Showing 207001 words to 210000 words out of 224014 words
da yake huci ta ce "Ina fatan dai ba abun da ya sameka ko?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
Mama ta ce "Duk saboda wannan jairar yarinyar ne, da ba zata bari a zauna lafiya ba? Ina ke ina faɗa da gagararren ɗan daba saboda ɗorawa kai bala'i" Mama ta yi maganar tana ƙoƙarin kai mata duka, amma mai sunan baba ya tare ya ce "Ki ƙyaleta please, baki ga ta ji rauni a goshi ba, ki yi haƙuri"
Mai sunan baba ya sakata a gaba, ya kai ta chemist, aka duba goshin, Allah ya taimaketa babu ɗinki, suka dawo gida.
Mama ta kai ƙarshen ƙulewa da rumaisa yau, ta din ga yi wa ƴan mazan faɗa a kan biye mata wurin tare mata faɗa.
Kasancewar maƙwabcin su rumaisa malam shamsu, yana cikin ƴan kwamitin unguwa, shi ne mataimakin ƴan ƙato da gora, yana dawowa aka sanar masa da abun da ya faru a unguwar, nan da ya ji ya samu damar rama wulaƙancin da rumaisa da yayyenta suka yi masa, kai tsaye ya je ya sanar da ƴan sanda abun da ya faru.
Mama har ta bar sallahun a rufe gida, ƴan sanda suka yi sallama, suka ce sun zo tafiya da Aliyu.
Duk yadda aka so sasanta lamarin, abu ya gagara, ga Abubakar ya koma makaranta, Mai sunan baba da Usman suka bi bayansu, amma har wurin sha ɗayan dare, ƴan sanda suka ƙi bayar da Aliyu, ƙarshe ma suka sanar da su cewa sashin kula da manyan laifuka na bamfai zasu turasu, tun da Aliyu ya yi iƙrarin kisan kai.
Haka mai sunan baba suka koma gida, jiki a sanyaye, mama ta rasa in da zata saka kanta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, tare da ɗora zargin komai a kan rumaisa.
Adam kuwa bayan ya kammala cin abinci, ya tashi ya yi wa ammi sallama, ammi ta ce "Yauwwa, na ce ba" Adam ya ɗan tsaya yana kallon ammi.
"Dan Allah gobe in Allah ya kaimu, tun da da wuri zaka fita, kuma ka ce zaka je gidan gona, dama unguwar su matarka ne, zan baka saƙo ka kai wa rumaisa"
Adam ya kalli Ammi ya ce "Matata kuma? Kuma ni zan kai ssƙon?"
"Ban isa ba kenan?"
Ya ce "A'a tare da sunkuyar da kai"
"A yanzu kana da wata matar da ta wuce rumaisa ne? Zaka kai mata saƙo, kallonka kawai nake yi, har na je wurin turaki na dawo ba ka tambayi yaya muka yi ba, kuma ya zama dole ka din ga zuwa wurinta, saboda ta saki jiki da kai, kuma ka daina yi mata wannan muzuran"
Adam ya jinjina kai yana wasa da yastun hannunsa.
"Je ka, da safe in Allah ya kaimu kan ka wuce, ka biyo"
Bai ce komai ba ya fice.
Ayshercool.
Chat me on what's app, to subscribes yours
08081012143
*PAID BOOK NE, ₦500 NE VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA, 08081012143*
Gaba ɗaya ji yake duk wani girma da mutuncinsa sun zube, kamar shi ace wai zai je wurin wata ƴar yayyiyar yarinya yayi zance da ita, wai zai aureta, ko aurensa na fari aisha ta kammala deegree ya aureta, wannan shi ba ya tunanin ko primary ma ta gama.
Mama kuwa kwana ta yi ba barci, sai addu'a kawai da take yi, ji take tamkar ta rufe rumaisan da duka, dan bayan gama ƴan koke-kokenta tuntsirewa ta yi ta hau bacci.
Mama ta kalleta ta girgiza kai ta ce "Allah ya shiryeki, ya ganar da ke"
Da asubar fari, bayan rumaisa ta idar salla, ta tafi ɗakin su mai sunan baba ta yi sallama, suka amsa mata.
Ta leƙa ta ce "Yaya usy jiya kun dawo da yaya aliyun?"
