Showing 87001 words to 90000 words out of 163036 words

Chapter 30 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

459

tsararo Shash.....”
      Bata kai ƙarshe ba ya tareta da faɗin, “To ke da kike jin kin isa ki sake sakawar ki fito ɗin zan tabbatar miki isar tawa kuwa.” ya ƙare magana yana jefa mata hijjab ɗin a saman cinya ya maida hankalinsa ga cire ruwan da ake ƙara masa dan ya ƙare. Mamaki ne, ko takaici, ko tsoro ne ya saka Lulu yin sagade tana kallonsa oho itama bata gama tantancewa ba. Idanunta sunyi masifar kaɗawa ga tarin masifar da take tattarowa na mata kai kawo a ƙirji. Ƙarasa miƙewa tai tana hucin bala'i, hakan yasa hijjabin ya faɗi ƙasa. Shima miƙewar yay duk da baya jin ƙarfin jikinsa, sai kawai ganinsa tai a jikin ƙofa yana saka mata key”.
      “Kai wai mika ɗauki kanka ne?”.
   “Duk yanda zuciyarki ta baki”.
“Mtsoww banda lokacin ka ban hanya na wuce”
       “Idan kinbi abinda nace kenan. Saɓanin hakan na nufin cigaba da zama a ɗakin nan matsayin kinzo ke nan”.
       “Mtsoww kana buƙatar ganin likita. Wlhy kaban hanya kona illataka”.
     “Muyima juna illa dai. Dan wlhy idan kinga kin bar ɗakin nan to kin saka hijjab kuwa. In ko ba haka ba kimayi kiran waya gida tun yanzu a fara tattara miki kayanki a aiko miki”. Ya na gama faɗa ya bar wajen ƙofar yana zira keys ɗin cikin aljihun 3 quarter ɗinsa, sai ma ya shige toilet abinsa. Karo na biyu kenan da take jin an mata wulaƙanci mafi muni, randa ya kaita dawanau da kuma yau. Wai ita illiterate drivern nan nata zai ce ma sai ta saka hijjab sannan ta fita a ɗakinsa. Uncle You duk ya ja mata wannan rainin da tozarcin. In ba haka na velleger ɗin nan ko'a hanya yama isheta kallo ne bare har ya kalla cikin idonta wai ya bata umarni. Lallai dole ne ma wannan drama ɗin ya tsaya a haka. Dan bazata iya wannan auren contract ɗin ba kuwa.....
        Motsin fitowarsa ya katse mata tunani. Ta buɗe idanunta da suka gama kaɗewa da ɓacin rai ta ɗan bisa da kallo. (Ƙaton banza) ta faɗa a zuciyarta tana mai kauda idanun nata da ga kansa. Saman katifarsa ya koma ya zauna, jug ɗin kununsa ya buɗe ya zuba a cup, sai kuma yasa sugar kaɗan da madara ya juya. Jan jikinsa yay baya ya zauna da ƙyau ya fara shan abunsa hankali kwance tare da ɗaukar wayar tasa ya fara sana'ar buga game ɗin ball tamkar ma ya manta da ita ne a ɗakin.
    Fiitt yaji an warce wayar. Sai ya ɗago a ɗan zabure ya kalleta yana wani ɗan buɗe baki. Harara ta watsa masa kai kace Luulu eyes ɗin nata zasu zubo ƙasa ne. Kansa ya shafa yana wani ƙasa-ƙasa da nasa idanun. “Madam ni fa hararar nan tana sani tunanin kamar nayi wani abu, gaskiya in dai ana son a rabu lafiya to a daina, kin san abinka da ba sabin ba tuzuru da mata”. Ya ɗan sake ɗago ido ya kalletan sai kuma ya maidasu ƙasa kamar mai jin kunya.
       Iya matuƙar kunnuwa kam Lulu ta kai maƙurar kunnuwa. (Mi wannan abin yake nufi?) Ta ayyana a zuciyarta, tsaf kuwa ta fahimtar da ita inda ya dosa. Wani irin waro idanu tai da faɗin, “What! Wait! Wait! Wai mi ma kake nufi?!”. Tsabar yanda take jin masifa da ɓacin rai takaicinsa jikinta har wani tsuma yake yi. Ya samu yanda yake so, dan kuwa ta kunnun fiye ma da yanda yake buƙatar. Idanun ya sake ɗagowa ya kalleta cikin son sake kaita maƙura ya ce, “Ni fa Madam ina jin kunya ne, amma idan kince na nuna miki a aikace sai na rufe ido, kema Please ba sai kin kalle ni ba sai ma mu kashe fitil......”
      Wani irin mugun wawura ta kaima filos ɗin saman sofar ɗakin ta shiga jefa masa su ɗaya bayan ɗaya. Hannu ya sa ya dinga kare kansa. Ta ce, “Kai har ka isa ma yin wannan tunanin a kai na, har abada kai gaban abada ma ƙazamin yatsar hanunka ma bai isa zuwa ko kan veil ɗina ba ma illiterate velleger!”.     
      Dariyar da ke neman kufce masa ya keta faman dannewa. Dan muryarta har rawa ya ke na matsanancin takaicinsa, filos ɗin da ta gama loda masa a jiki da jifa ya shiga janyewa yana faɗin, “Ba sai kin ƙirƙiri hanyar maidani asibiti ba. Ni dai ina tsoratar miki ganin aikin jahilin baƙauyen nan a aikace. Dan kin san mu idan muka ɓalle ba'a iya taro mu saboda ƙazamin hannun nan da wahala idan zaiji bari fa. Sannan ki bar fassarani in da banje ba karki lalatama Ammah yaro tun ban tafasa ba ki ƙona ni Aliyu ba inda kike nufin na nufa ba”..........✍️

