Showing 78001 words to 81000 words out of 224014 words

Chapter 27 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1101

to wallahi ban yafe maka ba taɓa mini nono da ka yi, ina ta kaffa-kaffa da mutuncina, ina kula da kaina amma ka shaƙoni hannunka yana taɓa wurin, kuma bayan idan namijin da ba muharramin mutum ba ya taɓa shi ciki yake yi, to wallahi Allah ya isa ban yafe ba, kuma idan ciki ya sameni sai na kwaso maka yayyena mun zo har gidanku na gaya wa mamanka abin da ka yi mini, kuma na faɗa an saci kuɗin talakawa an je karatu ƙasar waje. Mu zuba mu gani daga maƙiyiyarka  RUMAISA MAHMUD ƘANƘARA ƊORAYI TUNGA ƘANWAR MAZA Kazo ka kasheni*

Zuruu takawa ya yi yana bin takardar da kallo, zuciyarsa na sake karkata ga ruma aljana ce. Ya maimaita sunanta *RUMAISA!* Tunani ya tafi yi, ko ya ga wani abu mai kama da nono a ƙirjinta ranar da aka kai masa ita.

Ta yaya aka yi ta gano gidan su har ta kawo wannan takarda? Rubutun nata cike yake da wauta da ƙuruciya.

"Zan ƙure miki gudu, zan gane idan ma ba mutum ba ce, da ni ki ke zancen" ya maimaita wasiƙar nan ya fi sau goma, babu abin da ya fi ƙular da shi irin wai ya taɓa mata nono, duk da bai riƙe cikakkiyar suffarta ba, amma shi ba ya tunanin akwai wani nono a jikinta.


Mama ta haɗawa ruma kayanta cif, da zummar gobe da sassafe za su tafi ita da yaya Aliyu, yau kuma Alhamis za ta je za su yi exam ta ƙarshe, haka kurum mama ta ji ba ta son tafiyar nan da ruma, amma ta bar hakan a alhini, kasancewar ruma ba ta taɓa nisa da ita na kwanaki ba, ga kuma rashin ji irin na ruman.

Uniform ɗin ruma sun sha guga, karin nan ya tsaya ɗoɗar Abdallah ne ya goge mata su, sai ƙamshi take, sai dai kamar kullum tana tafe tana zira hannu a aljihunta tana ciye-ciye.
Kamar a mafarki ruma ta ga an wanketa da ruwan kwatamin ruwan sama da aka yi ya kwanta, ƙazantar ruwan har fuskarta. A gigice ta tsaya cak, ta buɗe idonta, dan ta ga wani mara mutuncin ne ya ci mata zarafi haka?

A hankali ya sauke glass ɗin motar, suka yi ido huɗu da Rumaisa. Bakinta mutuwa yayi ta ma kasa magana gaba ɗaya.

Buɗe motar ya yi ya fito yana ƙare mata kallo.

"Ko zaki rama ne, ko da yake ba ki da abin ramawa ai, banbancin talaka da mai arziki kenan, na ga saƙonki, abin da ki ka ce na taɓa ɗin ni ban ganshi ba ranar, shi ne na biyoki yanzu in duba in gani ko akwai".

"Wai kai ɗan iska ne?" Tayi maganar ba tare da jin nauyinta ba, ga babban mutum kamar Takawa, saboda ya kaita bango.
Maganar ta dake shi, amma ya ce "Eh shi ne, yayyen naki maza da ki ke taƙama da su, sai na kamasu na rufe, kuma na rushe gidan na ku, na ga ta tsiya".

Karo na farko da ruma ta tsaya aka sakata kuka, hawaye ya wanke mata fuska.

"Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai taƙamarka kuɗi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuɗin naka da sarautar ta ka sai ka durƙusa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka" tayi maganar har da dukan ƙirjinta.

Girgiza kai ya yi, ya buɗe motarsa ya shiga, ta durƙusa ta ɗebi taɓon wurin ta fara watsa wa motarsa, ya taka reverse ya sake wanketa da taɓon wurin ya tafi.