Abdallah ya ce "Wuce ki bawa mutane wuri, duk ba ke ki ka janyo ba, karfa kawai"
Mai sunan baba ya kalli Abdallah ya ce "Kar ka kuma gaya mata haka, bai dawo ba a can ya kwana, duk saboda ke, gaba idan ki ka sake, ke zan kai musu in karɓo shi, dan mun fi son sa a kan ki, mara kai kawai"
Sumi-sumi ta juyo za ta fito, ta fuskanci kowa haushinta yake ji yau.
Usman ya ce "Wallahi yau da na ga malam shamsun nan a masallacin asuba, ji na yi kamar na ɗaga shi na wurga shi cikin kwalbati, shi ne babban munafukin da ya je ya kai wa ƴan sanda"
Mai sunan baba ya ce "Ba ruwanka da shi, ku bari mu kashe wannan case ɗin tukuna".
Abdallah ya ce "Ni malam lawan mai shago na kusa kifawa mari, ya biyo ni wai rumaisa ta yi masa asarar ƙwai cret huɗu, wai in zo in biya, na ce masa sai dai mu yi kokowa ya ɗiba, gaba ɗaya mutane fuska biyu ce da su".
Rumaisa da take tsaye tana jin su da sauri ta ce "Wallahi ko kret ɗaya bai yi ba, bai fi guda shida ba fa"
"Au laɓe ki ke yi mana ko?" Abdallah ya faɗa yana nemo abun duka.
Da gudu ta shige ɗakin mama, sai dai irin kallon da maman ta yi mata, ya sanya ta rasa in da zata saka ranta.
Haka ta tsuguna ta takure, da duku-dukun mama ta shiga kitchen, ta girka abinci, gari na yin haske, ta ce lallai mai sunan baba ya taso su tafi station ɗin.
Mai sunan baba ya ce "Mama, idan kin je wurin nan babu abun da zaki iya a kai, ki bari zan je ni da Usman"
Mama ta ce "Ni dai ka ƙyaleni na je na ga a yaya ya kwana?"
"Lafiya ƙalau ya kwana, kuma in sha Allah zamu dawo miki da shi, ki yi haƙuri" da ƙyar mama ta yadda, ta basu abincin suka tafi.
Rumaisa ta ce ita ba zata tafi makaranta ba, sai yaya Aliyu ya dawo.
Mama ta ce "Aikuwa ba ki isa ba, sai kin shirya kin tafi, wataƙila kan ki dawo na huce, dan da na kalleki haushi nake ji, haka kurum saboda ke kin saka an kulle mini ɗa, mara jin magana" shiru rumaisa ta yi tana kallon mama, kenan yanzu mama ta daina son ta?.
Jiki a sanyaye ta shirya, mama ta hanata kuɗin makaranta, ba babban abun da ya sake ƙular da mama, irin yadda rumaisan ta zauna ta naɗi abincinta, kamar abun bai dameta ba sosai.
Haka ta tafi makaranta, tana tunani kala-kala, amma har ga Allah abun ya dameta.
Kamar yadda ammi ta buƙata, da safe Adam ya je gidan, a lokacin su iman duk sun tafi makaranta.
Ya ɗau sabir yana yi masa wasa, sai dai ƙememe yaron nan yaƙi dariya, sai bin sa da yake da kallo.
Ammi ta fito suka gaisa, ta ce "Yanzu wurin aikin zaka tafi?"
"Eh, na biyo na karɓi saƙon ne".
Ammi ta ce "To, tun da baka tambayeni ba, ni bari na gaya maka yadda muka yi da turaki".
Ya sunkuyar da kai yana wasa da hannun sabir.
"Mun tattauna da shi, ya ce mini in bari ya dawo daga umara, zai yi magana da su wambai, dan na san akwai ƙalubale, tun da rumaisa ba jinin sarauta ba ce, ko ƴar wani sananne ba, dan haka zai yi muku Addu'a a can, da ya dawo aka daidaita kuɗin aure za'a kai, bayan salla idan Allah ya kaimu za ayi"
"To, Allah ya wuce mana gaba".
