Showing 96001 words to 99000 words out of 224014 words
tarko daban-daban".
Mummy ta jinjina kai ta ce "Shikenan, bari mu ga zuwa yaushe, na cigaba da sanya musu ido, duk wani motsinsu uwani na gaya mini, kuma na ce lallai ta kawo mini maganin da waccan 'yar tsintuwar ke shafa masa".
"To shikenan, to bari mu ga yadda abubuwa zasu kaya".
***
Har azahar babu wanda ya kula su ruma, masu kuka na yi masu addu'a na yi, ga yunwa ta addabeta a gida wataran ƙarfe bakwai ta karya, amma har bayan azahar babu wanda ya kulasu balle ya basu wani abu.
Tashi ruma ta yi ta samu ɗaya daga cikin 'yan bindigar ta ce "Bawan Allah yunwa nake ji, ku bani abinci na ci"
Wani mugun kallo ya yi wa ruma ya ce "Zo ki cinyeni, an gaya miki nan wurin hutu ne da jin daɗi?".
"Ai ni ba mayya bace da zan cinyeka, idan ma cin ne ban ga abin ci a nan ba, idan ba za a bamu abinci ba meyasa zaku kawo mu nan?" Ta na rufe baki yana hankaɗeta sai dai faɗi ƙasa ya saita ta da bindiga "Idan ki ka yi mini hauka, yanzu na lahira zasu yi maraba da ke".
Ruma ta kalli yadda ta faɗi ƙasa, wata irin zuciya ta harziƙota ta miƙe tsaye ta sake kallonsa ta ce "Na faɗa a bani abinci yunwa nake ji, ai daɗinta idan ka kasheni ba a wuta zaka sakani ko aljanna ba, hisabi na Allah ne, to na faɗa a bani abinci yunwa nake ji, harbeni maza kai kuma a ƙara maka kwanakinka a duniya"
Babu alamar tsoro ko shakka a tare da ruma, kowa sai da ya Zubo mata ido, saboda ƙarfin halinta.
A fusace ya tashi yayi kan ruma, amma wani ya riƙe shi, ya ce kar ka kuskura, ƙyaleta idan ka yi mata wani abun za'a iya samun matsala, ka bari oga ya zo ya faɗi ya za ayi".
Huci ya din ga yi yaso ya tattaka ruma, ko ya keta mata haddi a gaban mutanen wurin, ya kawo ƙarshen harshenta.
"Ni baka kyauta mini ba da baka bari ya kasheni na huta ba"
"Wato ke dai bakinki ba zai mutu ba ko?"
"Idan har so ku ke na yi shiru, to ku kasheni ko ku mayar da ni gidanmu, wannan ai zalunci ne ni yunwa nake ji" tayi maganar tana share hawaye.
Dattijon nan ne dai na jiya ya ce "Yarinya ki yi shiru da bakinki, kar su citar da ke, wannan mutanen ba ayi musu haka".
"To ni yunwa nake ji" tayi maganar har cikin zuciyarta.
Duk wani kurari da zare ido ruma taƙi yin shiru, kamar ma da gayya take yi dan ta tunzurasu su yi mata abin da za su yi mata.
***
Har dare mama ba ta san abin da ya faru ba, kuma an rasa wanda zai gaya mata, sai mita take musu cewar ita fa ta kasa haƙuri ta kira gwaggo idan an dawo da ruma ta haɗata da ita, amma wayar gwaggon ba ta shiga. Sun yi mamaki da duk jin rediyon mama ba ta ji batun kai harin ba.
Ganin tana ta surutu ita kaɗai ba wanda ya tanka mata, ya sanya ta magantu "Wai ba zaku gaya mini meke faruwa ba ne? Duk cikinku fa yau babu wanda ya ci abinci, kun ƙi walwala kun ƙi magana, kuma kun ƙi gaya mini menene?"
Usman ne ya tashi ya ce "Mama sai da safe, ni dai bana jin daɗi ne".
Babu wanda ya bawa mama amsa, a hankali duk suka watse daga tsakar gidan, mama ta sha jinin jikinta ta fara tunanin menene ya faru haka, da basa son gaya mata?.