(*ALHAMDILILLAH, TIRKA-TIRKA, YA KUKE GANIN ZATA KAYA A TSAKANIN RUMAISA DA TAKAWA? WACE IRIN LARURA CE DA TAKAWA, KUMA MEYE ALAƘARSA DA MAITA DA HAJIYA JAMILA TA FAƊA? YA ZATA KASANCE? WANE DEAL NE KHALIFA YA SAKA SAMHA? MEYE TARIHIN GIDAN SU TAKAWA, DA ASALIN GABARSA DA ƊAN UWANSA. ME ZAI FARU IDAN RUMA TA JE KATSINA??? WA RUMA ZATA AURA, SHIN ZA TA NUTSU KO KUWA? KAR AYI BABU KU, MAI BUƘATAR BOOK2 YA TUNTUƁENI TA LAMBAR WAYATA 08081012143 YA YI PAYMENT*


Ayshercool
Whats app only, ban da kira Please 🙏 0808101214




[8/22, 11:40 PM] Maman Aslam: *Na gamaku da zatin Allah kar wanda ya haɗa mini document ɗin littafina, mallakina ne, nike da alhakin amfani da abina yadda nake so, kar wanda ya juya mini abin ta kowacce siga, duk wanda ya haɗa mini document ɗin littafi ya fitar ban yafe masa ba! Kuma ina fatan Allah ya bi mini hakkina!*
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

*AYSHERCOOL*




Cikin damuwa Huzaifa ya dube shi ya ce "To me ka gani da ba ka yarda da shi ɗin ba?"

Cikin sanyin jiki Yasir ya ce "Wallahi kawai, ni mutanen cikin motar ne ba su yi mini ba"

Tsaki Huzaifa ya yi ya ce "Ka fiye matsala wallahi, dan Allah kar ma muje gida ka yi wannan zancen ka ɗaga mata hankali" Yasir bai kuma cewa komai ba, suka tafi gida, sai dai shikaɗai ya san abin da yake ji a jikinsa.

Ruma kuwa da suka tafi, sai kallon hanya take, tana murmushi dan tun da take, ba ta taɓa tafiya mai nisa ba, kuma ta yi sa'a a wurin taga take, dan haka take ta leƙe tana murmushi. Sai dai tun shigarsu, Aliyu ya lura da Mutanen da suke zaune a  gaban su, tun da suka hau motar mutanen suke waya da wani yare, wayar taƙi ci taƙi cinyewa, gashi ba mai iya fahimtar abin da suke faɗa a wayar.

Ruma kuwa sai surutu take wa Aliyu, kamar an jefeta a ka, ta ce wannan ta ce wancan. Aliyu dai bai tanka mata ba, sai Adduoi yake yi yana cigaba da kallon mutanen da tsarguwa da wayar da suke ta yi.

Ruma ta ɗauko wayar nan ta wurin Yasir, ta din ga ɗaukar kanta a hoto, ga wayar duk a ragargaje amma sai ɗagawa take tana hoto, har da hoton hanya ɗauka take, ta hau yin videon cikin motar tana ɗaukar mutane.

Ko da suka bar gari suka shiga jeji, sai wannan mutane suka ce wa direba ya sauka daga kan kwalta, ya tafi ta gefen titi kan burji, ba tare da musu ba kuwa direban ya bi umarninsu, kuma aka rasa wanda zai yi magana a kan hakan kowa yayi shiru.

"Wai ya na ga ana bin gefen titi, ga kwalta ɗoɗar a lailaye?" Ruma ta yi maganar har sai da kowa ya waiwayo yana kallonta. Ɗaya daga cikin mutanen ya yi murmushi amma ba wanda ya kulata.

"Ke uban wa ki ka ji yayi magana, sai ke haziƙa mazaruƙs, kar na sake jin bakinki ko na make ki" Aliyu yayi mata maganar cikin kashedi. Tura baki ta yi ta kawar da kanta gefe. Sai dai ba aje ko ina ba, ruma ta fara cewa Aliyu ita fa wannan zaman motar ya isheta.

"Wallahi idan baki kiyayeni ba sai na zane miki jikinki, ni na yi dana sanin tahowa da ke, babu wanda ake jin bakinsa sai ke? Ki rufe mini baki na gaya miki"

Kamar zata yi kuka ta ce "To ni fa na gaji ne, kuma yunwa nake ji, su wannan mutanen na gaba, ba tun da muka taho suke waya ba suke surutunsu, babu wanda ya damesu sai ni zaka ce na ishi mutane, ni wallahi yunwa nake ji ulcer ta zata tashi"

Riƙe kunnenta Aliyu ya yi ya ce "Yi mini shiru, a gidan uban wa ki ke da ulcer?"