"Amin, wai da ce mini yayi, Jamil ya ce ko za'a maye gurbin Fulani da samha, ni dai ban ce komai ba na shigar da maganar rumaisa, dan ita ta fi kwanta mini"
Adam har mamakin ƙaunar da Ammi take yi wa rumaisa yake yi, tabbas da so samu ne, Samha ta maye gurbin aisha, dan ita ta isa mace da hankalinta da iliminta, kuma Samha ta daɗe tana son shi, ya san hakan, amma ammi ta dage a kan wannan ƴar yayyiyar Yarinyar.
Ya numfasa ya ce "Allah ya kyauta"
Ammi ta miƙa masa leda ta ce "Gashi nan, sabuwar jakar makaranta ce, da litattafai da turare, ka kai mata ka ce ina gaisheta"
Adam ba yadda ya iya, ya karɓa ya amsa da to.
Ya fita riƙe da ledar kayan a hannunsa, ya san zuwansa wurin Yarinyar nan, ba abun da zai ƙara masa sai raini.
A harabar gidan ya tarar da Mahmud, tun da ya dawo yana ganin shige da ficen motocinsa, amma basu ta ɓa haɗuwa ba sai yau, yana tsaye a wurin parking space ɗin Adam, kusa da in da zai ɗau motarsa.
Adam bai kula shi ba, shi ma bai kula shi ba, ya je ya buɗe motarsa ya kunna, ya ɗan jima a ciki, amma ya ga Mahmud ba shi da niyyar matsawa, ya din ga danna horn, amma Mahmud ya yi burus, ba tare da wani ɓata lokaci ba Adam ya bawa motar wuta, yayi reverse, ai kuwa ya buge Mahmud, ko kaɗan Mahmud bai kawo Adam zai yi masa haka ba, kan ya ankara ya ga Adam yana ƙoƙarin bi ta kansa, ba shiri ya mirgina, Adam ya ja motar da gudu ya bar gidan.
Ma'aikatan gidan suka yo kan Mahmud suna yi masa sannu, suna ƙoƙarin ɗaga shi, sai dai ciki gwasalewa ya nuna musu shi zai iya tashi, sai dai abu kamar wasa, da ya miƙe ɗin ƙafa taƙi takuwa.
***
Rumaisa tana hanya tana addu'a, Allah ya sanya yaya Aliyu ya dawo, Allah ya sa komai ya wuce, sai dai ko da ta iso gida, ta tarar da Usman da mai sunan baba amma babu Aliyu. Cikin damuwa ta ce "Yaya usy ina yaya Aliyun yake?"
"Ke, case ɗin nan fa maƙabcinmu malam shamsu, ya yi uwa yayi makarɓiya yana ta kambama abun, gaba ɗaya ma sun ƙi saurarmu a station ɗin, wai sai DPO ya zo, DPO na zaci wanda ku ka yi case ɗin nan ne kwanaki, ashe an canza wani, sun kafi wai sai an je state cid tun da aka yi iƙrarin kisan kai".
Rumaisa ta ce "Na shiga uku, ba fa yaya Aliyu ne ya ce zai kashe shi ba, shi ne ya ce zai kashe shi".
"Koma menene ba ke ki ka janyo ba rumaisa, duk abun da mutum zai gaya miki sai dai ya shiga ta kunnen dama ya fita ta hagu, saboda wautarki kin jefa ɗan uwanki a wahala"
Usman ya ce "Dan Allah mama ki daina faɗar haka, ƙaddara ce"
A fisace mama ta ce "Rufe mini baki, ko na make ka, ai duk gidan nan babu mai koya mata rashin ji irin ka"
"Allah ya baki haƙuri, ba ri mu yi salla mu koma".
Adam kuwa ko kaɗan bai ji babu daɗi ba abun da ya yi wa Mahmud, dan a lokacin nan yadda ya hasala, da ya samu dama sai ya taka shi da mota uban kowa ya huta, ya sauke masa wannan girman kan da rashin mutuncin da yake ji da shi.
A haka yake wurin aiki, ya gama abun da yake yi ya fito, yana da niyyar zuwa gidan gona, sai dai dole ya je ya kai wannan saƙon kan mama ta ɓata ranta.
Mahmud kuwa ƙarshe, sai ka shi sashin Mummy aka yi, a rikice take tambayarsu maiya same shi, suka gaya mata Adam ne ya buge shi da mota.
