Showing 90001 words to 93000 words out of 224014 words
ce cinnaka, guda biyar kawai zan ɗauka gasawa zan yi na ci"
Zaliha ta ce "Dan Allah ki fito kar su ganki".
"Wai suwaye ne? In sun ganni ba ruwanku ni kaɗai na ɗauka" ta zuba masarar a mayafinta ta fito. Kamar suna tsoron ruma suka sake rufa mata baya suna zazzare ido.
Sun yi tafiya mai nisa sun kusa gida, suka ji ana musu magana "Ke daga ina ku ke?" Gaba ɗaya suka tsaya suka waiwaya, wani dogon mutum ne a tsaye, sanye da rawani hannunsa saye a cikin tsummar rigarsa, ya ma dai fi kama da mahaukaci.
Ruma ta ƙare masa kallo za ta yi gaba abinta.
"Ke ina magana zaki tafi?" Ya daka mata tsawa.
Cikin tsiwa da rainin hankali ruma ta ce "Haba babana ke fa ka ce mana, kuma na ga dai ba aikenmu ka yi..."
Da sauri zaliha ta riƙe hannun ruma ta ce wa mutumin "Dan Allah ka yi haƙuri, baƙuwa ce ne a garin".
"Baƙuwa amma mara tarbiyya ko? Ba ta san nan ina ne ba? Kuma ba ta iya ladabin yin magana da manya ba, Meye wannan ta riƙo?"
Ruma ta ja da baya ta ce "Nifa ban gane ba, me na yi maka zaka ce mini mara tarbiyya? Mangwaro ne da masara" tayi maganar tana buɗe masa mayafin.
"Waye ya baki izinin ɗaukar masarar?"
Ruma da haushi ya fara kamata ta dake ta ce "Yi haƙuri ban san gonarka bace, idan yayana ya zo ɗaukata daga birni zai baka kuɗin masararka, ni na tafi sai kun taho" ta ɗau kayanta tayi gaba.
Su kuwa jiki na rawa suka tsaya suna sauraren mutumin.
"Lallai dagaci, wato har da kawo baƙi marasa ɗa'a ba tare da ya nemi izini ba, har su zo su karya mana doka, to zai gane kuskurensa da mu yake zancen, ku wuce ku tafi".
Da gudu suka tafi gida domin sanar da abin da yake faruwa.
Suka tarar da iya na tuhumar ruma ina ta samo wannan kayan, amma tayi shiru ta ƙi magana.
Su zaliha ne suka kwashe komai suka gaya wa iya.
"Mun shiga uku ruma, ai mu garin nan ba a mana haka, a zaune muke ƙarƙashin umarnin 'yan bindiga, suke da garin, ki daina haka ba ruwanki da kowa, duk wanda ki ka gani a garin nan girmamashi to ba ruwansu da ke, amma idan ki ka yi musu rashin kunya sai su yi miki illa".
"To ku mayar da ni gidanmu mana, ni ba wanda ya isa yayi mini wani abu, dan ni ƙanwar maza ce zane mutum yayyena za su yi. Kawai sai ya ce mini mara tarbiyya shi tarbiyyar ce ta saka yake yi wa mutane magana a haka, ni a kano kowa ya san ina girmama mutane raini ne ban so, ni na zata ma mahaukaci ne".
Iya ta kwantar da murya ta ce "To na ji, amma dai dan Allah ki kula, bari Alhaji ya shigo zai je ya basu haƙuri, 'yan bindiga ne sai su illataki, muma bin umarninsu ne ya sanya muke zaune lafiya"
Ruma ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Wai iya su waye 'yan bindigar nan?"
"'yan tayar da ƙayar baya ne, Allah ne kawai ya san meye aƙidarsu"
Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Meye ƙayar baya kuma, sai ka ce wasu kifaye?"
"Ba zaki gane ba ko na yi miki bayani, amma dai bisa umarnin su muke zaune, sai abin da suka ce muke yi"
"To suma shugabanni ne zaɓarsu ake yi, na ji kin ce ba kwa komai sai da izininsu, ko 'yan sanda ne su?"
