Showing 135001 words to 138000 words out of 224014 words
asibiti za a canza mata.
Suka shiga tambayarsa dalili, amma ya ce likita ne ya bada shawarar hakan.
Daf da magariba Bashir ya isa gidansu takawa, bayan yayi ta kiran lambarsa amma yaƙi ɗagawa.
A harabar gidan suka yi kiciɓis, Bashir ya tattara nutsuwartsa ya ce "Allah ya baka yawan rai, ina ta kiran lambarka ka ƙi ɗagawa".
Ƙoƙarin tureshi Adam yake ya wuce, amma Bashir yaƙi matsawa ya ce "Tuba nake, amma ka tsaya ka saurareni, wallahi babban uzuri ne ya sameni, na gaya maka yarinya na tsinta, ta kuɓuto daga hannun 'yan bindiga"
A fusace Adam ya ce "Ka je ka yi abun da kake so mana, ai ban yi maka magana ba, ambulance sarkin taimako ka je ka yi ta yi mana, tun da ni tawa buƙatar ba buƙata bace".
Bashir ya ce "Dan Allah Adam ka saurareni ka ji"
"Ba zan ji ba, bana son ji" yayi maganar a fusace zai wuce.
"What if yarinyar tana da alaƙa da aikin da ka bani? Ka rage zafin zuciya ka dinga cin ribar rayuwa, ka zo mu je zuwanka ka ganta yana da muhimmanci, za a iya samun muhimman bayanai a tare da ita, yanzu haka Ammi na asibitin". Cak Adam ya tsaya yana kallon Bashir.
"Ka zo mu je, ina tabattar maka da cewa, yarinyar nan za ta iya zama ita ce makarin abun da muke nema, ka yi haƙuri ka yadda mu je".
"Amma meya kawo ammi cikin zancen nan".
"Dole ce, dole ce ta shigo Ammi cikin lamarin nan, kuma har zuwa yaushe zamu cigaba da wannan ɓoye-ɓoyen? Ka zo mu je" Adam bai kuma cewa komai ba, ya bi Bashir motarsa.
Wani katafaren asibitin kuɗi Bashir ya sanya aka mayar da rumaisa, sai dai ba ta iya taka ƙafafuwanta, saboda raunukan da suke jiki, mama tana yi mata wanka tana kuka, haƙoranta sun yi yellow, gashi nan a cukurkuɗe, fatar rumaisa duk cizon ƙwari, haka zalika cikin kayanta duk ƙwari, Mama ta sanya almakashi ta ragewa rumaisa gashinta, saboda tana da cukurkuɗaɗɗen gashi mai tsayi.
Mama ta tsorata da ta ga uban gwal ɗin da yake cikin ɗan kwalin da yake ƙugun rumaisa, ko da mama ta matsa mata da tambaya, sai ta hau kuka.
Abinci ma da ƙyar ta ci kaɗan, ta kwanta ta cigaba da aikin bacci.
A hankali take motsawa, tana buɗe idonta da kaɗan-kaɗan, tana tsoron kar ta buɗe idonta ta ganta a duhun dajin nan, ko wurin su sule.
Ganinta ta yi a wani wuri na daban, dan har aka canza mata Asibiti mama tayi mata wanka, ba a hayyacinta take ba, ko ina farin tiles da farin ƙwai, ga sanyin ac da yake ratsata, a hankali ta fara shaƙar wani irin daddaɗan ƙamshin turare, ta din ga kallon mutanen ɗakin ɗaya bayan ɗaya, wata babbar mace ta gani a zaune tayi mata kama da wanda ta sani.
A hankali ta ga su Aliyu da Usman a wurin, ga wasu dogarai masu kaya kalar na bayi da mama ta ce mata.
Gabanta ne ya faɗi da ta yi tozali da Adam a kan gwiwoyinsa, rungume da jariri hawaye na zuba daga idonsa.
Cikin ihu ta ce "Wayyo Allah mama, kina ganinsa ko ni kaɗai nake ganinsa?"
Mama ta ce "Waye?"
"Wannan mugun mutumin" tayi maganar tana nuna Adam.
A rikice mama ta ce "Me yayi miki?"
