Showing 162001 words to 165000 words out of 224014 words

Chapter 55 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1108

duk surutun da aka din ga yi ba ta faɗi in da sabir yake ba.

Washegari ma haka aka ɗora zaman makokin aisha, samha kuwa tun da sassafe ta taho kano, sai dai ta rasa wani mood yakamata ta shiga, na farinciki ko akasin haka? Duk yadda ta so ta ji lamarin ya ratsata ta kasa, babban fatanta Allah yasa da gaske Aisha ba ta raye.

Sai da ta isa gida ta tarar da tarin mutane, sannan ta tabattar da gaske aisha ta mutu, tun daga waje ta fashe da kukan ƙarya, dan kar a fuskanci wani abu, kai tsaye ta nufi cikin gidan tana kuka kamar gaske.
Nan yan makoki suka din ga rarrahinta suna yi mata nasiha a kan aisha addu'a take buƙata ba wannan kukan da take yi ba.
Abu kamar gaske, Samha ta din ga kuka tana tumami, ana rarrashinta da ƙyar ta yi shiru, ta tafi ɗakin mamanta ta kwanta ta samu bacci.

Sai bayan la'asar sannan Hajiya Asama'u ta shiga ɗakin ta tashi Samha.

Ta dubi Samha ta ce "Ke yanzu Samha dan aishar ta mutu ki ka zauna kina wannan uban kukan kamar ni na muty? Yarinyar da ta hanaku rawar gaban hantsi a wurin mahaifinku, har wani kukan mutuwarta zaki yi?".

Samha ta ɗan duba bayan mama, ta ji babu almar wani zai shigo, sannan ta dubi mama ta ce "Mama na dole ne, ko ba kowa ba wasu san da cewa ina son Adam, idan har na nuna ban damu ba, wasu ma ai sai su ce ina murna da rasuwarta ne, nima na dole ne kukan, amma mama ya aka yi ta mutu wai? Sannan ina ɗan da ta haifa ɗin?"

Mama ta kwaɓe baki ta ce "Mhmm, su suka san me suka yi mata dai, wai can in da ta tafi karatun a can ta zo haihuwa ta rasu, jiya nan suka zo da jaririn, ammma sun ƙi fito da shi yanzu, tun jiya ake fama amma Giwa taƙi faɗar in da yaron yake sai ɓoye shi take sai ka ce ciwo".

Samha ta jinjina kai ta ce "Taɓ a nan aka yi mata sutura kenan?".

"To waye ya ga gawarta, wai a can london ɗin ta mutu aka binneta, haka suka ce fa, ni ko yaushe ta yi cikinma oho, na ga dai tana can tana karatu, to can ya bita yayi mata cikin? Ko kuwa da cikin ta tafi Allah masani, saboda wata lalacewa ma, ita ya turata karatu ƙasar waje, ya zo yana nema ya haikewa iman".

Samha ta girgiza kai ta ce "Mama ba haka aka yi ba, batun iman wannan wani abu ne da Mummy ta shirya shi, amma yadda abubuwan ne suke wakana, akwai wani abu a ƙasa, amma dai bari na yi wanka na sauya kaya".

Ta tashi ta ɗau wayarta ta shiga banɗaki, lambar Khalifa ta nemo, ta kira shi, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.

Ba sallama ba komai ya ce "Ya akwai labari ne?"

"Eh kusan haka, Allah ya yi wa matar adam rasuwa ne".

"Na ji labari" ya katseta.

"A ina ka ji?".

"Kin manta fitacce ne shi? Labarin duk ya karaɗe dandanlin sada zumunta".

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, sai dai an ce a can london wai aka binneta, ba a kawo gawarta ba, sai jaririnta kawai".

Da sauri khalifa ya ce "What? Jariri kuma? How a wace maƙabartar aka binneta a London ɗin? Suwaye suka halarci jana'izar ta a can?"

"I don't know, nima abun da na zo na tarar kenan" ta bashi amsa.

Khalifa ya yi dariya ya ce "Shikenan, kin zo mini da labari mai daɗi, wannan ma wani abu ne na yaƙar adam".

"Amma dai ina fatan ba cutar da shi zaku yi ba, sannan ina son cire hannuna a contract ɗin nan, tun da ma dai wadda ta hanani rawar gaban hantsin ta mutu, ina ga na samu chance"

Khalifa ya ce "Haka ki ke gani?"

