Showing 210001 words to 213000 words out of 224014 words

Chapter 71 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1066

din ga bin Adam da kallo, da mamakin ina suka samo Adam.

Adam ya dubi malam shamsu ya ce "Kai kuma, daga yanzu idan zaka yi gulmar, ka din ga nunawa mutanen unguwar ni, ka ce nine wanda yayi mata cikin shegen ta haifa, ta dawo ya karɓi abun sa, idan da wanda zai ɗau mataki a kan hakan ƙofa a buɗe take. A saya mini shi a ceil, sai na waiwaye shi"

Cikin tashin hankali ya ce "Dan Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama ka yi haƙuri, ka yafe mini, wallahi kuskure ne"

Adam ya ce "Kai Yanzu wannan da ko magana ma ba ta iya yi ba, ba ta san ma'anar abunda ake faɗa ba, ta yi maka kama da mai cikin shege? Ƙaddara ƴar ka ce zaka je kana faɗar wannan maganar?"

Ya sunkuyar da kai yana girgiza wa.

"Ko da wasa, ka kuma gaya mata wannan mummunar maganar, sunana Adam Sharif Galadima, zaka ga abun da zai biyo baya"

Ware ido malam shamsu ya yi, a radio yake jin sunan Adam, sai kuma ya san shi ne mamallakin katafaren gidan gonar da yake cikin unguwar, cikin tsuma ya ce "In sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, tsautsayi ne"

Duk da wannan abun da Adam ya yi wa rumaisa bai burgeta ba, aka bawa Aliyu kayan sa, suka fito daga station ɗin, Adam ya rungumo Aliyu suka fito, Usman ya riƙo rumaisa, mai sunan baba ya fito shikaɗai ya kama gabansa.

Cikin motar Adam suka shiga, ya kunna suka fita, suna tafe ya ce "Aliyu, dan Allah daga yau komai za ta tsoka no, ku ƙyaleta ita kaɗai ko zaneta ne ayi, ka ga yanzu haka kurum ta janyo maka kwanan ceil"

Aliyu ya ce "Ba ayi haka ba babban yaya, tuba muke yi"

"Ai ni ko ba a tare mini faɗa ba, ina da ƙarfi"

"Rufen baki ko na cillaki ta tagar nan" Usman yayi maganar yana nuna mata taga.

Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, Adam da Aliyu kuma suna taɓa hira, rumaisa har mamaki take yadda yau Adam ya buɗe baki yana magana haka da Aliyu.

A ƙofar gidan su rumaisa Adam yayi parking, Aliyu ya yi ta masa godiya, Adam ya ce "Ka daina wannan godiyar mana, kar ka saka na ji kunya, ai kai nawa ne Aliyu a gaida mama" suka yi musabaha ya fita, Usman ya buɗe motar ya fita, rumaisa har ta fita Adam ya ce "Ke tsaya, Ammi ta bani saƙo na baki"

Rumaisa ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Sunana rumaisa, ba ke ba" yai kamar bai ji ta ba, ya ɗauko ledar wurin ammi ya miƙa mata, ta ƙare masa kallo ta ce "Ni ammi ba ta ce za a kawo mini wani saƙo ba, ni ba zan karɓa ba, duk wani abu da ya fito daga wurinka bana so, balle nan gaba ka ce mini kwaɗayayyiya, gidanku da nake zuwa saboda sabir ma, a dole na haƙura, saboda gorin da ka yi mini, ina ji ina gani ina ƙaunar ɗana, amma ka saka na yi zuciya na daina ganinsa, ni ba zan karɓi abunka ba" ta tsallaka ta shige gida ta bar shi da kayan a hannu.

Ayshercool.
Chat me on what's app, to subscribe yours.
08081012143

PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143.




Sororo ya bi rumaisa da kallo, dan ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, ba ya son mama ta fito ta ce za ta yi masa godiya, dan haka ya shige motarsa ya ja ya bar ƙofar gidan.

Mama kuwa murna ta din ga yi da ta ga Aliyu, nan da nan ta ce Yasir ya ɗora masa ruwan wanka, ta kalli Usman ta ce "Ina yake, na yi masa godiya?"

Rumaisa ta ce "Ai ya tafi" mama ta harareta ta yi mata shiru, dan haryanzu ba ta huce ba, da abun da rumaisan ta aikata.