Bashir ya ce "Rumaisa, ki kwantar da hankalinki, ba mugu bane ba, kwatancen da matar nan ta baki, shi na yi tracking, mutanen da ta gaya miki gidan sirikanta ne kuma iyayenta, Adam abokina kuma shi ne baban jaririnki, shi ne mijinta".
(Danƙari!🥺)
Ayshercool.
₦500 ne via 0009450228
Aishs Adam Jaiz bank
Sai a turo shaidar biya ta 08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
*ƘANWAR ₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*
Kamar sokuwa haka ruma ta bi bashir da kallo, daga bisani ta ja wani uban tsaki ta ce "Dan Allah ka daina raina mini hankali, wai komai nawa sai wannan mutumin ya shigo ciki, to wallahi ba shi bane ba, ɗana ne ba shi ne babansa ba". Ko cikin gushewar hankali takawa ba zai manta wannan muryar me shegen karaɗi da tsiwar tsiya ba. Shi kansa mamaki yake yadda aka yi rumaisa take shigowa cikin rayuwarsa a bazata. Ya ɗaga jajayen idanunsa ya na ƙare mata kallo.
Usman ya ce "Rumaisa, kin ga ki nutsu kin ji, shi a ina ki ka san shi?"
Ta kalli Bashir, sannan ta ɗan kalli takawa, ta girgiza kai ta ce "Ni ban san shi ba, ku karɓo ɗana ku bani, ba shine babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba".
Bashir shima ya ƙarasa gaban rumaisa ya ce "Rumaisa, ba cewa ki ka yi tace miki ita 'yar turakin kano ba ce? Ta ce miki giwar Galadima ce sirikarta ba, to ai ga giwar Galadima nan, Adam kuma ɗanta ne" ruma ta yi shiru ta tafi tunanin abun da ya faru ita da Aisha.
Lokacin da ta kammala bawa Aisha labarin abun da ya faru a tsakaninta da Adam, ta din ga yi mata dariya ta ce "Kamar na san mutumin nan da kike bani labari".
Rumaisa ta ce "Taɓ, aikuwa idan ɗan uwanku ne sai dai ki yi haƙuri dan ba shi da mutunci, bama ki san shi ba anty aisha".
Aisha ta kalli ruma ta ce "Ɗan gidan marigayi Galadiman Kano ki ka ce ko?"
"Oho masa, amma dai kamsr haka aka ce"
"Amma da ƙarfin hali kike ruma, dan ƙarfin hali babban mutum ki yi masa wannan rashin kunyar?"
Ruma ta taɓe baki ta ce "Ai ni Allah kaɗai nake tsoro"
Aisha ta yi murmushi ta ce "To ki yafe masa mana my baby rumaisa" ruma ta daki ƙasa ta ce "Ai ko shine zai zo gabana ya ce na yafe masa ba zan yafe masa ba, kin ga rashin muntucin da yayi mini, har da ce mini 'yar talakawa, yanzu da ciki ya fito mini da ya taɓa mini nono fa, ina zan saka kaina?"
Tayi dariya ta ce "Ai bai fito ɗin ba, kuma gaskiya kar ki yi masa sharri dan kin tsane shi, you are still a baby, ina wani nono a nan banda sharrinki ruma? Ko kwatan nawa ba su kai ba fa, ko ganinsu ba ayi"
Rumaisa ta ce "Wallahi sun fara fitowa, mama ta ce duk wanda ya taɓa ciki zai fito mini, kuma korata za su yi daga gidan su, yanzu da ya sa an koreni fa, ni fa bana son ma su fito, idan ba haka ba mama zata hanani yawo ba riga, yanzu ma hanani take yi"
Aisha ta yi dariya ta ce. "gaskiya ki daina zaginsa tun da dai ba a korekin ba, kin yi masa sharri, ina wani abun taɓawa a nan" tayi maganar tana sake tuntsirewa ruma da dariya.
Ruma ta ce "Wallahi ya taɓa, kuma idan Allah ya sa na bar nan idona idonsa zai gane bashi da wayo, ana i gobe zan zo katsina, yayi mini wanka da kwata a tsakiyar layi, wai har da cewa na yi masa sharri da nace ya taɓani, wai zuwa yayi ya duba ya ga ko akwai wani abu a ƙirjina ki ji ɗan iska fa"
Aisha ta dafe ƙirji ta ce "Wayyo zuciyata, haba baby rumaisa sunan mijina adam, kar ki sa kishina ya tashi. Amma ni nawa Adam ɗin shima yana da zafin zuciya, baya son raini ga miskilanci, amma idan ki ka fahimce shi, mutumin kirki ne, mai son kulawaga iya soyayya, sai dai...." ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce "Ruma zaki auri Adam?"
