Showing 42001 words to 45000 words out of 224014 words

Chapter 15 - Kanwar Maza 1&2 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1079

nan wuri muna da baƙi"

Ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce "Wai su waye suka zo, na ga ƙofar gidanku ma da mutane"

"Ban sani ba, ba zaki wuce ba sai na zane ki?"

"Dan Allah ɗan uwanmu mangwaro zaka san mini, ka ga dai yau ba sata na yi ba ko?"

Dariya ya kwashe da ita ya ce "A ina na zama ɗan uwanku?"

"Ai kai ɗan uwanmu ne na Musulunci"

Girgiza kai ya yi, zai wuce ta ya shiga cikin lambun, amma ta biyo shi.

"Wai ke baki da hankali ne, na ce miki muna da manyan baƙi masu wurin ne suka zo"

Cikin ko in kula ta ce "To ni ina ruwana, koma suwaye ai mutane ne ba mala'iku ba, dan Allah in biyoka ka san mini, ni sai na je na tambayo mai unguwa ma, na san shi zai ce ka bani"

Ya ƙarewa ruma kallo tsaf, a rashin hankalinta, tsaf za ta aikata abin da ta faɗa, na zuwa tambayo mahaifinsa, gashi yana tare da baƙi, ya dubeta ya ce "Yanzu abin da za ayi, ki zauna ki jirani, bari baƙin su tafi sai na baki"

"To, bari na je na zauna, kuma idan baka fito ba, biyoka zan yi"

"Wallahi ki ka shigo, zane miki jikinki za su yi"

"Su waye wai?" Ta yi maganar tana sake leƙa lambun.

"Kin ga tsaya, bari na je na samo miki" ya ƙarasa maganar tare da shigewa cikin lambun.

Dandamalin wani gida ta samu, ta ajiye jakarta, ta ɗebi duwatsu ta hau 'yar carafke.
Tun 'yar carafken na ɗauke mata hankali, har ta gaji da jiran ɗan gidan mai unguwa. Ta zube duwatsun ta tashi, ta je ƙofar shiga lambun ta tsaya, ta ɗaga murya ta ce "Ka cika alƙawari, zan shigo fa" magana ta fara ji ƙasa-ƙasa na mutane, alamar za a fito, ba ta yi niyyar matsawa daga bakin ƙofar ba, sai da ta hango akuya na shirin watso mata litattafanta, ta ci, ta nufi wurin jakarta, ta ɗau jakar ta na zagin akuyar, har da kiranta mayya mayuwanciya kamar tana magana da mutum.

Tana waiwayo wa, taga mutanen sun fito, sai dai kusan duk sun yi rawani, sai mutum ɗaya da suke takewa baya, shi kuma suit ce ma a jikinsa.

Da gudu ruma ta kwaso, ta tsaya daga baya ta ce "Laaa sarki ne wannan?" Jin 'yar shilar muryarta ya yi, tamkar busar wata 'yar sarewa a kunnensa, duk da akwai dandazon yara da suke wurin, galibi suna zuwa idan har ya zo, saboda ya kan basu kuɗi. Har ya ɗan juyo, zai waiwayo ya ga wacece a cikin yaran, bai juyo gaba ɗaya ba, dogon hancinsa kawai ta iya ganowa, ya ɗauke kansa ya shige motar da aka buɗe masa.

"Sarki ka ganni, ka juyo ka kalleni, ko dai ba sarki bane ba, na ga sarki ba ya saka ƙananan kaya ai"

"Ke! Hattara yarinya 'yar talakawa, ba a yiwa takawa karan tsaye"

Shiru ta ɗan yi ta dube shi ta ce "'yar talakawa kuma, to wallahi gidanmu akwai abinci, mu ba talakawa bane ba, kuma ba gara ni ba ma, Idan mu ka je kallon hawa mandawari, mama ta ce mini masu irin kayanka bayi ne, sayar da su ake yi zamanin baya a karɓi kuɗi"
Kowa waiwayowa ya yi yana kallon ruma, ya yin da dogarin ya zabura ya yo kan ruma, aikuwa ta kwasa da gudu ta tayar da uwar ƙura, shi kuma ya bita yana a tare ta.

Da ƙyar ruma ta kai gida afujajan, ta na ta haki kamar numfashinta zai ɗauke, ta shige ɗakin mama ta ƙule ta na ta sauke numfashi.