Babu wanda ya saurari su ruma sai bayan la'asar, aka zo da wasu kuloli a kan babur, aka rarraba musu wata busashshiyar gurasa, gaya guda ɗai-ɗai, sai pure water ɗaya tamkar mabarata.
Ruma ta kalli gurasar nan, duk uwar yunwar da take ji, amma a rasa me za a bata sai wannan takurarriyar abar a bushe, babu mai babu komai a jiki.
Gashi duk ta bushe kamar ƙanzo.
Ruma ta gasta ta fara ƙoƙarin haɗiya, amma ta kasa haɗiyewa, da ƙyar ta dannata da ruwa, daga gutsura ɗayar nan ba ta ƙara ba ta shanye ruwanta ta yar da ledar, sauran kuwa tuni kowa ya kama gurasar nan suka cinye.
***
Duk wata tattaunawa su Usman da sauran 'yan uwansa sun yi, amma sun rasa ta ina zasu ɓullowa lamarin, duk in da zasu buga sun yi, amma babu wani labari game da in da su ruma suke, gashi da wani ya ce zai je katsinan mama za ta gano akwai abin da yake faruwa, dan a yanzu haka ma duk ta tsargu, mussaman yadda suka daina walwala ga kuma ta fara shiga damuwa rashin shigar wayar gwaggo.
Su huzaifa ma sun gano abin da yake faruwa, sai dai yanayin ruɗewa da Huzaifa da Yasir suka yi, ya sanya mama cigaba da jefa musu zargi da kuma kokwanto.
Yau ƙarfe tara na safe taga duk sun fito daga ɗakinsu sun jeru a tsakar gida, kamae kullum babu wanda yake walwala a cikinsu, kuma babu mai sunan Baba a cikinsu.
Mama ta girgiza kai ta ce "Koma menene Allah yayi muku maganinss, tunda ni dai ina tsakaninku ba zaku gaya mini ba".
Ta fito daga banɗaki kenan, Abubakar yayi sallama ya shigo da jakarsa ta makaranta, sai dai kallo ɗaya tayi masa shima ta ga tsananin tashin hankali a fuskarsa.
Mama tayi saroro tana kallonsa, cikin ƙarfin hali ta ce masa "Kai kuma me ya dawo da kai yanzu?"
Suka haɗa ido da Aliyu, Aliyu ya sunkuyar da kai, Yasir kuma ya hau goge hawaye.
"Saddiƙu, dan Allah kai ka gaya mini menene? Ku daina ɓoye mini koma menene, na kasa nutsuwa sun ƙi su gaya mini abin da yake faruwa, na rasa gane kansu, dama har akwai abin da ban cancanci in sani ba?"
Abubakar ya ajiye jakarsa ya kamo hannun mama ya ce "Mu je ɗaki mama sai mu yi magana"
Mama ta buge hannunsa ta ce "Ba in da zani, ku yi ta riƙe abin ku a cikinku nima bana son ji, idan abin da bana ƙauna a rayuwata bai wuce ganin fuskokin da ba sa son damuwata in gansu cikin damuwa ba, ko ba zan maganta muku ba ai na yi addu'a" ta juya za ta wuce ɗakinta.
"Mama ruma ce" ya furta a hankali, cak mama ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya, ta ji maganar ta sa kamar bai faɗeta dai-dai ba.
Ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Mutuwa ta yi?"
"An yi garkuwa da ita, a garin su Iya, a cikin harin da aka kai ƙauyen har da ita aka ɗauka".
Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mama za ta iya cewa ko mutuwar iyayenta ba ta girgizata kamar wannan abu da ta ji yanzu ba, ji ta yi kamar ba a hayyacinta ta ji maganar ba, tamkar an mata yayyafin wuta, Rumaisa a hannun 'yan biniga, gara ace kashe mata ita suka yi, ta tura a ɗauko mata gawarta, amma ruma 'ya mace ƙarama a hannunsu a tsakiyar dajin Allah, Allah kaɗai ya san me za su yi mata, ga halin ruma da ta sani na rashin kunya da surutun tsiya, tsaf za su illata ta.
