Showing 174001 words to 177000 words out of 224014 words

Chapter 59 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1129

ba ta so.

Sai da ta zo kwanciya barcci, sannan wata irin kewar sabir ta sake kamata, ta rungume fulonta, ta rintse idonta, ta din ga hango fuskarsa yana kallonta yana lumshe idonsa.
Kamar an kunnawa zuciyarta wuta, haka ta din ga jin wata irin ƙishirwar son sake ganin sabir, tamkar ta yi tsuntsuwa ta tashi. Ta sake rintse idonta, tana sake tuna yadda take kwana gata sabir a asibiti, ganinsa da ta yi yau ta sake jin du rintsi duk wuya sai an bata ɗan ta.
Haka kurum ta hau kuka, tana sake jin tsana da haushin adam a zuciyarta, a ganinta duk shi ya ƙulla a ƙwace sabir a hanata shi.

Cikin ikon Allah, takawa ya farfaɗo gaba ɗaya, ammi ta saka shi a gaba ta din ga tambayarsa a kan meyafaru har ya shiga wannan yanayin.

Ya ɓoye yaƙi gayawa ammi dalili, ya ce mata bakomai, kamar kullum ta din ga yi masa nasiha tare da fatan Allah ya bashi lafiya da mafita a kan lamuransa.

Washegari da safe rumaisa kamar ta saka kuka, mai sunan baba ya kafa ya tsare, ya sanya rumaisa a gaba ta shirya cikin uniform ɗin ta da suka sha guga, kamar ta fashe saboda takaici, ba ta son makarantar nan, ya sakata a gaba ya tafi kaita makaranta.

A ofishin shugaban makarantar ma, sake jajantawa rumaisa abun da ya sameta malamai suka yi, suka yi mata barka da dawowa tare da fatan Allah ya sanya ta nutsu zamanta a hannun ƴan bindiga ya zame mata darasi.
Gaba daya hankalinta ba ya kansu, tunaninnta kawai yadda za ta ga sabir, mai sunan baba ya gama clearing ɗin abun da yakamata, aka ce ta tafi aji, amma ajin baya zata koma saboda an riga an yi mata nisa a karatu.

"Kaii repeating aka yi mini, kenan ba zan yi candy da wuri ba, taɓ wallahi ba..." Gum ta rufe bakinta ba ta ƙarasa maganar ba, saboda kallon da mai sunan baba yayi mata, tana ji tana gani aka mayar da ita ajin baya.

A ranta ta ce 'Wallahi ba zan zauna a ajin baya ba, sai a zata ma daƙiƙanci ne ya saka aka yi mata repeating"

Da aka fita break, ƴan ajinsu da suka yi gaba, suka din ga tsalle suna murna, rumaisa ta dawo.

Sam ta ƙi shiga sabgar kowa, ta ɗau littafinta ta din ga zana hoton sabir a bayan litattafan ta. Har aka tashi ba ta san me aka yi ba.

Da ta koma gida mama tana ta murna, tana tambayarta ya aka yi a makarantar?

Rai a ɓace ruma ta ce "saboda tsabar tsanar da mai sunan baba yayi mini, ya sa aka yi mini repeating, wallahi ba zan zauna a ajin nan ba, ni ajin yan candy ma zan koma" ganin rumaisa za ta ɓata rai, ya sanya ta shareta.

Can rumaisa ta kuma cewa "Mama dan Allah in anjima, ki ce yasir ya rakani gidan su hauwwaliya na duba ƙafarta"

Mama ta ce "Kuma kin yi tunani mai kyau, kya je ki gaishe su, su ga kin warware sosai, amma sai gobe in Allah ya kaimu"

"Dan Allah mama in je yau"

"Goben in Allah ya kaimu ma sai na ce ba zaki je ba"

"To ki yi haƙuri, Allah ya kaimu goben".

Adam kuwa gaba ɗaya wunin ranar bai fita ba, ya san dole Jabir zai zo nemasa, ya bar saƙon ko jabir ya zo, a bashi haƙuri ba zai iya ganin kowa ba.
Ya kulle kansa a ɗaki, ya kunna wayarsa ya hau social media, ya ga yadda labari ya baza ko in, ga tarin kiran waya da saƙonni daga ƴan jarida, mutane sai comments suke kala-kala.
Ganin wayar na neman caza masa kai, ya sanya yayi jifa da wayar, gaba ɗaya ya ji ya rasa ƙwarin gwiwar da zai sake fuskantar duniya, da ƙudurinsa na son kawo ƙarshen yi wa ƙasa da harkar tsaro ɓarna. Ya ji ya rasa ƙwarin gwiwar bincikar waɗanda suka yi garkuwa da matarsa.