Nan da nan ta hau ta fara bala'i "Wannan wane irin wulaƙanci ne, anya Adam bai fara shaye-shaye ba? Ko dai haryanzu haukar ce a kansa, tayaya zai taka ka da mota? Wallahi ba zan lamunta ba sai na ɗau mataki"
Mahmud ya ɗan cije lips ɗin sa ya ce "Ki rabu da shi zan rama ne, yanzu ni dai ƙafata zafi take yi ki yi wani abu a kai"
"Wallahi ba zan ƙyale ba, Fauziyya ɗauko key mu tafi asibiti kawai, Allah ya sa ba wani abun ne ya samu ƙafar ba"
"Mummy, dan Allah ki rabu da shi, am just testing his anger, ashe yana nan a yadda yake bai canza ba" yayi maganar cikin zolayar Mummy.
Cikin fushi ta ce "Ka rufe mini baki, this is an serious issue, ba zan bari ba" ganin yadda ta ɗau zafi ya sanya shi yin shiru yana kallon ƙafarsa.
A ƙofar gidan su rumaisa, Adam ne a tsaye, yake kiran wayar Aliyu, amma shiru bai ɗauka ba, wayarma a rufe take, ya kira har ya gaji, ya aika yaro ya ce ace ana sallama.
Usman ne ya fito, domin duba waye, ya tarar da Adam a tsaye, ya ƙarasa yana wani basarwa, suka gaisa sama-sama.
Adam ya ce "Aliyu nake nema, na kira wayarsa ba ta shiga"
Usman ya kalleshi, ya lura ta su ta zo ɗaya da Aliyu sosai.
Ya ce "Ya ɗan haɗu da tsautsayi ne" ya bashi amsa a taƙaice.
"Wane irin tsautsayi kuma?"
"Eh waccan yarinyar ce ta tsokano ɗan daba, ya je tare mata, kuma dama ta yi rigima da maƙwabta, shi ne mai gidan ya saka aka kama su, tun jiya muke zuwa police station, an ƙi sakinsa, yanzu ma komawa zamu yi"
Mamaki ne ya sha kan Adam, duk rumaisan ita kaɗai ta janyo wannan tarzomar.
Cikin mamaki ya ce "Wai duk ita wannan Yarinyar ce ta yi faɗa da ɗan daban?"
Usman yayi wani irin murmushi ya ce "Wannan ta wuce tunaninka, ka san ƙanwar maza ce, bamu raineta da tsoro ba"
Adam har cikin ransa ya ji babu daɗi kama Aliyu da aka yi, ya ji da rumaisan aka kama ita da ta janyo abun.
Ya ce "Ko zan iya magana da maman?"
Usman ya ce "Ok, bari na yi mata magana".
Bayan an yi wa Adam iso ya shiga gidan, ya tarar da rumaisa a takure a falon mama, sai rarraba ido take yi, suka gaisa da mama ya sanar mata da Usman ya gaya masa abun da ya faru"
Mama ta ce "To, yakamata ka sake tunani a kan auren nan naku, ku gidan sarauta ba kwa son shirme, rumaisa kuma Allahn da yayi ta ba ta ji ko kaɗan, faɗa da maƙwabta faɗa wai har da ɗan daba, yaron da har kisan kai yake yi"
Adam ya kalli in da rumaisa take, ta haɗe rai saboda yadda mama ke kwance mata zani a kasuwa, ya ce "Me ya haɗaki da ƴan daba, har aka kama Aliyu?"
Shiru ta yi tana wulƙita ido, mama ta ce "Zaki yi bayani ko sai na mareki?"
Ƙasa-ƙasa da murya ta faɗi abun da ya faru, ta wani fannin tana da gaskiya, a kan me zai aiketa sayen sigari.
Adam ya ce "Ba damuwa mama, bari mu je a fito da shi, ba wani state CID, wani station ɗin ne?"
Usman ya ce "Dama yanzu zamu koma da mai sunan baba sai mu tafi gaba ɗaya " wani mugun kallo da mai sunan baba ya yi wa Usman ya sanya yayi shiru, Sarai Adam ya ganshi, dan haka ya ce "Bari mu je da wuri, kuma dole ita ma a tafi da ita".