Mama ta biyo ta ɗakin ta na faɗin "Ke!ke ruma ke da waye haka? Yanzun ma tsokanar ki ka yo ko? Tun yashe aka tashi 'yan makarantar ku, amma Allah bai nufe ki da shigowa ba sai yanzu ko? Ba zaki fito ba ina yi miki magana?"

Sumi-sumi ta fito, tana waige-waige sannan ta mayar da idonta kan mama.

"Daga ina ki ke?"

Ruma ta ɗan ɓata fuska ta ce "Mama ba ko ina fa"

"Zaki gaya mini ko na bari sai ya shigo?" Cikin kiɗima ruma ta ce "A'a, dan Allah kar ki yi mini haka, wallahi kallon sarki na tsaya, a lambun mai unguwa, shi ne wani bawa ya ce mini 'yar talakawa, shi ne" sai kuma ta yi shiru.

"Shi ne me?"

"Cewa na yi, ai gara ni ba baiwa ba ce, shi fa kayan bayi ne a jikinsa, wanda ki ka gaya mini ɗin nan ranar da muka je cikin gari kallon hawa, shi ne ya biyo ni da gudu"

Tafa hannu mama ta shiga yi tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dama can na aike ki, na ce idan an tashi ki dinga zuwa wani wur?" Ta girgiza kai.

"Saboda tsabar rashin kunya da rashin hankali, ki ka tsaya kina cewa babban mutum bawa, daga yi miki bayani ranar, ke ba zaki taɓa hankali ba ko? Ina ma ya kama ki ya yi miki dukan tsiya, na gaji da halinki ruma, ki na girma ki na sake shiga dawa, gaba ɗaya babu alamar hankali balle nutsuwa a tare da ke. Ki je ki cigaba da abin da Allah ya nufe ki da yi, Allah ya gani na yi iya yi na, ban yi miki irin wannan tarbiyyar ba Allah ya shiryeki"
Ruma ta yi shiru, tana sunkuyar da kai kamar gaske.

A ɓangaren karatu, an samu sassauci daga halin ruma, kullum Usman ya na ba ta ƙwarin gwiwa, a kan kar abin da ya bata tsoro, duk wani abu da wani zai yi, ita ma za ta iya.
A makarantar islamiyya kuwa, tun da malam Habibu ya taɓa hannunta garin karɓar bulala ta daina bin sa, sai dai yau ta zauna a ajinsu, gobe ka ganta a wani ajin, ɗaukar magana kuwa ba ta fasa ba. Dan saboda tsaurin ido, har manyan 'yan matan nan haka take zagewa ta yi musu rashin kunya, ba abin da ya yi mata zafi. Kuma ku san ko yaushe ta na cikinsu, ba ta yawo da sa'aninta.

****
"Allah ya taimake ki Hajjaju Mummy"

Murmushi ta yi cikin isa da izza ta ce "Abin ƙauna, ka yi breakfast ɗin ne?"

"Eh, na yi" ya yi maganar ya na zama a kusa da ita.

Ta saka hannu ta shafi sumar kansa ta ce "Mahmud, ya kamata a rage sumar nan"

Yayi murmushi ya ce "Haba Mummy, wannan sumar yadda ki ka ganta ki bar ta kawai"

"Hmm to ai shikenan, ya shirye shiryen komawa school?"

"Alhamdilillah, ina nan ina yi, very soon zan koma"

Fauziyya ce ta fito falon riƙe kofin shayi, ta kalli Mahmud ta ce "Yaya Mahmud, barka da safiya"

"Yauwwa, ina Ruky, ban ganta ba?"

Ta nemi wuri ta zauna ta ce "Ba ta tash ba, bacci take yi" ya kalli agogon hannunsa ya ce "By this time?"

Mummy ta ce "Ka san ta na karatun dare, dole ta yi bacci da safe"

Ya jinjina kai ya ce "Haka ne".

"Amm Yaya Mahmud, takawa ya dawo fa, yakamata ku haɗu kan ka koma, kun daɗe baku haɗu ba" tsuke fuska ya yi, ya kalli Fauziyya ya ce "Yaushe ki ka fara tsara mini abin da zan yi a rayuwata? Ubana ne shi da lallai sai na ganshi? Na gan shi jiya mana so what?"