Sai da Ammi ta yi da gaske, sannan ya buɗe ɗakinsa, har ya samu ya ci abinci, amma bai gaya mata abun da yake faruwa ba, saboda kar ya sake ɗaga mata hankali.


Rumaisa yau ji take yi kamar salla, saboda yau zata kuma zuwa ta gano Sabir, dan a yanzu babu abun da yake faranta mata rai sama da haka.
Yau da rumaisa ta je makaranta, ƙin zama ta yi a ajin da aka kaita, ta tafi ajinsu ta yi zamant, ta ce ba ta ga wanda ya isa yayi mata repeating ba, sai dai a gaji a koreta daga makaranta gaba ɗaya, wanda da za ayi mata haka da shi ta fi so, dan ita ba ƙaunar makarantar take yi ba.


Mai martaba a yau da kansa ya dira a gidan su takawa, wanda hakan ya sa gidan ya cika maƙil da hadimai, da jami'an tsaro, masu kaiwa suna komowa, tun daga farkon titin har cikin gidan.
Bai sauka a ko ina ba, sai a sashen Ammi.
Mummy na jin labarin zuwan mai marataba, ta tarkato yaranta ta bazamo sashin ammi, da sunan zuwa kwasar gaisuwa a wurin mai martaba sarki.

Ƙafa da ƙafa ya zo ya yi wa Adam ta'aziyyar mutuwar aisha, sakamakon baya gari lokacin da abun ya faru.

Mai martaba ya numfasa ya ce "Turaki yayi mana bayanin komai yadda al'amarin ya faru, sai dai bai kamata a ɓoyewa duniya gaskiyar abun da ya faru ba, maƙiya za su iya amfani da wannan damar, wurin cutar da kai, kamar yadda zancen ya fasu har wata gidan jarida suka wallafa, kuma ba zai wuce saboda ƙoƙarin da ake yi wa ƙasa ba, ya sanya miyagu ke ta ƙoƙarin bayyana laifinka, amma ayi haƙuri a daure, a cigaba da abun da ake yi kar a fasa Allah zai shiga lamarin"

Adam ya risuna ya ce "In sha Allah, muna fatan mai martaba ya cigaba da sanya mu a addu'a".

"Addu'a kullum cikin yi muku ake, kuma ko dan albarkacin mu babu wani abu da wani zai iya yi ya cutar da ku a kan gaskiya a ƙasar nan, a cigaba da ƙoƙari. Ita kuma 'yar mu Allah ya jiƙanta ya raya mini wannan kyakykyawan jikan nawa" yayi maganar yana shafa kan Sabir da yake hannunsa.

Mummy ta risuna tana "Allah ya taimaki mai martaba, mun gode da wannan karamci, Ubangiji Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya ƙara maka lafiya da nisan kwana"

"An gaisheki amaryar Galadima, , ƴar malam kin ƙi halin malam, mai martaba ya amsa kuma yana godiya" wani irin takaici ne ya kama mummy, jin yadda hadimin mai martaba ya amsa mata.

Aka karɓi jaririn aka miƙawa ammi, shamaki ya dubi ammi ya ce "Mai martaba ya bawa jariri gidaje guda biyu, ya bashi dawakai guda uku, sannan mai martaba ya yi umarnin a  gina masallaci sadaka ga mahaifiyarsa. Sannan idan ya shekara uku a duniya mai martaba ya ce a kai shi umara"

Nan dogarai suka ɗauka da "Godiya yake mai martaba, godiya yake Allah ya baka yawan nasara. Mai bayarwa da dama hagu ba ta sani ba"

Takawa ma risinawa yayi, suna yi wa mai martaba godiya.
Dogaransa suka kare shi ya tashi tsaye, har zai fita ya hangi iman a gefe a zaune.

