Showing 222001 words to 224014 words out of 224014 words
kanta da kasa gaya musu abun da take gani a tare da adam, da alamu suka nuna mata su basa gani, ita kaɗai kawai take gani.
Usman kuwa cewa yake "Wallahi ba zaki yi mana baƙin ciki ba dan ubanki, haka kurum ke fa ki ke son auren mai kuɗi, kuma Allah ya kawo, ki ce ke ba kya so, kin yi kaɗan yarinya, dole ayi auren nan, ko ba komai ma hau doki, kina kallo albarkacinsa aka fito da Aliyu, yanzu malam shamsu har gaisheni yake, saboda yadda ya kankaro mana mutunci, sai kin je".
Cikin kuka ta ce "To ni bana son shi"
"Uban da ya sanya, ki ka amince tun da fari, shi zai sa ki haƙura ma a yanzu" gaba ɗaya aka ƙi goya mata baya, ta din ga surutai da koke-koke suka ƙi kulata.
Ammi da suka tafi gida, jikinta sanyi yayi, da ganin yadda rumaisa duk ta rikice lokaci ɗaya, kuma ta ga bai kamata ta ɓoye musu wasu abubuwan a kan Adam ba, amma tana ji a jikinta rashin lafiyar ta sa abu ne da ya shafe shi, da shi da ita rumaisan, ta din ga fatan Allah ya sanya hakan ba zai zama cutarwa ga rumaisa ba.
Nusaiba ta din ga tambayar ammi yadda suka yi.
Ammi ta ce "Sun amince, rumaisa ce dai take nema ta ce ta fasa, amma ina ganin rigima ce kawai irin ta ta, kuma kai takawa, kamar yadda na gaya maka a baya, dole ka sassauta ka mayar da kanka dai-dai da ƙuriciyarta, bana son ayi auren nan ya zaman tana jin tsoronka, ko tana ganin kamar ba ka da imani"
Adam bai iya fahimtar abun da ammi take faɗa sosai, ya kwanta a kan 3seater, ya lumshe tabbas.
Iman kuwa tausayinsa da na ita kanta rumaisan ya kamata, mussaman da ta ji cewar nan kurkusa sosai za ayi auren.
Har dare yayi, ko abincin kirki rumaisa ta ƙi ci, sai koke-koke, suka shareta suka cigaba da harkokinsa, usman sai tsara yadda abubuwa za su kasance yake yi.
Mama ta kira yaya Abubakar a waya, ta sanar masa da batun, ya ce zai shigo kano, Yakamata tun wuri su san me suke ciki, su san mai yakamata a fara tanada na auren rumaisa.
Jin abun da yaya Abubakar ya faɗa, ya sanya rumaisa jin kome za ayi mata ba zata iya barin gidan nan ba, sai dai idan an yi auren ya dawo gidan ya zauna, ko ya barta a gida ya bata sabir kamar yadda aka yi mata alƙawari.
Tashi ta yi ta nemi wuri ta yi kwanciyarta, saboda hirarrakin ɓata mata rai suke yi.
Daga nesa take hango shi cikin hayaƙi, a hankali hayaƙin yake bajewa, yana ƙara kusantota, ganinsa ta yi cikin sarƙa hannu da ƙafa, ga idonsa na ci da wuta a wannan karon ba hayaƙi kawai yake yi ba, fiƙarsa duk ta fito daga bakinsa, ga faratansa sun yi zaƙo-zaƙo. Tunkarota yake yi, yayin da ita kuma take ja da baya, cikin tsoro da razani.
Duk iya ƙoƙarin ta na addu'a, ta kasa dan ji ta yi tamkar an danne mata masarrafar tunaninta, zuwa maƙoshinta, ta kasa Addu'a.
Tun tana ja da baya, har ta kai bango, fizgota yayi da ƙarfi, ya danna mata faratansa a maƙoshinta.
"Wayyo Allahana mama na shiga uku, Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Ko sallame sallar da take mama ba ta yi ba, ta yo kan rumaisa jin tana ihu, kamar wadda za a kashe.
Mama ta fizge net ɗin rumaisa, ta riƙota tana tambayarta "Lafiyarki kuwa? Menene?"
Rirriƙe mama ta yi tana mayar da numfashi, hannu ɗaya kuma ta riƙe wuyanta, da take jin kamar yana yi mata zafi.
Tuni Aliyu da mai sunan Baba suka taso da gudu suka yo ɗakin mama, saboda yadda kururwar rumaisa ta cika gidan.
Mama ta jijjigata ta ce "Rumaisa menene ki yi magana mana"
"Mama baban Sabir ne, shine"
"Me yayi miki?" Numfashi take saukwa, amma ta kasa gayawa mama abun da ta gani.