Mummy ce ta katse hirar, ganin Mahmud har ya ɗau zafi ta ce "Is ok, ya isa haka, ku dai idan ya shigo ku je ku yi masa sannu da zuwa, bana son ƙananun maganganu irin na gidan nan".



Sannu a hankali yake danna system ɗin da ke gabansa, kamar ya na tausayaa mata, hannunsa ɗaya kuma riƙe da cup ya na shan tea, idan ba ka kalleshi sosai ba, zaka ɗauka Mahmud ne a zaune.
Muryarta ce take dawo masa kunnesa, kamar a yanzu take magana *laa sarki ne wannan? Sarki ka juyo ka kalleni* ya tuna ƙarfin hali da ta dubi ɗaya daga dogarinsa, ta ce masa bawa, koma dai wacece a muryarta ya ji akwai yarinta da kuma tsananin tsaurin ido, idan sarkin ne shi a haka zata yi masa magana kenan, ba girmamawa?
Iman ce ta fito daga sashin Ammi, hakan ya kaste masa tunaninsa, ta ƙaraso falon ta zauna, ta kalle shi ta ce "Barka da hutawa ranka ya daɗe" tun ɗazu Nusaiba take falon, tun da suka gaisa ta ja bakinta ta tsuke, ta kasa ce masa komai, shi ma kuma bai kulata ba, amma Iman na fitowa ya yi murmushi.

"Barkanki dai auta ta Ammi, kin tashi kenan?" Ta jinjina masa kai sannan ta ce "Once again Ya hanya, ya kuma ibada?"
"Alhamdilillah, ya karatun?"

"Ina nan ina ta yi Yaya, ka yi mini Addu'a kuwa da ka je?"

Ya jinjina kai ya ce mata "Sosai, ban yiwa kai na Addu'a da na yi miki ba, na so mu tafi tare da ke, amma na san Ammi ba lallai ta yadda, sai dai ku je umarar azumi ke da ita"

Iman ta yi murmushi ta ce "Nima ina yi maka addu'a sosai yaya, Allah ya kawo abin da Ammi take ta fata"

Nusaiba ta jinjina kai, da wani ne ya tsare Yaya da wannan maganar da ya shiga uku, to wa ma ya ga fuskar hakan, ai sai Iman ɗin.

"Iman, ai kuma zaku iya samarwa Ami abin da take burin, ku fito mana da tsayayyu, a wuce wurin kawai"

Iman ta ɗan rausayar da kai ta ce "Sai dai Anty Nusaiba, amma ni dai kam sai a hankali " tayi maganar jiki a sanyaye.

Alama ya yi mata da hannu da ta zo.
Ta tashi ta tafi in da yake ta zauna, ya matsa kusa da ita, yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Na ji abin da ya faru lokacin ina Saudiyya, abin bai yi mini daɗi ba sam, da Ammi ta yi shawara da ni, ba za ta yanke wannan hukuncin ba, ai Allah ke da rayuwar kowanne bawa. Ki ɗau abin da ya faru a matsayin Mafi alkhairi, Allah ya tanadar miki mafi alkhairi, ni kai na example ne a gareki, dan haka mu cigaba da Addu'a gaba ɗaya" ta jinjina masa kai ta na share hawaye.

*******
Usman ne a zaune ya gama cin abinci, ya kalli Abdallah ya ce "Kai ka san wani hau da wannan Anas ɗin yayi mini yau?"

Abdallah ya ce "Sai ka faɗa"

"Wai ni zai tara ya ce mini ya na son ruma, yarinyar da ko ciwon kan ta ba ta sani ba, ni kuwa na ci ubansa, sai kaɗan na kikkifa masa mari"

Abdallah ya yi dariya ya ce "Ba abokin ka bane ba, na ga filin ball ɗin ku ɗaya ma"

"Dan abokina ne, sai ya ce yana son ƙanwata, mahaukacin ina ne shi?"

"Amma wallahi yaya Usy ba ka kyauta mini ba, 'yan ajinmu na Islamiyya su yi ta labarin saurayi, ni kuma ba ni da saurayi, duk wadda ba ta da saurayi fa wai baƙin jini ne da ita, sai an kai ta wurin malamai sun yi mata Addu'a "

Abdallah ya ce "Saurayin uban wa? Ke ya zaki yi da wani saurayi, ko yake shi Anas ɗin ne ma mara hankali, shi ma irinki ne ai mara kan gado perfect match"

Ɗan saroro ta yi ta ce "Wai Anas ɗin gidan mai taya?"