Ya ce "Ahhh giwa, wannan buzuwar ƴar ta ki tana nan dama, ko da yake an ce mini bafullatana ce? ta daina zuwar mana, Allah ya jiƙan mai babban ɗaki, lokacin da muka kai mata ziyara a Saudiyya kan ta rasu, take tambayar ina wannan buzuwar ƴar ta giwar Galadima, a lokacin bamu sani ba ko kuna tare ko kin mayar da ita, mai babban ɗaki tana sonta"

Ammi ta yi murmushi ta ce "A'a muna tare mai martaba, ai tun da kuka saka baki a kan maganar nan, muke tare da ita"

"Allah sarki, baki fuskanci wani abu ba binta, wataƙila albarkacin yarinyar nan ne Allah ya kawo muku yaron nan cikin aminci, Ubangiji Allah ya yi jagora, Allah ya raya mana su baki ɗaya"

Ammi ta amsa da amin mai martaba.

Ba ƙaramin ƙulewa Mummy ta yi ba, yadda mai martaba ya mayar da hankali a kan yaran ammi, har da agola, amma ita ko kanta bai bi ba.

Mai martaba na tafiya, mummy ta fice fuuuuu ta bar sashin ita da su Fauziyya.

Bayan fitar su Ammi ta ce "Iman, mun yi laifi fa daina zuwa gidan mai martaba da ki ka yi, balle ki je gaishe shi,  kin ga har ya magantu, Allah sarki mai babban ɗaki, lokacin kina ƙarama rigingimun da aka yi ta yi a kan ki,  cewa ta yi sai na bata ke, na din ga kuka, ita tsaya mini a kan riƙonki".

Iman ta ce "Ammi tsoron zuwa gidan nake, fulanin yola ta hana ni zuwa, saboda yarima Hashim, kin san ai abun da aka yi mini su da Mummy"
Ammi ta ce "Na ji, kar ki yi kuka, jikina na bani mijinki mutum ne na gani na faɗa, karki damu autata"

Kunya ce ta kama Iman, Nusaiba ta ce "To ni fa, ko ita kaɗai ake yi wa Addu'a"

"Ke dai nusaiba baki da girma sai na jikinki, kishi ki ke iman ɗin?"

"To shikenan ma, ni na yi zuciya" Nusaiba ta tashi za ta fita, iman ta tashi ta bita da gudu tana yi mata dariya.

Ammi ta mayar da hankali a kan adam, da fuskarsa sam babu walwala, ta dube shi a tsanake ta ce "Mai martaba yake magana a kai ne, na ji yana cewa an yi amfani da gaskiyar abun da ya faru ana sukarka, meyafaru?"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Wata gidan jarida ne suka yi posting a social media, cewar aisha ta mutu a hannun 'yan bindiga, ko kuma ni na kasheta na yi tsafi da gangar jikinta tun da ba aga gawarta ba ma"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, adam waye ya aikata wannan abun? Waye ya fitar da wannan zancen har da sharri haka?"

"Nima ban sani ba, ɗazu na ɗauko wayata a mota, kira daban-daban da saƙonni daga ƴan jaridu, suna buƙatar wai na ce wani abu a kan lamarin na kashe wayar ma gaba ɗaya".

Ammi ta dafe kai, ta rasa me ma za ta ce ko ta yi? Abubuwa kullum sake rikicewa suke yi.

Da la'asar yasir ba dan yana so ba, ya saka rumaisa a gaba zai kaita cikin gari, suna tafe yana mita, sai da suka je titi, sannan rumaisa ta ce "Dan Allah Yasir taimakona zaka yi"

"Taimakon me?"

"Dan Allah gidan su sabir zaka rakani na je na ganshi" wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Ba zani ba, yaushe ki ka je ki ka ganshi? Ba zani ba ba nan muka yi da mama ba".

Riƙe hannunsa ruma ta yi ta fara kuka "Dan Allah yasir, wallahi na kasa bacci jiya, ba zamu daɗe ba dan girman Allah" ganin tana kuka ya sanya jikinsa yin sanyi.

"Kin yarda zaki wanke mini uniform, ki ɗaukar mini jakata zuwa islamiyyar"

Da sauri ta ce "Eh wallahi na yarda"

"Shikenan mu je, saura idan buƙatar ki ta biya, ki yi mini rashin kunya".

"Ai ba ma zan yi ba"

Ya tarar musu abun hawa, suka hau suka tafi.

Suna tafe yasir yana danna waya, can ya ce "Kaii"

Ruma ta ce "Menene?"