"Babu ɗaya ruma, kawai dai ku yi ta mana addu'a, muna zaune ne dan kawai mun san ko mun bar nan ba in da zamu je, bamu da wurin zuwa"
Ƙwaƙwalwa ruma ta shiga wani tunanin na daban, ba ta kuma cewa komai ba, ta shiga wata sabgar.
Tana missing ɗin gida sosai, ga wayarta ta mutu ba caji tama barota cikin kaya a gidan gwaggo.
Kullum da safe cikin bata rubutu da banka mata hayaƙi ake a gidan, wai maganin tsarin jiki na baki maita da aljanu.
Ruma kuwa ta ce ita ba zata sha wani rubutu ba, warin tawadar nan amai zai sakata. A kwanaki biyu kacal ruma ta fara buwayarsu, saboda sai ƙoƙari take sai ta aikata wani abu da zata tsokano mutanen nan.
Yau da yamma kasuwar ƙauyen take ci, dan haka suka shirya su uku zasu tafi kasuwa, iya tayi ta jawa ruma kunne a kan rashin ji da kuma yi wa mutane tsiwa, sannan ta basu kuɗi suka fita suka tafi.
Kasuwar ƙauye ce dai, amma ta burge ruma sosai da sosai, ga kayan gargajiya nan kala-kala.
Sai dai abin da ya bata mamaki, yadda ta kan ga wasu mutane masu rufaffiyar fuska suna kaiwa suna komowa, hannayensu saye a cikin rigunan su.
Shagon wani mai awo suka shiga suka zauna, za su sai wake, da alama su lawisa sun san shi, sai hira suke. Suna cikin hirar wani mutum yayi sallama suka amsa masa, ya shigo ya zauna, bai ce musu komai ba, suma kuma ba wanda ya tanka masa.
Ruma ta ce "Ni fa hausar nan taku dariya take bani".
Mai awo ya ce "to hausar mu tafi daɗi ai, na ji kamar hausar kanawa ki ke yi ko?"
"Eh mana, ni 'yar kano ce, hausarmu mai daɗi, garinmu ma yafi naku kyau sosai da sosai"
Mai awon ya ce "Ai mu ma dan nan ƙauye ne, amma garinmu yana da daɗi da kyau".
Ruma ta yi dariya ta ce "Ba wani nan, garin naku da baku da iko da komai, wai sai an baku umarni mutum da kayansa, kano kuwa ba haka bane, abu idan naka ne naka ne kawai. Kuma ku ba damar baƙo ya zo sai a din ga tuhuma waye wannan, kano kuwa ba a haka?. Haka wani zanƙalelen mutum kamar mahaukaci ya tsayar da mu yana tambaya wai wacece ni?"
Zaliha ta ɗan daki cinyar ruma tana ƙifta mata ido, amma ruma taƙi shiru.
"Wai me awo suwaye masu yawon nan da rufaffiyar fuska kamar munafukai" a tare suka kalli ruma, sannan suka kalli mutumin nan na zaune.
"Ya naga kuna kallona kamar an ritsa mara gaskiya? Bawan Allah ko kai ka san su?" Ta yi maganar tana kallon mutumin
Ya girgiza kai ya ce "A'a, amma ina ga ko sune masu garin da ake faɗa".
"Wai sune 'yan ta'addan?"
Ya rausayar da kai ya ce "Wataƙila"
Ruma ta ce "Amma kuwa ba su kyauta ba, ba su yi wa kansu adalci ba, su dinga ƙwacewa mutane kaya, nima fa da zamu zo garin nan a kan bindigogi na zo, ina 'yan ta'addan ne a mota ɗaya muka hau da su"
Ya ɗan waro ido ya ce "Haba dai, baki ji tsoro ba?"
Kamar ya kunna ruma, ta gyatta zama ta ce "Ni ban ji tsoro ba, a cikinsu fa wani har kaza ya sai mini, yayi kalar masu kirki, amma ban san meyasa suke kashe mutane ba, kullum a rediyon mama sai an ce sun kashe mutane, abun tausayi, ku yi ta Addu'a kuna musu nasiha, ko zasu daina".
Mutumin yayi murmushi ya ce "To shikenan, kuma kanawa ku tayamu da Addu'a, amma na yi mamaki da ki ka ce a kan bindigogi ki ka zo, kuma ba ki ji tsoro ba"
Ruma ta yi wani irin murmushi ta ce "Baka sanni bane ba, yayyena maza bakwai" ta yi maganar tana nuna masa da yatsunta.