Abdallah ya ce "Ƙwarai kuwa"

Ta ce "Taɓ, Astagfirullah Allah ba irin wannan ba, kenan addu'a ta ba ta karɓu ba, ina ta Addu'a Allah ya bani saurayi mai kyau, mai kuɗi, mai ƙarfi sosai wanda zai din ga goyani kamar girman brownstrawman na wrestling, kawai sai wani Anas ya ce yana so na, wata uwar ƙeyarsa kamar sirdin keken baban su Ade, gashi siriri da kaɗan ya fi taliya. Ina ga sai na ƙara dagewa da Addu'a ".

Usman ya ce"Ke, kina halitta ne da zaki din ga kushe wasu? Kin ga ki shiga hankalinki, ba ke ce baki da kamun kai ba, dole kowa ma ya ce zai ce yana son ki, kuma wallahi idan ba ki shiga hankalinki ba, sai na bashi ke"

"Allah ya kiyaye, wallahi ba zan aure shi ba, gashi baƙi ƙirin kamar an rina shi".

"Ke zan ci ubanki na kuma jin kina kunshewa wani halitta, ke kyan ne da ke. Ni kullum fatana Allah ya baki miji na gari ko ya fi biri muni" mama ta yi maganar a hasale.

"Mama biri kuma, ba amin ba gaskiya, dan Allah idan irin wannan addu'a ki yi mini ki daina, ni wallahi kyakykyawa na ke so"

"Kyan banza da na wofi, kyan ɗan maciji ki auri kyan ya din ga gasaki ba gara mummuna na gari ba"

Ruma kamar za ta yi kuka ta ce "Ina wani abin arziki a muni"

Mama ta hau ruma da faɗa, ruma ta yi shiru, amma a duk sa'ar da mama ta ce Allah ya bata miji nagari duk muninsa a zuciyarta za ta ce ba Amin ba.

Yau ruma Alla-Alla take gari ya waye, sai murmushi take ita kaɗai.

Yasir ne ya lura da ta na fara'a, dan haka ya ce "Wai ke murmushin me ki ke yi ne haka?"
Ta gyara zama ta ce "Ka san tun da na shiga sakandare, ban yi faɗa da kowa ba, so nake na zama 'yan mata, in din ga tsayawa a cacar baki, to ni cacar baki ba ta biya mini buƙata, na fi son na haɗawa yarinya malaman jikinta, muka yi faɗa da wata yarinya, ka san ni ba na zagi, ta dinga zagina in gaya maka, amma ban yi kuka ba.
Kawai yau na ga babarta ta zo makarantar mu, da ƙyar ta shiga ofishin principal saboda girmanta, ina ga ta yi rabin bangon ɗakin mama.
Kai ina ga fa ta yi yakuzuna na jikin receiver girma, koma ta fishi, shi ya sa nake son Allah ya kaimu gobe, za ta gane ba ta da wayo, ba dai har da cewa babata tsohuwa ba ce, wallahi a jikin allo zan zana babarsu.




Ayshercool
08081012143
[19/07, 8:42 am] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.







14

Buɗe baki Abdallah ya yi ya na kallon ruma, bil haƙƙi take maganar har cikin zuciyarta.

"Ke fa hankali bai wadaci ƙaramar ƙwaƙwalwarki ba, sai ki je allo ki zana babar wasu, idan aka zana taki zaki ji daɗi?"

"Ai ni na yi alƙawarin na daina dambe, ta zageni na kasa ramawa, saboda ashar take yi, ni kuma bana zagi, gaba ɗaya ta cuceni ta ɓata mini rai, ni kuwa ba ta san ba a taɓani a ci bulus ba, wallahi sai ta gane kurenta"

Abdallah ya girgiza kai ya ce "No, ki nemi wata hanyar dai, amma ban da iyaye, ba abin wasa bane"

"Iyaye ba abin wasa bane, ta ce mini mara tarbiyya babata tsohuwa, sai na ci buhun ubanta, ranar ma a sanyi ta sameni, da sai na tayar mata da aljanu na yi mata dukan tsiya, to bana som daga shigata makarantar a tsaneni ne, ayi mini mummunar shaida". Duk yadda Abdallah ya so nusar da ruma, ta yi biris ta ƙi fahimta ta yi alwashin ramuwar gayya a kan abin da aka yi mata.