       



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣9️⃣


__________________

Shin Ko kunada labari Yan zuru Mamar zee zee mai maida tsohohuwa yarinya wadda ta shahara wurin haka kayan mata kamar haka
Kamar hadin amare
Hadin mai jego
Hadin bazarawa d sauransu
Kamarsu
Kaza
Ciccibi
Zuma
Zabo
Yan shila
Gumbuna
Tsimn kankana d rake
Tsimn boom
Tsimin tabaje d saurans

Muna maraba da sayen daya Ko sari sokoto state nation wide delivery 08068526455

___________________

.......Banza ta masa yanzun kam, dan ta tabbata ta cigaba da kulashi ƙarshenta fasa masa kai zatai kawai ya baje a ƙasa ko zata samu sassaucin tuƙuƙin da zuciyarta ke mata. Ta fara takaicin daɗewar Uncle Yousuf. Wayarta ta ɗauka tai kiransa, bugu biyu kuwa ya ɗaga. Muryarta na nuna alamar ɓacin ran da take ciki ta ce, “Papa wai kana ina?”. Ya fahimci ranta a ɓace ya ke, dan haka ya bata amsa da “Gani nan a hanya”.
     “Papa bama ka nan?” ta faɗa a shagwaɓe, batare data jira cewarsa ba ta cigaba da faɗin, “ALLAH idan bakai sauri kazo ba zanma mutumin nan duk abinda zuciyata ke ayyana min na tsanesa”. Ƙitt ta yanke kiran kafin ma Uncle Yousuf ɗin ya samu damar cewa wani abu. Smart dariyarsa ya ke kwasa a zuciya, a zahiri kam ya fuske yana shan kununsa idonsa a tv. Ring ɗin wayarsa ya sashi kallar wayar dan tana a wajenta har yanzun. Itama wayar take kallo a yamutse cikin kuma harara. Sai dai bata da alamar bashi....
      “Ni dai ki daina hararar min waya karta fashe ba kuma kuɗin sayen watace da ni ba gaskiya” yay maganar yana miƙo hannu ya ɗauka. Hararar da take ma wayar ta maida a kansa. Sai kuma tai ƙwafa dan tayi alƙawarin bazata sake tanka masa ba. Amma zai gane kurensa dan sai ta koya masa hankali. Kiran Uncle Yousuf ɗin yay back dan har wayar ta riga ta katse. Yana ɗagawa da ga can ya ce, “Aliyu su sameni waje ba sai na shigo ba anjima zan dawo in sha ALLAH”.
     Cikin girmamawa ya amsa masa da to. Yana ajiye wayar ya dubi hijjab ɗin da ta jafar saman katifar sannan ya kalleta cikin komawa serious. “Kin shirya tafiyar ne ko nace masa ya je kawai ke kin tare?”.
         “ALLAH ya isa tsakani na da kai”. Ta faɗa cikin tare masa numfashi. (Sai dai fa ALLAH ya isar) shima ya faɗa a zuciya. A zahiri kam sai ya ƙara ɗaukar hijjab ɗin ya miƙa mata baice komai ba. Sai da taja kusan minti ɗaya tana zabga masa muguwar harara sannan ta warce hijjab ɗin da ga hannunsa. Dan zuciyarta ta gama bata shawarar kawai ta saka ɗin ta bar ɗakin maganinsa kuma tayi da ga baya. Sannan ko mi Uncle Yousuf zai mata sai dai yayi yau ɗin nan sai an warware wannan auren dan taga raini ya ke son haddasa wa tsakanin ta da drivern ta. Baba kuwa zata fito ta faɗa masa gaskiya idan ta tubure dai ai dole ya barta. Karan farko a rayuwarta da ta saka hijjab bayan sakawar yin salla. Amma da sunan fita waje