Jikin mama ne ya hau rawa, ta sake ƙare musu kallo, Huzaifa da Yasir suna ta kuka, Aliyu kuma ya sunkuyar da kai, haka Abdallah, Usmsn kuwa barin tsakar gidan ya yi, babu mai sunan Baba ko ba a gaya mata ba ya tafi katsinan ne.
Ta yinƙura da niyyar ɗaga ƙafarta, ta tafi luuu gaba ɗaya suka yi kanta suna kiran sunanta
Ayshercool
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Sosai suke girgiza mama, amma ko motsi ba ta yi, a gigice Abdallah ya ɗebo ruwa ya din ga shafa mata a fuskarta Usman ya ɗauko mafici yana yi mata fifita.
Aliyu ya kalli Usman ya c "Usman wani ya je ya samo napep mu kaita asibiti da sauri".
Usman ya ce "Ko nan da zaure ba zan iya fita gani nake komai zai iya faruwa kan na dawo, sai dai ko su Yasir".
Yasir da yake riƙe da hannun mama ya ƙara ƙanƙame hannun, ya ƙi tashi yana kuka.
A hankali mama ta yi tari, ta fara motsawa tana Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Babban fatanta Allah ya sa idan ta buɗe idanunta ace mata mafarki take yi.
Sai dai tana buɗe ido ta kalli fuskokin su Huzaifa, hakan ya tabbatar mata a zahiri ne, ruma an yi garkuwa da ita.
Sannu suka din ga jerwa mama, amma ta kasa amsa musu, a hankali ta ce "Ku kira babana, dan Allah ya juyo gida kar ya je, mu bar wa Allah komai".
"Amma mama meyasa?"
"Kar yaje ya tayar musu da hankali ko shi ma wani abun ya same shi, zuwan nasa babu abin da zai ƙara ku kira mini shi a waya, ya dawo gida dan Allah".
Jiki a sanyaye Abubakar ya janyo wayarsa a aljihunsa ya kira lambar Umar.
Mai sunan Baba na ɗagawa Abubakar ya ce "Akhi mama ta ce ka dawo gida, bata yarda ka je ba?"
A hasale Umar ya ce "A kan me zaku gaya mata, kun san ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba dan me za a gaya mata? Wannan ai ba yi ba ne, idan wani abu ya sameta fa?"
Shima Abubakar da zuciyarsa ke a kusa ya hayayyƙo masa "Kai saurara ni ka ke wa shouting? Da wanne zan ji ne? Har zuwa yaushe zamu cigaba da ɓoye mata. zamu dawo mata da rumaisa ne idan bamu gaya mata ba? zaka din ga yi mini hayaniya kai kaɗai kake cikin damuwar ne? Duk ta shiga damuwa ba mai cin abinci kowa baya walwala kuma an ƙi sanar mata abin da ke faruwa, zuwa yaushe za a cigaba da ɓoye mata, idan ka ga dama ka dawo idan ba ka ga dama ka je ka yi abin da ka ga dama"
Umar yayi wa ɗan uwansa uzuri, damuwa ce ta sanya ya sauke masa, dan Sadik ba dai haƙuri ba. Suna gama wayar Abubakar yayi cilli da wayar zai tashi mama ta riƙe shi.
Cikin tawakalli da ƙarfin hali ta ce "Yi haƙuri, kar ka yi fushi dan Allah, ka lallaɓo mini shi ya dawo ka san halinsa"
Abubakar yayi ajiyar zuciya zai yi magana wayar mama ta fara ringing a ɗaki, Yasir ya je ya ɗauko, mai sunan Baba ne yake kira.
Mama ta karɓa da sauri ta kara a kunnenta ta ce "Babana dan Allah ka dawo gida" tayi maganar muryarta na rawa.
"Ki yi haƙuri mama, daga sallar asuba na wuce, ina Katsina yanzu haka na kusa ƙarasawa ki yi haƙuri ba abin da za zan aikata, zan je wurin jami'an tsaro ne, ki kwantar da hankalinki in sha Allah za ta dawo lafiya ".
"To" kawai mama ta ce ta saki wayar, tana wata irin ajiyar zuciya, zuciyarta sai wani irin zafi take yi mata, amma idonta ya bushe babu hawaye.