Sannan ta ɗora da cewa "Ni ba komai ne yake bani tsoro ba, na ce musu dan Allah su buɗe mini in gani ko da gaske suke bindiga ce, kai ka ga yawan bindigar? Allah ya kyauta kawai" ta miƙe tsaye ta ce "Bari na je na sayo gyaɗa" tayi waje.
Lawisa ta yi ƙasa da murya ta ce "Zaliha tashi mu gudu kar yarinyar nan ta ja a harbemu a tsakiyar kasuwar nan".
"Ya ya za ayi mu gudu mu barta?".
Mai awo ya ce "Ranka ya daɗe ayi mata haƙuri baƙuwace kuma yarinya ce, ayi haƙuri dan Allah" mutumin bai ce komai ba ya cigaba da danna wata waya mai madannai.
Gaban mai gyaɗa marau ruma ta duƙa, tana saya wani mutum ya wuce tare da bigeta da wani abu, kuma ko waiwayowa bai yi ba yayi gaba abunsa.
Da gudu ta tashi ta bishi "Malam ka bugeni, ba ka ji ba na ce ka bugeni fa"
Ya waiwayo yana kallon ruma.
"Ba ka ji ka buga mini wani abu a bayana, kuma ba ka bani haƙuri ba"
Ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce "Ni ne zan baki haƙurin?"
"Eh mana, wani abu fa ka bugeni da shi a bayana, ai ka waiwayo ka bani haƙuri ko?"
Zai yinƙura kenan ya ji an danƙi hannunsa an ja shi. Wani mutum ne shima mai rufaffiyar fuska ya riƙe shi.
Cikin tsiwa ta ce "Bana yi wa manya Allah ya isa, amma wallahi ban yafe ba, Allah ya haɗaka da wanda yafi ƙarfinka kaima ya ci zalinka"
Idon kowa ya dawo kan ruma, ita kuwa ko a jikinta, ta koma ta sai gyaɗarta da ruwan leda, ta koma shagon mai awo.
Ko da ta koma, ta bi su ta bawa kowa leda ɗaya ta gyɗa, har da wannan mutumin da ya shigo ya zauna.
Ta kalli mutumin ta ce "Ɗan uwanmu kana da 'ya'ya?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
Ta kuma bashi ɗauri biyu ta ce "To ka kai musu wannan, ga ruwa ma na baka. Ku kuma ku tashi mu tafi, 'yan garin nan ba su da mutunci, wani ya bugeni da wani abu a baya, kuma yaƙi bani haƙuri ni kuwa na masa Allah ya isa, kuma wallahi na koma gida sai na je na gaya wa 'yan sanda, abin da ske a garin nan da abin da na gani ana yi! Sai na faɗi komai"
Ayshercool.
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Ba ta ji ko ɗar ba da ta yi maganar, ta ɗau abubuwan da ta saya, mutumin nan ya bi ruma da kallo, har zata fita daga shagon ya ce "Ƙawata yaushe zan zo kano na kawo miki ziyara, in ga Kanon da ake cewa ta fi garinmu kyau?"
Murmushi ta yi ta ce "Idan ka zo kano ka ce wurina ka zo sai yayyena sun naɗa maka na jaki ni ma su karairayani, cewa za su yi kai saurayina ne, amma dai Kano tana da kyau sosai, sai watarana ɗan uwanmu"
Ta yi waje, su lawisa suka bita kamar munafukai.
Jerin babura ne suka din ga shigowa cikin kasuwar ko ta ko ina, suna ɗaukar mutanen nan masu rufaffiyar fuska suna barin cikin kasuwar.
Ruma ta ce "Zaliha wai wannan mutanen idan suka idan su ka bar nan ina suke tafiya a kan bauran nan?"
Jiki a sanyaye zaliha ta ce "Cikin daji suke tafiya, ruma mutumin nan fa na cikin rumfar nan shima fa sune, ɗan uwansu ne" waro ido ruma ta yi ta ce "Haba dai? Amma nake hira da shi?".
"Shiyasa ake ce miki ki iya bakinki, kin zage sai zuba ki ke har da cewa zaki gaya wa 'yan sanda".