"Eh mana, babu abun da yayi saura ai"

"Ba zai yiwu ki saɓa yarjejeniyar mu haka kanki tsaye ba, dole ki kammala mini aikina".

A fusace samha ta ce "Kai saurara, ba fa 'yar ka ba ce ni, ka daina yi mini magana da isa kana bani umarni, ka kiyayeni" da haka ta kashe wayarta tana tsaki.

Kwanaki uku aka yi aka watse daga makokin aisha, sai dai adam sam baya hayyacinsa, kana kallonsa ka san a tashin hankali yake, ko abinci baya iya ci, haka yake tafiya gidansa, ya zauna ya saka kayan aisha a gaba yana kallonsu.
Ranar da suka rabu ya tuna, da zai yi tafiya, lokacin kwananta biyu da dawowa tana yi masa magiyar ya barta ta yi tafiya, ya din ga jan kumatunta yana yi mata dariya ya ce "Cikin nan naki ya sanya kumatunki ƙara cika, kuma sun fi daɗin wasa a haka" kwaɓe fuska ta yi za tayi masa kuka ta ce "Dan Allah ka mayar da maganata serious please ka bari na je".

"Ki bari idan na dawo da kaina zan kai ki, kin ji fulanina".

Kamar ƙaramar yarinya ta shiga turza ƙafarta za ta yi kuka ta ce "Dan Allah kar ta mutu ban je na dubata ba".

Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Bana son rigima fa, ke ba ki ga yadda cikinki ya tsufa ba, kin san hatsarine ki fita a san kin dawo, a sirri fa na bari ki ka dawo, tun da kin kasa riƙe kanki, sai kin dawo wurin mijinki"

Buɗe baki ta yi ta ce "Ni haka nace maka?"

Dariya yayi mata ya ce "Idan ma baki ce ba, yanayinki ya nuna ai, tun da ki ka dawo ko waje ban leƙa ba, soyayya kala-kala kawai nake sha, ki yi haƙuri jibi zan dawo in sha Allah sai na kai ki"

Idonta ne ya cika da hawaye, amam ya mayar da abun jokes, ya cigaba da ja mata kumatu yana kashe mata ido.

Da ya zo nan a tunaninsa ya durƙushe a kan gwiwoyinsa, yana kallon kujerar dressing mirror da ta zauna, suka yi wannan abu, da washegari ya ga message ɗin ta na ban haƙuri, a kan ba zata iya jiran dawowoarsa ba jikin kakarta ya tsananta da yawa.

Ya dinga zubar da hawaye yana surutai a hankali, wata irin kewarta tana ratsa shi.
Wani abu ne mai kama da bacci ya ɗauke shi, kawai sai ganin rumaisa ya yi a kan kujerar, tana zaune tana ta yi masa dariya, 'Sarki mai koriyar alkyabba, ka ɗananiba dokinka" tayi  masa maganar tana murmushi, daga bisani ta taso ta nufo shi, tare da miƙa masa hannu, ya miƙa hannunsa zai riƙo nata, kawai yayi firgigit ya farka yana kalle-kalle. Ɗan tsuke fuska ya yi, ya tuna yadda ya din ga fama rumaisa tana yi masa gizo a baya, da ƙyar ya daina ganinta, kwatsam yanzu ma ta cigaba da yi masa gizon, ba dan ya ganta tare da 'yan gidansu ba, to da babu shakka zai gazgata cewar aljana ce ita.

Kusan kwanaki ukun nan, rumaisa ta ƙi sakin jikinta, kusan kullum cikin kuka take a kan a dawo mata da jaririnta, tun mama tana ta tata har ta gaji ta ƙyaleta, abinci ma sai an yi kamar za a zaneta sannan take ci. 'yan islamiyyarsu tawaga guda suka yo, har da malamansu suka sake zuwa dubata, amma mirsisi taƙi kulasu, taƙi magana.

Kwanaki huɗu da sallamar su, mama ta ce wa usman yakamata su je gida su yi wa ammi gaisuwar rasuwar aisha.
Mai sunan baba na jin jaka ya ce bai yadda ba, kar su zata wani abun suke nema a wurnsu, tun da sun yi musu gaisuwar a asibiti ya isa.