*****
Nasihar da takawa yake yi mata, a hankali ta ji ta ratsata sosai da sosai, daga ita har shi suna fuskantar jarrabawa daban-daban, wanda hakan yake jefa Ammi cikin damuwa.

Nusaiba ta kalli Takawa da Iman ta ce "Iman 'yar gidan yaya, Ammi ta ki yayan ma naki"
Murmushi iman ta yi tana sake gyara zamanta.

Turo ƙofar falon aka yi, suka ɗaga kai gaba ɗayansu suka kalli ƙofar. Jabir ne ya shigo, da sallama a bakinsa. Suka amsa masa gaba ɗaya, hankalinsa ya na kan Iman ya na ƙare mata kallo. Hakan ya sanya ta haɗe rai tana ɗan kawar da kai gefe.

Yayi murmushi ya kalli Adam ya ce "Ni zaka yiwa haka, ka dawo amma sai dai na ji a gari ko ka neme ni"

Takawa yayi murmushin gefen baki ya ce "Ai idan ka san na dawo, zaka dameni ne ka sani yawo a gari, shi ya sa na yi shiru so nake sai na huta, shi ya sanya ma ban zauna a gidana ba, na yo nan"

Nusaiba ta ce "Uncle J, ina wuni?"

"Lafiya lau Nussy, Iman ba magana ne? 'yar rigima"

Ba dan ta so ba ta ce gaishe shi, gaba ɗaya kwanan nan ba ta son abubuwan da Jabir yake mata, wanda ta kasa gane kan su.

Suna tsaka da hirar sai ga sallamar su Fauziyya da Ruƙayya, tare da Samha suka shigo falon.
Gaban Iman ya faɗi da ta ga Samha, musamman wani irin kallo da take bin ta da shi, da Iman ɗin ta kasa gane wane irin kallo ne.
Jabir suka fara gaisarwa, sannan cikin girmamawa suka gaida Takawa. Cikin halinsa na ko in kula da kuma tsare gida ya amsa musu.

Fauziyya ce ta gyara zama ta ce "Yaya ashe ka dawo, bamu san ka dawo ba, sai ɗazu Mummy ta ce mana, ai ka dawo"

"Eh na dawo" ya faɗa a taƙaice.

"Masha Allah, ya ibada?"

Ya amsa da "Alhamdilillah"

"To Allah ya sa an yi karɓaɓiyya".

Samha ta gyara zama, ta na yiwa Adam wani irin shu'umin kallo, ta ɗan murmusa sannan ta ce "Takawa, ni fa kwance jaka na zo yi, daga zuwa wurin su Fauziyy, na ji suna cewa za su shigo yi maka sannu da zuwa, na ce bari na biyo su in yi sannu da zuwa, kuma a bani tawa tsarabar"
A hankali ya ɗago idonsa, ya kalli Samha, ya ɗan yi murmushi tare da girgiza kai amma bai ce komai ba.

Jabir ya dubi Iman ya ce "Iman, duk kin maƙalƙale mana shi, kamar ke kaɗai ki ka yi kewarsa, ki barmu mu ma mu gana da shi sosai mana" yayi maganar da sigar wasa.

Noƙe kafaɗa ta yi kamar ƙaramar yarinya, sai dai suna haɗa ido da Samha, samhan ta sake yi mata wani mugun kallo, da ya tilasta mata sunkuyar da kai.

"Jama'a ya shirin bikin Jamilu Turaki, Takawa akwai kilisa fa ranar Juma'a"

Adam ya girgiza kai ya ce"Kai, ƙyaleni da wata kilisa, duk na gaji, ni ban so ku ka san na dawo ba ma, ina buƙatar hutu sosai "

"Amma ba dai ka na nufin, ba zaka yi hawan ba, Jamil ɗin guda?"

"Sai na yi tunani tukuna, idan ina da time"

Jabir ya ce"Ba ruwana, kai da shi"

Tsarguwa da rashin sukunin da idanun Samha suka sanya Iman ne ya sanya ta miƙe ta ce "Ni dai sai an jimanku,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login