A fusace mai sunan baba ya ce "Wulaƙancin naki da iskancin har ya kai ki din ga yi mana ihu cikin daren nan? Kar ki kuskura ki kaini bango, na kuma jin bakinki sai na zaneki, ki yi addu'a ki kwanta, idan ma kina yi ne saboda ba kya son auren, to kin yi kaɗan"
Mama gaba ɗaya jikinta yayi sanyi ta kuma cewa "Me ki gani ya razanaki haka?" Rumaisa ta yi shiru.
Mai sunan baba ya ce "Ba wani abu da ya razanata, shirmenta da take yi ne yake zuwar mata har a mafarki"
Aliyu ya yi tsaki ya ce "Rigimarki ba ta ƙarewa, har tausaya bawan Allah nan nake faman da zai sha" ya fice daga ɗakin, mai sunan baba ma ya fice.
Duk iya rarrashin mama, da lallaɓa yaro a matsayin ta na uwa, ta yi, amma rumaisa ta ƙi gayawa mama ainihin abun da ya faru, haka mama ta ƙyaleta ta sake tayar da salla.
Tsoro ya hana rumaisa ko rufe idonta, dan haka ta tashi ta je ta yi alwala, ta zo ta tayar da salla ita ma, sai dai tana yin raka'a biyu, wani nannauyan bacci ya ɗauke ta.
Mama tana jin yadda rumaisa ke ta surutai a baccin, kamar tana hannun ƴan bindiga.
Sai da mama ta sanyata a gaba tana ta tofa mata adduoi, har mama ta fara tunanin, ko rumaisa na da aljanu ne, maganar aure ta taso za su fara motsawa.
Dan haka ta ƙudurce a ranta, dole ta nema mata maganin sheɗanu.
Ta cigaba da sallolinta, tare da tsananta addu'a a kan lamarin auren nan da yake tunkarosu.
***
Mamaki Samha take ba ɗan kaɗan ba, ganin irin surƙuƙin ƙauyen da suke kurɗawa, ita da Mummy da kuma Hajiya Lubabatu.
Kasa ɓoye mamakin ta yi ta ce "Wai yanzu Mummy har nan ku ke zuwa? Ni fa ma fara jin tsoro"
Mummy ta yi murmushi ta ce "Yaro yaro ne, ke ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake, tafiya duk nisanta da surƙuƙinta, in dai da biyan buƙata ai shikenan, tafiya ɗazu ce".
Hajiya Lubabatu ta ce "Ke idan babu wannan ƴan biye-biyen mutum ya zauna lafiya, mussaman a irin gidajen sarautar nan, ai ni tun da Allah ya taimakeni, na kaɗa duk wata mata da ta raɓi gidana, na ga tsuguno ba ta ƙare mini ba, sai na dangana da mallakawa Jabir kujerar galadima,"
Samha ta ce "Takawan fa? Ba gidansu sarautar za ta koma ba".
Mummy ta zunguri Hajiya Lubabatu, sannan ta ɗora da cewa "Yauwwa, mun kusa ƙarasawa, daɗinta kowa yake gani, idan muka je sai ya katse ya sauraremu".
Samha ta ce "Ni fa idan za a kasheni, ban san hanyar komawa ainihin titi ba, gaba ɗaya kaina ya juye".
Hajiya Lubabatu ta ce "Zaki zama ƴar gari ne da zarar kin waye".
A cikin surƙuƙin ƙauye sosai mutumin yake, dan an fita daga gari sosai wurin kamar daji, a nan aka yi masa wani shinge, suka tarar da tarin mata da maza a wurin, da masu zubin hannu da shuni, da masu saffa-saffa, ga marasa lafiya kuma, wasu abun nasu ma dai ba kyawun gani.
Ba tare da ɓata wani dogon lokaci ba, bayan an sallami na ciki, suka shiga, wurin duk an kafe ƙahuhuna da ƙwarangwal ɗin dabbobi, ga wani irin wari da tsamin turaruka da magunguna da ɗakin yake yi. Mutumin yana zaune cikin wasu tsummokaran kaya, ga wasu irin kayan tsubbu a gabansa shi kansa duƙun-duƙun da shi, kamar ba ɗan Adam ba, ga idonsa ɗaya hakiya ta rufe, ɗayan kuma a juye ga idon jawur.
Sai da kan Samha ya sara, ta nemi faɗuwa, Hajiya Lubabatu ta riƙeta suka zauna.
Mummy ta ce "Barka da warhaka malam, ya aiki ya ƙoƙari"
"Lafiya ƙalau, kin yi nusau, ko buƙata ta biya ne, ko kuma dai kin fasa aikin da ki ka buƙata, tun da ki ka ce mana akawai maganin da ake masa amfani da shi, muke jiran ki kawo mana maganin mu yi aiki a kai, amma mun ji ki shiru".
