Showing 144001 words to 147000 words out of 224014 words

Chapter 49 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1118

ido, amma ta yi ta ƙoƙarin kar su zubo. Ya gama surutansa ya tashi ya tafi.

Kamar zata kifa haka take sauri, yau ko bari ba ta yi daren yayi ba, saboda yadda maganar ke mimtsininta ji take idan ba ta je ta kai rahoton ba, wani zai rigata.
Sashin Mummy ta isa, ta nemi iso aka yi mata, mummy na ganin yadda baba uwani ta shigo jiki na rawa ta san akwai magana, dan haka ta sallami barorinta, ya rage daga ita sai baba uwani. Ta dubeta ta ce  "Meyasa ki ka shigo mini a yanzu? Sai kin saka an fara zargin mu, ina fatan dai abun da ki ka zo mini da shi, mai muhimmanci ne ba shirme ba?"

"Allah ya baki yawan rai, wani ƙwai ne yake gangarowa daga kan dutse, kuma da alama idan ya fashe zai yi warin da zai addabi kowa".

Mummy ta yi ajiyar zuciya ta ce "Bani labari".

"Alamu sun nuna akwai wani abu da giwa take ɓoyewa ita da ɗan ta, dan tun jiya sun kasa sukuni, sun gaza zaune sun gaza tsaye, dan ita yau ta hana kowa ya je in da take har 'ya'yanta, shi ma kuma tun da ya fita shi da wani abokinsa bai kuma dawo ba, suna ta ƙumbiya-ƙumbiya, amma ina nan zan sanya ido, da na ji ƙyas zan kawo miki rahoto"

Mummy ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ta kaɗaice ta hana kowa zuwa in da take, ciki har da 'ya'yanta, lallai abun da yake cikin ƙwan nan, ba ƙarami bane ba, ki cigaba da sanya ido, ƙwan ya fashe a kan idonki, kuma da zarar ya fashe ina son ki riga kowa sani, ya kuma nice wadda za ta fara jin ko menene, ina nan ina jiranki, haka zalika nima zan sanya ido a nawa ɓangaren"

"Allah ya baki masara, in Allah ya yarda za ayi duk abun da ki ka ce, na barki lafiya" Mummy ta ɗaga mata hannu alamar zata iya tafiya.

Baba uwani ta tashi tana murnar yadda ta sanya farantawa uwar ɗakinta ta ɓoye.

Unguwar su ruma ta ɗauka cewar ta dawo, magana har islamiyyar su, gaba ɗaya unguwa ta ɗauka, aka din ga yi musu addu'a da tayasu murna.
Huzaifa ne yayi hankalin cewa a kira katsina a waya a sanar musu da anga rumaisa, dan gaba ɗaya ma sun manta da batun su.
Sai da mai sunan Baba ya kai mama ta ga nata likitan, sannan suka tafi Asibitin da rumaisa take.
Gaba ɗaya rumaisa ta kasa daina kuka, saboda farincikin ganin 'yan uwanta gaba ɗaya a tare da ita, da ta motsa a tambayeta me take buƙata.

'yan uwa da abokan arziki kuwa da maƙwabta tuni suka fara sintiri a asibitin, domin duba ruma, kowa yazo da ɗan abun alkhairinsa da zai bawa rumaisa.

'yan uwansu na kano kuwa suma tuni suka cika asibitin, wannan su zo wannan su tafi, sai ga hauwwaliya ma sun zo da sandarta ta dogarawa, kasancewar tun karayar da ta yi kan a sace rumaisa ba ta warke ba. Suka rungume juna.

Ruma ta ce "Hauwwaliya gurguwa ki ka zama ne? Na ganki da sanduna"

Hauwwaliya ta ce "Ke ba gurguwa na zama ba, kin manta na karye ne?"

Ruma ta ce "Au haka ne fa, ban zo na ganki ba ma fa aka saceni".

"Allah sarki rumaisa, kin ga idi, zaman hannun 'yan bindiga an ce wahala ake sha fa"
Ruma ta yamutsa fuska ta ce"daina tuna mini dan Allah, wuya ko da magani babu daɗi"

Likita ne yayi sallama shi da nurse, mama ta yi musu sannu da zuwa, mai asibitin ne da kansa ya kalli ruma ya ce "Sai ka ce mun kwantar da shugaban ƙasa, 'yan dubiya daga wannan sai wancan, kamar ba wani mara lafiya sai ke" ruma tayi murmushi tana kallon trolleyn da suka shigo da ita, tana fatan ba za ayi mata allura ba.