wai ta suturta jiki abune da bai taɓa faruwa ba koda da ga ɗakin barcinta ne zuwa falo kuwa. Yako mata matuƙar ƙyau duk da iyakarsa gwiwa, ga shi kuma mai hannu. Ƙamshin da yake na turaren wuta da aka turara masa yay matuƙar saka mata nutsuwa. Shima a hankali ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya acan ƙasan maƙoshi yana kallonta ƙasa-ƙasa. Sai dai yayi kamar ba kallon nata yake ba har sai da ta balla masa harara da faɗin, “Malam sai ka buɗe ai ko” cikin jan tsaki ta ƙare maganar.
       Ɗagowa yay da ƙyau ya dubeta. Da ace zata yarda hoto zai mata, amma yasan son yin hakan wani sabon yaƙi ne kuma. Dan haka ya shanye maitarsa ta son yin hoton ya miƙe batare da yace komai ba ya nufi ƙofar. Koda ya buɗe ya bata hanya sai da ta zuba masa hararar nan dai da jan tsaki a kausashe ta ce, “Sai na koya maka hankali wlhy” sannan ta fice. Wani shegen murmushi ya saki da kai hannu ya shafo kansa yana binta da kallo. Sai da ya ga ta ɓacema ganinsa yay ƙaramar dariya da faɗin, “Mu koya ma juna dai ƴar madara” ya ƙarasa fitowa ya bita duk da baya jin ƙarfin jikinsa.

      Tunda ta fito Uncle Yousuf yay wani sagade yana kallonta kamar wata sabuwar halitta. Aiko ta ƙara ƙullewa da haushi. Fuuu ta wuce ta buɗe motar ta shiga batare data tanka masa ba. Hannu ya kai ya tare bakinsa dan dariya ke neman kufce masa. Dai-dai nan Smart ya fito. Jin jina👍 yay masa da hannu yana wani kashe ido ɗaya. Smart yay murmushi kawai da ɗan shafa kai, cikin basarwa ya ce, “Uncle sannu da dawowa”.
         Ƙasa-ƙasa Uncle Yousuf ya ce, “Ya akai ta saka hijjab?”.
      Yanzu kam ƙaramar dariya Smart yayi, sai dai kafin yace wani abu ta katsesu da faɗin, “Papaaa!”. Yanda taja sunan kamar zatayi kuka ya sashi faɗin, “Sorry Baby gani nan zuwa”. Shi dai Smart dariya suke bashi ma. Buɗema Uncle Yousuf ɗin yay yana faɗin, “Deen ya samu Nasreen sai dai anjima na kawoshi ayi haƙuri”.
           Cikin rashin damuwa Uncle Yousuf ya ce, “Oh to bara mu kama hanya. ALLAH ya ƙara lafiya you are the best Son”.
      Murmushi Smart ya sake yi yana ɗan kai dubansa ga Lulu. Ta ɗauke kanta gefe irin ma bata buƙatar kallonsu ɗin nan. Godiya ya ƙarama Uncle Yousuf ya rufe motar yana matsawa gefe har sai da ya ga wucewarsu sannan ya koma cikin gidan yana dariyar ƴar balaja'un tasu. Dan ba yace tasa ba tunda ance masa anma fasa auren.. yana shiga ɗakin da gyalenta ya fara cin karo, da alama zamewa yay ya faɗi sanda take saka hijjab ɗin batare data sani ba itama. Hannu yasa ya ɗauka ya ɗan jujjuyashi, ƙamshi yake na fitar hankali dan Lulu bata san sassautama turare ba, gashi kuma da kusan kala bakwai take amfani. Iska ya ɗan furzar da buɗe drawer ɗinsa ya jefa gyalen sannan ya zo ya kwashe filos ɗin da ya sha jifa ya maida saman kujerar ya koma kan katifar ya kwanta shiru kamar mai barci.......

