganar tana dafa bango, saboda jirin da take ji.

Ya waiwayo ya kalli Yasir ya ce "Ɗauko mata zanin mama" Yasir shima jiki na rawa ya tafi ɗakin mama, dan hankalinsa ya tashi sosai.

Ya sake duban Usman ya ce "Ɗan ɗora mata ruwa ya yi zafi, ta yi wanka" cikin damuwa Usman ya ce "To meya sameta?"

Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "May be is her fisrt period"

A razane Aliyu ya ce "What! Rumaisan? How old is she? Yarinya ce fa sosai"

Usman ya ce "Ikon Allah"

Mai sunan Baba ya miƙa mata zani ya ce ta ɗaura ta fito. Ta ɗaura ta fito ya bata kujera ta zauna, Usman ya zuba ruwa ya wanke banɗakin. Ruma kuwa jikinta sai rawa yake yi tana tunanin ƙarshenta ne ya zo.

Usman ne ya fita sayo pad, sai dai babu wanda ya san ya ake amfani da ita.

Gaba ɗayansu suka diririce, musamman ganin yadda ruma ke kuka, Huzaifa kamar ya tayata kukan, ita sam ba ta san menene ya sameta ba, mai sunan Baba ne kawai yake ta wani basarwa.

Aka kai mata ruwa tayi wanka, usman ya tattare kayan da ta cire, ya zuba a bokiti ya zuba musu ruwa.

Gaba ɗaya mai sunan Baba ya rasa ta ina ma zai fara, gaba ɗaya baya manta lokacin da aka haifi ruma, kamar jiya aka haifeta haka yake gani, wai ita ce yau period ya zo, yarinyar da ko ciwon kanta ba ta sani ba, ban da tarin rashin hankali da rashin kunya ba abin da ta sani, duk wani abu da ya shafi rayuwa ba saninsa ta yi ba.

Sai da yayi browsing, sannan ya ga yadda ake amfani da pad, ya nuna mata, har zuwa yadda ake discarding ɗin ta, ta karɓa ta saka, sannan ta saka kaya.

Ya kalli su Usman ya ce "Su basu wuri, za su yi magana" ba musu duk suka fita.

Ya kalli ruma ya ce "Kalleni nan" ta ɗaga kai ta kalleshi.

"Ko akwai wani abu da ya haɗaki da wani?"

Ta ce "Eh" gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa ya ce "Menene?kuma waye shi?"

"Wani mutumi ne, ruwan kwata ya watsa mini da motarsa jiya da safe".

"Ba wannan nake nufi ba, ko akwai wani wanda yayi miki abin da bai dace ba, ko wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki?"

Tunowa ta yi da takawa, yadda ya cakumota, amma tayaya za ta fara yi wa mai sunan Baba wannan bayanin, ai kan a kai ga takawa, ita zai fara tattakawa, a karon farko da ta yi masa ƙarya ta ce "Babu kowa"

"To idan ma akwai ki ka ƙi faɗa, idan na gano sai na yankaki na zuba a rijiya, kuma wannan yanayi da ki ka shiga, duk wanda ki ka bari ya taɓaki ko yayi miki wasan banza, ciki zaki yi kuma mutuwa zaki yi" gaban ruma ne yayi mummunan faɗuwa, meye makomar taɓata da takawa yayi? Ta yi ciki kenan?.

Haka suka shimfiɗa tabarma a tsakar gida, suka kewaye ruma, yau har masu zuwa ball ba wanda ya fita, suna ta jera mata sannu, ban da masu fifita da masu ba ta abinci.

A haka mama ta dawo ta tarar da su, cikin mamaki ta dube su ta ce  "Wai har yanzu jikin ne?"

Usman ya ce "Tun da ki ka fita a haka take"

Mama ta ce "To Allah ya ƙara afuwa, wallahi ina can muna fama, da ƙyar aka samu aka ɗora yarinyar nan, tana jin jiki, sannu 'yar auta" ruma dai ba ta amsawa mama ba, ta sake lafewa a cinyar Aliyu.

Mai sunan Baba kuma yana gefe kamar mai gadi, yana kallonsu.

Mama ta kalli kayan ruma da suke shanye, gidan ko ina tsaf, amma ko girkin dare ba su ɗora ba.

Mama ta ce "Yasir, tashi ka ɗora mana ko taliya ce a ci da daddare" gaba ɗaya basu da walwala kamar wadda aka ce musu ruman mutuwa ta yi.

Cikin damuwa mama ta ce "Wai me yake faruwa ne duk na ga kun yi jugum-jugum? Duk dan ba ta da lafiya ne ku ka zo ku ka tare a wuri ɗaya haka, ba an sayo mata magunguna ba?"

Duk shiru suka yi, suna sunkuyar da kai aka rasa mai iya yi wa mama bayani.

"Mama fitsarin jini fa nake yi " Ruma ta yi maganar daga kwance.

"Wane irin fitsarin jini kuma? A garin yaya?" Mama ta yi maganar a tsorace.