"Ai malam maganin ne yaƙi samuwa, duk wata hanya da zan bi a samu, ba a dace ba, amma ba haƙura na yi ba, ina nan zan dawo. Gamu tare da baƙuwa, ƴar facalarmu ce, da ita da shi yaron Adam, duk iyayensu ƴan uwa ne, ta daɗe tana son shi, amma ya auri ƙanwarta, yanzu ƙanwar ta mutu, amma uwarsa na son aura masa wannan ƴar tsintuwar da na taɓa baka labari, kuma wannan ɗin ta kuma rasawa, shine muke son ayi wani abu a kai".
Yayi shiru, sannan ya ɗebi wata ƙasa ya zuba a wani fai-fai, ya dinga juya hannunsa, sannan ya kalli fai-fan ya ce "Tirƙashi, tabbas ga maganar aure nan, sai dai ita yarinyar tana tafe da wata irin guguwa mai ƙarfin gaske, sai kun tashi tsaye sosai"
Cikin sauri Samha ta ce "Malam so nake kar auren ya yiw....."
"Aure sai an yi shi, ma'aunin ƙaddarar yarinyar da zai aura ya rinjayi tasa, sai dai idan ɗayansu ne ya mutu"
Kamar Samha za ta yi kuka ta ce "Dan Allah malam a kasheta, ba zan iya jurewa ba a wannan karon"
Mummy ta ce "Malam, ka san yarinyar, wadda ka taɓa yi mini aiki a kanta ce shekarun baya, kawai ka yi wani abu a kai"
"To ya aka yi ƙasa ba ta nuna mini ita ce ba? Ban ga taurarinta sun fito a cikin nasa ba, amma duk da haka babu damuwa, ta jiramu a waje, zan bata abun da za ta yi"
Samha ta jinjina masa kai, ta yi godiya, sannan ta tashi ta fita ta bar su Mummy.
Hajiya Lubabatu ta ce "Malam, ya ake ciki ne? Haryanzu galadima yana nan a raye, ga lokaci yana ƙurewa, bana son wani dalili da zai gifta, da Jabir zai gaza mallakar zunzurutun dukiyar nan da sarauta".
"Allah ne mai kashewa da rayawa ba ni ba, dole ki cigaba da jira, ke kuma ya aka yi?" Yayi maganar yana kallon Mummy.
"Malam, kamar aikin da yake tsakanin yaran nan ya fara sanyi, kamar mahamud ya sassauta ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan, sannan malam yadda yake yinƙurin yin auren nan, a sake damalmala lamarinsa, bana ƙaunar ganin wani cigaba a tare da yaran nan".
Malamin ya ce "Ina iya ɓata aiki ne, ba sauya ƙaddarar bawa ba, zan yi abun da ya dace a kai, ku tafi ta kudu, ku ajiye abun sadaka a mararraba ta uku, sannan shekara ta kusa, za a shayar da ƴar baƙa ta arewa da jini, sai dai ta daina samun jinin da take sha, dan haka za ayi mata sadaukarwa da wani abun, na sallameku".
Da haka suka fita, Samha take ce musu bai faɗa mata mai za ta bashi na aiki ba, suka ce kar ta damu, suka yi abun da ya ce sannan suka tafi gida.
***
Abubakar ya dawo, sun kuma tattauna sosai a tsakaninsu, a kan auren rumaisa, suka yanke shawarar a sake jarraba sayar da gonarsu, domin a samu abun yi mata kayan ɗaki.
Ɓangaren rumaisa kuwa, sai koke-koke take a kan ita fa ba ta so, gashi har fargabar kwanciya bacci take yi, saboda munanan mafarkan da take yi, ta je ta samu malaminsu a islamiyya ta ce ya bata Addu'a, tana yawan yin mugun mafarki ya bata shawara da cewa "A duk lokacin da ki ka yi mummunan mafarki, ki nemi tsari sannan kar ki gayawa kowa, ki din ga kwanciya da alwala, sannan ki kwanta da ɓangaren dama, ya zamana kina Adduoi na safe da na maraice, sannan ki karanta na kwanciya barci, idan razana ki ake yi a mafarkin, ki daina tsorata, ba abun da yake samun bawa sai da iznin Ubangiji, kin riga kin yi azkar kin nemi tsari, babu abun da kuma zai cutar da ke".
Rumaisata riƙe maganar malaminsu, ta dage da addu'a da alwala, shine ta ɗan samu rangwame.
Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, tun da su ammi suka tafi, sai ana gobe kai kuɗi suka yi waya da mama, ranar juma'a bayan an saukko daga Masallacin juma'a, mai girma turaki da wasu manya a masarautar kano, suka kai kuɗin auren rumaisa gidan ƙanin mahaifinsu, naira dubu ɗari biyar, suka saka wata ɗaya rak.
Ƙanin mahaifin rumaisa ya nemi su ƙara musu lokaci, saboda shirin aure, ba abu ne mai sauƙi ba, amma suka ce basa buƙatar komai, rumaisa kawai suke son a kai musu, dan haka wata ɗaya suka saka.
Ayshercool