"To ba gara a gaya wa 'yan sandan ba, tun da ku tsoronsu ku ke ba za ku iya ba, ai taimakonku zan yi, ke nifa DPO ɗin unguwarmu ma ya sanni, tun da na karya wata yarinya ya sanni, dan haka sai na je na gaya masa".
Lawisa ta ce "Ke waye ya ce miki aikin 'yan sanda ne?, sojoji ma fa ake turowa, amma haryanzu abu ya gagara mu samu tsaro "
Tunawa ta yi da batun da aka yi, na da sanin wasu daga jami'an tsaro ake zirga-zirga da makamai amma ba yadda suka iya.
Ƙarar wani abu ruma ta ji, da bata taɓa jin sauti irinsa ba, sai gani tayi mutane suna gudu, mutumin da yake tafiya a kusa da su ya faɗi cikin jini.
Aka buɗewa mutanen kasuwar wuta. Tuni ta nemi su lawisa ta rasa sun arta, ita kuwa ta kasa gudun, ta kasa gaba ta kasa baya, sai rungume kayan sayayyar ta da tayi tana rarraba ido, mutane sai faɗuwa suke cikin jini.
Ji ta yi an kama hannunta an ja ta da gudu, an bi ta bayan kasuwar da ita, ba ta san ko waye ba, sai da suka bar cikin kasuwar, sannan suka tsaya.
Mutumin da ya zauna a rumfar mai awo ne, sai dai shima a wannan karon fuskarsa a rufe take, da kayansa da kuma muryarsa ta gane shi ya ce mata "Yi sauri ki bar wurin nan, ki tafi gida" daga haka ya juya ya barta.
Ikon Allah ne ya kai ruma gida, dan ba ta taɓa ganin tashin hankali kamar wannan ba, mutane kwance a cikin jini an kashe su.
Ko da ta je gidan babu kowa, ta zube kayan hannunta a tsakar gida ta zauna, ta yi shiru tana cigaba da jiyo ƙarar harbe-harbe sama-sama.
Ta yi kusan mintuna ashirin, sai ga iya da su lawisa sun shigo, da alama ita suka tafi nema.
A gigice iya ta ƙaraso in da ruma take tana faɗin "Rumaisa babu abin da ya sameki ko? Bari gobe in Allah ya kaimu da sassafe azo a mayar da ke, mutanen nan sun sake waiwayo mu, ina fatan babu abin da suka yi miki"
Ta kalli jikinta, ba abin da ya sameta sai dai jini duk ya taɓata. Iya ta saka ruma ta yi wanka ta canza kaya.
Sai dai ruma ta kasa magana, dan ta tsorata da abin da ta gani, gawar mutane kwance a cikin jini.
Da ƙyar ta iya cin abinci, ta nemi wuri ta kwanta, sai dai bacci ya gagari ruma sai tsananin zurfin tunani.
Ruma tana jiyo iya da sauran mutan gidan, suna mayar da zance da irin ɓarnar da aka yi a harin na yau, a nan ta ji irin masifu da tashin hankalin da suka fuskanta a baya, wanda haryanzu suna kai.
Tun da Allah ya sa ruma ta buɗi ido, ba ta taɓa ganin tashin hankali kamar wannan ba.
****
Takawa jiki yayi kyau, ya daina jin abin da yake ji, ya cigaba da sabgoginsa a Abuja, sai dai duk yadda ya so ya gama abin da yake ya dawo kano abu ya gagara.
Tattaunawa ce ta musamman suka yi, ita ma tattaunawar sai dare suka yi ta, sai bayan sha biyun dare sannan suka gama, ya fito zai tafi masaukinsa, dan ko direban bai nema ba yau.
Ya biya wani restaurant ya ci abinci, sannan ya nufi makwanci. Tun safiyar yau yake fama da fargaba da ya rasa dalilinta. Yana tsaka da tuƙi gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa gabansa ya faɗi, ƙirjinsa yayi wani irin bugawa da sai da burki ya kusa ƙwace masa a tsakiyar titi. Da ƙyar yayi parkinh ya kifa kansa a kan sitiyari, ya dafe ƙirjinsa sa hannu ɗaya, yana jin yadda zuciyarsa ke tsananta bugu.