Mama ta ce "Idan ma sun ƙi yarda, ku basu ita ku dawo mini da Aliyu" sanin ba ta da gaskiya ya sanya ta sunkuyar da kai ta yi shiru.
Mama ta so bin su, amma kasancewar yanzu magana ake ta siriki, mama ba zata iya shiga motar Adam ba.
Bayan tafiyarsu mai sunan baba ya ce "Amma ba kya ganin yawan shigarsu cikin al'amuranmu da yi mana alfarama, ba zai saka nan gaba su cigaba da kawo buƙatunsu ba, kuma ba yadda muka iya sai mun bi ba?"
Mama ta ce "Babana ka san na fi kowa taka tsantsan da gudun duniya, bana jin hakan, shi ya sanya na amince"
Ya ɗan rausayar da kai ya ce "Shikenan, bari na bi su a napep"
Suna tafe Adam yana kallon rumaisa ta mudubi, sai wani gyatsine baki take yi, tana harare-harare kamar mai shirin iskokai.
Cikin station ɗin suka shiga, aka yi musu iso wurin DPO, cikin sa'a suka tarar da malam shamsu a station ɗin yana ta cigaba da zigar kai su Aliyu CID.
Adam ya ce "Case ɗin ƙanina na zo mu yi magana a kai, na san shi ba mai laifi ba ne"
Malam shamsu ya ce "Ta ina, yana mana iƙirarin kisan kai a cikin unguwa"
Usman ya ce "Wai kai malam shamsu meye yake damunka, meye ribarka idan an rufe Aliyu ne?"
Mai sunan baba ne yayi sallama ya shiga, suka amsa masa ya nemi wuri ya zauna.
Adam bai ko kalleshi ba ya cigaba da magana ya ce "Da ku ka caje Aliyu kun same shi da makami?" DPO ya ce "A'a"
"Good, ɗayan fa, abokin rigimar ta sa"
"Eh, mun kama shi da wuƙaƙe da tabar wiwi"
Suna cikin maganar aka shigo da su Aliyu.
DPO ya kalli rumaisa ya ce"Ni mamakina ma da wai duk a kan wannan Yarinyar ce ta haɗa faɗan, ke meye ya haɗaku?"
Ta cunkusa baki ta ce "Cewa yayi na sayo masa sigari, kuma ni ba ƴar iska ba ce ba da zan taɓa sigari ina ƴa ma ce mai mutunci "
Adam a ransa ya ce "Ko wa ya tambayi jinsinta kuma oho'
Malam shamsu ya kada baki ya ce "Ƴar iska kum ta nawa, zance da ya cika unguwa"
Zabura rumaisa ta yi ta ce "Yaya usy ka ji ko? Yanzu idan na yi magana ace ba na jin magana, da kunnenka ka ji yana ce mini ƴar iska, ni fa bar ƴar iska ba ce ba, bana wasan banza da maza, meyasa ake ce mini ƴar iska?" Ta yi maganar hawaye ya wanke mata fuska.
Malam shamsu ya ce "Ke da aka ce an yi garkuwa da ke, ki ka dawo da ɗa, ai ba abun mamaki bane ba, tun da kowa ya san a unguwar nan ba ji ki ke yi b.... Mai sunan baba ya daki tebur da ƙarfi ya ce "Ya isheka malam"
DPO ya ce "A gaban nawa, da rashin mutunci da rashin sanin darajar doka".
Malam shamsu ya ce "Tuba muke Yallaɓai".
Usman yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Uban waye ya saka ki yi kuka a gabnsa, salon ya rainaki, idan ya kuma gaya miki ki ce kin yi ɗin"
Adam ya numfasa ya ciro ID card ɗin sa ya bawa DPO ya ce "Ina son a bi tsarin doka, a bani Aliyu sannan a tura mai laifi gaba"
Ware ido DPO yayi ya ce "Ranka ya daɗe dama kai ne? Ai da ko waya ka yi ya wadatar ba wani abu in sha Allah, case ya mutu daga nan"
"And, shi wannan da yayi iƙirarin kashe Aliyu da wannan yarinyar, a kai mini shi state CID, sannan a kamo mini yaransa ma, zan bincika wanda ya saka aka sake shi ana tuhumarsa da kisan kai"
Dpo ya ce "In sha Allah ranka ya daɗe" baki buɗe malam shamsu ya