Mama ta ce "Kai ka san ba zamu je wurinsu domin neman wani abu ba, amma dai-dai gwargwado sun yi ɗawainiya da ƙanwarku, kuma babu laifi dan an bisu gida an kuma yi musu gaisuwa, shi ne abun da yakamata ai, tun da rashi suka yi. Shi dai mai sunan baba ba haka ya so ba, amma babu yadda ya iya haka ya haƙura ya ƙyalesu.

Mama ya shirya ya saka rumaisa ta shirya, ta ce usman da Aliyu suka raka su, ruma sai murna take ko ba komai, zata ga Sabir, sai jin daɗi take yi, ta shirya cikin riga da hijjabi, sannan ta kawo face mask ta saka.
Usman ya ce "Meye kuma na rufe fuska?".

"Bana son a din ga kallona duk in da na je"

Ya ce "Ko kuma baki da gaskiya ba, ko kin yi wa wani laifi"

"Haba yaya usy, yaushe na dawo da zan nemi maganar ma".

Yayi murmushi ya ce "Ashe kina sane ki ke neman maganar"

Gyara zaman hijjabinta ta yi, ba tare da ta sake magana ba suka tafi.

Gidan galadima kuwa, ammi ta karɓo sabir, su iman sun kewayeshi suna kallonsa, yaron haƙurinsa har yayi yawa, ba ya kuka sai ya ga dama, sai dai yayi ta bacci.
Babu in da ya bar adam, kamarsa ɗaya sak da adam, an yi masa wanka an shirya shi, nusaiba tana bashi madara a feeder.

Iman ta ce "Allah sarki rayuwa, Allah ya yi wa anty aisha rahama, mun ci buri sosai a kan haihuwar nan, duk da yadda ake ɓoyewa ba a son a san da cikin, amma tayi buri a kan cikin, kusan kullum sai ta turo mini hoton siyayyar da ta yi wa baby".
Ammi ta ce "Rayuwar duniyar kenan, amma ba zan taɓa manta yadda aisha ta mutu ba, Allah ka kawo mana tsaro a ƙasarmu, ka ƙara kiyaye al'ummar musulmi" suka amsa da amin.

Adam ne ya yi sallama, suka amsa gaba ɗaya, su iman suka shiga gaishe shi, bai iya amsa musu ba sai jinjina musu kai kawai da yake yi.

Ya durƙusa ya gaida ammi. Ammi ta amsa masa tare da tambayarsa ya haƙuri.
Muryarsa a raunane ya ce "Alhamdilillah"

"Allah ya yi mata rahama, Sannan a cigaba da haƙuri duk mai rai mamaci ne". Ya jinjinawa ammi kai, tare da zura hannunsa a aljihunsa, Saboda vibrating da wayarsa ta fara.

Bai san mai lambar ba, amma ya ɗaga tare da yin sallama.

Aliyu amsa sannan ya ce "Aliyu ne yayan rumaisa, mun zo mu yi maka gaisuwa ne, mun shigo cikin gidan bamu san ina zamu bi ba, a wurin bashir na karɓi lambarka".

Adam ya ce "Ok babu damuwa, bari na zo gani nan" ya miƙe ya ce "Ammi ina zuwa".

Rumaisa kuwa riƙe ƙugu tayi tana ƙarewa harabar gidan su takawa kallo, ga motoci gefe guda kuma ga burgar dawakai, ko ina sai manyan bishiyu da ƙanana, sai kalle-kalle take kamar 'yar ƙauye, ga dogarai suna ta shiga suna fita, suna kaiwa da komowa a harabar.

Rumaisa ce ta fara hango adam ya nufo su, ya rame sai uban wuya, da dogon hanci, idon nan nasa jawur ya ƙaraso in da suke yana yi musu sannu da zuwa.
Risunawa ya yi ya ce "Mama sannu da zuwa, ya gida?".

Cikin kulawa mama ta ce "Lafiya lau, ya ƙarin haƙuri?"

