Showing 180001 words to 183000 words out of 224014 words
mamaki ta kalli securityn ta ce "Waye ya ce kar a sake barina na shiga?"
"Takawa, shi ya ce kar ki sake shiga idan kin zo in ba shi ya ce ba"
"Kam bala'i, wai wannan wane irin mutum ne, shi wane irin azzalumi ne, idan har ba zan din ga shiga ba, ya bani ɗana mana, ai dai ya san ba maula ce take kawo ni ba ko?"
"Ke da shi ne wannan, matsa daga nan"
Wata irin zuciya ta turnuƙo rumaisa ta ce "Wallahi ba in da zani sai an bani ɗa na, wallahi yau sai na shiga gidan nan, wane irin mugun mutum ne shi, ba shi da imani ba shi da tausayi, wallahi sai na shiga sai dai ku kasheni" ta yi maganar tana tunkarar gate ɗin.
Tare gate ɗin ɗaya yayi, cikin tsawa wani ya ce mata "Ki ka motsa daga nan sai na harbeki"
"To ka harbenin mana, sai me? Allah sai na shiga"
Gaba ɗaya ta rasa abun da za ta yi, ta fashe da kuka, saboda uwar wahalar da ta shawo, kan ta samu ta zo, amma ta tarar wai an hanata shiga.
Ta fi mintuna talatin a tsaye a rana tana kuka, ɗaya daga cikin masu gadin ya ce "Wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce haka?"
"Kai ne baka santa ba, kwanakin baya ta taɓa zuwa gidan nan, zata aikata fiye da abun da ta yi yanzu"
Kamar daga sama, ta hango shi yana tunkaro ƙofar gidan, sanye da ƙanan kaya, kunnensa ɗaya da Bluetooth, fuskar nan tasa fayau ya yi ƙiba abunsa, kan ya ƙarasa gate ɗin rumaisa ta tashi da gudu, ta je ta riƙe rigarsa tana kuka.
Sororo yayi yana kallonta, "Shi ne kace idan na zo kar a sake barina na shiga, ka san da haka ka karɓe mini yarona? To ka shiga ka ɗauko mini sabir ba zan sake zuwar muku gida ba"
Ɗaya daga cikin security zai yi magana, ya ɗaga masa hannu ya dakatar da shi, ya kalli rumaisa ya ce "Wane jaririn ki ke magana a kai?"
Waro ido rumaisa ta yi ta ce "Ni zaka rainawa hankali ka mayar mahaukaciya, wato ma baka san wane jaririn nake magana a kai ba, wallahi sai na ɗebo maka ƴan sanda, ko kuma tun da kai ma ɗan sanda ne, na san haɗa baki zaku yi, alƙali zam je na gaya wa, kuma ka bani ɗana ba zan sake zuwar muku gida ba"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, mu shiga ki ga ɗan na ki, sakar mini rigata".
"Wallahi ba zan cika ka ba, ka gudu su hanani shiga" ta ƙara riƙe masa riga, suka nufi gate ɗin.
"Ranka ya daɗe, Yallaɓai ya ce kar a sake bari ta shiga".
"Ni kuma na ce sai ta shiga, ko nima an hana ni shiga ne?"
Ya girgiza kai, suka buɗe gate ɗin, suka shiga, sai da suka zo ƙofar shiga sashen ammi, sannan ta saki rigarsa ta shiga ciki da sauri.
Sai dai tana shiga babban falon ammi, abun da ta gani ya razanata.
Turus! Ta yi ta tsaya, Adam ta gani a zaune sanye cikin suit farare, da shi da ammi a falon, sabir a kan kujera yana barci.
Ta waiwaya ta kalli hanyar da ta shigo, sannan ta kalli in da Adam yake.
Ammi ta ce "Rumaisa daga ina haka?"
Ta ƙarasa ta zauna, safarta tayi futu-futu saboda tafiyar ƙafa, ta zauna ta ce "Tun safe nake tahowa, da ƙyar na zo gidan nan, dan na ga sabir, amma da na zo aka hanani shigowa, wai ya ce idan na zo kar a sake barina na shigo, sai kuma na ganshi ya zo wucewa zai shigo gidan nan, tare muka shigo na bar shi a waje, amma kuma da na shigo na ganshi a nan a zaune, a waje da ƙanan kaya na ganshi, amma kuma a nan na ganshi da wasu kayan". Tayi maganar tana kallonsa.