Usman ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Wato ainihin, muna tunanin, wato ko.. abin nan na mata da suke duk wata, wato haila shi ta fara" waro ido waje mama ta yi ta ce "Ban gane ba"

Mai sunan Baba ne ya karɓa yayi wa mama cikakken bayanin abin da yake faruwa.

Mama ta yi salati tare da tafa hannu ta ce "Ruma haila, iko sai Allah girma ya riga hankali zuwa, a yanayin jikinta ban taɓa kawo zuwan wannan abun yanzun ba, ikon Allah"

"Mama wai menene ya sameni?"

"Girma ki ka yi" mama ta bata amsa.

Mama ta sake kallon igiya da kayanta a kan igiya, ta jinjina kai ta ce "Lallai ƙanwar maza, yanzu har ɗan kamfan ma ku kuka wanke mata? Iko sai Allah to Allah ya shiga lamarin, amma akwai badaƙala".

"Mama wai mutuwa zan yi?"

"Ba mutuwa zaki yi ba, abin da yake hana 'yan makarantar ku salla shi ne ya zo kanki". A gaban su Yasir mama ta zauna tana yi mata bayanin komai, sai a yanzu ta gane wasu daga cikin karatun da aka yi musu a Islamiyya in da suka dosa.

Gaba ɗaya jikin ruma yayi sanyi, babu babban abin da ya tsorata ruma, sai cewa da mama ta yi ita ma yanzu za a din ga rubuta mata zunubi idan ta yi saɓo.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku, dan Allah kar a rubuta mini zunubi".

Aliyu da ta kwanta a kan cinyarsa ya ce "Wallahi sai an rubuta miki, gara tun wuri ki nutsu ki shiga hankalinki"

"Astagfirullah, dan Allah mama kar a rubuta mini zunubi, ba na jin magana, dan Allah mama kar a din ga rubuta mini zunubi bana son na mutu yanzu. Wayyo Allahna"

Mama ta ce "Iko sai Allah, na ga yadda za ayi wannan lamari da wannan yarinyar mara kan gado".

Har zuwa washegari aka samu zazzaɓi ya sauka, amma jikinta babu ƙwari, mama da kanta ta kaita banɗaki za ta yi mata wanka, sai dai pad ɗin jikinta ba ta ɓaci ba, mama tana yi mata wanka ruma tana ɓoye ƙirjinta.
Mama kawai ta yi dariya ta cigaba da silleta.

Da ta fito da ita kuwa, tuni sun haɗa mata tea, Yasir ya ɗauko mata kayan sawa, har da pad ɗin da zata saka.

Mama kawai girgiza kai ta yi, gaba ɗaya sun wani nutsu sun damu, duk saboda ƙanwarsu.

Ruma ta yamutsa fuska ta ce "Ni ba zan saka wannan abar ba, damuna take yi?"

Mama ta ce "A haka zaki zauna?"

Ruma ta ɗaga kai alamar eh.

"Aikuwa kya ɓata jikinki, a haka jininki ya ƙare, ni babu ruwana" mama kan ta mazewa take yi, amma lamarin ya zo mata a bazata, ba ta taɓa kawo wannan abu nan kusa a kan ruma ba.

Da ƙyar ruma ta yadda ta saka pad ɗin nan, duk nasihar da mama tayi mata, tare da bayani, lokacin salla na yi ta ɗau buta ta ce ita alwala za ta yi.

"Wai ke wace irin yarinya ce ne haka? Ba na yi miki bayanin babu salla, babu azumi, ga duk wadda take haila ba".

"To ni mama da wanne zan ji, kin ce mini za a din ga rubuta mini zunubi,. Yanzu kuma kin ce ba zan salla ba, in shiga wuta kenan?"

"Wai ke Meyasa duk bayanin da za ayi miki, ba zaki tsaya ki fuskanta ba sai dai ki yi ta wauta, Allah ne ya ɗauke miki, sai kin yi tsarki zaki yi salla" Aliyu yayi Maganar a fusace dan ya fara gajiya da halin ruman, ana mata bayani tana bauɗewa.

Tun ranar da ya ɗan zubo ɗin nan, bai sake zubowa ba, ruma ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi, ga pad ta isheta gaba ɗaya abin duniya ya isheta.

Tun daga kwana ɗayan nan ya ɗauke, mama da kanta ta kaita banɗaki ta koya mata yadda ake wanka, babu babban abin da yake cigaba da ɗagawa ruma hankali, cewa da mama ta yi, ita ma za a fara rubuta mata zunubi.
Ta tattara laifin kacokan ta ɗora shi a kan takawa, wanda a dalilinsa duk haka ta sameta, dan daga watsa mata taɓo ya sa ta fara rashin lafiya, wannan abun ya zo mata.

Mama ta ce a bar tafiyar su katsina, sai bayan ruma ta gama warwarewa zuwa wani satin.

***
Takawa kuwa har zuwa yanzu, bai daina jin muryar ruma ta na zuwar masa ba, abin har mamaki yake bashi. Wasu lokutan a zahiri yake jin muryar tana yi masa gizo, gashi tun daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login