"Alhamdilillah"

Haka ya bi su usman duk suka gaisa, amma bai kula ruma ba, ita ma ba ya kula shi ba.
Ya ce "mu shiga daga ciki"

Rumaisa dama tun da ya zo yana fara magana, ta wani juya ƙeya, irin ba ta ma san yana wurin ba, sai dai kamar yadda ta ga ya rame, haka shima ya ga tayi rama, ta fi cikowa kwanaki uku baya da aka sallameta daga asibiti.

Yayi musu jagora zuwa ciki, rumaisa ta gwalala ido, ganin kayan alatun da ke falon ammi, ya wuce da su babban falon, ya ratsa da su zuwa falon ammi, wanda bai kai wanda suka baro ba.

Yayi musu iznin su zauna, ya kira ɗaya daga cikin barorin ammi, ya ce a karɓi su rumaisa. Ya ce "Bari na yi wa ammin magana".

"To ina ɗana yake?" Ta yi maganar ba tare da ita kanta ta yi niyyar maganar ba.

Banza yayi mata bai kulata ba, sai da ya juya zai bar falon, sannan ya ce "Na kai shi koyo yadda ake gaida mutane"

Aliyu ya ce "Ai da abun duka ka samu ka zaneta wallahi, mara kunya kawai".

Adam yana barin falon, rumaisa ta miƙe tsaye, ta sake zama a kan kujerar ta ce "Wayyo laushi, Innalillahi kujerar nan ta ji katifa yasin, kujerar masu kuɗi daban take, har na tuna wata kujera da na gani a gidansu wata 'yar ajinmu, kujerar nan duk ƙashi, sai soso duk a waje, na ƙusa ta kusa tsarge mini mazaunai"

Usman ne ya talle mata ƙeya ya ce "Gaisuwa fa muka zo, ki ke yi mana surtu, shashasha" shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa kamar ta Allah.

Mama ta ce "Rumaisa yaushe ki canza halaye zuwa na banza ne? Dama haka na koya miki rashin gaida mutane ko?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ki yi haƙuri"

Aka zo aka din ga jere musu kayan abinci kala-kala, da na sha, ita dai rumaisa burinta ta ga Sabir.

Adam ya je ya tarar da ammi ta aiki su Nusaiba, daga ita sai sabir a ɗakin, ya ce "Ammi kin yi baƙi".

Ammi ta ce "Suwaye, na ce duk wanda yayi gaisuwa ya tafi ina son hutawa ne".

Rasa mai zai cewa ammi yayi, dan ko sunan rumaisa ba ya son kamawa, ya ce "Yarinyar nan ce, da mamanta da yayyenta suka zo yi mana gaisuwa".

Cikin rashin fahimta ammi ta ce "Wace yarinyar kenan?"

"Wannan yarinyar da ta zo da Sabir" Sabir ɗin ma da ya faɗa ji yake kamar ya kwafsa, kasancewar rumaisa ce ta sanya masa sunan.

Cikin fara'a ammi ta miƙe tana faɗin Allah sarki.

Adam ya karɓi Sabir a hannun ammi, da niyyar ya gwanyawa rumaisa, suka fito falon.

Ko ammi ba ta kalla ba, ta miƙe tsaye tana jiran Adam ya ƙaraso ta karɓi Sabir, amma ya canza hanya ya yi wani wurin. Ai ba su ankara ba rumaisa ta bi bayansa da gudu tana "Ka tsaya in ɗauke shi, ka zo ka bani ɗana".

Ayshercool.


paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*



Da fari bayan bayyanar rumaisa, mama ta zaci ruman nutsuwa ta ɗan ratsata, amma ina sai ta ga akasin abun da ta yi tsammani, halinta yana nan yadda yake, Aliyu na ƙwala mata kira amma ta rufawa takawa baya.
Murmushi ammi ta yi ta ce "Ƙyaleta, shi ma dai neman magana ne ya sanya ya ɗauke shi zai fice, da na san haka zai yi da ban bashi sabir ɗin ba".

Usman ya ce "Ai gara da ya hanata, ƙin gaishe shi ta yi, sai tambayarsa ina ɗan ta dan ba ta da kunya"

Mama ta girgiza kai ta ce "Rumaisa ai sai fatan Allah ya shirya. Hajiya ina wuni ina gajiya?" Ta yi maganar tana mayar da kallonta ga Ammi

Ammi ta ce "Lafiya lau Alhamdilillah, ya gida ya iyali?".