Adam bin rumaisa ya yi da kallo, yana mamakin anya kanta ɗaya, jin ta ce da ƙafa ta taho, kuma yanayinta ya tabattar da hakan.
Ammi ta ce "Ohh Mahmud ya shigo gari kenan?"
"Waye Mahmoud? Ba shi na gani a waje ba kenan?".
"Ba shi ki ka gani ba" Ammi ta bata amsa.
Rumaisa ta gyara zamantaz tana shafan kan Sabir, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah ya sa idan na fita na ganshi na bashi haƙuri ban san ba shi bane ba, na yi ta masa masifa*.
"Amma rumaisa ba makaranta zaki je ba na ganki da uniform?".
"Makaranta zani, amma na kasa jurewa, ba bu abun da nake so sai in ga sabir, amma na zo wai an hanani shigowa, ban da dalilin sabir ma ni mai zai kawoni gidan nan, ina ga ma alhakin yaran mutane da nake cin zali ne ya kamani, Allah ya jarrabeni da son yaron da ake wulaƙanta ni a kansa, bakomai wataran sai labari"
Maimakonsa ammi ta ji maganganun rumaisa sun yi tsauri, sai ma wani irin tausayinta da ya kamata, lallai rumaisa tana cikin jarrabawa ta gaske saboda sabir.
Ammi ta riƙe hannunta ta ce "Rumaisa, babu mai wulaƙantaki a kan sabir, sabir ɗanki ne, ki yi haƙuri zan ɗau hukuncin da ya dace a kan Adam, amma daga yanzu duk lokacin da ki ke son ganinsa, akwai lambata a wayar mamanki, ki kirani ni kuma zan saka a kawo miki shi, ko na kawo miki shi da kaina, kin ga yanzu kin yi missing school, bari ya mayar da ke gida, tun da dama wurin aiki zai koma"
Rumaisa ta girgiza kai ta share hawaye ta ce "A'a, zan koma gida da kaina, kuma ba zan sake zuwa gidan ba, balle masu gadi su ci mutuncina a waje kamar yadda aka yi mini yau kamar ƴar maula" tayi maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.
"Kiyi haƙuri, in sha Allah hakan ba zata sake kasancewa ba, babu mai sake wulaƙanki a kan sabir, ko shigowa gidan nan, tun da gidanku ne, bari a kawo miki ruwa ki sha, ki ci abinci sai ya mayar da ke gida".
Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode, dama sabir kawai nake son na gani, ban ci wani abun ba balle yayi tunanin ina fakewa da son ganin sabir ina zuwa kwaɗayi".
Kalaman rumaisa ya tabattarwa da ammi rumaisa ba wauta da ƙuruciya kawai ta iya ba, ta san mutuncin kanta, kuma tana girmama kanta.
Ta ce "Ai na baki haƙuri, kuma na gaya miki zan ɗau mataki a kansa, kuma ko me zai ce ki rabu da shi, abun da ki ka yi masa a rayuwa bai isa ya biyaki ba, ladanki yana wurin Allah, tashi mu je ki sha ruwa ki sake karyawa, wannan tafiyar da ki ka yi na san kin gaji sosai" da ƙyar rumaisa ta amince ta tashi ta bi ammi, dan tana ganin mutuncinta da darajarta, amma ba dan haka ba, sai ta ce ko iskar gidan ba zata shaƙa ba balle ruwa, saboda cin mutuncin da aka yi mata.
Ammi ta kai rumaisa falonta, ta saka a ka kai mata abinci, ta fita ta bata wuri dan ta ci, ta dawo ta tarar da Adam a falo.
Rai a ɓace Ammi ta ce "Ban ji daɗin abun da ka yi ba ƙwarai da gaske, muzanta yarinyar nan da aka yi a waje, a kan me zaka ce kar a sake barinta ta shigo?"