"Wani labari na gani, ke dama baban sabir ɗin nan shi ne Adam Sharif Galadima?"

"Wai wannan mai tona asirin mutanen, ba wani nan ba shi ne ba"

"Dan ubanki ƙarya zan yi miki?"

Rumaisa ta ce "Taɓ, ba shi bane ba, shi wannan yana abun arziki ne?"

Yasir ya ce "Ke ba wannan ba, wani labari aka wallafa wai, ya sayar da matarsa yayi tsafi da gangar jikinta, kuma jaririn da aka ce nasa ne, ƙarya ne rainawa mutane hankali ake"

Wani takaici ne ya turnuƙe rumaisa ta ce "In ji uban wa?"

'oho, wani gidan jarida ne suka wallafa"

Rumaisa ta ce "To rubuta musu ka ce ƙarya suke yi, wannan yaron nice nan na zo da shi"

Yasir ya ajiye wayar ya ce "A'a ba ruwana"

Rumaisa ta ce "Zan yi waya katsina a kawo mini wayata ni na rubuta, wannan ai sharri ne"

"Ke dalla rufewa mutane baki, zaki saka na ƙi rakakin wallahi"

Ta riƙe bakinta ta ce "Na daina in sha Allah"

Da haka suka ƙarasa gidan su Adam, rumaisa har da ɗan tsalle za su je ta ga Sabir.

Sai dai rumaisa ta yi ta mamakin ganin layin duk kashin dawakai, duk da abun mamaki bane, amma yanayin wurin ya nuna an yi wani sha'ani a wurin.

Yanzu babu wanda yake yi wa rumaisa shamaki da shiga sashen ammi, sai dai ta jira ta ce wurin ammi suka zo, ak shiga da su sashen Ammi.

Ko da ammi ta ga rumaisa sai da mamaki ya kama ta, shekaranjiya rumaisan ta zo, yau ma kuma gata.
Ammi ta ɓoye mamakinta, ta yi musu maraba, a nutse Yasir yake gaida Ammi, rumaisa kuwa ko gaisawar ba ayi ba, ta koma kusa da ammi ta ɗau Sabir.

Shi kansa takawa kallon rumaisan take, wannan nacin na ta ya fara yawa.

"Rumaisa ya mamanki"

"Tana lafiya ƙalau" ta ƙarasa maganar tana jujjuya sabir da yake bacci, wai sai ya tashi ya ganta.

Hakan kuwa aka yi sai da sabir ya buɗe ido yana miƙa, wasa rumaisa ta yi masa, ya geɓare baki ya fara murmushi.

"Laaa kun ga, yayi mini dariya, Yasir kalli yana yi mini dariya, ya gane ni, sabir ummanka ce rumaisa ka gane ni ko?"

Ammi ta ce "Ikon Allah, ko bacci bai fiye dariya ba, lallai ya ganeki, ke ya fara yi wa dariya".

"Kaii dama kewarsa ce ke damuna, na yi ta mafarkinsa, na cewa mama a rakani mandawari na duba ƴar uwarmu Hauwwaliya, na cewa yasir dan Allah ya rakoni na ga sabir ɗina"

Ammi kallonta take tana murmushi, tana jin daɗin yadda sabir ke yi wa rumaisa murmushi.

"Rumaisa baku gaisa da baban sabir ba" ruma ta ɗago ta kalleshi ta ce "Ni ma bai kulani ba, yauwwa ammi wai da gaske shi yake shayar da shi?"

"Shi wa?"
Rumaisa ta nuna Adam ta ce "Haka ya ce mini, wai idan aka bani sabir bani da abun da zan shayar da shi, na ce masa ana bashi madara, wai ba a bashi madara shine yake bashi abun da ake bawa jarirai wai ni idan an bani sabir me zan bashi?"

Paid book ne ₦500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*



Dariya ce ta kuwa kufcewa ammi, ta ce "A'a rumaisa wannan maganar dai taku ce ba tawa ba"

Takawa dai ko kallonta bai yi ba, dan ya fuskanci yarinyar ba ta da kunya sam.

"Amma dai ammi ai ni ban taɓa ganin maza suna shayarwa ba, shi kuma ya ce mini haka, kuma dai na ga shima ƙirjinsa babu komai"

Ammi rasa amsar da za ta bawa rumaisa ta yi, can sai hankalin rumaisa ya ɗauke daga kan maganar.