"Kowa lafiya ƙalau, ya kuma ƙarin haƙurinmu".

"Haƙuri mun gode Allah"

Mama ta ce "To Allah ya sa ta huta, Allah ya rahamsheta"

Ammi ta amsa da "amin ya rabb, ya jikin rumaisa kuwa ina fatan ta wartsake gaba ɗaya"

Mama ta ce "Jikinta dai da sauƙi, amma taƙi sakin jiki kullum kuka ita sabir, yau ne ma ta ɗan saki jiki har da hira da ta ji an ce za a zo gaisuwa".

Ammi ta ce "Allah sarki rumaisa, Allah dai ya bata haƙuri"

Hira suka ɗan shiga taɓawa da mama, har ammi take ɗan gutsura mata kaɗan daga cikin halin da take ciki, na dangane da ƙalubalen rasuwar aisha, daga ita har adam, haka nan ammi take jin yadda da mama a cikin ranta.

Rumaisa kuwa bin adam ta cigaba da yi, tana cewa ya bata ɗan ta, amma yayi banza da ita ya cigaba da tafiya.

"Wallahi idan ba ka tsaya ka bani ɗana ba, sai na yi maka ihu na tara maka mutane" bai ko tsaya ba balle ta sanya ran zai kulata. Kan ta ankara tuni ya sulale ta wata ƙofar ta neme shi ta rasa.

Komawa ta yi falon da ta baro su mama tana kuka.

Duk suka bita da ido, ammi ta ce "Rumaisa lafiya? Menene?"

Cikin kuka ta ce "Ba guduwa yayi da sabir ɗin ba, ina ta roƙonsa yaƙi kulani, ya bi ta wata ƙofa ya gudu"

Ammi ta ce "Subhanallah, takawa fa wasu lokutan ba shi da girma sai na jikinsa, bari kan ku tafi zai zo har nan ya sameni"

Mama ta ce "Rabu da ita, yanzun nan zamu tafi, can gida ina ta baƙi, yan dubiya da jaje"

Ammi ta ce "Allah sarki, na zata zaku wunar mini, baku ci komai ba fa"

"Wallahi karki damu"

Rumaisa ta ce "Dan Allah mama mu ɗan jira ko zai dawo ".

Aliyu ya ce "Ba in da zai dawo, ba dai ke fitsara ba, gara ayi maganinki ai"

Ammi ta yi murmushi ta ce "Yauwwa, dan Allah wata alfarma nake nema, idan Allah ya kaimu jibi, ina son a kawo mini rumaisa, za'a kaita wurin turaki, mahaifin aisha, abun da zai hana a kaita yanzu, haryanzu yana karɓar gaisuwa kuma yana cikin alhini, amma ya buƙaci ya ganta, ko zuwa jibi ne in Allah ya kaimu sai ko turowa na yi a ɗaukota".

Mama ta ce "Yayyenta za su rakota in Allah ya yarda, babu wata damuwa Allah ya yi mata rahama, ai ko bai nemeta ba ya ci taje ta yi masa gaisuwa "

Ammi ta yi ta yi wa mama godiya, da kanta ta raka su har harabar gidan, rumaisa kuwa sai kuka take yi, ammin tana bata haƙuri, tare da yi mata alwashin hukunta adam.

Ko da suka taho hanya, mita ta cigaba da yi tare da cewa da ta san ba zata ga Sabir ba da wallahi ba zata bi su ba, dan ita saboda sabir ta je.

Su Aliyu ne suka tanka mata, mama kuwa shiru ta yi mata, sai da suka je gida, ta dirar mata da faɗa, faɗan da tun da ta kuɓuta daga hannun yan ta'adda ba ta yi mata irinsa ba, sakamakon rashin hankalin da ta yi wa takawa yau.

Takawa kuwa ya kai awanni uku bai dawo ba, har wayarsa ammi ta din ga kira, yana ɗakinsa ya kulle kansa da shi da sabir, sai da ya daidaici su ruma sun tafi, sannan ya mayarwa da su iman sabir, ya fice ba tare da ya bari ya haɗu da ammi ba dan kar ta yi masa faɗa a kan abun da ya yi.

Yana fita gidansa ya wuce, ya je ya kulle kansa, ya kashe wayoyinsa, dan baya ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login