Cikin ladabi Adam ya ce "Tuba nake, ba na yi haka ne domin ɓata miki rai ba, amma yawan zuwanta gidan nan akwai matsala, bana son ta shiga cikin wani hatsari saboda ni ko ayi amfani da ita wurin cutar da waninmu"
Ammi ta ɗan yi shiru ta ce "Ban ƙi ta taka ba, amma a ƙuruciya irin ta ta, da irin ƙaunar da take nunawa gudan jininka bai kamata a ɗauki wannan matakin kai tsaye a kanta ba, ba tare da bin wasu hanyoyi da ba zata ga an wulaƙantata ko cutar da ita ba. Tana da matuƙar wayo da kaifin basira, dan haka abun da ka yi mata dole ta kirashi da wulaƙanci da tozarci, kar ka sake yanke makamancin wannan hukuncin ba tare da izinina ba".
Ya risuna ya ce "In sha Allah"
"Ka biya ka fara ajiyeta a gida, ka sanar musu halin da ake ciki, don a saka ido sosai a kan ta ta daina missing makaranta, kuma kar ta sake yin wannan doguwar tafiya haka a ƙafa ita kaɗai"
Ya jinjinawa ammi kai.
Rumaisa ta fito, idanun nan sun yi ja ta ce "Ammi zan tafi".
"Maman Sabir har kin gama, bari ya mayar da ke gida" rumaisa ta kalli Adam sannan ta kalli ammi za ta yi magana, ammi ta girgiza mata kai ta ce "Ba'a jayayya da umarnin giwar galadima" Ammi ta yi mata maganar cikin gargaɗi, haka ya tilastawa rumaisa yin shiru.
Adam ya miƙe yayi gaba, rumaisa ta durƙusa ta sumbaci goshin sabir, sannan ta bi bayan Adam.
Kamar yadda ransa yake a haɗe, haka ita ma ta tsuke ta ta fuskar, babu alamar wasa da yarinta.
"Laa ka ga, bawan Allah" Adam ya ji maganar rumaisa, tsayawa yayi ya waiwaya bayansa, da gudu ya ga ta nufi jikin bishiyar dabinon da ke tsakiyar harabar gidan. Mahmud ne a tsaye yake waya, amma ya katse wayar ya zubawa rumaisa ido yana jiran ta ƙaraso.
Ta ƙarasa tana ɗan haki ta yi murmushi ta ce "Ashe ba kai ne shi ba?"
Mahmud ya ce "Shi wa?"
Rumaisa ta nuna masa in da Adam yake.
"Na zata shine da na ganka ɗazu, idona ya rufe sosai da ɓacin rai, ga gajiya kuma kuna kama sosai da sosai, dan Allah ka yafe mini na yi maka rashin kunya a gaban mutane"
Yayi murmushi ya ce "Kin ga jaririn naki?"
"Na ganshi, Allah ya saka maka da alkhairi da ban ganshi ba yau, da ina ga mutuwa zan yi. Ɗa na ne fa anty aisha ta bar mini shi, amma ya ƙwace shi kuma wai ya hana ni shigowa gidan nan"
"Wace aishar?"
"Kai baka san ta ba? Kai ba ɗan nan gidan bane?".
"Eh ɗan nan gidan ne, amma bana ƙasar jiya da daddare na dawo".
"Au ho, to in gaya maka sace ni aka yi a katsina, sai aka sato anty aisha matarsa, ta haihu ta rasu ta bar mini jaririn na kuɓuto da ƙyar, bayan na yi kwanaki ina wahala, amma ya ƙwace ɗan kuma wai idan na zo kar a sake barina na shigo, dan Allah wannan ba mugunta ba ce ba?"
Mahmud ya yi murmushi ya ce "Bai kyauta miki ba gaskiya"
"To kai baka taɓa zuwa sashin ammi ka ga jaririn ba, au ashe fa ka ce jiya ka dawo, ba ka ga ɗan nawa ba, mai kyau tubarkallah, ai na san ammi zata nuna maka shi ma, tunda a gidan nan ka ke"
"Eh a gidan nan nake, amma ni ba a sashinsu nake ba, ni ɗan Mummy ne".
"Wacece kuma hakan?" Ta tambayeshi tana ɗan gyatsine fuska.