Su ruma kuwa yau kwana na huɗu kenan suna hannun 'yan bindiga, ba wanka ba wanki, ga azabar yunwa ruma ba ta iya cin abin da ake bata, ruwan nan ɗaya idan an basu da shi take sha idan tana jin fitsari ta yi. Duk azabar kashi irin na ruma, ta matse abin ta ba ta yi.
Tun da ruma take ba ta taɓa kawo tsintar kanta a irin wannan halin ba.
Ga duka da wasu lokutan ake yi wa wasu, duk da ita babu wanda ya taɓa dukanta, amma ana dukan wasu ciki har da mata, 'yan bindiga su dake su su taka su da ƙafa.
Wani tarihi ruma ta tuna da aka taɓa basu a islamiyya, a rayuwarta tana son malaman da suke basu tarihi, dan duk abin da take zata nutsu ta saurara.
Akwai ranar da malamin yayi musu tarihin Annabi yunus da kifi ya haɗiye shi, ya karanta *La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*
Har ruma ta ce "Kai malam amma kifin da ya haɗiye annabi yunus, dai yayi girman duniyar nan?"
Malamin ya yi murmushi ya ce "Meyasa ki ka ce haka? Kin san girman duniya kuwa?"
"To ai malam kifin da inuwa mai kifi yake sayarwa, da wanda ake talla ko ɗan tsako ba zasu iya haɗiya ba, amma na ji ka ce kifi ya haɗiye mutum"
"Kifi ne dai babba ruma, amma ba kamar girman duniya ba, kuma ba a gaya mana girman kifin ba a Alqur'ani, abin da nake son ki riƙe yanzu shi ne, falalar wannan addu'a da annabi yunus Alaihissalam ya karanta, a duk lokacin da kika shiga wani mawuyacin hali, ko ki ka shiga hannun wasu azzalumai to kema ki karanta Addu'ar da Annabi yunus Alaihissalam ya karanta *La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*"
"To malam, in Allah ya yarda zan din ga yi, to wace addu'a zan yi idan na yi wa mama laifi kar ta yi mini faɗa ko ta saka mai sunan Baba ya sakani kama kunne?" Jik tambayar da ta yi, ya sanya 'yan ajin suka kwashe da dariya.
"A'a ai dole idan ki ka yi laifi ayi miki faɗa ko a hukunta ki, amma a duk lokacin da kike fargabar haɗuwa da wani, mugu ko maƙiyi sai ki karanta *Allahumma inni as'aluka min nuhurihim, wa'auzubika min shuriruhim*"
Ko da ruma ta tuna da wannan tarihin da malaminsu ya yi musu sai ta fara nanata "*La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*"
Ihun wata mata ne ya sanya ruma waiwayawa taga ko dukan na ta ake, amma taga ɗaya daga cikin mutanen yana jan ta tana ihu, tana a taimaka mata. Babu wanda ya tanka mata mutumin yayi cikin dajin da ita.
Ɗaya daga cikin 'yan bindigar ya ce "Ai gara hakan, tun da 'yar matsiyata ce ba za su biyan kuɗin da aka ce su karɓeta ba".
Kusan awa biyu mutumin ya dawo ba tare da ita ba.
Ta ji wasu a kusa da ita suna magana ƙasa-ƙasa "Innalillahi, ita ma sun mata fyaɗe sun kasheta" Ruma ji tayi kamar ta tambayesu meye fyaɗe, tunowa tayi lokacin da take tambayar mama meye fyaɗe su Aliyu suka din ga hantararta.
A take ta fashe da kuka, saboda yadda take kewar gida, duk suka juyo suka kalleta.
"Ke meye haka?"
"Mama" ta faɗa cikin kuka.
"Yi mana shiru ko in taka ruwan cikinki"
"Wallahi ba zan yi shiru ba, wayyo Allah mama yaya Aliyu yaya usy dan Allah ku zo ku ɗaukeni zan mutu, wayyo Allahna" kuka take sosai kamar wadda wani iftila'in ya afkawa.
Wata mata ce ta din ga rarrashin ruma tana bata haƙuri da ƙyar ta yi shiru, ta cigaba da nanata addu'ar nan.