***
Gari yayi tsit kamar an yi ruwa an shanye, duk wannan balahira da ta faru har aka yi aka gama, babu jami'in tsaro ko ɗaya da ya bayyana a wurin, sai da ƙura ta lafa waɗanda aka karkashe wa 'yan uwa, suka je suka ɗebo gawarwaki, aka yi musu sutura ana jiran gari ya waye a sallacesu, wasu gawarwakin ma ba a samu ɗebo su ba saboda tsoro.
Dare ya tsala sosai, farin wata ya haske gari, ko ƙwaƙwƙwaran motsin wani abu ba ka ji, ciki har da ƙwari.
Idanunta tarwai, babu alamar bacci zai ɗauketa ko da kuwa ɓarawo ne. Daga can ƙasa-ƙasa ta fara jiyo jiniyar babura suna kusantowa. Ta runtse idanunta tana hango yadda a abubuwa suka faru ɗazu a kasuwa, sai dai ƙarar baburan suka cigaba da kusantowa yana cika mata kunne.
Hannu ta saka ta toshe kunnuwanta, tare da sake rintse idanuwanta. Dan ƙarar baburan na sake hasko mata abun da ya faru
Ba ta san iya adadin lokacin da ta kwashe a haka ba, ta sauke hannuwanta, iface-iface ta din ga jiyowa ana salatuttuka, hayaniya ta yi yawa a ilahirin kewayen gidan.
Muryar mijin iya ta jiyo yana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mutanen nan sun sake dawowa, mai kuma suke nema da mu? Me suke buƙata?"
Iya ma cikin kuka take salati tana "Allah kana gani, Allah bamu da wani gata sai kai, Allah ka duba mu".
Wani irin ihu da gurnani kunnuwan ruma suka jiyo mata, kai daga jin ihun ka san wadda take yi a cikin masifa take.
Muryar wani magidanci suka ji yana ta magiya "Dan girman Allah ku yi mini rai, 'ya ta dan Allah ku rufa mini asiri"
Ƙarar harbi suka ji, daga nan basu sake jin muryar mutumin ba, sai kuka da ihun yarinyar. Wadda ruma sukan yi wasa tare.
Gaba ɗaya kururuwar mata da hargowar mutanen ta karaɗe ƙauyen, haɗi da harbe-harben bindiga.
Kan iya suyi wani yunƙuri, wasu irin zaratan maza su kusan huɗu sun afko cikin gidan.
Mijin iya ya tsaya ƙyam, babu tsoro a tare da shi ya ce 'Haka muka yi da ku? Kun saɓa alƙawari mun yi duk abin da kuke so, amma bamu tsira ba, so kuke lallai sai mun fita mun bar muku garin, idan mun fita ina kuke son mu je?"
Cikin tsawa wani ya ce "Ba tuna mana alƙawari muka zo ka yi ba, aiki muka fito yi, kai ku kama shi ku ɗaure mana shi" aikuwa suka kama dattijon suka yi masa ɗaurin huhun goro, suka rufe masa baki, sannan suka afko cikin ɗakin.
Lawisa da zaliha sai kyarma suke yi, ruma kuwa tayi zuruu da ido, tana ganin sarautar Allah, abin da take ji a radion mama yau gashi a zahiri ba labari ba.
Hargitse kayan ɗakin suka shiga yi, wasu kuma suka zaga suka kwance garken dabbobin da ake kiwo a gidan, suka yi waje da su.
Ɗaya daga cikin su, ya zo ya danƙi ruma ya fara janta.
Cikin kururuwa iya take faɗin "Ka yi wa Allah da ma'aikinsa ka ƙyale yarinyar nan, baƙuwace 'yar amana ce, dan Allah karku cutar da ita".
"Kai wuce da ita" ɗayan yayi umarni cikin tsawa. Iya ta yinƙura zata yi magana, ɗayan ya saka bakin bindiga ya buga mata a ka ta zube a ƙasa sumammiya.
Ruma ta zura silifas ɗin ta, ɗayan yayi waje da ita yana janta. Ko da suka fita ko waiwayowa ba sa yi, su Zaliha sai kuka suke suna kiran ruma, amma suka ce idan suka kuma magana sai sun harbesu.
Ko da suka fita tuni duk sun tattara waɗanda zasu tafi da su, a