Yayi murmushi ya ce "To yaya jikin naki?"

"Da sauƙi, amma haƙarƙarina fa yana mini ciwo haryanzu"

Ya ce "Mu ga wurin, ya aka yi haƙarƙarin yake yi miki ciwo?"

"Sule ne ya takani a wurin, wani jibgege, nauyin ƙafarsa kamar tsauni". Yayi murmushi yana ƙoƙarin miƙa hannunsa ya ɗaga rigarta ya duba, amma ta riƙe rigar ta tsareshi da ido.

"Dubawa zan yi na gani"

Aliyu ne ya taso, ya kama rigar tata zai ɗaga "Yaya Aliyu ni kar ka buɗe mini jiki a ganni"

Aliyu ya ce "Ke dallacan, ina tsintoki a ka yi kanki ko ɗan kwali babu, wa zaki yi wa iyayi? Ko shi wanda ya taka kin kin yi masa iyayin?"

Tana zumɓura baki ya ɗaga rigar, likitan ya danna haƙarƙarin, ta saki wani marayan kuka.

Ya ce "Is ok, zan rubuta muku hoto in sha Allah, ayi mini hoton wurin, da kuma kanki".

"Wurin mai hoto za a kai ni? Ayi mini a waya mana, bana son motsawa ko ina ns jikina ciwo yake"

Ya girgiza mata kai ya ce "X-ray nake nufi, ba hoton passion ba, sauko yau ki taka ƙafar nan na gani" ta girgiza masa kai ta ce "Tana yi mini ciwo fa"

"Sai fa kin taka yau saukko, da yayi ki ka yi gudu ki ka fito daga daji?".

Shiru ta yi sannan ta ce "Ikon Allah ne ya fito da ni" ta fara ƙoƙarin saukowa a hankali ta tsaya a kan ƙafarta. Likitan ya ce "Good, taka a hankali mu gani". Tana ƙoƙarin ɗaga ƙafar, amma ji take kamar ba a jikinta take ba, dan haka ta kasa.

Likitan ya ce "Riƙe hannuna, ki ɗaga ƙafar a hankali, bana son ganinki a kwance kullum"

Noƙe kafaɗa tayi, ita ba zata riƙe hannunsa ba.

Ya saka hannu ya riƙo na ta hannun, ya ɗan ja ta sai da ta ɗaga ƙafar sai da ta yi ƙara saboda ciwon da ƙafar take yi.

Usman ne ya taso, ya cire hannun ruma da ga na likitan ya ce "Zamu zagaya da ita in sha Allah, in dai ƙafar ce zata din ga takata" murmushi yayi ya girgiza kai, ƙiri-ƙiri ba sa iya ɓoye kishinsu a kan ƙanwarsu, zai duba mata rauni, Aliyu ya taso ya buɗe masa da kansa, yanzu kuma Usman ya zare hannun ruma daga nasa.

Ya rubuta musu duk abun da yake so a kawo masa, ya fita daga ɗakin.

Hauwwaliya ta dogaro sandarta, Usman kuma yana riƙe da rumaisa suka fita zagaya asibiti.

A hankali rumaisa tana takawa, har suka je ɗakin da jaririnta ke kwance, nurses na kula da shi, sune suke yi masa komai. Ruma ta daɗe a wurinsa, sanann suka fito, a wurin komawa ɗakimta kuma ƙafa taƙi takuwa, ƙarshe sai Goyata Usman yayi ya mayar da ita ɗaki.

Ammi ba ta fito ba sai la'asar, shi ma da ta fito tea kawai ta saka a kai mata, shi kawai ta iya sha, kai da ka ganta ka san a tashin hankali take.
Wayar Adam take ta kira amma ba ta shiga.

Ta fito falo ta tambayi barorinta ko Adam ya shigo? Suka ce mata tun safe da ta raka shi ya fita, bai kuma dawowa ba.
Ammi ba ta samu wayar Adam ba sai magariba.

"Ina ka ajiye wayarka nake ta kira amma ba ta shiga?".

"Ammi na kashe wayar ne, saboda bana son a dameni da kiran waya".

"Wannan ba hujja bace, ka san dole zan neme ka ai, ya ake ciki akwai wani abu ne, ko yarinyar ta yi magana a kan Aisha?"