"Ammi" ta faɗa a hankali.

"Na'am umman sabir"

Rumaisa ta washe baki ta ce "Wayyo daɗi, ammi na ji daɗi, Allah ya amsa dukkanin buƙatinki, na fili da na ɓoye ya biya miki buƙatunki na alkhairi, na ji daɗi da ki ka kirani umman sabir"

"Amin rumaisa, in dai kin ji daɗi, ina son ki din ga saka baban sabir a addu'a, Allah ya biya masa buƙatunsa".

"To ammi, ai saboda ke zan yi masa addu'a ba dan halinsa ba"

"Subhanallah, meye da halin nasa?"

"Ba ki ga yadda ya tsaneni ba? Hmm baki san halinsa ba ne"

Wani ƙarfin hali sai rumaisa, mace da ɗan ta, amma tana faɗin ba ta san halinsa ba ne.

Ammi ta ce "Rumaisa takawa mutumin kirki ne, fiye da yadda ki ke tunani, kawai mutum ne mara son hayaniya da shiga sabgar mutane".

"To ni dai saboda ke zan yi masa addu'a kawai"

"Yauwwa rumaisa, maƙiya sun saka shi a gaba, wai cewa aka yi shi ya kashe aisha ya yi tsafi da gawarta, kuma sabir ba ɗan sa bane ba"

Ruma ta waro ido ta ce "Wai dama da gaske yasir yake, muna tafiya a hanya ya gaya mini, Innalillahi kam bala'i, to shi kuma yayi shiru" ta yi maganar tana ƙare masa kallo.

Sai kuma ta sake cewa "To shine yayi kuka da aka faɗi haka? Na ga kamar idonsa yayi ja?".

"A'a ba kuka ya yi ba, addu'a dai zaki din ga yi masa"

Ruma ta ce "Taɓ, ammi kin san wani abu?".

Ammi ta ce "A'a".

"Nifa wallahi dan mutanen duniya sun tsaneni suna yi mini sharri, in dai Allah yana so na shikenan, kin ganni a unguwarmu ce mini ake ƙanwar maza, wai idan na yi tsokana yayyena suna tare mini, eh wataran suna tare mini, idan aka koma gida kuma su hukuntani, har gida aka je aka cewa mama wai bani da tarbiyya, tun da ƴan unguwarmu suka yi mini tambarin rashin ji na daina jin nauyin kowa. Idan na yi musu abun arziki ba a zuwa a gayawa mama ko yayyena, da na yi rashin ji, za su zo su faɗa. Ni kuwa tun da na gane haka na daina saurarawa kowa, idan na yi tsokana ta ko a zaneni, ko.....

Jin zancen nata ba kai ba gindi ya sanya yasir cewa "Bari mu tashi mu tafi".

Ammi ta girgiza masa kai, ta ce "Baka ga hira muke yi ba, ina jinki umman sabir"

Ta sake gyara zama ta ce "Tun da na fuskanci ƴan unguwar nan ba sa yaba mini a kan abun arziki, ya sanya na zauna a kan kalmar rashin ji, idan aka ce na yi abu bana jin shakkar in ce na yi ko kasheni za ayi, idan ban yi ba komai za ayi mini ba zance na yi ba. Allah kaɗai nake tsoro shi ya halicceni kuma jin tsoronsa dole ne. Wallahi ammi a kan gaskiyata sai da a kasheni, kin san bala'in da na gani a hannun 'yan bindiga kuwa? Hmmm ai wallahi idan nice shi, zan kalli duk wanda ya ce na kashe matata na ce na kasheta idan kana da alaƙa da ita ka nemi shaida ka kaini kotu.
Ba dai baba mai farin rawani ne baban Anty Aisha ba, kuma ya ce mini ya san baban sabir ba zai cutar da anty aisha ba, to wallahi sai na kalli uban kowa na ce masa na yi ɗin. Ai su yadda na fuskanci mutane, idan suka yi maka ƙage, ka yi ƙoƙarin kare kanka, to zasu yi ƙoƙarin su ga sun sake binciko wani laifin saboda zasu gane ka tsorata, yaya usy ya ce mini, na koyi rayuwa nikaɗai a lokacin da babu wanda zai taya ni ƙwatar ƴancina, sannan na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login