Usman ya ce "Ina saƙon da na ji ya ce ki tsaya ki karɓa?"

Ta kwaɓe fuska ta ce "Ni ban karɓa ba, cewa na yi ya koma da abun sa ba na so"

Cikin takaici ya ce "Dalla matsa ƴar baƙin ciki, ke da ba roƙarsa ki ka yi ba, kawai sai ki ƙi karɓowa"

"Taɓ, haka kurum yayi mini gori wataran"

"Uban waye ya ce miki wanda aka haifa a cikin arziki yana gori? Ai idan kin ga mai kuɗi yayi gori, to dama matsiyaci ne, daga baya yayi arzikin kuma wataƙila a tsiyarsa zai mutu" ba wani fahimtar abun da yake faɗa ta yi ba, ta shiga harkokin ta. Sai dai ta kasa sakin jikinta, duba da yadda mama ta haɗe rai, taƙi kulata.

Aliyu ya yi ta basu labarin irin abubuwan da malam shamsu ya din ga faɗa a kansu da rumaisa, na ɓatanci da yadda ya ziga a ka kulleshi, duk ba a same shi da makami ko wani laifi ba.

Usman ya ce "Gajiyayyen wahalalle, irinsu ne masu ƙarewa a tsiya, kuma idan bai yi wasa ba, sai na ɗaga shi na buga da ƙasa. Ai ni abun da gayen nan yayi masa ya burgeni wallahi, da ya ce shi ne uban ɗan kuma ya karɓi abun sa".

Rumaisa ta yi farat ta ce "Yauwwa, na ji ya ce wai shi ne yayi mini cikin, to dama shi cikin yin sa ake yi, yi wa mutum ciki ake yi"

Aliyu ya ce "Bismillahi, ashe haryanzu hankalin da saura".

Ganin kowa ya yi mata shiru ya sanya ta ce "Yaya usy baka bani amsa ba".

"To me zan ce miki, wai ke haryanzu kanki a tukunya yake, baki san meye rayuwa ba, baki san me yakamata ki din ga tambaya ba, Allah ya sa mai sunan baba ya ji ki, shi sai ya baki amsa"

"To me na yi daga tambaya?"

"Idan kun yi auren sai ya baki amsar"

Aliyu ya kalli usman ya ce "Kai fa wasu lokutan sai a hankali, kai ba ka ji kunya ba kake gaya mata hakan?".

"To yaya zan yi mata bayani, ita kai kamar computer abun da ka zuba mata kawai shi ta sani, idan suka yi auren ai aikace za ta gani"

Aliyu ya ce "Kaii usman lafiyarka kuwa? Kar ka gurɓata mata tunani malam"

Mama da ke ɗakin ta ce "Ke, ki taso ki zo ki kunno mini maganin sauro" mama ta kirata, dan katse waccan hirar da suke yi, dan idan aka zurafafa rumaisan ba ganewa zata yi ba, kuma wani zancen za ta ɓallo.

***
Yanayin fuskar Ammi kawai ya kalla, ya san akwai matsala.

A nutse ya ce "Ammi na dawo"

Ta kalleshi, ta kalli ledar hannunsa ta ce "Wannan ledar fa?"

Ya kalli ledar ya ce "Saƙon da ki ka bani ne, ta ƙi karɓa"

"Saboda me?" Ammi ta tambayeshi cike da tuhuma.

"Ta ce baku yi waya ba, baki ce mata zaki aika mata da saƙo ba, dan haka ba zata karɓi abun hannuna ba na zo daga na yi mata gori wataran"

Ɗan jimm ta yi, ta wani fannin rumaisa tana da gaskiya, kuma ammi ta sake jinjina lallai rumaisa tana da tarbiyya.

"Dole fa ka sauke wannan shan ƙamshin, da sarautar ka dawo dai-dai level ɗin ta, domin ku fuskanci juna kai da ita, dan ba zan lamunci ku yi aure, ku din ga zaman doya da manja ba, kamar wasu maƙiya"

Adam ya ce "To in sha Allah" dan ya rasa mai zai cewa ammin.

Ta sake nisawa ta ce "Sannan na ji abun da ka aikata, Jamila ta zo har falon nan ta nuna ni da yatsa, ka saka mota zaka kashe mata ɗa, adam ƙiyayyar da ka ke yi wa ɗan uwanka har ta kai haka dama? Ka yi yinƙurin kashe shi?"