Ruma ta waro ido ta ce "wane Adam ɗin? Ni da ban yi tsawo na girma ba za ayi mini aure?".
"Adam da kuke faɗa, ki yafe masa ko dan albarkacin yana da sunan mijina"
Ruma ta turɓuna fuska ta ce "Ai wallahi ko yayanki ne ba zan yafe masa ba, da in auri Wannan gara na mutu ba aure, kuma ni miji kyakkyawa nake so, kuma mai kuɗi"
"In dai kuɗi ne akwai su ruma, kuma ai kyakykyawa ne"
Rumaisa ta dubeta ta ce "Ba fa mijinki ba, wannan da muke faɗa nake gaya miki, mai suffar mugwaye da wata banzar motarsa in sha Allah sai an sace motar ma".
"In an saceta ma zai sai wata, kuma ya sai miki kema, banda faɗan rashin gaskiya ke fa ki ka fara zaginsa a social media, amma tsabar rigimarki kina ta zaginsa, kin ci sa'a da bai ɗaureki ba, ko ya sa a zaneki ba".
"Oho ni dai ban yafe ba"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "I love your confidence my dear, you can face the challenges. Jikina na bani wani abu game da ke, zaki iya ruma" tayi maganar tana jan kunatun rumaisa ta ce "Kamar haka mijina yake wasa da kumatuna".
"Anty Aisha, yake taɓaki? Ba a wasa da maza fa" ba ta bawa ruma amsa ba, sai dariya da take yi mata, tana fatan Allah ya tabbatar da abun da take ji game da ruma.
Ranar da zata rasu bayan ta haihu, ta riƙe hannun rumaisa ta ce "Baby rumaisa, idan Allah ya sa kin kuɓuta, ni 'yar gidan turakin kano ce, amma kar a nemi mahaifina kai tsaye a nemi sirikata, idan ba zaki iya riƙe jaririn nan ba, ki danƙa mata shi, Hajiya Binta giwar Galadima, uwar gidan galadiman kano, sirikata ce ita zaki danƙawa jaririn nan, ɗan ta shine mijina" a lokacin gaba ɗaya ruma ta manta da wani adam balle ta kawo shi a lissafi da aisha ta yi zancen galadima.
Ko da ruma ta zo nan a tunaninta sai ta tambayi kanta 'Kenan da gaske shi ne mijinta?' a zahiri kuwa ta fashe da kuka ta ce "Wallahi ba shi ne babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba" a bata iya tafiya ta fara ƙoƙarin dirowa daga kan gadon tana miƙa hannu ta ce "Ni ku bani jaririna, ba ɗansa bane ba, ni ba ta ce mini in bawa kowa ba, ku bani ɗana" mama tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.
Bashir ya miƙawa Adam hannu ya ce "Ka ga Adam, kawo yaron nan, gaba ɗaya a ruɗe take, kamar ba ta hayyacinta ne ma, kawo a bata shi kan muga yadda hali zai yi".
"Bashir ka haukace ne? Taya ka ke cewa in baka ɗana ka bawa wani?".
"Wallahi ba ɗansa bane ba, ku bani ɗana" ruma tayi maganar tana kuka.
Bashir ya karɓe yaron, ya miƙawa rumaisa, ta rungumeshi tana fashewa da kuka ta ce "Cewa ta yi idan ba zan iya riƙe shi ba, in bawa giwar Galadima ni ban santa ba ma, ban san a in da take ba, amma ni dai zan iya riƙe yarona, ai cewa ta yi ta bar mini shi har abada nice mamansa". Gaba daya ɗakin aka zubawa sarautar Allah ido.
Ammi da tun ɗazu take zaune kamar an shukata, ta kasa magana sai tasbihi kawai da take yi, ta tashi sannu a hankali, ta je kusa da rumaisa suka matsa mata ta zauna.