"Cikina ne ya fara ciwo, yunwa nake ji"

"Wallahi zan zaneki idan baki shiru ba" haka ruma tayi shiru tana ƙoƙarin goge hawaye.

Sai da suka zo wani ƙaramin ƙauye, mutanen nan suka ce a tsaya, nan ma direban ya bi umarninsu ya tsaya, kowa yana son yin magana amma yana tsoro.

Aliyu ne ya fara fusata ya ce "Direba ya na ga an tsaya? Mu da muke sauri?"

Direban ya ce "Dan Allah ku yi haƙuri, wani saƙo za su karɓa mu wuce, yanzun nan ba daɗewa zamu yi ba in sha Allah"

Aliyu ya ce "Amma ai ba a haka, sai a nemi alfarmar na mota ba a tsaya kawai ba, wannan shiga hakki ne ai"

Sai da Aliyu ya yi magana, sannan sauran mutanen cikin motar suma suka fara ƙorafi a kan abin da aka yi.
Yayin da mutanen suka yi shiru ba su kula kowa ba.

Sun kai mintuna sha biyar, sannan wasu mutane suka ratso cikin dajin  a babura, mutanen suka sauka, suka karɓo wata uwar jaka, sannan suka dawo motar. Ɗaya daga cikin su ya dubi ruma cikin gurɓatacciyar hausar sa ya ce "Ke ki ka ce ki na jin yunwa ko?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.

Ya bata wata baƙar leda, ta karɓa ta ce "Na gode" Aliyu ya bi ruma da kallo dan ya rasa me yakamata yayi mata, kawai ba ta san mutum ba ya bata abu ta karɓe.

Gasashshiyar kaza ce a ciki, da ruwan roba, ta waro ido ta ce "Laa yaya kaza ce"

Ya harareta ya ce "Mayya, tun da baki taɓa cin kaza ba, idan ki ka ci sai na miki dukan tsiya"

Ta ɓata fuska ta ce "To in mayar masa, in ce ka hanani ci?" Banza yayi mata, ganin bai kulata ba ya sanya ta saka hannu ta hau cin abarta.

Da ta ci ta ƙoshi ta ɗaure sauran, ta kwanta a jikin Aliyu ta hau bacci.

****
Lafiya Adam ya sauka a Abuja, ya sauka a hotel ɗin da zai zauna na kwanaki biyu, dan ba ya son a san da zuwansa, shi ya sanya ya sauka a hotel, sai dai gabansa ya tsananta faɗuwa ya rasa dalili, ya kira Ammi ya kai sau uku, amma ta ce masa komai lafiya babu wata matsala.
Da yamma ya shirya ya ce bari ya ɗan fita ya je wurin abokansa, ko ya ɗan rage damuwar da ya rasa meya haddasa masa ita.
Sai dai yana fita harabar hotel ɗin, ya ji kansa ya wani sara, yayi ƙoƙarin basarwa  ya fita, amma ya kasa ƙafarsa ta yi masa nauyi ya ji yana nema ya faɗi, a hankali ya juya ya koma ɗakin da ya sauka, ya nemi wuri ya kwanta, saboda yadda yanayin jikinsa ya sauya tamkar zai fita hayyacinsa.

***
Ruma na farkawa daga baccin da ta yi, ta cewa Aliyu kashi take ji, shi kuma ya ce sai dai ta riƙe kayanta sai sun sauka, don ko zata yi hauka ba zai saka a tsaya ba, ba zai bari ma ta yi kashi a daji ba.
Ta din ga matse ƙafa tana nema ta yi masa kuka, har sai da ta fara janyo hankalin mutanen da ke motar.
"Wai kai ba ka ga yarinya bace ne? A tsaya ta yi mana" cewar ɗaya daga cikin mutanen da Aliyu ya kasa yarda da su.

Aliyu ya ce "A'a ba zata yi ba, idan mun je in da zamu ta yi" ya bawa mutumin amsa yana tsuke fuska. Ai bayan batun kashi ta cigaba da kuka, ita fa zai zubo, kuma ta gaji da zaman motar nan. Kan Aliyu ya yi magana motarsu ta yi faci, a tsakiyar jeji.