Adam ya yi shiru, ba tare da ƙoƙarin kare kansa ba.

"Kai a rayuwarka duk yadda nake tausaya maka, da yin iya ƙoƙarina a kan ka, baka gani ko? Kullum burinka ka tsokano abun da za ayi ta yi mana surutu, saboda wannan zafin zuciyar ta ka ko? Gobe in Allah ya kaimu ka je ka yi masa sannu, sannan ka bata haƙuri, magana kuma har ta kai kunnen wambai yana nemanka"

Dam ƙirjin Adam ya buga, ya je ya duba Mahmud, ya bawa Mummy haƙuri, sannan wambai yana nemansa.

Cikin dakiya ya ce "To, in sha Allah duk za a yi" ya juya ya fice daga ɗakin.

Ko abinci kasa ci yayi, abubuwa sun yi masa zafi sosai kwanan nan, ya tara ayyuka sosai a office, gashi duk iya binciken da yake ya gano, ko garkuwa da aisha shiri ne ya kasa samun komai, amma wasu daga cikin bayanan rumaisa, na nuni kamar da akwai wani abu a ƙasa,gata gardamammiya ya san idan jajjagenta zai yi ba zata yi magana ba, sai ta ga dama. Ga wannan batun auren nasa da ammi ta sako shi a gaba a ƴan kwanakin nan, babu damar ya motsa, sai ta yi zancen rumaisa, shi gaba ɗaya baya farin ciki da wannan auren.
Ga surutan da ake ta yi a kansa a media, kullum ƙazafi kala-kala, ayyukansa da ya ɗauko kan sace Aisha hankalinsa ya rabu biyu duk yayi sanyi, bai samu sun kammalu ba, tun sa shi ne jagoran aikin.

Ji yayi kansa ya fara ciwo, ga wani irin jiri da ya fara ɗibarsa daga zaune, a hankali ya ja jikinsa ya kwanta, gaba ɗaya bai san ta ina zai fara ba da matsalolin nasa.

***
Yau mama ko sallar asuba ba ta tashi ruma ba, sai da Usman ya tsula mata wayar caji a ƙafa ta tashi, ta yo alwala ta yi salla, ta gaida mama, amma maman taƙi amsawa.

"Mama wai dan Allah ba zaki kulani ba?" Ta yi maganar cikin damuwa.

"In kulaki in ce miki me? Ai ki je ki yi rayuwarki ruma nima zan yi tawa, ƴaƴana suna buƙatar rayuwata, ɓacin ranki ba zai ƙarasani ba, na yi magana a samo langa-langa ayi miki ɗakinki, dan ba zan cigaba da zama ɗaki ɗaya da ke, kina zucguna mini ba"

Ba ƙaramin mamaki mama ta bawa rumaisa ba, dan a ganinta mama ta daina sonta, ta tashi jiki a sanyaye, ta je yi shirin makaranta, ta tafi ba tare da ta sake kula mama ba, sai dai abun yayi ta damunta, ga wani irin son ganin sabir da take yi, ga kuma alwashin da ta ci a kan sa.

Ita kanta wasu fitintinun da take yi, tana son ta daina amma Allah ya gani, ba za a taɓa ta ta ƙyale ba.

Adam kuwa, Yau kamar wanda aka gayawa wani mummunan saƙo haka yake jin sa, komai ba ya yi masa daɗi, tasbihi kawai yake yi ko ya samu sassauci, ammi kuma ta sake nanata masa cewar ya je ya aiwatar da abun da ta ce na bawa Mummy haƙuri da duba Mahmud domin komai ya wuce.

Ba a son ransa ba sai domin cika umarnin ammi, ya nufi sashin Mummy.

Sai dai da ya tambayi Fauziyya, ta ce masa suna ɗakin Mahmud.

Kai tsaye bai jira wani iso ba, ya shiga sashin da Mahmud yake, yana zaune a kan gado, an ɗaure ƙafarsa da bandeji, da alama ƙashin ƙafar ya taɓu, amma ba irin so serious ɗin nan ba.
Mummy na gefen Mahmud tana takura shi ya ci abinci.