Mai sunan Baba kuwa yadda yaje ya tarar da gwaggo ne ya sanya jikinsa yin sanyi, ya tarar iya ma tana asibitin ita da mijinta, gwaggo sai kuka take ba ta ko cin abinci, likitoci na ta fama jininta ya sauka abu ya gagara, saboda yadda ta addabi kanta.
Tana ganin mai sunan Baba ta sake rushewa da kuka, "Dan girman Allah ku yi haƙuri, ku yafe mini umaru ban zaci abin zai kasance a haka ba, tsananin ƙaunar da nake yi wa ɗan uwana ce na mayar kanku, ban yi hakan dan baƙanta muku ba, son da nake wa ruma ya sanya na hanata, da na san haka za ta faru da ba zan ce ma azo da ita ba, ku yafe mini dan Allah" gaba ɗaya suka fashe da kuka, har su iya da su Lawisa da aka sace ruma a gabansu.
Ganin yadda dattijuwar ke cikin tashin hankali ita da iyalanta ya sanya ya ji duk jikinsa yayi sanyi, idan ya ce zai ɗaga musu hankali bai yi musu adalci ba, tun da suma ba da son ransu hakan ya faru ba.
Ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon gwaggo sannan ya ce "Ki daina kuka, ko dan saboda a samu jininki ya sauka, yanzu ya ake ciki an sanar da jami'an tsaro ne ko kuwa ya ake ciki?"
Dagaci ya ce "Ka san garin namu, jami'an tsaro ba su fiye bamu agaji ba, mu da su mutanen muke yin sulhu, duk abin da muka saka jami'an tsaro wata ɓarnar suke yi mana, amma dai saboda ita rumaisan mun sanar da jami'an tsaro, amma sun ce mu jira abin da 'yan bindigar suka ce sai a sanar musu, muna nan muna jira haryanzu dai ba su yi mana aike ba".
Mai sunan Baba yayi shiru ya ma rasa abin da zai ce, ƙarshe ya yanke shawarar a kai shi wurin 'yan sandan domin ya ji meye abin yi.
Ɗanlami ya ɗauki mai sunan Baba suka tafi, sai dai daga ƙauyen da aka sace su ruma zuwa wurin 'yan sandan uwar tafiya ce mai zaman kanta, da ko menene zai samu 'yan garin ba lallai su samu ɗaukin jami'an tsaro.
Ganin girma da kwarjini da kuma ganin cewa Umar ba ɗan garin bame ya sanya DPO garin tsayawa ya saurare shi.
"To ɗan uwa idan zan baka shawara ka koma gida kawai ku yi addu'a, bin bayan mutanen nan aikin sojoji ne bana 'yan sanda ba, mu mun yi iya namu ƙoƙarin, sai dai mun bar sallahun idan sun yi wata magana a sanar mana, haryanzu dai ba su ce komai ba"
Shiru kawai mai sunan Baba yayi, ba zaka ƙara sanin lamarin tsaron ƙasarmu ya taɓarɓare ba sai wani iftila'i ya afka maka.
Ba tare da samo wata mafita ba, mai sunan Baba ya kamo hanyar kano.
Gidansu ruma kuwa tamkar an yi mutuwa, ko magana mai sauti ba sa iya yi, tun da mama ta ɗan samu ƙwarin jikinta ta hau sallaya, canza alwala ce kawai take ɗagata, yunwa kuwa ko jinta ba ta yi.
Ba yadda ba su yi da mama ba a kan ta ci abinci, ta ce su ƙyaleta kawai.
Ko da ta ji sallamar mai sunan Baba, ji ta yi kamar zai ce mata ga ruma nan ya dawo mata da ita, amma ko da ya shiga ɗakinta ta kalleshi ta ganshi shikaɗai, sai ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta ji zuciyarta ne neman karyewa.
Ya ƙarasa gaban mama ya zauna, su Abdallah duk suka zubo masa ido, amma ya rasa ta ina zai fara yi musu bayani.
Mama ta sake ɗaga kai ta kalli ta mai sunan Baba, ya girgiza mata kai ya ce "A dage a cigaba da Addu'a