Fasinjoji suka din ga tsaki suna mita, masu ruwa suka ɗaura alwala kasancewar azahar ta yi, suka yi salla.

Wanda ya bawa ruma kaza ya kalli Aliyu ya ce  "Abokina tun da an tsaya gyara motar, ka shiga da ita ta samu wuri ta biya buƙata mana".

"Ɗan uwa ai na gaya maka ba abin da zata yi sai mun je, ƙyaleta ƙarya ma take ba wani kashi da zata yi"

Kowa yayi salla amma banda wannan mutanen, ana ta fafutukar sauya taya, tabbas da a gari motar nan ta lalace, da ba abin da zai hana Aliyu ya canza musu mota, saboda bai yadda da mutanen nan ba, shi ya san me ya gani, kuma yana tsoro yayi magana su cutar da su.
Aliyu yana salla, ruma ta tsaya tana ta ƙarewa dajin kallo tana ɗaukar hoto da akwalar wayarta kamar abin da ta fito yi kenan.

"Ɗan uwanmu ku ba kwa sallar ne?" Ruma tayi maganar tana zama ɗan nesa kaɗan da ɗaya daga cikin mutanen.

Ya kalleta ya ce "Sai mun je gida zamu yi"

"To wai Meyasa kuke ta sawa ana tsayawa a hanya ne? Duk ku ka ja muka daɗe fa"

Ya ce "Saƙo muka karɓa a wurin 'yan uwanmu"

Ruma ta jinjina kai ta ce "Sune suka baku kaza ku bani na ci?"

Ya waiwaya ya kalli wanda ya bawa ruma kazar ya ce "Tun da ki ka cewa yayanki yunwa ki ke ji, yayi wa 'yan uwanmu waya, ya ce su sayo kazar, dama zamu karɓi saƙo a wurinsu, shine ya karɓo miki ya baki"

Ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, kuna da kirki, to ku baku da gida, 'yan uwan na ku a daji suke ba gida ba?Na ga daga daji suka fito kuma babu gida a cikin daji ai"

"Eh, bamu da gida a daji muke rayuwarmu".

Cikin mamaki ta ce "Kai sai ka ce wasu kuraye, ku wane yarene to?"

Ya haɗe rai ya ce "Ke kin isheni fa, bar nan gurin"

Ruma ta ce "Yi haƙuri, dama ko a gida haka ake cewa na fiye tambaya, na daina, ina son sanin abubuwan da ban sani bane".

Bayan ta yi shiru, sai ta hau tattaɓa jakar hannunsa ta ce "Wai kai ba zaka ajiye kayan nan ka huta ba, ba ka jin nauyi"
Saurin janye jakar yayi yayi mata shiru.

"Na ji kamar wasu ƙarafa, kayan gwan-gwan ne a ciki? Su kuma kna zaka kai su"

A fusace ya ce "Ke tashi ki bar nan wurin kan na illata ki?" Yayi mata maganar cikin tsawa, ko girgiza ba ta yi ba, sai ma tsare shi da ta yi da ido, wata lamba ce a jikin jakar, wannan jaka dai ba za ace kaya ne a ciki ba, sai dai lambobin jikin jakar sun ɗau hankalinta sosai.

Aliyu ne ya figo hannunta yana zaginta.

"Yarinya ce, ka daina dukanta mana babu kyau yarinya ce ƙarama" yayi wa Aliyu maganar yana riƙe hannun Aliyu.

Aliyu ya rasa haɗin mutumin nan da rumaisa, da ya yi mata faɗa sai ya hau ce masa ya ƙyaleta yarinya ce, ko ina ruwansa oho.

Haka ya haƙura ya ƙyale ruma, tun da mama ta kira ya ce mata haryanzu basu isa ba, ya sanya mama shiga cikin damuwa, saboda ya ci ace sun je, amma ta ji suna hanya.

A haka aka gyara motar suka hau suka cigaba da tafiya. Ruma ta durƙusa ta taɓa wata jaka da kuma buhu da ke ƙarƙashin kujerar da take kai.

"Wai dan Allah kayan waye wannan da ba za a saka masa su a ƙasan kujerarsa ba sai ta mu, ni fa sun isheni na yi kawaicin na gaji, sun addaba mini".