Kamar yana gaban Ammi, ya girgiza kai ya ce 'Ta ƙi magana, ta ce bata san komai ba".

Cikin rashin fahimta Ammi ta ce "Kamar yaya?"

"Haka dai ta ce"

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ka zo ka sameni, asibitin zamu tafi yanzu ".

Ya sauke numfashi ya ce "To gani nan" ya ajiye wayar yana jin yadda kan sa ke sara masa, saboda damuwa da tunani.

Sai kusan ƙarfe tara na dare sannan Takawa ya zo tafiya da ammi, sai a lokacin su Iman suka samu damar ganin ammi.

Cikin damuwa Iman ta ce "Ammi ina zaki?, yau gaba ɗaya bamu ganki ba"

Cikin ƙarfin hali Ammi ta ce "Ku yi haƙuri, wata unguwa zamu je, yanzun nan zamu dawo ba daɗewa zamu yi ba" daga haka ta yi gaba ta bi bayan takawa suka fice.

Iman ta ce "Yaya Nusaiba, akwai matsala fa, Ammi suna ɓoye mana wani abu ba sa son mu sani".

Nusaiba ta ce "Nima na gani, amma bari mu jira mu gani".

Ita iman abubuwan sun yi mata yawa, ga maganganun wambai, ga zancen da yake yawo a kan su da takawa, ga abun da take gudu Jabir ya furta wai yana son ta.

Kamar kurame haka su Ammi suka ƙarasa Asibitin da rumaisa take.

'Yan dubiya duk sun watse, sai Mama da Abdallah mai sunan baba suna ta shirin tafiya gida, Mama ta wanke jaririn nan tas, an haɗa madara an bashi, ya gama sha ruma tana rungume da shi, tana kallonsa tana tuna irin yadda suka sha gwagwarmaya kan su kuɓuta.

A hanyar barin asibitin, mai sunan Baba suka haɗu da Adam da Ammi, ɗan kallon kallo suka yi da shi da takawa, amma babu wanda ya kula wani, suka wuce.

Sallamar su Ammi ce ta dawo da rumaisa daga tunanin da take yi, ta ɗaga kai ta kallesu ba tare da ta amsa sallamar ba, Abdallah da mama suka amsa suna yi musu barka da zuwa.

Ruma ta ɗan ƙare musu kallo, fuskar takawa kamar ta mai amai da gudawa, duk yayi wani iri, mama ta basu wurin zama, suka gaggaisa ammi ta dubi ruma ta ce "Maman baby ba magana?"

"Ina wuni" Ammi ta ce "Lafiya lau, ya jiki ya baby kuma?"

"Lafiya lau".

Ammi ta ce "To Alhamdilillah"

Mama ta ce "Jiki da sauƙi kam, domin yau har ta tattaka, gobe in Allah ya kaimu zamu je mu kaita hoton ƙafar da kai, da kuma haƙarƙari da take kuka da shi".

Ammi ta ce "Allah sarki, karki damu, zan aiko s kaita".

Mama ta ce "A'a kar ɗawainiyar ta yi yawa, zamu kaita in sha Allah"

Ammi ta ce "Ɗawainiya ta wuce tserato wa da ta yi da wannan jaririn, ai duk abun da muka yi mata bamu faɗi ba".

Mama ta ce "Rumaisa kawo jaririn su ganshi mana".

"Amma mama kar ki bashi ɗana"

Mama ta ce "Shi wa?"

"Wancan mutumin" tayi maganar ba tare da ta kalli Adam ba.

Guntun tsaki mama ta yi, ta karɓi jaririn, ta miƙawa Ammi shi, Ammi ta karɓe shi tana murmushi tana ƙare wa yaron kallo, kamannin adam ne sak yaron ya kwaso.

Ta dubi ruma ta ce "To maman baby, ba a saka masa suna ba haryanzu?".

Ruma ta ce "Na saka masa suna, sunansa Mahmud!" A tare Ammi da Adam, suka ɗago suka kalli rumaisa, ita kuwa ta basar dan ba ta san me ta yi ba.

Paid book ne ₦500, via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Ayshercool.
08081012243










https://chat.whatsapp.com/G9XU8tDJMjq02zlZMHurZ5*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*








*₦500 ne, via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*



Ammi sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ita aishan ce ta saka masa wannan sunan?"