Ta dafa kafaɗar rumaisa idonta fal hawaye ta ce "'ya ta, nice giwar Galadiman kano mai rasuwa, Adam kuma ɗana ne, shine mahaifin wannan jaririn, kuma mijin Aisha".
Ruma ta girgiza kai ta ce "A'a wallahi ba shi bane ba, ni fa ba zan bawa kowa ba, ni ta ce ta barwa shi".
Ammi ta ce "To shikenan, na ji babu mai rabaki da yaronki, Ubangiji Allah ya baku lafiya gaba ɗaya, yanzu ki bayar da shi a mayar da shi sashen kula da yara".
Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ba zan bayar da shi ba, haka kurum ya bishi ya sace shi, da in bashi ɗana gara na koma wurin 'yan garkuwa da mutanen".
Huzaifa ya ce "To fa ana wata ga wata".
Ammi ta ce "To shikenan, rungume shi da kyau, kin ga bacci zai yi kema ki kwanta ki huta" a'a ba zan rufe idona in je ya gudu da shi ba.
Miƙewa Adam yayi jikinsa yana rawa, amma Ammi tayi masa wani irin kallo, tayi masa nuni da ya fita, yayi gaba ya tsaya ya waiwaya yana kallon rumaisa, da jaririnsa da yanzu ya shiga tunanin ina uwarsa? A wane hali kuma take ciki?".
Suna tafe a hanya babu wanda ya iya cewa komai, sai Bashir da yake yi wa Adam nasiha "Adam dole sai mun bi yarinyar nan a hankali har yanzu a rikice take, kuma a cikin firgici ba ƙaramar azaba ta sha kan ta fito da yaron nan ba, kaga Yarinya ce ƙarama ikon Allah ne ya fito da su, dan ita ma ba gama sanin ciwon kanta tayi ba, a sannu zamu bita mu ji a ina ita Aishar take, sai mu zo mu yi shiri".
Daga Ammi har takawa, babu wanda ya ce wani abu, kowa da abun da yake saƙawa a zuciyarsa, adam bai taɓa tunanin abubuwa su cukurkuɗe masa haka ba.
Suna zuwa gida ammi ta wuce part ɗinta, adam ma bai jira bashir ba, ya rufa mata baya.
A falo nusaiba ta tare ta tana tambayarta, "Ammi wai ina ki ka tafi haka, mun dawo daga islamiyya kawai muka tarar ba kya nan, kalli dare har ya fara yi fa" sai dai fuskar ammin ta nuna mata ba lafiya ba. Kan ta yi magana ta ga adam ya shigo ya bi bayan anmi, hakan ya sanya ta sha jinin jikinta.
A ɗaki ya tarar da ammi, ta ajiye carbin hannunta da mayafinta, hawaye tuni ya wanke mata fuska.
"Ammi dan Allah ki tsaya ki saurareni, kar ki yi mini haka".
Ta kalli Adam ta ce "In saurareke ka gaya mini me adam, yanzu a duniya akwai abun da zaka iya ɓoye mini? Ta ina zamu kalli duniya mu fara bayanin abun da ya faru? Ta yaya duniya za ta yadda da cewar jaririn nan ɗanka ne? Da yaya zaka yi wa turaki bayanin abun da ya samu 'yar sa, shikenan mun zama masu son kai kenan, idan maganar nan ta yaɗu ina zan saka kaina, ina ta ƙoƙarin toshe waccan kafar wannan ta ɓullo, adam kana me garin yaya haka ta faru ka ɓoye mini, ɗan da ba a san da cikinsa ba kawai mu ce ga ɗa meye shaidarmu ba ƙarya muke yi ba, ina ita Aishan?"
Adam da ya gama rikicewa ya ce "Dan Allah ammi ki fahimce ni, zan yi miki bayani bani da laifi, ba domin na ɓoye miki na yi duk abun da na yi ba"
Ammi ta katse shi ta hanyar cewa "To domin ka faranta mini ne? A tunaninka zan yi murna da hakan ne?".
Ya girgiza kai tare da goge hawaye ya ce "A duniya bani da makusancin da ya fiki, daga ni har aisha, kin san komai Ammi, kamar yadda muke ta neman magani tsawon shekaru huɗu, aka dace cikin jikinta ya zauna, bayan ɓari da take ta yi babu ƙaƙƙautawa a dalilina, cikin nan babu wanda ya san da shi,