Mummy ta wani haɗe rai, Mahmud ya yi wa Adam kallo ɗaya, ya mayar kan abincinsa, aka rasa wanda zai amsa masa sallamar da yayi.

Hakan ba ƙatamkn ƙulara da shi ya yi ba , ya ji kamar yayi ficewarsa, amma ya san makircin Mummy.

Ya dubi Mummy ya ce "Na ji baki ji daɗin abun da ya faru ba, am sorry for it, shi kuma Allah ya bashi lafiya" ya juya zai fita Mummy ta ce "Dan Allah Adam wace irin ƙiyayyace kake nuna mana haka? Har ka taka ɗan uwanka da mota, meyake damunka ne?"

"Ba mayar da magana, ko bibiyar tarihi na zo mu yi ba, na baki haƙuri kar a sake saka mahaifiyata a duk wani abu da zan yi, ni na yi laifi ba ita ba"

"Amma Adam ni kake gayawa haka? Da na isa da kai, ko giwa ta nuna maka ina da muhimmanci a wurinka ai da ban tunkareta ba, kai zan yi wa sanin yi maka maganar ba shi da amfani, ba zaka saurara ba ya sanya na sameta".

"Kuma shine har da gayawa wambai? Idan haka ne maiyasa maganar ba ta tsaya iya nan ba?"

"Magana ake yi ta rai fa adam, yinƙurin taka shi da mota ka yi".

Mahmud ya ce "Mummy ki ƙyale shi dan Allah, kin san abnormal yake, kuma ko da ya takani da mota, za a iya ɓugewa da cewa ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa, sai dai zan sake ɗaukar nauyi, gidan jaridar fallasa su wallafa cewa ka yi yinƙirin takani da mota ka kashe ni" Mahmud yayi maganar cikin zunzurutun izgilanci.

A zafafe Adam ya juyo, ya ɓarar da kayan abincin, ya shaƙe Mahmud zuciyarsa na tafasa.

Mahmud ya kalli cikin idon Adam ya ce "Ka daina jin haushi idan an ce baka da lafiyar ƙwaƙwalwa, duk mutumin da bai iya sarrafa fushinsa ba, ƙwaƙwalwarsa babu lafiya ".

"Kai adam, ka cika shi kar ka kashe shi mana, jama'a ba kowa a kusa ne?" Mummy ta fara kwarmato.

Sanin cewa mutuncinsa zai sake zubewa, muddin aka sake zuwa aka gansu a yanayi mara daɗi shi da Mahmud, kuma ran ammi zai sake ɓaci, ya sanya shi sakin Mahmud, ya fice da sauri.

***
Maƙwabta suka yi ta shigowa yi wa mama jajen abun da ya faru, na kama Aliyu, sai dai a wannan karon mama a tsorace take da mutanen, dan kar su je su yi musu wani sharrin.

Rumaisa ta saba sa ta dawo, mama za ta ce mata, ga ruwan wanka ta wanke wannan gumin da ƙarin ranar, idan an gama abinci ta ci ta yi salla ta tafi islamiyya, amma yau ta dawo ba ruwan wanka, ga mama ba ta kulata ba, haka ta yi abun da zata yi ta tafi islamiyya.

A ƙa'ida, ta kan ci abinci sau huɗu zuwa sama a rana, ba wai abincin take tsayar da hankalinta ta ci ba, zaɓe-zaɓe ne da ita, ga irin cin abincin yara take yi, tana ci tana wasa, ko da ta fara ta ce ta ƙoshi. Kullum ta dawo daga islamiyya sai ta ci abincin yamma, sai dai a yau ɗin ma mama ba ta ajiye mata abincin ba, gashi bata mayar da hankali ta ci na rana sosai ba, bugu da ƙari ta ga mama ta ɗora tuwo a matsayin abincin dare.

Ba ta kula kowa ba, sai kukanta suka jiyo a ɗaki, Usman ya leƙa, ya tarar ta kwaso kayanta, tana ta ninkewa tana zubawa a bagco tana kuka, kamar mai shirin yin yaji.

Cikin mamaki ya ce "Ke! Meye haka?"

"Haɗa kayana nake yi, cikin dare idan kowa yayi bacci in bar gidan nan, tun da dai ba a ƙaunata" maimakon ya ji haushinta, wata uwar dariya ce ma ta kama shi.