Mutumin nan dai ya waiwayo ya ce wa ruma "Yi haƙuri, mun kusa sauka ma, namu ne zamu ɗauke".

"Wallahi ɗan uwanmu ba dan naka bane ba, sai an cire mini su, da na wannan mai jakar ne da ya hantareni sai ya kwashe kayansa ya mayar da su wurinsa, ɗazu daga tambaya ya yi mini tsawa".

"To kiyi haƙuri" ɗayan ya waiwayo ya kalli ruma, ruma ta zaro masa ido kamar tana kallon yaro.

Aliyu dai ya sunkuyar da kai yana cigaba da addu'a, shi ba abin yayi wa ruma magana ba ko ya rufeta da duka ba.

Sun shiga katsina, a wani ƙaramin ƙauye suka tsaya zasu sauka, mai jakar nan ya kalli ruma ya ce "Ke sauko, zamu ɗauki bindigoginmu".

Tsit kowa ya yi, ruma ta ce "Wace irin bindigogi kuma?"

"Zaki sauko ko sai bomb ɗin ciki ya tashi da ke?"

Tankaɗata Aliyu yayi suka sauka, aka ɗaga musu kujera, aka fara fito da jaka.

"Dan Allah da gaske bindiga ce a ciki?"

Yayi murmushi, ya zugewa ruma jakar, ƙananan bindigu ne, ƙirar pistol.
Ya ce "Waccan jakar kuma da kike tambaya meye a ciki ɗazu, bullet ne a ciki"

Ta ɗan waro ido ta ce "Kashe mutane ku ke yi kenan, tun da dai na ga ku ba 'yan sanda bane kuma ba sojoji ba?"

Ya girgiza wa ruma kai ya ce "A'a 'ya ta, aikin Allah muke yi ake biyanmu"

"Aikin Allah ai ba a biyan mutum, Allah ne zai biya mutum da lada"

Yayi murmushi ya ce "Ba zaki gane ba, Ubangiji Allah ya yi miki albarka ya rayaki, da 'ya ta na raye da ta yi kamar ke"

"To ta na ina yanzu 'yar ta ka?"

"An kasheta ita da babarta, Allah ya rayaki" ya kalli Aliyu ya ce "A lallaɓata dan Allah, sai wataran 'ya ta" yayi maganar yana ɗagawa ruma hannu.

Wata narkekiyar mota ce ta yi parking, mai kyan gaske aka ɗora kayan bindigar a ciki, suka shiga motar aka ja suka tafi.
Ruma ta ɗauko wayarta ta fara dannawa.

Aikuwa Aliyu ya dinga zaginta, har da zagin da bai san iya shi ba, dan ruma ta kai shi maƙura yau, gaba ɗaya ruma ba ta da hankali ba ta san ciwon kanta ba, shi tun da suka hau motar, suka yi nisa ya gane bindigogi ne a buhun da ke ƙasan kujerarsa, kuma yana fuskantar yaren da suke yi kaɗan-kaɗan, 'yan ta'adda ne mutanen, amma ruma sai hauka take zubawa da wauta saura ƙiris ya karɓi shegiyar wayar nan ya jefa ta ta window. Sai dai yana tsoron yin hakan dan ya ga mutumin nan ya zaƙe a kan ruma kar yayi masa wani abu idan ya taɓata.

Direban ya ce "Wallahi bawan Allah Yarinyar nan mai sa'a ce, dan ni na zaci ma da zasu sauka tasa ta zasu yi a gaba su tafi da ita, ko su kasheta surutunta yayi yawa, ba a yi wa wannan mutanen haka"

Aliyu ya ce "Eh kaima ai azzalumin ne, da ka ɗauko mu mota ɗaya da wannan mutanen".

"Megida ba laifina bane ba fa, kullum akwai irinsu da suke shige da fice zuwa garuruwa, ba su fiye cutarwa ba sai in kun musu rawar kai, mu ma abincinmu da rayukanmu muke karewa".

"Amma jami'an tsaro na garin nan, ga su a tasha, amma ake safarar makamai a tsakanin garuruwa suna gani?"

"Lallai ɗan samari zancen ka ke so, lamarin ƙasar nan ta mu ai sai dai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, idan ka matsa sai ka kwana a ciki amma manyanmu sun san komai"

Aliyu ya girgiza kai ya ce "Allah ya kyauta".

Sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login