     ____________★

       “Dama sai da na faɗa muku wannan yaron sam baiyi kama da driver ba amma kuka ƙi yarda. Yanzun ai kun yarda ko?”.
    “Baita relax bafa munƙi yarda bane ba. Kawai dai a munce da kai akwai dai wani a ƙasa nunasa da sukai matsayin wanda zata aura. Kaima fa kasan shekara kusan uku kenan ina bibiyar rayuwar yarinyar nan, na sani ka sani bata tare da kowane namiji. Kuma yaron nan binciken mu ya nuna mana kwata-kwata bai wuce wata ɗaya ma da fara aiki tare da su ba. Kuma ƙaninsa ne ya kawosa ma matsayin driver gidan”.
         “Humm Honorable karka yaudari kanka mana. Ka zauna kayi tunani da hankalinka dan ALLAH. Wata ɗaya da kaisa gidan matsayin driver, amma an ɗauki ƴa an bashi a jiya matsayin mata! Bafa babyn roba bace. Anya bai kamata ka tabbatar da akwai wata a ƙasa ba. Ni da kai duk mun san wanene Jiƙamshi ai bama buƙatar ƙarin bayani”.
      Ido suka zuba masa su duka biyun. Maganganusa na musu kaikawo a zukata da tasiri ɗaya bayan ɗaya. Kamar an tsikari Hon. Misau ya zaburo yana karkaɗa hannu. “Gaskiya fa maganarka abar a duba ce Baita. Ko kun lura ma tsakanin Alh. Sulaiman da yaron akwai magana. Kun dai san waye Sulaiman Garko baya raina abokin gaba. Sannan a labarin da nake samu yanzun nan shima ɗan Sulaiman ma yaje massalacin cikin shirin auren yarinyar amma ya yanke jiki ya faɗin jin an ɗaura da wannan ɗin, shi kuma Sulaiman ɗin baije massalacin ba”.
          “Eh to lallai akwai ƙullaliya a ƙasa”. Cewar Hon. Nakowa. Alh. Baita ne ya bashi amsa da “Babba ma kuwa. Dan tabbas Alh. Sulaiman nada tasa manufar na son yaronsa ya auri yarinyar duk da kuwa ɗiyar ƙanwarsa ce. Kuma shine sanadin auren uwar yarinyar da Isma'il ɗin”.
     “Yess wannan gaskiya ne. Dan sai yanzu kuka dawo da ni cikin hankali na. Wai ya akai ma mu tun kafin yau muka kasa gane yarinyar nan ɗiyar Isma'il Jiƙamshi ce”.
          “Lokaci ne bai yiba kawai sai yanzu”.
    “Amma lokacin nan kam bai mana adalci ba. Sai dai inaga ya kamata muma muyi amfani da wanda ke kaɗawa a yanzun”.
         “Kamar ya?”.
     “Muna buƙatar zuwa duba ɗan Sulaiman asibiti, mu gyara abinda muka ɓata a baya sannan mu sabunta abota”.
     Gaba ɗayansu kai suka shiga kaɗawa da gamsuwar abinda Hon. Nakowan ya faɗa. Dan haka suka miƙe a tare Alh. Baita na faɗin, “Da zafi-zafi akan bugi ƙarfe..”