Ruma ta ce "A'a, ni na saka masa, sunan babana ne, ina son sunan sosai"

"Ba shi ne sunan da na yi niyyar sakawa ɗana ba, ba zan saka wannan sunan ba" Takawa yayi maganar cike da iko, sai da mama ta ɗan ji babu daɗi, ko da zai canza sunan bai kamata ya faɗa a gaban ruma haka ba, ba za ta ji daɗi ba.

"Ka ga ba fa ɗanka bane ba, tun da ni ta ce ta barwa shi, ɗana ne Mahmud na saka masa, kuma ba zan canza ba" ta yi maganar tana yi masa kallon banza.

Ammi ta ce "Madalla, suna mai girma da karama, Ubangiji Allah ya raya Mahmud, ta zauna maman baby, mun karɓi sunan" kallon da Ammi ta yi wa takawa ne ya sanya shi haɗiye maganar da yayi niyyar yi.

Ammi ta dubi ruma ta ce "Rumaisa, Haryanzu baki gaya mana ya ki ka baro aisha ba? akwai buƙatar ki bawa Adam haɗin kai wurin amsa tambayoyin da zai yi miki, tun da shi ma jami'in tsaro ne. Yaya Aisha take? Ya aka yi ki ka fito da ke da jaririn babu ita?"

Rumaisa ta ɗan yi shiru tana wasa da gefen bedsheet ɗin da take kai, hawaye ya taru a idonta, sai dai babu tsammani ta yi ƙara tana kare fuskarta da hannunta, da sauri mama ta ƙarasa wurinta tana tambayarta ko lafiya?.

Jikin ruma sai rawa yake yi, ta rungume mama tana ɓoye fuskarta.

Mama ta ce "Rumaisa ki yi magana mana, menene?"
Ruma ta ɗago a hankali tana duba jikinta ta ce "Sha tara ne ya harbe wani mutum jininsa ya ɓata mini jiki".

Jiki a sanyaye mama ta ce "A asibiti fa ki ke a tare da mu, duba ki gani, jikinki babu komai babu jini" mama tayi maganar tana nuna mata rigarta, sai dai duk da haka ruma sai haki take kamar ta yi gudu.

Ammi ta ce "Haryanzu akwai sauran razani a tare da ita, dole ta razana tun da ki ka ga haka, Allah kaɗai ya san abubuwan da ta gani. Bari mu tafi ta samu ta huta, sai dai duk da ban san zuwa yaushe za a salleme ku ba da yaron nan, zan roƙi alfarmar ku, ya ɗan zauna a wurinku kan a sallami rumaisa, muna ƙoƙarin shawo kan wata matsala ne, kan mu kai shi gida kowa ya sani" abun ya ɗan ɗaurewa mama kai, wace irin matsala kenan? Amma ba ta tambaya ba ta ce "A'a babu damuwa, Ubangiji Allah ya raya mana shi a bisa tafarkin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam".

Ruma daga kwance ta ce "Ni fa ba wanda zan bawa ɗana, ɗana ne fa".

Ammi ta ƙarasa gaban gadon ruma, ta shafi kanta ta ce "Dama naki ne, aro zaki bamu ai, Allah ya baki lafiya ya tsare gaba" ta yi maganar tana murmushi.

Ruma ta amsa da Amin, daga nan suka yi sallama suka tafi.

Suna tafe a hanya Ammi ta ce "Gaskiya akwai matsala, idan har yarinyar nan ba ta yi bayani ba, dole mu nemi yadda zamu yi"

Takawa ya ce "Ammi, ni fa na riga na gama shirin tarar kowane irin ƙalubale zan fuskanta, na san duk yadda muka kai ga ɓoye lamarin nan, nan kusa zai baiyyana, ko da a yanzu ma kalli a halin da nake ciki, kuma kar ki manta, da dogarai uku ki ka zo wurin nan, a gabansu aka faɗi komai, na san a kowane lokaci maganar nan zata watsu".

Ammi ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Lokacin da Abokin ka bashir ya yi mini waya, babu halin in fita nikaɗai, kuma ban san kiran me yayi mini ba, wannan dalilin ne ya sanya na tafi da su, kuma jiya na ja musu kunne a kan su yi shiru da bakinsu".

Ya girgiza kai ya ce "Ammi, kin manta gidan nan ne, lokacin da aka fitar da zancen ina shaye-shaye na yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login