"Waye ba ya ƙaunar ta ki?".

"Ba mama ce ba, ta daina kulani, wallahi duk faɗan da aka yi da ni nice mai gaskiya, ya za ayi ace in sayo sigari? Kuma dan meyasa wannan shamsiyyar zasu din ga ce mini ƴar iska, sai ayi ta yi mini abu ba zan rama ba"

Usman cikin salon tsokana ya ce "Gaskiya babu daɗi kam, yanzu to ina zaki tafi?"

"Tun da ba a sona a gidan nan, katsina zan koma wurin ƴan bindigar, wurin su barde, au ashe an kashe barde to dai daji zan koma na yi bukka na zauna a ciki" ta yi maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.

Usman kamar ya shiɗe dan dariya, Aliyu da su Huzaifa kansu dariya suke yi mata.

Aliyu ya ce "Mama ki yi biko, saboda ke za ayi yaji"

Mama ta ce "Idan ta tafi nima na huta, Allah ya raka taki gona, ku ƙara mata kuɗin mota".

Jin furucin mama ya sanya ta sake tunzura tana kuka ta ce "Shikenan, bakomai"

Ta ɗauko bagconta tana kuka, Huzaifa ya ce "Allah sarki rumaisa, zamu yi kewarki sai a darul salam" ta sake fashewa da kuka.

Yasir ya ce "Rumaisa a yafi juna, Duk in da ki ka je ki zauna lafiya da mutane, koda yake ai kin ce a bukka zaki zauna ke kaɗai, Allah ya kiyaye hanya ga wannan" ya baya naira ɗari. Ta saka hannu ta karɓa, suka cigaba da tuntsra mata dariya, ita kuma bil haƙƙi da gaske barin gidan za ta yi.

Ta waiwaya tana kallon mama, ta ga mama ko a jikinta, jajjagenta ma take yi, ta nufi hanyar soro.

Abdallah ya ce "Yarinyar nan fa ba hankali ne ya game jikinta ba, bari na bi bayanta.

Ta dafe kayanta ta fita waje, ta tsaya tana tunanin wace hanya za ta bi, kamar sama sai ga mai sunan baba.

Ya kalleta ya ce "Meye haka? Ina zaki? Kukan me ki ke yi?" Ya jejjero mata tambayoyin.

"Tafiya zan yi" ta faɗa tana share hawaye.

A kausashe ya ce "Zuwa ina?"

"Mama ba ta so na, kowa ya tsaneni shi ne na ce barin gidan zan yi, an bani kuɗin mota ma" tayi maganar tana nuna masa kuɗin hannunta.

Takaici ne ya ƙule mai sunan baba, gaba ɗaya rumaisa ba ta da wayo wasu lokutan cikin takaici ya ce "Dalla wuce ko na mareki"
Za ta yi Magana, ya daka mata tsawa zai kai mata duka, ta taka da gudu ta koma cikin gida.

Abdallah da ya biyo bayanta kuwa, dariya kamar zai shiɗe.

Mai sunan baba ya biyo bayanta zuwa gidan, su Usman ya saka a gaba ya din ga yi musu masifa, saboda sun bar rumaisa ta fita, ba sa tsoron ta yi wani wurin.

Mama ta ce "Ka daina yi musu faɗa, ita ta haɗo kayanta ta ce barin gidan za ta yi"

Mai sunan baba ya yi wa rumaisa wani mugun kallo ya ce "Zaki wuce ki ajiye kayan nan, ko sai na zaneki, idan ki ka bar gidan, wurin uban wa zaki je, mara wayo" sumi-sumi ta shiga ta ajiye kayan a falon mama.

Har dare suna yi mata dariyar abun sa ta yi, wanda hakan ya sake tunzarata.

Mama tana kallon rumaisa ta tada kai da kayanta, ta ƙi yin shimfiɗa ta kwanta, kuma ba ta ci Abincin dare ba.

Mama ta girgiza kai ta ce "Ubangiji Allah ya shiryeki, ya rabaki da wannan rashin ji haka rumaisa, idan auren nan alkhairi ne Allah ya tabattar da shi, ya san silar shiriyarki ne".
Ta gyara mata kwanciyar, ta lulluɓeta.

***
Takawa ya ji zafin maganganun Mahmud sosai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login