★★......

    Sai a safiyar yau aka samu dai-daituwar Tajuddeen yanda ya kamata. Faruwar hakan ta kawoma Alh. Sulaiman ƴar nutsuwar dawowar hankali cikin jikinsa. Yana matuƙar so da ƙaunar Tajuddeen. Dan shi kaɗai ne ɗansa tilo namiji. Sauran huɗun duk mata ne. Amaryarsa kuwa Abasiyya bata taɓa haihuwa ba har yanzu shekararsu kusan goma kenan kuma da aure. Dan haka ya ɗauki son duniya ya ɗorama Tajuddeen fiye da kowa a gidan. Gata yake masa na bala'i sai dai kasancewar mahaifiyarsa Hajiya Turai tsaye take kan tarbiyyar ƴaƴanta Tajuddeen ɗin bai lalace ba. A asibitin ya kwana, sai yanzu da Hajiya Turai ta zo dan ita gida ta koma ta kwana. Da ƙyar ta samu ya tafi gida dan yin wanka. Koda yaje gidan wayar da yake amfani da ita a kiran Smart ya lalubo. Yana ƙoƙarin kunnata amaryarsa ta shigo, ƙaramin tsaki yaja yanda bazataji ba yana ajiye wayar. Sannu da zuwa tai masa da tambayar mai jiki. Amsa mata yay a taƙaice da bata umarnin haɗa masa ruwan wanka. Duk yanda yake son kiran shegen yaron nan a ransa dole ya cije har sai da yay wankan ya tsakuri abincin da ta ajiye masa. Yana kammalawa ya ce ta kwashe ta bashi waje yana buƙatar hutawa. Baki ta taɓe da tattare kayan ta wuce, a ranta tana ƙun ƙunin takaicinsa da ga shi har matar tasa. Sai dai kuma ranta fes jin auren da suka so ƙullawa bai ƙullin ba, ta kumayi alƙawarin yin amfani da wannan damar ƙanwarta ta samu cikar burinta ita ma, amma dai zata basu lokaci har Tajuddeen ɗin ya samu lafiya...
         Tana fita ya sakama ƙofar key, bedroom ɗinsa ya shige nan ma ya saka key sannan yay zaman ƙasaita cikin sofar ɗakin da waya a hannu.......✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣0️⃣


........Idanunsa da ke lumshe ya buɗe a hankali ya saukesu akan wayarsa da ke ruri. Har wayar ta kusa tsinkewa yana kallon number da ake kiran nasa da ita, sai kuma yay murmushi yana mai cije gefen lip ɗinsa da ɗaukar wayar ya sa a hansfree tare da maida idanunsa ya lumshe, cikin nutsuwarsa da deep voice ɗin nan ya ce, “Assalamu alaikum. Ina magana da waye?”.
       Alh. Sulaiman da ke huci da ga can ya ji wani irin takaici ya sake maƙure masa maƙoshi. A kausashe ya ce, “Da ubanka ne. Kai har kai ne zan kira ka ce min da waye?”.
           Murmushi Smart ya saki mai bayyana sautin da har ya shiga cikin kunnen Alh. Sulaiman. Babu alamar ɗar a tare da shi ya ce, “Yes kaima uba ne kam. Dan koba komai na auri ɗiyar Sister ɗin ka. Uncle ina yini. Nafa gode da ƙyauta ALLAH ya saka da alkairinsa, insha ALLAH nan da wata tara zakuga tukuycin jika maybe ma sunanka zai ci. Sai dai bazanyi fatan ya gadoka ba, mai asalin sunan nake son ya gada da ƙyawawan halayensa nagartattu....”
       “Yaro baka san wuta ba sai ka taka. Kana tunanin kai har karanka ya kai tsaiko kenan? Da har zan baka aiki ka koma gefe da tunanin cin dunduniyata! Wlhy ba kai ba hatta ahalinka sai sunyi nadamar kasancewarka a cikinsu. Ni Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko sai na maida rayuwarka abar kwatancen da ko faɗar sunanka akai sai an tofar da yawu....”
       

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login