"Babata ce, ko baki san mata biyu ne a gidan nan ba? Anyway na ga kamar jiranki yake yi, ki je kar ya zo nan wurin ya karairayaki, shi yafi masa komai sauƙi"
Cikin fitsara rumaisa ta ce "Wallahi wuce nan, na gode sosai ba zan taɓa manta taimakon da ka yi mini ba yau, kuma ka na da kirki fiye da wancan mutumin, dan Allah ka je ka ga ɗana a wurin ammi, sunanshi Mahmud ana ce masa sabir" tana maganar ta yi gaba tana murmushi.
Turus Mahmud yayi ya bi rumaisa da kallo, Adam ya sanyawa ɗan sa sunan Mahmud? Ya tambayi kansa, dan abun da mamaki.
Wurin motar adam ta nufa, da tuni ya kunnata, ya fito ya saka ana karkaɗewa motar ƙura.
Ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce "Bawanki ne ni da zaki shanya ni ki tafi yawon surut?".
Ta kalleshi ta ce "Ba yawon surutu na tafi ba, godiya na je yi masa na bashi haƙuri. Ya nuna mini karamci saboda ni ɗan adam ce bai koreni ba ɗazu da na rasa nutsuwa ta ina kuka ba, ya taimaka mini na samu abun da nake so". Ta yi maganar irin ko maganar ta yi masa daɗi ko kar ta yi masa bai shafeta ba.
"Tun daga lokacin da ki ka sake shigowa rayuwata, ki ke ta wasu irin halayya da son nuna lallai akwai wani abu a tsakanina da ke, ina ɗaga miki ƙafa albarkacin yaron nan da kuma ƙuruciyarki, idan ki ka cigaba da wannan abubuwan ki ka shiga trap ɗi na zaki sha wahala na gaya miki, and as from today kar ki sake zuwar mana gida, abun da ki ka yi Allah ya baki lada, bana buƙatar sake ganinki a cikin gidan nan da sunan kin zo ganin yaron nan, idan kuma ki ka cigaba da zuwa zan nesanta shi da ke, nisantawa mai tazarar gaske da ba zaki iya cimm masa ba, dan haka idan ma wani abun ne a ranki ya sanya ki ke bibiyarsa, ki saka abun da na gaya miki a ranki. Idan har zaki cigaba da bibiyar yaron nan, za'a iya amfani da ke a cutar da shi, dan haka bana buƙatar sake ganinki a kusa da shi" yayi maganar cikin kashedi.
Cak ta tsaya ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi, sai wasu irin hawaye da suke zubowa daga idonta.
Ayshercool
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
*₦500 ne, via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*
"Meyasa baka ɗau maganar mahaifiyarka da muhimmanci ba, har kake yi mini wannan barzanar a bayan idonta? Ko ba komai tana tausayina wataƙila ta san me nake ji game da sabir" ta saka idonta cikin nasa, wanda hakan ya sanya musu faɗuwar gaba a tare, cikin jarumta da ƙarfin hali ta daki motar Adam ta ce "Idan har bayan mutuwar anty aisha an yi umarnin a kashe sabir, na ɗau duk wani riski Allah ya dafa mini na kuɓutar da shi, kana tunanin bayan kuɓutarmu ne wani zai haɗa kai da ni a cutar da yaron da na ɗaukarwa babarsa alƙawarin kula da shi? Wace irin zuciya ce a jikinka?"
Ma'aikatan wurin ne suka tunkarosu, amma adam ya dakatar da su, saboda rumaisa ta faɗi wani abu mai muhimmancin gaske.
"Kai ka san abun da ya haɗani da kai ai tun farko, kuma ban janye abun da nace ba, ba zan taɓa janyewa ba kuma. Sabir idan ka ga dama ka kai shi bangon duniya, ka yi duk abun da kake ganin ya dace. Mara imani ban taɓa tsanar abu a duniya ba kamar kai, ko ƴan bindiga da na zauna a hannunsu wataran suna mutunta ni. saboda furucin da ka yi a kaina, wai a haɗa baki da ni a cutar maka da ɗa, na gode daga yau ba zan sake zuwar muku gida ba in sha Allah, in dai ni ƴat halak ce mama ce ta haifeni su yaya usman ne